Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sam baya so sabodashi wai sona yakeyi muyi aure shinefa naketa binsa a hankali danmu rabu lfy. Lokacin dana tabbatar da kece macen da price manosh yake k'auna se kishi ya kamani saboda yadda na dad'e ina k'aunarsa shinefa na biya saddam kud'i harda kukata na gaya mishi k'arya tare da b'ataki agunshi,shi kuwa yace seyayi maganinki shine ya d'aukeki dukda taimakona amma gashi gashi tun ina duniya Allah yayi miki sakayya maryam dan Allah kiyi hakuri ki yafemin. Maryam ma kwalla takeyi dan yadda lubna ta bata tausayi,rungume juna sukayi lubna tanata kwalla ga azaba da takeji a jikinta. Dukkansu se suka tsinci kansu cikin nishad'i alokacin da suke rungume da junansu,harta kukan da lubna takeyi seta denashi wanda basan dalilin tsayawanshiba. Maryam ta saketa tace karki damu lubna nayafe miki har cikin ziciyata wlh fatana shine Allah yasa kar saddam ya ambaci sunanki idan an kamashi,idan kina da number'n shi kiyi sauri ki kirashi. Haka kuwa akayi number biyu duk a kashe suke seta sake kiran d'ayan liyin cikin sa'a ta shiga,ya d'auka tare da cewa hello my luv kiyi hakuri da abinda na miki kece kika tunzurani alokacin danaga kyakkyawan suranki kuwa sena sake haukacewa naji bazan iya kyalekiba,wlh dama d'aukeki nayi muka tafi kawai muci gaba da zamammu dan gaskya baiwarki daban bby kin had'u sosai. Zazzafar hawayene suke zubowa daga idanunta tace saddam ka cuceni ka cuci rayuwata wlh bazan tab'a yafe makaba mugu azzalimi d'an iska Allah ya tona asirinka...kuka ma tsanani ta fashe dashi,shi kuwa saddam se dariya yakeyi tare da cewa Allah sarki lubna bby kiyi hakuri kinji,koda an kamani nayi miki alk'awarin bazan tab'a anbatar sunanki a cikiba koda kuwa kasheni za'ayi tunda dama bani da iyaye shikenan nima sena bisu,ki kwantar da hankalinki kuma ki goge nanmaba a wayanki karki sake kirana dannima yanzu zan yarda sim d'in ne ki kula da kanki kuma ki yafemin my luv byeee. Kukan taci gabadayi,maryam ta rungumeta tanata rarrashinta. Aduk lokacin da maryam ta rungumeta setaji wani sanyi a ranta har bata so maryam ta saketa wlh,maryam tace lubna ya isa haka miyi mubar nan muje gida ki gayawa mahaifiyar komai karki b'oye mata,lubna tace wlh bazan iyaba maryam sedai inbar garinnan inje wani gurin,maryam tace ina kuma zakije bayan ga iyayenki anan lubna dolene mahaifiyarki ta sani wannan ba maganene da zamuyi shuru akaiba,saboda idan asirinmu bai tonu yau ba,tofa tuabbas zai tonu watara wanda hakan zaifi miki ciwo da zafi ina nufin kamar idan kikayi aure dolene mijin daya aureki zansan cewa keba budurwa bace wanda hakan zaija miki babban matsala wlh,amma idan kika gayawa mahaifiyar komai zaizo da sauki insha Allah. Lubna dai tak'i yadda da shawaran maryam,haka maryam ta gaji ta rabu da ita tace to shikenan Allah yasa karki d'auki ciki lubna,dan inhar kin d'auki ciki tofa nida kaina zanje har gidanku in gayawa iyauenki komai bazan b'oyeba,amma inhar baki da ciki toni na cire hannuna akai sedai kiyi k'okari ki dinga shiga cikin ruwan zafi safe da yamma insan samunema ki nemi ganyen magarya ki tafasashi da jan kanwa kina zama a ciki insha ALLAH zaki had'e amma fa bazaki koma kamar budurwaba sedai kuma zaki had'u sosai. Lubna taji dad'i sosai tace nagode sosai maryam gaskya keta dabance wlh nagode sosai,maryam tayi murmushi tace karki min godiya lubna,amaimakon godiyan da zakimin,inaso idan kin samu dama toki taimaki mutum uku suma kuma kice su taimakawa wasu ukun. Murmushi lubna tayi tare da sake rungume junansu suna masu matuk'ar farin ciki dukkansu. Ahankali suka fito babu kowa agun dan haka sukayi sauri suka k'araso bakin titi suka suka sami nape se gidansu lubna. Suna tafya lubna daga gani kasan tfyarta ya canja dukda dagewa da takeyi dan kar'a gane amma dole duk wanda ya ganta zesan akwai wani abu. Sun isa palo inda taga mahaifiyarta na zaune tana kallo,sallamarsu shiya juyo da fiskanta gunsu... Maryam tace hajiya khadeeja,hajiya khadeeja tace maryam tare da mik'ewa ta rungumeta sema a lokacin ta lura da lubna a gefe data tsaya tana kallonsu. Mum d'in lubna ta saki maryam tare da k'are musu kallo dukkansu,suma kallonta sukeyi dan sun tsorata sosai da irin kallon da take musu. Maryam tace hajiya dama lubna 'yarkice,kuma kece mum d'in marwan? Hajiya jikinta a sanyaye tace eh nice dama kunsan junane keda lubna? Tace a'a ta had'u da tsautsayine machine ne ya bugeta ni kuma ina sayya lokacin senaji ta fad'o ta jikina,to dai naga ta k'asa mik'ewa shine na rakota gida. Mum d'in lubna tace subhanalillah tare da zuwa gun lubna tanata dudduba jikinta tana mata sannu to Allah ya kare na gaba yanzu inane yake miki ciwo? Lubna tace k'afatace mum da k'yar nake takawa,tace sannu ai dole muje a duba miki kafan agun masu duban kafa koma kinyi targad'e waya sani. Shuru lubna tayi yayinda mum ta zaunar da ita tace sannu maryam ki zauna bari in kawo miki abun sha,ashe kuma haka ya faru,maryam tace eh wlh,mum tace to Allah ya kare na gaba Allah ya toni asirinsu,maryam ta kalli lubna tace ameen sannan mum ta wuce. Maryam tace nizan tafi idan kinga period naki seki gaya min,koma dai me ake ciki zamuyi waya dan yanzu kin zama k'awata lubna,murmushi tayi tace nagode maryam kin zama kamar 'yar'uwata na jini wlh bazan tab'a mantawa dakeba,wlh a tsorace nake har yanzu,maryam tace ki dena tsoro mudai jira tukunna nayi miki alk'awarin zanyita tayaki da addu'a Allah ya bamu mafita akan wannan lamarin,lubna tace ameen. Sega mum ta shigo da abin tab'awa kad'an maryam taci tace nizan tafi hajiya nagode sosai da hidimar da kikayi a gidanmu,mum tace bakomai maryam kigaida mutanen gidan dukka,tace zasuji,mum tace bari insa driver ya maidake,tace a'a wlh dasu yah ibrahim mukazo idan mun gama zaidawo ya d'aukemu yanzu kasuwan zan koma,tace eh to bari drivern ya maidake kasuwan,tace to hajiya nagode sannan ta kalli lubna tace to Allah ya sauwaka ya kiyaye nagaba,lubna tace ameen nagode. Mum d'in lubna ta rakata hargun mota sannan suka tafi. Hankalin mum d'in lubna a tashe tare da tunani mai zurfi a cikin ranta ta shige gun lubna tana mata sannu. Maryam se taji dad'i sosai a ranta tace dama hajiyace mahaifiyar marwan da lubna,gaskya sunyi sa'an iyaye domin hajiya khadija macece mai kirki sosai sannan tason maryam ita. Wayan maryam ne ya far k'ara ta duba taga samira ce,tace hello samira kuyi hakuri ganinan na kusa isowa,samira tace okey. Bayan ta ajiyene call d'in manosh ya shigo ta d'auka tare dayin sallama,ya amsa sannan yace Alhamdulillah apple mun kama saddam,k'irjinta ya buga sosai tace haba peach,yace wlh kuwa yana can gurin horo,tace tokun saki wannan mutumin,yace karki damu bazan cutar dashiba,gobe zan sakeshi insah Allah,tace to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,yace ameen apple kin gama sayayyanne? Tace eh nagama amma yah ibrahimma ya shigo jimetan kawai zamu koma tare,yace ok toshikenan ki gaishesu senazo kinji,tace yaushe zakazo,yace sedai zuwa gobe insha Allah,tace har gobe kwana d'aya fa kenan ban gankaba,dad'i yaji data nuna damuwarta agareshi,yace kinaso inzone,tace eh amma bakomai yau da goben duk d'ayane,yace to lnagode zanzo gobe da safe kinji,tace Allah ya kaimu,yace ameen aunt ki gayamin wani abu,tace *i luv u* tare da katse wayar dan kunya dataji. Dariya yaketayi tare da sauke wani ajiyar zuciya yace *i luv u 2 apple* yusuf yace tofa ai bata jikaba sedai ka sake kiranta,manosh yayi murmushi yace waya gayamaka taji mana,dariya sukayi tare da wucewa.. Maryam tayiwa drivern godiya ta tafi gunsu rash tayi d'an sayayya kad'an sannan suka kira yah ibrahim yazo suka wuce gida a motar da manosh ya sayawa maryam. Kowa gida ya wuce maryam taje ta watsa ruwa tare da alwala tayi sallah tayi addu'oi sosai. Abdallah ne ya shigo sunata hira da auntyn shi har magrif sannan ya tafi masallaci. Anata zuwa yiwa maryam da iyayenta barka harda malamai manya. Koda yaushe suna waya da lubna tana tambayarta akan shiga ruwa zafi,tace eh tana shiga sosai dan yanzu kamma tfya normal takeyi. Dad'i sosai maryam taji kuma sam bata gayawa kowa komai akan lubna,hakama shi saddam duk azabar da ake gana mishi yace shine kawai yayi ra'ayin sace maryam wabu wanda ya sashi,hakan yasa suka kaishi gidan yari aka kulleshi acan,shi kuwa d'ayan tuni an sakeshi har gidansu maryam yazo yayita mata godiya tare da tabbatar mata da cewa daga yau ya zama mutumin kirki ya dena d'aukan abun tsakaninshi da mutane sedai taimako. Dad'i maryam taji sosai tare dayiwa Allah godiya... *** Bayan wata d'aya lubna taga period nata yazo kamar dai yadda ta saba. Murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya sannan ta kira maryam ta gaya mata komai, murna sosai itama tayi tace shikenan lubna nagode,lubna tace nice da godiya damuwa d'ayane yanzu shine idan nayi aure,maryam tace inga kawai ki gayawa mahaifiyarki danki samu mafita,lubna tace sam bazata fad'aba,maryam tace to shikenan duk yadda ake ciki zamuyi waya se'anjuma. Maryam tana kwance a d'akinta wajen 10:pm seta kira yah ibrahim a waya,yayi mamakin ganin kiranta amma seya d'auka yace hello aunty lfy dai koh? Tace lfy lau kayi hakuri na tasheka,yace bakomai akwai wani abune? Tace dama shawara nake nema agunka akan wani abu daya dameni wanda bazan iya gayawa koda mahaifiyata bane bare kuma wasu amma haka kawai naji zuciyata ta raya min cewa na gaya maka yah ibrahim. Yace to aunty ina sauraronki,tace yah ibrahim wata baiwar Allah ne ta had'u da jarabawa kuma se muka had'u da ita a wannan lokacin da abun ya sameta. Nan dai maryam ta kwashe lbrn da lubna ta bata tun farkon had'uwansu da saddam har zuwa fyad'en daya mata ta gaya mishi tas sedai bata gayami ko wacece yarinyarba kuma bata gayamishi abunda lubna da saddam suka mataba kawai dai lbrn shak'uwar saddam da lubna ta bashi batare data gaya mishi sunayensuba. Shuru ibrahim yayi dan yama rasa mezaice,yace amma meyasa tak'i sanar da iyayenta,aunty wannan babban maganace wanda dole se manyanta sunsan dashi,dan haka kigaya mata ta cire wani tsoro a ranta ta sanar da iyayenta tunda ba laifinta bane wannan shine kawai shawaran da zakibata. Maryam tace yah ibrahim wlh nayi iyakan k'ok'arina dan in fahimtar da ita amma seta nunamin cewa garata gudu koma ta kashe kanta akan ta sanar dasu. Yah ibrahim yace aunty wanene wannan yarinyar? Tace kayi hakuri yah ibrahim bazan iya gaya makaba domin nayi mata alk'arin zan b'oye sirrinta. Shuru yayi yace to aunty gaskya shawaran da zan iya bata kenan dan shine kad'ai mafita agareta. Maryam tayi shuru tace yah ibrahim zan gayamaka kowacece amma inhar zaka taimaketa,yace wace irin taimako kuma ni zanyi mata aunty? Maryam ta gyara murya tace yah ibrahim taimakon da nakeso kamin shine ka amince zaka aureta. Shuru yayi tare dayin murmushi yace in auretafa kikace aunty? Tace kwarai yah ibrahim,a rayuwata babu wanda nake k'auna da burin ya zamanto mijina irinka yah ibrahim,jira nakeyi ka dawo daga bautar k'asa se'in sanar dasu baba, amma muna namu Allah yana nashi segashi su manosh sunje gun baba batare dana saniba sun nemi izini kuma baba ya amince musu,hakan yasa na amincewa manosh na kuma cigaba da addu'a wanda hakan yasa naji ina son manosh har cikin raina kai kuwa na maka matsayin " *soulmate*" d'ina, yah ibrahim wlh kaina fara so a raina kuma har gobe kai *soulmate* d'inane... Maryam bata k'arasa maganaba ta fara kwallah,yah ibrahim kuwa wani zazzafar k'aunarta yake shigansa,yace aunty kidena pls ya isa haka kinji? Tace yah ibrahim dan Allah ka amincewa buk'atata wlh yarinyar tanada hankali gata fara ce kyakkyawace sosai bugu da k'ari zaka ilmartar da ita sosai tafannin addininmu. Yace shikenan aunty na amince koda mummunace ita tunda dai ke kika zab'amin ita na yarda zan aureta kidena kuka kinji aunty, "i will do anything just for you aunty" shikenan? Bazan iya misalta muku farincikin da maryam ta shigaba,bata san lokacin datace "i love you so much uncle" dad'i yaji yace to wacece ita yarinyar? Tace sunanta lubna k'anwar marwan ne wanda zai auri rashida. Mamaki sosai yayi yace to shikenan ki kwanta kiyi bacci zanzo da safe kinji,tace to nagode sosai seda safe... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *dedicated to mace tagari*❤)*❤)* 47-48 Washe gari da safe yah ibrahim yaje suka gaisa da mama sannan sukayi hira sosai da aunty harta bashi number lubna dan dama tun a jiyan ta sanar da lubna komai,dukda dai lubna taji kunya sosai,amma setaga koba komai ai asirinta zai rufu tunda shi yah ibrahim yasan halin da ake ciki kuma ya amince zai aureta a hakan. Lokaci yanata tfy,ibrahim da lubna suna waya sosai dan ta turo mishi da pic nata ta whatsapp shima kuma ya tura mata amma bai tab'a zuwa gidansuba. Koda yaga pic d'in lubna mamaki sosai yasha dan kawai seyaji k'aunarta na k'aruwa a cikin ranshi tare da addi'an da yakeyi akanta. Itma lubna ta yaba sosai dan yah ibrahim ba irin mazan da mata zasu k'ishi bane. Hakanan suketa soyayyarsu,wanda har abdallah yasan lubna suna gaisawa sosai. Ita kiwa maryam seta tsinci kanta cikin farin ciki da kwanciyan hankali mara misaltuwa. Ranan taje jimeta aike tana cikin keke nape seta hango manosh tsaye da wata budurwa wanda sam bataga fiskartaba saboda yana tsayene dab gabanta. Kuma ta tabbatar da cewa manosh ne dan taga motarshi sannan kuma ga marwan a gefe yana tsaye rai abace,se taga manosh ya bud'ewa budurwa kofar motarshi na baya harta shiga se kuma ta sake fitowa ya bud'e mata gaba ta shiga. Maryam ta kira number manosh dan tabbatarwa,ai kuwa seta ya d'auka tare da cewa hello,tace ya kake,yace lfy lau zan kiraki anjuma kinji,tace meyasa kana wani abune? Yace eh kiyi hakuri zan kira kinji,tace ok sannan ta kashe wayar tanata binsu da kallo setaga shima ya shiga mazaunin driver yaja suka tafi yayinda marwan yake tsaye agun rai a b'ace. Hankalin maryam ta tashi sosai ta rasa meke mata dad'i,tace wato dama da manosh yake cemin mata 2 ko 4 zaiyi kenan yana neman wata...? Da wannan tunanin ta koma girei,bayan ta ajiye aiken da mamanta tamatane seta wuce d'aki ta kwanta har yanzu manosh bai kirataba ita kuwa ta kasa hakura seta kirashi. Hello apple kiyi hakuri wlh am busyne shiyasa ban sake kirankiba,tace busyn me kenan,yace ki bari kawai hidiman dewa pls kimin hakuri zan kira pls,tace bakomai se'anjuma,yace ok tnx luv u,shuru tayi tare da katse wayar. Abin ya d'an dami manosh amma dayake yana da abinyi sosai sebai sake kirantaba. Har la'asar bai kiraba,ita kuwa maryam abin yana cinta sosai a rai,manosh bai kirataba harse bayan magrib yace da ita am so sorry apple zanzo bayan sallan isha kinji,shuru tayi mishi,ya sake nanata tace sekazo tare da katse wayar,sake kiranta yayi ta d'auka batare datayi magana ba,yace apple are you okey? Tace ues am fine,yace amma naji muryanki wani iri,tace bakomai sekazo... Abun ya dami manosh sosai dan haka suna idar da sallan isha suka taho shida muh'd da marwan. Kamar kullum muh'd da marwan sun tafi k'ofan gidansu rash da mota shi kuwa manosh suna zauren gidansu maryam inda ta shinfid'a mishi k'aramin carpet tare da kawo mishi fruit kamar yadda ta saba dantasan yana son fruit sosai shiyasama bata rabuwa dashi a gida. Manosh yaga canji sosai tattare da ita hakan yasa ya ajiye wayarsa a gefe ya maida kallonshi gareta,ita kuwa kanta na kallon cikin gidansu kyakkyawar gefen fiskanta yake kallo tare da b'akin takalmin dayayiwa kafarta kyau yace apple lfy kuwa,tace lfy lau batare data kalleahiba. Yace toyana ganki haka kodai bakya jin dad'i ne,tace a'a lfyta k'alau,yace tomeyasa tunda nazo yau baki kalleniba kuma gashi sam baki sakeba kamar namiki laifi? Juyowa tayi suna kallon juna har cikin ido sannan tace kwarai kuwa kamar ka sani,seta sake mayar da kanta gefe, murmushi yayi yace pls apple ki bari fushin bai karb'ekiba wlh tomenayi nikuma yau? Ta sake kallonshi da kyau sannan ta juya,murmushin ya sakeyi yace kidena min wannan kallon kina bani tsoro wlh,shuru tayi batace komaiba,yace wai dagaske kike yine aunt,to pls ki gayamin laifina so that in nemi yafiyarki kinji,tace bakomai zan shiga gidane, yace ok to jeki mana yau harse kin nemi izinin shiga gida? Tace ina nufin zanje in kwanta bacci nakeji,shuru yayi yana kallonta cikin mamaki seyace ok badamuwa bari inji kosu marwan sun gama,nanya kira marwan tare da sawa a handsfree yace ya kun gamane mu wuce? Marwan yace kaji gayennan fa danka gama muma semu gama,manosh yayi murmushi yace bahakabane bata jin dad'ine shiyasa,amma shikenan bari na shiga masallaci nima inji karatu idan kun gama seku tab'ani,marwan yace ok ka gaisheta pls,yace zataji. Manosh ya kalleta yace apple zan tafi kije kiyi baccin kinji,mik'ewa tayi batare datace komaiba zata shige yace tsaya ki tafi da carpet d'in. Cak kuwa ta tsaya ya nad'e tare da d'aura mata tiran friut d'in danko d'aya bai shaba yau,tausayinshi ya kama maryam se kuma bataji dad'in abinda ta mishiba,matsowa yayi kusa da ita inda suke jin kamshin turaren junansu yace gashi,friut d'in ta kalla sannan ta kalli idonshi wanda shima idon nata nake kallo cike da tausayi ta kawar da kanta gefe tare da karb'a ta wuce da sauri batare datace mishi komaiba yanata binta da kallo harta tafi sannan shima ya fito ya shiga masallaci amma shi kad'ai yasan abinda yake damunshi hakama ita maryam d'in koda ta shiga gida friut d'in tasa a gaba tanata kallo tare dajin kwalla yana zuba a fiskanta. 9:30pm su marwan sukayi hon wa manosh wanda har ita maryam taji hon d'in kuma tasan sune zasu wuce,sam bataji dad'in abinda tayiwa manosh ba. Manosh yace musu yau sam banganewa apple ba,akwai wani abu amma tak'i gayamin. Muh'd yace kodai jikintane to,manosh yace sam bahakabane akwai dai wani abu daban dan sam tak'i sakemin yau kamar wanda nayi mata wani laifi kuma tak'i cewa komai. Abin ya d'aure musu kai sosai haka suka koma gida yayita kiran wayanta amma sam tak'i d'agawa yayi texs shima shuru bata amsa mishiba hakan ya tabbatar mishi da cewa fushi takeyi dashi. Washe gari tun asuba yake kiran numberta amma tak'i d'auka abin ya dameshi sosai dan sam jiya bai samu yayi bacci gashi kuwa yau zaiyi tfya zaije lagos ama 2days kawai zaiyi,haka yayi sallama dasu mum da marwan sannan ya tafi. Koda yaushe seya kira number apple amma sam bata d'auka daga karshema ta rufe wayan nata gabad'aya. Abun yayiwa manosh ciwo sosai,bayan abunda ta mishi ranan shi baiyi fushiba,bai kuma san laifin daya mataba dan haka shima yasa a ranshi cewa bari dai yad'an kyaleta na 2days maybe kafinnan zata huce. Da magariba maryam ta bud'e wayanta amma ga mamaki bataga texs d'in manosh ko d'ayaba. Hakan yasa tad'an damu kad'an tanata zaman jira har bayan isha shuru. Manosh dai bai sake kiran maryam ba harya gama 2days nashi a lagos ya dawo gari. Kuma so da yawa idan suna tare dasu rashida yakan kirasu su gaisa amma sam ya dena kiranta,hakan yasa ta damu sosai kuma tana matuk'ar son ganinshi. Yau wenesday bikinsu manosh saura 9days kawai,abun ya dami maryam sosai tanata tunani aranta. Bayan ta idar da sallan azaharne sega wani yaro yazo yace auntyn yara ana kiranki a waje,tace wanene,yace wanda yake zuwa gurinkine,nan taji dad'i a ranta dajin cewa manosh ne, tace to jeka kace ina zuwa. Atamfa tasa d'inkin riga da siket tare da himar kalan atamfar peach colour tayi kyau sosai. Tunda take fitowa yake kallonta harta k'araso da sallamarta,ua amsa tare da cewa kin kyauta apple da kika maidani haka,fiskanta a had'e tace kaima ai ka kyauta. Yace menayi,kalonshi tayi har cikin ido tace bansaniba,yace ni kikema wannan kallon ko, wlh appale idan kika shiga hannuna ko hmmm. Kunya sosai taji tare dayin mirmushi tace ina wuni,lfy ya mama,lfyanta k'alau,ya rashin kirkinki,tace muna fama dukkanmu,mirmushi yayi yana danna wayanshi. Tace ka fara ko,nifa bana so mun magana kana tab'a waya,kallonta yakeyi harda dakewanta,wayan nashi ya d'ago yace kalli nan,juyowa tayi tana kallonshi inda ya nuna mata wayan,mamaki sosai tayi da ganin pic nata akan wayan lalli kuwa wato dama d'auka hoto kakeyiko,murmushi yayi yayinda pic nata suketa wuce akan screen nashi kala kala,mamaki sosai tayi wato duk lokacin da suke tare pic yaketa mata yana k'are mata kallo. Katseta yayidan ya sauke wayanshi k'asa yace tun randa mukazo shop din baba nakeda pic naki har ranan yau. So duk lokacin da nake tare dake muna hira ina kallon ki a wayana,tace oh shiyasa ni kake cemin in dena kallonka ko,yace eh mana ni bana so ana kallonane shiyasa,murmushi tayi tace ina miher,yace oho ban saniba,tace haka kace ko,yace eh nima yau na dawo daga lagos kwanana biyu acan dana dawo ban sameta a gidaba taje gun k'awarta. Maryam tace baka gari? Yace yes ai kece kika cazamin kai shiyasa nima na tafi,kuma nayi iyakan k'okarin in sanar dake kink'i picking call nawa bansan wani irin laifi nayimikiba. Tace lallai ka kyauta,yace wlh bani da laifi apple kece da laifi dan haka kibani hak'uri,murmushi tayi tace bashakka kuwa ai kamin laifine shiyasa,yace to amma idan na miki laifi bazaki gayaminba apple sedai kiyita wulak'antani dan kinsan ina sonki ko? Tace hmm su so manya,kallonta yakeyi sosai yace bakiyardaba kenan,tace dakam ina sane da wannan son,amma ayanzu kam bansaniba konice ko kuma ita. Kallon juna sukeyi yace me kikace apple? Tace eh aikaji abinda nace. Yace pls ki gayamin ban ganeba,tace wata yarinyace na ganku da ita ranan kana tsaye dab da ita marwan yana gefe,harka bud'e mata k'ofa kuka tafi kuka bar marwan agun,kuma na kiraka alokacin amma sam kaki kirana da sunan daka saba gayamin sema cemin kayi wai zaka kirani anjuma shine baka kiraniba harse bayan magrib shine kukazo kaida muh'd da marwan. Tabbas manosh ya gane komai dan haka ya shiga yin dariya sosai kamar bashiba,yace kardai kicemin shine dalilin dayasa kika min wannan horon,shuru tayi tana kallonshi rai ab'ace shi kuwa dariya sosai yakeyi yace haba aunt gaskya bakimin adalciba dama ashe kina da kishi apple,dariya sosai manosh yakeyi wanda hakan ya tfyar da hankalin maryam ta tsaya kallonshi tana murmushi,dariyanshi yana mugun kasheta dan wani kyau na musamman yakeyi,manosh ya lura da irin kallonsa da takeyi wanda ita kanta basan tanayiba,hakan yasa ya dena dariya shima ya tsaya kallonta tare da juyawa yaga ba mutanen sam a inda isuke,hakan yasa yace mata zonan aunt,se yanzu ta dawo saiti tace nak'i,yace pls ki matso apple,tace meyasa,yace toki dena pls kallona banso saboda kina tafiyarmin da hankali aduk lokacin da kike kallona wlh. Shuru tayi tare da kallon wani girin gabad'aya kunya ya kamata shima ya lura da hakan dan haka ya kira marwan a waya yace abokina gani agun aunt,marwan yace kace komai ya daidaita kenan?manosh yayi murmushi yace zai daidaita dai kasan meyasa take fushi dani,marwan yace seka fad'a menen wai? Yace randa dad ya aikemu muka fito se muka tsaya a gefen gidan man su muhsin. Marwan yayi dariya yace kardai ince taganka kaida lubna lokacin da nake mata fad'a? Dariya manosh yayi yace to wlh fushin da takeyi dani kenan waita d'auka budirwatace. Dariya sosai sukeyi marwan yace haba aunt har kina sa ran abokina zai iya hango wata bayan ke,murmushi tayi tana sauraronsu,marwan yace wlh lubna ce k'anwata kuma laifi tayi yasa nake k'okarin hukuntata shine abokina ya shiga tsakaninmu yace muje mu maidata gida,danace bazan jeba suje shine yace da lubna tota dawo gaba ta zauna se suka tafi ni kuwa ina jiranshi yadawo wannan shine gaskya aunt,ai wlh ki kwantar da hankalinki mu sam iyayenmu zamu gada mata d'aya kawai is okay,manosh yace a'a nidai 2 zanyi dan nama gaya mata kuma tsarin gidanama na mata biyune,nagode daka wankeni marwan sena shigo,yace ok a gaisheta,manosh yace zataji amma gaskya na canja mata suna daga *apple zuwa jealousynah*, ba marwan kad'aiba harda ita maryam dariya sosai tayi wanda harshi marwan yana jiyowa. Bayan sun gama dariyanne manosh yace *jealousynah* ina so mufitane bazamu jimaba kije ki sanar da mama kinji? Tace nifa bana son wannan sunan,yace okay apple,murmushi sukayi tare tace inane zamuje? Yace cikin jimeta amma yanzu zamu dawo kinji,tace to bari inje in gayamata,ok yace da ita sega abdallah yazo gunshi. Mama tace to maryam ki kula da kanki ki kuma ji tsoron Allah aduk inda kike,tace to mama nagode sannan tafito. Tace nagayamata,yace ok muje harda abdallah,nan abdallah ya bud'e mata gaba yace auntynah kishiga,murmushi tayi tace kaidai ka shiga nizan zauna a baya,haka kuwa akayi suka kama hanyan jimeta,shi kuwa manosh wayansa ya d'auka yayiwa maryama texs nan ta duba kamar haka tagani. _Hi my jealousy_ _I love you so verry much_ _Kuma ki dena wahalar dani pls,saboda ni manosh nakine ke kad'ai batare da kowaba,kwanaki kad'an suka rage in mallakeki apple jealousynah_. Murmushi sosai taketayi bayan ta gama karantawa,shi kuwa yanata kallonta ta mirrow yana tayata murmushin. Tun daga nesa abdallah yake gango wani had'add'en gida mai penti cream da kuma d'an army green yace gaskya gidancan ya had'u,manosh yace ko,abdallah yace sosai wlh koba hakaba aunty? Maryam ta kalli gidan tace hakane k'anin aunty. Daidai gidan manosh ya tsaya,dama maigadi yana baiwa flower ruwa ata wajen gate dinne,da sauri ya ciro remote a aljihunsa ya danna se gate d'in ta bud'u sannan suka shige ciki,daga maryam har abdallah bud'e ido sukayi sosai suna kallo.. [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTU'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *dedicated to nurcee lurv*😘😘❤ 49-50 Bayan sun fitone manosh ya rik'o hannun abdallah kamar wani yaro k'arami yace muje d'an gaban goshin aunty. Murmushi abdallah da maryam sukayi,ya kalli apple yace muje _jealousy_ tare da mata gwalo ya kashe mata ido d'aya wanda ya bata dariya tana biye dasu. K'ofa ya bud'e suka shiga palon farko babbane sosai wanda yasha wll peper army green mai tsadan gaske da labule ga kujeru da standart AC,can gefe kuwa daining ne shima komai army green ne harda frdje d'in. Akwai d'aki babba komai white ne a ciki,se kuma d'ayan d'akin blue amma bakomai daga gani kasan d'akin boys masu zuwane. Se katon kichine da store wanda farin tiles ne kota ina ansa gas da frezer ne kawai. Abdallah ya kalli aunty yace abokina white d'akinnan na wayene,yace nawa ne,blue d'in kuma na

Chapter 8 of 17