Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masu abin hawa kina musu dariya? Toh bari kiji inkikasa wasa a tafiyan nan wlh sai nace babu inda zaki, sannan sbd tsaban kinrainani wato nabaki awa biyar akanki dawo gda shine kikayi xamanki sbd tsabar kinnrainani ma shine kike ganin kinfi qarfin kid'aga waya ki kirani kice xaki koma gda. Meena tace "wlh ba haka bane nadauka kana gurin aikin kane shiyasa nayi tunanin komawa da kaina, a firgice Hafeez yaqara matse ta da bango wnda gabad'ayansu sunajin numfashin juna, Hafeez yamatso da kanshi daf da fuskar Meena yace" an gaya miki cewa aiki na yafiki muhimmanci ne ko kuwa bakisan cewaa..shiru Hafeez yayi ya kasa qarasa abinda yake son cewa. Sake mata hannu yayi sannan yanuna ta da yatsa yace toh bari kiji ban amince ko da kinyi wannan tafiyan ki ke yawaita hawan motan haya ba ko kice xakisawa mutane gyale, can kuma Hafeez ya kufula yace ke daga yau ma nayi canceln sa gyale a gareki, inkinga kinsa gyale toh daga ke sai nine acikin gdan nan kinajina ko? Da sauri Meena tace ehh! Hafeez ya gyara tsayuwansa ya kalli Meena dakyau sannan yace in kunne yaji jiki yatsara, d'akinshi ya wuce yabar Meena tsaye. Huuhh!! Shine abinda tace kawai tashiga d'akinta A gajiye takwanta bisa gadonta tadafe goshinta, cikin zuciyarta tace "hmmm Yaya kenan dama nakawo haka araina sbd naga take takenka kwana biyun nan sokake ka hanani wannan tafiyan shiyasa kake tsiro da rigima kala kala nikuwa nasan halinka dan haka a ynxu dai baxan biye maka muyi ta rikici ba, balle kasamu galaban hanani yin wannan tafiyan. Kiraye kirayen sallahn la'asar din da akeyine yasa Meena tayi hanzarin tashi tanufi toilet tad'auro alwala. Abangaran Hafeez kuwa wani irin abune yatsaya mishi arai nan yafara jerowa kanshi tambayoyi wai mema yasa nadamu da lamarin wannan yar qauyen ne mema zaisa naji kishinta ohh my god kar fa najawa kaina raini agun wannan bakauyiyar yarinyar (nidai Munay dariya nayi, nace araina babu mai amsa maka wannan tambayoyinaka sai munturo maka JUMAYMA Yar bincike ta bincika mana kai LoL) Hakanan Hafeez yayi ta faman sintiri cikin d'aki shi kad'ai yarasa abunda ke mishi dad'i domin gabad'aya jiyayi bayason abinda zaisa Meena tayi nisa dashi. Tunani barkatai Hafeez yayi tayi har dai shima yajiyo kiran sallahn yatashi yad'auro alwala yanufa masallaci. ** ** Bayan dawowar Hafeez a masallaci haka kawai ya tsinci kansa da son xaman falo, kasancewar Meena nacikin kitchen, shiyasa ya zauna yana kallon dukk wani shiga da ficenta. Haka nan Hafeez yayi xaune har Meena tagama kirginta ta jerasu a dinning table ta wucewarta d'akinta domin ta shirya kayan da zata tafiya dasu gobe. *Washe Gari* Tunda asubar fari Meena ta tashi kmr yadda tasaba tad'aura abin brkfst ta jerawa Hafeez a dinning area, sannan tashiga toilet ta silla wankanta, tana fitowa tashafa versiline sai powdr Meena bata yarda tayi wata doguwar kwalliya ba domin talura a yan kwanakin nan Hafeez na matuqar nuna kishinsa akanta Wanda ita kuma hakan yan burgeta yana kuma bata tsoro, wata atamfarta tad'auko tasa sannan ta sanya hijabi har gwiwa. Travelling bag dinta tajawo ixuwa falo, sannan tanufi sashen Hafeez ta kwan kwasa mishi kofa. Hafeez nacikin d'akinsa yafito a wanka kenan yaji kmr ana buga kofa, jallabiyansa ya jawo yasaka sannan yaje ya bud'e kofan. Meena yagani tsaye cikin shirinta na tafiya ga kuma nan jakar kayanta a gefe, haka kawai Hafeez ya tsinci kansa da fad'uwar gaba. Jiki a sanyaye hafeez yadubi Meena yace "har kinfito? Meena tace eh! Ina kwana Hafeez yace lpy Lou. Mamakine Yakama Meena don yau ko ince ynxu taga wani irin canji atattare da Hafeez komai yakeyi tamkar Wanda bashi da lakka ajiki haka nan ya kama jakar Meena yasa a booth din motarshi. Har gdan Baba Rabi yakaita, Hafeez yashiga sungaisa da Baba Rabin sannan yamusu Allah kiyaye hnya. Bai wani jima ba a gdan yayi sallama da Baba Rabi, Meena har tayi xamanta domin bata da niyyar mishi Rakiya, sai da Baba Rabi ta doka mata harara sannan ta tashi tabi bayansa. Xakujini anjima don jin ci gaban lbrin, ynxu banda caji ne. Tnxs oll😘 ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:06PM, 8/6/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣8⃣ Wurin Motarsa kai tsaye Hafeez yanufa yayin da Meena tarufa masa baya, bud'e motan yayi ya xauna batare da ya rufe ba, hakan ne yabawa Meena dama bud'e daya site din itama tazauna. Wata irin nannauyar ajiyan zuciya Hafeez yayi sannan yamaida dubansa ga Meena yace "idan kukayi tafiyan sai yaushe zaku dawo? Meena wacce ke wasa da gefen hijabinta kai duqe tace naji Amma nacewa sati d'aya xamuyi mudawo, dammm! Gaban Hafeez yafad'i amma sai yayi saurin dakewa yace olryt" shiru sukayi gabad'ansu na d'an wani lkci, can dai Hafeez yace "amm Balkisu takirani ta sanar dani cewa drivan Dr Muh'd ne xaikiku can Gwazan ko? Meena tace eh shine.. Ciro kudi Hafeez yayi sannan yamiqawa Meena yace gashinan susha mai a hanya, kar6a tayi sannan tayi mishi godiya, Hafeez ya maida kallonsa ixuwa wani gefe batare da yakalli Meena ba yace "i hope kinji gargad'in danayi miki cewa banda sa gyale " Meena tace insha allahu zankiyaye hakan. Murmushin jindadi Hafeez yayi yace "vry gud of u"Meena dai batace komai ba. A dan gaggauce Hafeez yace ni xanwuce kada nayi latti Allah tsare hanya, Hafeez sai tsintar knsa yayi dacewa "ki kula da kanki Meena" Insha allahu shine abinda Meena tafad'a sannan tafice a motan, sai da Hafeez ya 6acewa ganinta sannan tashiga gda. Hafeez na isa cikin falo gabad'aya sai yaji dukk gdan yamasa fili babu Meena ba Balkisu, wata irin kewa ce tadinga shigarsa Wanda hakan yasa Hafeez yanufi dinning area yaxauna kawai sai tsintar kansa yayi yanacin abinda Meena ta girka masa Hakanan Hafeez yagama cin ferfesunsa sannan yazuba kunun gyad'a yafara sha yana lumeshi idanu, cikin ransa sai tunani yakeyi haka dama Meena ta iya girki bansani ba Oh my God!! Hafeeez yabud'e cikinsa sosai yakwashi girki. Bayan ya kammalane yanufi d'akinsa domin ya shirya zuwa office. ** ** ** Balkisu da kanta ta tura Habu driva yad'aukisu Meena, hakanan suka kama hanya, cikin ikon Allah sun samu isa garin gwaza lafiya. Yan'uwa da abokan arziqi kowa yayi farin cikin ganin Baba Rabi, haka nan su Baba Rabi sun sami tarbo mai kyau awajan yan'uwansu (kasancewar iyayen Baba Rabi sunjima da rasu, a hannun kawunta ta taso) Khadija yar gdan kawu Usman tun zuwan Meena gdan nan Allah ya had'a jininsu khadija tayi farin ciki sosai da xuwan Meena(kawu Usman shine kawun Baba Rabi) yaransa guda biyar mata hudu daga ciki dukk sunyi aure sai khadija auta. Meena ma tajidadin kasancewa da Khadija sosai, gashi sunkasance sa'anin juna, khadija tabawa Meena wata hud'u shiyasa inkagansu atare tamkar wasu twns, Tun zuwansu gwaza Meena kullum tana tare da khadija tana d'aukan lesson domin kuwa khadija akwai wayo da son gayu shiyasa kullum Meena na tare da ita tana koyan wasu abubuwan. Abangaran Hafeez kuwa fushi yake da Meena wanda ita batasan ma yanayi ba,..fushi yakeyi sbd Meena bata kirashi tasanar dashi sun Isa lafiya ba, sai abakin Balkisu yakeji. Kullum Hafeez wayanshi na kusa dashi yana jiran call daga Meena amma shiru kakeji, da xarar Hafeez ji kira yashigo wayansa da hanzari xai jawota yaduba a tunaninsa Meena ce takira, Hafeez nason kiran Meena a koda yaushe amma girman kai yahanashi aikata komai. *Bayan Sati Daya* Dakyar Hafeez yaga wucewan sati dayan nan domin kuwa jinsu yake tamkar shekara d'aya wani irin farin ciki Hafeez yake ji idan ya tuna cewa Meena yau zata dawo kmr yadda tafad'a mishi, hakanan Hafeez yatsinci kansa da fita waje yana sadaka sbd farinciki. A gajiye Hafeez yakoma gda falo ya kwanta domin yahuta, baifi wucewan minti biyu ba yafarajin bacci na fisgarsa, kmr daga sama yaji wayansa Na ringing da farko har ya share har ta tsinke baid'aga ba sai da aka sake kira a karo na biyu sannan yasa hannunsa ya lalubo wayar d'aukan kiran kawai yayi batare da yaduba sunanan ba. Cikin muryan bacci yace "hello" a bangaran Meena tace Assalamu alaikum, lkci d'aya Hafeez ya fahimci mai mgn firgigit ya miqe ya xauna dasauri Hafeez yace Meena kece? Meena tace eh Yaya nice dama nabugo insanar maka cewa akwai wani biki da zamuyi anan bazan samu damar zuwa yau ba inaso zanqara wani satin sbd in.....kafin Meena taqarasa abinda take son fad'i tuni Hafeez ya katse wayan. Wani irin numfashi Hafeez keyi cike da tashin hnkli sbd tsabar takaici baisan lkcin da yayi wurgi da wayansa ba yace "ohhh no Meena baki Isa ba I cnt tollrt it any more idan baxaki iya dawowa da kanki ba nizanje nadawo dake, tsawan wannan satin dakikayi bakisan halin damuwar dakikabar ni aciki ba, am vry eager to c ur cute face Meena. Hafeez nafad'in haka yanufi d'akinsa da sauri car keys dinsa ya Zara yadawo yadauki wayansa afalo ya fice a gdan. Hafeez na kan hanya yakira Dr Muh'd yace yanaso Dan Allah yabashi aron Habu driva zai rakashi izuwa wani waje, Dr Muh'd yace okay Abokina ba damuwa. Asibitinsu Dr Muh'd Hafeez yanufa yad'auki Habu driva yace dashi yanaso yarakashi garin da yakaisu Meena a yau din nan. Cike da bin umarninsa Habu driva ya harba motansa izuwa garin gwaza. ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:54AM, 8/7/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣9⃣ Kasancewar Habu driva yasan gdan kawu Usman hakan yasa suka nufi gdan kai tsaye. Meena ce zaune tsakar gda ita kadai ta rafka uban tagumi tunani ne sosai aranta addua kawai takeyi kar Allah yasa Yaya Hafeez yace baxa tasamu daman tsayawa bikin nan ba, Meena tayi nisa sosai cikin tunaninta sai jiyayi andafata a hnkli tadago kanta, Khadija tagani tsaye, ae kuwa bashiri tasakar mata murmushi, cike da kulawa Khadija ta duqa daf da Meena tace sister anya lpy kuwa? Wani murmushin yaqe Meena tasakeyi sannan tadubi Khadija tace "sister lpy Lou mekika gani?" Khadija tace a'a naga kinxauna ke kadai kin zuba uban tagumi ko dai kina tunanin Shine? Dasauri Meena tace haba dai khadija wlh ba haka bane kawai nadamune sbd inason natsaya bikin Hamza (hamza qanin Kawu usman ne) Khadija tayi murmushi sannan tadafa kafadan Meena tace "kema bnda abinki banace ki kira mijin naki kisanar masa cewa kina son yabaki damar qara wasu kwanakin ba?. Meena tashare kwallar dake qoqarin zubo mata tace "wlh sister na jarabba hakan hasalima dana fadamishi bai ce dani qala ba kawai yakashe wayansa. Khadija tace ohhh wlh kina damuwa da abinda baikamata ace kindamu ba, kikasani ko ntwrk ne ko rashin caji kibari anjima kisake tryn. Murmushin yaqe Meena tayi tace oky. Khadija tace yauwa kokefa, nan taja hannunta tace tashi ma muje kasuwa daxu Baba yabamu kudin sayen anko yakumacemin haddake dan haka kisaki ranki kitashi mutafi. Jiki ba kwari hakanan Meena ta tashi tashirya suka tafi kasuwa. Su Meena ko minti uku basuyi da tafiya kasuwan ba sai gasu Hafeez sun kunno kai cikin anguwar. Dai dai kofar gdan Habu yayi parkn, kafinma yace da Hafeez wani Abu tuni Hafeez din yafahimci cewa nan ne gdan. Fitowa sukayi daga cikin motan sannan suka sami yaran dake wasa kofan gdan suka aiki daya daga cikinsu akan yaje yace wai ana sallama da Meena Yaron kuwa dagudu yashiga cikin gdan kmr yadda aka umarce shi, yana zuwa yace "wai inji wani mutumi awaje yace ana sallama da Meena" Amma nadaga cikin d'aki tajiyo muryan yaron da sauri tafito waje tace da yaron "waye ke sallama da Meena?" Yaro yace shima baisani ba, Baba Rabi tace da yaron yatsaya nan tashiga ciki tad'auko hijabi tace da yaron suje tagani. Koda fitar Baba Rabi izuwa waje Hafeez tagani tsaye jingine da mota, dasauri taqara wajansu tana musu sannu da zuwa, Hafeez kam sai waige waige yakeyi inda xai hango Meena. Baba Rabi tace "sannunku da zuwa Hafeez kai ne tafe? Hafeez yayi murmushin yake yace wlh kuwa Baba nine, Baba Rabi tace toh sannunku da zuwa kushigo daga ciki. Dakin Kawu Usman Baba Rabi tasauqe su Hafeez, bayan sunqara gaisawane baba Rabi takawo musu ruwan sha. Sannan tace da Hafeez yad'an jira kadan Meena sunfita ita da yar'uwarta, shiru Hafeez kawai yayi, tunanin inda Meena taje a wannan yammacin kawai yakeyi. Abangaran Meena kuwa suna can kasuwa wajen siyan anko, bayan sungama ne Meena tace sister inaso kikaini inda ake siyan gyale da hijabi, haka nan Khadija takaita gurin da tabuqata, Meena tasaima kanta hijab kallan ankon nasi sannan tasaima Khadija Gyale itama kallan ankonsu. Haka nan suka gama siyayyansu cike da farinciki suka koma gda. Mai taxi na ajiye su Meena fitowan nan da zatayi idanuwanta sukayi tozali da motar Hafeez, rass!! Gabanta yafad'i, amma sai tadake domin tana tantama kmr ba motansa bace, hakanan suka kwashi kayansu suka nufi cikin gda. ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:57AM, 8/7/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode4⃣0⃣ Suna shiga cikin gdan da sallamarsu kafin sunemi waje suzauna Baba Rabi tace "kee! Aminatu daga xuwa kasuwa kuje kudawo shknan sai kumaida gari naku kuje kuyi xamanku, Meena tace Amma wlh ba haka bane mund'an tsaya siyan wasu abinne shiyasa mukadan jima. Baba Rabi tace toh ae kunkyauta sai kitashi kije d'ankin Kawu Usman kinyi baqo, dasauri Meena takalli Baba Rabi tace "Amma baqo kuma"? Baba Rabi eh kawai tacemata tabar wajan. Khadija tadubi Meena tace sister tashi kije natabbata babu wani namijin daxaixo yanemiki har ayimishi izinin zuwa d'akin Kawu face mijinki, plss tashi ki kintsa kijeki. Kafin Meena tace wani Abu Khadija taja hannun Meena izuwa d'akinsu, nan ta tsara mata kwalliya mai kyan gaske Khadija da kanta tabud'e akwatin Meena taza6o mata wasu riga da siket masu kyau tace tasasu. Batare da Meena ta musawa Khadija ba hakanan tadauki kayan tasa, sai da tashirya tsaf sannan tasanya hijab tanufi d'akin kawu usman. Qamshin turaren Meena ne yadoki hancin Hafeez, dasauri yad'ago kansa Meena yagani tana qoqarin xama bisa kujerar da yake zaune. Meena wacce gabanta yatsananta Faduwa cikin siririyar muryanta tace sannu da zuwa Yaya ina wuni? Hafeez ya kura mata idanu ko qiftasu bayayi, shiru yayi tamkar baxaice komai ba , can dai yace Meena ba wannan ne yakawoni ba "Habu driba kam tun shigowar Meena yabar d'akin" Meena tayi shiru tana sauraren Hafeez taji da wacce yaxo. Hafeez ya matso daf da Meena yace zuwa nayi domin inaso kimai maitamin abinda kikace lkcin da kika kirani awaya d'axu. Shiru Meena tayi takasa cewa komai sai faman wasa takeyi da d'an yatsanta,, Hafeez yaqufula sosai yace ko bakyajina ne nace kimaimaita abinda kikafad'a daxu. Cikin tsananin faduwar gaba tafara mgn tamkar ta mai in'en "tace umh uhm dama cewa nayi inaso kabani dama domin na samu halartan bikin Hamza. Hafeez yace okey dukk satin da kikayi anan basu isheki bane,? Meena tayi shiru! Hafeez yace kibani amsa mana ko kuma baki san cewa kinbar mijinki shi kad'ai cikin wani hali na kewa ba? Kewa?? Shine abinda Meena tamai maita cikin xuciyarta, Hafeez yace toh bari kiji nazo intafi da mamata kuma ayau din nan komin dare xamu bar Gwaza mukoma Maiduguri, Meena tad'ago kai fuska a maraice tace "Dan Allah yaya kayi hkri kabarni ko kwana biyu ne inqara. Cike dajin haushinta Hafeez yace kinsan Allah bari kiji wlh ko awa d'aya bazan bari kiqara ba, kuma kitashi ynxun nan kije kihado kayanki inajiranki a mota. Hafeez nafad'in haka yatashi yabar d'akin, a tsakar gda ya tarar dasu Baba Rabi.. nan yaduqa har qasa yayi musu sallama yace "Baba ni zan wuce ynxu" Baba Rabi tace haba Hafeez baka tsoron kuyi dare a hanya, murmushi yayi sannan yace Bakomai insha allahu, nan yayi musu godiya yafice a gdan yakoma cikin motarsa yana zaman jiran fitowan Meena. Abangaran Meena kuwa dagudu ta tashi takoma d'akinsu Khadija sai faman kuka takeyi, Baba Rabi nazaune cikin d'aki taga wulgawar Meena dasauri ta tashi tabi bayanta. Ko dashigarta ta tarar da Meena na kuka tana had'a kayanta, Baba Rabi tadubi Meena tace "ke kuma miye kikewa mutane kuka?" Meena wacce kuka yaci qarfinta tafashe dawani sabon kukan tace " Amma Yayane yace yaxo tafiya dani bayan Kuma nafadamishi cewa muna da biki. Baba Rabi wani uban tsaki taja tace "mtsww aekin wofi kawai yoo dama inkika zauna bikin kawu Hamza uban mexaki tsinana toh kisani dukk wani abu marar muhimmanci dakike tunani yafi miki bin umarnin mijinki domin kuwa bikin Kawu Hamza kodake ko bake xa'a daurashi dan haka kirufewa mutane baki tun baki tarawa kanki jama'a cikin d'akin nan ba. Meena kam gabad'aya takawo iya wuya wani irin takaicine ya sarqe ta, dasauri tashirya kayanta tsaf tayi sallama da kowa kafin Khadija tadawo tayi saurin ficewa tabar gdan (khadija na gurin Sa'idu tailor ta kaimusu kayan ankonsu dinki) Fushi Meena tayi sosai dan haka tana xuwa tasa kayanta a booth tabud'e gdan baya tazauna. Hafeez naganin haka yafito daga gaban mota yadawo baya inda Meena ke zaune, kowa na gdan yafito yayi musu Allah kiyaye hanya. Batare da Bata lkci ba sukabar cikin garin gwaza, suka kama hanyan Maiduguri. ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [7:59AM, 8/7/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episod4⃣1⃣ Su Hafeez sunyi nisa sosai da tafiyarsu amma da gashi har Meena ba wanda yace da wani uffan! Hafeez nema tunfara tafiyansu yaketa satar kallon Meena sbd kwalliyar dake fuskarta baqaramin kyau yamata ba. Ajiyar zuciya Hafeez yayi a hankali ya maida bayansa ya kwanta jikin mota sai fama tunani yakeyi a cikin xuciyarsa, "Hafeez ke tambayar kanshi dama akwai watarana da xataxo ni Hafeez zanso wata fiye da Rafee'a ohh gosh! Nan yafara tunanin ya akayima yafara son Meena badly haka"? Hafeez na cikin tunaninsa wayar dake riqe a hannunsa yana jujjuyata nan tafara ringing. Firgigitt! Hafeez yayi yadawo daga duniyar tunanin da yatafi, cike da kasala Hafeez yadubi wayan don ganin mai kiransa. Sunan Dr Muh'd Hafeez yagani ya bayyana akan screen din wayarsa hanxarce yad'uki wayan gamida karawa a kunnesa "hello Abokina Allah yasa bakayi nisa ba wlh Balkisu ce bata lpy tana fama da laulayi tundazu take damuna akan nakiraka nace tabari zuwa an jima idan ta huta amma Sam taqi, a hanzarce Hafeez yace ya salam tana kusa plss bata wayan. Hafeez na amsan wayan Balkisu tafashe da kuka tanafadin Dan Allah Yaya Hafeez kayafemin mutuwa xanyi wayyoo Allah na bayana xai fashe yaya, gabad'aya Hafeez ya rikice kashe wayan kawai yayi sannan ya umarci Habu driva da yaqara gudu. Baifi tafiya 3Omint ba su Hafeez sukashiga cikin garin Maiduguri, direct gdan Balkisu suka wuce kmr yadda Hafeez yace. Suna isa cikin gdan da sauri Hafeez yanufi ciki batare da yajira su Meena ba. Meena kam batasan meke faruwa ba, amma a hanzarce itama tabi bayan Hafeez. Hafeez na isa cikin falon yafara kiran Balkisu! Billyn mama!! Shiru yaji dasauri yanufi wani d'aki inda nan ne yake tunani d'akin Balkisu yake. Kafin Hafeez yaqarasa d'akin sai ga Dr Muh'd nan yafito daga d'akinshi dasauri yakira sunan Hafeez yace "no abokina gatanan kwance a d'akina nayimata allura ne tayi bacci, fuska d'auke da damuwa Hafeez yace plss mike damun Balkisu Dr Muh'd yana jin nauyin amsa masa tmbyarsa amma babu yadda ya iya domin yaxama dole ya amsa masan. Jan Hafeez yayi izuwa wani corido sannan Dr Muh'd yadubi Hafeez yace "abokina munsami qaruwa ne Balkisu nad'auke da cikin wata biyu, sai dai da mtsl. Dasauri Hafeez yace mtsl Kuma? Mtsl kmr tame kenan, Dr Muh'd yace kasan dai nikadai iyayena suka mallaka arayuwarsu shiyasa tunda girma ya riskeni suka takura akan lallai sai nayi aure domin suma suga jikokinsu suncika gdan nan. Toh sai dai ba'anan gixo ke saqar ba, Balkisu tasamu ciki sai dai yana masifar azabtar da ita kome taci baya xama acikinta dukk tarame tafita hayyacinta kullum tana cikin ciwo. Nikuma tausayinta yajani nayi tunanin zubar da cikin, sai dai kafin na kai ga aikata hakan iyayena sunce muddin nabari cikin dake jikin Balkisu ya zube to basu yafemin ba. A gsky Hafeez ina cikin damuwa domin ni lfyr Balkisu tafimin komai arayuwata. Murmushi Hafeez yayi sannan yashiga kwntarwa Dr Muh'd hankali dukk da kasancewar shima nasa hanklin a tashe yake. Sai qarfe Tara da rabi Na dare su Hafeez suka bar gdan, suma suka nufi nasu gdan, Meena kam hadda hawayenta ganin yadda Balkisu tarame lkci d'aya gashi har suka bar gdan bata samu ta farfado ba. Restaurant yafara wucewa dasu don sunci abinci, Amma Hafeez gani yayi maza sunyi yawa agurin cin abincin Dan haka take away kawai yayi musu suka nufi gda kai tsaye.... ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:52AM, 8/8/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode4⃣2⃣ Tun sanda Hafeez yaje gwaza yad'auko Meena suka dawo yaga canji a tattare da ita sosai domin gabad'aya ta kauracewa ganinsa dukk abinda tasan zai had'ata hnya da Hafeez Meena tajanye , hakan kuwa baqaramin d'a hanklin Hafeez yayi ba gad'aya yashiga damuwa ga uban taurin kai ko ince girman kai da yahanasa kai kanshi gareta balle yasan halin da take ciki. Yau ya hakasance weekend, hakan yasa yau Hafeez na gda bai je ko ina ba,..Wanda a bangaran Meena kam hakan bai mata d'adi ba domin tanason fita zuwa d'aura musu abin brkfst gashi kuma Hafeez yayi zamansa a falo. Gabad'aya Meena taqagu Hafeez yabar falon Dan tasamu damar wucewa a hankali Meena taske tabud'e kofan d'akinta taleqa ko Allah zaisa taga Hafeez nan amma sai taga wayam! baya cikin falon, hakan yasa tafito a hanzarce tanufi kitchn. Dai dai lkcin ne kuma Hafeez yafito daga waje hannunsa d'auke da wasu takaddu daganin alama daga waje yafito dasu, dasauri Meena tashiga kitch abinta. Hafeez kam murmushi yayi gamida girgiza kansa domin yaga lkcin datashige kitchen dasauri, falo yanufa ya ajiye tarin takaddunsa sannan yanufi kitchen din. Meena ce tsaye cikin kitchn ta tawani riqe qugu tana tunanin abinda yakamata suyi brkfst dashi. A hankali Hafeez yashiga kitchen din batare da sanin Meena ba, Meena kam sai ji kawai tayi an rugumota tabaya tsamm. A tsorace tad'an juya Hafeez tagani take anan tasauya kamaninta tawani turbune fuska kamar zatayi kuka, a hnkli Hafeez yajuyo ta tafuskance shi sannan ya riqe hannayenta cikin muryan rad'a yake mata mgn "haba Meenata fushi kikeyi da d'an bawan Allah nan? plss kimin afuwa wlh a lkcin jinayi bnda control inba d'aukoki nayi ba u know i really miss u alot Meena ynxu yakama ki juyo ixuwa ga mijinki kimanta da komai kimin afuwa kinji matar da babu irinta." Hafeez nagama surutunshi Meena tadungujeshi dasauri tabar masa kitchen din, hnklin Hafeez gabad'aya yatashi riqe goshinsa yayi sbd yadda yaji knsa nasara mishi cikin sanyin jiki haka Yaja jiki yanufi hnyar falo. Kmr daga sama Hafeez yajiyo muryan Balkisu tana kwala mishi kira tunkamin tasamu taqarasa cikin falon. Dasauri Hafeez yajuya Balkisu yagani da gudunta tanufato shi, a hanzarce Hafeez yaqarasa wajenta yana fad'in ke Billyn mama kanki d'aya kuwa? A cikin wannan yanayin dakike ciki shine kike wa mutane gudu haka? Balkisu ta turo baki cike da shagwa6a tace ni gaskiya yaya cikin nan ya takuramin wlh shikenan ni baxanyi abinda nakeso ba. Hafeez yayi murmushi yaja hannunta suka nufi cikin falo, bayan sun zauna ne Hafeez yadubi Balkisu yace "lpy kuwa Balkisu naganki da sassafe?" Balkisu tace lpy law wlh dama My precious ne yayi tafiya takama ynxun nan izuwa wani qauye shine yacemin sai xuwa dare xai dawo dan haka yace nashirya yayi dropn dina anan domin bai yarda yabarni nikad'ai ba.sannan dama nazo ma da anty amarya wani lbri mai dadi, Hafeez yace "minene yafaru" dasauri Balkisu tamiqe tace yaya inaxuwa. Kafin Hafeez yace wani abu ta tashi da sauri tanufi d'akin Meena Koh da shigarta ta tarar da Meena kwance tayi rufda ciki, dasauri Balkisu ta qarasa ta kwnta a hnkli cikin sand'a yadda Meena baxataji ba,..Meena kam batamaji shigowarta ba Dan tayi nisa sosai da tunani sai jitayi ana huramata iska a kunne dasauri tarazana tace miye haka ya.....shiru tayi takasa qarasa abinda takeson cewa sbd wacce tagani a gabanta. Dasauri Meena ta tashi zaune tadubi Balkisu cike da zolaya tace "a'a gawa taqi rami kece yau a gdan namu"? Balkisu tahad'e fuska sosai tadubi Meena sannan tace Anty Amarya koda baki cemin komai ba tabbas akwai abinda yake faruwa a gdan nan sbd daga ke har Yaya na lura bakwa cikin walwala, keda mukayi alqawari dake amma sai nazo naga sa6anin haka domin tunshigowata gdan nan idanuna suka ganemin cewa Yayana nacikin matsanancin damuwa wanda cikin alqawarinmu nafad' a miki cewa banaso kibarshi cikin kewa ko damuwa sbd laluran dayake fama dashi. Wata irin nannauyan ajiyan xuciya Meeena tayi sannan tadubi Balkisu tace "wlh ba haka bane amma kimin afuwa insha allahu zangyara kuskure na". Murmushin yake Balkisu tayi sannan tace Allah yasa. Cike da sanyin jiki Meena tace Ameeen!! Lkci d'aya kuma Balkisu tasaki jikinta da Meena daga bisani kuma taja hannun ta tace " yauwa Anty amarya taso muje wurin Yaya domin naxo muku da kyakkyawan labari. Meena tadubi Balkisu tace "kyakkyawan lbri kuma?" Balkisu tace sosaima kuwa kedai taso muje. Meena tace to Balkisu banqi takiba Amma kiyimin afuwa Bari nasamu nad'aura mana abinda mukaci, dasauri Balkisu tace plss kawai kidafa mana indomie muci kinsan Yaya ma naso. toh kawai Meena tace sannan ta tashi tanufi kitchen tad'aura

Chapter 8 of 10