Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita nakeson kasancewa har k'arshen rayuwata, wani irin abune ya soki zuciyar Suhailat a fusace tace toh shikenan naji yanxu inaso kasanar dani tsakanin RAFEE'AT da SUHAILAT wa kake so?? Wani murmushin takaici Hafeez yayi yanuna Suhailat da d'an yatsa yace what do u mean kina nufin zand'auke kine inbar Rafee'at to bari kiji indai wannan shine tunaninki toh gwnda tunda wuri kicanja shi domin kuwa Rafee'at wani b'angarece ta rayuwata bazantaba iya rabuwa da ita ba koh da kuwa sama da k'asa zata had'e, cike da masifa Suhailat tace ohhh haka ma zakace toh wlh inhar baka zab'eni amatsayin wacce zaka aura ba toh wlh inatabbatar maka dacewa sai ka tafka babbar hasara arayuwarka domin bakasan koh ni wacece ba indai matuqar ina raye wlh babu kai babu auran waccan k'idahumar. Hafeez murmushi yayi ya dakatar da Suhailat yace dakata mallama inamai gargadinki kadaki k'ara cewa matar aure na k'idahuma, maikike zato dama haka kawai zan aureki banda tabbas din koke wacece Rafee'at kuwa tunbata mallaki hankalin kanta ba Allah yard'auramin sonta so ni inaganin bbu yadda za'ayi Na zab'eki nabar ta kingane ae dan haka ki kwntar da hnklinki ayi taron nan lpy kikoma hannun mahaifanki. Hafeez nafadin haka yasa kai yafice zuciyarsa gaba daya ajagule. Yana fita falo yanufa, mommy naganinsa tadubesa da murmushi tace yauwa Hafeez ynxu kuwa nake k'okarin nemanka, kaga tun mutane basu fara taruwa ba inaso kaje oasis bakery ka ansoma Balkisu birthday cake dinta. Hafeez yace toh Momy bari inyi sauri inje indawo, karaff Balkisu tace yaya Hafeez plsss nima zanbika da sauri ma Aysha (ummi) autar Momy tace yaya nima zanbika, a hnkli Hafeez yaduk'a wajan autan Momy yace swry ummi bazan iya zuwa dake ba sauri nakeyi zanje nadawo kinji karki damu zanzo miki da ice-cream, gyada masa kai tayi takoma gurin momynta tahau saman kujera taci gabada wasanta. Balkisu kam binshi tayi abaya cike da zumud'i ta marairaice fuska plsss Yaya znbika wlh baxan dameka da surutu ba. Okay kawai yace da ita har yanufi hanyar fita kuma chan sai yajuyo ya kalli Rafee'at wacce kanta ke k'asa tak'i yarda suhada ido sbd fushi takeyi dashi, a hnkli Hafeez ya kira sunanta Rafee'at d'ago knta tayi a hnkli tadubesa shikuwa Hafeez naganin tadubesa yahada hannayensa alamar neman afuwa sannan yayi mata nuni da inyadawo zaimata bayanin komai, murmushi tayi maisauti sannan ta gyada masa kanta. Da sauri yabar falon yana murmushi, sunafita yanufi parkn spc yadauki mota suka nufi oasis.z Abangaran Suhailat kuwa waya tadingayi tana fad'awa frnds dinta cewa Hafeez yaci amanarta ya yaudareta ashe yana da mata baifada mata ba, dukk wnda tak'ira sai dai yabata hkri, ganin haka yasa takira daddynta tafada masa maganganun da sukayi matuk'ar girgiza shi hnlkinsa gabadaya yagama tashi, Suhailat kam nagama fadin sak'onta takashe wayarta, gabadaya lkci daya tazama zautacciya hnklinta yagama fita akanta sbd zafin kishi, hakanan tacire d'an kwalin kanta tanata faman sambatu da neman mafita domin kuwa acewarta da taga auran Hafeez da wata gwnda taga mutuwarta dan haka da sauri tabud'e k'ofa tanufi hnyar kitchn koh da shigarta tadauki sabuwar wuqa sai shek'itakeyi cikin zuciyarta tace koh inbisu falo inkashe kowa da kowa sannan nima inkashe Kaina, har tafara fita a kitchen din kome ta tuna kawai saita koma kitchen din nan tafara mgn cikin sambatu wlh sai dai mumutu gabadayanmu bazai yuwu namutu nikadai ba, surutan da takeyine yajawo hnklin Iya ladi mai aiki wacce take k'okarin wanke babbar tukunya awaje kasancewar tana bakin window din tawaje hakan yabata damar lek'awa bak'uwan nance tagani tana k'okarin bude silinda na gas, ga kuma surutan da wannan baquwar takeyi hakan ya bama iya ladi tsoro dan haka tafara ihun Neman taimako tafadin Hajiya! Alhaji! jama'a yar k'unan bak'in wakece wannan bakuwa da gudu tanufi cikin gda don tasanar dasu ta'addancin da ake shirin aekatawa kasancewar da dan taxara shiyasa take gudu tananeman agaji. Mommy ce tafara jiyo ihuun neman taimako kmr iya ladi ce a kitchen ae da gudu suna Kalmar salati suka nufi kitchen din gabadayansu, mommy na bud'e k'ofa Suhailat na cinnawa gas din ashana ae kuwa take anan gdan yayi wata irin girgiza tamkar antada bomb take gdn Yakama da wuta ta ko'ina. Kafin iya ladi tak'arasa ciki tuni Gas din yatashi take itama tasamu nata domin kuwa girgizan nan yasa tayi wata mummunan faduwa Wanda yayi sanadin sumanta.. Inallilahi wa'inna ilaihiraji'un....... ®NWA [11:52AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:08AM, 7/15/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣3⃣ Cikin tsananin tashin hankali gabad'aya jama'ar unguwar kowa yafito, kowa sai mamakin faruwar wannan al'amari yakeyi, Alhaji shehu makocin su shine yayi tunanin kiran fire servirce(motar yan kwana-kwana) bayan shud'ewar wasu yan mintina kuwa sai ga sunan da gudu sunshigo cikin layin ba su tsaya jinkirin komai ba suka zago babban tiyo dinsu sukafara zuba ruwa tasaman gdan, Dakyar akasamu wutan nan ta mutu bayan yan wasu mintuna kenan wasu maza guda uku ma'aikatan fire service cikin shirinsu na aiki suka tunkari hayakin suka afka cikin gdan. Koh da shigarsu suntarar da gawawwaki tare waje guda gabadaya sunk'one ta yadda koh fuskokinsu ba'a iya ganewa, haka nan suka dibi gawawwakin bisa abin daukar gawa suka fitar da su izuwa waje, sai da suka gama kwashesu sannan sukashiga bincike acikin gdan. Suna cikin lalubensu ne Allah yasa sukaci karo da iya Ladi wacce ke kwance sumammiya da gudu suka k'arasa wajenta ganin cewa tanada sauran numfashi yasa sukayi saurin dauketa don bata taimakon gaggawa. Hafeez ne tafe shida Balkisu sai surutu take zuba masa Hafeez yadube Balkisu yace ohh Balkisu ke kam daban kike ina yanxun nan da zamu fito kikamin alqawarin cewa baxaki dameni da surutu ba sai gashi tunba'aje koh inaba kin isheni da surutu ynxun nan sai in ajiyeki anan ki hau mashin, dasauri Balkisu tasa tafin hannu tarufe bakinta tana dariya. Chan kuma Balkisu tajuya bayan mota tazura hannunta a sit din baya tadauko robar ice- cream wanda suka siyoma autar Momy. Balkisu tace amma gsky Yaya Hafeez nima zansha roba daya, Hafeez girgiza kansa yayi yace ohh gsky babu rabonki anan wannan dukk na aura ne. Balkisu ta turo baki cike da shagwab'a wai ita tayi fushi. Hafeez dai bai kulata ba domin hnklinsa gabadaya yanaga Rafee'at BURINSA bai wuce ya Isa gda da wuri ba don yasamu damar bawa Rafee'at hkri sannan dole ne yasamar wa Suhailat ticket a yau din nan gobe takoma garinsu da irin wannan tunanin Hafeez yashiga cikin layinsu. Dan dazon jama'a ne suka k'awanye ko ina na cikin anguwar cike da mamaki Hafeez yadinga horn ana bude masa hanya har ya samu ya isa k'ofar gdansu, inalillahi wa'inna ilaihiraji'un shine kawai abinda Hafeez ya iya furtawa dagudu suka fito atare shida Balkisu suka nufi cikin gda, gawawwaki suka gani jere a kwance anrufe da fararen kyalaye Hafeez ne ya nufi wajen da gudu yanafadim meyafaru ne mekefaruwa haka? gabadaya illahirin jijiyoyin wuyansa dukk sunfito bude gawarwaki yafarayi daya bayan daya Hajiya Hauwa yafara gani gabadaya illahirin kammanunta sunsauya gabadaya tak'one nan Hafeez yashiga girgizata yana fadin plss uwata kitashi dan Allah haka yashiga bude gawawwakin yana sambatu, Balkisu kam Sam tak'i kuka tsayawa tayi kyam waje guda chan kuma tafara tafiya a hnkli ta isa kan gawar autan Momy tabude ta nan Balkisu tashiga jijjigata tanafadin ummi! Autan Momy! Kitashi ga ice- cream nakawo miki plsss kitashi qanwata kitashi!! wlh wasa nake miki bazan sha ice-cream dinki ba. Dasauri ta Isa kan gawan iyayen nata natafara fadin Abba kace ummi ta tashi plss Momy ya kukayi shiru ne kunmanta yau ne birthday na Dan Allah karkumin wannan wasan kutashi mushiga cikin gdanmu Yaya Hafeez kace Umma ta tashi anty Rafee'at ba ynxu kikamin alqawari zaki kaini park ba plss kitashi anty Rafee'at nan tashiga ihuuu tanafadin iyayenta sutashi. Jama'ar anguwan kowa ya tausaya musu, a hnkli cikin tausayawa Alhaji Shehu yakaraso garesu yana lallashinsu Hafeez Balkisu kuyi hakuri iyayenku kam sun amsa kiran mahaliccinsu Hafeez da Balkisu atare suka fadi k'asa summanmu. Yan cikin anguwansu kam wasu sai dasuka zubda kwalla sbd tsananin tausayinsu domin kuwa dukk wani dake cikin anguwar matuqar yasan family din Alhaji Abdullahi Shariff toh tabbas yasan irin wannan family din ake kira Happy family. Da gaggawa motar ambulance ta kwashesu akayi asibiti dasu don basu taimakon gaggawa, inda kuma Alhaji shehu makocinsu yayi tsaye agaban wannan gawarwaki har sai da ya tabbatar ankaisu makwancinsu, Allahu Akbar. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 7/16/2016] MUNAY✍ 🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣4⃣ La'illaha'ilallah muhammadur-rasulullah S.A.W, shine abinda iya ladi tafara furtawa lkcin da tadawo cikin hayyacinta da gudu nurse din dake kusa da ita taje ta kirawo Dr, Dr da xuwansa kuwa nan yashiga yi mata wasu yan gwaje-gwaje yana gamawa ya girgiza kansa nan yajuya ga nurse din dake tsaye yabata umarnin tamiqo masa allura da hanzarinta kuwa ta miqo masa take anan yasakeyi ma iya ladi wata allurar kankace me tuni bacci yadauketa.. Balkisu tunkafin su isa asibiti tasamu farfad'awo sa6anin Hafeez wandake kwance cikin halin RAYUWA Ko MUTUWA! da isarsu asibitin wasu maza majiya k'arfi suka taimakawa nurses din nan aka daura Hafeez bisa gadon daukar marasa lpy I.c.u suka nufa dashi kai tsaye. Abangaran Balkisu kuwa wata nurse ce taxo ta tafi da ita izuwa nurses station(wurin zaman nurses) gabadaya nurses din dake gurin babu abinda sukeyi ma Balkisu face nasiha da ban hkri na rashin da sukayi. Yan'uwa da abokan arzik'i kuwa gaba d'aya sun sami damar halartan jana'izar su Alhaji Abdullahi kowa sai jimamin wannan rasuwa yakeyi mai cike da abun al'ajabi, hakanan gdansu Rafee'at suma dukk sunjigata da wannan al'amari. Likitoci da kyar suka samu kan Hafeez domin zuwa yanzu yanayin nasa ana iya cewa alhmdllh, Balkisu kam gabad'aya tazama kurman dole tak'itace da kowa uffan wasu irin hawaye masu k'unci da rad'ad'i kawai ke zuba a kuncinta. Misalin k'arfe uku da rabi na dare Hafeez ya farfado, a hnkli ya fara bud'e idanunsa tun yanaji suna mishi nauyi har dai yasamu ya bud'esu gabadaya cikin natsuwa yake kiran sunan mahaifan nasa chan kmr wucewa wasu yan sakwani Hafeez ya miqe zaune cikin tsananin firgici take yaji kansa yafara Sara mishi drip din dake sanye a hannunsa ya fisgeshi sannu a hnkli ya zaro k'afafunsa qasa tamkar d'ankoyan tafiya haka yafara fita a cikin d'akin. Balkisu Na zaune daga bakin k'ofa tarafka uban tagumi sai zubda kwalla takeyi maganar bacci kam babushi gabad'aya bacci ya k'auracewa idanunta. Tana cikin wannan Halin ne taji andafa kanta tare da kiran sunanta da sauri tad'ago ganin Ya Hafeez ne tsaye akanta tamiqe da sauri ta rungumeshi wani irin sabon kukane ya zo mata Wanda Hafeez shi Sam kukan yak'i zuwar masa, a hnkli yake Shafa kan Balkisu Alaman lallashi Suna cikin hakane Dr din dake kula dashi yafito daga office dinsa kenan ya hango patient dinsa tsaye, da sauri yak'arasa gurin yana isa yariqe hannun Hafeez yana k'okarin mai dashi cikin dakin, Dakatar dashi Hafeez yayi cikin wata raunanniyar muryansa yace no Dr karka damu am ok nagode da k'okarinka akaina. "A ynxu banida wani BURI illah naga k'anwata cikin walwala, nan ya cigaba da Shafa kan Balkisu yanafadin k'anwata Sam kadaki damu domin natabbata mutuwar mahaifanmu dasa hannu wasu aciki inkuwa har hakan takasance nayi imani da maikowa mai komai saina d'and'ana musu abinda suka aikatawa family na sannan Balkisu.." Bai k'arasa fadin abinda yakeson cewa ba sai ga wata nurse nan da gudunta tak'araso wajen Dr din tanafadamishi cewa wannan tsohuwar tafarfado amma jikinta ya Matsa sosai. Cikin nuna tsananin damuwa Dr yadafe goshinsa yana fadin ya salaam, nan ya mai da dubansa ga Hafeez yace I thnk itama she ix part of ur family! Hafeez najin haka yace da Dr din plss suje sugani kowaye ce, Dakyar Hafeez yasamu suka k'arasa d'akin da iya Ladi ke ciki, iya Ladi na nan kwance sai jujjuya kanta takeyi tanata furta Kalmar shahada. Hafeez naganin Iya Ladi baisan lkcin da ya kwala mata kira da k'arfi ba, a hnkli ta waro idanunta ganin Hafeez tsaye akanta yasa take ta k'ok'arin ganin ta tashi zaune amma Sam hakan yafaskara sbd wata irin hajijiya dake d'awainiya da ita, da sauri Hafeez ya duqa daf da ita. Iya Ladi babu abinda tafara furtawa sai Hafeezu yar k'unan bakin wake ce! Hafeez yayi sururu yana tambayar wacece yar k'unan bakin wake? iya Ladi tace" wannan bak'uwa taka da Kuka zo tare itace tayi sanadiyyar gobarar da tashi dasu Alhaji da Hajiya domin naji lokacin da yarinyar take fadin sai takashe Ku kai da Rafee'atu atunaninta kana cikin gdan shine tabude silindan gas yayi ta linking daga bisani ta kyasta ashana nayi k'okarin gudun Na sanarwa Hajiya abunda ke faruwa amma Allah bai bani iko ba har wannan yarinya tasamu galabar kona gdan, take anan Hafeez yamiqe tsaye yafara ja da baya yanafadin no! no!! no!!! Suhailat karkimin haka kinsalwantar dani Suhailat kin ha'inceni kin durqushemin rayuwa kin kassarani kin maidamu marayu no Suhailat dama abunda kike shirin aikatawa kenan? dana sani daban fita a gdan ba, yana fadin maganar yana jada baya har ya isa jikin bango nan yashiga gwara kansa yanafadin nayi nadamar saninki arayuwata natafka babban kuskuren amincewa wata diya macce bayan Rafee'a na,Suhailat kinci amanata bazanyafe miki ba! Bazantaba yafemiki ba! Kincuceni kincutar da Balkisu inallillahi wa'ina ilaihiraji'un, ganin bashida niyyar daina gwara kansa a bango Balkisu tazo da gudu ta rungume shi tanafadin yaya kadaina plss kadainan dakyar da taimakon Dr suka samu Hafeez yadaina amma sai wani irin numfashi yake fiddawa yanata sambatu, Iya ladi dake kwance tace Dan Allah Hafeezu karka kafadamin cewa su Hajiya da Alhaji sunrasu?. Hafeez ya sadda k'asa yace iya Ladi sai dai mu sami dangana domin kuwa Suhailat ta aikatamin abunda har namutu da tabonshi zankoma ga mahallicina, nayi kuskuren amincewa diya macce a ynxu bayan Balkisu babu wata diya macce da zansake yarda da ita Suhailat kin ha'inceni bazan taba yafemiki ba. Iya Ladi najin kalaman Hafeez nan take tafahimci cewa su Hajiya Allah yayi musu rasuwa, take anan tafirgice jikinta yaqara tsanantawa babu abinda take furtawa sai neman gafara. Kafin wayewar gari kuwa iya ladi tace ga garinku(iya Ladi ta amsa kira) Hafeez da Balkisu nasamun labarin rasuwar iya Ladi take anan sukaje komai yadawo musu sabo. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [9:00AM, 7/18/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣5⃣ Tashin hankali wanda ba'a samishi rana, a yaune Alhaji Kabeer musa wato mahaifi ga suhailat yayi dirar mikiya acikin garin borno bai wani sha wahala ba kasancewar Alhaji Kabeer da abokin Hafeez yaxo dashi tundaga taraba state kasancewar abokin Hafeez din yasan gdansu shine musababbin dayasa Alhaji Kabeer ya tisa k'eyarsa agaba. Da isarsu barno kai tsaye gdansu Hafeez suka nufa, koh da shigarsu Cikin anguwar Ahmed(abokin Hafez)ya nuna masa gdnsu Hafeez kafin ma driva yasamu damar parkin motar tuni Alhaji Kabeer yabude murfin motar yafito yanufi hanyar gdan da aka nuna masa, mazan dake zazzaune daga gefen gdan yan karban gaisuwa tuni ma'aruf(qanin alhaji abdullahi) yataso daga cikinsu don tsaida wannan mutumin dake k'okarin tunkarar gdan da yakasance a kulle, gashi dai daganin mutumin kasan cewa baicikin natsuwa. dan haka da sauri suka isa kofan gdan atare, ma'aruf nazuwa yafara tambayar wannan mutumin yace" mallan lafiya kuwa? Naga kataho a hargitse kana qoqarin bude wannan gdan gashi dai naganka amma babu alamar dangantaka ko sanayya atattare da kai zan iya sanin ko kai waye" Cikin zafin rai Alhaji kabeer ya dubesa yace"nikuwa nahada dangantaka da wannan gdan tunda yakasance ya'ta tana hannunku, uncle ma'aruf ya k'ufula sosai ganin cewa wannan mutumin yazo masa da rainin hnkli waye kuma yarsa? Da sauri uncle ma'aruf yasake jefa masa wata tambayar akaro na biyu" waye yarka kuma? amma dai ba'anan gdan ba? Alhaji kaber yace kwarai kuwa a wannan gdan ne koh ba nan bane gdansu Hafeez Abdullahi. Kamar daga sama sukaji ance eh nan ne, da sauri sukajuya a tare don ganin mai basu amsa. Hafeez ne tsaye rungume da hannayensa a kirji, fuskan nan tashi tayi fayauu tsakanin jiya da yau gabadaya Hafeez ya rame ya chanja kammanu' a hnkli yake tafiya kasancewar har ynxu bayajin qarfin jikinsa , qarasawa yayi wajan nasu yanuna daddyn Suhailat yace"koba kafadamin ba nasan cewa kaine mahaifin suhailat ko ba komai ga kammaninku nan yanuna, ka kasance mahaifin mai kisan kai azzaluma.. Da sauri dadyn Suhailat yadakatar dashi tahanyar nunashi da yatsa yace "kai Yaro dakata waya baka ryt din ambatarwa yarinyata wadannan munanan alkaba'in? "maza kaje kafito min da yarinyata" cikin tsananin fushI Hafeez yace tirrr da hali irin na yarka. Ko dayake dama hausawa sunce juma'ar da zatayi kyau tundaga laraba ake iya ganeta,sannan dukk wata tarbiya tana farawa daga gdane sai dai ga dukkan alamu daga kai har yar'taka wacce kake tutiya da ita Sam babu wannan alamun atattare da ku. Tuni hawaye masu ciwon gaske sun wanke fuskar Hafeez' Daddyn Suhailat ne yadakatar dashi tahanyar cewa "nace kaje kafito min da diyata ko kai kurmane?" Take anan ran Hafeez ya6aci gabadaya kamanninsa suka sauya, jaa da baya yakamayi cike da masifa yakewa Daddyn Suhailat bayanin dukkan abubuwan da sukafaru ta sanadin yartasa' Daddyn Suhailat najin wannan bayani tuni gume ya wankesa, sbd tabbas yasan yartasa zata iya aikata abunda yafi haka, sannan bashida ryt din da zaixo yatada husuma sbd Suhailat da kanta tafadamishi dukkanin abinda tayi niyyar aikatawa, take anan yaji wata irin nadama marar iyaka, cikin ransa kuwa fadi kawai yakeyi inama lkcin baya xai iya dawowa domin ya gyara kuskuren da ya tafka akan rashin bawa Suhailat ingantaciyyar tarbiya. Mgnr da Hafeez keyice tadawo da Daddyn Suhailat daga dogon tunanin da yatafi" ae ina mai tabbata maka cewa saina dauki fansar ta'addancin da dabbar diyarka ta aikatamin domin tun sanda wannan al'amarin yafaru nake tunanin tayaya za'ayi naga mahaifin Suhailat domin nadauki tawa fansar dukk da cewa Suhailat tariga da ta mutu toh amma ko ba komai idan nadauki fansar abunda ta aikatamini zansamu sassauci. Da sauri kuwa Daddyn Suhailat yad'ago kai gamida cewa fansa Kuma? Wacce irin fansa? Hafeez yayi wani murmushi mai ciwo "yace fansar abinda ta aikatamin domin nayi alwashin sai na salwatar da rayuwar nata iyayen, sai kuma alhmdllh gashinan ka kawomin kanka. Daddyn Suhailat najin haka ae da sauri yakoma gefen uncle ma'aruf yanafadin Subahanallahi Hafeez kasan abinda kake cewa kuwa? Hafeez ya turbune fuska yace tabbas nikuwa na san abinda nake cewa sai dai natabbata bazaka amincewa hakan ba har sai kaga nadauki mataki. Uncle Ma'aruf ne ya dakatar da Hafeez daga munannan alqawarinsa, Hafeez kam yayi nisa sai sambatu yake yanafadin sai yakashe mahaifin Suhailat, mazan dake zazzaune cikin rumfa masu amsar gaisuwa sune suka taso Dan ganin abun yaqi qarewa. Dakyar akasamu Hafeez ya dan sauqo sannan ya umarci Daddyn Suhailat daya bacewa ganinsa tunkafin yakira masa hukuma..sbd baya qaunar ganinsa balle jin sunan diyarsa. Tuni Alhaji Kabeer yabar cikin garin borno. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣6⃣Alhaji kabeer sbd tsananin rud'ewa bai samu daman komawa da Ahmed ba, anan cikin garin borno ya barsa. Hakan ne yabawa Ahmed din damar zuwa yayi ma abokin nasa ta'azziya da jajen abunda yafaru, daga bisani kuma ya jasa gefe nan ne yayi masa bayanin dalilin zuwansa da yadda akayi yazo sannan Ahmed yad'aura da yimasa bayanin ko wacece Suhailat, kwarai da gaske Hafeez yayi matuqar mamakin jin lbri Suhailat wata irin nadama ce tadinga addabar zuciyar Hafeez take yaji gabadaya dukk yatsani kansa. *Bayan Wata Daya* Yan'uwa danginsu Hafeez babu yadda basuyi ba akan suna son tafiya da Balkisu tazauna a hannunsu amma Hafeez ya qeqasa qasa yanuna sam bai amicewa hakan ba, dole suka rabu dashi kowa Yakama gabansa. Bayan kwana 2 Hafeez yasa aka gyara masa gdansu dake cikin federal lowcost chan suka koma shida Balkisu domin a cewar Hafeez baxai iya sake rayuwa acikin gdan da sukayi rayuwa da mahaifansa ba. Dama ya lafiyar kura balle kuma anta6ota, wasu irin sabbi halaye Hafeez ya qirqirowa kansa gabadaya yakoma miskilin gaske. Gashi ynxu kwatakwata Hafeez baya yadda da kowa sannan idan kaga fara'ar Hafeez ko murmushinsa toh tabbas yana tare da Balkisu ne. *** BURIN HAFEEZ a kullum shine yaga cewa ya bawa Balkisu ingantacciyar rayuwa kamar sauran yara, sannan tuni Hafeez ya qudurta a ransa cewa tunda yarasa Rafee'ansa toh babu shi babu kula wata d'iya macce, wannan shine yabama Hafeez damar nunawa dukk wata diya macce k'iyayya 6aro-6aro matuqar bai had'a jini dake ba, hakan yasa tsakanin macce da Hafeez kuwa babu komai sai tsantsar hantara da nuna zafin rai domin acewarsa "dukk halinsu d'aya" Dukk irin yawan yan matan dake nuna tsantsar soyayyarsu ga Hafeez amma Sam basu fuska balle ya amince dasu, sai dai suyi ta nacinsu su gaji. Abangaran Balkisu kuwa bata da wani Buri da yawuce taga cewa yayan nata ya mance da komai yayi auransa don fuskantar sabuwar rayuwa, amma hakan yafaskara. Gashi Hafeez kullum yana cikin kad'aici da damuwa Wanda hakan yayi sanadiyyar jawo masa hawan jini, tun Balkisu na nuna damuwarta har tasaba da kafiya irin na yayan nata. Amma sai dai Zuwa ynxu Balkisu taqudurta a ranta cewa sai ta rusa dukk wani BURI na yayanta akan qin son aure wanda atunanin likitansu ya basu shawaran cewa lallai Hafeez yana buqatar macce wadda zata kula da rayuwarsa sosai. Wannan shawara ta Dr muh'd ta matuqar tsayawa aran Balkisu domin tasan abune mai wahalar yuwuwa kasancewar Hafeez yatsani macce arayuwarsa, shiyasa dukkanin wani tunaninta yatsaya akan taya za'ayi auran Hafeez yasamu yuwuwa? Balkisu da kanta tasan cewa Hafeez baida wani BURI da yawuce yabata kyakyawar kulawa, ita kanta tasan hakan nafaranta mata rai dahakan kuma take alfahari dashi domin ya zama tamkar uwa uba a gareta sbd babu abinda tanema tarasa, toh amma sai dai ganin walwala da farincikin yayan nata yafi mata komai arayuwa. "Dan haka kema Balkisu tunda ynxu kingirma kin mallaki hnklin kanki kinfahimci minene rayuwa yakamata kikawo sauyi da farinciki arayuwar tilon Dan' uwanki" Balkisu tayi nisa sosai cikin tunanin ta, jitayi anata buga mata k'ofa da sauri tamiqe tanufi k'ofan ta bud'e. Hafeez ne tsaye yasakar mata murmushi itama murmushintayi masa tace" yayana jiki yayi sauqi kenan?" Kyad'a mata kai yayi yace sosaima naji sauqi, ynxun nan ma Nadawo daga masallaci najiki shiru ne yasa nace bari inzo indubaki. Balkisu tad'an waro idanu waje tace "Yaya anyi kiran sallah ne? Hafeez yadubeta da mamaki yace "kina nufin bakiji kiran sallah ba? Gashi kuma ga dukkan alamu idanuwanki basuyi kama dana mai bacci ba, aikin me kikeyi haka Wanda ya d'aukemiki hnkli? Ganin Hafeez yatsureta da tambaya yasa tayi saurin cewa Yaya bakomai kawai Allah baisa naji kiran sallah bane, kafin Hafeez yace wani Abu tuni Balkisu ta tajuya cikin d'aki da sauri tafad'a toilet. Kasancewar lkci yaqura alwala kawai tayi tafara gabatar da sallah. Balkisu tajima zaune bisa sallayah sai jero aduo'i takeyi tanamai roqon Allah yashige mata gaba Ya kuma bata ikon cika alqawarin da tadauka nakawo farinciki a rayuwar d'an uwan nata. "Cigaban lbrin" ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [2:40AM, 7/21/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣7⃣ Haka rayuwa taciga da kasancewa, a kullum Balkisu bata da wani tunanin da yawuce tayadda za'ayi auren yayan nata yakasance? Wacce hanya zatabi? wazata tunkara da matsalarta? Gashi dai Hafeez baya bari takula qawayenta balle tasamu wacce zatayi shawara da ita don nemawa kanta mafita. Shiyasa a kowanne dare yakasance Balkisu bata iya runtsawa, kullum tana mai miqa wuya da neman taimakon ubanji dan haka takai kukanta ga mai kowa mai komai. ** ** ** Yau tsawan sati d'aya kenan Balkisu na ziryan zuwa gdansu Meena amma kullum bata samunta,(Burin Balkisu shine taga cewa ta taimaki Meena, amma ga dukkan alamu Meenah a tsorace take da Balkisu shiyasa take gudun dukk wata hnya daxata hadasu.) Yau yakasance ranar Asbar, Wanda hakan yayi dai dai da Balkisu bata da lectures dan haka tun qarfe bakwai na safe tashirya tsaf kafin Hafeez yafito kasancewar tasan qa'idar sa dukk weekend sai 11 yake fitowa dan haka tayi amfani da wannan damar tafice tanufi gdansu Meena. Balkisu na isa qofar gdansu Meena hakan yayi dai-dai da fitowar ta daga cikin gdnsu fuskar nan ta ta sha6e-sha6e da hawaye ga hannunta d'auke da bokatin alala, Balkisu naganin haka tayi saurin fitowa daga cikin motarta gami da kiran Meena! Meena da sauri tawaiwayo don ganin mai kiranta, wacce tayi tsammanin kuwa ita tagani dan haka ta tsaya kmr wacce aka shukata. Dasauri Balkisu ta rufe motanta ta isa ga Meena cikin muryan jajenta Balkisu tace" haba Meena mai yayi zafi haka a kullum nazo bana tarar dake sai kace wacce keqoqarin cutar dake look Meena yakamata kiyarda dani wlh Burina shine kawai inga cewa nataimaka miki sbd nariga nadauki alqawarin hakan"! Sadda kai qasa Meena tayi sannan ta d'ago takalli Balkisu da wani irin murmushinta mai ciwo, a hnkli Meena taja wani gauran numfashi sannan tace" tabbas baiwar Allah nagode da dukk wani qoqarinki akaina sai dai inaso kisani cewa bana buqatar taimakon kowa, plss naroqeki ki janye qudurinki akaina sbd dukk yadda kikaso haKan baxai faruba sbd wasu dalilai dasu ka kasance sirriina Dan haka na roqeki plss kiyi nisa daga cikin rayuwata gashi ina matuqar ganin girmanki" dasauri Balkisu ta tari numfashinta tace" plss Meena yakamata ki yarda dani inaso kisanar dani dukkan lbrinki sbd hakan ne kad'a xaibani damar sanin koke wacece da kuma yadda zansamu sauqin taimakawa rayuwarki domin jikina yajima yanabani wani abu daban.. Meena tagoge d'an guntun hawayen dake qoqarin zubo mata batare da takoma kallon Balkisu ba tajuya bayanta gami da cewa"na fad'amiki tun a lkcin baya cewa sanin lbrin rayuwata babu abinda zai qareki dashi nidai shawarata agareki kijanye dukk wani burinki nason taimakawa rayuwata nagode" Meena nafad'in haka tad'aura bokatin alalarta a kai taratsa gefen Balkisu tawuce. Balkisu tsayawa tayi sororo tana tunanin kafiya da taurin kai irin na Meena, "gashi bansan dalili ba a kullum zuciyata naqara azalzalata akan lallai na taimaki Meena, sai dai kash ga dukkan alamu

Chapter 3 of 10