Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da zaura an d'auketa wayanta a kunne yake inaso kabin min line nata pls insan a ina take da sauri dan Allah. Da sauri faruq ya fara neman line na maryam amma baiga komaiba da tana inda babu netwrk,nan ya sake duba kira na k'arshe daya shiga wayarta ba'a d'aukaba yaga lokacin tana *gurore* sannan yanzu baya iya ganin inda suke. Faruq ya kira manosh yace captain d'azu kaine ka kirata last kuma ya shiga lokacin tana gurore. "Whats! Gurore fa kace faruq? Faruq yace tabbas captain karka damu zanci gaba dabin line d'in inga suna inda ba netwrk ne. Katse wayan manosh yayi yace ina tausaya musu wlh tunban kamasu kowaye yayi miki wannan aikin "he will pay for it wlh" dan bazan barshiba. Marwan yace muje gida mu shirya manosh,manosh yace no karka damu ka koma kawai yanzu motarmu zaizo zamu bi bayansu,marwan yace ok "dude but pls becarefull,daidai nan motan sojojin ya iso wani ya fito daga gaba manosh ya shiga sannan shi ya shiga baya suka tafi,sega majid yazo suka wuce girei gun iyayen maryam,koda marwan ya gaya musu inda maryam take mamaki sosai sukayi,mahaifiyarta kuwa kuka sosai takeyi,makota sunata bata hakuri. Abdallah yana zaune a masallaci tare da samari da sauran yara anata karatun qur'an amma abdallah hawayene kawai yakebin fiskanshi. K'awayentama duk sunzo sunata kuka Manosh ya kira muhsin yace pls zan tura maka pic na apple kai gidan TV da radio dake adamawa dukka duk wanda yaba da wani bayani akwai babban kyauta ageshi,mihsin yace ok "dude" pls ka kwantar da hankalinka insha Allah za'a sameta cikin k'oshin lfy,manosh yace Allah ya amshi addu'anmu tnx "dude" sannan ya katse wayan. Maryam ta fara bud'e idanunta tare dayin addu'a harta gama bud'esu dukka tana k'arewa d'akin da take kallo. Katiface kawai a d'akin da wani zanin gado se tsami yakeyi ga akwati da tarin taba wiwi dasu totolin sune kawai a wannan d'akin. Nan danan taji gabanta ya fad'i tanata addu'a tare da mik'ewa ta murd'a kofan amma setaji a kulle yake,nan ta tuna da wayanta datasashi cikin pants nata tun lokacin da suka bige mata abincin babanta. Da sauri tasa hannunta akan pants d'in cikin ikon Allah taji har yanzu wayan yana jikinta,hamdala tayiwa Allah sannan ta ciroshi da wuri dama a silent yake,kodata duba missed calls babu adadi a cikin,da sauri ta kashe wayan gabad'aya dan ganin 7:00pm ne ko sallan azahar batayiba. Kofan data gani ta bud'e taga toilet ne amma babu kyan gani sam a cike yake da k'azanta,hancinta ta d'aure da d'ankwalinta ta shiga da yake akwai ruwa ga kuma morning fresh da izal nan da nan ta wanke shi tas sannan tayi alwala wayanta yana cikin pants nata ta shinfid'a d'ankwalinta tayita biyan sallolinta. Tana cikin yin sallanne se taji ana bud'e kofan tare da shigowa. Daga jin muryanshi kasan d'an giyane,yana cewa daga zuwanki har kin fara mana kashi ko kashi kin bud'emu da wari kota ina,koda yake shinkafa da wake kuka dafa a gidanku yau shiyasa,ga abinci nan idan kin gama sallan sekici,bayan ya ajiyene ya d'auki kwalin sigari sannan ya tafi. Bayan maryam ta idar da sallolintane tare,dayin addu'in neman tsari sannan ta dubi abincin daga gani a resturant aka sayo,amma sam bata ciba seta tashi tasa sakatan d'adkin ta ciki sannan tashiga toilet ta kunna wayanta tare da kiran number'n mahaifinta bai d'aukaba dan yana tlband'aki,dan haka ta sake kiran mahaifiyarta bugu d'aya ta d'auka tare da cewa maryam,maryam tana magana a hankali tace na'am mama sannan,ta fara kuka tana cewa mama ya kuke ku kwantar da hankalinku ina halin lfy amma bansan a ina nakeba...bata k'arasaba taga call d'in manosh,tace mama zan sake kiranki bari inyi magana da manosh,to maryam Allah ya kareki zan sake kiranki bayan kunyi wayan kiyi k'ok'ari kozaki gane inda kike dan azo a taimaka miki su waye suka d'aukeki? Maryam tace wlh mama har yanzu bansan komaiba ina kullene a wani d'aki banga kowaba har yanzu. *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*suketa nanatawa ita da mamanta suna hawaye amma ita maryam daurewa takeyi kar ajita tana waya azo a karb'e. Banyan maryam sun gama hira da mamane se call d'in manosh ya shigo. Da sauri ta d'auka tare da cewa hello peach,wani sanyi yaji har cikin ranshi yace apple ina fata basu miki komaiba,cikin muryan kuka tace eh bakomai amma ina jin tsoro sosai dan ga dukkan alamu mutanen bana garibane domin kayan shaye shaye ne cike a d'akin kota ina peach,hankalin manosh ya sake tashi sosai yace ki b'oye wayan apple zan kiraki anjuma i love you aunt ki kula da kanki pls zanyi k'ok'arin gano inda kike kinji? Ok Allah ya taimaka peach bansan inda nakeba bare in gaya maka,pls aunt ki dena kuka "i will soon come to you" nasan inda kike already,ina nake pls ka gayamin,calm down apple kina *numan* ne nima yanzu haka muna numan d'in zanzo inda kike yanzu ki b'oye wayanki zan kiraki anjuma okey? Ok thankyou,i luv apple,i luv u too byeee... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *dedicated 2 miemie bee*👄 33-34 da sauri maryam ta share kwallanta dan kar azo a ganta. Manosh kuwa wani iri yaji a ranshi sam baiso ya bartaba amma babu yadda zaiyi,awaje ya samu muh'd sukayi sallama ya sake jaddada mishi cewa ya kula mishi da apple shidasu majid. Manosh ya isa kd lfy,yana isa maryam ya fara kira,taji dad'i sosai suka d'an tab'a hira sannan sukayi sallama. Hajiya iya dake zaune a gefen maryam tace surukin nawa kenan shine ba'a tab'a kawo minshiba,dariya maryam tayi tace saurin me kikeyi hajiya ai dole zaizo ya gaisheki dan kece babbar k'awa. Dariya sukayi dukkansu maman rashida tace to maryam mudai zamu wuce Allah ya baki lfy,tace ameen mama nagode. Hajiya tace ni wannan mota naki semun rabata gaskya,ya zaiyi ya kawo miki bai kawomin,rash da maman maryam sunata dariya,maryam tace karki damu wai yasan ke baki da k'afane bazaki iya tuk'iba kinga ni se inyi ta kaiki duk inda zakije ko? Nanma dai dariyan akayi daidai lokacin samira zahida da ameena suka shigo da sallama. Bayan an gaisane su maman rash suka fita inda yah ibrahim ya mayar dasu a motar maryam. Maryam da k'awayenta se hira sukeyi tare da tayata murnan samun mota. Sosai maryam take samun jama'a harda malaman islamiyyansu se zuwa gaisheta akeyi dayake ita mai jama'a ne sosai. Daga masu kawo mata fruits se masu bata kud'i,su kansu doctors da nurses d'in sunata mamaki har tambaya sukeyi wai maryam d'innan 'yar wayece a garinnan dan yadda jama'a suke sintiri agunta. Shi kanshi dr muh'd yaji mamaki sosai,dan haka ya kira manosh yace gaskyaka samu mata wlh ka rik'eta da kyau sannan mu dami su dad akan ayi maganan aurennan da wurifa. Dad'i sosai manosh yaji yace insha Allah. Maryam ta samu sauk'i sosai koma ince ta warke. Da yamma miher da mum nata sukazo inda miher ce tayi driving nasu gwanin sha'awa. Lokacin maryam ta idar da sallan la'asar kenan tana addu'oi setaji bud'e kofa tare da sallama,mamantane ta amsa musu dan rash ta koma gida. Koda maryam ta idar,kunya sosai taji da ganin mum d'in manosh. Kanta a sunkuye tace sannu da zuwa,mum tace yawwa maryam sannu ya jiki,maryam tace da sauki ina wuni,tace lfy lau ya kika k'ara ji da jikinki,tace da sauki,mum tace to Allah ya k'ara lfy Allah kuma ya yaye miki,maryam tace ameen gabad'ayansu sannan mum ta zauna kusa da maman maryam akan carpet dake shinfid'e a k'asa,ita kuwa miher ta zauna a gefen maryam tana zolayarta matar bro kin samu lfy se kuma magan aurenku da bro,ahankili tayi maganar cikin zolaya tana dariya. Maryam data kasa sakewa dan kunyan mum murmushi kawai takeyi,miher tace wlh ki dena jin kunyan mum dan bata da matsala sam wlh garama ki saki jikinki bro yace in kawo miki wannan,flower ne d'an k'arami maiban sha'awa,amma maryam taqi karb'a dan kunya,miher se dariya takeyi tace idan bakya so shikenan se in gaya mishi yanzunnan,muntsinin miher tayi ta cinyarta batare dasu mum sun ganiba. Daroya sosai miher takeyi tace shikenan nifa wasa nakeyi kar anjuma inji kin cijeni,mirmushi sosai maryam tayi tajin kalmar miher amma sam taqi tayi magana,mum ma ta lura da cewa maryam a takure take dan haka tace miher mu tafi ko donmu barta ta huta. Murmushi maryam tayi miher ta mik'e,maryam tace mun gode Allah ya kare,mum tace ameen sannan tayi gaba itada maman maryam. Ai suna fita maryam ta karb'e flowern tace wlh sena had'aki da captain kinata sani magana bayan kinsan bazan iyaba ko,miher tayi dariya tace nima ai zan gayamishi harda muntsinin da kika min,dariya sukasa dukkansu sannan tace miher mungode sosai ku bakwa gajiya da d'awaiyinane pls bana buk'atar wani abu kuma dan Allah ya isa haka mana,miher tace dani kikeyine,kallonta maryam ta tsayayi tace ni kike mannawa hauka ko,miher tace "am sorry our wifey" ban isa in manna miki haukaba wlh amma wlh mum bazata tab'a yarda inzo dubaki empty hand bane nizan tafi nabar mum tana jirana zamuzo gobe nida *my majid* kafin a sallameki *apple* tate dajan lallausar kumatun maryam. Dariya sosai maryam takeyi yayinda miher ta fita da sauri tana mata byee,ita kuwa murmushi takeyi tare da cewa tonagode Allah ya kiyaye hanya. Maman maryam ta bud'e ledojin kayan tea ne manyan gwangwanaye da kuma fruits. Mama ta kalli maryam tace sude basa gajiya wlh,mamansu tana da kirki wlh gata da sauk'in kai kamar ba matar mai kud'iba kuma naga soyayyarta akanki sosai wlh. Maryam tayi murmushi tace wlh mama hakama miher tana sona sosai wlh gaskya ba laifi Allah yasa su d'aure a haka,mama tace ameen sannan sukaci gaba da hiransu irinna *uwa da 'ya*. Yau aka sallami maryam,babantane ya d'aukesu a motarshi inda sukaitawa dr muh'd godiya, cikin girmamawa yace wlh bakomai baba Allah ya bata lfy,suka amsa da ameen sannan maryam tace nagode fa sosai da k'ok'arinku Allah yabar zumunci,murmishi yamata tare da cewa ameen aunty bakomai semunzo girei,tace wlh na hutar daku hakama yayi wlh sannan ta tafi yana musu Allah ya kiyaye. A girei ma tinda maryam ta dawo zuwa ake ana gaisheya. Bayan kwana biyu ne miher tazo da drivernsu da kula sabuwa babba a hannunta peppe chikeen ne a shike. Murna sosai maryam tayi da daginta suna d'an tab'a hira sannan ta mik'e tace zan tafi dan akwai inda zanje wlh sannan ta bud'e zip na jakanta ta ciro flower tace inji camtain. Murmishi maryam tayi tace nagode bari in wanke kulan ki tafi dashi,mihe tace no wlh danke kawai na sayi kulan dan haka shima nakine. Gidiya sosai maryam tayi tare da rakota har waje sukayi sallama. Bayan tfyantane samira da rsha sukazo sukaita hira,maryam ta d'ibo musu kazan sunaci suna hira inda maryam take sanar dasu cewa gobe za'azo tambayarsu. Washe gari da misalin 10:00am na safe iyayen manosh dasu marwan sukazo girei domin tambayan auren 'ya'yansu. Dama baban maryam yasan da zuwansu dan haka shima ya nemo mahaifin samira da kuma 'yan unguwa dan shine uban maryam da rashida dukka. Koda sukaga mahaifin manosh masu ji mamakiba dan yah ibrahim ya musu bayanin komai kuma yace ya yafe harma da maman rash,amma baban maryam yace dole za'a sanar dashi kodon yasan yayi kissa kuma *azumi sitti* yahau kansa. Zuwan manya sukayi da iyaue su majid,dan seda sukayi tambayan zahida da amina sannan sukazo girei. Karb'a na musamman aka musu inda aka gaggaisa kuma aka fahimci juna ansa aure nanda 3month. Bayan an gamane sukayi godiya sannan suka tafi. Bayan sun koma gidane mahaifin maryam ya kira mahaifin manosh yace dama inaso muyi wata magana mai muhimmancine akan wani bawan Allah daka tab'a bugewa akan hanya girei shekaru biyu da suka shige,idan baka mantaba akwai wata yarinya dataketa bin motarka a wannan lokacin tana kuka. Jikin mahaifin manosh yayi sanyi dan baizai tab'ance wannan rananba. Baban maryam yace to wannan mutumin bakowabane illa mahaifin rashida wanda marwan yake neman aurenta,tun daga wannan lokacin daga bugeshi ko minti goma bai k'araba Allah yayi mishi rasuwa. A wannan lokacin akwai wanda ya ganka shine da kukazo girei yace lallai kaine wannan mutum, yanzuma na gaya maka hakanne dan kasan cewa azumi yahau kanka,sannan yana da kyau ka nemi gafarar iyalansa,wanda ya gankan bakowa bane illa d'an cikinsa wanda yazo ya gaisheku mai suna ibrahim wato yayan rashidan kenan,amma sunce sun yafe har abada sun d'auki kadda. Mahaifin manosh ya sauke ajiyar zuciya yace nagode sosai alhaji Allah yabar zumunci,kuma wlh naji dad'i sosai da yadda kamin magana a sirrance Allah ya saka da alkhai kuma insha Allah gobe zanzo gun iyalan marigayin,wlh tun wannan lokacin nima bani da sukuni kuma na koma girein na tambayi wani matashi akan wani da aka buge da mota nan ya tabbatar min da cewa Allah yayi mishi rasuwa,wlh tun daga wannan lokacin na kamu da hawan jini kuma nayi azumina sittin,sannan nayi aike zuwa ga iyalan wannan mutumin a wannan lokacinma sedai na hana abayyana sunan,kuma nasan nayi kuskure sosai wanda hakan shiyasa na gyara halayyata da dama alhaji nagode sosai kuma insha Allah gobe inanan zuwa girei da safe. Mahaifin maryam ya tuna da randa akazo da abinci da kaya da kuma kud'i har *dubu d'ari uku* wai a baiwa iyalan marigayi,kuma sunyita tambaya daga gun waye aiken yazo amma sam basu samu amsaba. Kamar yadda mahaifin manosh ya fad'a da safe yaje shida mahaifin marwan da kuma drivernsu,inda suka samu mahaifin maryam a gida dan baije ko inaba tunda yasan da zuwansu. Shiya musu jagora har cikingidansu yah ibharim suka gaida da iyalinsa sannan suka bada hakuri tare da musu gaisuwan rashin. Suka amsa tare da cewa cewa ai kwananshine ya k'are dan haka bakomai sun yafe wlh,godiya sosai mahaifin manosh yayi tare da musu alkhairai sosai sannan kuka fito tare da yah ibrahim yana rakasau da baban maryam. Bayan fitowansune mahaifin manosh yake tambayan ibrahim akan aikin da yakeyi,nan ibrahim ya gaya masa cewa bai dad'e da gaba NYSC nashiba yana jirane tukunna,nan mahaifin manosh ya bashi *card*nashi yace ya same ran monday.godiya sosai ibrahim yayi dan yasan kawai aiki za'a bashi. Lokaci yanata tafiya angwaye se himma suke bayarwa wajen aikin ginin gidajensu da zasu tare da amarensu. Manosh kusan kullum seyaje girei tun bayan dawowarshi,ranan suna hira yake tambayar apple wani irin gida take so,dadai tak'i gaya mishi,amma da taga zai b'ata rai tace ita dai ranta nason gidan sama,sannan ya kasance *milk da d'an army green*. Murmushi manosh yayi yace shikenan nagode. Itama murmushin tayi tace amma pls karka takura kanka danni kai nake so ba gidaba dan haka kakyi komai d'an daidai pls,dad'i sosai yaji yace shikenan apple zanyi d'an daidai *mata 4* dariya sosai tayi tace bakomai tunda dai nice *uwar gida* Soyayyarsu abun burgewa wlh domin mai tsafta ce. Maryam ce zata kaiwa babanta abincin a shop nashi tana cikin tfy se wata bak'ar mota ta tsaya,da sauri suka fito maryam bata zata gurinta zasu nufoba kaiwai suka big'e abincin hannunta ya zube a k'asa,kan tace wani abu sunsa mata hanki a hanshi mai d'auke da magani take ta mance inda take sukayi saurin jefata cikin mota suka fizgi motar a guje. Adaidai wannan lokacin iyayen maryam sukaji gabansu ya fad'i atare suka hau fad'i *Hasbunallahu wani'imal wakim* suketa nanatawa... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 billylosh*❤)* 37-38 hankalin manosh a taahe ya kalli d'aya daga cikin sojojin yace ina tausayawa duk wanda yayiwa maryam haka wlh. Miher ce zaune ita da mum nata a palo suna jimamin abinda ya fari da maryam se wayanta ya fara k'ara da sauri ta d'aga tare da cewa hello lubna,lubna tace miher ya gida naji bro marwan yana cewa anyi kidnaping maryam d'in da bro manosh zai aura? Miher tace wlh kuwa lubna,lubna tace subbahanalillah yanzu su waye sukayi wannan aikin,miher tace wlh har yanzu dai shuru tukunna amma ansan inda maryam d'in take yanzu haka,lubna tace haba alhamdulillah a ina aka sameta,miher tace bawai an sametabane fa,andai gano inda take a *numan ne*. Lubna tace har numan aka kaita kai Allah ya tona asirinsu zanzo gobe insh Allah,to sekinzo nagode. Koda lubna ta ajiye wayan miher se ta kira wani tace hello *saddam* ya akayi har su bro suka gane cewa maryam tana numan,aikinka baiyiba saddam domin yanzu haka su captain suna numan dan haka kuyi gaggawan d'agata daga numan ku k'ara gaba da ita zan tiro maka da kud'i yanzu a account naka saddam idan asirinmu ya toni zansha wuya agun bro marwan wlh seya kusan kasheni pls indai da gaske kana sona tokayi wani abu plss saddam. Murmushi yace karki b'ata bakinki bbynah, yanzu zamubar adamawan ma kwatakwata karki damu sweetheart zan nuna miki cewa da gaske nake k'aunarki bari na nemo wani abokina,lubna taji sanyi a ranta tace nagode sena jika. Maryam kuwa dama ta kashe wayan gabad'aya tasa a cikin pant nata. Yadda aka ajiye mata abincin haka sukazo suka samu,yace wato bakici abincin bako,bai jira jin abinda zata ceba ya toshe mata baki da hanci da wani hankachif fari take ta mance inda take seya d'auketa cak se mota suka kama hanya,cikin ikon Allah kuwa ba'a tsaidasuba har suka bar numan. Tfy sukeyi hankalinsu a kwance suna dariyan mugunta yana cewa *captain manosh* zanga iya kwarewarka kafin in shiga hannunka kuwa sena gama lalata budurwan naka tukunna dan nasan idan na shiga hannunka tofa tawa ta k'are shiyasa nima zanyi abinda nakeso tunda dama banida iyaye se kawai in bisu bayan na shana hhhhhhh... Manosh se kiran line na maryam yakeyi amma shuru, seyayi tunanin kodai tana tare da mutanenne shiyasa bata bud'e wayanba. Nan dai yace bari yad'an k'ara jira. Anan ne muhsin ya kirashi yace "dude" na raba hotunanta kota ina yanzu haka ma ana haskawa a gidan *TV GOTEL* , *NTA* da kuma *ATV* duk anta haska hotunanta,manosh yace nagode abokina pls kuyita tayamu da addu'a sannan kuyita bada sadaka Allah ya bamu sa'an gano inda take,muhsin yace ka kwantar da hankalinka abokina insha Allah zamuga maryam cikin k'oshin lfy dan maryam tana da halayya masu kyau. Iyaye maryam kuwa hankalinsu yad'an dawo jikinsu da sukaji lfyarta k'adau amma dai har'a yanzu suna cikin tashin hankali sosai. Duk girei seda akaji zance sace maryam auntyn yara,dan haka aketa addu'oi babba da yaro kai harta almajirai idan sukaji lbrn tofa suna komawa gun malaminsu suka gaya mishi,yace musu kwarai yaji a radio dan haka kota ina addu'oi maryam take samu. Hajiya iya kuwa tafi kowa tashin hankali ana zaton,ko menene dalili oho? Kuka takeyi safe da dare tare da addu'an Allah ya baiyana maryam. K'awayen maryam sun zama abin tausayi musamman rashida data tina kalmomin data dinga gayawa maryam ranan,dan haka ta dinga kuka tare da kewar aminiyarta. Hakama abdallah ya shiga wani hali sosai dan ganin maryam yakeyi kamar yarsa da cike ciki d'aya,yah ibrahim nema yake lallashinsa dan kowa yasan irin k'aunar da take tsakaninsu hakama ita maryam d'in tana ji da abdallah fiye da,sauran yaran. Manosh baiga kiran maryam ba har 12:00pm dan haka yasan cewa akwai matsala,kuma shi yasan babu wadda ya gayawa cewa maryam tana numan daga iyayenshi se iyayen maryam se kuma friends nashi,dan haka abin ya dameshi sosai gashi faruq yace mishi wayan maryam a kashe yake bazai iya gane inda takeba dole se wayanta yana kunne. Da misalin 2 na dare suka isa wani jeji tare dabi cikin jejin daba kowa se wani d'an k'aramin gini daba'a k'arasashiba nan suka tsaya suka fitar da 'yan kayayyakin da suka taho dashi suka dai kimtsa gurin se suka kwantar da ita akan bargo sannan suka zauna a gefe. Saddam ya kira lubna yace hello bbynah mun iso lfy,tace sannu da hanya a inakuke yanzu? Yace muna jihar bauchi cikin gefe da *jejin yankari* ido lubna ta zaro tace har bauchi,yace yes bazasu tab'a tunanin zamuzo bauchiba,dad'i taji har cikin ranta tace nagode bbynah aikinka ya gyaru,murmushi yayimata yana busa sigarinshi yace bbynah gaskya bazan kyale yarinyarnanba dolene sena tab'ata fa,hankalin lubna ya tashi tace no bbynah kafa cemin ni kad'ai ce yarinyar da kake so taya za'ayi kashe min haka kuma,wato dama kana cin amanata kenan ko? Saddam yace wlh ba haka bane bby shikenan wlh bazan mata komaiba amma kinsan ked'in kince dole semunyi aure kafin muyi wani harka kuma gaskya ni a matse nake wlh,lubna ta murgud'a baki tace karka damu idan mun gama wannan aikin zakasha mamaki da irin gift d'in dazan baka wlh bbynah,nan saddam yaji dad'i yace okey my luv shikenan sekin jini,tace ok but pls karka mata komai indai har kana sona,yace wlh bazan mata komaiba karki damu bbynah. Maryam bata farkaba har asuba,ta jita ak'asa nan ta tashi da sauri tana addu'oi tare da k'arewa gurin kallo setaji hawaye a fiskan,kukan tane ya tashi mutum guda d'aya da yake kwance daga gefe dan sauran kam duk sun shiga gari neman abinci. A gigin baccin yazo inda take yace ke 'yanmata yane? Kallonshi takeyi tare da cewa bawan Allah inane nan kuma? Yace nan jihar bauchine ta gefen jejin yankari. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* maryam taketa fad'i sannan tace karfe nawane yanzu? Ya duba wayanshi yace 5:30am,tace ina zan samu ruwa nayi sallah,nan ya d'auko pure water ya mik'a mata tare da ciro bindiga a aljihunsa yace kinga wannan,wlh idan kikayi wani kuskure sena pasa kanki dashi,jikinta na rawa tace to alwala kawai zanyi inyi sallah. Komawa yayi ya kwanta ita kuwa jiki na rawa ta koma gefe tana alwala. Bayan nan ta koma cikin ginin tare da lekashi taga dai bacci na damunshi sosai,dan haka ta ciro wayanta ta kunna tare da da turawa manosh texs sannan ta kashe wayar tahau yin sallah. Manosh daya kasayin bacci yana zaune a mota a numan seyaji texs ya shigo wayanshi,da sauri ya duba _hello peach,sun d'aukeni daga numan zuwa jejin gefen yankari dake jihar bauchi gurin babu kyan gani a tsakiyar jeji muke cikin wani kango da babu ko rufi asaman pls peach do something ka kulamin da iyayena plss da kuma abdallah nah byeee_..... Manosh ji yayi kamar zaiyi hauka dan yadda yakejin k'irjinji yana tafasa. Kwana d'aya kawai amma dukya fita hayyacinsa haka ya juya ya koma girei ya dad'a baiwa iyayen maryam hak'uri tare da kwantar musu da hankali,sannan yasa aka kira mishi abdallah yace kayi hakuri abdallah maryam tana cikin jarabawane amma komai zai wuce ina tabbatar maka da cewa auntynka zata dawo insha Allah kuma dukda halin da take ciki sam bata mance da kaiba tace ingaisheka abdallah. Rungume manosh abdallah yayi yana zubda kwalla shima manosh daurewa kawai yayi sannan ya kalli yah ibrahim yace ka kula dashi dan sak'on maryam kenan akanshi. Manosh ya shige mota ya wucegida a galabaice,toilet ya shige ya watsa ruwa sannan ya fito yasa jaket maroon da black yana k'ok'arin fitowa sega mum nashi da miher,nan ya koma lallausar gadonshi *milk colour* yad'an jingina yana kallonsu. Kuka miher ta farayi tare da ciro wayanta ta d'aukeshi hoto taje har kusa dashi tace kalli yadda ka zama fa bro, kwallan idonshi ya share tare da kamo hannun miher yace karki damu zan koma normal ne bayan na samo apple d'ina. Mum tanata kallonsu tare da tausayawa d'an nata tace Allah ya baka sa'a *son*, yace ameen mom nina tafi sena dawo,har waje miher ta bishi tanata kuka harya tafi.... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated to Hasiya Ahmad & Maryam Adamu Girei* (TAHIRA)💐🌹🌺 39-40 Bayan maryam ta idar da sallah ne taketa hamman yunwa,dan tunda ta baro gida bata sake cin abinciba se ruwa data sha,gata da *ulcer*. Lek'owa tayi taga har yanzu bacci yakeyi,dan haka taje inda yake tanata crwa 'bawan Allah×2' ahankali ya bud'e ido tare da tasowa ya zauna! Kallon juna suka tsayayi domin sun tabbata akwai inda suka tab'a had'u dukkansu d'in. Can maryam ta tuna shine mutumin da mota ta tab'a bigeshi a hanya harta taimaka mishi yahau mashine aka kaishi hospital tabbas shine wannan. Wani sanyi taji a ranta tare dayin mirmushi tace bawan Allah dama kaine ka rabani da iyayena? Shuru yayi yana kallonta cikin mamaki yace dama kece yarinyar da aka d'auke? Kallonshi ta tsaya yi tana mamaki tare da cewa aka d'auke ko kuka d'auke bawan Allah. Bayansa yaketa waigawa sannan ya mik'e tsaye cikin hanzari yace banina d'aukekiba abokin aikinane,maganar gaskya nidai ba mutumin kirki bane wannan ranan da muka had'u dakema sata naje nayi aketa bina tare da fasamin jiki,dak'ar nasamu na gudu shine na b'ullo ta girei har muka had'u dake kuma na miki k'arya kika tausaya min tare da taimakona. Maryam tayi shuru tana sauraranshi tace to bawan Allah dan Allah ka gayamin abu guda d'aya wanene yasa a kamoni? Shiru yayi yace bazan gaya mikiba sedai in taimakeki in baki wayana ki kira duk wanda kike buk'ata indar har kinaga za'a iya taimaka miki,shuru maryam tayi tace to ai nabar wayata a gida ban kuma san numbern kowaba sena iyayena da k'awayena. Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toki gayamin numbern iyayenki,nan ta gaya mishi numbern babanta yasa ya kirashi,bugu d'aya ya d'auka lokacin suna tare da dad d'in manosh yaje yi musu jaje. Maryam tace baba nice yanzu haka ina jihar bauchi cikin jejin dake gefen yankari,baba yace to wannan numberfa? Tace baba karka damu lfyata lau babu abinda ya sameni sedai ina jin yunwa sosai har k'irjina ya fara min ciwo,subhanallah maryam haka suka barki da yunwa dan basu da imani tun jiya? Baba sunban abinci amma bazan iya cibane ka gaida mama kuma dan Allah karka kira numbern nan domin na d'aya daga cikinsune ya taimakamin idan ka kira suka gane zasu kasheshi. Hankalin mahaifinta a tashe yace shikenan maryam na fahimceki amma dan Allah ki daure kici abinda suka baki kodan lfyarki,to baba ya mama take,lfy lau karki damu damu maryam ki kula da kanki,insha Allah zaki dawo garemu da izinin Allah,Allah ya amshi addu'ar mahaifina na gode....bata k'arasa maganarba ta katse saboda kuka daya ci karfinta. Mahaifin maryam hankalinsa a tashe ya kira manosh ya gaya mishi komai,manosh yace karka damu baba insha Allah zata dawo kudai tayamu da addu'a. Shi kuwa bawan Allah kallon maryam yakeyi tare dajin tausayinta ya bud'e ledanshi ya d'auko *maltina da biskits*

Chapter 6 of 17