Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
d'aya ya bata ta karb'a tare dayin godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha. Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka _slm 2u my aunt_ _bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan inji sanyi a raina_. Yours miher.... Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da _thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode* Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee... Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in gudu yakeyi kamar zai tashi sama.. Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan taji zuwan mota. Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba. Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi. Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy? Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah. Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?... Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza. Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai kuwa. Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 Adon gari group*❤)*❤)*❤)* 41-42 Hajiya khadija ce zaune agidansu maryam tanata kuka,maman maryam se hak'uri take bata,tace yanzu fisabilillahi me maryam tayi haka dahar za'a d'auketa a rabata da iyayenta,se kuma ta sake fashewa da kuka mamace taketa bata hak'uri. Auntyn yara ta dubi tsohon dade rik'e da hannunta yana tab'a inda aka harb'etan da hannayensa,cikin ikon Allah sam bataji zafiba. Se alokacin da take kallon tsohonne seta tuna cewa wannan shine wannana tsoho mai farfad'iyan data tab'a taimakawa lokacin daya fad'i akan titi rananne farkon had'uwanta da *peach* shiyasa bata bance fiskanshiba sam. Murmushi tayi tace baba,yace na'an maryam kin ganeni ashe,tace sosaima kuwa meya kawoka nan bab ya jikinka? Murmushi yayi yace jiki da sauk'i maryam tun bayan rabuwana dake na taimakawa mutane hud'u yanzu kece ta biyar,tace eyyah baba Allah ya saka da alkhairi,dama a nan jihar bauchi kakene? A'a a jihar adamawa nake ca *hong* ayyah baba a hong kake dama toya akayi kazo nan? Maryam saboda ke nazo danaga kina cikin damuwa kuma dama nace kece mutum ta biyar dazan taimakawa shiyasa nazo. Har zatayi magana ya katseta da cewa maryam ki saurari abinda zan gayamiki da kyau,tace to baba ina jinka amma akwai wanda ya kamata mu had'u dashi nasan kuma sun iso yanzu gashi sun karb'e wayana nasan zaiyita nemana baba. Yaga dai ta damu sosai seyace karki damu zan kaiki har inda suke kiban hankalinki anan maryam,tace to baba ina jinka yare da kallon hannunta daya d'aure mata bayan wasu abubuwa dayayi wanda basan meneneba. Baba ya kalli maryam yace nasan zaki gayawa mutane cewa *lubna ce* tasa akayi miki haka ko? Tace eh baba,yace to karki gayawa kowa maryam,cikin mamaki tace meyasa amma dolene in gayawa iyayena ai,baba yace harta iyayennaki kada ki gaya musu komai kuma bana so ki tabbayeni dalili indai har kin yadda dani kinsan bazan cutar dakeba to rashin gayawa kowa shine afi akhairi a gareki maryam. Mamaki sosai ya baiyana a fiskar maryam tace to baba idan ban fad'a an d'auki matakiba ai zata sake bin wata hanyan,yace bazata sakeba maryam maganar gaskya niba mutum bane kamar ke maryam ni alja....bai k'arasaba maryam ta tsorata sosai tare da mik'ewa tana komawa dabaya dukda dai tasan batasan kota inda zatabiba. Baba ya mik'e yace maryam karkiji tsorona ki d'aukeni kamar kina tare da mahaifinkine,dan Allah karki sanar da kowa cewa lubna ce ta miki haka kigayawa kowa cewa su saddam ne,sannan yanzu haka bawan Allah can yana can hannu sojojin zasu gana kece zaki iya dakatar dasu tawajen gayamusu cewa shi bayida hannu taimakonki yake da niyanyi shine suka miki rauni kinji maryam? Cikin rawan jiki dama tunda taji shiba mutum bane taketa add'ua,setace to baba dan Allah inaso in koma gida,yace ba gidaba maryam karki rud'e ki nitsu kinji,kibi wannan hanyan gabanki zaki samesu nina tafi. Yana kaiwa nan ya b'ace,gudu maryam tasa tare da kiran sunan manosh...! Kamar daga sama manosh yaji muryanta ta gefensu da sauri ya juya ya nufin gun da gudu yana apple, "where are you?" Can ya hangota tanata gudu tana juya bayanta har suka iso gun juna. Kallon juna suka tsayayi yayinda take ta waige waige,manosh ya lura da cewa bata cikin hayyacinta sam. Sunanta ya kira aunt? Da sauri ta juyo se'a sannan ne ta dawo hayyacinta nan ta tsaya kallonshi cikin so da kuma tausayin yadda taga ya zama. Sunanshi ta kira tare da murmushi tace manosh,shima murmushin yayi tare da k'are mata kallo da wuri yakai hannunshi gurin hannunta da aka harbeta sannan ya juya yana kallonta cikin tuhuma. Ita kanta tasan dalilin kallon nan tace wani bawan allah na hango shine yayi saurin d'aukeni ya kuma taimakamin sosai shinema ya d'aure min hannun. Manosh yace yarone ko tsoho? Har cikin ido take kallonshi ta kuma gane me yakenufi wato yana kishi wani ya tab'a jikinta kenan. Tace tsohone manosh kamar mahaifina yake kuma wlh ba wani tab'a jikina sosai yayiba abun nashi daban al'ajabi kuma sam bana jin wani ciwo yanzu,murmushi yayi mata dan yasan sam maryam bazata mishi k'aryaba ya yadda da ita har cikin zuciyarshi. Matsowa yayi kusa da ita gab kad'anne a tsakaninsu kunya sosai taji sannan ya mata kwarjini sosai ta yadda bazata iya had'a ido dashiba. Hannunshi ya mik'a mata mana'a tazo su tafi,amma sam tak'i bada hannunta tanata jan himar nata da d'ayan hannun. Murmushi yayi yace Alhamdulillah "i'm so happy to see you apple" kanta a sunkuye tace "me too" sannan ya d'auki wayanshi ya kira babanta yace baba mun sameta lfyanta k'alau gatanan yanzu zau taho,maryam ta karb'i wayan tana kallonshi tare dayin dariya tasa a kunnenta tace hello baba,yace alhamdulillah 'yar baba Allah ya amsa addu'armu barka 'yata,mirmushi tayi wanda yaji dad'i sosai tace baba ina mama,nan mama ta karb'i wayan tace maryam Alhamdulillah bari naje kichin na dafa miki abinci 'yar albarka,dariya tayi tace ina sonki mamat semun dawo na kuma gode sosai da addu'oinku. Bayan ta gamane ya kira miher da mum nashi nanma suka gaisa sannan ya kira su marwan suka sakegaisawa daidai lokacin suka iso gun otansu manosh d'in. Maryam ta hango bawan Allah yana ta zubar da jini a k'afanshi yayinda wani yake gyara mishi k'afa. Da sauri tace peach me kuka mishi haka,wlh sam bayi da laifi kokad'an dan shinema wadda yake kiran baba a waya,sannan taimakona yakeyi sam bayida hannu a ciki dan Allah ku rabu dashi,manosh yace apple pls karkisa baki a ciki,tace pls manosh ka saurareni wlh..ya isa apple,yana da hannu mana tunda ya biyosu kuma ai shima yasan da zance sacekin inhar da gaske yakeyi meyasa bai sanar da 'yan sandaba. Shiru maryam tayi dan yadda taga ran manosh ya b'aci cikin k'ank'anin lokaci da sauri tabar gun ta koma jikin motarsu tana zubda kwallah. Manosh yabi bayanta tare da bud'e mata gaban motan yace shiga mu tafi,ba musu ta shiga ta zauna daga tsakiya tana ci gaba da kukanta wanda babu sauti hawaye awai kake hangowa yana zuba. Hankalinsa ya tashi nan ya shigo gaban shima yana zaune tagun k'ofa driver a ya shiga maryam tana tsakiyansu sannan sauran suka tattaro tarkacen su saddam da wannan mutumin a bayan motan suka kama hanyan. Maryam ta share kwallanta kanta a sunkuye dan gabad'aya a takure take. Manosh yace da driver idan kaga wani shop ka tsaya agun,yace ok sir. Maryam ya kalla yace apple me zakici,tace ni banason komai,yasan cewa fushi tayi yace dolene kici wani abu dan kina jin yunwa sosai,tace ni banajin yunwa muje kawai,nan driver ya tsaya suka fita shida manosh nad'an wasu lokuta sannan suka dawo amma drivern bai shigo motaba. "Anosh yace apple karb'a kici,tayi kamar bata jishiba,ya sake cewa bana so mu fara haka dake pls apple ki barni inyi aikina inyaso zan barshi daga baya amma ba yanzuba kinji? Ko kallonshi batayiba tace amma nace maka babu hannunshi fa,yace yes aunt i know bincike kawai zanyi akan wanda yasasu kuma shi yasan kowanene,tace nima na sani ai saddam sunanshi kafin kuzo suka gudu,yace eh saddam dinma akwai wanda ya sashi ai,tace pls peach indai kana sona to kawai kabar maganan tunda Allah yasa nadawo nina yafe wlh,murmushi yayi yace ok apple eat first okey,tace nifa bazanci komaiba seka janye,yace tona janye karb'i apple d'in kici pls,karb'a tayi yana mata murmushi sannan shima ya fara cin nashi ita kuwa sam ta kasa ci tana rike dashi. Ta lura da cewa yana kallonta dan haka tace nifa bazan iya cin komai ayanzuba senaje gida,bakinshi ya matso dashi daidai kunnenta yace "kinaso inyi fushi dake koh?" Kunya taji tace wlh bazan iya cin komaiba kayi hakuri,shuru yayi bai sake ce mata komaiba sunata tfy har suka iso *yola*. Dad'i sosai maryam taji suka wuce da bawan Allah can barac nasu inda ya mik'awa manosh wayan maryam yave lokacin da take wayane ya karb'e wayan,bayan ya ajiye wayan shine na d'auke. Manosh ya karb'a sannan yazo suka wuce girei itadai maryam tanata tausayawa mutumin can dasuka kama,ahanyane manosh ya bata wayanta,tanata godiya tace a ina ka samo dan ai wayan tana hannun saddam ne,nan yagaya mata komai daidai lokacin suka iso k'ofar gidansu maryam a girei... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 matan kwarai grp*💐🌹 43-44 k'ofan gidansu maryam a cike yake da jama'a kowa yana jiran dawowar auntyn yara,koda akaga motan sojoji ya tsaya da sauri aka nufo motar anata hamdalah da mata murna sosai,musamman abdallah hannu ya d'aga sama yanayiwa Allah godiya. Su manosh suna tsaye daga waje yanaganawa da jama'a,ita kuwa ta wuce gida dasu rash da sameera daidai sauran jama'a. Maryam ta rungume mahaifiyarta tana murmushi bayan nan ta zauna bada lbrn abinda ya faru amma sam tace batasan bayasa a mata hakanba,nan dai kowa yayita tofa albarkacin bakinsa. Can akajiyo hayani a waje nan take kowa ya fito,yarane da almajirai suketa tsalle da wak'a. _Alhamdulillah auntyn yara ta dawo,ta bayya,Allah mungode maka daka dawo mana da auntyn mu lfy lau_. Hahahah sunatayi manosh ya nufin gurin se zuba musu kud'i yaketayi yara se k'ara murya sukeyi suna d'iban kud'i yah ibrahim ne yazo ya koresu yace toya isa haka mungode kowa ya wuce gida,nan suka watse suna murna. Dariya manosh da ibrahim sukayi sanan suka wuce gunsu baba suna magana,maryam ta wuce band'aki tayi wanka tare da d'auro alwala tazo tayi sallolinta sannan taci abinci sosai dan dama tana jin yunwa. Bayan ta koshine tace mama da sauran wani abincinne zan zubawa manosh a kula ne,mama tace eh akwai,nan taje ta had'o a kula ta kawowa maryam tace gashi,godiya tayi tare da mik'ewa taje palon babanta tare da sallama suna zaune da yah ibrahim da kuma abokinsa soja wato yusuf maryam ta ajiye musu abinci sannan ta koma ta d'auko plate da kuwa ruwan sanyi tare da exotic d'in da hajiya khadija ta kawo musu. Bayan ta fitane yah ibrahim ya zuba musu ba laifi kuwa sunci sosai sannan sukace zasu tafi. Maman maryam tazo suka gaisa sannan ta musu godiya,manosh ya kira maryam ya sanar da ita cewa zasu tafi ta kwanta ta huta,godiya sosai ta mishi yare da jajdada mishi cewa karya cutar da bawan Alla can,murmushi yace yace "yes my princess"tambayoyi kawai zai amsamin nayi miki alk'awarin bazan cutar dashiba matuk'ar zai amsamin tambayoyin da nake buk'ata agunshi. Dad'i taji sosai tace yaushe zaka sake zuwa? Yace se jibi akwai wani abune,tace yes ina son *flower* murmushi yayi yace angama aunt gobe mum da miher zasuzo zan aikota dame kuma kike so? Tace da *peach d'inah*,dariya yayi itama haka sannan suka tafi. Yah ibrahim ya shigo gida sunata hira dasu rash daga k'arshe suka tafi..... Washe gari da safesartuday ne,dan haka su marwan suka da safe sukayiwa maryam barka sannan suka d'anyi hira suka tafi. Da misalin 11:00am mum d'in manosh da miher sukazo nanma dai suka zauna kad'an,miher dasu maryam sunata hira a d'akinsu yayinda ta mik'a mata flowern da bro nata ya bayar akawowa marya,dad'i sosai taji tare da lumshe ido su miher da rash se dariya sukeyi mata suna zolayarta. Awa d'aya su miher sukayi sannan suka tafi sesu zahida da amina sukazo,bak'idai sosai suketa zuwa da abin arziki babu wanda yake zuwa empty. Hajiya iya ce zaune a gaban maryam tanata kuka tana rungume da maryam,maryam da mamanta duk kansu ya d'aure da irin kukan hajiya iya. Amma se suka d'auka kodon k'aunarda takeyiwa maryam ne. Saddam ne zaune a d'akinsa ya kira lubna a waya yace kina ina,tace ina gida me nakeji wai maryam ta koma gida? Yace kizo mu had'u dan muyi magana,tace ok amma bazan fito da motaba zanzo yanzu semu had'u,yace ok. Babu wani b'ata lokaci lubna ta shirya cikin after dress black tahau nape se daidai gate d'in gg ta kira saddam a waya tace ina daidai gg,yace wlh motata tayi pashi bamma bar gida ko zaki k'arasone semu fito tare,bata soba dai amma dan bataso asirinta ya taunu setace to gashi kayiwa mai napen kwatance. Nan suka d'auki hanya har inda saddam ya kwatanta musu,se kuwa gashi ya fito daga d'akinsu yazo yabiya mata kud'in dan ita batada canji. Bayan mai nape ya tafine saddam yace ki shigo mana kar wani wanda ya sanki ya ganki anan kinga se'a ganki kamar mutumiyar banza,haka tabishi a baya suka shiga sannan ya kulle k'ofan ta key,lubna data zauna aiseta mik'e tare da cewa ya kuma ka rufe kofan saddam? Take ya canja ido yace ashe ki muguwace munafuka ban saniba,kece kike gayawa maryam inda muke kaita dan azo a kamani in fita daga rayuwarki ko lubna,hakazakimin,wlh to bazan barki hakaba sena lalata miki rayuwarki kafin in bada kaina. Kuka lubna ta farayi tace haba saddam wlh bansan komai akan abinda kake fad'aba taya za'ayi in kira lubna kuma,dan Allah karkamin haka saddam wlh karyane duk wanda ya gayamaka karya yakeyi wlh,nan dai lubna ta rikice ta fara kuka. Shuru sadda yayi yace kiyi hakuri lubna na d'auka koda gaskene wlh,bakomai share hawayenki mu tafi domin yanzu ni suke nema abokina ya yaudareni wlh amma zanyi maganinshi baisan wayenibane shiyasa,juice ya zuba mata da sauri ta karb'a tasha batare dayin wani tunaniba ta shanye tas dama datajin k'ishi. Shi kuwa saddam wayo ya mata dan kartayi kuka ta tona mishi asiri dan haka ya juba magani a ciki ai kuwa take lubna ta fara fita hayyacinta,saddam kuwa ya tashi ya fara cire kayan jikinshi tas tana iya ganinsa bakomai a jikin,nan hankalinta ya tashi tana k'okarin tashi amma ina seta fad'a kan katifarshi kamar macacciya,da sauri ya rabata da kayan jikinta tas se lashe baki yakeyi kamar tsohon maye,yahau shafeta tare da wani irin gigicewa da ganin kyakkyawar suranta. Cikin k'ank'anin lokaci ya rabata da budurcinta gashi ya kwashi romo sosai danshi a tunaninshi an dad'e da sanin lubna saboda irin shigan dayaga takeyi. Bayan ya gamsune yayi saurin watsa ruwa ya shirya tare da kwashe kud'ad'en dake jakarta ya d'auki akwatinsa ya gudu da motarshi. Koda lubna ta dawo hayyacinta kuka sosai takeyi tare da tsinewa saddam albarka tana tuna yanzu shikenan ya gama b'ata mata rayuwa ya zatayi kenan? Miher ce kawai ta fad'o mata arai harta d'auki wayarta zata kirata kuma seta tuna cewa koda yaushe miher suna tare da majid kuma tasan dole miher zata fad'a wanda idan bro marwan yaji shikenan nata ya k'are. Kuka sosai lubna takeyi gashi jikinta duk jini haka ta rasa yadda zatayi kawai se maryam ta fad'o mata a rai data tuna da abinda wani tsoho ya gaya mata akan maryam,ai kawai seta kira maryam. Lokacin su maryam sun shigo jimeta dasu yah ibrahim dasu sameera,mamaki tayi sosai da ganin kiran lubna,seta d'auka hello,lubna cikin miryan kuka take magana hello maryam dan Allah ki gafarce akan abinda na miki nasan kinsan komai amma dan Allah ki rufamin asiri dan yanzu hakama Allah ya saka miki akan abinda na miki maryam sadda ya cuceni yamin fyad'e bazan iya kiran kowaba seke,saboda abunda wani tsoho ya gayamin dan Allah maryam ki taimaka kizo saddam ya gudu yanzu haka ina d'akinsane a bayan gg idan aka sani za'a kasheni a gida musamman bro marwan maryam dan Allah ki rufamin asiri. Shuru maryam tayi ta kasa cewa komai,kuma batasan ya za'yi tabar su rash taje ita kad'aiba. Nan tace ok inazuwa tare da kashe wayar, tace yah ibrahim dan Allah ku saukeni anan ku shiga kasuwan rash idan naje na gama zan gaya muku inda nake sumu tafi,yah ibrahim yace to shikenan sannan ta sauka tahau nape se bayan gg,nan dai ta kira lubna tayi musu kwatance suka k'arasa har gun sannan ta sallameshi ya tafi,ta sake kiran lubna nan taji k'aran wayan a kofar gabanta,da sallama ta shiga taga lubna a kwance cikin jini,tsorata sosai tayi tare da dasa key a kofan tana ta addu'a,ta k'arasa ta taimaka mata ta mik'e ta rakata toilet dake kicin d'akin sannan ta tsaya daga bakin kofa tana mamakin abinda ya faru. Wayartace tayi k'ara ta d'auka hellow peach,yace apple nah kina ina,k'irjinta ya buga tace ina jimeta munzo sayayyane dasu yah ibrahim idan muka gama zan sake kiranka muna cikin kasuwane,yace ok badamuwa,tace ina kake? Yace muna kan aiki yanzu zamuje inda saddam yake zaune ne mu kamashi,tace a ina kuka sameshi peach,yace wai yana bayan gg yanzu haka muna hanyane,tsoro ya kama maryam tace to shikenan sena kiraka,yace ok byee. Maryam tace lubna fito su manosh suna hanyan zuwa nan domin sun samu lbrn cewa saddam yana nan karsuzo su tarar damu anan gashi na mishi karyam idan ya samemu anan tofa ina cikin tahin hankali,lubna take zawo ya kamata haka tayitayi a toilet d'in tana kuka,ita kuwa maryam se kallon windo takeyi tare da k'ara rufe ko ina a d'akin,daidai lubna ta fito tasa kayanta da sauri jikinta se b'ari yakeyi tausayinta ya kama maryam har seda tayi kwalla,seta d'aga zanin gadon taje ta wanke da ruwa tazo ta bazashi akan gadon sannan maryam ta kwashe mata wayanta da sauran kayan makeup nata tasa a bag na lubnan suka yunk'uro zasu fita kenan sega motar su manosh,aida sauri suka wuce toilet sunata addu'a ita kuka lubna zawone ya sake kamata haka tayitayi tana hawaye sosai dan yadda take tsoron bro marwan barema kuma aji cewa an mata fyad'e ne hmmmm... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁 Writren by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 khafeelat abdulhafis*❤)* 45-46 tsayawar mutar sukaji,ba lubna kad'aiba ba harta maryam a tsorace take,gashi tayiwa manosh karyan cewa tana kasuwa kuma yanzu idan ya ganta a d'akin saddam kimarta zai ragu a idonsa addu'anma dakyar take iyayi,ita kuwa lubna idan ka gantama dole kayi kwalla dan tausayinta. Muryan manosh sukajiyo yana cewa ya kuma naga padlock a k'ofan,hakan yana nufin saddam ya sake tserewa kenan?yusuf yace ai mu b'alla kofan kawai k'ila sawa yayi a rufeshi ta baya dan muyi tunanin bayanan. Maryam da lubna aise suka tsure suna *innalillahi wa inna ilaihirraji'un* jikinsu se rawa yakeyi. Bawan Allah ne yace duk yadda akayi saddam guduwa yayi baya ciki domin banga motarshiba lallai yasan za'azo nemanshi shiyasa ya gudu,manosh yace ina kenan kake tunanin zai tafi?yace numan zai koma inda yakai maryam,wanine yazo wucewa manosh yace kai ina wanda yake zama anan?mutumin yace d'azu ya fita da kayansa dewa ya zuba a mota da gudu yabar nan. Manosh yace muje yusuf,nan danan sukabi bayan saddam gudu sosai manosh yakeyi da mota. Basu maryam kad'aiba,harta ni *sad-nas* seda nace *alhamdulillah* wani irin ajiyar zuciya maryam ta sauke tare da k'arayin godiya wa ALLAH sannan suka fito. Lubna tace kwad'o fa naji sunce ansa ajikin k'ofan to taya za'ayi mufita kenan,maryam ma abun ya bata mamaki tace towaya mana kwad'o kenan? Gwada bud'e kofar tayi cikin mamaki taga kofan ya bud'u,kallon juna sukatsayiyi ita da lubna dukkansu mamakine ya bayya a fuskarsu,maryam tace shikenan gaskya muyi hanzarin barin nan,dan nima su yah ibrahim suna jirana. Lubna ta rik'o hannunta tace kije maryam niki barni anan dan bazan koma gidaba wlh bro marwan zai kasheni. Maryam tace ki dena fad'a haka lubna aiba a son ranki bane fyad'e aka miki kawai ki fad'a musu gaskya,lubana tace wlh na gwammace insha wani abun in mutu amma sam nikam bazan iya komawa gidaba maryam bazaki ganebane,ba'asan ina da alak'a da saddamba,idan kuma aka sani to za'amin kallon mutumiyar banza za'ace dama mun saba iskanci dashine baza'a tab'a uarda fyad'e yaminba wlh nan ta fashe da kuka sosai.. Tausayinta ya kama maryam tace toke meya had'aki dashi lubna? Lubna tace wlh kawai yaketa bibiyata waishi yana sona,ni kuma danaga 'yan shaye shayene se tsoro ya kamani dan kar sumin wani abu shiyasa na tsaya muka dai gaisa duk dan mu rabu lfy,so dewa idan maza suna takuramin saddam shine mai taimakona dayake anganshi ana tsoronshi dan ansan zai iyayin kissa ma indai a kainane,kuma babu wanda yasanshi a gidanmu hakan ya bani daman sakewa dashi dan taimakona da yakeyi,nima ina mishi kyautan kud'i sosai amma

Chapter 7 of 17