Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tari takeyi suna kallon juna da manosh wanda babu alamun tausayi a fiskanci gashi su marwan sun kasa karb'armaryam a hannunshi kuma da hannu d'aya ya shaketa. Marwan yace manosh meke damunkane me kuma haka,aunty cefa saketa mana dama ashe gaskiya zaka kasheta kenan? Yace eh kasheta zanyi dan wlh baki isaba maryam kinyi kad'an,maryam ta fara fita hayyacinta tana magana dakyar tana cewa yah ibrahim zai kashenifa. Ibrahim yace marwan matsa baya,ba musu marwan ya matsa dan abin yabasu tsoro,ran yah ibrahim a bace ya bige hannun manosh da dukkan karfinsa take manosh ya fad'i akan carpet,ita kuwa maryam bayan ya ibrahim ta koma tare da rik'e mishi riga tana tari tace yah ibrahim kaganiko,wlh bazan zauna dashiba,tausayinta ya kamasu dukkansu,da sauri marwan ya d'auki wayanshi ya kira dad d'in manosh yace dad kazo gidan manosh akwai babban matsala. Shi kuwa ya ibrahim zaunar da maryam yayi akan kujera ya nufi kan manosh yanata karatun qur'an danya fahimci cewa balaifin manosh bane tun lokacin da yaga irin kallon da manosh yakeyiwa maryam kafin ya nufi kanta. Maryam dai kuka kawai takeyi marwan yace mata sannu,shi kuwa ibrahim karatu kawai yakeyi da k'ira'a irinta abdallah,hakan yasan maryam tsananta kukanta sosai fiye dana dah. Take manosh ya fara magana yana cewa wlh ibrahim idan ka shiga hannuna zakasha wuya,ni kake yiwa haka ko,wlh to maryam zatasha wuya aguna tunda ni kake wahalarwa,ibrahim dai baya ko sauraronshi karatu kawai yakeyi yayinda maryam ta tsaya dayin kukanta suna mamaki ita da marwan cewa dama manosh yana da aljanune kenan? Sallamar dad da mum ne ya juyo da maryam da marwan,shi dai yah ibrahim karatu kawai yakeyi yayinda manosh yaketa surutai. Maryam ta sunkuya k'asa ta gaishesu kanta a sunkuye suka amsa dad ya nufi gunsu manosh,ita kuwa mum mamakine ya shikata da abinda ta gani,yau manosh d'antane da aljanu? daidai nan manosh yace kayi hakuri ibrahim zanyi magana wlh zanyi magana ka dena k'onani dan naga bakada imani ko kad'an,ibrahim yace kai kana da imanine,me manosh yayi maka haka kake k'okarin kashe matarsa? Yace nifa ka dena dangantani da naniji ni macece,ibrahim yace macece ke? Tace eh tunda na fara ganin manosh naji ina sonshi saboda kyawunsa yamin,toh tun a wannan lokacin na shiga tsakaninsa da duk wata macen dake fad'in duniyannan wanda bazaiji mace tamishibama bare har yace yana sonta,dukda dai baya wasa da ibadanshi amma senayi nasara akanshi,se rana d'aya ya had'u da wannan makiran wai ita maryam,ibrahim yace karki sake ce mata makira domin zan k'ona gabad'aya,tace saboda kana sonta kenan,meyasa ka bari akayi aurensu da manosh d'ina to tunda dai itace yarinyar daka dad'e kana kauna? Kunya sosai ibrahim yaji,yace ki dena min wannan shirmen ki gayamin abinda yasa kika shigo rayuwarsu,tace tunda ya had'u da maryam ya fad'a mata ra'ayinshi akanta,abin yamin zafi nayi iya k'okarina in cutar da maryam d'in kuma amma shegiya na kasa samun nasara akanta,ibrahim yace ta Allah batakiba tafi karfinkine shiyasa. Hhhh tayi dariya tace wlh batafi karfinaba ina tarata ne kawai,nice nake hana manosh kallon ko wace mace,shiyasa nasashi tsanan kallo,duk wata mace da zata dinga kallonshi tise nasa tsanan hakan agareshi,itama maryam d'in batajine ai amma soda yawa ina gaya mata cewa bana son kallon da takemin amma taqi,tunda akayi auren banbar manosh yaje kusa da maryamba,duk lokacin dayayi yunk'urin zuwa se'in rikitashi inyita bashi wahala,sena tabbata yaji jiki sannan nake barinsa idan ya farka da asuba kuma garau yake se kuma wata daren,dan bana barin yazo d'akinta sam itace take zuwa gaisheshi da safe,shine yau ta ibi kafafunta taje gunshi daidai lokacin da nake bashi wahala,yayi iyakar kokarin yaga ya hanata karasowa inda yake,amma dayake ita d'in mai taurin kaine sedata k'araso dan taga halin da yake ciki,shine na shike jikinsa nake son kasheta domin in rabata dashi.. Jikin kowa a palon yayi sanyi tare dajin mamakin abinda aljanan take cewa. Ibrahim yace to ina gargad'inki daki fita daga jikinsa kona k'onaki,tace wlh bazan fita ibrahim ina tausayinka wlh,yace baki fitabako,nan yaci gaba da karatu se ihu takeyi tana cewa kayi hakuri wlh zan fita amma tabbas zan dawo wannan alkawarine kuma wlh bazan kyale maryam ba,danya d'auki son duniya ya d'aura mata wanda hakan yana k'ona min rai sosai,ibrahim yace toke akwai aure a tsakanin ku damu ne,tace eh nida manosh kam wlh akwai aure a tsakaninmu,ibrahim yace menene sunanki? Tace sunana SHUKRA,yace to shukra ina miki gargad'i na karshe ki fita a rayuwarsu idan ba hakaba zakisha wuya,tace lallaima yah ibrahim wlh kona fita zan dawo kuma idan ka rabani na masoyina senayi maganinka,yace kiyi koma menene sannan yaci gaba da karatu babu sassauci,ihu takeyi tana cewa wlh zan fita kayi hakuri ibrahim mugu zan fita wlh, aisam bai saurareta yanata karatu se kawai akaji manosh yayita attishawa,dukda haka ibrahim bai tsayaba seda yayi sosai sanan yayi hamdala ya koma gefe ya zauna. Tare da gaisawa dasu dad,se godiya suke mishi harda marwan da jikin yayi sanyi. Wayan ibrahim ne yayi k'ara ya duba yaga baban maryamne ya d'auka hello baba,baba yace ibrahim lfy baka dawoba mamanka ta damu an kiraka shuru,yace lfy lau baba yanzu zan dawo insha Allah,yace to Allah ya kare,yace ameen sannan ya katse yaga time har 11:20pm. Yace toni zan koma sedai inda hali kar'a barsu sukad'ai agidan,dad yace mungode sosai ibrahim badamu semu tafi gida dukkanmu inyaso zuwa gobe sesu dawo,ibrahim yace to nagode aunty kiyi hakuri kinji komai yawuce insha Allah,cikin sanyin murya tace nagode Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan suka fita shida marwan ya rakashi. Mum tace sannu maryam aima kinyi k'okari wlh jeki ki had'o nuku kayanu koda kala d'ayane semu tafi ko,tace to tare da mik'ewa shi kuwa dad yanata kallon d'ansa cike dajin tausayinshi wanda har yanzu bacci yakeyi bai farkaba. Marwan ya shigo daidai lokacin maryam ta fito da kit se dad ya tashi manosh kuwa yana farkawa yagansu ciki da mamakin ganinsa kwance a k'asa kumaga marwan,mum tace son muje gida,yace mum lfy,tace lfy lau ga dad naka a bayanka,juyowa yayi da sauri ya kalli dad tare dajin kunya ya gaisheshi,se dad ya mike yace zamuje gidan dakai da maryam gobe seku dawo,mamaki sosai manosh yayi amma bazai iya cewa komaiba se toh. Maryam ya hango rik'e da kit a hannunta kanta a sunkuye marwan yajawoshi yace muje. Marwan yayi musu sallama ya wuce gida,manosh yace dad bari nakaimu,bamusu dad ya bashi key d'in tare da shiga gaba,mum da maryam akuma suna baya ahaka suka isa gida. Koda suka isa se mum tace kuje side naka seda safe,daga shi har maryam kunya sosai sukaji tare da wuce. Suna shiga ya rufe ko ina,ya juyo suna kallon juna da maryam,murmushi tamishi shima haka tare da rungumeta yace apple kiyi hakuri kinji,bansan dalilin dayasa su dad sukajeba kuma sukace muzo nan,amma gobe zan tambayeahi kinji,murmushi tayi tare da d'agowa suna kallon juna tace kanaso in dinga kallonka? Yace eh mana,sedai fa aduk lokacin da kike kallona fita hayyacina nakeyi,tace wannan karon babu abinda zai faru inane d'akinka,yace mujene,kai ta d'aga mishi aise ya d'auketa kamar bby ita da kit d'in dukka ae d'akinshi,akan gado ya ajiyeta tare da karb'an kit d'in ya ajiye a gefe yace namance wayaya wlh ni kwata kwata banganebama,tace karka damu wayanka yana cikin kit d'innan na d'auko mana komai,yace yaushe marwan yaje gidanmu,tace tare dasu mum yazo nina kirasu nace ina tsoron gidanmu,shine sukazo d'aukanmu. Kallon maryam yakeyi tare dajin mamakinta harzaiyi magana se tace pls peach nifa amaryace koka manta,inaso in watsa ruwa,inda take yazo tare da rungumeta yace i luv apple,tace i luv u too peach,sannan ya cire jallabiyanshi dagashi se boxer tayi saurin juya mishi baya ahankali ya cire mata doguwar rigan se wandon sleeping dress nata kawai,kunya sosai taji tayi saurin kare k'irjinta da hannayenta dare da rufe idanunta. Juyo da ita yayi a hankali yana kallonta,batare data bud'e idoba tace inaso inyi wankane cikin wata irin murya,d'aukanta yayi cak se toilet shida kanshi yayi mata wanka tanajin yadda yake gogeta da sosonshi cikin wani irin salo,ita kuwa idonta arufe tana jin kunya. Seda ya wanketa sannan ya dawo da ita d'aki yayi pecking idonta yace bari inje inyi nima kinji,shuru tayi batace komaiba ya wuce toilet. Da sauri goge jikinta tasa rigar bacci dogo har kasa,sannan ta d'auki wayanta ta kira yah ibrahim,bugu d'aya ya d'auka yace hello aunty,murmushi tayi tace yah ibrahim ka koma lfy,yace lfy lau harma na kwanta,ya captain,tace lfyanshi mun gode sosai yah ibrahim,yace bakomai aunty seda safe ko,tace to sannan ya katse wayar yana maijin kaunarta har cikin ranshi sam baiyi bacciba.... [7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas 61-62 Bayan manosh ya fito daga wanka ne,tace peach ka kira marwan kaji ya isa lfy,wayanshi ta mik'a mishi ya kirashi,marwan yace lfy lau wlh harma na kwanta,manosh yake toseda safe,yace yawwa. Kayan baccinsa ta bashi yasa tare da fesa turare sannan yamatso har inda take kwance ya mannata da jikinshi yace apple bamuci amarcinmubafa kina sane,shuru tayi kamar bata jishiba seya janyota jikinshi yana mata wasu salo na soyayya tace dan Allah ka bari ba'a gidannu mukebafa ni ina kunyan su mum. Yace aibazasu jimuba,tsakaninmu dad'an nisa,tace nidai pls kayi hakuri semun koma gida,haka ya hakura suka kwanta amma suna manne da junansu kamar zasu had'i juna. Washe gari mum ta kirashi inda suka zauna da dad ya gaya mishi duk abinda ya faru jiya,mamaki sosai manosh yayi sannan dad yaci gaba da mishi nasiha yana cewa nasan baka wasa da ibada manosh amma ka k'ara himma,gidiya sosai yayi sannan ya tafi musu da abin karyawa. Maryam tayi kyau tana zaune yazo da abinci ya zuba musu sukaci suka koshi se yaketa kallonta,yace apple abinda ya faru kenan dama,kai ta d'aga mishi,ya matso ya runguneta yace kiyi hakuri kinji,tace bakomai wlh aiba laifinkabane komai ya wuce. Manosh yaso su kma amma mum tace sam su bari se magariba,haka suka kasance a cikin d'aki har dare bayan sunyi salla se driver ya maidasu da kulan abincinsu. Seda suka gama komai yace tazo suyi sallan nafila,bayan sun idarne ya wuce kan gado ita kuwa ta mik'e ta cire himar tare da zanin jikinta dayake rigan baccin daya d'auko mata guntune sosai iya cinya. Tana cier zani tayi sauri kashe wuta ta kwanta a gefe,dariya yayi yace kunyata kikeji,shuru tayi batace komaiba in banda tsoronshi daya cika mata zuciya. Ahankali yake mata wasanni har suka shagala sannan captain ya hankad'oni waje anan bakin k'ofa na tsinci kaina bana iya jin komai se kukan maryam. Tun tanayi a hankali na dauriya harta kasa hakura,se kusan 11pm kafin na samu dama shiga ciki lokacin manosh ya kunna wuta yana rungume da ita ta baya yana bata hakuri,ita kuwa ko motsibatayi in banda kuka. Toilet ya wuce ya wanke jikinsa sannan ya dawo ya kwanta a bayanta ciki dajin tausayinta. Wutan naga ya sake kashewa zuwa iri 2:30am naji kukan maryam se dad'uwa yakeyi shi kuwa captain numfashinsa kawai kakeji. 3am na samu ganin maryam kwance babu yadda take dan wuya datasha agun captai. Bayan ya fito daga toilet yaje ya wanketa tas,sannan ya shiryata, kan gadon nasu kuwa babu jini ko kad'an akai,ita kanta maryam tayi mamakin rashin ganin jinin,dan yadda tasha azaba. Shi kuwa captain se washe baki yakeyi ya same maryam daidai gata masha Allah zanzan ya jita yadda ake buk'ata🙈 Sorry apple,am very sorry akay? Shuru tayi tare da matsawa daga jikinshi wai ita a dole tana fushi dashi,murmushi yayi yace haba aunt wlh balaifina bane pls karkiyi fushi dani,cikin muryan ban tausayi tace amma kanaji inata baka hakuri koka saurareni,dariya abun ya bashi yace to ai bana jinkine apple amma kinsan ai bazan miki hakaba ko jealousynah,murmushi tayi tace ka tafi d'akinka ka barni,yace haba apple am sorry bazan sakeba kinji,lumui ta kwanta ajikinshi ya matseta sosai a haka sukayi bacci Bayan sunyi sallan asubane yace bari na fita kozan sami chemis a bud'e in nemo miki magani jikinki yayi zafi sosai,tace to peach karka dad'e pls,yace bazan dad'eba aunt tare da manna mata kiss sannan ya tafi. Duk chemis d'in a rufe suke dan haka ya kira muh'd yace bari nazo na karb'i magani agunka mana apple na fama da zazzab'i wlh,dariya muh'd yayi yace ai dama ina tausayin aunty randa ta shiga hannuka,dariya manosh yayi tare da katse wayar ya isa gidansa. Magani muh'd ya had'a mishi yana dariya kai kuwa baka mata a hankali bane,koda yake ashe kaid'in sojane komai da zafin nama akeyinshi,duka manosh yakai mishi yace ashe kaima majid ya b'ataka ban saniba,muh'd ya gudu gefe tare da kiran marwan a waya yace marwan ganiga captain yayiwa aunty bad-bad shine yazo neman magani,ai da duka manosh ya biyoshi,shi kuwa muh'd yayi saurin shigewa gate d'in gidansa ya rufe yana dariya,shima manosh dariyan yakeyi ya shiga mota ya wuce tare da d'aukan kiran marwan yace 'yansa ido me kuma zaka gayamin,marwan yace idan ka isa gida kashewa aunty ina mata sannu,dariya manosh yayi yace zan had'u daku,marwan yace nidai ka isar min da sakona bari in gayawa muhsin. Ai kuwa nan danan muhsin ya kira manosh yace haba captain ba sauk'i sam kodai bakaga aunty namu 'yar chukula bace,manosh yace wlh karka sake ce mata 'yar chukula dan wlh idoce ita chukulan amma a ciki ba haka abin yakeba,dariya sosai muhsin yayi yace naji kaje neman magani dama kai baka tanadi maganiba bayan kasan yadda kake,manosh yace d'an isa karku sake kirana ya katse yana dariya. Yasan cewa majid zai kirashi dan haka yayi saurin kiran majid yace kaikuma mezaka cemin? Majid yayi dariya yace nidai kawai kabar aunty se bayan 3days kafinnan ta samu lfy sosai dan idan ka sake afka mata yau tofa dole muje asibiti jinya,manosh yace kaifa iskancin naka daban ne amma zan rama d'an iska wayasan wuyan da sis miher tasha agunka,majid yace duk wuyar da zatasha dai bazaikai na matar sojaba dai hhhhhhhhh,manosh yace zaci ubaka wlh majid idan muka had'u zaka gane,majid yana dariya yace ai bazama mu had'uba jibi zanyi tafiya nida my luv,manosh yace ai zaka dawo d'an iska ai gara kowa dakai wlh,majid yace captain ba suki Allah sarki aunty walh ina tausayinta hhhhh. Da dariya sosai manosh ya shigo d'aki tare da rungume maryam yace in hada miki tea? Tace a'a ruwa kawai zata sha,nan ya bata tasha da maganin sannan suka kwanta bacci. 11:30am suka farka inda ya wuce yayi musu wanka suka shirya sanna ya had'a musu tea da bread ta soya musu egg suka sha tana jin kunyanshi sosai. Shi kanshi ya lura da haka bayan sun gama ya d'auketa se d'akinshi can suka koma suka kwanta yana mata hira mai dad'i ita kuwa se dariya takeyi cikin k'ank'anin lokacin ta sake dashi sosai sukaci gaba da soyayyarsu. Mum ce ta kira maryam suka gaisa take tambayarta babu wata matsala dai ko,maryam tace bakomai wlh,tace to shikenan Allah ya muku albarka tace ameen tare da kallon manosh tana dariya. Manosh da friends nashi suka shirya sukaje yiwa surukansu gidiyan aure kamar yadda akeyi,sannan ya bada kud'i sosai dan a k'ara fad'ad'a masallacin unguwansu ya kuma bada kud'i a gyara musu gidan. Godiya sosai maryam tayi tare sadu zahida dan duk sun yiwa iyayensu hidima sosai. Ya ibrahim kuwa girma dad d'in manosh ya k'ara mishi a companinsa dake kaduna wanda aka bashi asistan director a gurin. Kud'i sosai yake samu cikin k'ank'anin lokaci ya sayi mota EODbarka na musam maryam da rash sukaje sukayi mishi,murna sosai mama tayi da ganin yadda maryam ta k'ara kyau, itama maryam dad'i taji sosai da ganin yadda aka gyra musu gidansu,rash ta shigo tana tayi musu hotuna,inda maryam take sanye da green atamfa tasha ado tare da coffee bag a hannunta. Da yamma mazajensu sukazo d'aukansu, inda suke koyawa matansu driving,sannan result ya fito duk aka sasu a FUTY YOLA inda dukkansu suke level one. Hmmm sosayya sosai suke zubawa junansu,inda duk suke d'auke da ciki amma na marya dabanne dan wahala sosai takesha. Lubna kuwa taga ba sarki se Allah dan haka tatsai da zuciyanta kawai agun yah ibrahim musamman lokacin da bro marwan ya kirata yace lallai ta cire son manosh a ranta dan manosh baya ganin kowa se maryam,sannan yace mata ibrahim mutumin kirkine ga addini wanda duk wani uba ko yaya zaiso ace 'yarsa ko k'anwansa ta auri miji irin yah ibrahim. Hakanne yasa lubna saduda tabashi dukkan soyayyarta,inda suke soyayyarsu mai tsafta sosai. Ciwon maryam se gaba gaba yakeyi,abun harya fara damun kowa,tunba yah ibrahim da iyayen manosh bare sunsan abinda shukra tace,amma dukda hakan se suka barshi akan laulayin cikine,hakadai taketa fama ga laulayi ga zuwa makaranta ga kuma kula da peach. Hajiya hadiza mahaifiyar lubna da kuma hajiya iya kullum idan suka had'u banda kuka da nadama babu abinda sukeyi. ********* Kwanci tashi su maryam har sunyi hutu,se abin yad'an mata sauki kad'an. Mum da mamanta kusan kullum suna hanya zuwa dubata,kuma sam har yau yah ibrahim bai gayawa kowa abinda ya faru,iya tsakaninsu kawai sukabar zance. Cikin maryam yafi nasu rash girma da kuma yawan watanni,ranan tana yankawa manosh fruit kawai seta zube a k'asa,dab kuwa lokacin manosh yazo gida,ai da sauri ya d'auketa se hospital d'insu muh'd, tun azahar akace musu haihuwace amma har magriba tanata fama. Hankalin mama da hajiya iya ya tashi sosai dama tunda manosh ya kira baba yace ga maryam sunzo haihuwa se yah ibrahim ya kaisu hospital d'in. Addu'a maryam taketa samu kota ina,mama kuka kuka takeyi dan bazata tab'a mance haihuwan maryam ba wanda bata cikin hayyacintama ta haifi maryam d'in. Hajiya iyace taketa kuka tana rarrashi mama,maryam bata haihuba har 2 na dare,anan akace jinin jikinta yayi kad'an dole asa mata wani,yah ibrahim kamar zaice a d'ibi nashi dayake yanaba mutane sosai jininshi. Amma seyayi shuru manosh ne yabada nashi aka sama mata. Ana kiran sallan asuba maryam ta haihu amma sam bata iya gane kosu waye akanta. Kukan bby ne yasa kowa yasan maryam ta haihu,dan manosh yaso ya kwana a hospital d'in amma dan kunyan su mama yasa ya tafi gida sam ya kasa bacci 4am cib yazo hospital d'in yana dawowa daga masallaci yaji kukan bby,hamdala yayi tare dajin farin ciki aransahi. Mata biyune suke kula da bbyn, d'aya ta fito tace dasu maryam ta sauka lfy an sami 'yan biyu. Manosh ya kasa b'oye murnanshi yace maryam fa,lfyanta k'alau dai ko,tace eh lfyanta k'alau sedai tasha wahala sosai dan haka tana buk'an hutu yanzuma ruwa nasa mata,hamdala kowa yakeyi muh'd yace bari na shiga na dubata,lokacin an rufeta bbys kuwa an shiryasu tsaf,dama ba kaya d'aya aka rik'oba. Suka fito da yara kyawawa kamar iyayensu,manosh yace zan iya shiga inga maryam,sukace eh kaje,da sauri ya wuce baima kalli jariranba,inda mama da hajiya iya suka k'arb'esu. Manosh yana shiga ya rungumeta tana bacci,muh'd yace kwantar da hankalinka idan ta farka garau zata tashi insha Allah,ina taya baban twins murna,murmushi yayi yace nagode sannan suka fita danta samu bacci sosai. Boy ne da kuma byy kyawawan gaske,manosh da muh'd suka karb'esu tare da murna. Daidai sega yah ibrahim yazo tare dasu mum d'in manosh. Murna sosai akayi kowa se cewa yake masha Allah. Kinya yasa manosh barin gurin ya kira mai shiryawa bbys nashi d'aki yace matata ta haifi wtins mace dana miji dan haka ka shirya gobe sekazo a gyara musu d'aki.yana ajiyewa yayita kiran abokan arziki yana shaida musu haihuwan maryam kowa se tayashi murna yakeyi,kafi 8am hospital ya shiga da friends nasu ga kuma su rash da miher. Gefe d'aya hajiya iya ta koma tanata kuka tare da cewa ohh Allah,meyake shirin faruwane dani,kodai lokaci yayne dazan fasa wannan kwan kowa ya sani.. [7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas *dedicated to hama gee muh'd*❤🌹 ❤)* 63-64 maryam bata farkaba har se azahar,koda bud'e ido mum d'in manosh ce da mamanta zaune suna mata sannu maryam,kunya sosai taji dan tasan cewa ta haihu. Mum ta kira manosh a waya tace to "son" maisunana ta farka seka kwntar da hankalinka kaci wani abun ko,mirmushi yayi tare da cewa thankyou mum ina zuwa yanzu. Maman maryam tace Allah ya gagara cin abinci ko,mum tace wlh yaqi sam duk ya rud'e, kunya sosai maryam taji,mum d'in manosh ta had'a mata malt da peakmilk aka bata tasha sannan aka bata nama mai zafi sannan suka bata guri danta sake. Yah ibrahim ne ya shigo da mamanshi,murmushi takeyi tace yah ibrahim,yace na'am sannu ya jiki,tace da sauk'i ciki dajin kunyarsa,yace Allah ya baki lfy ya kuma raya mana twins,tace ameen a ranta,afili kuma tace nagode,sannan suka gaisa da maman rash inda ta ajiye mata tuwon shinkafa da kuma kunun gyad'a mai zafi. Haka dai akaita shigowa su k'awayenta da kuma abokan manosh musamman muh'd dayake shine doc d'inta. Manosh baizo hospital ba se 3:10pm shida maigidanshi,bayan sun gaisa dasu mum ne seya mishi jagora har d'akin marya. Tana kwance tana d'an hutawa kamar yadda doc yace abarta ta huta dan tana buk'atan hutun. Da sallama suka shiga,manosh yayi saurin d'aukan himar nata yasa mata tare da kashe mata ido d'aya sannan yace yallab'ai bismillah,cikin mamaki maryam taga babban mutum ya shigo,sunkuyar da kanta tayi tace ina wuni,yace lfy lau mmn twins mun samu k'aruwa,tace hmm tana murmushi,yace toh Allah ya raya manasu tafarkin addinin musulunci, tace ameen mungode,yace amma babu wani problem ai ko,manosh yace yes bakomai amma dai doc yace tana buk'atan hutu sosai inga zamu kai jibi kafin a sallamemu,oganshi yace ok to Allah ya bata lfy,manosh yace ameen "sir ga bbys d'in,nan suka k'arasa suka d'aukesu shima manosh se yanzu ya k'are musu kallo se wani farinciki yakeyi wanda oganshi se kallonshi yakeyi,yace gaskya dole kayita smiling irin wannan kyauta da Allah ya maka gaskya se godiya,manosh yayi dariya yace "thankyou sir" yace boy zai zama soja kenan shima,dariya sukayi dukkansu harda maryam,sannan yayi musu sallama manosh ya rakashi gun mota inda driver yake jiranshi sannan ya dawo gun apple nashi. Da gudu ya rungumeta ita ta sake langwamewa a jikinshi ta matseshi sosai tana cewa i luv u peach,yace ai wasane apple,nene nake k'aunarki kamar zanyi hauka wlh peack mai zafi ya manna mata yace thankyou so much apple,kai ta d'ago tana kallonshi mai d'auke da alaman tambaya,yace yes saboda kinyi k'ok'ari gashi kinsha wahala sosai wlh "im sorry for what i did to u apple" tace me kenan? Yace (dana shigeki mana) amma dai munga riban hakan tunda gashi mun samu yara har 2 a lokaci d'aya, ya rad'a mata akunnenta. Dariya sosai takeyi shima haka,slm sukaji tayi saurin janye jikinta daga nashi,shi kuwa bai matsaba dan yasan dai basu mama bane. Miher ce ta shigo tana murmushi tave eyye maman twins kamar bake kika haifesuba,manosh yace karki yarda kowa yagansu yasan itata haifesu kidena hura mata kai dan yanzu kam ta tsufa saura inyo mata amarya,wani irin kallo ta watsawa manosh tare da cewa wlh peach kaga bana sofa,dariya sukayi shida miher ya tashi yana cewa jealousy tare da d'aukan boy d'in dan miher ta d'auki girl. Tace peach matso dashi nan pls,ba musu yakai mata tanata k'are mishi kallo tace mai kama da bbnshi,miher tace wannan kuma mai kama da mmntaba,dariya sukayi yace wani suna kike so aba girl d'in? Tace boy d'infa,yace a'a banda boy ke kizab'a sunan girl ni kuma inzab'a na boy,tace to ayiwa su mum da mama da ni kakwara,miher tace lallaikam nima na amince shikenan maryam ta haifi maryam,hhhhh sukayi dariya,manosh yace thanks naji dad'in hakan kuma na amince,amma wani suna aza'a kirata dashi? Maryam tace *Alfiyya*, miher tace "wooo! what a nice name" gaskya sunan yamin dad'i,maryam tace nagode,manosh yace thankyou *mom alfiyya*, miher tace bro boy kuma zakayiwa majid takwarane ko,hhhh sukayi dariya,yace kunji mara kunya ko,hhhh sannan ya mik'e yace se nan da 3days zakuji sunan boy nah. Bayan manosh ya fita miher ta zauna sunata hira tare da shirin yadda suna zai kasance. Hajiya iya ta shigo tanata murna tana cewa sannu da zuwa mai gida da kuma kishiya,hhhh maryam tace bakya kishi,tace banayi tunda na samu sabon mai gida. Hakadai akaita hira koda yaushe mum d'in manosh tana hanyan zuwa duba jikokinta musamman datasan takwara aka mata ita da mmn maryam dan duk sunansu d'ayane. Yau kwana uku da haihu aka sallami maryam,gidan mijinta aka maidata inda yapendo ladi take zaune da kuma nafisa itace mai girki. Manosh ya sanar da apple sunan yaro "ABDALLAH" dad'i sosai taji mara misaltuwa,dan duk tunaninta zaiyi wa mahaifinsane takwara. Rungumeshi tayi sosai tana murna harda kwalla,dan har azuciyarta tanada niyan yiwa abdallah takwara amma sam bata san ran yanzu bane. Hawayen ya share mata yace bana so ki sake kukan rashin abdallah apple danga abdallanki ya dawo.murmushi tayi tace nagode sosai peach,kai dabanne acikin sauran mazaje shiyasa akoda yaushe nake k'arayin godiya wa Allah daya bani miji kamarka,peach ina maka k'aunar dabasan iyakacinsa,fata akoda yaushe shine Allah yabarni dakai har' aljanna. Rungumeta yayi sosai danjin dad'an kalamanta masu kwantar da hankali da kuma shiga rai,har seda ya kwantar da ita akan gadonsa sunata kissing junansu,dakyar ta kwaci kanta ta gudu d'aki tana mishi gwalo shikuwa murmushi kawai yakeyi tare dajin k'aunarta na ratsa jijin jikinsa. D'akin alfiyya komai pink ne kamar yadda kuka sani,shi kuwa abdallah blue,basena na tsaya yin bayanin yadda d'akin zai kasanceba,saboda ku masu karatu kunsan wanene manosh kua kunsan abunda zaiyi❤)* Yau suna harta motanta 307 sayarwa manosh yayi ya saya mata benz sabudal. Kar kuga yadda akayi wani decorection agidan,'yan makarantansu su maryam kowa se kallo dasan barka,idan kanajin ruwan kud'i tofa anyi ambaliyansa agun maryam da yaranta, ranan gidan a cike yake da 'yan media se d'auka akeyi, gift kuwa maryam ta samu hardana hauka. NOKIA manosh ya saya guda 100 irin masu tosh d'innan wanda a yanzu kusan 8k suke haka yasa aka k'era mishi ya raba a suna,banda sauran tarkacen da akayi wanda bazasu irguba. Idan ka kuna wayan sunan abdallah da alfiyyane yake bayyana maimakon kaga NOKIA,hmmm naso ace *fans* kunje sunan zaku wanke ido taass. Kula sosai suka samu daga maryam har yaran. Inda aka tura manosh k'asar waje kuma zaikai 3 to 4 kafin ya dawo. Haka ya shirya ya tafi danba yadda ya iya. Yana can miher,zahida da rash suka haihu. Manosh baya gari akayi suna,suma kunsan ba bayaba,shagali sosai akayi. Satinda manosh zai dawo

Chapter 11 of 17