Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
huci take kmr zakanya, murmushi Mallan Zakiru yayi domin kuwa bai yi mamakin ganinta ba don yatsammaci haka. Mallan Zakiru yadubi Yagana yace "toh ynxu kuma Yagana wanne laifi nayi haka da har nacancanci ki biyoni gda da masifa? Yagana ta gyara tsayuwa cike da masifa tace "ae kuwa kace dani haka tunda ka gama rainamin hankli wato ashe sai da Meena kayi? Kafadamin suwa kasayarwa da ita a nawa kasaidata? Mallan Zakiru yayi murmushi cike da dattijantaka yace "akan naira dubu uku kacal kuma suma kudin suna hannunki, kinga kenan ashee bani kad'ai naci ribar sai da Aminatu ba. Nan fa Yagana tabud'e murya tana tadajijiyoyin wuya ita alafurr adawo mata da Meeena, Mallan Zakiru kam yau dukk jiyayi lamarin Yagana ya kai mishi mak'ura wata uwar tsawa yabuga mata wnda tayi sanadiyyar shiga natsuwarta. Sheqeqe Yagaña tayi tana bin mallan Zakiru da kallo cike da mamaki, Mallan Zakiru yadubi Yagana cikin tsananin fad'a yace "wlh kedai tirrr Allah wadai da hali irin naki Yagana wlh ina mai tabbata miki cewa kiyi gaggawar canja halinki kiji tsoran haduwa da mahallicinki domin kuwa a kodayaushe lkci yana iya kuremiki. "Dama mai kika d'auki kanki? Kind'auka cewa ke kadaice kike da kwakwalwa da tunanin yadda zaki cutar da wani toh kisani dama irin wannan lkcin nakejira, najima inatunanin ta yadda za'ayi Na ku6utar da Aminatu daga hannunki sai gashi Allah maji roqon bawansa ya amsamin addu'ata da najima inayi akan yabani ikon da zankubutar da Aminatu sai gashi yakawomin hnya mafi sauqi, kuma bari kiji infad'amiki Aminatu dai na gdanta ma'ana gdan mijinta bakuma zanfadamiki inda take ba balle kije kitada musu qayarbaya sbd jahilci irin naki. Gwalo idanu waje tayi tadubi mallan Zakiru tace "Zakiru nice jahilar"? Mallan Zakiru yajinjina kansa yace"kwarai kuwa" Nan fa Yagana ranta yaqara 6aci cikin tsananin fada tashiga nunashi da d'an yatsa tace "wlh kajira kaga abinda xai biyo baya wlh dani kake mgn" Mallan Zakiru yace "ae shi sharri kare ne kuma mai shiyake bi insha allahu babu abinda xan gani sai alkhairi, kuma indai aminatu ce tayi aure a babban gda gdan dasuka san darajar mutum, gdan da inhar keda zuri'arki zasuyi shekara goma kuna tara dukiya bafa zaku iya sayen koda karen gdan ba, balle kiyi tunanin zuwansa" Mallan Zakiru nafadin haka Yagana tayi kwaf ta kad'akai tafice a gdan cikin tsananin fuskata. "Mtsssw aikin banza kawai yarinya kin grma bakisan kingirma ba, baki da wani aiki sai tunanin kanki da ahalinki nawa rayuwar duniyar take da zaki d'auki son duniya kid'aurawa kanki" Inna dai natsaye bata ce komai ba, sai bayan da komai yalafa sannan suka zauna yake bata lbrin dukk abin da yafaru. Innah taji dad'i sosai da jin wannan lbrin. ** ** ** ** ** ** ** A bangaran Amarya Balkisu kuwa gabad'aya famlyn ango sun hallara don d'aukar amarya, amma Balkisu tace sam batasa Xancen ba, ita bbu inda zataje har sai ankawo Meena cikin gdan ta sadata da yayanta sannan, babu irin lallashin da basuyi ba amma furrr taqi amincewa a dole suka hkra suka zauna zaman jiran isowar matar Hafeez. Ba'awani jima ba kuwa sai ga yan d'aukan amarya sun iso, hakanan Hajiya Nana ta lullu6e fuskar Meena akashiga da ita cikin gdan, Bayan sun gama bud'arsu da shewarsu ne Balkisu tazo da kanta taja hannun Meena suka shiga d'akinta don suyi mgn. Meena kam tun isarsu gdan babu abinda take sai kuka daga ita har Balkisu babu mai ba wani hkri, dakyar Balkisu tasamu tayi controlling din kanta sannan tashiga roqon Meena da ta kular mata da yayanta nan Balkisu tashiga fad'awa Meena abinda Hafeez yafiso da wanda baya so. Meeena kam sai kuka takeyi kmr ranta zai fita, hakanan Balkisu tagama fad'amata dukk abinda yakamata sannan takama hnya har zata fita sai tajuyo tace "Meena Dan Allah kikasance mai juriya da hkri kmr yadda nasanki sannan ynxu da zarar hidimar bikin nan taqare xancika miki naki alqawarin" tanafadin haka tashare hawayenta tafice a d'akin. D'akin Hafeez Balkisu tanufa nan ma wani sabon kukan tasha, wannan karon hadda Hafeeez shima yazama tamkar wani qaramin Yaro sai kukan yakeyi, Balkisu ta d'ago da jajayen idanunta tadubi Hafeez tace "plsss yaya ka kula da Meena kmr yadda kake kula dani hakan zaisani farinciki, girgiza mata kai kawai yakeyi batare da yace komai ba. Dakyar Anty munnawara matar uncle ma'aruf ta 6an6are Balkisu daga jikin Hafeeez, sai kuka sukeyi gabad'ayansu. Hakanan Hafeez yanaji yana gani akatafi da Balkisu gdan auranta. Wani irin k'unci yakamaji Wanda hakan yasa ciwon xuciyarsa ya tashi dakyar yasamu yasha magani ya kwanta. Meena kuwa Hajiya Nana takaita asalin d'akinta Wanda ya kasance mallakinta, d'akin kam ya matuqar had'uwa da tsari komai tsaf tsaf nacikin d'akin. Hakanan kuwa Meena tanemi gado ta kwnta wani irin karkarwan d'ari tashigayi ga knta da yake tsananin sara mata sbd ciwo, nan tadunqule waje d'aya ga wani irin azababben tsoro daya dinga shigarta kmr ta shid'e. ®NWA [1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [12:57AM, 8/1/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣8⃣ Dukk addu'ar da tazo bakin Meena ita kawai take karantowa, runtse idanuwan tayi sosai bata ko k'auna bud'esu sbd tsananin tsoro, yayin dashi kuma gogan nata ke d'akinsa kwance yanata sharar bacci sakamakon magungunan daya d'irkawa cikinsa. A bangaran Meena kam dak'yar tasamu itama baccin yayi awon gaba da ita daf da asuba, dan haka bata wani samu ishashen bacci ba, hakanan ta daure ta nufi toilet alwala tad'auro sannan tazo tagabatar da sallah. Bayan ta idar da sallah ne tarafka wani uban tagumi cike da damuwa, Misalin qarfe takwas na safe Meena ta tashi tanufi falo sbd wata irin yunwa da taji ta gallabeta har wani irin duhu duhu take gani dakyar tasamu tafita koh Allah zaisa ta samu abinda tasawa cikinta. Koh da fitar Meena Daniel tagani yanata zirga zirga tsakanin kitchn da dinning area, shiru tayi tana binsa da kallo domin ita dai batasan ko waye shi ba. Meeena na nan tsaye kmr wadda aka shuka, Daniel ne yasake fitowa daga cikin kitchn a karo nabiyu hannunsa dauke da flask din ruwan zafi kmr ance ya waiga sai ganin Madam yayi a tsaye kmr wata marar gaskiya, ae da sauri ya ajiye flask din ya qaraso gareta cike da grmamawa yace gud murng madam, kintashi lpy? Cike da mamaki Meena ta amsa lpy kalw, sannan Daniel yace ni sunana Daniel nine ke kula da store room Na gdan nan da kuma kitch, gyad'a kai kawai Meena tayi hankalinta dukk yana wajen dinning area ita dai burinta tasamu abinda taci. Ganin hakane yasa Daniel yace am swry 4d disturbn u madam, d food is ready da sauri yaqara kan dinning din nan yafara bud'e mata abubuwan da ya girka kala kala, Meena kam riqe baki tayi cike da mamaki tadubi Daniel tace "Daniel dukk suwaye zasuci wannan abincin? Daniel yace "madam boss ne yace ake girka enough abinci yadda kowa zaici ya qoshi", Cikin zuciyar Meena tace uhumm boss kodai runbu irin wannan almubazzaranshi haka. Sinasir da miyan allayahu shine kad'a Meena taga zata iyaci Dan haka d'aukan plat kawai tayi Daniel ya taimaka mata tazuba abincin, d'aukan plat dinta tayi ta koma falo domin jitayi bazata iya zaman dinning table dinba, zamatayi sosai tafara bawa cikinta haqqinsa. Hafeez kam yau baqaramin makara yayi ba wurin tashin sallah sai qarfe bakwai da rabi ya farka a gaggauce yashiga toilet yadauro alwala, yana gama idar da sallah yakoma toilet din yayi wanka yazo yasake shiryawa tsaf abinsa, sai wani sauri yaketayi kmr wanda xaitashi sama yau dai Hafeez ko za6en kayan sawanshi bai tsayayi ba sbd yau bashida niyyar wuni acikin gda balle abokan wasanshi suzo su sami damar takura mishi, Qarfe takwas da rabi nayi Hafeez har yagama shirinsa. Meena kam har tagama cinyye sinasir dinta, wani qatoton qashi ta tsaya gwaigwaya sai faman ko kuwa takeyi dashi, tana cikin wannan halin ne sai ga Hafeez yafito daga d'akinshi cikin sauri sbd baya so ya hadu da wannan Meenan da Balkisu ta d'aura mishi nauyin da bazai iya cikawa ba. Hafeez nafito wa cikin harban falo wata yarinya yagani tayi zaman dirshan tanata faman ko kuwa da qashi, wani irin abune ya tsaya awuyan Hafeez domin shi arayuwansa yatsani yaga anacin abinci da hannu balle kuma ita wannan ga dukkan alamu dambe takeyi da qashi. A fusace Hafeez yanufi falon yana xuwa yace "ke dabbar ina ce miye hakan? Wacece ke ? Wannan wanne irin qazanta ne?" Meena kam batayi tsammanin da mutum tsaye kusa da ita ba, tsawa kawai taji andoka mata Wanda ya mugun razana ta har qashin hannunta ya su6uce ya fadi😂 da sauri taduqa tad'auki qashinta tamiqe tsaye gamida juyowa domin Meena kam tuni tagane mekiranta da dabba sunan, shi din ne kuwa tagani tsaye fuskan nan a turbune babu alamar wasa acikinta. Wani irin shock Hafeez yashiga ganin wannan fitsararriyar yarinyar agabanshi domin kuwa har abada baxai manta wannan face din ba, da saurinshi kuwa ya zaro idanu cike da mamaki yace "ke wat ar u doing here? Meya kawo ki cikin gdana? Meena kam quramishi ido tayi gabanta sai bugun tara-tara yake, nan fa Hafeez yafara kiran Daniel! Daniel!! Daniel!!! da qarfi Hafeez ke kiranshi kmr wanda yaga dodo agabansa. Dagudu Daniel yaqaraso yace "yes boss am here" Hafeez yanuna Meena da hannu yana kallon Daniel yace "Daniel who's dis girl?" Daniel ya yadubi Meena wacce ke tsaye hannu riqe da qaton qashinta wani yawu Daniel had'iye cike da tsoro domin shi baisan wacce irin amsa xaibawa boss din nashi ba, dominshi a tunaninsa koma wacece ai shi zai fisa saninta... Daniel!!! Da qarfi Hafeez ya koma kiransa cikin fushi yace "I'm not tlkn to u"? Who's dix girl? Daniel ya sadda kai qasa yace boss I think she is ur wife, amma nibensashi ba fa. Meena kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Hafeez yadubi Meena up and dwn yace cabb badai wannan abar itace matata ba? Meeena naganin Hafeez xai wuce gona da iri kawai ta ratsa tagefenshi tawuce kitchn ta ajiye plat din sannan ta wanko hannunta. Dasauri tanufi d'akinta ta banko kofa, ganin tashiga cikin d'akin nan ya tabbarwa kansa cewa lallai wannan yarinyar itace wadda aka had'ashi da ita? Tabbb juyawa Hafeez yayi izuwa d'akinshi take yaji yafasa fitar da yayi niyyar yi. Dakinsa shima ya shiga da sauri. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:53AM, 8/1/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣9⃣ Kai da kawowa Hafeez ya dingayi cikin d'akinsa gabad'aya jiyayi Balkisu tagama 6ata mishi rai sbd tarasa wacce zata hadasa dashi sai wannan fitsararriyar yarinyar wata qazama da ita yar qauye. Wani irin haushin Meena yadinga ji, jiyayi kmr yaje yarufeta da duka. Abangaran Meena ma haka abun yake d'akinta tashige tana zuwa tafada kan gadonta,nan tafara kuka wani irin haushin Hafeez da tsoransa ne suka tsayamata a cikin xuciyarta lkci d'aya cikin ranta tace "wato dai shi wannan uban masifan bashi da aiki sai cewa mutun dabba qyaattt" Meena tayi kwafa cike da jin haushinsa tace ae kuwa zan nunamaka halin dabbancin. Tun daga wannan ranar Meena ta umarci Daniel da yake kai mata abinci cikin d'akinta, dan haka yasa ynxu kwata kwata Meena da Hafeez sunbar had'uwa dukk da cewa suna gda daya. ** ** ** ** BAYAN SATI DAYA. Tuni Balkisu tad'auka qarara izuwa babbar kotu dake cikin jaharsu, da taimakon Dr Muh'd Balkisu ke gudanar da komai batare da sanin Meena ba. Sai da akayi sati guda currr ana abu d'aya shari'ace aka gudanar inda Mallan Zakiru yazo takanas har kotu shida wasu sauran mutanen cikin anguwarsu, suka bada shaidan cewa lallai Yagana itace ta kashe d'anta. Sbd irin kudin da Balkisu tanarkawa yan'sanda shiyasa sukaje har gdan Yagana suka suka titsa qeyar ta izuwa police station, nan fa suka shiga yimata horo na azaba kala kala akan lallai ta amsa laifinta na kisa, dakyar Yagana ta amsa laifinta ganin tana shirin shurawa zuwa lahira. Bayan Yagana ta amsa laifinta ne kotu tayanke mata hukuncin d'aurin rai da rai a gdan yari tare da horo maitsanani kasancewar yadda tayi wasa da hankli hukuma. Balkisu tayi farinciki da samun nasarar da sukayi, hakanan akafito da baba Rabi dukk ta wani tsufa ta rame ta d'an canja kammanu. Sunanan tsaye mallan zakiru dasu Balkisu, yansanda sukazo wucewa da Yagana hannuta saqale da ankwa ana qoqarin wucewa da ita gdan yari. Dasauri Mallan zakiru yatsaidasu nan fa yayi tayiwa Yagana tuni akan abubuwan dasuka faru yace" ynxu dai gashinan kinga qarshenki (Allah yashiryi masu halin sonkai irin Na Yagana) Baba Rabi kam sai godiya take ta jerowa Balkisu, daga bisani ne Baba Rabi ta dubi Balkisu tace "baiwar Allah ko zan iya sanin koke wacece"? Balkisu tayi murmushi cike da farinciki tace "baba karki damu zanfad'a miki koni wacece amma da farko inaso ki kwntar da hnklinki kinatsu sbd nima yarkice kmr Meena" Da sauri baba Rabi tadubi Balkisu tace yan nan kinsan aminatu ne Dan Allah tana ina? Kiwa Allah kifadamin koke wacece INA aminatu Na dan Allah kitaimaka ki kaini gareta, Balkisu tace Baba kwantar da hanklinki ynxuma wajan Meena zankai ki yanzu insha allahu zakiga Meena, wani irin hawayen farinciki ne ya lullu6e Baba Rabi. Kofar wani katafaran gda Baba Rabi taga anyi parkn, cikin girmamawa Balkisu tace "Baba fito mushiga daga ciki", kurawa Balkisu idanu Baba Rabi tayi tana yimata wani irin kallon tuhuma cikin ranta tace "anya kuwa banyi kuskuren amincewa da wadannan mutanen ba, bansani ba ko masu yanke kan mutane ne" tana cikin wannan tunanin ne taji muryan Balkisu tace "Baba karkiji komai wlh babu abinda zamu miki kizo muje nakaiki wajan Meena" jiki a sanyaye haka nan baba Rabi tarufawa Balkisu baya suka shiga cikin gdan. "Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Anty amarya Meena" cewar Balkisu dai dai lkcin da suke qoqarin shiga falon. Meena kam nacikin d'akinta tana d'an wasu gyare- gyaren ta juyo kmr ana sallama, kuma kmr muryan Balkisu tajiyo domin dai ita tasan cewa bata kai matsayin da Hafeez zai mata sallama ba. Dan haka da sauri ta tashi tafice a d'akin da sauri tanufi falo. Da gudu Meena ta isa falon don tarbon Balkisu, Tursuuu Meena tayi ta tsaya cike da mamaki galala tayi da baki domin abinda taganewa idonta (tsawan shekara tara da suka shige Meena bazata taba mance wannan nagartacciyar fuskar ba) fashewa tayi da wani irin kuka mai tsanin ban tausayi. Zaku jini anjima don jin cigaban lbrin, nagode. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:07AM, 8/2/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣0⃣ Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya lullu6e Meena da gudu taqarasa wajan Baba Rabi, rungume junansu sukayi a tare suna ta kuka, Balkisu da Dr Muh'd kam suna daga gefe sai murmushi sukeyi. Daga Meena har Baba Rabi anrasa mai lallashin wani, kuka sukeyi gwanin ban tausayi, dakyar Baba Rabi ta share hawayenta nan fa tashiga Shafa fuskar Meena ta ko ina sai mamakin girmanta takeyi, yayin da itama Meena sai kallon ta takeyi jiki take kmr ta manne a jikin Baba Rabi. Bayan sun natsu sun zauna Meena ta umarci Daniel da yakawo musu drinks, cike da bin umarninta yakawo drinks kala kala yadiresu musu shi. Sai da suka d'an samu suka sharuwa sannan Meena tadubi Balkisu tayi ta zabga mata adduo'i nafatan alkhairi tare da yimata godiya, Balkisu sai murmushi takeyi. Ana cikin hakane Dr Muh'd yatashi yace "shi zai koma office" nan yayi sallama dasu yafice Balkisu har wurin mota tarakashi daga bisani takoma cikin gdan. Meena kam ana nan liqe da Baba Rabi dan jitake kmr wani zai k'wace mata ita, Balkisu dai sai dariya take mata. Meena tadubi Baba Rabi tace 'Amma' (sunan da Balkisu ke kiran Baba Rabi dashi knan) Baba Rabi tadubi Meena tace "Naam Aminatu" Meena ta shagwa6e fuska tace Amma kintafi kinbarni cikin wahalalliyar rayuwa naga rashin gata naga tozarta naga walaqanci naga.....dasauri Baba Rabi ta toshe mata baki tace "haba Aminatu minene kike fad'a haka yakamata ace kin yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau a matsayinki na muslma, sbd wannan halin da muka tsinci kanmu jarabawace ta ubangiji dukk abunda Allah yarubuto cikin k'addararka to tabbas babu makawa sai tasameshi" Dan haka karki wanisa damuwa aranki ko kice zaki dinga tuna baya hakan bashi da kyau, ynxu ita wacce kike son yin mgn akanta ae gashinan taga qarshen sakamakonta. Balkisu ta jinjina kai tace tabbas Baba wannan haka yake, Baba Rabi ta gyad'a kai tace toh kinga in hakane kuwa bai kamata kidinga tuna abinda yariga yawuce ba, Na ma gode Allah dayasa nasameki da ranki cikin k'oshin lafiya gashi har kinyi aurenki a gdan mijinki kinga wannan ma wata baiwace ta ubangiji Dan haka ki gode masa kiqara gode masa a koda yaushe Allah yana tare da mai gaskiya sannan yana bayan masu hakuri. Da sauri Meena tafada jikin Baba Rabi taqanqameta tana kuka, cikin zolaya Balkisu tace wlh anty amarya in baki daina wannan kukan naki ba xand'auki Baba mutafiyarmu, dasauri Meena ta dubi Balkisu ta d'an turo baki cikin shagwa6a. Baba Rabi tanumfasa tace "miye naga kina turo baki ae da gaskiyar Balkisu sbd a yau insha allahu inaso naje garinmu nasadu da dangina. Balkisu ta gyara zamanta ta fuskanci Baba Rabi tace "Baba sai dai fa kiyi hkri koda zakije garinku to ba yau ba sbd muma muna buqatarki kusa da mu, sannan kada kidamu ba'anan zaki zauna ba akwai gdan da muka ajiye miki na mussaman a Famfamari, Riqe ha6a Baba Rabi tayi cikin nuna jindadi da farinciki ta waro idanu tace dukk nikadai? Irin wannan d'awainiyan anya kuwa baiyi yawa ba? Balkisu tace haba dai Baba wanne irin yawa kuma kema fa tamkar mahaifiya kike agaremu dukk abinda zamu iya yiwa mahaifanmu to zamuyi miki dukk da cewan Mahaifan namu basa raye" Baba Rabi ta goge hawayen dake kwaranyo a mata a fuska, nan tashiga sawa Balkisu albarka gamida yimata ta'azziyar rashin da sukayi. Babban tashin hnkli Meena tashiga yayin da taga Ammanta na qoqarin fita a cikin gdan, kuka takeyi sosai ita fa lallai sai tabisu. Balkisu tace haba Meena miye hakan? Sai kace wadda Baban guduwa zatayi, kiyi hkri mana tunda Yaya Hafeez baya nan kibari idan yadawo xai kaiki shi da kansa. nan fa Meena tace batasan zancen ba. Dole Balkisu takira Hafeez tasanar dashi cewa tanaso zasu d'an fita wani waje tare da Meena, batare da 6ata lkci ba Hafeez yace Allah kiyaye. Cike da farinciki Balkisu tad'aukesu a mota suka nufi Famfamari inda gdan Baba Rabi yake, Wani d'an matsakacin plat house ne mai kyan gaske, falo daya da d'akuna uku da toilet da kitchn sannan kowanne bed room da toilet dinsa. Masha allahu gda yayi kyau da tsari, Baba Rabi dai sai godiya take tana sama Balkisu albarka. Bayan sun gama gyara ko ina Na gdan Balkisu tace da Meena ta shirya tayi dropn dinta a gda ita zata wuce gdanta tad'aura abinci. Nan ma dakyar Meena ta yarda suka tafi cike da kewan Ammanta. Akan hanyarsu takomawa gda Balkisu tadubi Meena tace "toh anty amarya nacika miki dukkan wani alqawari naki inaso nima kicikamin nawa kikular min da yayana tamkar yadda uwa zata kula da d'anta. Dammm!! Gaban Balkisu ya buga a hnkli ta kalli Balkisu jiki a sanyaye ta gyad'a mata kai gamida cewa insha allahu. Balkisu tayi murmushinta mai sanyi, dai dai nan suka iso kofan gdan, Meena tayi sallama da Balkisu jiki a sanyaye haka tabud'e get din tashiga, motar Hafeez tagani ajiye wurin parkn motoci wato hakan nanufin yadawo? damm! Taji gabanta yabuga sbd alqawarin da tayiwa Balkisu ne yafad'omata. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:21AM, 8/2/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣1⃣ A hankali ta murd'a k'ofan falon tashiga ciki, Hafeez tagani tsaye hannunsa d'aya sanye cikin aljihu d'aya kuma yana amsa waya ya juya bayansa, cikin tafiyar sand'a kmr wacce bata da gaskiya Meena ta nufi hanyar d'akinta tana isa bakin k'ofa dai dai nan Hafeez na gama waya. Wani uban tsawa yadaka mata yace "keee!! Zonan nan" Meena sai da tad'an figirta a hnkli ta juya akalarta izuwa falo, Hafeez ya watsa mata wata uwar harara cike da jin haushinta yace ke gdanku ba manya ne? Kina ganin mutane baxaki gaishesu ba ko ba akoya miki bane? Meena ta turo baki a hnkli tace INA wuni, mtssw Hafeez yayi tsaki yace " bansani get out wuce kiban waje" Meena ta juya da sauri tashige d'akinta tana gunguni. A hnkli Hafeeez yace "Mtssw village girl gal kawai"cike dajin haushin ganinta yanufi d'akinsa. •° •° •° •° Yau ya kasance weekend Hafeez na nan gda sai wasu aikinsa yakeyi a system insa, zaune yake a falo sanye da farar jallabiya gabad'aya ya maida hnklinsa akan aikinshi. A bangaran Meena kuwa a kullum bata da wani tunani da yawuce taya zata fara jawo hnklin wannan uban yan girman kan yakarka to izuwa gareta har tasamu tabashi kulawan. Cikin tunanin da takeyi ne wata dabara tafad'o mata dasauri ta tashi tanufi falo, dama cikin shirinta take tsaff, cikin natsuwa Meena ke tafiya har ta isa cikin falon Hafeez tagani zaune yanata aiki a hnkli taqarasa gareshi tace "assalamu alaikum" dasauri Hafeez ya d'ago kanshi Dan ganin wacece keyimishi sallama. Meena yagani tsaye gabansa sanye da wasu material riga da siket sun matuqar amsar jikinta tayi kyau abunta "koshi Hafeez cikin ransa sai da ya yaba wannan shiga" amma a zahiri sai cewa yayi wa'alaikissalam, nan kuma yatsaya sheqeqe yana kallonta cike da nuna isa yafara kusheta yace ke kuma fa miye hakan zaki zo kitsaya akan mutane? Dasauri kuwa Meena ta zauna cike da sanyi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa ciki ciki yace "lpy" Meena taqara da cewa sannu da aiki Hafeez yad'ago kanshi ya watsa mata wata uwar harara batare da ya amsa mata ba ya maida kanshi sannan yaci gaba da aikinsa, Meena na nan tsugunne Chan tasake cewa "amm kayi brkfst kuwa"? Hafeez yakawo iya wuya wani irin haushi yaji tabasa ina ruwanta da cikinsa, kallonta yakomayi ya watsar da yinta yacigaba da aikinsa. Meena takawo iya wuya danne zuciyarta kawai takeyi dan haka dasauri ta tashi tabar gurin, d'akin ta takoma cike da jin haushin wannan izza da mulki na Hafeez. Hafeez na nan zaune Daniel ya had'o kayan brkfst akan tire yanufi d'akin Meena dashi, yana zuwa yafara kwankwasa k'ofar d'akin a hnkli, da sauri Hafeez yajuyo dan ganin mai k'wank'wasa kofan d'akin Meena, Daniel yagani tsaye hannunsa d'auke da abinci da sauri Hafeez ya taso dai dai lkcin Meena tabud'e kofa. Wani irin takaici ne ya turnuqe Hafeez "cikin zuciyarsa yace lallema yarinyan nan yaushe ma tawaye da har zata fara bada umarni ana kawo mata abinci?sannan ma tarasa Wanda zata sa ya kaimata abinci sai Daniel da irin wannan shiga nata" Meena ce ta katse masa tunanin da yakeyi, jiyayi tace sannu Daniel har ka kammala Daniel yace "yes madam" hannu tasa zata amshi abincinta Hafeez yadakawa Daniel tsawa yace "oyaa maida abincin nan kitchn" jiki na rawa Daniel yajuya da abincin ixuwa kitchn kmr yadda boss din nasa ya umarce shi. Juyawa yayi gurin Meena fuskan nan a turbune ya nuna tada hannu yace "ke yar qauye bari kiji kinyi kad'an kidinga bada order a gdan nan wai dan akaimiki abinci daga yau irin rana tayau bana so in qara ganin Daniel kofar d'akinki danufin wai yakai miki abinci kinajina koh? Kije da kanki kid'ibawa kanki inba haka ba kixauna da yunwa" har Hafeez ya juya xai tafi sai kuma yadawo ya dubi Meena duba na walaqanci yace "ke yar qauye inaso daga yau kezakina shiga kitchn da kanki kidafa abinci, take anan kuma yashiga kiran Daniel! Jiki na rawa Daniel yaqaraso yace "yess oga" Hafeez yadubi Daniel yace as 4rm today inaso karka qara bin umarninta nacewa ka kawo mata abinci' Hafeez yariqe kunnensa yana mainuna alamar warning ga Daniel sannan yace "and then daga ynxu ita zata ke dafa abincinta" Daniel yace okay oga. Hafeez nafad'in haka yajuya yabar wajan, Meena tsayawa tayi tana binsa da kallo cikin xuciyarta tace "jibeshi da anyi magana yawani cewa mutum d'an kauye qyaatt" juyawa tayi cikin d'akinta tad'auko hijabi tanufi kitchn dan tasamu abinda tasawa cikinta domin kuwa Meena intaji yunwa bata wasa da abinci. Sumi sumi tanufi kitchn don tad'aura wani abun,...Hafeez na nan zaune ta ratsa ta gefensa tawuce, juyowa yayi yana kallonta tsaki yayi cikin xuciyarsa yace "village gal" Kitchen Meena tashiga nan tafara laluben abinda zata dafa, tana cikin tsaka da dubawa ne taga hango kwalin indomie da sauri ta janyo kwalin tad'auki indomie biyu nan ta kunna rishow kasancewar bata iya amfani da gas ba. Take anan Meena tafara dahuwar indomie dinta wnda taji albasa da attaruhu, ae fa nan gda ya kaure da qamshi Hafeez kam mayen indomie take anan yajiyo qamshi na dukan hancinsa wani irin yunwa yaqarajin tashigesa kasancewar dama baiyi brkfst dinsa ba. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:00PM, 8/3/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣2⃣ Dasauri Hafeez yamiqe yanufi kitchen din, dai dai lokacin ne kuma Meena ke qoqarin juye indomie dinta a plat, yawun Hafeez ne yatsinke sai wani had'iyar yawu yake (sbd Hafeez na mutuwar son indomie shiyasa ma kullum gdan baya rabuwa da kwalayen indomie) Cikin natsuwa Meena ta bud'e fridge din dake ajiye cikin kitchen tabud'e tad'auki exotic mai sanyi sannan taduqa tad'auki indomie dinta. Hafeez

Chapter 6 of 10