Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Rafee'at am on ma way" Rafee'at tad'ago da idanuwanta Wanda sukayi rau rau alamar tanasonyin kuka, dasauri Hafeez yace no Rafee'at plss karmuyi haka dake karki manta cewa a dukk inda nakasance zuciyoyinmu natare da juna so pls stop worrn, ga waya i will always tray to call u kmr yadda nasa ba so plss no need to worry. Rafee'at tad'ago jajayen idanuwanta a hnkli ta sauqesu akan Hafeez cikin wata irin dushashiyar murya tace"wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka Haba my man yakake tunanin cewa baxan shiga damuwa ba karkamatanta cewa Kaine dukkan wani farincikina da walwalata kariga kasabarmin daganinka a koda yaushe ynxu kenan idan kayi wannan tafiyar sai dai kawai inkamajin muryanka? wasu zafafan hawayene suka dinga kwaranya a fuskar Rafee'at hakan kuwa baqaramin d'agawa Hafeez hnkli yayi ba. Dole Hafeez yadaurewa xuciyarsa ya shiga aikin rarrashinta dakyar yasamu tayi shiru, sannan yyi mata sallama ya nufi airport xuciyarsa cike da alhenin rabuwa da abinda yafi komai qauna. Hakanan Hafeez ya Isa cikin garen Lagos tamkar wani marar lafiya. Da isarsa kuwa Camp dinsu yanufa kai tsaye, yana xuwa yanufi dakin kwanansu, Hafeez sai da ya tabbatar yasamu ruwa ya watsa yayi sallahn azahar dinsa sannan yaxaro wayansa yafara kiran mutanen gda yana mai sanar dasu cewa ya isa lafiya. Sanda Balkisu ta Amshi wayan suka fara tadinga jansa da surutu gami da jero masa tambayoyi akan yadda garin Lagos din yake. Waje yafito yaxauna yana ta waya da Balkisu sai biye mata kawai yakeyi yakasa katse wayar, cikin hakan ne Rafee'at tayita kiran layinsa user busy har wajan awa daya Amma still busy Dan haka Rafee'at ta qufula sosai nan da nan tatura masa msg. Hafeez na cikin tsaka da waya yaji wata yar qara tashigo cikin wayarsa a hnkli yaxame wayar daga kunnensa don duba Wanda yaturo sak'on sunan Rafee'at yagani Dan haka da sauri yakatse wayar da yakeyi ya shiga inbox din don duba sak'on nata: ®NWA [11:49AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode7⃣ _tabbas my man jikina yana bani cewa tunkafin tafiyar tayi nisa zaka mance da wata Rafee'a da wakake yin waya haka? da har akasamu damar daukemin hnkalinka alhalin kasancewa zan nemeka tabbas zuciya ta tana cikin qunci_. Wannan saqo na Rafee'at baqaramin d'agamasa hnkli yayi ba, da sauri kuwa yashiga contact dinsa ya lalubo nmbn ta nan yafara kiranta. Wayan yayi ta ringing amma sam taqi d'agawa Hafeez kam bai fasa kira ba hakanan yyi ta kiranta koh Allah xaisa tad'aga amma daga qarshe Rafee'at kashe wayanta tayi, Hafeez nakira yaji swtch up.ae kuwa bai san lkcin da yayi wurgi da wayansa ba...Wata murya yaji kamar daga sama ance "fushi bai dace da kai ba. Kamata yayi kayiwa dukk wani da kake tare dashi uzuri kasancewarka mutum mai cikkiyar kalama, da sauri Hafeez ya d'ago kansa Dan ganin mai yimasa wannan shishigin, wata gajeriyar matashiyar yarinya yagani duqe a gabansa yayin da take qoqarin daukar wayarsa a hnkli tad'ago tamiqa masa wayar gami da yin murmushi tace" ni sunana Suhailat Mas'ud 4rm taraba state. Murmushin yaqe Hafeez yayi gami yimata godiya yasa hannu zai amshi wayarsa da Sauri ta janye hannunta gami da girgiza masa kai alamar A'a, Hafeez cikin mamakinta ya dubeta da alamar tambaya a fuskarshi? Suhailat tayi murmushi wnda kumatuta suka lotsa wani lumshe idanuwa tayi gami da cewa baka sanar dani sunanka ba gashi kana qoqarin amsar wayarka daga hannuna. 'Hafeez' kawai yace mata a d'an tak'aice, Suhailat tayi yar dariya har da buga k'afafunta cike da zolaya tace Mallam Hafeez wannan dukk fushi ne haka? Hafeez sororo yyi yana kallon zak'ewa irin na wannan yarinya. Dan haka tashi kawai yyi da nufin bar mata wurin, da sauri tasha gabansa tana fadin am srry sir! Ga wayanka afuwan, tana Miqa masa wayan tabar wajen cikin sauri. Hafeez kam d'akinsu yanufa, yana xuwa yafada bisa yar qaramar katifansa, wani uban tsaki yaja mtssw! 'Cikin Xuciyarsa yana maijin haushin d'abi'un wasu matan. Chan Kuma kamar Wanda aka tsikara daukar wayansa yayi yacigaba da Neman layin Rafee'ansa. "Hafeez dakyar yasamu layin Rafee'at yashiga xuwa ynxu har ta sauqo daga dogon fushinta, tadauki wayan cikin lumana Hafeez yyi mata bayanin cewa da Balkisu yakeyin waya ba da kowa ba.hakanan ya lallashi abarsa abinka da masoya tuni sunmanta komai. Abangaran Suhailat kuwa qarqashin wata darbejiya tasamu ta xauna taxuba wani uban tagumi, zuciyarta cike da kwad'ayin son sake ganin wannan kyakyawan saurayi domin "kuwa lkci daya Suhailat taji bata da wani abin so da qaunar gani face Hafeez" Tundaga wannan lkci ya kasance Suhailat tafara bibiyar Hafeez gami da cusa kanta a gareshi dukk da cewan bata ga alamun wargi a tattare dashi ba.Amma kullum tana cikin yi masa wasu yan d'awainiya. Zuwa ynxu kuwa kwalliya tafara biyan kudin sabulu domin kuwa Suhailat tafara samun Hafeez yadan fara kulata ba kmr da dayake yawan shareta ba. *Wacece suhailat* Suhailat kabeer Musa yar asalin jalingo ce cikin taraba state, mahaifin Suhailat wato Alhaji kabeer musa shahararren dan siyasane ya hau muqamai da dama anan cikin jaharsu, matansa biyu Zainab itace uwar gda sannan sai Saffiya itace mahaifiyar Suhailat. Suhailat ita kadai Allah yabawa mahaifinta kasancewar uwar gdansa bata haihuwa, shiya Saffiya da Alhaji Kabeer suka dauki son duniya suka k'wallafashi akan tilon yarsu, hakan yasa tuntasowar Suhhailat bata ta6a Neman abu tarasa ba shiyasa takeyin yadda taga dama, dukk wani gdan club dake cikin taraba babu wnda Suhailat bata sani ba.Kasancewarta mai yawan son chasu da kuma wasu yan shaye shayenta masu saka maye. Koh karatun da takeyi a ynxu kudi da Isa ne yasa take taka dukk wani matsayi datake son takawa acikin rayuwarta."Suhailat Tasha haduwa da samari kala kala wadanda take furta musu kalmar so wasu su amince don dukiyarta wasu kuma su amince don samun jikinta. Iya tsawon rayuwar Suhailat bata taba ganin saurayin da takeyiwa zazzafar qauna ba kmr Hafeez Wanda shikuwa bai ma san tanayi ba. Wannan kenan! ®NWA [11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode8⃣ Shak'uwar Suhailat da Hafeez a kullum k'ara ha6aka takeyi, yayinda Suhailat tacigaba da nunawa Hafeez tsantsar so da kulawa. Wanda abangaran Hafeez bai ta6a zaton abin haka yake ba. Rayuwa suke gudanarwa mai cike da fahimtar juna. Hafeez ne da Suhailat zaune bakin baranda suna hirarsu kmr yadda suka saba, Hafeez ne yadubi Suhailat yace sis nikuwa intambayeki mana. Suhailat tayi wani fari da ido gamida muskutawa tadubi Hafeez tace okay inajinka. Hafeez yyi gyaran murya gamida yin murmushi yace akwai wani abu dake dauremin kai agame dake, dammm!! Gaban Suhailat yabuga cike da fargaba tace"jst go street 2 ur qstn pls" Hafeez yace olryt dama abinda kedauremin kai shine naga kina amsa suna biyu wato Suhailat mas'ud koh Suhailat Kabeer, wata irin sassanyar ajiyan zuciya Suhailat tayi yyin da tuni gumi yagama wanke ta. Cike da fara'arta tace aff! Dama wannan ce tambayarka? Gyad'a mata kai Hafeez yyi gamida kallonta, Suhailat tayi murmushi tace"Ma'ud sunan wan mahaifina ne nataba zama a gdansa ashekarun baya so gsky yana matuqar jidani shiyasa wasu har suke zaton cewa koh shine mahaifina, Hafeez ya bude baki kenan da niyar qara jeho mata wata tambayar kawai sai phone dinshi yafar ringin da sauri ya zarota daga cikin aljihunsa' sunan da yasanyawa mahaifinshine ya bayyana akan screen din wayarshi"ABBA" da dauri yadauka gamida yin sallama. Abba ne keyiwa Hafeez mgn cikin nutsuwa yace "Hafeez kanajina? Cike da ladabi Hafeez yace inajinka Abba, Alhaji abdullahi yayi murmushi mai cike da dattijantaka. Sannan yace Hafeez jiya munyi magana da Mahaifin Rafee'at yanunamin cewa yana son ya aurar da diyarshi toh kasancewa xa'ayi birthday din yar'uwarka Balkisu shiyasa nayanke shawaran cewa ranar birthday dinta sai ayi engaged dinku kaga lkcin mutane suntaru sai ayi abu daya kowa ya shaida. Wani irin farinciki ne marar misaltuwa Yakama Hafeez baimasan lkcin da yayi wani tsallen farinciki ba. Cike da zumud'I Hafeez yace Abba komai yayi dai dai tabbas hakan ma yayi. Hafeez yanufasa yace Abba birthday din Balkisu on 28 ne koh? Abba yace"eh on 28 ne. Hafeez da qarfinsa ya furta yesssss! "Abba ne yace lfy kuwa? Hafeez yadanji kunya amma kasancewarsa tsayayyen namiji yace no Abba kawai naga abin ne yaxomin a yadda nakeso sbd on 27 zamu kammala komai namu mu mudawo gda. Abba ma da kansa yaji dadin wannan labarin sbd yana matuqar son kasancewa tare da d'an nasa. Dan haka yasamishi albarka gamida yimishi kyakyawan fata. Hafeez dai sai yak'e hakura yakeyi. Yayin da Suhailat tayi shiru tana kallon Hafeez itama sai murmushi takeyi, sbd tasan tabbas akwai abunda aka fadamishi Wanda yasashi farinciki. Hafeez naqare wayan yamaida dubansa ga Suhailat fuskan nan tashi d'auke da farinciki marar misaltywa, Suhailat tawani lankwashe kai gami da lumshe idanu a hnkli tasauqesu akan Hafeez tace "Hafeez mai yasanyaka farinciki haka"? Hafez yasake murmusawa yace "Suhailat I have a surprise 4 u, amma not now sai on 28. Cike da D'auki da Farinciki Suhailat tace olryt Allah yakaimu. Ameeeeeeen kawai yace, a hnkli yatashi Yakoma makwancinsa nan ya fara dialin numbn Rafee'ansa inda tadauki wayan sukayi tahiransu cike da kulawa da qaunar junansu. ®NWA [11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode9⃣ Hafeez ne sanye da kayanshi na NYSC wnda sukayi matuqar amsarshi, zaro wayarsa yyi wacce take gefen aljihun wndonsa. Numban Suhailat yakira wayan bata jima tana ringin ba Suhailat tadauka yace da ita yana son ganinta, cikin k'ank'anin lkci kuwa sai ga Suhailat gata ta baiyana agaban Hafeez. Cikin nutsuwa Hafeez yace yauwa Suhailat dama so nake muje kirakani kasuwa kinsan nafadi miki cewa za'ayi birthady din Balkisu da kuma surprise din da nace xan miki, so inaso kikaini shagon da xansamu kayan mata kmr su less da atamfa da sauransu kinsan tafiyan mu yana daf da gabatowa Cike da mamakinsa tarik'e ha6a tana kallonsa, cikin muryan zolaya tace a'a Hafeez waza'a ayima siyayya haka? "Hafeez yace ba nafada miki cewa I have suprise 4 u ba. So jst watch me, Suhailat ta gyad'a kanta gami da gyara wani dan yalolon gyalenta tadubi Hafeez da murmushi tace olryt mutafi am ready. Taxi suka tara ya kaisu wani tamfatsetsen shago dake cikin garin Lagos, da shigarsu Hafeez yafara yin abinda yakawosu wato zab'en kayan da yasan xasu matuk'ar amsar Balkisu, ita kam Suhailat tsaye tayi tana kallonsa dukk farinciki ya isheta. Hafeez ne yajiyo ya dubi Suhailat cikin zolaya yace Suhailat plss zabamin kayan da kikasancewa sunyimiki a matsayin zab'inki less material atamfa dukka kizab'amin choice dinki masu kyau, wani irin farinciki ne ya mamaye xuciyar Suhailat domin wani tunani nata na daban datasa acikin xuciyarta. Nan fa Suhailat tashiga za6en wasu danqara danqaran less masu kyau da tsadar gaske, da zarar Suhailat taza6o kayan sai tanunawa Hafeez tace "wannan yayi kuwa"? Hafeez kawai sai yace nidai kiza6amin kalar skin dinki wanda kikasan zai Amshi kalar jikinki. Nan fa Suhailat fara washe baki tana murna farinciki da jin kalaman Hafeez "Hakanan takasance dasu Hafeez har suka gama siyayyarsu suka koma masauqinsu" ************************* Yau yakasance ranar Saturday Wanda yayi daidai da ashirin da 27 ga watan Nowamba(27-November) hakan takasance ranar da wadansu daga cikin d'aliban xasu koma gda.. Hafeez ne tsaye agaban trolley bag dinsa, da ganin alamunsa tsaye yake yana jiran wasu. Suhailat ce tafito tsab cikin shirinta na dark blue din atamfa itama tafe take tana jan jakarta cikin sauri taqaraso gaban Hafeez tana murmushi , abinda Hafeez yafara tambayarta shine ya daddy ya amincewa tafiyarki kuwa? Suhailat tayi wata irin ajiyar zuciya tace wlh yabarni but yacemin only 2days ana gama birthday din inkoms gda, Hafeez yace woww vry gud har naji dadi, sbd ticket din mutum biyu nayi bookin. Airport suka nufa kaitsaye da xuwansu basu fi 30mnt ba jirginsu ya d'aga sai borno. Su Hafeez na sauqa drivansu na xuwa Dan haka shiga kawai sukayi suka nufi gda, suna cikin tsaka da tafiya sunxo daf dashiga anguwarsu wata akuya tadan gifta musu take anan drivan yadan ja birki da sauri Wanda hakan yyi sanadiyar zubowan kayan dake cikin handbag din Suhailat, waiwayowan nan da Hafeez zaiyi idanuwansa sukayi tozali da wasu munanan abubuwa wnda suka fado daga cikin jakar Suhailat. Cikin tsananin tashin hnkli Hafeez yazaro idanunsa gameda nunata. Dam! Gaban Suhailat yabuga. ®NWA [11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣0⃣ Gabadaya hankalin Suhailat ya gama tashi, nan take tafara had'a zufa dukk da kasancewar sanyin AC n dake ratsa kowanne sassa Na cikin motar. Cike da mamaki Hafeez ke dubanta ji yayi bakinsa ya masa nauyi murya qasa-qasa yace Suhailat miye wannan nake gani acikin jakarki? Dasauri "Suhailat tafara sosa kanta gamida neman mafita cikin in'enar mgn ta dubi Hafeez tace amm uhum! Ae kasan Rukky wacce muke daki daya da ita wlh itane take shan wadannan syrup da kwayoyin toh na hanata tak'i ji shiyasa nikuma nakwashe kayan mayen nata na boye ajaka, gashi Sam namanta banzubar ba am swryy plss. Suhailat nagama fadin haka Hafeez yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya gamida yin murmushi yace" huuu wlh Suhailat u really scared me!" Wani irin murmushi Suhailat tayi kai da gani kasan qaqaroshi tayi. Dasauri tasa hannu takwashesu tabude window da nufin ta zubar, Hafeez ne ya dakatar da ita yace"tabarsu anan cikin motar zai zuba su a shara. Suhailat kam shiru tayi gabadaya jikinta yayi sanyi hnklinta ya gama tashi,sbd gabadaya gani takeyi Hafeez yagama harbo jirginta. Qarar horn din da driva ya danna ne ya fargar da Suhailat daga dogon tunanin da ta tafi, kmr daga sama tajiyo muryan Hafeez yace Suhailat"mushiga daga ciki koh? Dasauri ta bude murfin mota jiki a sanyaye, ta ziro qafafunta jitayi gabadaya sunmata nauyi. A hnkli tafito suka fara nufar cikin gda. Ae kuwa sai ga Balkisu da gudunta tanufosu, jikin Hafeez tad'ale tamkar wata qaramar yarinya, oyoyoo yayana! Nan tabashi pick agoshi, a hnkli Balkisu ta maida dubanta ga Suhailat cike da zumud'i tasaki hannu Hafeez takoma wajen Suhailat wani murmushi Balkisu tayi tace kece anty Suhailat koh? Suhailat tadan saki fuskarta tadafa kan Balkisu tace eh nice Billy, Balkisu ta k'yalk'Yale da dariya jin ance mata billy, tadubi Suhailat tace anty Suhailat kema Billy xakicemin irin na uncle ma'aruf?.Hafeez ne ya ja hannun Balkisu yace oya parrot mushiga daga ciki am very eager to c my mum, da sauri suka shiga cikin falon gami da sallamarsu. Mahaifan nasa ne suka fito daga d'akinsu atare, cikin shigarsu ta alfarma kai dagani kasan yau rana ce ta farinciki a garesu. Da sauri Hajiya Hauwa tafito fuskarta dauke da fara'a, Suhailat tafara tarbo (kasancewar sunsanta awaya suna gaisawa, sannan Hafeez ya sanar da su zuwanta) Suhailat dukk farin ciki yagama dabaibayeta ganin yadda iyayen Hafeez suka tarbeta tamkar dama suntaba haduwa. Bayan sungama gaishe gaishensu da nuna farinciki da kewar juna, nan Hajiya Hauwa ta umarcesu da suje dining area suci abinci, Balkisu najin ance haka taja hannun Suhailat "anty xomuje nan taja hannunta Suhailat suka nufi dining, yayin da Hafeez yarufa musu baya tunkafin su zauna Balkisu keta zuba mata surutu" Suhailat kam wani irin son Hafeez ne ke qara shigarta ganin yadda families dinshi suka karb'eta hannu bibbiyu. Abincine kala kala aka tanadar musu, Suhailat dai tace sinasir take so ae kuwa Balkisu tazuba mata sinasir din mai yawa tace da ita sai tacinye nan dai akayita raha cike da so da qaunar junansu. Bayan sun kammala cin abinci ne Hajiya Hauwa ta umarci Balkisu da ta nunama Suhailat d'akin da zata kwanta, ae kuwa ba musu taja hannunta anty tashi muje. Suhailat dai biye take da ita tamkar rak'umi da akala, gabadaya Balkisu tagama shiga ranta yarinya gata kyakawa tamkar yayanta yarinyar akwai saurin shiga rai. Bayan sun isa cikin d'akin ne Balkisu tace anty ga d'akin nan kishiga toilet kiwatsa ruwa bari inje inhada miki coffee mai d'umi kisha. Kafin Suhailat tace wani Abu tuni Balkisu tafice. Suhailat murmushi tayi gamida girgiza kanta a hnkli tace Naughty girl. Toilet tafada tayi wnka sannan tafito. Tana fitowa Balkisu nashiga, batareda tace uffan ba ta ajiye coffee din a gefen gado tafice. Suhailat tayi murmushi takaici cikin zuciyarta tace "uhmm nimai zanyi da wani coffee ae ynxu buqata ta kawai insha kayan aiki(syrup) in wartsake gajiya mtsww" tanafadin haka tabi lafiyar gado ta kwanta batare da biyan sallolin da suke kanta ba. Abangaran mahaifan su Hafeez kuwa gabadayansu sunhallara a falo suna tsara yadda birthday din Balkisu da enggd din Hafeez zaikasance. Hakanan sukayita sharwarinsu har akayi kiran magrib Abba da Hafeez suka nufi masallaci yayin da Balkisu tanufi d'akin Suhailat don ta tasheta Sallah.Momy kam tuni tanufi sasheenta. Abba da Hafeez kam basu dawo gda ba sai da suka gabatar da sallahn isha'insu. Sannan suka nufi gda, sai da kowa ya hallara sannan sukanufi dining area sukaci abinsu, gabadayansu ranar raba dare sukayi sunata hirarsu cike da nishad'i, daga bisani ne kowa yanemi makwancensa. ®NWA[11:51AM, 10/15/2016] My Nabss: [5:03AM, 7/14/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣1⃣ Tunda sanyin asuba masu decoration suka bugama Hajiya Hauwa waya cewa gasunan K'ofan gda batare da b'ata lokaci ba tayi musu Iso, masu decoration nan sukafara aikinsu gda yadauki haske da kyawun gaske. Sai da Hajiya Hauwa ta tabbatar da cewa angama gyara gdan tsaf sannan takoma sashinta, bayan ta idar da sallah sannan tashiga toilet ta watsa ruwa. Tana idar wa ta zauna gaban dress mirror ta tsara kwalliyarta tamkar wata budurwa. Sashen Abba tanufa koda shigarta ta tarar yana toilet murmushi kawai tayi, kai tsaye tanufi wardrop dinsa tafitar masa da wata shadda galila mai matuqar kyau da sheqi, tana gama zab'a mishi sai gashinan ya fito fuskan nan d'auke da murmushi cikin muryan rad'a yace yan matana kinyi kyau, Hajiya Hauwa tayi murmushi Wanda hak'uran makkanta suka bayyaina, cike da zolaya Abba yace "a'a irin wannan kwalliya haka? Ashe kwalliya ake tsaramin shiyasa yau ba'a tashemu zuwa massalaci ba? Hajiya Hauwa tayi yar dariya tace"yau Alhaji na lura yan zolaya ne akanka. A'a wanne zolaya ae ba zolaya yau din ne naga kinfi koyaushe kyau, "nagode tace masa yayinda take k'okarin barin d'akin. Koh da fitarta d'akin Hafeez tanufa shima ta tashesa sannan tanufi d'akin da Suhailat take bayan ta tasheta sannan tawuce d'akin uwar gayyan. Koh da Hajiya Hauwa tashiga d'akin Balkisu ta tarar da Ita zaune bisa sallayah tana sharar hawaye, cikin tsananin damuwa da tashin hnkli Momynta qarasa kusa gareta a hnkli ta jawota jikinta tace"Balkisu lfy kuwa? Balkisu Wanda kuka yaci k'arfinta ta k'ara rungume momynta tanaci gabada kuka, Hajiya Hauwa batayi yinqurin Hana takukan ba sbd batasan mine dalilin yinsa ba. Balkisu sai da tayi kuka mai isarta sannan tad'ago tadubi mommynta cikin sark'ewan murya tace Momy Dan Allah kiyafemin dukk laifuffukan danayi miki, da sauri mommy ta tallabo fuskar Balkisu ido cikin ido takalle cike da kulawa tace "haba Balkisu meyaparu haka me akayi miki haka karfa kimanta cewa yau ranarkice yakamata ace yau kinfi kowa farinciki meyaparu dake kike kuka,? Balkisu tadubi mommyn nata fuska araunane tace wlh Momy nikaina narasa dalilin wannan kukan nawa kawai dai yau inajin tamkar wani Abu mummuna zai faru dani, Momy tayi murmushi tace "Balkisu kenan insha Allahu babu abinda zaifaru ki kwantar da hanklinki tashi kije kishiga wanka. Jiki a sanyaye tace to mommy,ba wani gardama ta tashi tanad'e sallayan da tayi sallah' sannan tashiga toilet don ta watsa ruwa. Hajiya Hauwa kam falo tanufa tana jiran iyalen sufito suga decoration din da akayima falon. Basu wani jima ba dukkaninsu sukafito tsab cikin shirinsu na alfarma, bayan sunhallara afalon ne Hajiya Hauwa ta lura ba Suhailat cikinsu Dan haka tadubi Balkisu tace"Balkisu jeki kirawomin Suhailat" toh kawai tace Balkisu tamik'e da nufin taje Hafeez yadakatar da ita yace kiyi zamanki barin je infito da ita. Hafeez yanatafe yana waya da Rafee'ansa awaya. Abangaran Suhailat kuwa tun lkcin da Momy ta tasheta taje tayi Sallah bata tashi ba sai ynzu. Shiyasa sai ynxu tafito a wanka tasanya wani Riga da wando mai zubin fakistan kalar lemon green da orange kayansun matuqar amsarta zamatayi akan chair din dake gaban dress mirror tazauna tafara tsarawa kanta kwalliya, bayan tagama tak'urawa kanta ido domin kuwa tasan cewa ita kanta tahadu dan haka cikin zuciyarta tace" Suhailat kiyi matuqar kyau sannan yaune yadace kisanar da Hafeez sirrin zuciyarki da kuma BURINki nason aurenshi dix is d ryt tym da zaki fadamishi" k'wank'wansa k'ofan da akeyine yadawo da ita daga dogon tunaninta. A hnkli tace yes com in! Murd'a k'ofan yayi yashiga gamida sallamarsa, Suhailat ta amsa masa da murmushinta kasancewar ta gane muryanshi cike da zumud'i Suhailat tajuyo damm! Gabanta yafad'i domin Hafeez ba qaramin burgeta yayi ba domin sai a ynxu ne ma tagano aenahin kyawunsa. Akasalance ta gaida Hafeez..Hafeez bai amsa mata ba har sai da yagama waya. Sannan ya maida dubansa ga Suhailat tace a'a Suhai irin wannan kyau haka karfa kihadawa mazan Borno go slow, murmushi Suhailat tayi tace wlh kai dai kafaye zolaya wallahi Hafeez yayi murmushi gamida zuba hannayensa cikin aljihun wndonsa yace kiyi sauri Momy najiranki lkci na qoqarin wuce, Suhailat tad'anyi fari da idanuwanta tace okay badamuwa ganinan zuwa amma kafin nan Hafeez pls inaso infada maka wata muhimmiyar mgn, Hafeez yace olryt ba damuwa amma kibari anjima zamuyi mgnr ynxu inada Wurin zuwa kokin manta nace zanyi suprsn dinki? Wani irin farinciki ne yakama Suhailat tace olryt badamuwa inajiranka. Okay yace mata adan tak'aice sannan yafice daga d'akin, yana fita falo yasanar dasu gatanan fitowa sannan yace yatafi ya dauko Rafee'at don ta halarci birthday din. Hajiya Hauwa tayi murmushi tace toh Hafeez" plss kada kaje kayi zamanka kana zuwa kad'aukota kujuyo sbd afara prgrm in dawuri kar mubatawa guest dinmu lkci, "insha allahu Momy ynxu zanje nadawo. Yanafadin haka yafice a falon. Suhailat ce tafito cikin wani irin taku nata tamkar mai tausayin k'asa haka taqaraso cikin falon sannan tagaida Momy da Abban, Balkisu ce ta taso daga inda take zaune taqarasa wajen Suhailat tazauna sannan tace gud murng my Anty, Suhailat najin dadin yadda Balkisu ke bata kulawa, a hnkli tace billy am fyn ya shirye shiryen birthday? Balkisu tace gashinan munayi kinga yadda mommy tasa aka gyara falon? Suhailat tace nagani wlh falon yyi matuqar kyau. Suhailat tace yauwa baki fadamin ba how old ar u now? Balkisu taji kunyan tambayr Suhailat din, dariya tayi gamida rufe fuskanta tace am 13yrs old today. Suhailat ta tafamata tace very gud billy. Suna cikin haka sai ga sallamar Hafeez tare da Rafee'at sunshigo, Rafee'at sanye take da hijabinta hakan yyi matuqar fitar da ainahin kyawunta, Hankalin Suhailat gabadaya yagama tashi ganin Hafeez tare da wata kyakyawar yarinya sunjero a tare sunayima junansu murmushi wani irin azababben kishi ne ya turnuk'e Suhailat, Da shigarsu Rafee'at taduqa har k'asa cike da ladabi ta gaishesu gabadayansu kowa yana farincikin ganin Rafee'at amma banda Suhailat wadda tayi duqu duqu da rai kmar zata fashe sbd tsananin kishi., Suhailat da Rafee'at suna hada ido rass!! Gaban Rafee'at ya buga wani irin kishi taji marar misaltuwa domin kuwa ta tabbata itace Suhailat din da Hafeez kebata lbri ynxu a hnyarsu ta zuwa. ®NWA [11:51AM, 10/15/2016] My Nabss: [12:49PM, 7/14/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣2⃣ Wani irin azababben kishi ne ya turnuk'e Suhailat, sanin da tayiwa knta cewa bata da control yasa tayi saurin barin falon tanufi d'akin da yakasance masak'inta, da shigarta ta banko k'ofa da gudu tanufi kan gado tana maida wani irin numfashi mai wahalar fita. Tana cikin wannan halin ne taji ana k'wank'wasa k'ofa shiru tayi batace komai ba Wanda ke k'wank'wasa wan jin ba'a tanka masa ba yayi tunanin koh ba mutum cikin d'akin bude k'ofan yayi a hnkli ya zura kansa gamida cewa Suhailat! Jin muryan Hafeez yasa tayi sauri mik'ewa daga kwance da take"tace na'am, da fara'a kuwa d'auke a fuskarsa yak'arasa ciki yayin da Rafee'at ke biye dashi fuskan nan nata adaure tamau! Hafeez nashiga ciki yace yauwa Suhai yau zanbaki surprise dinki, dama sonake in nuna miki matar aure na wannan itace zan aura sunanta Rafee'at kuma ayaune insha allahu za'ay enggd dinmu after birthday din Balkisu. Dam! Gaban Suhailat yabuga hnklinta yatashi wani irin kishi ne ya gama sark'eta take anan tafarajin gari Na yawo da ita dasauri takoma bisa katifa tadafe kanta Wanda ke tsananin sara mata, dasauri Hafeez ya matsa daf da ita yace"Suhailat lafiya kuwa?" Wani irin murmushi ta k'ak'aro tace no bakomai kainane ke d'an saramin, plss inba damuwa inaso zanyi mgn da kai,kai dai. Rafee'at najin Suhailat tace haka kafin ma Hafeez yace da ita wani abu tuni tabar d'akin zuciyarta kmr zata fito sbd tsananin takaici da kishin Hafeez. Rafee'at nafita a d'akin Suhailat tamik'e tsaya idanuwan nan nata gaba daya sun rine zuwa jaa! Cikin tsananin masifa gabadaya idanuwanta sun gama kullewa " tace amma wlhy Hafeez kaci amanata ka yadudareni. Ashe dama kanada wacce kakeso shine baka tab'a bani damar fahimtar haka ba' toh kasani hakan dakayiwa zuciyata ba k'aramar illah kayimata ba domin kuwa sonka yayi min rami mai zurfin gaske acikin zuciyata, Adalilin son da nake makane yasa nabiyoka izuwa garinku ashe bansani ba kai kana da wacce kake so nikuwa koh oho koh? Tsananin Mamaki ne qarara d'auke a fuskar Hafeez cikin tsanin tashin hnkli yasa hannu yadakatar da Suhailat daga sambatun surutan datakeyi masa' dakata Suhailat plss stop dix jokes of urs irin wannan wasan baidace dake ba Sam domin kuwa ni amatsayin yar'uwata nadaukeki nabaki muhalli irin na Balkisu acikin rayuwata so plss stop dix nonsense! Ran Suhailat gabadaya yagama b'aci tadubi Hafeez da raunannun idanuwanta tace wlh matsayinka yawuce dukk yadda kake tunani acikin zuciyata ni matsayin mijin Aure nadaukeka kuma dukk wani mahaluk'I danake tare dashi yasan da haka, sai kai kad'aine zakacemin baka lura da irin kulawa da tarairayar da nake baka ba? Ran Hafeez ma gabadaya yagama b'aci a fusace yace olryt nagode da kulawarki gareni amma kisani Rafee'at itace BURIN HAFEEZ ita kadai nake so ita nakewa soyayya ta asali da

Chapter 2 of 10