Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mishi haka tofa bazai yafeba,sannan dole se hukima ta shiga shicin zance wanda hakan zai iya janyo wata babban rigima tsakanin familys harma yakai gidan yari. Amma alhamdulillah yazo gidan sauki tunda duk gashi Allah ya had'a zuri'a a tsakaninmu" bazamu iya cewa komaiba se Allah ya kare nagaba,sannan nagode da kulamin da yarinyata da kukayi,nagane manufar hajiya iya da kuma dalilinta. Sedai ba haka ya kama a bullowa lamarinba,ita a tunaninta lokacin ina fama da talauci ta yadda bazan iya rik'e koda yarinya d'ayaba,se kuma gashi Allah yabani kyauta biyu a lokaci guda,tofa musani Allah baya d'aurawa bawa abinda bazai iyaba,tunda shiyabani su toshizai bani hanyar da zan renosu,alokacin bani dashi,yanzu kuma ina iya rike mutanen daba jininabama,kamar yadda kuka rikemin lubna. Bakomai hajiya Allah ya yafemu gabad'aya. Har k'asa hajiya iya ta sauko tana kuka tare dayin godiya,hakama mahaifiyar maryam tace tayafe bakomai. Nanne dad d'in manosh yayi magana kansan a sunkuye dan kunya,yace mungode sosai alhaji Allah yabar zumunci,wani lokacin mata basu da tunani,duk abinda zuciyarsu ta rayamusu shi kawai sukebi tabare dasunyi shawara da kwakwalwarsuba,aduk lokacin da zuciya ya raya maka abu maikyau ko mara kyau tofa ana so mutum yayi shawara da kwakwalwarsa domin zuciya zata kaika ta baroka,yanzu kai dakayi hakuri wlh inda wanine bazai hakura,kuma kaduba abinda lubna tayiwa maryam,da maryam ta fad'a awannan lokacin toda abu ya lalace tun daga wannan lokacin se daga baya kuma za'aji kunya,kuma dukkune sanadin faruwar hakan. Hajiya da girmanki amma ki aikata irin wannan abu haka babu dad'inji,sannan kuka b'oyemin akan tsintota akayi wannan wani irin tunanine haka? da wani akayiwa hakan da sunanmu ya gama b'aci,yanzu haka kunyan had'a ido dasu nakeyi wlh mungode sosai Alhaji zamu tafi,yana kaiwa nan ya fito suka biyoshi a baya,bai k'arasa gun motaba ya yanke jiki zai fad'i da sauri su majid suka tallafoshi aka sashi cikin mota ida muhammad yaketa faman dubashi yace ai jininsane yahau sosai. Subhanallah ake ambato agun,da sauri suka shige se jimeta inda akayi hospital dashi. Dad d'in marwan baida hawan jini sam,amma yau gashi dr yace hawan jinine ya kamashi sosai. 'Ya'yan nashi sunyi iyakan k'ok'arinsu agun dan kula da mahaifin abokinsu. "Shi kuwa mahaifin manosh,yana cikin damuwa wanda har yake jin ciwon kai mai zafi,amma haka ya daure yana nan akan abokinsa. "Su maryam kuwa fitowa sukayi daga d'aki sukazo gun hajiya iya kamar yadda babansu ya umarcesu. Dan tun lokacin dataji abinda ya sami d'an nata shikenan aka rasa gane kanta. Hakuri aketa bata,itama hajiya khadijan sam ta kasa sakewa,hakan yasa tace zata komar da hajiya iya gidansu can na jimeta tunda akwai masu girki,ita zata tafi asibiti gun mijinta. Haka aka rakosu har waje suka tafi. Maryam sebin motar nasu da kallo takeyi har sukayi nisa sannan lubna ta kamo hannunta tace aunty kidenasa damuwa aranki pls komai ya wuce kamata yayi ace kina murnan samun k'anwa. Jiki sanyaye ta juyo suna kallon junansu tace lubna,bakya jin komai gameda abunda ya sami daddynkine? Lubna tace daddyn bro marwan dai. Maryam ta dafa kafad'arta tace lubna har gobe har jibi shima daddynkine sannan inaso ki nuna damuwarki sosai akanshi kamar yadda kike nunawa akaina inhar kinasona da gaske. Jikin lubna yayi sanyi ta wuce gida tasa himar nata har k'asa tace mama baba zanje duba daddy,babu wanda ya hanata,seda tazo dabda maryam tace zanjene saboda ke saboda kuma shi daddy bayi da laifi sansan zanjene dan bro marwan bayanan,nasan koba komai zan d'ebemasa kewa. "Maryam tanata bin lubna da kallo harta dena kallonta zata shiga gida kenan setaji ana kiran sallan la'asar,koda ta juyo dan ganin mai kiran sallan seta wannan tsohonne dai wanda ta taimakawa a farkon littafin... "Marwan ahankali yake tfy harya isa gun abokinshi yace kaini masaukina. Bamusu ya kaishi batare dayace mishi komaiba,saboda yadda yaga marwan yasan bazai samu kowace amsa daga bakinshiba. "Bayan ya saukeshine marwan ya fita yace nagode,abokinsa yace yaushe zanzo to?" Dan numberka kona kira bana samu. Marwan yace zan kiraka sannan ya shige. Rashida tanata safa da marwa setaji nocking,da sauri taje ta bud'e kofa taga marwan atsaye kansa a sunkuye dukya galabaita yayi wani iri kamar maiyin azumi. Hakan ya tabbatar mata da cewa baici komaima,kallonta yakeyi cikin tausayi ga kwalla dasuke yawo a idanunsa. Tausayinshi ya kamata,ta rungumeshi sam ajikinta tana kuka tana cewa waime yake faruwane luv,dan Allah ka sanar dani bana son yadda nake ganinka ahakannan pls luv, baice da ita komaiba se kwallan da yake zubarwa,ahankali ta cire masa kayan jikinsa itama haa ta jashi zuwa toilet inda ya zama kamar jariri haka ta wankeshi tas sanan itama ta wanke jikinta ya d'auki towel itama haka suka fito a tare,yasa kaya tasake janshi wuza gun cin abinci amma sam yakici da k'yar tasashi yaci kadan sannan ya koma gado ya kwanta. Bayan ta gama komaine tazo inda yake tana tsunbatan sassan jijinsa a hankali tana kallonshi har cikin ido. Shi kuwa sam hankalinsa baya jikinsa,lips nashi ta far kissing ahankali cikin nutsuwa,shi kuwa idanunsa arufe yana jin yadda take mishi,kamar a mafarki yaji muryan manosh yana cewa marwannnnn Azabure,ya mik'e rash tace lfy luv,yace my luv manosh naji yakirani wlh ahine. Rash ta mik'e tace manosh fa kace,to a ina yake? Allah yasa dagaskene luv dabanda zaikai aunty farinciki maza muje muduba,bamusu yanufi k'ofa ita kuwa tasa himar ta fito,se juye juye sukeyi suna duba kofofin d'akinan ko zasuga fitowarsa koma suji muryanshi. Can yasakejin marwannn,ai kuwa yana juyawa seyaga manosh yana k'ok'arin fitowa daga wani d'aki amma sam j'afarshi baya motsi kaman an manda da superglue. Da gudu suka k'arasa gun,amma ina take kofan ta kulle kanta. Bugawa marwan yakeyi kamar zai b'alla kofan amma ina,sunan manosh yaketa kira yanacewa prince gani ka bud'e kofan pls kaida waye? Shuru babu amsa,seyaga k'ofa ta bud'u da kanta,dasuka shiga shiga amma babu alaman mutane acikin d'akin. Marwan yace ina bazai yuba wannan duk sharrin shukrah ce,duk yadda akayi suna nan,lallai bazan bar nanba senagano captain,nan suka zauna sunata addu'oi,ita kuwa rash tsone ya kamata sosai dan tabbas itama taga manosh da idanunta... " aunty kuwa koda tsohonnan ya idar da kiran sallah,gunshi ta k'arasa tace baba,murmushi yayi mata yace inatayaki murnan samun 'yar'uwarki. Murmushi tayi mai had'e da tsoro tace nagode,nakuma tuna da abinda ka gayamin a yanzunnan. Yace masha Allah maryam zan tafi,tace baba dan Allah mijinafa,kokasan inda shukrah takai min shi? Dan Allah baba kataima. Baba yace wacece shukrah? Jikin maryam yayi sanyi tace baba aljanace ita,ta rabani da mijina tsawon kusan wata hud'u kenan ba'asan inda yakeba. Baba yace ta ita maryam bansan komaiba akan wannan kimana tausayamiki sosai,Allah ya bayyana miki shi,kuci gaba da addu'a maryam babu wani abu dazai gagara,sannan kisa a ranki cewa Allah zai dawo miki da mijinki,karki dogara da wani kinji? Jikinta sanyaye tace to baba nagode tare da kwalla a idanunta. Ahankali tabar gun masallacin tayi hanyar komawa gida saboda mutane sun fara zuwa sallah,kan ta karasa kofar gida ta juya amsam bataga baba ba,kuma babu alamarsa tagurin. Mamaki,sosai tayi tayi da gudu ta shiga gida tana kuka ,hankalin iyayenta a tashe suke tambayanta ko lfy,tace gamo tayi da aljani. Iyayen suka tsaya kallon junansu,mahaifinta yace maryam wani irin gamo? Nan maryam ta basu lbr tun daga farkon had'uwansu da baba stohonnan har kuma taimakon daya mata a jejin yankari lokacin da saddam ya harbeta da bindiga a hannu da kuma abinda tsohon ya gaya mata akan lubna. Mamaki sosai iyayen sukayi,babanta yace maryam anya kuwa lfyanki lau? Tace wlh baba lfyta lau yanzuma shinagani shine wanda kukaji muryanshi ya kira sallah. Baba yace ajani ya kira sallah kuma maryam? Tace eh wlh baba nasan bazaku yaddaba amma wlh shida kanshi yagayamin shiba mutum bane aljanine. Baba yace to Allah ya karemu dadukkan 'yan'uwa musulmai,suka amsa da ameen sannan ya fita zuwa masallaci yanata kalle kalle tare da tambayan jama'a ina wanda ya kira sallah yanzu? Wanine yace tun d'azu yabi tacan,baba yace shibazai tsaya yayi sallan bane? Yaro yace oho mishi tsohone kodai zaije ya dawone oho mishi. Haka dai su baba suka idar da sallah amma wannan wannan tsohon bai dawoba,baba kuwa ya jinkirta yanata karatun qur'an a masallaci harya isar amma baiga kowaba haka ya wuce gida. Lokacin suna cin abincine se maryam tace baba har yanzu lubna shuru kodai sun wuce gidane itada yah ibrahim,mama tace kirasu kiji,bamusu ta d'auki wayarta ta kira lubna,cikin nuryan kuka lubna ta d'auka tace aunty zan dawo anjuma kad'an,maryam tace ya jikinnashi? Lubna tace da sauki yana bacci,maryam tace yanaji muryanki kina kuka lubna? Lubna ta share kwalla tace aunty daddy ya saki mummy. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *To you readers! They say LIFE is a mirror: if you frown at it, it frowns back: if you smile, it returns the greeting*. *Is that true?*😄 87-88 Sakifa kikace lubna,tace eh sannan ta katse wayar. "Maryam ta kalli iyayenta tace baba wai daddyn marwan ya saki hajiya khadija" duk basuji dad'in lamarinba,amma babu abinda zasu iyayi akai haka suka gama cin abinci suka wuce dan k'arasa shirye shiryensu. Kusan 10:00pm yah ibrahim ya kawo lubna gida,idan suka dad'e suna magana da baba kafin ya tafi. Ranan dai basuyi wani baccin kirkiba dan gobe zasuyi tfy. Maryam kuwa tama rasa meke mata d'ad'i. "Washe gari da safe mahaifin maryam ya sanar da tfyan da zasuyi a masallaci don yiwa maryam aiki,sannan kuma yasake rokon jama'a ayita addu'a wa surukinsa wato manosh Allah ya bayyanashi. Addu'a sosai aka musu awannan lokacinma. Da misalin suka gaida abuja,suna suna zaune 9:10am yah ibrahim yazo ya kwashesu a mota inda suka wuce hospital mahaifin marwan sannan suka wuce airpot. 10:20am jirginsu ya tashi sauka dama komai ya zama ready yah ibrahim ya gama komai suka wuce zaman jiran tfya india. Marwan kuwa suyita addu'a har rashida ta fara bacci,shine ya d'agata yakaita d'aki ya kwantar da ita sannan ya koma yayita zama harya gaji sannan ya dawo shima hakadai suka wayi gari. "Bayan sunyi breafast ne marwan ya sake komawa d'akin amma bakoai aciki" mamaki sosai yakeyi abu kamar a drama?" Rash ce ta biyoshi hakadai suka sake dawowa d'akinsu inda take ce mishi itata sayi waya kuma tayita kiran numbern 'yan gida baya shiga dan haka ya bata numbern su majid,sam marwan yak'i yama karb'e wayan. Nan rash tayi fushi tace waime kake nufine kakawoni nan ka ajiyeni babu wani bayani jiya haka ka fita ka barni bakaika dawoba seda lokaci ya kure waima ina kajene marwan? Cikin mamaki yake kallonta yau sunanshi ta kira kai tsaye. Yace luv yau nine kuma marwan? Sannan zargina kike kome dakike min wannan tambayoyin? Tace eh zarginka nakeyi saboda abirkice ka dawo jiya kamar wani bugagge idan ka gaji da zama danine nikam kamaidani gidanmu gabad'aya kacanja kadena bani hakkina idan ka sau matan banza awaje toka sallameni intafi gidanmu nan ta fashe da kuka. Shi kuwa marwan maganganun nata sun mishi zafi sosai gashi dama yana da damuwa,baice da ita komai yafita yabar mata d'akin tanata kuka. Shukrah waike wani irin muguwace haka? Hahahha lallai kam manosh ka samu baki,wlh indai bazan samekaba tofa sedai in hallakaka itama maryam d'in ta rasaka tunda kai taurinkai kakeji dashi,danka samu na sake maka bakinka ko,tokamin bankwana manosh semun had'u a kiyama.............. Ihu mai k'arfi manosh yasa,awannan lokacin kuwa su yah ibrahim zasu tafi dama wayoyinsu akashe yake. Juyowa yayi yana kallon aunty se faman kuka takeyi tana tsaye,gunta yazo shida lubna sukace lfy aunty muje mana? Kuka ta fashe dashi tace sam bazatajeba ta fasa,mutanen gun suka tsaya suna kallonsu,da k'yar mahaifinta yashawo kanta ta yarda se waige waige takeyi har suka wuce tana kwalla. Yah ibrahim ma kwallan yakeyi dan yana mugun tausayawa aunty sosai. Haka suka wuce cikin jirgi tana tsakiyan mamanta da kuma lubna jirgi ya tashi.. Rash kuwa tayi kuka harta gode Allah can sekashi ya dawo tanata had'a kayanta ciki kit. Kallonta yakeyi tare da tambayar ina zakije? Ko kulashi batayiba ta gama komai tazo wucewa seya kamo hannunta ya matseta a jikinshi yana cewa haba luv meyake damunkine,meyasa bazakin uzuribane yanzu har zaki iya tfya kibarni? Tace shiyafi komai sauk'i wlh. Yace luv bakigane bane ina cikin damuwa dan Allah kimin uzuri pls my luv,rungumeta yayi tsam yace inada bukatarki atare dani kece zaki kwantar min da hankali amma kuma shine kike gayamin maganganu kike k'ok'arin tfya kibarni? Pls luv kiyi hakuri i luv you so much. Hawayene kebin idanunta inda tace i luv you too bazan tab'a barinkaba kaine kab'ata min rai ai. Yace kiyi hakuri pls kinji,tace yawuce tana murmushi inda suke kallon junansu daga nan ta fara kissing nashi shima haka har suka sulale akan gado hmmmm. Manosh ne kwance a k'asa baya cikin hayyacinsa se muryan wani mutum da yakeji yana cewa manosh bud'e idanunka ka kalli jirginsu matarka ya tashi,amma ina manosh bazai iyayin komaiba a wannan lokacin. Mutumin yace manosh gacan aunty cikin jirgi daure ka mata fatan Allah ya kiyaye hanya. Shuru kakeji kamar gawa, ni kuwa *sad-naa* kallonsu nake kamar a tv babu halinna in gane inda suke,haka dai nayita cija baki ina zubda kwalla tare da kallon jirginsu aunty harna dena hangoshi. Ganin hakan yasa mutumin ya d'auki manosh kamar an d'auke wuta haka na dena kallonsu,sena koma hilton gunsu marwan inda suke manne da junansu a cikin bargo,gadukkan alamu dai marwan yana biyan bashin kwanakin da suka wuce ne hahahaha! "Mutuminnan bai tsaya ko inaba se gidan manosh,dahar zai shige sekuma ya tuna da cewa ai babu kowa a cikin gidan inbada mai gadi. Hakan yasa ya baina a daidai bakin gate rik'e da manosh a hannusa kamar dai yadda ake rik'e jarirai. Mai gadi yaji ana buga gate,kuma sam mutumin baikaima hannunsa kusa da gate ba. Da sauri yazo yana cewa wayene gidan babu kowa seni kadai mekuma kuke sone...? Mai gidansa yagani wato captain manosh a hannu wani tsohon mutum,Alhamdulillah maigadi ya furta yana kwallan farinciki tare da cewa Allah majirok'o bayinsa alhamdulillah.... [6:44pm, 4/2/2017] Hamagee: [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas 😄 *this page is for you kanuna guys*👞👟👞 *You know what? i can stop laughing*😄🌺 89-90 maigadi yakasa rufe baki,ya kuma rasa mezaiyi a wannan lokacin. "Tsohon yace bamu taburma mana, bamusu maigadi yaje ya d'auko carpet nashi mai kyau wanda aka kawo mishi tsaranban makka ya shinfid'a cikin rawan jiki yace bisimillah. Tsoho ya zauna tare da kwantar da manosh yace ahanya na sameshi kwance babu yadda yake,bayan na d'aukosane nake tambayarsa inda yake waye mahaifinsa shine dai ban samu amsaba,kawai senaga hotonsa a gurare da dama an manna,shine na tambayi jama'a suka kwatantamin gidansa tare da nuna farin cikinsu. "Mai gadi Allahu Akbar" "Tsohon yace nidai zan tafi dan akan hanya nake nabar iyalita tana jirana can" Maigadi yace dan Allah kad'an jira barina sanar da iyayensa,amma sam tsohon yaqi yace shidan Allah yayi badan asan yayiba dan haka ya tafi amma inaso ka gayawa matarsa ina tayata murna,kace mata inji baba. Koda tsoho ya fito lokacin maigadi yana kiran numbern aunty amma sam baya shiga. Hakan yasa ya kira numbern dad d'in manosh bugu d'aya kuwa ya d'auka tare da cewa kana lfy,maigadi yace lfy lau alhaji se alkahiri yauga oga yanzunnan wani mutum ya kawoshi a stintarshi yayi kwance a k'asa,gashinan...dad d'in manosh ya katseshi da cewa kana nufin d'an manosh? Maigadi yace shidai alhaji gashinan amma baya halin lfy. Subhanallah ganinan..... Dad yana ajiye waya yayita Hamdala yana godiya wa ALLAH tare da d'aga hannayensa sama da sauri ya kira malam da kuma aminansa da duk dai nakusa dashi. Kowa yaji lbr se godiyawa Allah. "Mahaifin majid ne ya kira majid suna hospital akan dad d'in marwan" koda suka sami lbrn murna da farin ciki baya misaltuwa. Shikansa dad d'in marwan dukda dai jikin nashi yayi tsanani amma sedayayi murmushi tare dayi godiya wa Allah ya kalli abokan d'an nasa dukyaga suna burin ganin aminunsa daga idanunsu ya gane hakan. Anitse ya tashi ya zauna yace karku damu muhsin kuje kuga abokinku aina samu lfy ku isarmin da gaisuwata agareshi kafin nazo. Bamusu suka fati cikin d'oki inda yake ta binsu da kallo Manosh kwance maigadi yayita yayyafa mishi ruwa amma sam ko motsawa baiyiba daidai nan motoci suketa hon abakin gates yayi saurin bud'ewa suka shihshigo. "Daga dad d'in manosh har abokansa bansan suwaye suke mararin ganinsaba harda gudunsu suka k'arasa gun. Majid ne ya karb'i key yabud'e gidan muhsin da muhammad kuwa suka d'auki manosh se cikin palo inda duk gurin yayi k'ura. Akan kujera suka kwantar dashi kamar gawa baya ko motsi. Kowa ya tsaya kallo manosh inda kowa yake zance zuci akan yadda suka ganshi. Muhammad ya gwadashi ya tabbatar da cewa yana da rai,hakan yasa akayita masa addu'oi ana tofawa a ruwa ana yayyafa mishi,shi kuwa malamin man habbatus sauda dadai sauran had'in su man juda yaketa shafa mishi ajiki. "Aikuwa segashi ya fara motsawa ahankali amma idanunsa a rufe yake motsawa da dukkan jikinsa" Murmushi abokansa suka farayi tare dacigaba da addu'an" Mahaifinsama addu'a yaketa mishi, shi kuwa malami mai ruk'yya se karatu yakeyi. "Ahankali manosh ya fara bud'e idanunsa yana rufesu hardai ya bud'e garau inda yakebin kowa dake palon da kallo d'aya bayan d'ayan harya gama sannan yace ruwa zansa. Malam ya bashi ruwan addu'an muhammad ya tallafosa aka bashi ruwan ya shanye tas yace ak'ara mishi,hakan yasa aka gane lallai ya dawo hayyacinsa saboda manosh yana son shan ruwa sosai kobayajin k'ishi. Bayan an k'ara mishine yace zaisha fruit,hakan yasa akan yana jin yunwa. Cikin mintuna goma mahjid yafita nemo fruit ya dawo ya wuce kichine ya d'auki plate da wuk'a yadai yanka yadda zai iya sannan ya dawo ajiye agaban manosh inda yaketa binsu da kallo kamar bai sansuba. "Majid yace ga fruit d'in" "Ido manosh yasa akan fruit d'in" bayan wasu dak'ik'ai seya girgiza kai alamun bazai shaba. Muhsin yace kasha mana abokina nasanka da son fruit fa. Manosh ya girgiza kai yace ba irin wannan nake shaba. Majid yace kamar yah? Wanne kake sha to? Kafin manosh yayi magana muh'd ya tuna da irin fruit da aunty take mishi seyace kana nufin irin wanda aunty take maka? Da sauri ya d'aga kai yana kallon muh'd cikin alamun tambaya? Muh'd yace eh na aunty kake so koh mai irin fiskarka?? Ihu mai karfi manosh yasa wanda dukkansu seda suka tsorata harda malamin. Manosh yacigaba da ihu yana cewa nooooh! Dad shukrah ce wlh tacuceni tagama dani dad ya rik'o dad nashi da k'arfi yana kuka. Dad yace son saurara mune anan babu shukrah ka saurareni kaji? Ahankali ya nutsu yace "dudes?" Nanne abokansa suja san cewa yana cikin hayyacinsa sunda ya kirasu da wannan sunan *dude*" murmushi sukayi tare da rungumeshi sukace Alhamdulillah Allah mun gode maka _we are so happy to see "dude_" "Murmushin k'arfin hali yayi yace _thankyou_, sannan ya kalli dad nashi yace dad mum fa? Yace suna hanya itada driver dasu abdallah,murmushi manosh yayi yace ina dad d'in marwan? Tare da juyowa da sauri ya sake kallon su majid yace ina marwan? Shuru sukayi dan suma tunda ya tafi suketa nemansa basusan inda yajeba tunda numbernshi baya shiga kuma bai kira kowaba har yanzu. Manosh ya sake maimaita tambayarsa ina marwan? Muhsin yace kaima kasan da yana gari da tare zakaganmu yayi tfya ne. Manosh yace ok dad nashi fa? Dad yace yana asibiti bayida lfy,subhanallah harda asibi dad,meyake damunsa to? Dad yace my son kana da buk'atan hutu dan haka muje gida idanka huta zakaji komai. To yace da dad d'in nashi yana kallon su muhsin da alamun tambayan *ina aunt?*😬 sukuwa dake sun gane abinda yake tambaya,bayaso sukuwa dake sun gane abinda yake tambaya,bayaso dad nashi yajine saboda yana kunyan dad nashi. Se suka ce yawwa gasu mum sun iso,ai abdallah da alfiya suna ganin dad nasu suka ruga aguje suka haye jikinsa ya rungumesu yana sauke ajiyan zuciya kad'an-kad'an. Mum kuwa da umma mahaifiyar yah ibrahim hawayen farin cikine ya lullub'esu sunkasa cewa komai se murmushin farinciki. "Manosh yace mum umma ina yininku,sukace lfy manosh barka Alhamdulillah Allah ya dawo mana dakai,kunyansu yakeji sosai bai iya sake cewa komaiba sesu alfiya dasuketa damunsa da surutu. Mum tace kuzo nan bayida lfy kubarshi idan ya huta sekuyi hiran,abdalla yace yaudai da ddynmu zamu kwana,mum tace tabbas kuwa amma sekun barshi ya huta,da kyar majid ya lallab'esu suka koma gun mum inda malam yace to Alhamdulillah inaga shikenan ai nizan tafi. "Dad da malam ne waje suna tattaunawa inda malam ya bashi magani yace manosh ya dinga shafawa a jikinsa,sannan ya samu hutu kuma a dinga mishi karatu koyayi da kansa. Godiya sosai dad yamishi yabashi abun sadaka amma sam malam yak'i karb'a yayi tafiyarsa. Maigadine yazo da wuri yace alhaji ogan ya tashi? Dad yace eh Alhamdulillah yana halin lfy,maigaji yaji dad'i sosai yace to masha Allah zan iya shigowa? Dad yace eh bisimillah. Tare suka shigo yagaida ogansa,cikin fara'a manosh ya amsa sannan yatafi yana farinciki sosai. Iyayensu majid sukayi addu'oi sosai sannan suka tafi inda dad ya rakasu. Alfiya da abdallah kuwa gurin wasan lilonsu suka wuce se wasa sukeyi. Bayan fitan su dad ne manosh yacewa majid ina miher ne? Majid yace taje suna k'awarta ta haihu,tun d'azu nake neman numbernta dan in sanar da ita amma baya shiga" Manosh zaiyi magana kenan seka dad ya shigo yace toku tashi mutafi gida,ba musu suka tashi tare da tallafawa manosh ya tashi tare da k'arewa gidan kallo ko ina yayi kura sosai. Haka suka tafi inda muhsin ya d'augo abdallah a sama yana cewa wlh nikam agidanmu zan kwana,muhsin yace bakaga gidan yayi k'ura bane aidole se anzo anyi share share. Manosh suna tfya atare hargun mota inda ya shiga motarsu majid yana rik'e da alfiya a ciyarsa yana gyara mata gashi seyace rad'a mata cewa _ina mummynkine dasu babanta_? Alfiya kuwa tabashi amsa da k'arfi ta yadda kowa zaiji tace tayi tfy ai bata gayamaka bane? "Kunya sosai yaji dansu dad sunjisu" "Hakan yasa yayi shuru har seda motansu dad dasu mum yayi gaba sannan nasu manosh d'in inda shida abokansane kawai se kuma su abdalla dansuki binsu mum sunce gurin daddynsu zasuje" Se yanzune manosh ya juya da sauri yacewa muhsin kai wai ina *aunt* ne babu wanda yacemin komai,kunyansu dad ne yahanani tambayarta wlh _where is my wife_ muhammad dake driving yace ba alfiya ta baka amsaba,tayi tfy wlh,majid yace tfya mai nisama kuwa,muhsin yace akallah zatakai 3month kan ta dawo ba. Kallonsu manosh ya tsayayi d'aya bayan d'ayan yace wai meyasa kukemin hakane bawasa nakeyibafa kunsani ina apple d'ina? Abdallah yace daddy apple ta tafi *india* batada lfyne shine suka tafi ita da mama da baba da kuma uncle ibrahim da aunty lubna duk suka tafi.... [7:18am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *_If no one in d enter world cered about you, did you really exist at all?_* _i thankyou so much 4d luv nd care fans_, i *love you all*❤🌺❤)* ❤)* 93-94 Isarsu manosh hospital dad d'in marwan yana bacci. "Amma dole ya farka,dan abdallah sedaya tasheshi yana cewa bappa tashi ga daddyna ya dawo" Da sauri ya farka,inda ya nuna farincikinsa sosai tare da mik'owa manosh hannusa ya janyoshi har zuwa inda yake yana rik'e da hannunsa yace d'ana nayi matuk'ar farincikin ganinka sosai wlh Allah mungode naka. Manosh yace nagode daddy ya jikin,yace da sauki sannan ya tsuguna ya gaida hajiya khadija dake zaune akan carpet. Tunda yafurta cewa yasake amma sam tak'i tfya saboda rashin lfyan dayake cikin kusan babu wanda zai kula dashi shiyasa ta zauna. Itama ta nuna farincikinta sosai da dawowar manosh,haka dai sukaita hira sosai sannan sukai sallama inda manosh yace mishi zai dawo zuwa bayan isha. "Koda suka fita gidan *tv gotel* dake hanyan hayin gada ta hanyar gire suka tafi" Ma'ana gidan tv da radio na *alhaji atiku abubakar* da kowa ya saninshi. Shiga sukayi inda akaso jinta bakin manosh kasancewan ko'ina anji lbrn b'atansa kuma ansan cewa aljanace ta d'aukeshi. "Nan dai manosh ya fara bada lbr kamar haka... Lokacin muna zaune da matata *aunty'n yara*, dan ranan sam ban fita aikiba munata hira. Kawai senaga wata mace tana kirana da cewa lokacin tfyanmu yayi dan haka inzo mu tafi,sam nayi banza da ita,seta naga tana k'ok'arin cutar da aunty da wani abu wanda bansan meneneshiba,ganin hakan yasa nacewa aunty ta kwauce amma tak'i saboda batasan dalilin fad'in hakanba. Nikuma babu yadda zanyi dantafi karfina,hakan yasa namik'a mata hannuna shine bansake sani komaiba se bayan wasu lokaci dana b'ude idona sena ganni a wani gida na alfarma wanda babu alaman k'ofa bare window. Bayan na gama bin gun da kallone sena maida kallona gun ita wanda nake gani. Cemin tayi barka da farkawa mekake son ci? Nace mata babu komai inane kuma nan? Tayi murmushi tace dani masauk'ina kenan anan zancigaba da zama har muyi aire da ita. Nace mata aini ina da aure,tace wacece matar nawa? Amma sam nakasa tunawa da komai akaina bare har in kira sunan wani nawa. Ganin hakanne yasa tayi dariya tare da zuwa inda nake tashafi kaina tace my manosh karka damu kakuma kwantar da hankalinka dan kazama nawa nima na zama naka yanzu kaji? Dan haka gayamin mezakaci? Kaina girgiza mata nace bana son komai inaso ta maidani inda ta d'aukoni,amma setace ainazo kenan bazan sake komawaba saboda na baro wannan duniyan mutanen nan duniyansu na aljanu nake. Ban iyawa cewa komaiba itama kuma haka har lokacin sallah yayi wato magrib. Ita da kanta tazo tacemin lokacin sallah yayi tayimin nuni da wani gun acikin inda muke wanda bazai wuce taku shiddaba tace dani toilet ne idan inada buk'aka. Mamaki sosai naji dan nidai ganin gurin nayi kamar irin kumbo ind'in aka jera masu kama da gwala-gwalai se shek'i sukeyi,ban iya hakuri nanufi gurin ahankali,ajikin kumbon naga wani guri kamar alaman kofa ce amma kuma baida girma sosai danko kainama bazai shigaba bare kuma nikaina. Gurin k'ofa nad'an sa hannuna senaga kofar nata girma kamar di ana bud'e gate mai taya haka wannan k'ofar ta bud'e inda idanuna suka makance da wasu irin abubuwa burgewa dana gani aciki,bansan lokacin dana shigaba. Nakusan 1hr ina kalle-kalle kafin yayi alwala nasake sa hannuna agun seya bud'u. "Tana tsaye tana kallona tare dayin murmushi tayimin nuni da sallaya mai kyau naje nayi sallah ta agun. Bayan na idarne nake tambayanta ita tayi sallan ne? Tace dani batayiba kuma bazatayi harsena

Chapter 15 of 17