Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a ciki tanata fesawa flowers d'in ruwa tana sanye da toyobo himar milk colour dogone har k'asa kuma mai hannu bakama iya ganin kayan da yake jikinta. Da sauri ta fito dan a tunaninta flower aka zo saya,ahankali suke fitowa majid ne ya fara fitowa tare dayin sallama sannan suma suka fito da irin sarin indian nan na maza jajaye se binsu da kallo takeyi harta hango manosh wana shi farin sarine a jikinsa duk wanda ya gansu dole su burgeshi. D'an murmushi kad'an tayi tare da amsa sallamar majid tace sannunku,majid yace yawwa,setace ina kwananku,suka amsa lfy amma manosh bai amsaba kallonta kawai yakeyi,bayan sun gaisane tace lfy dai ko,muhsin yace lfy lau munzo sayan flower ne,tace flower kuma ai naga kuna tare damai sayarwan,muh'd yace eh hakane amma mu naki mukeso,murmushi tayi wanda yake k'ara mata kyau batare datace komaiba,majid yace zan iya sanin sunanki dan nidai sunana majid,tace ni kuma sunana MARYAM amma auntyn yara akekirana,majid yace wow maryam babban suna,muhsin yace lallai yanzu mun zama 7 emms kenan,bata gane maganan muhsinba amma setayi shuru,muhammad yace meyasa ake kiranki da auntyn yara,tace yarane suka samin sunan,majid yace alamu ya nuna kina son yara kenan,murmushi tayi tace eh,majid yace munzo gurin mahaifinkine,tace ok yaje gida amma inaga yana hanyan zuwa nan. Muhsin yace nidai sunana muhsin,wannan kuma muh'd seya nuna manosh dayake tsaye yana waya da miher tana cewa wato bro shine ka tafi ko sallama babuko,yace wannankuma sedai ya gaya miki da bakinsa,murmushi tayi tace lallai fa dukknku "emms" muhsin yace eh shiyasa nace yanzumun zama 7 emms kenan akwai d'ayanmu shi bai samu zuwaba sannan akwai k'anwarmu ita M ce. Dariya tayi wanda ya baiyana fararen hakwaranta tace masha Allah,manosh ya gama waya yana binta da kallo yace ni ai bata gaisheniba bare in gaya mata sunana,kanta ta kawar gefe tana mirmushi tace ina kwana,yace seda na rok'a,shuru tayi ta rasa me zatace,majid yace tunda dai ta gaisheka ai shikenan,yace to lfy ya kike,tace fy lau kodai zaku k'arasa ne naga har yanzu bai dawoba wata k'ila akan yanya kuke,muhammad yace ta ina gidan yake,tace hanyan nan dai zaku mik'e duk wanda kuka gani a hanya ku tambayeshi gidansu auntyn yara za'a nuna muku,majid yace to mun gode amma ke kad'ai anan bakya tsoro,tace tsoro kuma aiba komai tana murmushi,muhsin yace to maryam auntyn yara bari muje idan muna dawowa zan sayi flower'n,dariya tayi tace to sekun dawo sannan suka shige motan shi kuwa manosh ya matso kusa da ita yana kallonta,kunya sosai taji tace kai bazaka tafi bane,yace zan tafi amma inaso in miki tambaya kafin in tafi,tace to ina jinka amma kanta na kallon wani gurn,yace akwai wanda yayi sallama agidanku akankine? Shuru tayi tare da kallonshi cikin kunya tace a'a amma ban saniba ko tagun babana,ahankali yake maganan yace akwai wanda yake zuwa gunkine? Tayi saurin mayar da kanta gefe tace a'a,murmushi yayi yace Alhamdulillah nagode AUNT semun juyo,shuru tayi batace komaiba ya wuce ya shiga mota suka tafi tanata binsu da kallo tana jin farin ciki a ranta kome dalili oho. Har k'ofar gidan aka kaisu tare dayin sallama da Alhaji muh'd ATTAH. Ya fito yaga dai bak'ine dan baisansuba,da sauri suka sunkuya dan gaishesa,amma dayake mahaifinnata mai ilimin addinene seyace a'a a'a karku sunkuyamin wlh ku mik'e dan Allah,dad'i sosai sukaji azuciyarsu kuwa sukace lallai akwai SUNNAH agidannan,bayan sun mik'e yace to bisimillah ku shigo,suna biye dashi a baya har palonshi,inda ya musu nuni da kujera suka zauna sannan suka gaggaisa. Mahaifin maryam yace sedai ban ganekuba wlh, wani yarone ya shigo da sallama tare da kawo musu FARO WATER mai sanyi yana ajiyewa tare dayin gaisuwa ya fita. Muhammad yace eh baba abokinmune yazo neman izini akan maryam, baba yace Allahu Akbar ayya kuma sam maryam bata gaya min zaku zoba wlh,muh'd yace eh gaskya ita kanta bata sanmuba muna dai ganintane se mukayi tambaya akanta shine shine mukazo amma dai sun tab'a had'uwa dashi abokinmu. Baba yace Allah sarki toba damuwa an muku izini zaku iya zuwa a nan kuke ne? Muh'd yace eh muna nan a cikin jimeta tare da iyayenmu, ni sunana muh'd wannan majid,wannan muhsin sannan abokinmu kuma muh'd manosh. Baba yace to alhamdulillah bakomai Allah ya tabbatar da alkhairi,suka amsa da amin baba mun gode sosai, sannan ya tashi ya shiga cikin gida gun maman maryam ya gaya mata cewa tazo su gaisa,himar tasa baba yana gaba ta tsuguna daga waje shikuwa baba ya shiga cikin palon yace ga mahaifiyarta ku gaisa,sunkuyar da kai sukayi k'asa dukkansu sukace ina kwana mama,tace lfy kun zo lf,sukace lfy lau,tace to madallah sannunku da zuwa,sukace sannu mama sanna ta shige ciki bayare dasun gantaba. Majid da muhsin suka d'auki ruwan sukace to baba mu zamu tafi,baba yace to madallah mun gode sosai Allah ya kiyaye hanya kugaida gida,suka ce amin baba sannan suka fito baba ya bisu har kofar gida sannan ya koma ciki. Ajiyar zuciya manosh ya sauke suka kalleshi suna murmushi angon maryam,dariya yayi sannan yace majid kira mana yaran can mana,take sukazo muhsin ya bud'e but d'in mota yara suka dinga shiga da kayayyaki gidansu maryam. Bayan sun gamane baba ya fito yace haba ku kuwa harda d'awainiya haka to Allah ya saka da alkhairi mungode,sukace bakomai baba sannan baba ya koma gida,yaran kuwa kud'i majid ya rarraba musu naira d'ari d'ari sabbi se godiya sukeyi da murna sannan suka tafi. Auntyn yara kuwa shuru taga baba bai dawoba bare kuma su majid,can seta hango motarsu na zuwa. Bayan sun isone se muhsin ya fito yace to ina flower nawa,tace wanne kake so,ya nuna wani yace wancan,anitse taje ta kawo mishi,yace nawane,tace 500 ne,yace to abani guda 2,nan ta sake kawo mishi,daidai lokacin suma suka fito,se muhsin ya karb'a tare da bata 1000,ta karb'a tace tona gode da ciniki,yace bakomainima na gode da sayarwa,dariya tayi,muh'd yace mun godefa auntyn yara ko kuma ince auntynmu mu zamu wuce toh,tace bakomai to Allah ya kiyaye hanya,sukace ameen se muhsin ya mik'awa manosh flower d'aya ya karb'a yana kallon muhsin d'in,sannan ya mik'awa maryam d'ayan amma bata karb'aba tace ya kuma kake bani,yace ka'rbi se in gaya miki,bamusu ta k'arba yace to dukkanku inaso ku shinshini flower'n sannan ya shige mota suka barsu su biyu rik'e da flower. Manosh yakai hancinsa kan flower'n uana kallonta kefa,murmushi tayi tare dakai flower'n kusa da hancinta tace nidai banji komaiba,manosh yace toni naji,tace me kenan,yace sosayyarki tare da ajiye mata flower'n yana murmushi yace ina wayarki? Agefenta ya hango INFINIX HOTNOTE ya d'auka yasa number'nshi yayi flashing wayanshi sannan ya ajiue mata wayan yace sekin jini AUNT. Murmushi kawai takeyi tana rik'e da flowern,suka sauke glass d'in motan tare da cewa byee AUNT, murmushi sosai takeyi tace tona gode,kamar had'in baki sukace karki mana godiya,idan kin samu hali ki taimaki mutum UKU suma kuma kice su taimakawa wasu UKUN,suna mata murmushi sosai itama haka,shi kuwa manosh hannu ya d'aga mata batasan lokacin data d'aga masa nataba suka tafi. "Wooow so sweet" ni kaina SAD-NAS sun burgeni bare kuma FANS... [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas 9-10 maryam ta tsincin kanta dabin motansu da kallo tana murmushi tare da ajiye flowern hannunta tace kenan neman izini sukaje gurin baba akai? Manosh kuwa murmushi da jin dad'i kawai yakeyi su majid sunata yaba kyawu da nutsuwa irinna maryam,muhsin yace gaskya abokina kayi sa'a dan wlh ganin maryam yafi jinta. Muh'd yace sosai kuwa muma dai Allah yasa mu samu k'awayenta,dariya manosh yayi daidai nan wayansa ta fara ringing,majid yace kodai maryam d'ince,manosh yace haba kai kuwa meka d'auketa kenan 'yar gaggawa? Majid yace no nidai banceba,manosh yasa wayan a kunne tareda cewa hello abokina ya akayine,marwan yace lbr zaku bani mana mun samu karb'uwa kuwa,manosh yayi dariya yace kaida ka sani kuma,marwan yace aaah "congrats dude" kadai samomin friend nata ko,dariya sukayi dayake suna iya jiyo abinda marwan yake cewa,muhsin yace muma da mukaje bamu samuba bare kuma kai,dariya marwan yayi yace to ai abin rabone,muh'd yace sosai to har yanzu dai rabon namu bai rantseba tukunna kaga majid dayake d'an iskane se dariya yake mana waishi ai yana da miher,marwan yace rabu dashi ba laifinshibane captain ne ya b'atashi ai tunda yace ya bashi miher tun da wuri,any way se kun iso ya banji muhsin bane,muhsin yace abokina aure kawai nakeso nima shiyasa ka jini silent,dariya sukeyi sannan marwan ya katse wayar yana dariya. Mahaifin maryam seda ya rabawa makwabta abin alkhairin dasu manosh suka kai,sannan ya rabawa yaran da suka shiga da kayan sannan ya koma shop d'inna. "Maryam tace sannu baba,yace sannu 'yar baba bak'in da sukazone yasa banzo da wuriba sunzo neman izinine akanki. Shuru maryam tayi dan kunya daya kamata tace baba zan iya tfy gida,yace eh jeki,sannan ta bashi kud'in cinikin seta tafi tana mai jin kunya. Koda ta isa gida mahaifiyarta ta gaya mata komai tare da alkhairin da suka kawo. Murmushi kawai tayi tana bin kayan da kallo,wayar tace ta soma ringing,koda ta duba number'n manosh ne seta tashi ta shige d'akinta tare da d'aukan wayan tace assalamu alaikum,wa'alaikumus salam AUNT,murmushi tayi dan tasan shine setace na'am kun isa lfy,yace lfy lau ya muka barki,tace lfy mun godefa Allah ya saka da alkhairi,yace amin,tace inasu majid,yace duk sun wuce gurin aiki dama akan aikinsu na tattarosu,tace eyyah,yace bazaki tambayeni sunanaba,murmushi tayi tace to ina sauraro,yace a'a ai baki tambayeniba,shuru tayi tana murmushi a hankali,manosh ya sake kiran sunanta AUNT,tace na'am ina sauraon sunanka,yace sunana maryam,dariya tayi wanda shima ya sashi dariyan sannan yace eh mana,tace maryam ai sunan mata ne bana mazaba,yace sunana muh'd manosh mu biyune agun iyayenmu nida k'anwata miher,sannan ni SOJA ne amma friends d'ina suna kirana da prince wannan shine lbrna a tak'aice. Dariya sosai maryam tayi dan yadda yayi bayaninshi da sauri sauri tace masha Allah yanzu kai d'in soja ne,yace banyi kama da sojaba ko,tace gaskya kam,yayi murmushi yace to ai k'aramin sojane ni ba babba ba shiyasa,murmushi tayi kawai batace komaiba,yace aunt ya kikayi shuru kona dameki ne,tace a'a bakomai,yace to kefa,tace sunana maruam ni kad'aice agun iyayena na gama secondary skul muna jiran result,manosh yace ok to Allah yasa muga alkhairi,tace ameen,yace suwaye friends naki na kusa, tace rashida muh'd,amina babale,samira jauro da zahida abba,ya e duk a girei suke,tace rashida da sameera suna gireizahida tana jimeta,amina kuma tana yola. Yace ok kuma ku 5 kenan,tace eh,yace to duk ki gaishe min dasu pls,tace zasuji nagode,yace ok byee,tace byee tare da katse wayan ta sauke wani ajiyar zuciya tana murmushi. Miher taji dai bro manosh yana waya kuma tasan da mace yakeyi,abin ya dameta sosai seta kira LUBNA a awaya tace k'awata gaskya kina sanya dewa kuma wlh na hango matsala,lubna tace kamar ya matsala,miher tace ina tunanin bro manosh ya fad'a soyayya da wata dan kamar naji suna waya ya kamata kiyi mishi magana yanzu gaskya kar asamu matsala. Hankalin lubna ya tashi tace da gaske kikeyi miher,miher tace wlh kuwa,lubna tace pls miher ki tambayi majid tunda saurayinkine pls kinsan babu yadda zanyi in tuntub'i bro marwqn da irin wannan zancen amma tunda ke budurwan majid ne pls miher,miher tace bakomai zan tambayeshi amma dukda haka "you have to do somethin friend" lubna tace sosai ma kuwa zanyi nagode byee. Bayan sun gama wayane lubna ta ciza baki tace ina wlh bazai tab'a yuwaba,duk wanda tayi k'ok'arin shiga tsakanina da manosh wlh sena d'auki mummunan mataki a kanta ko 'yar gidan uban wayece ita. Yaune manosh zai tafi abuja yana sanye da kakin sojojinshi yayi matuk'ar kyau ya fito da 'ayar k'aramar kit d'inshi a hannu ga kuma bindiga a aljihunsa yace mum zan wuce a mana addu'a,tace to Allah ya kare ka kula da ibada sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake,miher da take gefe tace mum kullum sekin gaya mishi haka aiya zauna a kanshi,tace to ai addu'ace kuma d'an adam azijine,manosh yace amin mum rabu da ita yarantace,miher tace wlh bro niba yarinya bace "am a big gal"dariya sukayi suka rakoshi har waje driver yaja suka tafi air port. A hanyane ya kira maryam yace aunt kin tashi lfy,tace lfy lau ya mutanen gida,yace lfyansu lau yanzu na barosu ina hanya zan tafi abuja sannan zanyi 1week kafin in dawo karkiga shuru banzoba,tace ok Allah ya kiyaye hanya Allah kuma ya bada sa'an tfy,yace ameen aunt thankyou so much,tace wlcum,yace ki kulamin da kanki kinji,tace to nagode,yace ok byee sannan ya katse wayar. Ita kuwa maryam seta tsinci kanta dason sake ganinshi dan ad'an lokaci kad'an da had'uwansu amma se taji tana sonshi sosai a ranta,dan tunda take babu wanda ya tab'a zuwa yace yana sonta sedai taji yara suna cewa aunty ai wane yace mana kece matarshi ko kuma wane yace mana ke zai aura, amma babu wanda ya tab'a sallama a gidansu se manosh. Lubna ce kwance a d'akinta daya sha kayan duniya tana tambayan miher a waya toya ake cikine,miher tace wlh da gaskene amma nima majid yak'i gayamin mum ne na tambaya take cemin wai ai har sunje neman izini a girei yarinyar take. Ran lubna se tafasa yakeyi tace shikenan nagode,miher tace bro manosh yayi tfy yau kuma zai jima dan haka ki shirya yana dawowa sekizo,tace insha Allah miher nagode sannan sukayi sallama. Hankalin lubna in yayi dubu ya tashi setace wlh dolene in fara shige shige gun malamai dan samo kan manosh kota halin k'ak'a koma wacece wannan yarinyar zan ganta ai kuma zanga dame tafini,kyaune ko gashi ko hasken fata ko kuma dukiya koma dai menene zakici ubanki wlh tunda kika shiga tsakanina da masoyina. Manosh yana isa ya kira mum nashi sannan ya kira maryam,yace aunt na iso lfy,kunya taji sosai dan bata kirashiba tace to Alhamdulillah,yace baki damu danibako aunt,gashi ko kirana bakiyiba,tace am sorry bahaka bane,yace to menene,tace kayi hakuri zan gyara,dad'i yaji sosai yace toba komai I LUV U,kunya taji tayi shuru tana jinsa,ya kira sunan aunt,tace na'am,yace bakiji abinda nace bane,tace "me too" tare da katse wayan dan kunya dataji, shi kuwa dariya yakeyi yanaji sonta na k'aruwa a ransa... [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNT'YN YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd 11-12 Auntyn yarane take koya musu karatu a cikin gidansu dan har black bord babanta ya mata dan koyar da yara,gidan nasu d'an daidaine ba wani gidan masu hali bane,amma dai koda yaushe gidan tass yake. Tsakar gidan flour ne na silinti se'a shinfid'a katuwar taburma ana karatu. Marwan ne a hanya zuwa girei duba abokinsa da bayaida lfy,ya kira manosh a waya amma yayita ringing bai d'aukaba. Bayan yaje sund'an tab'a hirane se yayi mishi sallama ya kama hanyan koma,kiran salla yaji muryan k'aramin yaro nan danan imani ya k'ara ratsa marwan yace kai bari dai na k'arasa kawai nayi la'asar tunda an kira. Har gun masallacin ya isa ya paka motarshi ta gefe seya hango wani yara,ya k'ara gun masallacin yayimasa sallama yaron ya amsa tare da cewa salla zakayi,marwan yace eh wanene ya kira sallah yanzu,yaron yace nine,marwan yace masha Allah amma kana da murya mai dad'i menene sunanka,yace sunana ABDALLAH,marwan yace suna mai dad'i gaskya inaso mu kulla abota dakai,abdallah yace to shikenan ya sunanka,yace marwan,abdallah yace kaima sunanka da dad'i ga buta kayi alwala a nan girei kake,yace a'a ina jimetane,abdallah yace ayyah nikam anan girei nake kagama gidanmu can ba nisa,marwan yace to ashe zan dinga zuwa kana koyamin k'ira'a,dariya abdallah yayi yace sedai kaje gun Auntyn yara ta koya maka itace malamata,yace waye kuma Auntyn yara,abdallah yace itace malamata kokuma ince malamar yaran unguwannan harma dana nesa. Marwan yace bari dai muyi sallah ko semuyi hira,yace to sega yara sun fito daga gidansu maryam mata sun wuce gida maza kuma sun nufi masallaci. Kowannen sallama yayiwa 'yan masallacin sanan suka hauyin alwala,marwan yana ta ganinsu abun ya burgeshi sosai. "Bayan an idar ne marwan yace da abdal muje can muyi hira se in tafi. Bayan sun k'arasane yace ina jinka kagani na mijine kuma babba kanaga auntyn yaran zata koya min karatun, yace a'a kam kayi girma sedai in zaka dinga zuwa masallacinnan daga magrib zuwa isha kullum ana karatu da kuma litattafai masu yawa. Dad'in hirannasu sosai marwan yakeji yace to yaran can da suka fito daga gidancan fa kodai koyarwa ake acan,yace eh auntyn yara ce mai koyarwa bayan azahar zuwa la'asar,biyanta akeyi,abdallah yace a'a fisabilillah dai ai auntyn yara kowa natane kuma kowa ya santa babba da yaro babu wanda zai iya gaya maka halinta don ta cika goma cip cip. Dariya sosai marwan yayi yace matar aurece,abdallah yace a'a budurwace kuma kuma kasan me,marwan yace a'a,abdallah yace auntyn yara macece mai tarin ilimin addini dana boko gata da son mutane sam bata da kyamar d'an adam aduk yadda ta ganshi,kuma tana son taimakon dan adam,gata kyakkyawa sosai amma kuma 'yar karamace. Dariya sosai marwan yayi yace kai abdallah duk ita kad'ai kodai ka kara da nakane,yace wlh da gaske ko inkirata ku gaisa ne,marwan yace a'a kace mata me? abdallah yace ince mata tazo abokina yana so su gaisa,marwan yace zata fito,yace eh zata fito bari inje. Maryam tana sanye da aldoguwar riga jah ta nad'a gyalen akanta tana k'okarin fitowa,se abdallah yayi sallama ta amsa tare da cewa abdalla rashida fa ta shirya kuwa,abdallah yace wlh ban saniba zaku fitane,tace eh zamuje jimeta duba zahida ba lfy,yace to muje dama gunki nazo zaku gaisa da abokina. Mamaki ya kama maryam tace aboki kuma,yace eh,tace to muje se suka fito a tare. Marwan ya zubawa budurwan kallo har suka k'araso tayi mishi sallama ya amsa sannan suka gaisa,tace to abdallah mun gaisa nizan wuce,abdllah yace to ai shima jimeta zaije abokina ka sauketa dan Allah. Marwan yace tobakomai abokina auntyn yara muje,batayi mamakin jin sunata a bakin marwanba,se tace a'a wlh da wata k'awata zamu tafi yanzuma gidansu zanbi kafin mu wuce,abdallah yace abokina yayatace bari naje na kirata yana juyawa sema ga rashidan tahowa,yace kama ganta,murmushi maryam tayi tace daga yin aboki se kuma a d'aura mishi nauyi,abdallah yace to ai hanyanku d'aya,marwan yace sosai kuwa kuma ai zan samu lada ko,abdallah yace kwarai lokacin rashida ta iso suka gaisa sannan abdallah yayi mishi sallama har ya juy se kuma yace abokina bani numbern wayanka,marwan yana fad'a mishi shi kuwa yana sawa a wayansa sannan yace nagode sena kiraka,marwan yace tonagode sena sake zuwa. Rashida ta kaftawa maryam ido akan ta zauna a gaba,badan tasoba hakata zauna ita kuma rashida tana baya suka tafi. Koda suka fara tfy babu wanda yayi magana acikinsu,se marwan yace auntyn yara ina zakuje a cikin jimeta,tace gurin NTA ,yace ok gaskya abdallah yarone mai hankali yaron ya shiga raina sosai wlh,maryam tace mungode,yace yace inzo zaki dinga koyamin karatu,tayi murmushi tace toba damuwa seka zo,marwan ya d'auki wayanshi yace hello Majid yane,majid yace ka dawone,yace na kusa isowa dai,yace ok idan ka shigo kamin waya,marwan yace ok sannan ya katse wayan. Babu wanda ya k'ara cewa komai har suka iso har gidan,sannan suka fito tare da cewa mun gode fa,yace bakomai wlh kozan dawo in maidakune,maryam tace a'a za'a mai damu mungode sosai,yace to shikenan nima na gode. Har seda suka shige gidan sannan yabar gurin yanata yaba kyau da nutsuwan maryam da kuma halaiyarta da abdallah ya gaya mishi. Hira sosai sukayi da zahida sunata nishad'i gwanin sha'awa,zahida tace samira tacemin sunje mubi ko,maryam tace eh wlh se gobe zasu dawo, zahida tace ku tashi muje YAKUBU SHOPPING LPAZA zan sayi always da kuma kayan ado sun k'are,rashida tace ashe dai kin warke to muje kar muyi dare. "Shopping sukayi dukkansu d'an daidai sedai maryam tayiwa yaranta tsaraba. Harsunzo fita se maryam taga key wata ya fad'i daga cikin bag nata batare data saniba, da sauri ta d'auka ta bita hargun motar k'irar HENESI tace 'yar'uwa kin yarda key d'inki,yarinyar ta juya suka had'a ido ta karb'a tare da cewa ayya nagode sosai kuma kinga keyn motatace wlh bansan ya fad'iba nagode sosai,maryam tace karkimin godiya 'yar'uwa inaso kema ki taimaki mutane uku a rayuwarki sannan suma kice su taimaki wasu ukun,murmushi tayi tace to shikenan ya sunanki,tace sunana maryam,tace eyyah ni kuma sunana LUBNA,tace ok sannu lubna se anjuma,lubna tace dan Allah bani number ki mana,nan taba maryam wayanta tasa mata number sannan tayi flashin,maryam tace zanyi saving lubna ko,lubna tace eh nagode sannan ta wuce gunsu zahida suka tafi. [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd 13-14 maryam basu koma gidansu zahida dan gudun kar dare yayi musu daga nan sukayi sallama har suna k'ok'arin tare mota sega drivern manosh yayi parking tare da fitowa suka gaisa se yace oga ne yace inzo in maidaku gida. Murmushi maryam tayi tace to mungode,har zata bud'e gaba seyace no madam ku zauna a baya bakomai,batasoba amma haka suka zauna ya kaisu har gida sannan suka mishi godiya. Marwan ne ya kira abdallah a waya suna hira yake tambayarshi cewa auntyn yara tana da saurayine? Abdallah yace eh akwai dai masu sonta dewa amma babu wanda take tsayawa dashi gaskya,meyasa to,yace wlh ban saniba nidai ban tab'a ganin tana hira da waniba a matsayin saurayi kana sontane? Marwan yace aboki kashe wayan zan kiraka kaji,abdallah yace to tare da kashewa. "Marwan ya d'auki call d'in manosh yace captain busy busy nakiraka d'azu dan naje girei dama in tambayeka akan apple ne kuma inje mu gaisa se kuma baka d'aukaba. Manosh yace wlh ka bari kawai aikin namu ne se'a hankali harka dawo kenan,eh tun d'azuma,manosh yace ai kuwa gidansu ba b'oyayye bane a girei sunanta maryam amma amfi saninta da auntyn yara. K'irjin marwan ya buga yace auntyn yara,manosh yace eh wlh tanada son yarane shiyasa ake kiranta da hakan. Marwan yace ok sedai inka dawo semuje kawai,yace to shikenan sannan sukaci gaba da hiransu. Bayan sun gamane ya sake kiran abdallah yace abdallah kabar wannan maganan auntyn yaran kaji,abdallah yace meyasa,marwan ya bashi lbr tas akan maryam da manosh abokinsa ko kuma ince amininsa. Abdallah baiji dad'iba dan ayau kawai amma se yaji yana son marwan kuma yanaso su kasance tare da auntyn yara. Marwan yace ya kayi shuru,yace bakomai wlh naso had'aka da aintyn yara abokina kana da kirki sosai,marwan yayi murmushi yace karka damu abokina shiyafi dacewa da auntyn yara danshi bai tab'a furtawa mace kalmar soba se akanta,ni kuwa nayi sosayya abaya har an gama komai da komai na auranmu ana saura 2weeks tayi zazzab'i na kwana d'aya shikenan ta tafi ta barni,tun lokacin ban kara furtawa wata mace kalmar soba shekara guda kenan. Lbrn yabawa abdallah tausayi yace Allah ya jikanta da rahama,yace ameen. Abdallah yace amma abokina dan Allah in tambayeka mana,marwan yace ina jinka,abdallah yace kana son auntyn yara? Marwan yace eh shiyasama na kiraka dan inji ko an mata miji,to ashe itace aminina yake bamu lbrnta kaga gara danyi shuru dan haka maganar ya zama sirri a tsakaninmu kuma kagayawa auntyn yara koda mun sake had'uwa wataran karta nuna mun tab'a had'uwa kaji? Abdallah yace Allah sarki abokina insha Allah zan gaya mata kasan me,yace a'a,yace da har ina tunani idan airenku ya tashi da auntyn yara zakayi mana walima namu na MAZA wanda zanyi karatu sosai dan yadda nake son auntyn yara kuma k'awar yayat ce. Dariya sosai marwan yayi yace to ai yanzuma bai b'aciba za'ayi insha Allah ka zauna cikin shiri kawai zan gayawa abokina ayi mana waliman mazan kaji,dad'i abdallah yaji yace wlh kana da kirki nagode,marwan yace nima na gode seda safe. Maryam tana kwance a d'akinta abdallah ya kirata ya gaya mata komai. Mamaki tayi sosai tace eyyah dama shine abokinsu d'ayan kenan da suka gayamin bai samu zuwaba, abdallah yace eh shine,tace bakomai abdallah nagode kaji ka gaisheshi,yace zaiji sannan tace yau dai barita kira manosh. "Ringing d'aya ya d'auka tare da cewa slm aunt,yadda yake kiranta yana mata dad'i sosai ta amsa wslm ina wuni,yace lfy sannan ya katse ya sake kiranta. Ta d'auka tana murmushi tace ya aiki,yace alhamdulillah yasu mama,tace lfyansu lau min godefa kasa an dawo damu gida,yace bana son godiyanki aunt,meyasa bakicemin zaki fitaba,tace bakomai,yace to daga yau idan zakije wani wuri kidinga gayamin pls,tace to shikenan,yace me kokeyi aunt,bakomai,yace zakiyi bacci kenan,tace eh,yace bazaki min hiraba,mirmushi tayi tace name kenan,yace ina kikaje yau,tace munje duba k'awatace zahida bata da lfy,yace eyyah sorry Allah ya bata lfy ta ina take a jimeta,nan dai ta mishi kwatance yace ok nasan gurin ai akwai wani abokin dad nawa acan,tace eyyah,yace daganan kuma se kukayi ina,tace YAKUBU SHOPPING PLAZA,yace me kika saya kuma dawa kuka had'u mutane nawa suka tsaidake? Dariya tayi yana mirmushi yace "yes tell me" tace babu wanda ya tsaidamu sannan mun had'u da wata sunanta lubna, uace lubna? Tace eh nan dai ta bashi lbrn,yace ok akwai wata lubna dana sanine k'anwan marwan abokina da bai samu zuwaba ita k'awar miher sista nace shiyasa na sake tambayanki,tace eyyah tama bani number"nta. Yace hakan yana da kyau ai Allah yasa ita ce,tace ameen. Sunanta ya sake kira aunt,tace na'am,yace kin iya amsawa da NA'AM d'innan kamar ke kika k'irk'iri kalmar,dariya tayi sannan yace me burinki na gaba aunt,shuru tayi batace komaiba,yace tambayarki nakeyi fa,tace karatu,yace ehen seme,shuru tayi seyace aure,tace uhm,dariya yayi yace mezai hana kiyi auren sekiyi karatun a d'akin mijinki,kasa cewa komai tayi dan kinya,yace aunt bakice komaiba,tace tome zance,yace kice eh zanyi aure se incigaba da karatuna,dariya tayi sosai shima ya tayata,tace hmm,yace "whats is hmm?' Tace bakomai, yace aunt ki bari muyi aure sekiyi karatu kinji inaga hakan zaifi koh,batace komaiba,yace kokinaga bazan yadda kiyi karatubane,sisterna miher tana karatu 100 level kima majid ne zai aureta amma dole tayi karatu dokan dana kafawa majid kenan kuma ya amince,so kinga bakida matsala dani indai akan karatune aunt. Dad'i sosai taji tace to zanyi tunani akai,yace ok my apple kiyi tinani tare da shawara "i will be waiting okay?"tace ok nizan kwanta,yace to aunt ma'assalam,tace bissalam tare da katse wayar tana mai farin ciki tare da k'ara jin sonshi na ratsata. Washe gari maryam ta shirya taje gun wata makwabciyansu mai suna Hajiya iya. Tsuhuwace mai kirki dason mutane kowa yasanta a unguwan,kuma kowa yasan yadda take k'aunar maryam sosai ta d'auketa kamar jikanta. Gata kala kala takeyiwa maryam dayake tana da d'a a yola

Chapter 2 of 17