Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BURIN HAFEEZ Complet Ebook Created by Shuraih Usman Published @ www.hausaebooks.com.ng [11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION. Bismillahir-Rahamanir-Raheem. Episode 1⃣ Tasss!! Kakeji ya wanketa da kyakyawan mari, cikin hargagi da tsananin masifa yanuna ta da d'an yatsa yace "ke dabbar inace? Kina gani lokacin da nake 'ko'karin kauce miki amma saboda tsabar dabbanci da 'kauyanci irin naki shine kike 'ko'karin shigemin, salon naje nabugeki kijawomin zuwa asibiti" A gigice ta ri'ke 'kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i da azaban ciwo, batareda ta kallesa ba, cikin sassanyar muryanta tace "kayi ha'kuri, nima ba a son raina hakan yafaru ba, kaina ke tsananin min ciwo, hajijiya ce ke d'awaniya dani bansan lkcn da na tunkari motanka ba, kayi ha'kuri" Tana fad'in haka tudu'ka tad'auki bokatin awaranta wanda yazube a 'kasa, ta ratsa ta gefensa tawuce, sakin baki yayi yana binta da kallo, cikin zafin rai yace "ke!!!! Zonan" Batare da ta kalli inda yake ba tajuyo jiki asanyaye, qarasowa tayi gamida duqe kai cikin sassanyar muryanta tace gani, wani irin iska mai d'aci Hafeez yafurzar gamida xaro manya-manyan idanunsa fuska a hargitse yace ke waye ubanki agareni nan? Da har adalilina xaki xubar da kayan tallanki amma kikasa budan baki kice nabiyaki, damekike taqama stupid grl? Wasu irin xafafan hawaye ne ke kwaranya akan kod'ad'iyar fuskarta, cikin nuna rashin jindadin kalamansa tace" kai kuwa bawan Allah kai wanne irin mutun ne? Naga tunfarko nabaka hakuri sannan kayan sana'ata da suka xube bana buk'atar kabiyani" meka dauki kanka? Toh bari kaji niba irin yan'matan nan bane masu son cece kuce akan titi ba, sannan kana mgnr cewa waye ubana' umhm ubana shi ba kowa bane, kmr yadda kasani baxai iyaja da mnya kmr Ku ba. Tana fadin haka ta gyara jemammen silifas dinta wnda yake qoqarin fita a qafarta tacusa qafarta ciki tafara tafiya cike da sanyin jiki' cikin xuciyarta kuwa wani irin baqinciki da qunci gamida d'umbin damuwa ke d'awainiya da ita. Abangaran Hafeex kuwa ko k'wak'waran motsi yakasayi sbd tsananin mamaki da ya kamashi kasancewar tunda yake ganin yan mata kala-kala masu aji da marasa ajin babu wacce ya tab'a ciwa mutunci ta maida mishi da marta sai wannan jamammiyar talakar yarinyar" cikin tsananin fushi Hafeez ya fara takawa da nufin isa gurin wannan yarinyar, ae kuwa da sauri wata kyakyawar matashiyar yarinya tafito acikin motar da sauri gamida riqo hannunsa tace "plss Yaya Hafeex don't do dat 4god sake, tundaxu ina kallonku fa kasanar da ita laifinta Kuma wannan baiwar Allahn ta amsa laifinta har tabaka hkri" plss yaya kaxo mutafi gda ni ynwa nakeji gabadaya am vry tied, Fuskan nan ta Hafeez kuwa kokad'an babu fara'a yace look Balkisu pls ki k'yaleni inje inkoyama yarinyan nan tarbiyya,sbd na lura kokad'an bata da manners, cike da shagwab'a Balkisu tafara bubbuga qafafunta kmr xatayi kuka "plsss yaya nidai ka kyaleta kaxo mutafi gda," Hafeez yasake waiwayan wannan yarinya amma tuni tab'acewa ganinsa..wata uwar kwafa yayi gamida Jan tsaki ba haka yaso ba dan haka bashida wani xab'i dayawuce yashiga mota sutafi.cikin qasan xuciyarsa kuwa wani irin haushine yacikasa sbd gabadaya haushin knsa ma yakeji da bai qara marinta ba. Al'asfar Restaurant yawuce da ita kai tsaye, sbd Hafeez Sam bai qaunar ganin Balkisu na complain akan yunwa, abinci kala-kala masu kyau da tsada yasa aka kawo mata. Taci sosai"shikuwa Hafeez sbd b'acin rai koh abinci yakasaci, babu yadda Balkisu batayi akan Yayan nata yaci abinci ba amma Sam yaqi., hakanan Balkisu tadaure itama tadanci abincin ba wai don ranta yaso ba.. Jiki a sa6ule suka nufi gda, shigarsu keda wuya Hafeez yanufi sashensa cike da 6acin rai' abangaran balkisu kuwa nadama ne gamida Danasani fal acikin xuciyarta.domin kuwa ita kanta tasancewa itace silar wannan fushin nasa Sbd tahanashi aikata abinda take ganin shine dai-dai, Acikin wannan dare kuwa daga balkisu har Hafeez babu Wanda yaruntsa, sbd kowa da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa. Abangaran Balkisu kuwa talashi takobi gamida alqawarin sai tanemo wannan yarinyar a dukk indatake, sbd tabama yayanta damar cikar Burinsa. Da wannan tunanin nannauyan bacci yyi awon gaba da Balkisu. ®NWA [11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode2⃣ K'aran alarm din k'aramin agogon dake cikin d'akin ne yafara amsa kuwwa, mai nuna alamar lkci yayi' Balkisu nadaga cikin bargo tamiqo hannunta dan tsaida wannan k'aran kasancewar agogon na gefen gadonta.hannu tasa ta danna wani abu sannan k'aran yatsaya, a hnkli ta zuro qafafunta daga kangadon datake kwance yayinda idanuwanta ke lumshe, tanufi toilet, tana shiga ciki tayi brush sannan tadaura alwala, bayan tafito tafara gabatar da sallahr asubanta kasancewar lkci yayi Balkisu na idar da sallah kamar wadda aka tsikara ta tashi da sauri tafada toilet tayi wanka, dasauri-dasauri ta shirya tsaf cikin atamfarta mai ratsin orange da lemon green, Balkisu dukk da bawata doguwar kwaliiya tayiba amma kayan sunmatuqar amsarta, gyalenta tadauko Wanda yyi matchn da kalar kayanta tayafashi gamida daukar handbag dinta tanufi hnyar falo. Daniel! Daniel!! Whr ar u? Dasauri Wanda Balkisu takira da Daniel yafito daga cikin kitchn sanye da kayanshi na kuku' dasauri ya iso gaban Balkisu cike da rissinawa Daniel yace yes madam gani, Balkisu tadubi Daniel sannan tasake duban dining area kafin tace wani abu tuni Daniel yafuskanci abinda takeson tambaya" dasauri yace am very swry yau nadan makarane bnsamu na kammala brkfst din da wuri ba. Balkisu tadanyi jimm kmr baxatace komiba chan dai tanumfasa tace "it okey ynxu dame dame ka kammala"? Daniel yace madam sos din kwai ne sai ruwan xafi na tea ynxu ne nakeson daura ferfesun, Balkisu tace okay jeka kawomin tea da sos din its OK. Dasauri Daniel yashiga kitchn yaxo gaban Balkisu yacika umarninta nan da nan yahada mata breakfast, balkisu na kammalawa ta dauki handbag dinta gamida kallon agogon dake daure atsintsiyar hannunta 7:30am tagani Dan haka dasauri takira Daniel tabashi umarnin yayi sauri ya kammala brkfst din sbd ynxu Yaya Hafeez xai fito yin breakfst...cike da bin umarnin ta yace okay. Parkn space tanufa kai tsaye tadauki wata jar mota k'irar jeep, dasauri mai gadi yabude mata gate ta fice a gdan" Balkisu bata nufi ko inaba sai bolori anguwar da suka hadu da wannan yarinyar, tanashiga cikin anguwar tafara tunanin ta ina xataga wannan yarinyar tayaya xata fara nemanta. Nan take dibara yafado mata, gurin mai sai da biredi da shayi dake cikin unguwar tanufa Wanda dukk abunda yafaru jiya a gabansa ne Dan haka tayi tunanin xuwa gurinsa koh Allah xaisa yasanta. Daga gefen hanya kadan tayi parking motarta bayan takulle sannan tanufi garesa. Balkisu na isa gurin mai wannan shayin yaganeta, cike da rissinawa Balkisu tagaidashi kasancewarsa dattijon mutum, Cikin sanyin mgn Balkisu tace baba Dan Allah kokasan wannan yarnyar tajiya da wannan Abu yafaru jiya, maishayi yyi shiru cikin ransa yace"anya kuwa yadace nasanar da ita gdansu domin kuwa bnsan wanne irin tashin hnkli xataje ma wannan baiwar Allah dashi ba?" Mgnr Balkisu ce takatse mishi dogon tunanin da yatafi, baba karka damu inason ganin yarinyar ne sbd inbata hkri akan abinda yafaru jiya, mai shayi yyi murmushi yace auu toh ae shikenan, nan mai shayi yyi mata kwatance gdnsu wannan yarinyar "yace daxarar kinshiga cikin kwanar kikace anunamiki gdan Yaganaa mai awara toh babu wnda baisaniba, Balkisu tayi mishi godia tanufi inda ta ajiye motarta dasauri tanufi cikin kwanar da wannan mai shayi yyi mata kwatance, Balkisu sai murmushin mugunta takeyi domin kuwa ayau tayi alqawarin saitadauki wannan yarinyar takaita gurin yayanta yacika burinsa koh xaisauqo daga fushin da yakeyi. Balkisu nashiga cikin kwanar tanemugun parkn, sannan tafito daga cikin motar gamida kwalama wata yarinya kira keee!!"xo yarinyar dake qoqarin wucewa tagaban Balkisu tatsaya indatake batareda taqaraso wajen maikiranta ba, ganin yarinyar batada niyyar qarasowa wajenta yasa balkisu tafahimci akwai alamar tsoro atattare da yarinyar, murmushi kawai tayi gamida jehoma yarinyar tambaya tace kokinsan gdan Yagana mai awara?? Yarinyar ta gyada kai gamida nunamata gdan da danyatsa tace gashi chan gdan maibishiyar mangwaron chan. Balkisu tagyada kai gamida murmushi alamar tagane, godiya tayima yarinyar dai dai lkcin tasa key tarufe motarta sannan tanufi gdan cike da Burin son ganin wannan yarinyar . Balkisu nashiga gdan tafara jiyo ihun mutun alamar ana dukanshi, Balkisu batasan lokacin dataqarasa cikin gdan da saurinta ba gamida riqe hannun wannan mata dake dukan wannan yarinyar. Dasauri yagana tadannawa balkisu wata uwar harara gamida tambayarta kekuma fa?? Waye ke daxakishigo min gda babu sallama bare nema ixinina, Balkisu tayi murmushi gamida cewa kiyi hkri nasan bankyauta ba.Amma wannan dukan dakikeyima wannan yarinyar ne yad'agamin hnkli banmasan lkcin dana shigoba, Dan Allah baiwar Allah kiyi hkri kimata afuwa kidena dukanta haka. Dasauri yarinyar da ake duka tamiqe tsaye Dan ganin wacece tashigo cikin gdansu Dan cetonta daga hannun yagana domin kuwa iya tsawon rayuwarta idan Yagana nadukanta qa'idane babu wani mutum da ya Isa yaxo yabata hkri ko yaceceta daga dukk wata axaba daxa'a gwada mata, Dan haka tamiqe daga duqen datake don ganewa idanunta. D'agowan daxatayi kuwa idanunta sukayi toxali da wannan yarinyar wanda fad'a yahad'ata da yayanta. nan da nan jikin wannan yarinyar ya hau rawa bakinta narawar sanyi tadubi Balkisu gamida had'a hannayenta alamar Neman gafara tace Dan Allah baiwar Allah kiyi hkri inba haka ba kuma kawai kikaini police station domin kuwa nasan abnda yakawoki kenan. Abin yamatuqar bama balkisu dariya gamida tausayin yarinyar, a hnkli Balkisu taja hannunta suka nufi waje, yayinda jikin wannan yarinyar yacigaba da kad'awa alamar sanyi domin kuwa gabadaya illahirin jikinta a jik'e yake jagafff!. ®NWA [11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode3⃣ Batare da Balkisu tace uffan ba,haka taja hannun wannan yarinyar har inda tayi parkin din motarta,suna isa Balkisu tadubeta cike da kulawa gamida tausayawa gareta. Cikin nutsuwaa Balkisu tace "Baiwar Allah inasoki kwntar da hnkli ki abinda kike tunani bashi naxo aikatawa a gareki ba sbd kedin baki chan-chanci haka ba"inaso kiyishiru, kidaina kuka,kisanar dani ya sunananki"?Wata sassanyar ajiyar xuciya tayi sannan tashare hawayenta tadubi Balkisu tace,"sunana AMEENATU amma anfi kirana da Meena" Balkisu tayi murmushi, mai k'ayatarwa cikin kulawa ta dafa kafadan Meena tace"gashi sunanki mai dadi da ma'ana, ke kuwa Meena mekikayiwa mahaifiyarki haka har takemiki irin wannan mummunan dukan"??? Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, sbd tambayar da Balkisu tayimata baqaramin tab'amata zuciya yayi ba.Meena tasaddakanta qasa gamida hadiye wani kakkauran yawu tace Dan Allah baiwar Allah kigafarceni amma baxan iya sanar dake lbrina ba sbd sanin lbri na babu abnda xaiqareki dashi, sai dai abinda kika tambayeni baxanqi baki amsa ba sbd ko ba komai kinceceni a lkcin da bantsammaci hakan ba, Wani dogon numfashi Meena taja gami da qara tattare xaninta Wanda yake ajiqe, tadubi Balkisu tace wannan abun yafarune sbd laifin danayimata wanda cikin tsautsayi awaranta yaxube wato ajiye da abin nan yafaru toh shine tace lallai sai nabiyata kudinta nikuma gashi banda kudin biyanta shinefa yau da safee Aleesha tayi fitsarin kwance tadaura laifin akaina alhalin tasan cewa baninayi ba shine tad'ebo ruwa masu sanyin gaske takwaramin ajikina dukk dai hakan baimata bashine taqara da dukana kuma nasan tayi hakane dan tafanshi kudinta. Meena nafadin haka tadubi Balkisu da murmushi maicike da baqinciki da qunci,"tace nayi mamakin ganinki cikin gdanmu domin kuwa ni bantaba ganin wani mutum yaxo da nufin ceto naba sai ke kuma naji ddi ngd" Balkisu mamaki ne yagama Lullub'eta domin kuwa acikin lbrin Meena tabbas akwai alamar tambaya aciki? Dan haka Balkisu batayi qasa a gwiwaba wurin sake tambayar Meena, a hnkli Balkisu tace amma dai Meena Yagana ba itace aenahin mahaifiyarki ba koh? Dasauri Meena tace a'a itace mahaifiyata banda wata mahaifiya da ta wuceta, Balkisu ta jinjina kai cikin rashin gamsuwa da mgnr Meena tace amma Meena ga dukkan alamu sun nuna.....balkisu bata qarasa abinda takeson fadiba Meena tayi saurin zame hannunta daga riqon da Balkisu tayi mata,dasauri tafara barin wajen gamida Yiwa Balkisu godiya tace Baiwar Allah ngde da taimakonki gareni dan Allah kimin afuwa bayan abinda nasanar dake ynxu bnsan komai ba.kiyi hkri nixankoma gda ayyuka na nan najirana, Meena na nafadin haka tasa kai tashige gda.. Balkisu kam shiru tayi cike da yin dogon nazari agame da rayuwar Meena domin daga dukkan alamu yarinyar na fuskantar k'alubalin rayuwa',cikin zuciyar Balkisu kuwa taqudurta axuciyarta tabbas sai ta taimakawa Meena domin kuwa yarinyar na buqatar taimako, Dan haka yaxama dole insan komai agameda rayuwarki. Balkisu nafadin haka tashige motarta, gda kawai tanufa kai tsaye domin kuwa xuwa ynxu kwakwalwarta tagama daukan xafi, dafarko tadauka abin xaixo mata dasauqi amma daga bisani Balkisu taga sa6anin haka, Domin kuwa har yanxu dan'uwan nata bai sauqo daga dogon fushin daya dauka ba. Tagane hakan ne sbd talura ko fitowa baiyi daga cikin dakinsaba, dan haka dasauri ta ajiye handbag dinta tanufi dining area tadauki plate tahad'a mishi breakfast maisauqinci wnda tasan shiyafi so, dakinsa tanufa domin kuwa tasan baici komai ba. Sanin halinsane yasa ynxu taquduri anniyar qin biyemasa gwnda tabishi da lallashi kasancewar tasan baida ishashiyar lfy... Kai tsaye ta nufi dakinsa ta kwankwasa gamida tura qofar' Balkisu nashiga cikin dakin tasaki plate din abincin dake hannunta da gudu taqarasa cikin dakin tanafadin inalillahi wa'inna ilaihiraji'un.... ®NWA [11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode4⃣ Cikin tsananin firgici Balkisu taqarasa cikin dakin, hnklinta gabadaya ya tashe ganin Hafeez kwance a qasa tamkar gawa. Dasauri taqarasa gareshi dakyar tasamu ta gyara mishi kwnciyarsa kasancewar bisa hannayensa yake a rigingine, Balkisu kam gabadaya tafita hayyacinta sbd tsananin rud'ewa sai faman sharar kuka take tanafadin"yayana plzz katashi dan Allah katashi kada kamutu kabarni kasancewa bani da uwa bani da uba kaine uwata kaine Ubana kaine dangina" plss Yayana katashi, nan Balkisu tashiga jijjigasa tanata faman sambatu' chan kuma ta tashi tafice waje da saurinta falo tanufa tadauki wayarta hannunta na makarkata dakyar tasamu tasaita kanta tak'ira family doctor dinsu, doctor muh'd najin abinda Balkisu tafadi mishi yyi saurin katse wayar gami da cewa gani nan tafe. Dasauri Balkisu ta wurgar da wayan takoma dakinsa da gudu, ruwa tad'ibo masu dan sanyi tafara shafawa Hafeez a fuskanshi, Balkisu na cikin wannan halin tajiyo sallaman Dr muhd dasauri taqarasa gareshi tana nuna masa irin halin da yayan nata ke ciki. Dr Muh'd ba tareda yace da Balkisu uffan yanufi kan Hafeez da saurinsa, yar qaramar jakar da yashigo da ita, ita yabude ya dauko abubuwan gwaje-gwajensa, Dr Muh'd yajima yana wasu yan gwaje gwajensa akan Hafeez Wanda daga bisani yadago kai yadubi Balkisu yace "pls Balkisu stop cryn sbd wannan kukan dakikeyi bashine zai basa Lpy ba hasalima sai dai yaqaramasa ciwon dake tattare dashi" domin kuwa a hali ynxu Hafeez baibuqatar kukanki, kulawarki kawai yake buqata,"ki kwantar da hklinki insha Allahu babu abinda xaisameshi" Dr Muh'd yaja dogon numfashi gamida cire gilashin dake sanye a fuskarshi yace amma Balkisu ya akayi kika bari hakan tafaru? Sbd nasha fada miki kidaina barin hafeez na dogon wasu tunanin wnda xasuke jefa xuciyarsa cikin mawuyacin hali, domin kuwa a Halin ynxu xuciyarsa na daf da bugawa dan Allah kiyi qoqarin bashi kulawa kamar yadda kika saba, Balkisu wadda kuka yaci qarfinta tadubi Dr Muh'd tace "Dr wlh nikaina wataran yaya Hafeez nafin qarfina akan irin wannan tunane tunanen nashi sbd ba tare muke bacci ba dakinsa daban dakina daban sbd haka wasu yan tunanin da Yaya Hafeez xaikeyinsu wlh banda masaniya" Dr Muh'd yadauki jakarsa yarataya gamida xuba hannayensa cikin aljihunsa, yadubi Balkisu yace kuma fa hakane but dearis only one way inaga idan har munbi to tabbas Hafeez xai kasance cikin walwala da kuma samun ishashiyar kulawa. Dasauri Balkisu tace Dr plss sanar dani. cikin nutsuwa Dr Muh'd yabar dakin, yayin da Balkisu tarufa masa baya da saurinta. Suna Isa cikin falo Dr Muh'd yadubi Balkisu yace"hanya dayace asamu ayiwa Hafeez Aure" dam! gaban Balkisu yabuga da qarfi, cikin tsaninin tashin hnkli ta xaro mnyan idanuwanta waje tace "Dr kamanta BURIN yaya Hafeez? Ni ina ganin wannan shawaran abune mai wuya. Dr Muh'd ya danyi murmushin yaqe yace I thnk dix is d only way out! Balkisu tace tabbas hakane amma insha allahu xangwada sa'ata koh Allah zaisa adace. Dr Muh'd yayi murmushi yace"any way nizan koma i'm in hurry" Balkisu tayi mishi godia sosai. Daga bisani takoma cikin dakin yayan nata don bashi cikakkiyar kulawa. ************************* Daren ranan nan Balkisu bata samu ta runtsa ba, sbd irin tunanin da ya addabi zuciyarta a gameda rayuwarsu da irin k'alubalin da suka fuskanta cikin rayuwarsu. Balkisu ganin cewa yawan tunanin babu abinda zai haifar mata sai damuwa da b'acin rai kawai tayanke shawarar tashi tayi nafilfilu don nemawa yayan nata sauqi agurin ubangiji. Hakanan kuwa ta tashi tafada toilet tadauro alwala tafara gabatar da nafilfilunta. 'Balkisu da xarar ta idar da sallah haka xata tashi taje tadubo irin halin da yayanta ke ciki.har ynxu Hafeez baisamu ya farka daga nannayan baccin da yakeyi ba kasancewar alluran da akayi mishi don yasamu kwakwalwarsa gamida xuciyarsa ta huta. Abangaran Balkisu kam Haka nan wannan dare ya xame mata tamkar gari baxai waye ba, Adua kawai takeyi har tadan samu bacci b'arawo yyi awon gaba da ita. Kmr yadda Balkisu tasaba hakane yau ma alarm din da tasaita shine yafarkar da ita daga nannauyan baccinta, ae kuwa dasauri ta tashi tafada toilet tadauro alwala tafara sallahn asuba. tana idar wa ta tashi tanufi dakin Yayan nata dan ganin yanayin dayake ciki. ®NWA [11:48AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode5⃣ Balkisu na fita kai tsaye tanufi d'akin yayan nata. A hnkli ta tura k'ofan gami da sallama, cikin nutsuwa tashiga cikin d'akin koh da shigarta bata ga kowa cikin d'akin ba. dan haka da sauri tak'arasa cikin d'akin, don tabbatarwa idanunta. Da shigarta ciki tajiyo motsin ruwa daga cikin toilet alamar akwai mutun aciki' Balkisu batasan lkci datayi wata sassanyar ajiyar xuciya ba. A hnkli taqarasa bed dinshi nan tahau gyara masa d'akinshi, cikin qanqanin lkci kuwa Balkisu ta gyara d'akin tsaf!. Hafeez ne ya fito daga toilet, towel daure a kirjinshi da wani d'an k'aramin towel dinkuma yana tsane kansa.fuskan nan tashi tayi fayauu da ita kai dagani ba tambaya kasan yana jin jiki. A hnkli yake tafiya har ya xauna bisa gado bai lura cewa akwai mutum a cikin d'akin ba har sai da ya yaye qaramin towel din da ya yane kansa dashi. Balkisu yagani tsaye a gabansa tanayi masa murmushi. Shima murmushin yayi mata Yace"yaushe kika shigo"? Balkisu tace ban dade da shigowa ba...sannan Balkisu tadan numfasa kadan tace"yayana ya jikin naka hope kaji sauqi? Hafeez yyi murmushi yace"am fyn Qanwata naji sauqi sosai ynxuma sallah zanyi" Balkisu taji dadi sosai har tabud'e baki xatayi mgn kome tatuna kuma sai tafasa, cikin murya mai nuna alaman tausayawa Balkisu tace"yaya kayi sallah ka kimtsa barin je indawo, kai kawai ya gyada mata,Da sauri ta fice a d'akin. Kai tsaye tanufi kitchn ita da kanta tahada masa brkfst kunun gyada ta hada masa da sos din kwai (wannan shine abinda Hafeez yafi qauna ya karya kummalo dashi) bayan tagama hadawa tajerasu bisa babban tray tanufi d'akinsa dashi. Koh da shigarta ta tarar da yayan nata cikin shirinsa tsaf tamkar ba shine yakejin jiki ba, Balkisu kam tayi matuqar farinciki daganinsa haka, Dan haka da fara'arta taqarasa ciki gamida ajiye tray din a gabanshi. Hafeez dai sai kallonta yake tamkar wata baquwa,ita kuwa Balkisu sai qoqarin servn dinshi takeyi. Tana gamawa ta miqa mishi plat da cup Wanda taxuba kunun gyada, Dasauri Hafeez ya zaro idanunshi gami da sake kallon Balkisu yace"Balkisu dukk waye xaici wannan abincin? Cike da shagwab'a Balkisu taturo dank'aramin bakinta tace"yayana kai xakaci mana kamanta tunyaushe rabonka da abinci, Hafeez murmushin yaqe yayi yace xan daici Wanda xan iya" Balkisu tace toh naji amma kaci sosai ga magagungunan ka chan barin dauko ma, Hafeez baice da ita komai ba sai binta kawai yakeyi da kallo. A hnkli ta tashi tanufi site bed dinshi tadauko ledan magungunansa, ajiye masa tayi a gabanshi sannan tafice a d'akin. Site dinta tanufa tana isa ta rufe kanta cikin d'aki da gudu tafada kan gadonta. Gamida riqe kanta Wanda ke tsananin sara mata gaba daya kanta ya gama kullewa, "cikin xuciyarta tace tabbas ina buqatan neman shawara toh amma wajan waxan nema? Shiru Balkisu tayi nadan wasu dak'ik'u chan kuma ta tashi tsaye tafara safa da marwa. Babu abinda Balkisu ke tunani sai shawaran da Dr Muh'd yabata, tabbas babu mai iya bama Yaya Hafeez kyakyawar kulawa face matarsa ta sunna, toh amma taya hakan zata kasance bayan tasan cewa cikin tsarin yayan nata babu mgnr aure aciki sbd wani BURI nasa da ya kwallafa aransa. Wasu irin zafafan hawaye ne suke gangarowa bisa kuncinta tausayin rayuwarsu kawai takeyi, sai a ynxu ne take k'arajin kewa da muradin mahaifan nasu a kusa. Sai dai babu hali... Tunanin rayuwarsu na bayane yadinga dawo mata jitake tamkar ynxu abubuwan suke faruwa. *waye Balkisu da Hafeez*? [11:49AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 ✨BURIN HAFEEZ✨ 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿 By ©MUNAY ®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION. Episode6⃣ Alhaji Abdullahi Shariff shahararren d'an kasuwa ne a fannin sai da filaye da motoci da gidaje, wannan itace sana'ar da Alhaji Abdullahi Shariff keyi tuntasowarsa na samartaka dukk da kasancewarsa goggen d'an boko amma sam aikin gwamnati baya basa sha'awa shiyasa tuntasowarsa yake yan buga Bugansa har Allah yasa sana'ar takarbeshi sosai Wanda sunansa yayi fice cikin qasashe da ma nan gda najeriya, Alhaji Abdullahi Shariff d'an asalin jarha borno ne cikin maiduguri, yana da mata daya Hajiya Hauwa da yaransu uku wato Hafeez shine babba sannan Balkisu da kuma yar auta Aysha wacce suke kira da Ameerah, wannan familyn na Alhaji Abdullahi da hajiya Hauwa suntaso cike da qaunar junansu. Hafeez kyakyawan saurayi ajin farko,matashine dan kimanin shakara ashirin da takwas(28yrs)d'alibi ne a makarantar gaba da secndry wato jami'a(university of Maiduguri) yana karatu a fannin lawyer inda yanxu suke qoqarin xuwa bautar qasa,(NYSC) Inda akatura Hafeez chan kudancin najeria wato Lagos. A lkcin da Hafeez xaitafi Lagos dan gudanar da bautan qasanshi Balkisu tashiga damuwa sosai kasancewar yadda suka shaqu da yayanta da kyar da lallashi ta daina kukan rabuwa da yayanta,.. hakanan Hafeez yatattara loage dinsa yayima mahaifan nasa sallama inda Abban nashi yayi masa nasiha akan abubuwan da suka shafi al'amuran rayuwa na yau da kullum hakanan Hafeez yyima iyayen nasa alqawarin kare mutuncinsa da addinninsa, Hajia Hauwa kam hakanan tasama d'an nata albarka gamida yimishi adua na fatan alkhairi,. Har parkn space suka rakoshi inda drivansu ke qoqarin fito da mota dan kai Hafeez zuwa airport, Balkisu tanaji tana gani yayan nata yashige mota suka fice a gdan..Da fitarsu kafin suyi nisa Hafeez ya umarci drivan nasu da yafara kaishi federal lowcost. Babu musu kuwa Ali driva yajuya kan motarsa yanufi anguwar da aka umarcesa. Kafin su isa tuni Hafeez ya fito da wayarsa don kiran wacce yakeson xuwa gareta.cikin daddad'a muryansa yafara mgn "hloo baby na gani nan shigowa anguwanku plss kifito inason naganki kafin nawuce" yana fadin haka yakatse wayar dai dai lkcin ne kuma driva yyi parkn alaman sun iso knan. Kmr shud'ewa minti biyar na hango wata kyakkyawar yarinya sanye da hijab dinta har qasa, tafiya take tamkar mai tausayin qasa a hnkli cikin tafiyarta mai cike da qasaita taqaraso inda motarsu Hafeez ke parke, da sauri Hafeez yafito daga cikin motar hard'e hannayensa yayi gamida qura mata ido tamkar zai had'iyeta, "Assalamu alaikum ,shine abnda tafurta lkcn isowarta" yayinnda Hafeez yyi firgigit alamar yatafi dogon tunaninsa, a hnkli yyi wata nannauyan ajiyar xuciya gamida Amsa mata sallamarta. Hafeez ne yadubi wannan yarinyar duba maicike da kewa, a hnkli Hafeez yace "toh

Chapter 1 of 10