Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Meena bazata ta6a bani had'in kai ba. Nan Balkisu tashiga tunanin taya za'ayi tasan lbrin Meena, gashi dai tasan cewa dukk yadda taso taji lbrin Meena baxata ta6a fara tunkarar Yagana ba. Cikin mota Balkisu tashi tazauna d'aukara kanta tayi bisa sitiyarin motan gabad'aya tunaninta ya kwance babu abinda take tunani face mafitar wanda zata tunkara. Kmr wucewan wasu yan'mintina Balkisu tad'ago da kanta da sauri wani irin murmushin farinciki tasakar wa kanta da sauri tace yess! Wannan shine kad'ai mafita, wuta tabawa motarta da sauri tafice a layin ta hau titi. Baifi tafiyar minti 2 ba tayi parkn motarta gefen hanya da sauri tafito ta tsallaka titin tanufi daya site din. Wurin Baba mai shayi tanufa, ko da isarta bata iske shi ba wasu yan samari guda hud'u ta iske sunata firar kwallo(ball) da sallama Balkisu ta isa garesu, gabad'aya suka amsa mata, cikin natsuwa Balkisu ta gaishesu bayan sun amsa sannan tace Dan Allah ina Baba maishayi wnda ke sai da shayi wurin nan? Daya daga cikinsu yace Allah sarki baba zakiru mai shayi kike nufi? Ae yau tsawon sati d'aya kenan bai fito gurin sana'a ba sbd ciwon qafa yasashi agaba. Balkisu tayi jimm! Tana jinjina al'amarin cikin ranta, chan tace Allah sarki Dan Allah koh zan iya sanin gdnshi? Wanda keyi mata bayanin yace eh ae bbu nisa. Nan yyi mata kwatance. Balkisu tayi musu godiya sannan tanufi motarta tajuya zuwa inda akayimata kwatancen, Balkisu batayi mamaki dan ganin cewa layi daya suke da su Meena ba, sai dai Mallan Zakirun gdnsa nafarkon shiga cikin kwanar, wanda sukuma Meena gdnsu nad'anda nisa tsakaninsu. Gdan da wadannan samarin suka kwantanta mata nan tanufa, shigatayi kaitsaye da sallamarta. Wata mata ta tarar tsakar gdn tana sassaqa wani itace dagani kasan magani ne, da sauri matar tadubi Balkisu cikin nuna rashin sani ta amsa sallamarta sannan tasaki fuskarta gami da cewa "sannu da zuwa baquwa iso daga ciki", Balkisu tayi farinciki da hakan ganin yadda yar dattijuwar matar ta tarbeta. Shimfid'amata tarbuma tayi sannan ta umarceta da tazauna, Balkisu nazama tagaida dattijuwar matar cike da ladabi. Cikin fara'a kuwa ta amsa sannan tace "sai dai bangane fuskar ba?" Balkisu tayi murmushi tace hakane Inna dama nasamu lbrin Baba zakiru bashida lafiya shine nazo naduba jikin nashi, murmushi tayi tace Allah sarki sannunki kinji angode sai dai mallan din baya gda yatafi ganin likitan gargajiya anan wani qauye sai zuwa anjima da yamma zai dawo, Balkisu tagyad'a knta tace toh shknan badamuwa Allah ya bashi Lpy ni zanwuce gobe in Allah yakaimu zandawo. Hakanan tafice a gdn tanufi gda tana mai addu'ar Allah yasa tasamu abinda take nema agarshi. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [7:04AM, 7/21/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣8⃣ Washe gari da sassafe Balkisu tafito tsaf cikin shirinta Na baqar doguwar jallabiya da d'an guntun hijabinta pink colour, dukk da cewa batayi wata doguwar kwalliya ba amma tayi matuqar kyau. Falo ta nufa sannan takira Daniel tasanar dashi irin brkfst din da xai had'a wa Hafeez, sannan takoma ta sanar dashi cewa bada ita zai had'a brkfst din ba. Hakanan Balkisu tafice batare da taci komai ba, domin a daren jiya da zarar Balkisu ta rufe idanunta Meena kawai take gani dan haka dakyar taga gari ya waye mata. Da fitarta kuwa bata nufi ko ina ba sai Bolori anguwansu Meena, "wannan karon Balkisu bata nufi gdnsu Meena ba k'ofar gdan Mallan Zakiru ta tsaya, A hnkli tafito daga cikin motarta ta nufi gdn Mallan zakiru, cikin zaurensa ta tarar dashi zaune yanata karatun al-qur'ani, jiki a sanyaye tayi masa sallama. Mallan zakiru na kaiwa qarshen ayaa! Ya tsaida karatunsa gami da amsawa Balkisu sallamarta cikin sakin fuska Fuskan nan d'auke da fara'a yace baiwar Allah shigo daga ciki, Cike da qarfin gwiwa Balkisu tashiga cikin zauren, tana qoqarin zama a qasa kenan mallan Zakiru yace haba ke kuwa yazaki zauna a qasa da wayonki? Balkisu tayi murmushi tace laaah! Baba wlh bakomai, Mallam Zakiru yace a'a ba'ayi haka ba d'an dakata, nan yashiga kwalama uwar d'akin nasa kira bayan ta amsa yyi mata umarnin takawo tabarma, cikin qanqanin lkci kuwa sai gata tafe da tarbama. Da zuwanta ta shimfid'awa Balkisu tabarma sannan suka gaisa amutunce Wanda bayan sungaisane daga bisani takawo mata ruwa sannan ta tashi takoma daga ciki. Balkisu taji dadin karamci irin na gdn Mallan Zakiru hakan kuwa yaqara bata qarfin gwiwar tinkararsa da tambayoyin da take qunshe dasu, Dan haka byn ta jajanta mishi ciwon qafansa, yace da sauqi, taqara daurawa dacewa Allah yabashi Lpy yasa kaffarane. ameeeeeeeen yace yanamai yin murmushi zauren yayi shiru na wasu yan mintoci can Mallan Zakiru yace "ae jiya mai d'akina take sanar dani cewa nayi baquwa tayi tayi mini misalinki amma Sam nakasa ganewa sbd Sam bantaba tsammanin kece ba amma ynxu dana ganki natabbar lkci daya cewa kece kika zo nemana jiya, Balkisu tayi murmushi tace Allah sarki, eh wlh haka ne nice Mallan Zakiru yadubi Balkisu da kyau yace Baiwar Allah lafiya kuwa?Balkisu ta gyara zamanta tafuskanceshi dakyau tace tabbas lfy dama naxo inyimaka wata yar tambayane, Mallan Zakiru yajinjina kansa yamaimaita abunda tafada "tambaya"? Balkisu tagyad'a kai alamar eh, Mallan zakiru yace toh Allah yasa nasani. Balkisu tad'an ja numfashi a hnkli sannan tace dafarko dai sunana Balkisu Abdullahi Shariff nazone inaso inyimaka wata yar tambaya akan rayuwar Meena inhar kasani. Sbd tun ranar da muka hadu da yarinyan nan Allah yasamin tausayinta araina naji zuciyata na azalzalata a ko da yaushe akan nataimaka mata, toh amma sai dai yarinyar kwata kwata taqi amincewa dani balle ta yarda dani na taimaka wa rayuwarta, da ita nake kwana nake wuni araina Dan Allah idan kasan wani abu dangane da rayuwar yarinyan nan toh ina roqonka da kasanar dani, wlhy bani da niyyar cutar da ita hasalima inason taimaka matane. Mallan zakiru yayi murmushinsa cike da dattijantaka, sannan yace" tabbas yarinya bakiyi kama da miyagun mutune masu cutarwa ba hasalima nasan waye mahaifinki marigayi Alhaji Abdullahi, Balkisu najin haka tayi murmushi farinciki tace eh hakane. Mallan Zakiru yace tabbas zanfadamiki ko wacece Aminatu, amma da sharad'i guda daya" Balkisu ta dan muskuta kadan tace Baba kafadi kowanne sharad'i ne insha allahu zanbi sharud'anka. Mallan zakiru yace madallah, dama sharadin nawa shine inaso kimin alqawarin cewa dukk wani abu dakikaji dangane da lbrinta hakan bazaisa kijuya mata baya ba?? Balkisu tace insha allahu nayimaka alqawari, Mallan Zakiru ya jinjina kansa sannan yadubi Balkisu...... ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:13PM, 7/22/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode1⃣9⃣ Mallan Zakiru yaja dogon numfashi mai cike da alhenin tuna abinda yajima yana damun zuciyarsa, a hnkli ya sake kallon Balkisu sannan yace "Wato mahaifin Aminatu Mallan suleman Wanda akafi sani da Sule, abokina ne shi tun tsawon shekara ashirin da suka gabata. Asalinsu yan Gwaza ne nan cikin jahar borno, Sule yakasance aminina tun awajen sana'armu ta gyaran kekuna da mashin anan babban get na Monday market, Sule nada mata daya Rabi wacce itama yar garinsu ce da aurensu atare muka gansu. Mallan Sule yakasance mutun mai son mutane gashi Allah yadaura masa son yara, sai dai kuma babban abunda ke damunsa shine yadda suka dauki tsawon shekaru goma sha biyu amma Sam Rabi ko 6atan wata bata ta6ayi ba. Hakan yasa Sule yayi tunanin qara aure, Rabi kuwa Sam bata tashi hnklinta ba kasancewarta macce mai sanin yakamata Sam batada yawan hayaniya, ana cikin hakane Sule ya auro Yagana, Allah cikin ikonsa Yagana nashiga cikin gdan baifi da wata uku ba sai ga d'an qaramin cikinta ya baiyanna. Ana cikin wannan hali sai ga Rabi itama cikin hikima da kyauta ta ubangiji sai gashi itama tasamu nata rabon, wai karkaso kaga farinciki awajan Sule. Abangaran Yagana kam abun ba haka yake ba, domin babu irin masifar da batayi ba wai Rabi munafukace dama tana haihuwa shine dantaga tasamu ciki wato itama shine takwaso nata sbd gasa. Haka nan kwanaki sukayi ta shud'ewa yayin da Yagana ke azabtar da Rabi batare da sanin shi abokin nawa ba, Gashi a kullum Yagana nayimata barazanar zata kasheta a dukk lkcin da ta kuskura tasanar da mijinsu irin abubuwan da take mata. ** Bayan wata tara Yagana ce tafara haihuwa tasamu d'anta namiji aka sha biki, bayan wata biyu itama Rabi Allah yasauqeta lafia inda itama tasamu diyarta macce wato Ameenatu. Haka nan sukaci gabada zama na rashin jindadi mussaman ma ita Rabi wacce take hak'uri da hallayar Yagana. Dukk wani hali na qunci da azabar da Rabi ke sha abokina Sule sam bashi da masaniya akai". Ana cikin hakane watarana muna cikin tsaka da aikin kanikan cinmu wani bawan Allah yakawo mana gyaran mota, Wanda mukuma bamu fiye son gyaran motociba sbd bamu kware da gyaranta ba, amma awannan ranar cikin ikon Allah sai wani bawan Allah yakawo mana gyaran motarshi Sule ne yakarba yadan soma gwada gyaranta. Dakyar Sule ya gano inda matsalar motar take, wato lagireto din motan ne yasamu mtsl dole Sule yaje yanemo "jak" wato abin dake d'aga mota, hakanan yasamu nadan taimaka masa yasa jak din motar tadantashi daga bisani kuma yasamu yashiga karkashin motan, Suleimanu na cikin tsaka da aikinsa wannan motan tayi kuskuran fadamishi a kirji,. 'Mallan zakiru yadan goge hawayen da yaxubo masa sannan ya cigaba da cewa" dasauri ma'aikatan da muke wajan muka kawo mishi taimakon gaggawa nan da nan muka samu muka d'aga motar daga kirjinshi, nan fa muka tari texi domin mukaishi asibiti amma kankace wani Abu rai yayi halinsa Allah yakar6i ran abinsa. Awannan lkcin Ameena naqarama bata mallaki hanklin kanta ba, ayayin da d'an yagana wato bakura shima yana qarami ga Yagana da tsohon ciki. Haka wannan mummanan al'amari yafaru da mu, domin a gsky a wannan lkcin na jima banji irin mutuwar da tashigeni ba kamar ta Sule Wanda hakan yasa tundaga wannan ranar banqara jin sha'awar wannan sana'a ba wannan shine musabbabin dayasa nakoma sana'ar sai da shayi. Mallan Zakiru yadan yi shiru cike da jimami yadubi Balkisu yace " Balkisu nayi rashin babban amini. Balkisu ta jinjina kai gabadaya tausayi yacikata. Mallan Zakiru yacigaba da mgn, " wato bayan sati biyu da rasuwar Sule sai ga wani sabon tashin hnkli Yagana taxo dashi wai ita a dole sai anraba gado tunda tanada d'a namiji ga kuma wani cikin ae tasan dukiyarta sai tafi yawa, awannan lkcin kuwa Sai da yayan Sule yashiga cikin mgnr. Nan ne yake tambayar Rabi ko ta amince araba gadon ynxu ko kuwa sai yaransu sundantaso, nan Rabi ta nuna ita dai abarshi zuwa lkcin da yaran suka mallaki hanklinkansu inyaso a wannan lkcin abawa kowa nasa. Ae fa nan Yagana tayi taya6awa Rabi maganganu marassa dadinji. Ranar wata alhamis ne muka sami wani mummunan lbri Wanda ya girgiza al'umar dake cikin wannan anguwa tamu. Domin kuwa Yagana cikin dare ta tashi takashe d'anta da hannunta sannan ta yayyaga rigar jikinta tayiwa kanta wasu tambari naciwuwuka tamkar ansameta an yayyageta da wuqa. Ganin tasamu nasara yasa tanufi d'akin Rabi ta ajiye gawar yaron sannan tafara ihuun neman agaji dasauri mutanen anguwa suka farka, kowa yyi shiru yana sauraren inda wannan ihun kefitowa. Bayan kowa ya fahimci cewa a gdansu Yagana ne ake wannan ihun hakan yasa jama'ar anguwa kowa yanufi chan dan ganewa idonsa. Koh da shigarsu cikin Gdan gabadaya jikin Yagana a yayyanke da wuqa ga kuma yaro kwance cikin jini, ae dasauri suka shiga don axaton jama'a barayine suka shigar musu. Amma da shigar jama'a cikin d'akin sai ga Rabi da wuqa a hannu dukk tarikice yayinda ita kuma Yanaga ke ta neman ceton jama'a. Ganin mutane suntaru yasa Yagana tacigaba da kuka tanafadin "shikenan Rabi kincika burinki naganin kin hallaka d'ana sbd kina baqin cikin gadon da wannan yaron zai samu, Hakanan Yagana takawo lbrin qarya tasanar da jama'a cewa Rabi ce takashe mata d'a sannan itama tayi qoqarin kasheta wai sbd gado. Rabi kam mamakine ya baiyyana qarara a fuskarta, wasu irin hawaye masu ciwo ne suka dinga bin kuncin Rabi tunfaruwar wannan al'amarin kuwa Rabi ko uffan takasa Cewa sai hawayen kawai datake ta xubarwa.... Kafin wayewar gari kuwa yan sanda suka zo sukatafi da Rabi police station Wanda daga baya kuma aka kaita koto bisa hujojin qarya aka kai Rabi gdan yari amatsayin daurin rai da rai. Haka wannan mgnr takarade cikin anguwa da sauran kewaye, wasu sun yarda jin cewa Rabi tayi kisan kai yayin da wasu kam basu yarda ba, sai dai Wanda sukafi yarda sune sukafi rinjaye. Hakan kuwa yasa mutunen anguwa suke nuna halin kyama da gujewa Aminatu hakan yayima Yagana dadi tasamu yadda take so. Bayan wasu yan kwanaki da faruwar wannan rikitaccen al'amarin Yagana tahaihu tasami diya macce, dukk da cewa ba haka taso ba. Dukk wata tsangwama da kyarar da Yagana keyima mahaifiyar Amina shine tadawo dasu kan Amina, inda take gana mata azaba kala kala tun Amina batayi wayo ba har ta girma ta fahimci duniyar datake ciki, sbd mutanen anguwan nan tamu gabadaya suntsaneta suna ganin cewa itama inta girma halin uwarta zatabi na kisan kai Mallan Zakiru ya fyace majina sannan yashare hawayensa yadubi Balkisu yace " kinsan wani abun mamaki kuwa"? Balkisu ta girgiza kanta tace a'a baba sai kafada. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣0⃣ Mallan zakiru yacigaba dacewa "wato yadda naga Aminatu nashan wahala tun tana yar qarama hakan yasa nayi tunanin cewa bari ind'aukota tadawo hannuna da zama, kasancewar nima har wannan tsufan yariskeni mai d'akina bata ta6a haihuwa ba.hakan yasa na shawarci mai d'akina akan mgnr d'auko Aminatu, hakanan itama ta nunajinddinta akan shawaran dana yanke. Shiyasa da wani yammaci nashirya naje gdan, inazuwa gdan natarar da Yagana nadukan Aminatu kmr wadda Allah ya aiko, da sauri na k'waceta daga hannunta bayan haka ban tsaya sauraren komai daga gareta ba nanuna mata cewa inason zantafi gdana da Aminatu takoma chan da zama. Kafin ma naqarasa abinda nakeson cewa Yagana tabuga wani uban salati nan tashiga kurma ihuu tanafadin "yau nashiga ukuuu ni Yagana wato Zakiru irin cin amanar da zakayiwa babban amininka kenan? Ana cikin haka sai ga jama'ar cikin unguwa suntaru danjin bahasin ihuun da takeyi, nan fa Yagana tashiga basu lbrin qarya wai zuwa tayi ta iskeni tsakar gda ina qoqarin yiwa Aminatu fyade wa'iyaxubillah" wato Balkisu tunda nake arayuwata ba'ta6ayimin sharri Wanda ya girgizani ba kmr Wanda Yagana tayimin. Jama'ar cikin unguwarmu kowa sai alawadai da irin halina yakeyi Wanda yagana ce taqaqaba minshi, wani irin tashin hnkli nashiga marar misaltuwa Dan haka cikin sanyin jiki najuya da nufin natafi gda amma Yagana ta ziga samarin anguwan nan tamu dasu rakani gda da ihuuu! Haka kuwa akayi yara da yan samari suka bini sunatayimin ihuuu wnda hakan yyi sanadiyar nafarajin wani irin hajijiya na yawo dani cikin rashin Sa'a inatafiya qafata ta kufce tafada cikin wani rami dakyar nasamu nacireta gabadaya qafartawa takumbura sbd ramin qarami ne, toh fa tundaga nan ne nahadu da ciwon qafa. Daga rana irin ta wannan lkcin ko gaisuwa bata shiga tsakanina da Aminatu bawai Dan inatsoran Yagana ba a'a sai dai inatsoran sharrin da Yagana zatakoma qaqabamin ko kuma Aminatu. Tabbas wasu sunfara fahimtar hali irin na Yagana shiyasa dukk rintsi dukk wuyan da Amina Zatasha babu mai kai mata d'auki gudun kar tayiwa mutun sharri domin Yagana tadaurawa mutum sharri ba komai bane agurinta. Shiyasa kowa ke gudun taimakawa Amina. Ana cikin hakane Yagana tatsiro da sabon iskaci na azabtar da Aminatu, da farko idan ta daura mata talla dukk abinda Aminatu tayo ciniki sai yagana tace bazata sammata kudi ladan guminta ba ko tasiyamata wani Abu sbd Amina hayatakeyi acikin gdanta, hakan yasa dukk randa Amina batayi ciniki ba toh ranar awaje zata kwana sbd batayi ciniki sosai ba balle aciri kudin hayarta. Dukk irin sanyin da akeyi akan Aminatu yake qarewa, sannan dukk wani aikin gdan itakeyin shi kama daga wanke-wanke shara wankin Yagana da na yarta girki zuwa wasu aike kuma komai nisan waje Aminatu da qafa zataje babu Wanda ya isa yataimaka mata, idan Amina tasamu tayi wad'annan ayyukan shine takesamu taci abinci a dukk lkcin kuma da Aminatu bata samu damar yin d'aya daga cikin ayyukan gdan ba toh awannan ranar batada abincin rana ko nadare koda kuwa rashin lafiya tayi. Mallan Zakiru nafadin Haka yafashe da kuka, Balkisu ce ma tayi qarfin Halin bashi hkri. Mallan Zakiru yadubi Balkisu yace "wlh Balkisu tunda nake arayuwata bantaba ganin mata marar imani kmr wannan matar ba, yarinya ace ita da gdan ubanta sannan ace wai tana haya sannan abincin da zataci sai tayi aikatau a gdansu, wannan al'amari na matuqar damun zuciyata. Gashi Aminatu tun da girma yarisketa yan samari sukafara zuwarmata manema auranta amma Yagana sai tayi tsaye tace musu ae yarinyar babu abinda ta iya sai kisa da yawace yawace, hakan yasa dukk samari suka fara gudunta sbd ko ba komai tarihi yanuna cewa mahaifiyar Aminatu na gdan Yari. Mallan Zakiru yyi murmushi yace kinji wannan shine d'an taqaitaccen tarihin Aminatu iya Wanda nasani, sannnan abinda yasa kikaji dazu na kafa miki sharad'in kada kigujeta shine kar labarin Yagana ya wargazamiki lissafi kema kigujeta kamar saura. Balkisu ta share hawayen da yagama wanke mata fuska tace " baba ko kadan babu haka acikin raina dukk da kasancewata yarinya mai qarancin shekaru hakan bazaisa na Gaza tunkarar Yagana ba, domin a ynxu danaji lbrin Meena sai naji gabadaya wutar son taimaka mata nadad'a ruruwa acikin raina. Baba Sam kada kadamu nayi alqawari insha allahu sai na ku6utar da Meena daga cikin wannan qangin rayuwan sbd a ynxu wani irin Tausayinta ne yaqara tasiri acikin zuciyata. Mallan zakiru yace "nikuwa insha allahu zantsayamiki zankasance dake a dukk lkcin da kika buqaci taimakona sannan zandage dayimiki addu'an samun nasara ba dare ba rana. Balkisu tayi murmushi mai sauti gabadaya farinciki ya lullumeta dajin kalaman mallan zakiru. Bayan sungama tattaunawarsu Balkisu tamiqe sannan tadubi Mallan Zakiru tace "toh baba ni zan tafi gda dukk yadda ake ciki insha allahu zanke sanar da kai" nan fa mallan Zakiru yayi tasawa Balkisu albarka. Hakanan Balkisu tanufi gda zuciyarta acinkushe babu abinda take sai tunanin yadda al'amarin zai kasance mussaman abangaran Yayan nata, dan haka a ynzu a shiryetake da ta tunkaresa da dukkanin buqatunta Dan ganin ta tarwatsa dukk wani BURI Na yayanta Dan kawo canji acikin rayuwarsa. ® NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣1⃣ Balkisu na isa gda qarfe sha biyu na rana na bugawa dai- dai. dan haka sashenta kawai tanufa kai tsaye, koh da shigarta saman gadonta tahau sharaff! Takwanta gabad'aya dukk ji takeyi tagaji. Chan tayi nisa cikin tunani sai jitayi cikin ta na mataguqi alamar yunwa na nuqurgusarta da sauri ta tashi tafice daga d'akin dinning area tanufa tea tahadawa kanta mai kaur sai soyayyan kwan da tad'iba da plan10 falo takoma taxauna sannan tafara bawa cikinta hakkinsa. Balkisu Na daf da kammala brkfst dinta sai ga Hafeez yafito daga cikin d'akinsa sanye da farar jallabiya d'akin Balkisu yayi niyyar zuwa har yanufi hanya kmr ance yajuyo sai hango Balkisu yayi zaune cikin falo, wata irin sassanyar ajiyar zuciya yayi wanda hakan yajawo hnkli Balkisu tajuyo, Hafeez tagani tsaye sakar masa murmushi tayi tana fadin Yaya har kafito? A hnkli Hafeez yaqarasa cikin falon tsare Balkisu yayi da idanunsa sannan yace Balkisu inakikaje ne tundazu dana farka nanufi d'akinki amma bakya ciki? Kuma nalura dake acikin kwanakin nan kina yawan fita ina kike zuwa?? Balkisu shiru tayi gabadaya tarasa amsar da zata bashi. Ganin bata da niyyar cewa komai yasa Hafeez yanemi waje yazauna qara kallon Balkisu yayi fuskan nan ba alamar wasa yace "ke badake nake mgn bane kinmin shiru? Balkisu gabanta ne ya shiga dukan tara tara bama uku uku ba sbd kalaman da bakinta ke qoqarin furtawa batasan yadda yayan nata Hafeez zai d'aukesu ba, a hnkli tad'ago kanta tadubi Hafeez da raunatattun idanuwanta cike da faduwar gaba Balkisu tafara mgn cikin sanyin murya "Yaya kagafarceni amma yazama dole ne intunkareka da wannan mgnr dukk da bnsan da wacce irin siga zaka kalli batuna ba, Hafeez yayi murmushi gabad'aya jiyayi Kansa yakulle domin kuwa yasan cewa qanwar tasa da wani abu mai muhimmanci take tafe, tunanin haka ne yasa Hafeez yadubi Balkisu cikin sigar lallashi yace oyaa qanwata go on ke nake saurare kifadamin dukkanin damuwarki namiki alqawarin zan magance miki ita matuqar bata fi qarfina ba. Da sauri Balkisu tace yaya insha allahu baifi qarfinka ba, sannan zanfadamaka damuwata amma matuqar zaka biyamin buqatartawa nikuma nayimaka alqawarin zanyimaka dukkanin wani Abu dakake so matsawar bai keta addini ba, Hafeez ya jinjina kansa ganin cewa qanwar tasa seriou take mgn yasa yayi saurin cewa OK jst tell namiki alqawarin biyamiki dukk wata buqatarki matuqar bai keta addini ba. Balkisu tayi murmushi tace yayana bai sa6a addini ba asalima addini ya horemu da aikatashi kuma bayan haka idan har ka aikata hakan nikuma xankasance cikin farinciki har abada. Jin Balkisu tace haka yasa Hafeez yace "okay sanar dani inajinki matuqar zaisaki farinciki. Balkisu tace "tunda kamin alqawari zanfadamaka sannan karkayi tunanin in nafadamaka zaka bijirewa buqatartawa, cike da qaguwa Hafeez yace "go on kenake saurare. Miqewa tsaye Balkisu tayi gamida tad'auke dubanta ga Hafeez a hnkli tace yayana inasone Dan Allah ka janye BURINKA nacewa bazaka tabayin aure ba, sbd ina buqatar ganin wata diya macce a cikin gdan nan matsayin matarka hakan zaisani farinciki matuqa Kuma.....! Kafin Balkisu taqarasa abinda take son fadi tuni Hafeez yataka mata burki ta hanyar daka mata tsawa keeee!! Balkisu rufemin bakinki awajan kinsan mekike fada kuwa? Ina mai gargad'inki dakiyi saurin janye wannan buqatartaki kicanja wata domin ina tabbata miki cewa wannan din bata samu shiga ba. Da qarfi Balkisu ta fashe da kuka kmr wacce aka aikowa mutuwa, Hafeez kam gabad'aya jiyayi hanklinsa yatashi domin azahirin gaskiya bayajin zai iya biyama qanwartasa wannan buqatar domin kuwa tsakani na da macce sai idanuwa "cewa Hafeeez" wannan kuka da Balkisu keyi gabadaya yatada hnklin Hafeeez da sauri ya qarasa gareta yace "kiyi shiru plsss bnson kisawa kanki ciwon kai, Balkisu tajanye hannunta daga riqon da Hafeez yayi mata Shiru Hafeez yayi ganin qanwartasa fushi take dashi yasa ya sassauto murya a hnkli yace "plsss Balkisu u have to understand cewa bana son aure bana buqatar kasancewa da kowa, nan gaba kad'an aurenki zakiyi hakan ma kawai ya isheni da zarar kinfara hayayyafa yaranki sun isheni sani farinciki sannan idan kinduba Bal....dasauri Balkisu tadakatar dashi cikin muryan kuka tace yaya wannan ba reason bane sbd kaikanka kasan cewa bani da saurayi hasalima baka bari Na kula kowa toh wakake tunanin zai aure ni har wadannan BURi naka sucika Wanda ka lissafo ynxu? Da sauri Hafeez yace nima sanin kanki ne cewa banida wacce nakeso waxan aura waxan so? Dasauri Balkisu tace wlh yaya believe me idan nacemaka nasamo maka mata nagartacciya Na yarda da tarbiyyan yarinyar akwai nutsuwa da hnkli attare da ita, dasauri Hafeez yakauda knsa hace "a ina kikasanta?" Balkisu murmushi tayi gamida cewa tabbas Yaya zaka Santa amma baxan fadama ko ita wacece ba har sai ka amincewa buqatata, Yaya Hafeex karkamanta cewa kaine uwata Kaine ubana Ashe kenan dama akwai watarana da uba zai kasance yabar yarsa cikin maraici da quncin rayuwa? Jin Balkisu tace haka gabadaya hankli Hafeez yatashi, dasauri ya 6ullo mata ta wata hanya yace "naji I will accept ur condition sai dai Inaso kisani cewa hakan zaifarune idan har yaxamto cewa kema kinsami mijin aure sannan xan amincewa buqatarki" Dasauri Balkisu tajuyo a firgice tace "Yaya wakake tunanin zai soni har ya aureni?" Jisukayi anbud'e labulen falo a hnkli yaqarasa ciki hannayensa sanye cikin aljihunsa cikin sassanyar muryansa yace gani. Muje zuwa donji wanene yashigo musu gda kai tsaye gamida amsa cewa shine zai auri Balkisu. ®NWA [11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣2⃣ A tare suka juya gabad'aya, Dr Muh'd suka gani tsaye murmushi ya sakar musu da sauri ya k'arasa ciki yace "am swry ban muku sallama ba afuwan Assalamu alaikum" miqawa Hafeez hannu yayi sukayi musabaha, can kuma falon yayi shiru nad'an wasu daqiqa gabad'ayansu kowa da abunda yake tunani cikin zuciyarsa' Dr Muh'd ne ya katse shiru ta hanyar cewa "tabbas Hafeez najima inason Balkisu a zuciyata sai dai na 6oye ne sbd ganin cewa baka bawa kowanne d'a namiji damar tunkarar taba, a haqiqanin gsky soyayyar da nakeyima Balkisu tawuce dukk inda kake tunani domin soyayyar Balkisu tayi tasiri acikin xuciyata Wanda hakan yasa nakasa ganin kowacce irin macce da daraja a idanuna, sannan a kullum sai nayi niyyar tunkarar ka da zancen amma sai zuciyata ta haneni. Shiru Hafeez yayi gami da dafe kansa gabad'aya jiyayi hnklinsa ya tashi domin kuwa a ynxu shi Kansa yasan bai da tacewa kasancewar Dr Muh'd abokine ga gareshi yasan koshi shi waye yakuma san halinsa Sannan yasan waye zuri'arsa. Balkisu kam dukk kunya ta isheta gabad'a jitayi kmr qasa tabud'e tashiga. Dr Muh'd ne yace "abokina idan ka amince min inaso kabani auran Balkisu, Hafeez kam jiyayi kmr ya d'aura hannu aka, da sauri ya qirqiro murmushin dole ya dubi Dr Muh'd cikin sigar zolaya Hafeez yace ashee kai ragon likita ne maitsoran macce? Dr Muh'd yace la! la!! la!! Ae ni ba Balkisu nake tsoro ba yayan Balkisun nake tsoro, gabad'aya dariya sukayi Hafeez yad'an bugi kafad'ar Dr Muh'd yace kai dai bawani. Dr Muh'd yakoma cewa "nidai babban yaya kai nake saurare kabani Balkisu? Hafeez yad'anyi murmushin yaqe sannan yadubi gefen da Balkisu ke zaune tayi shiru ta duqar da knta tana wasa da yatsun hannunta, sannan yasake maida dubansa ga Dr Muh'd yace "of cox y not da bazan baka ita ba amma nifa karkayi tunanin zanma qanwata dole" bari ynxu intashi inbaKu waje kud'an tattauna idan kunfahimci juna ta amince toh falillahil hamdu inkuwa har bata amince ba toh

Chapter 4 of 10