Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bana tunanin nima zan amince ko nayimata dole". Hafeez nafadin haka ya tashi yakoma daga cikin d'akinsa dan basu waje sud'an tattauna A hnkli Dr Muh'd yatashi daga inda yake yakoma gefen Balkisu cikin tattausar muryansa yad'an duqa daf da ita yace "toh Balkisu miye ra'ayinki agame da tayina ko ince buqatata? Balkisu kam dukk kunya ta isheta qara duqar da kanta qasa tayi,murya na rawa kmr wacce zatayi kuka tace " a'a ni ina ganin baidace na amsa tayinka ba domin kuwa wani 6angare na sashin zuciyata nasanar dani cewa kawai tausayina ne aranka da kuma son taimakamin ganin cewa Yaya Hafeez yayi aure matuqar nima nayi. Da sauri Dr Muh'd yace ko kusa Balkisu karki kawo wannan gur6ataccen tunanin cikin zuciyarki, wlh soyayyarki ta gsky ce acikin jini da 6argona yakamata ace tuntunima kinfahimci hakan wlh Balkisu believe me when I said banta6a son wata d'iya macce ba kmr ki ina miki wani irin so Wanda ni kaina yana bani tsoro plss kitaimakawa zuciyata nan yashiga yimata magiya Ganin yadda ya marairaice fuska kmr zaiyi kuka yasa Balkisu tace "to shikenan na amince ku gama mgn da yaya Hafeeez tana fadin Haka ta tashi da sauri tashige d'akinta gami da banko k'ofa direct gadonta tafad'a tanajin wani irin nishad'i marar misaltuwa na shigarta. Abangaran Dr Muh'd kuwa hannu yad'aga sama yana jero adduo'i na farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga ubangiji, yana gama addu'ansa d'akin Hafeez yanufa yayi knckn Hafeez ya amsa yes shigo jiki narawa Dr Muh'd yashiga cikin d'akin wani irin farinciki da nishad'i yake ji nashigarsa da sauri ya rungumi Hafeez yace " yes abokina adduar danajima inayi yau Allah ya amsamin Balkisu ta amince ynxu amincewarka kawai nake jira. Murmushi Hafeez yayi cikin zolaya yace congrat namaka murna, ynxu kabari idan muka gama tattaunawa da ita Balkisun zankiraka awaya muqarasar da mgnr, Dasauri Dr Muh'd yace "wacce mgn za'a gama ae ynxu angama komai tunda madam ta yarda ynxu kawai izininka nake nema sbd ina so inturo magabata na, Hafeez kam jiyayi gabansa yafad'i da sauri yace olryt karka damu I will giv u a call let Cike da zumud'i cikin fara'a Dr Muh'd yabar gdan. Hafeez kam gabad'aya yashiga damuwa jiyayi wani irin rashin sukuni ya ziyarcesa Dan haka da sauri yanufi d'akin Balkisu dan yanuna mata cewa shikam bai amince da wannan chakwakiyar ba. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [3:11AM, 7/27/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣3⃣ A hanzarce Hafeez yanufi d'akin Balkisu don ya nuna mata rashin aminciwarsa akan wannan tsarin deal din da takawo mai cike da rud'ani, a hnkli ya murza kofar d'akin jin bud'e take yasa yashige d'akin kaitsaye turuss ya tsaya cike da mamakin ganin Balkisu cikin wani yanayin dabai ta6a ganinta ba. Balkisu kwance take ta kife cikinta ta yayin da tad'an d'aga kafafunta tana lilasu earpies ne a kunnenta tana merming waqa cike da nishad'i" soyayyaa tayi mamaya tayi charaf ta chafkemin zuciya nasamu saurayi madubin duba inata murna" murmushi Hafeez yayi gabad'aya ji yayi jikinsa yayi sanyi a hnkli yafice daga cikin d'akin batare da tasani ba, falo yakoma yazauna gabad'aya tunanin mafita Hafeez Yake nemawa kansa amma dukk hnyar dayabi sai yaga cewa ya tauye dukk wani farinciki na qanwartasa, kan Hafeez yagama kulewa gabad'aya jiyayi bashida wata mafita ko dubara domin kuwa BURIN HAFEEZ shine yaga tilon qanwar tasa cikin farinciki dan haka komai xai iyayi dukk runtsi dan ganin ya inganta farincikin Balkisu. Take anan Hafeez yakira layin Dr M yasanar dashi cewa yanason ganinshi zuwa gobe, Dr M yayi farinciki dajin wannan kira dan haka addu'a kawai yyi yana maifatan Allah yakaimu goben. Abangaran Balkisu kam wani irin sabon yanayi taji nashigarta kasancewar dukk wunin ranan nan suna maqale da juna awaya ita da gwarzon likitan nata. ** ** ** Balkisu ce zaune cikin motarta tana zaman jiran dawowar Meena daga talla kasancewar yau Monday ta je skul shiyasa bata samu damar zuwa wajan Meena da wuri ba sai ynxun. Balkisu ta6ata kimanin awa biyu zaune cikin mota sai zabga uwar hamma takeyi, agogon dake d'aure bisa tsintsiyar hannunta take dubawa qarfe daya saura a hnkli tasauqe wata irin ajiyar zuciya, kmr ance d'ago kanki ae kuwa chan tahango Meena tafe da bokatin alalarta. Dasauri Balkisu taja motarta cikin sauri taqarasa wajan Meena a hnkli tayi parkn motarta daf da Meena, zuge glass din motar tayi a hnkli cikin rashin karfin gwiwa takira sunan Meena, da sauri Meena tajuyo ganin Balkisu ce mai kiran nata yasa tayi saurin niyyar barin wajan, da sauri kuwa Balkisu tafito amotarta gamida shan gaban Meena cikin raunatacciyar muryanta tace Meena plss ki dakata kisaurareni koh da sau d'ayane daga wannan baxan sake takuramiki ba namiki alqawari, zuwa ynxu gabad'aya Meena tagama tsorata da Balkisu jiki na 6ari Meena tace Dan Allah baiwar Allah ki kyaleni haka naroqeki da sauri Meena ta ratsata gefenta da nufin ta wucewarta, cikin sanyin jiki Balkisu tace "olryt Meena kije karki saurareni amma na tabbata kinfi kowa muradin son ganin mahaifiyarki tafito a gidan kaso, da sauri Meena tajuyo fuskarta d'auke da mamaki qarara. Murmushi Balkisu tayi tace " yes Meena nasan komai a gameda lbrinki babu wani 6oye 6oye ynxu daya rage a tsakaninmu, wlh kiyarda dani banida niyyar cutar dake hasalima nidake nakeson muhad'a kai mutaimaki juna, Meena tamaimaita abinda Balkisu tace mutaimaki juna?? Kmr ya mutaimaki juna? Balkisu tace "kwarai kuwa,kuma hakan nidake gabad'aya zai amfanemu, Murmushi Meena tayi tace " anya kuwa kinyi dogon nazari akan wannan maganar taki? Balkisu tace ae ynxu kece zanbaiwa damar yin tunani akan mgnr danaxo muki da ita. Meena ta gyara bokatin alalarta ta fuskanci Balkisu tace" okay fadi mgnr naji Allah yasa zan iya" Dafa kafad'arta Balkisu tayi cike da qarfin gwiwa tace no karki damu insha allahu hakan bazai gagareki ba. Balkisu tadubi Meena tace inba damuwa inason kizo mushiga daga cikin mota ta hakan zaifi sirri, dasauri Meena tad'ago tadubi Balkisu, Balkisu tamaqe kafad'a tace yadai ko dai har ynxu baki gama yarda dani bane? Meena ta girgiza kanta tace a'a ba haka bane mujee. Cikin motar Balkisu suka shiga Meena jitayi wani irin sanyi yaratsata a hnkli tadubi Balkisu tace inajinki kiyi sauri kada namakara. Balkisu tadubi Meena sannan tad'auke dubanta daga gareta tafuskanci gabanta, Sannan takira sunan Meena bayan Meena ta amsa sannan tasake cewa kinsan menake so dake? Meena ta girgiza kanta tace a'a sannan Balkisu tajinjina kanta a hnkli tasauke idanunta akan Meena tace "so nake ki auri yayana, da sauri Meena ta gwalo idanu waje gamida dafe kirji tace mekikace? murmushi Balkisu tayi domin batayi mamakin ganin Meena tayi shock dajin buqatarta ba, Balkisu tajinjina mata kai tace tabbas abinda kikaji shinafad'a inaso ki auri yayana domin inason ganin sauyi da farinciki a tattare dashi, da zaran kinyimin haka nikuma nayi alqawari konawa ne zankashe domin na d'aukaka qara ganin cewa Mahaifiyarki tafito daga gdan yari, sannan inaso karki manta cewa nasan komai agamedake basai kinyimin wani dogon bayani agameda matar babanki ba namiki alqawarin zanji da komai kedai kawai nabaki nan zuwa gobe kije kiyi tunani Gobe da yamma zandawo domin naji shawaran dakika yanke. Balkisu nafadin Haka tabudewa Meena qofa cikin sanyin jiki Meena tafice daga motar yayin da Balkisu kuma ta wuce tanufi gda nan tabar Meena tsaye cikin tunani. Note: akan masu complain cewa banason yin typn da wuri inaja muku rai, wlh sam bahaka bane karku manta fa cewa nabaku uzurina plss kumin afuwa insha allahu zanqoqarta nagode. ®NWA [11:54AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣4⃣ Cikin daren ranar Meena kasa runtsawa tayi, babu abinda take tunawa sai ranar da tafara had'uwa da yayan Balkisu irin yadda yanuna mata kyankyami da tsantsar tsana qarara a fuskarsa, dan haka tasan tabbas a zaman auransu xata cutu sai dai kome xainuna mata xa ta iya shanyewa sbd lura da tayin da bashine da kansa yaxo neman auranta ba hasalima qanwarsa yaturo to komiye dalilinsa nayi haka? Nan fa tafara jeroma kanta tambayoyi wnda ita kanta batada amsarsu. A ynxu kam gabad'aya tunanin Meeena yatafi akan yadda rayuwarta zata kasance a hannun wanda bai ko kaunar ganinta gashi kuma a wani 6angare tana buqatar mahaifiyarta kusa da ita, Dan haka ta gama yanke shawaran amincewa auransa don tasamu damar taku6utar da mahaifiyarta daga gdan kaso. Da wannan shawaran aranta har bacci 6arawon yayi awon gaba da ita. ** ** ** Washe gari kafin kowa ya tashi a gdan Meena tariga kowa tashi kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne tafara ayyukanta kafin qarfe 6 kuwa Meena tagama ayyukan ta tsaf, ruwan sanyinta tad'iba tashiga bayi ta watso ruwa, bayan tafito ne tadauki tallan kunun gyad'anta tanufi chan Bolori primary skull inda chan ne Meena zata had'u da Balkisu. A bangaran Balkisu kuwa ita ma sauri kawai take tayi sbd bata son ta had'u da Hafeez kasancewar tasan sai yayi ta jero mata tarin tambayoyi akan wacce take son had'ashi aure da ita, gashi ita kuma basu gama mgn da Meena ba Dan haka bata da kwakkwarar amsar da xata bashi, hakan ne ma yasa tayi tunanin tad'aga appointmnt dinsu wnda tace su haduwa da yamma tamai dashi zuwa da safe. Kafin Hafeez yafito kuwa tuni Balkisu tafice a gdan, Bolori primary skul chan tanufa a niyyarta dama intaje tasa yara sunemo mata Meena tunda dama nan ne wurin sana'arta, Balkisu nashiga skul din ba tawani sha wahalan neman Meena ba hangota tayi zaune ta rafka uban tagumi. Meena! Meena!! Kmr a mafarki taji ana kwala mata kira dasauri tayi firgigit ta juya, Balkisu tahango zaune cikin motarta dasauri Meena tamiqe tanufi wajanta. Murmushi Balkisu ta sakar mata sannan suka gaisa da junansu daga bisani tayi mata ixinin shiga cikin motar, a hnkli Meena tabud'e murfin motar tashiga. Jan motar tayi cikin nutsuwa suka bar gefen makarantar chan wata anguwa suka nufa, sai da Balkisu ta tabbatar sund'anyi nisa sannan tayi parkin, Da murmushi d'auke a fuskar Balkisu ta dubi Meena tace "toh Meena kmr yadda kikaji nace miki zanxo domin naji shawaran dakika yanke toh gani nan na iso gareki don jin shawarar da kika tsaida shin kin amince kuma kinshiryawa auran yayana?? Meena ta sadda kanta qasa hawayene kawai keta kwaranya cikin sanyin murya tace na amince da auransa matuqar xankasance tare da mahaifiyata. Balkisu tajinjina kai tace dakyau amma kinsan dalilina nason ki auri yayana? Meena ta girgiza kai alamar a'a Ajiyar zuciya Balkisu tayi sannan tamaida dubanta ga Meena gabad'aya idanun Balkisu sunrine izuwa ja! Cikin natsuwa takawo lbrin rayuwarsu tasanar da Meena, nan Meena tashiga jinjina al'amarin cikin zuciyarta tana mai tausaya musu sai dai kuma yadda taji lbrin Hafeez ta tabbata cewa kawai tad'auko ma kanta dala ba gammo ne amma kuma inta tuna mahaifiyarta sai taji wani irin kwarin gwiwa na shigarta. Balkisu tadubi Meena tace tabbas na yaba da kyawawan d'abi'unki da yadda kika iya maida mgn ga masu hali irin na yayana hakan yasa na tabbata cewa zaki iya dawo min da Yayana normal kmr yadda yake a lkcin baya. Murmushin yaqe Meena tayi sannan tadubi Balkisu tace "Allah dai yabani ikon cikamin alqawarinki sbd naga kinsa hope dinki akaina sosai, Balkisu tad'anyi yar dariya tace "Meena kikwantar da hnklinki kedai kawai kisa aranki daga gobe zuwa jibi muna iya xuwa a kowanne lkci gdnku dan neman auranki sannan inaso kada kifadawa kowa wannan mgnr har sai komai yakankama, cike da jin kunya Meena tace insha allahu. Meena har tabud'e kofar motan da niyyar tafita Balkisu takira sunanta, cikin natsuwa Meena tajuyo.Balkisu tace " aff namanta intambayeki yau mekike sai dawa ne? Meena tace kunun gyad'a ne. Balkisu tad'anyi murmushi kmr yadda hakan yaxama jiki agareta sannan tace" gabad'aya kunun na nawane? Meena tace na d'ari biyar ne zaro dubu biyu tayi ajakarta tamiqawa Meena sannan tace gashinan kiyi sadaka dashi haka har zuwa gobe kiyi manejin wannan bnfito da kud'i bane. Da farko Meena tanuna kin amincewarta sai da Balkisu tad'an lallamota sannan tasamu ta ansa. Direct gdan mallan Zakiru Balkisu tanufa don cika alqawarinta kmr yadda tafada mishi cewa dukk halin da ake ciki agame da Meena xataxo tasanar dashi (mgnr lectures kam yau bbu ita)hakanan ta juya akalar motarta izuwa gdan mallan Zakiru. ®NWA [1:14PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:37AM, 7/29/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣5⃣ (Very sorry readers nayi mistake din numbr nasa 23 sau biyu makin nasa 24 nayi mistk ynxu 25 xamu tashi) Kamar kullum yau ma ya kasance mallan Zakiru na nan cikin Zaurensa yana bitar karatu alqur'ani, da sallama Balkisu tasa kai cikin zauren tare da neman izinin shiga, cikin nutsuwa Mallan Zakiru yakai qarshen aya sannan ya rufe qur'anin ya ajiye agefensa, cikin sakin fuska yayi mata Iso Mai d'akinsa mallan Zakiru yashiga yakira dan takawo masa taburma, Inna takawo taburman tana qoqarin shimfid'awa Balkisu tayi saurin amsa ta shimfid'a tabarman, bayan ta xauna sannan suka gaisa sannan Inna, ficewa Inna tayi tabasu waje kmr yadda tasaba in mallan yayi baqi bata zama. Balkisu tadubi Mallan Zakiru fuska d'auke da murmushi kai dagani kasan tana cikin farinciki, "tace Baba kmr yadda na sanar dakai cewa dukk yadda ake ciki a game da Meena zansanar maka wato naafad'a mata inasone ta auri yayana ynxun nan muka gama mgnr da ita sannan ta amince zata aureshi nikuma nayi mata alqawarin bayan bikinsu zanfito da mahaifiyarta a gdan yari. Mallan Zakiru yyi murmushin jindadi yace "Masha allahu' Allah sarki Aminatu allah ya sanya alkhairi, Balkisu ta amsa da ameeen daga bisani Mallan Zakiru yadubi Balkisu fuska d'auke da damuwa yace "amma kmr yaushe ne kike xaton zaku turo magabatan ku don neman auran Aminatu? Balkisu tace "toh baba muna so mu tsaida ranan ne tukun, mallan Zakiru yajinjina Kansa sannan yace toh wacce shawara kika yanke agameda tunkarar Yagana don niman auran Aminatu? Balkisu tace Baba karka damu inaso ne in angama ajiye mgn d'aya zamu turo qanin mafaifinmu sbd in.... kafin Balkisu ta qarasa abinda take son cewa Mallan Zakiru yace "Sam kada kiyi haka sbd dukk cikin garin nan bbu wnda baisan waye mahaifinku ba nikuwa nafi kowa sanin cewa muddin Yagana tagano cewa Aminatu gdan masu hali zatayi aure toh fa baxata amince ba.Sbd dukk wata hanya da tasan zatabi don ganin cewa ta lalata wannan auran toh fa zatayi Kuma babu wnda ya isa yadakatar da ita, Dan haka inaso kibar komai a hannuna sannan kitabbatar da cewa cikin qanqanin lkci zakusa lkcin auran don gujewa fitina. Balkisu tad'anyi jimm! Sannan tadubi Mallan Zakiru sannan tace amma Baba kana ganin ta wacce hanya zamu bi? Mallan Zakiru yyi murmushi yace zansamo wani daga cikin kauyanmu inyimata nuni da cewa shine Wanda yakeson ya auri Aminatu amma fa dukk wani wakili ko waliyi Na ango zaifito ne daga 6angaranku. Nan Mallan Zakiru ya tsatssara ma Balkisu matakin da zasubi don gujewa sharrin Yagana Kwarai da gaske Balkisu taji dadin shawarwarinsa ae kuwa nan tayi taxu bawa Mallan zakiru godiya, tana mainuna jindadin taimakonsa gareta. ** *** ** *** Qarfe hud'u Na yamma na bugawa Dr Muh'd na isa gdnsu Balkisu don cika umarnin Hafeez kmr yadda yabuqaci ganinsa. Hafeez kam yau through out bai ko fita bakin get ba yana nan cikin d'akinsa yana sana'ar tashi wato tunani, kwan kwasa k'ofar dayaji anayine yadawo dashi daga duniyar tunanin da yatafi, a hnkli yamiqe batare da yace komi ba yanufi k'ofar bud'ewa yayi Dr Muh'd ne yagani tsaye cikin dakakkiyar shaddarsa mai kyan gaske sai wani zuba qamshi yakeyi, Hafeez yadubi Dr Muh'd har yaso yabashi dariya sai kuma yabasar hannu yamiqa masa suka gaisa sannan Hafeez yace dashi yaje Falo yad'an jira gashinan zuwa Dr Muh'd kam cike da zumud'i ya nufi falo yazauna dan jiran Hafeez Toilet Hafeez yashiga ya sakarwa kanshi ruwa yajima a haka daga Bisani kuma ya silla wankansa, qananan kaya Hafeez yasaka blue riga da baqin wando dukk da cewa Hafeez baifiye son qananan kaya ba amma yau su yaji yana muradin sawa turare mai dadin gaske ya fesa sannan yafice a d'akin. Falo ya nufa kaitsaye yana shiga kuwa ya tarar da Dr Muh'd na nan zaune yana jinran fitowarshi, murmushi Hafeez yayi ya girgixa kansa. Bayan sund'an tattaba hira sama sama' Hafeez ya dubi Dr Muh'd jiki a sa6ule yace "amm abokina wato dalilin da yasa nace kazo ina neman ka yau shine inason inji daga gareka shin kashirya auran Balkisu? In kashirya wa auran inaso nan zuwa gobe kaje chan sabon fege gdn uncle Ma'aruf kasanar dashi dukkan wani jawabi dakake tafe dashi akan auran Balkisu. Hafeez nafad'in haka ya sadda kanshi qasa cike da damuwa da qunar zuci, dasauri Dr Muh'd yamatsa kusa dashi a hnkli ya dafasa yace "tabbas abokina nasan kana cikin damuwa da alhenin rabuwa da tilon qanwarka amma kasani zaman Balkisu a gurina tamkar tana hannunka ne insha allahu nayimaka alqawari baxan ta6a cutar da qanwarka ba, zan riqeta amana tamkar kaine awajan sbd inason Balkisu sosai inayimata so Wanda baxan iyaganin abinda zai cutar da ita ba. Da sauri Hafeez yarungume Dr Muh'd yana kukan farinciki sannan yace "nagode maka abokina sannnan inaso kasa aranka cewa Balkisu amanace a hannunka sannan inaso idan zaiyuwu a d'aura auranku cikin wani sati if possible" Dasauri Balkisu taqaraso cikin falon fuskan nan sha6e sha6e da hawaye cikin muryan kuka tace haba Yaya Hafeez aure na nikad'ai nakeji kana mgn banji kana mgnr naka auran ba, karka manta da alqawarinmu sbd nariga nasamo ma nagartacciyar mata Wanda nake da hope din cewa zata kularmin da yayana yadda yakamata. Rasss! gaban Hafeez yafad'i, shidai bai San mieyasa Sam baya qaunar yaji anyi mishi mgnr wata d'iya macce ba, balle kuma harta kai ga mgnr aure. Jiki a sanyaye Hafeeez ya maida dubansa ga Balkisu yace "wai wacece wannan yarinyar dakike son Na aura wacece ita a ina kika santa ya akayi kikasan tana da nagartaccen hali meyasa kike son tilastani nayi aure?' a jere Hafeez ya watsoma Balkisu tambayoyi?" ®NWA [1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:52AM, 7/30/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣6⃣ D'ago Jajayen idanunta tayi Wanda suka rine sbd kuka, a hnkli ta sauk'esu akan Hafeez, wani irin kukane ya sake kubce mata Wanda ita kanta batasan dalilin yinsa ba, cikin dishashiyar muryanta tace "Yaya Hafeez karka ta6a tunanin cewa auran wacce nakeson had'aku zai zama cutarwa ko danasani a gareka wlh kayarda dani cewa nafi amincewa auran Meena atattare da kai" Meena!! Hafeez yamaimaita sunan da sauri k'urawa Balkisu idanu yayi gabad'aya sai yaji tabashi tausayi, gashi akan wannan Meenar da ta dage dole ne yaga cewa yadaure ya aurenta mutuqar hakan zai sata farinciki da walwala. Dasauri ya miqe tsaye daga zaunen da yake jawota yayi jikinsa ya rugumeta nan yashiga bubbuga bayanta cikin sigar lallashi, cikin murya qasa qasa Hafeez yace kwntar da hanklinki Billyn mama na amince zan auri dukk wacce kika kawomin ita matsayin matar aure, amma sai dai I have one request 4 u, k'ura mishi idanu Balkisu tayi alamar shi take saurare dasauri ya janye jikinsa daga nata sannan yaci gaba da mgn "na amince zan auri yarinyar da kikeson kawota cikin rayuwata sbd inada yaqinin cewa bazaki ta6a had'ani da wacce bata dace da rayuwata ba, sai dai kuma inaroqonki plss kada kitilastamin zuwa d'aurin auren sbd hnkli da kwakwalwata bazasu iya jurar ji ko ganin cewa wai yau nike aure ba plss kisamu komawaye ya wakilceni sannan dukk abinda kikaga yadace kawai kiyi nabar miki wuqa da nama" Hafeez nafadin haka yayi sauri yabar falon cike da d'acin rai. Jikin Balkisu gabad'aya yayi wani irin sanyi, a hnkli Dr Muh'd yaqaraso gareta cikin muryan lallashi mai nuna tsantsan tausayi ga masoyiyar tashi, nan fa ya xage damtse yayi ta tausar zuciyar cikin hikima da kwarewa, sai gashi kuwa cikin qanqanin lkci ta manta da komai. A Bangaran Hafeez kuwa d'aki yashiga ya kulle kansa ji yayi gabad'aya duniyar tamasa xafi. ** ** ** ** ** Kmr yadda Mallan Zakiru yayi ma Balkisu alqawari haka kuwa akayi yaje can qauyansu yasamo wani matashin saurayi dake aikin faskare. Abangaran Dr Muh'd shima yaje yasamu ya gana da qanin mahaifinsu Hafeez, wato uncle Ma'aruf, uncle Ma'aruf kam bayan binciken daya qarayi akan hallayan Dr Muh'd yasamu kyakkyawan yabo hakan yasa ya amince domin yafi kowa farinciki dajin lbrin. Dan haka cikin qanqanin lkci aka sanya lkcin bikin Hafeez da Balkisu Mallan Zakiru da kansa yaje har wajen Yagana yasanar da ita cewa d'an uwansa ne Wanda yaxo daga qauyansu yaga Meena yakuma nuna cewa yana son auranta, Yagana tayi farin ciki jin ancemata daga noma sai faskare sune aekinsa koshi faskare da noman aekatau dinsu yakeyi ana biyansa dan haka kenan su Meena za'a sha noma wani irin farin ciki ne ya lullu6eta datagama wannan tunanin, Dan haka batare da 6ata lkci ba tanuna amincewarta. Mallan Zakiru yyi matuqar farin ciki da hakan domin kuwa hakarsu daf take da cimma ruwa. Komai ya kankama yan'uwa da abokan arziqi anfara hallara, gwaggwanin su Balkisu da mamaninta dukk sunzo nan suka fara gyara diyar tasu Balkisu tafito fasss da ita baqaramin kyau tayi ba. Bangaran Yagana da yarta kuwa kullum basu da aiki sai gori da kyarar Meena wai tarasa Wanda xata jaju6o musu sai d'an kauye kauyan ma futuk nan fa zasu taru suyita dan gware tama kai.Meena kam ko uffan bata cewa dasu domin ita tunaninta a kullum bai wuce yadda zata kasance a wani gda a matsayin matar wani ba,sabuwar rayuwar da zata shiga kullum shike addabar tunaninta. Plan din Mallan Zakiru da Balkisu komai Na tafiya yadda suke so da taimakon ubangiji. RANAR DAURIN AURE Ranar juma'a da misalin qarfe biyu na rana bayan ansauqo a masallaci aka d'aura auran HAFEEZ ABDULLAHI SHARIFF tare da AMINATU SULEIMAN akan sadaki dubu hamsin, inda kuma suka sake garzayawa aka sake d'aura auran BALKISU ABDULLAHI SHARIFF tareda DR.MUHAMMAD SHU'AB GASHU'A an d'aura auransu akan sadaki dubu d'ari. *** Dubu uku Mallan Zakiru yacira daga cikin sadakin Meena yakaiwa Yagana yace gashinan wannan shine sadakin Aminatu, zokaga farinciki awajan Yagana nan fa ta sokare kud'in a ha6ar zaninta A cewar Yagana tunda Meena takala futuk ta aura to miye zata siyamata tunda dai d'an kudin da Meena kesamowa yaqare a kudin hayarta dan haka baxata siyamata komai ba. Da misalin qarfe hud'u na yamma Mallan Zakiru ya je gurin Yagana wani tsadadden material da sarqa da yan kunne da takalmi da kyale set komai yayi match kayan sun matuqar haduwa, Balkisu ce ta aikomishi tace yabawa Meena idan anzo d'aukar amarya tasanya ajikinta. Hakan yasa Mallan Zakiru yakawo kayan dan ciki alqawarinta. Yagana naganin kayan dake hannun Mallan Zakiru dukk tabi tawani rud'e, miqa mata kayan yayi yace "Yagana ga wannan kayan daga hannun mijin Aminatu sukafito yace dan Allah atabbatar da tasa wannan kayan zuwa an jima sannan kisanar mata cewa kartabari kokadan kayan sulalace sbd arosu yayi daxarar ta isa gdnshi ciresu xatayi yamaidasu inda ya aro, wata irin dariyar k'eta Yagana tafara dukk farinciki yabi ya lullu6eta. Hakanan akayi shagalin biki a bangaran Balkisu da Dr dinta, sa6anin Hafeez wnda ya kulle kansa cikin d'aki. Misalin qarfe tara na dare wasu irin manya manyan motoci tsadaddu ne sukayi fakin a k'ofar gdansu Meena, da sauri wata gwaggonsu Hafeez tashiga gdan Cikin shiga ta kece raini dukk da kasancewar dare ne amma shigar da tayi kallo d'aya zakayimata kasancewa an narka daloli. Yagana kam tabawa Aminatu kayan tasa baqaramin kyau sukayi mata ba, ganin tayi kyau abinta yasa Yagana dukk haushi ya isheta nan tashiga dangwarar kanta tanayimata gori sai wani kusheta takeyi. Ana cikin hakane Gwaggon Hafeez Hajiya Nana tashiga domin tafiya da Meena. Ae kuwa gabad'aya kan Yagana yad'aure shuru kawai tayi tana kallon ikon Allah azatonta dukk wad'annan manyan matan suma hayarsu akayi, al'amarin bai qara tsinkar da Yagana ba sai da tabisu zuwa waje taga wasu irin dan qara dan qaran motoci Wanda sune suka zo d'aukar amarya Meena. Yagana tanaji tana gani aka sanya Meena cikin mota sakeke tayi da baki cike da mamaki domin ita takasa gane wannan Al'amarin jitayi andafata da sauri ta juya Hajiya Nana ce cikin sigar lallashi take lallama Yagana domin ita a tunaninta Yaganan tana cikin alhenin rabuwa da diyarta ne, nan taciro dubu hamsin tamiqawa Yagana. Cikin mota takoma sukaja take anan sukabar cikin unguwar. Yagana na ganin haka ko gyale babu a jikinta balle takalmi haka tanufi gdan Mallan Zakiru cike da masifa domin kuwa bakin nan nata taf yake da tambayoyi Wanda babu mai amsamata su sai Mallan zakiru. ®NWA [1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:47AM, 7/30/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣7⃣ Jiki Na 6ari haka Yagana ta shiga gdan Mallan Zakiru ko sallama babu ta afka musu cikin gda, dai dai lkcin Mallan Zakiru yafito daga bayi hannunsa riqe da buta yana kiran mai d'akinsa ta kawo mishi abinci, Mallan Zakiru sai ji yayi ance "toh algungumi munafiki azzalumi mai sai da yaran mutane" da sauri Mallan Zakiru yajuyo danganin mai mishi wannan alkaba'iran Yagana yagani tsaye ko mayafi babu balle takalmi ta wani riqe qugu sai

Chapter 5 of 10