Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bai tsammaci fitowar Meena a lkcin ba jiyayi kawai sunyi karo da juna, dasauri Meena tace "subahanallahi" wani irin takaicine Yakama Hafeez ganin cewa ita kad'ai ta dafawa kanta indomen, duba jikinsa Hafeez yashigayi ko allah zaisa yaga inda ta6ata masa jiki yasauqe haushinsa akanta, amma sai dai anyi Sa'a babu inda jikinsa ya6aci,dan haka dubanta ya shigayi kmr wacce tayi wani abun. Meena kam tsaye tayi tanabinsa da kallo, Chan Hafeez yaqufula yace "ke yar qauye wannan wacce irin qaxamar dahuwa ce kikayi jibi yadda kikawani zabga tarugu sai kace wata maiyya. Meena tazaro ido waje tace "nice mayya Kuma?"batare da Hafeez ya kulata ba yace "common get out" Meena taratsa ta gefenshi zata wuce tana gunguni Hafeez yace "magana kike ne?" Meena ta manna masa ta wucewarta, Hafeez yayi tsaki yace qyatt yar qauye kawai sai wani faman big head kike xanyi maganinki very soon. Nan yashiga kwalawa Daniel kira! A bangaran Meena kuwa d'akinta ta wuce kaitsaye dukk haushi ya isheta mgnr Hafeez ce kawai ke mata yawo a kunnenya, kwafa tayi cike dajin haushi tace "tabb wato ni Hafeez zaicewa Maiya? Wlh sai yagane kurensa sai na mai dashi yazama mayen shima in yaso mahad'e muzama mayun mu biyu,..Meena sai faman cin indomien din ta takeyi wnda taji kayan had'i, tanaci tana masifa ita kid'ai a d'aki. •° •° •° •° Washe gari. Meena tunda safe bayan ta idar da sallah tanufi kitchn dan tasamu abinda tad'aura, mgnr Balkisu ce tafad'o aran Meena lkcin da aka kawota inda Balkisu ke sanar da ita abunda Hafeez yafiso yayi brkfst dashi wato soyayyan kwai da tea, dariyar mugunta Meena tayi, nan tashiga farfasa kwai wnda xatayi amfani dashi ta jajjaga tarugu mai yawa ta yanka albasanta tazuba maggi da kayan kamshi ta zuba cikin kwan ta bubbugashi sosai yabi jikinsa, nan tahau suyan kwan, daga gefe kuma tad'aura ruwan zafin tea dinsa Wanda tazuba lipton da citta suga da kalinfari da barkono sosai, ae fa nan qamshi ya karad'e gdan. Hafeez sai da ya tabbatar da cewa yayi wanka sannan ya shirya tsaf abinsa cikin shaddarsa sky blue sai hularsa wadda tayi matchn da kayansa, agogon hannunsa yad'auka yasa sannan yafesa turare yanufi hanyar fita, bud'e kofan nan da Hafeez zaiyi yaji kamshin ya doki hancinsa da sauri yaqarasa cikin falon ko da yaduba dinning area yaga anshirya komai tsaf tsaf kmr yadda aka saba, cikin hanzari yanufi dinning table yaxauna tare da duban agogon hannunsa qarfe takwas da rabi yana ganin haka yayi saurin zaro wayanshi dake aljihunsa, wata nmbr yayi dialing cikin natsuwa yake mgn yace "yes mansur am on ma way just giv me 15 to 20 mint a will b thr soon" yana gama wayar ya hau bud'e brkfst din ruwan zafin tea din yafara zubawa kadan cikin cup sannan yadibi kwan nashi cikin plat, wani irin kamshi mai dad'i ne yake ta doke hancinsa. Sai da ya tabbatar da ruwan xafin yad'an huce dai dai yadda zai iya sha sannan yajawo kusa dashi, plat din kwansa yasa agaba dasauri yadebo mai yawa yaddana a bakinsa yafaraci a hnkli yad'an lumshe ido sai da kwan yakai qarshe Hafeez yaji wani irin azababben zafin barkono ya ziyarci harshensa dasauri yafurzar ya dauki cup din tea dinsa ya kurba ko zaiji d'an ji dama, ae fa nan Hafeez ya miqe tsaye idanunsa sukayi jajir harshensa yadinga fiddowa waje sbd tsabar azaban da yakeji ko mgn yakasa(kasancewar Hafeez bayason abuda yaji SBD ulcer) Meena dake la6e tana kallonsa sai kwasar dariya take abunta, kara leqawa tayi don taga yadda yake daka tsalle ae kuwa tana sa kai sukayi ido biyu da Hafeez. NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:10AM, 8/4/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣3⃣ Hafeez nahad'a ido da Meena yatabbatarwa kansa cewa itace tahad'a masa wannan muguntan, dan haka a fusace yayi kanta sai dai Hafeez baisamu daman qarasawa gareta ba sbd wani irin abu da yatsaya a zuciyansa nan da nan yanemi hnklinsa yarasa jagwaaf yafad'i qasa gamida riqe kirjinsa yanata mutsu-mutsu a kasa. Abu dai kmr wasa wasa tun Meena na yar dariyarta har dai talura cewa Hafeez da gaske yake, ae da gudu Meena taqarasa inda yake kwnce nan tashiga jijjigasa tana kiran sunansa. Gabad'aya idanunsa suncanja kala Hafeez yajigata sosai zuciyarsa wani irin suya take masa. Meena ta lura abin nashi dagaske ne ba wasa dan haka dagudu tashiga kiran Daniel, Daniel yazo da hanzari ganin ogan nasa cikin wani hali hakan yasa yafahimci cewa ulcer dinshi ne yatashi dagudu Daniel yashiga d'akin Hafeez yad'auko maganinsa nan ya qoqarta yasamu yabashi maganin yasha. A hnkli Daniel yasamu yad'aga Hafeeez dakyar yataimaka mishi ya kaisa d'akinshi. Hafeez jiyayi tsanar Meena taqaru a xuciyarsa. A bangaran Meena kuwa jitayi gabad'aya jikinta yayi sanyi, sai ynxu takejin kwata kwata bata kyauta ba nadama tashigayi marar iyaka. Tunda wannan abu yafaru kuwa Hafeez bai qara bin tankan Meena ba, yar kulatan ma dayakeyi suna rigima kwata kwata ynxu ya daina. Mgnr abincinsa kuwa Daniel kedafa mishi kmr kullum. • • • • • • Meena abin duniya dukk ya isheta Hafeez ko kallon indatake baya son yi jiyayi gabad'aya yatsaneta, shiyasa da zarar gari yawaye yake Allah Allah yafice a gdan. Yayin da ita kuma Meena ke tunanin hanyoyin da zatabi dan taga cewa ta kyautata masa, Hanyar farko da Meena tafarabi shine da zarar Hafeez yafita zuwa office dinshi a wannan lkcin ne take shiga d'akinsa ta gyara ko ina ta wanke toilet tattara under wears dinsa ta wanke masa, haka kullum Hafeez idan yadawo sai yaga komai Na d'akinsa very neat. Ana cikin hakane Daniel ya samu Hafeez yasanar dashi cewa yanaso zai zaije enugu can garinsu domin gudanar da bikin kirisimeti, Hafeez yayi mishi izini sannan yad'auki kudi mai tsoka yabawa Daniel. Lkcin da Daniel zaitafi garinsu har qofan d'akin Meena yaje yayi sallama da ita, nan itama tayi mishi fatan adawo lafiya. *DA YAMMACI* A yammacin ranar ne Meena tashiga kitchen tad'aura tuwon semo da miyan d'anya ku6ewa, Meena taxage sosai tadafa abinci mai kyau da tsari dukk dan taburge Hafeez. Bayan Meena tagama girkinta ne takoma d'akinta toilet tashiga ta silla wankanta sannan tafito tashirya tsaf abunta cikin wata jar atamfarta mairatsin ash kala, atamfar taimata kyau sosai, simple mark up tayi sannan tanufi falo taxauna ta kunna Tv. Horn din motar Hafeez Meena taji, dasauri tamiqe taleqa window' Hafeez din ne kuwa ta hango yayinda yake qoqarin fitowa a mota, dasauri takoma maxauninta. Murd'a kofan falon yayi yashiga batare da ya lura cewa akwai mutun a falon ba, dasauri Meena ta taso da fara'arta tayi mishi sannu da zuwa batare da Hafeez ya kulata ba tasa hannu tana qoqarin ansar briefcase dinsa, wani irin takaici Hafeez yaji baisan lkcin daya tunkud'e ta ba tafad'i. Hafeez ko ajikinsa haka yatsallaka Meena yawuce. Dinning area yamaida dubansa yaga cewa tahad'a masa abincin dare tsaki yaja mtssssww stupid, Hafeez nafadin Haka yanufi d'akinsa. Jikin Meena yayi sanyi sosai a hnkli ta tashi a wurin tashiga d'akinta, saman gadonta tahau tarafka wani uban tagumi nan tashiga yin tunani kala kala akan yadda zatabi da hafeez nan dai tayanke shawaran zata jure komai dan ganin tacikawa Balkisu alqawarinta kmr yadda tacikamata nata. Magri nayi Hafeez ya d'aura alwalarsa yawucewarsa masallaci, bayan sun idar da sallah restaurant yanufa kai tsaye yacika tumbinsa, dukk da cewa yasan Meena tayi girki amma Sam baijin iyacin girkinta koda wasa. __•__•__•__°__°__°__•__•__• A kullum Meena tana qoqari sosai wajan kula da Hafeez, ta gyara mishi d'aki tasa roomfrshnr ta wanke toilet dinsa tagyara mishi kayansa, sannan tayi mishi girki kullum dukk da cewa Hafeez bayaci amma Meena dai dai da rana d'aya bata fasa abubuwan da takeyi ba, tsawa da gyara turi da masifar Hafeez baya hana Meena ta kyautata masa. Meena ce zaune a falo tanajiran shigowar Hafeez, sai jin tayi telephone Na qara (wato landline wnda kowa xai iya d'auka, kasancewar Meena batada waya) dasauri Meena tamiqe ta isa wurin da telephn din ke ajiye tad'aga wayan kmr yadda taga Hafeez nayi, sallama tafarayi sannan suka gaisa Take anan Meena tagane muryan Balkisu ne nidai naga Meena sai murmushi takeyi daga bisani kuma naji tace mekikace daqarfi!! ?? Gabadaya naga hankli Meena yatashi dasauri tajefar da wayan tanufi d'akinta. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:47AM, 8/4/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣4⃣ A rikice naga Meena tafito daga d'akinta sanye da hijab dasauri naga taja kofan d'akin ta rufe sannan tanufi hanyar waje a hanzarce, bakin titi tanufa kai tsaye da alamar tana jiran abin hawane. Kmr wucewan minti biyar Meena na nan tsaye bata samu abin hawa ba, sai ga Balkisu nan cikin motarta tun kafinma taqarasa tagane cewa Meena ce tsaye bakin titi. Dasauri Balkisu tayi parkn din motarta kusa da Meena, zuge glass din motar tayi lkcin ne Meena tafahimci cewa Balkisu ce, ae kuwa da hanzarinta taqarasa cikin motar. Bayan tashiga cikine Balkisu tafashe da yar dariya tace "a'a Anty amarya inazaki haka badai kice mgnr da mukayi bane dukk tafirgitaki haka ba?" Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar zuciya tace "haba Balkisu mai xai hana hanklina baxai tashi ba karki manta fa cewa basan garinsu mahaifiyata ba ynxu idan ta tafi tabarni batare da nabita naga dangina ba mai kike tunanin xaifaru? Gsky nidai xanbi Amma na xuwa garinsu, Balkisu tadubi Meena da murmushin nan nata tadafa kafad'arta tace "haba kekuwa Anty amarya ae baki bari naqarasa miki abinda nake son cewa ba kawai naga kinkatse call din shiyasa kikaga nafito a hanzarce". Ynxu koh da ace bin Baba Rabin zakiyi hakanan zakitafi batare da izinin yayana ba ko kuwa hakanan zakije hannu siddan babu kayan sawa balle tsaraba? Meena ta sadda kanta qasa tace "wlh dukk na rikice ne sbd bana fatan abinda xaisa nasakeyin nisa da mahaifiyata" Balkisu tace "hakane amma ae ba yau bane tafiyan nata sai jibi ne fa Dan haka muje namaidaki gda ki kwantar da hnklinki zanfad'awa Yaya mgnr tafiyan naku amma inaso kema kisameshi dakanki kifad'a masa, toh kawai Meena tace. Hakanan Balkisu ta mai da Meena gda sai faman zolayanta takeyi. ** ** ** Hafeez ne zaune awani tafkeken Restaurant yana cin abincinsa hnkli kwance, daga gefe kuma inda ya ajiye wayansa tashiga ruri! A hnkli Hafeez yajawo wayan 'luvly Sister' sunan da Hafeez yayi saving nmbn Balkisu shine ya baiyanna agaban screen din wayansa da sauri yad'auka gamida sawa a kunnenshi, bayan sun gaisa ne Balkisu ke sanar da Hafeez mgnr tafiyan Meena wnda zasu ita da mahaifiyarta, Hafeez yace "olryt Allah yakaimu lkcin" Balkisu tace ameen nan suka d'an ta6a hiransu daga bisani kowannensu ya ajiye waya. Abangaran Hafeez kam shiru yayi hakanan kuma sai yakejin kmr babu dadi, can dai kuma ya hori xuciyarsa tama daina damuwa da wannan yar qauyan ae ma inta tafi kahuta, inba ma tsabar rainin wayo ba Balkisu nake aure ko ita ae kamata yayi taxo da kanta taneme ixinina wato tanaji ita watace tafi qarfin takawo kanta knan?, hakanan Hafeez yayi tasaqawa da kuncewa a cikin xuciyarsa. Har dai yagama cin abincinsa sannan yanufi gda. Yau ma kmr kullum Meena tayi masa abinci ta ajiye dukk da tasan cewa baci xaiyi ba, haka nan bayan shigowarsa cikin gda har bakin kofa tabisa dan ta tarbeshi amma gayen nata ko kallon inda take baiyi ba, balle yanxu dama cike yake da haushinta akan qin xuwa da batayi da kanta tafara tambayarshi ba. Inda sabo kam Meena tasaba da irin abubuwan da Hafeez ke mata wanda zuwa ynxu kam har sun fara daina damuwarta. Misalin qarfe tara na dare Meena tashiga bayi tayi wnka sannan tad'airo alwala, kayan bacci tasaka masu sauqin nauyi hakanan tajawo xani tad'aura saman sleepn drss din sannan tasanya hijabinta ta gabatar da nafilfilunta kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne ta yankewa xuciyarta shawaran cewa gwnda taje a daidai wannan lkcin tasanar da Hafeez mgnr tafiyanta inba haka ba da safe koh da zata tashi olrdy ya fita. Hakanan ta gama yanke shawaran ta, ta amincewa zuciyarta, Dan haka d'akin Hafeez tanufa kai tsaye a hnkli tashiga knckn kofar,...sai da Hafeez yagama jan ajinsa kasancewar yasan babu wnda xai kwankwasa mishi kofa adaidai wannan lkcin sai Meena shiyasa sai dayagama jan ajinsa sannan yace yes come in! A hnkli Meena ta murd'a kofan d'akinta shiga. Hafeez tagani zaune bakin gado dagashi sai farar vest da boxsas yanata aiki da system inshi, da sallama tashiga cikin d'akin, Hafeez ya amsa mata sallamarta batare da yad'ago ya kalleta ba. Meena taduqa har qasa ta gaida Hafeez,..Hafeez kuwa ko kallo bata ishesa ba amaimakon ma ya amsa gaisuwansa datayi sai cemata yayi yes inajinki fad'i abunda yakawoki kinga aiki nakeyi. Meena ta had'iye wani yawu dakyar yawuce sannan ta sadda kanta qasa sbd jitayi gabad'aya Hafeez yayi mata wani irin kwarjini, cikin nutsuwa Meena tace "dama Amma nane xatayi tafiya xuwa gda shine nake so na bita" Hafeez yace "dakyau yar qauye xa'aje qauye kenan? Meena dai batace masa komai ba sai wasa kawai take da d'an yatsanta. Wani murmushin takaici Hafeez yayi sannan ya d'auko wata waya LG yamiqa mata yace ga waya nan inkinje kiyi amfani da ita, Meena ta amsa tayi godiya sannan Hafeez yad'auko bandir din kudi yan dari biyar biyar ya watsawa Meena cike da gadara yace gashinan wannan akaiwa tsohuwa nasan zata buqata. Mgnr Hafeez ta matuqar 6ataran Meena amma sai ta danne xuciyarta miqewa tayi cike da d'acin rai takalli Hafeez ta kalli kud'in har dai Meena tayi niyar sakar mishi mgn sai kuma nan da nan ta taushi zuciyarta, ajiye masa kudinsa tayi a qasa dai dai qarfarshi taficewarta a d'akin. Binta Hafeez yayi da kallo cike da mamakinta ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:27AM, 8/5/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣5⃣ Balkisu da kanta taje wani babban super market tahad'owa Baba Rabi tsaraba masu kyau na amfani, su sabulun wnka wanki turaren shafawa kwalayen biskuit da dai sauransu, hakanan ta kwasa tayi gdan Baba Rabi dasu ta kai mata. Baba Rabi tayi farinciki sosai da irin yawan hidimar da Balkisu keyi da ita, nan tayi tasawa Balkisu albarka gami da nuna farincikinta. Washe Gari. Tunda asuban fari bayan Meena ta idar da sallah batasamu ta kwanta ba sai da ta tabbatar da cewa tayi dukkan wani aikinta kmr yadda tasaba, agogon dake liqe jikin bangon d'akinta ne yabuga qarfe 6:30 a gaggauce Meena tafad'a toilet tayi wanka kasancewar tasa qarfe 7:00 Hafeez ke fita, gashi yau tanason tawuni gdnsu dan tasan irin shirye shiryen da yakamata suyi ita da Ammanta. Wata dakakiyar shadda lemon green wadda akayiwa aiki dazare orange, riga da siket ne su Meena tad'auko tasa (woww ni kaina munay sai dana yaba wannan shiga) dukk da ba wata kwalliya Meena tayi sosai ba amma tai matuqar kyau, nan tad'auko takalmi orange gyale orange. Motsin Hafeez taji yana qoqarin fitowa daga d'akinsa dasauri taduba agogo taga 6:57 a hanzarce ta zura wata qatuwar Hijabi tanufi waje. Ki6iss sukayi da juna Hafeez ke kokarin fita yayin da Meena tafito a d'akinta dasauri tace Yaya!! Mamakine qarara ya baiyanna a fuskar Hafeez jin cewa Meena ke kiransa da Yaya dukk da cewa bata fiye kiran sunansa ba, sannan a iyazatonsa yana tunanin tayi fushi da shi sbd abinda yayi mata jiya daddare. Tsayawa Hafeez yayi batare da ya juyo ba, a hnkli Meena taqarasa kusa dashi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa a takaice Lfy, Batare da nuna damuwa ba Meena tace "Dan Allah sonake kamin izini xanje gdnmu nawuni acan sannan inba damuwa inaso ka ajiyeni a gda. Hafeez har yayi niyyar cewa wani abu sai kuma yafasa, juyowa yayi yakalleta sama da wasa sannnan yace olryt nabaki nan da minti d'aya inbaki shirya ba xan wucewata. Ae Hafeez nacewa haka dasauri Meena ta miqe kafinma Hafeez yabar falon tuni tashige d'akinta hijabin dake sanye jikinta tacire tasanya gyalenta sai takalminta da tasa tad'auki wayarta a gaggauce tarufe d'akinta da kofar falo, kasancewar ita da Hafeez kowa nada nashi mukullin. Hafeez ne zaune cikin motarsa yana jiran fitowan Meena, hango ta yayi tafe sanye da gyale dasauri Hafeez yasake kallonta dakyau wani irin abu yaji ya d'arsu a zuciyarsa wanda shi kansa baisan miye ba wani irin kishi yaji domin kuwa ko da ace maqiyin Meena ne yaganta to tabbas dole ya yaba mata sbd tayi masifar kyau, cikin zuciyar Hafeez yace "lallai yarinyan nan ta rainamin hnkli ba ynxu naganta sanye da hijabi ba? Wato dan zata fita shine hadda wani sa gyale. Hafeez naganin Meena taqaraso ya watsa mata wata uwar harara, wanda hakan yasa Meena tasha jinin jikinta, a qufule Hafeez yace kee wato baki shirya fita zuwa anguwan ba shine kikayi westin tym dina? Meena tadubi kanta sama da qasa sannan tasake duban Hafeez tace "wlh yaya na shirya" Hafeez yadaure fuska yace kina nufin da gyalen nan zaki fita? Meena tafahimci abinda Hafeez yakeson cewa wato bai da tsarin son iyalinsa su sa gyale, dasauri Meena ta koma cikin gda tasanyo hijabi dukk da cewa hijabin sam baiyi matchn dakayan jikinta ba hakanan tasanya abinta domin ita dai buqatarta kawai ta jita ajikin Ammanta. Gdan baya Meena ke qoqarin bud'ewa dasauri Hafeez yace ke yar qauye wakike ajiye drivanki look inbaki shirya tafiyan ba nixan wucewata ko ancemiki banda abubuwan yine, jiki a sanyaye Meena tabude gdan gaba taxauna Hafeez yaja motan sukafice a gdan. Sanin datayi Hafeez baisan gdnsu ba shiyasa tadubeshi cikin sanyin muryanta tace "famfamari zamuje wurin masallacin juma'a, ko uffan Hafeez bai ce mata ba hakanan yaja motarsa yanufi anguwan da tafad'a mishi. Sunxo dai dai kofan gdan ne Meena tace sun iso tsayawa yayi a hnkli daga gefen hanya, Meena tasa hannu zata bud'e kofan Hafeez yace "ke tsaya yar kauye karki 6allamin murfin mota, zura hannunsa Hafeez yayi yabud'e mata kofan sannan yace, nabaki nan da awa biyar kikoma gda kinji abinda nace?" Ran Meena ya6aci sosai amma talura Hafeex neman rigima yakeyi shiyasa kawai ta gyada masa kanta tafice a motar. Meena taji dadin kasancewa da Ammanta sosai wnda har hakan yasa tashagala tamance da umarnin Hafeez. Qarfe 2 dai dai Hafeez yakoma gda amma still Meena bata dawo ba, wani irin haushi Hafeez yaji ganin cewa yadawo gda babu Wanda ta tarbeshi dukk da cewa baya kulata amma yau din sai yaji babu dadi. Wani irin tunani ne yazowa Hafeez lkci d'aya wanda yad'imautashi, dasauri ya zari car key dinshi yafice a gdan, gdansu Meena yanufa kai tsaye sbd tunawan dayayi cewa matuqar Meena tace zata koma gda tofa motan haya xata hau, tunanin Hakan ne yasa ya gaggauta zuwa yad'auko ta da kansa. Hafeez na danna kan motarsa cikin kwanar gdansu Meena nan ya hango abinda yad'aga masa hankali. ®NWA [1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:23AM, 8/5/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣6⃣ Hafeez Meena ya hango tsaye a kofar gdansu ta tsaida mai adai-daita sai faman murmushi takeyi mishi yayin da suke mgn ita da mai adaidaitan, wani irin kishi Hafeez yaji, nan fa jikinsa yafara kyarma a guje yashiga cikin layin ko gabansa ba ya iya gani mai kyau, Hafeez na pake motanshi kafinma yakasheta a hanzarce yabude murfin motan yafita batare da ya kashe motan ba. Gadan gadan Hafeez ya nufi kan mai adai daita, mai adai daita na cikin tsaka da ciniki da Meena sai ji kawai yayi anshaqo wuyansa ta baya ana dukansa ta ko ina. Dasauri Meena tafasa ihuu! Tana roqon Hafeez da yabar abinda yake yi, Hafeez kam kojin ta bayayi gabad'aya jiyake kmr ya kashe mai adai daitan sbd haushi,. ihuun da Meena takeyi ne yajawo hnklin mazan anguwar dakyar suka samu suka kwaci mai adai daita a hannun Hafeez. Idanun Hafeez gabad'aya sun rine sunkoma ja sbd tsananin kishi, a tsorace Meena tafara ja dabaya sbd gabad'aya Hafeez tsoro yabata sai wani irin huci yakeyi tamkar zaki cikin dawa, gawata uwar harara dayake jeho mata. Da gudu tashiga gdansu dai dai lkcin ne Baba Rabi takejiyo hayaniya daga waje dole tamiqe tanufi hnyar waje don ganin mekefaruwa, Meena ce tashigo gdan da gudunta sai faman waiwayen bayanta takeyi. Hafeez kam mutanen cikin anguwar sai tambayanshi sukeyi mai wannan bawan Allah yamasa? Kota Kansu Hafeez bai biba yanufi motarshi ya kasheta yarufe sannan yanufi cikin gdansu Meena din. Meena rungume Amma tayi dukk tsoro yacikata sai wani faman haki takeyi kmr wacce tayi gudun 3kilomita, Baba Rabi sai faman tambayarta takeyi Aminatu lpy kuwa meyaparu waye ya biyoki? Meena kasa mgn tayi sai faman kallon hanyar shigowa gdan takeyi a tsorace "domin atunani Meena hadda ita Hafeez zai hada" Hafeez ne yashigo gdan sallamarsa, Baba Rabi ta amsa mishi sallaman yayin da ta kura mishi ido tanajiran yafad'i da wacce yazo domin atunanin Baba Rabi shine Wanda ya biyo Meena,(domin kuwa Baba Rabi ko a hoto bata ta6a ganin Hafeez ba) Hafeez har qasa yaduqa ya gaishe da Baba Rabi, Baba Rabi ta amsa "lafiya kalaw" Lkcin ne Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar xuciya sannan tace "Amma wannan shine Hafeez yayan Balkisu" Baba Rabi ta fad'ad'a murmushinta sosai tace "Allah sarki kayi Hkri Sam ban shaida ka ba, nan tayi mishi iso ixuwa cikin gdan, A falo Hafeez yazauna Baba Rabi da kanta takawo mishi abinci tuwon semo da miyar allayahu zallah, drinks takawo mishi da ruwan sanyi. Baba Rabi da Meena kitchn suka koma suka fara had'awa Hafeez juice din kwakwa, Hafeez kam yunwa yakeji sosai dan haka bude kulan yashigayi tuwon semo yagani anyi malmalanshi ansa leda tsaf sai kuma miyan allayahu wnda taji manja, malmala d'aya Hafeez yad'iba yasa a plat bayan yazuba miyan allayahun nan fa yahauci, kafin Hafeez ya ankare tuni yagama da malmala guda"woww vry nyc Hafeez kawai ke fad'i yana lasan baki😋" Meena ce tashigo Hannunta d'auke da jug din juice din kwakwan, duqawa tayi tad'auki glass cup a kusa dashi batare da ta kalleshi ba tashiga zuba mishi. Kura mata idanu Hafeez yashigayi kmr yajawota kusa dashi haka yakeji, Meena nagama zuba mishi juice din ta tashi tabar falon a hanzarce. Hafeez jiyayi kmr baxai iya tashi awajan ba sbd wani irin qoshi dayayi, rabonsa da cin abinci kmr haka har yamanta, murmushi kawai Hafeez keyi shi kad'ai yasan abinda yasashi murmushin. Meena ce tashigo cikin falon wannan karon ba Hijabi, filas din da Hafeez yagamacin abinci dasu shine Meena tashigo danta kwashesu, Hafeez kam sai binta yake da kallo tamkar wata baquwa, Hafeez kam sai mamakin knsa yakeyi yadda ya lura cewa Meena naqoqarin zautar dashi lkci d'aya mamakin kansa yashigayi sosai wnda har Hafeez yakama tantamar anya kuwa shine? (LOL) sai da Meena ta gama kintsa falon sannan Baba Rabi tashiga falon suka sake gaisawa da Hafeez, Baba Rabi tasake da Hafeez sosai sai jansa take da fira, wanda shikuma Hafeez gabad'aya kunya tagama cikasa kasa sakewa yayi da Baba Rabi, bayan sund'anta6a hira sama sama ne Hafeez yaciro kudi Wanda shi Kansa baisan iyakarsa ba yace wa Baba Rabi gashinan tayi tsaraba, dafarko Baba Rabi qin kar6a tayi tace a'a ae Balkisu tayi musu hidima sosai dan haka baxata kar6i kudinsa ba, gabad'aya Hafeez jiyayi daraja da kimar tsohuwar taqaru a idonsa, dakyar dai Hafeez ya samu ya lallama Baba Rabi ta Amshi kudin,....daga bisani Hafeez yace da ita shi xai wuce gda dama yaxo ne dan yayi mata Allah yakiyaye hanya, Baba rabi nan tayi tasa mishi albarka tana mai nuna jindadinta sosai. Hafeez nafitowa Meena tasa Hijabinta tad'auki wayarta sukayi sallama da Amma, a hanzarce tarufawa Hafeez baya a tare suka fice a gdan. Gaban Meena sai dukan uku uku yakeyi gabad'aya taqisakewa sai faman takure kanta takeyi. ®NWA [1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:50AM, 8/6/2016] MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣7⃣ Daga Hafeez har Meena ba Wanda yace da wani uffan haka har suka isa gda, Hafeez nayi parkn Meena tayi sauri tafice a motan, tsuki Hafeez yayi cike da haushinta, a filin gdan Hafeez yayi parkn din motanshi baiko sami damar sakata ma ajiyarta ba, a hanzarce yarufawa Meena baya. Meena da sauri tabud'e kofan falon sannan tanufi d'akinta, isar take nan takama kofan da niyyar tabud'e sai jitayi Hafeez yace "kee! Tsaya anan Meena ko waigawa takasa tsaye tayi bakin kofar kmr wadda aka shuka. Hafeez nazuwa a fusace ya manna Meena ajikin Bango, take mata babban yatsanta yayi naqafa da qarfi Meena tasaki Yar qara, Hafeez yace "aikin banxa ashe kina mgn?, Meena ganin Hafeez ya kura mata ido ko kiftawa baiyi yasa tasadda kanta qasa, Hafeez gyad'a kai yayi yace "dakyau hakan Yatabbatar min da cewa baki da gaskiya sannan inaso kifad'a min uban waye yabaki izinin tare mai adai daita har kitsaya dashi kina masa dariya? Meena wacce sai mutsu mutsu takeyi tanason kwace kanta daga riqon da Hafeez yayi ma hannayenta gashi ya taka mata babban d'anyatsa yaqi sakewa, Meena kamar xatayi kuka tace nifa badariya nake mishi ba, kawai tambayarsa nayi anawa xaikain.....kafin Meena taqarasa abinda take son cewa Hafeez yadaka mata tsawa yace ni ba wannan natambayeki ba cewa nayi meyasa kike masa dariya? Meena tayi rau rau da idonu tace Dan Allah yaya kayi hkri baxan sake ba. Hafeez yace no ba laifinki bane laifina ne sbd kin raina ni ko? Meena ta girgixa kanta tace "a'a Hafeez yace okay toh yayane? Wato hakan ma yananufin cewa idan kukaje garin naku haka xakiyi behaving? Kina tare

Chapter 7 of 10