Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
da bayaninki ba, amma ga wata, me ye KAUNA?" "kauna" wannan itace mai neman tarwasa zuciya lokaci guda." " ya akayi kika san duk wadannan?" ya rubuto "saboda na jiye wa jikina." "idan nace karya kike banyi laifi ba?" "baka yi ba, idan na ji hujja!" "Very good. Zan kira ki yanzu don rubutu ba ya yi. Gabana ya fadi, bana son jin muryansa, firgitani zai yi,ya hargisa tunani na..................... Raki ta fara yi a hankali. "My husband ' nayi dariya, na dauka cikin yar jin kunya na fadi "HELLO" A hankali. "kina ji na?" ya fadi a hankali,nayi murmushi nace 'uhm' Zan baki bayani ta reference to me and you. Meena shi so abu ne mai wuya, idan kin manta bari na fada miki sbd tsananin son da nakeyi miki,ya sanya na zubda hawaye a gabanki,so ya haddasa mini kiyayyar dan uwana,sonki yasa na yiwa iyayena karya. Tsananin son da nake yi miki yasa 'yan uwa suke tausayina. Kauna kuwa itace tasa na lashi takobin dana kawo ki gidana. Kauna ta sanya na zuba miki ido kike yadda kika ga dama kauna ta sanya na danne wa zuciyata sha'awarki har saikin yarda don karin kanki. Meena lkcn da nake sonki banji kunyar kowa ba,haka na tunkareki da maganar,aka gargadeni amma na take maganar iyayena. Har yanzu baki sona,kawai kina dan tausayina ne sbd i believe cewar da kina sona wlhy. Meena da kin faranta mini rai kmr yadda na faranta miki. Anyway wannan kenan. Idan kin gamsu ina iya cewa mu kwana lfy. Nayi shiru kwalla kawai ke zubo mini a kumatu, kina jina meena? Da kyar na iya furta, uhm. Sai da safen kenan? Ya fada a hnkl. Nayi krfn hali, Allah ya kaimu. Daga ji ba haka yaso ba. Na kshe wayar da sauri tare da runtse idanuna tamau. Na jawo wa kaina daman hausawa na ce,baki yasan abinda zai fada,amma bai sanme za a mayar masa ba. Tun daga wannan rana ban kara buga masa waya ba,ko text. Shima haka koda muka hadu washe gari,bai nuna mini wani abu ba,kmr bamu taba wata magana ba. Ni ma kuwa na share. Haka zama yacigaba kullum ba dadi,ni a ganina shi namiji ya daure,sai ni mace na kasa? Na dauko alwashin in zamu kare zamanmu haka bazan taba zuwa inkai kaina ba,kmr yadda yake tunani. Tunanina ya tsaya wuri daya,shima sonda yake mini akwai rauni a ciki,sbd inba haka ba,yadda ya lura na kamu da sonsa,sai yazo muci gaba da rayuwarmu,amma ya basar sai ni? A dalilin yawan tunani da rashin cin abinci ya haddasa mini ciwon ulcer. Ranar da mukayi kwana uku da gana jarabawa ana sauran sati daya bikin ya abdullah,ina kwance daki cikin matsanancin ciwon zuciya,ji nakeyi kmr ta tsage don tsananin azaba. Na mike da kyar na nufi kitchen. Don Allah grace bani ruwa masu sanyi kwarai idan ma akwai wanda ya fara kankara bani shi. Ki zubo mini madara a cup kmr cokali hudu. Lafiya dai ko aunty? Na danyi murmushi tare da cije lebe, wlhy kirjina ke zafi kmr ya bude. Aunty ba zaki je asibiti a dubaki da wuri ba? Ke dai bani abinda na umarceki dashi da sauri. Da kaina na hada da ruwan sanyi na dama,kafa kai na yi ina sha harna shanye. Ina ajiye kofin wanda ya shiga cikina yana dawowa,gaba daya na amayar dashi nan da nan suka rude. Na mike zuwa daki,amma ina! Sai nayi kasa ragwab! Ihu suka saki lkc guda tareda dora hannuwa bisa kai. Ban kara sanin abinda ke faruwa ba, na bude ido na a hnkl na ganni kwance bisa gado na. Ya abdullah da ya faruk tsaye bisa kaina. Da sauri ya karaso,sannu meena! Na banka mishi wata uwar harara,yayi saurin sunkuyar da kai. Ya abdullah ya matso,sannu! Nayi murmushin krfn hali da dan guntun kwalla a idona, nace yauwa. Ya kike ji yanzu? Da sauki. Na fada a hnkl,bani ruwa insha dan Allah. Ya miko min robar. Babu mai sanyi? Ke dai sha wannan sbd yanzu ance ki daina shan ruwa masu sanyi kwarai, da abu mai zafi ko maiko da mai yaji. Ko sauraronsa ban tsaya yiba, na amshi ruwan nasha, waya ja mini? Na tmbyi kaina. Ya abdulla ya zauna bakin gadon, meena! Ya kira sunana a hnkl, na kalleshi ba tareda na amsa ba,kanki farau karatu? Kawai kin dauki damuwa da tunani kin dorawa kanki, har ya janyo miki ciwo?likita yace, kina fama da yawan tunani,wanda ya haddsa miki matsanancin damuwa,baki cin abinci yadda ya kamata. Kwalla suka zubo mini, ya faruk ya matso. Don Allah meena kiyi hkr..... Kallon dana banka mishi ne yasa maganar ta makale bai karasata ba. Ya abdullah ya kalleni ya kalleshi,yana son fahimtar wani abu kmr zai yi magana,sai ya mike, Bari na dan fita waje ina zuwa. Har yakai bakin kofa na kwala masa kira, ya waigo, don Allah hada mini ruwan wanka a toilet. Kafin yayi magana ya faruk ya mike, je ka kawai bari na hada mata. Yana fita ya kalleni,tuni kaina ke kallon bango tunda naji ya fadi haka. Meena! Meena!! Meena!!!! Dake fa nike kika kyaleni,kinji? Baki yi mini magana? Allah ya baki hakuri,fushi kike yi da ni meena? To kiyi hakuri na tuba don Allah a gafarceni." Abinka ga SO hana ganin laifi nan da nan zuciyata ta karaya,tausayinsa ya kamani. Na fashe da kuka,ya rungumeni a jikinsa ya lallashi,"sorry laifinane,banza kara ba,please." wallahi meeena ina sonki,banson abinda ke bata miki rai.yanzu ki fada mini me ye damuwarki har ulcer ta kama mini ke? Na fizgi jikina,"yaushe rabonka da na ganka?ya u sati nawa kenan baka zama agida?sai cikin dare kake dawowa,ya ay bazan damu ba? Yayi murmushi,"wannan yasa kika damu har ulcer ta kamaki?" kin manta hidimar Abdallah kai na take meena? zirga-zirga tayi mini yawa shiya sa,ke kuma naga ba ki damu dani ba shi yasa. "shiya sa kake waya da yan matan ka idan ina falo ko?" ya kyalkyalce da dariya "au ashe ana kishina? Yi hakuri daga yau na bari.muje nayi maki wanka... Na kudundune fuskata ina fadin" Allah ya sauwake mini". "haka kika ce?" na daga kai. "lallai akwai ranar maida magana." ya kwaso iyayen magunguna ya nuna mani." wadannan duk ki tsare shansu,dr yace insha Allahu tunda bata kamaki sosai ba zaki rabu da ita during short period of time. A bar damuwa da yawan tunani, aringa cin abinci kada yan biki su zo a ganki a rame,kinsa kuwa duk wanda ya yi mini magana wallahi cewa zanzi ciki gareki." Na kwalo ido,ya fice yana dariya "kiyi wankan zance lifechamp a gyara dakunaan baki,saboda yan daurin aure. Ikon Allah,cikin kwana 2 na murmure har na dan fara maida jikina,saboda magungunan yawancin su duk na cin abinci ne. Ina zaune falo su ya abdallah suka shigo da buhunan kaji da saura kayan dafe - dafe kala- kala. "malama ki tashi yau fa zakuyi aikin nan." " na sani. Akaiwa su merry su fara gyarawa kafin nazo." hafsa nake jira ta ce sun kusa shigowa abuja. Hohoho ina ruwan garaje,don dokin zuwan nasu ne aka make falo?" "amma zakuje gidan amaren ko?"q ya bukata. Nace " komin dare kuwa" karfe sha daya da rabi suka iso.moya hudu cike da mutanen kano da garhi. Tsalle,ihu,murna har sai da muryata ta dushe, aiki ya hana mu kebe da hafsa,sai wajen hudu da rabi na figeta mukayi lambu." "hafsa kinyi kiba wallhi" tayi dariya"ke kuma kin rame" "bari ke dai,labari ke cike da cikin nan nawa.ina alhassan?" Yana kano,yace na gaisheki,sai jibi zasu iso ana gobe daurin aure... Kwana nawa zai yi? Na bukata. Daya yace,sbd zai tafi germany sarowa abbansu motoci ranar litinin. A ni hafsa,kina sonsa? Ta kyalkyace da dry,sosai ma. Na tabe baki,kowa abinsa zam-zam banda ni hafsa. Kamar yay? Hafsa auren dole nayi,bana soyayya ba,daga baya Allah ya dora mini jarabar sonsa,lkcn da shi kuma bata ni yake ba. Kin cika zargi wlhy,bakin fada mini ya baki hkr ba? Eh! Amma nothing change ya kamata ace daga wannan mun zama normal ma'aurata hafsa. Ta dafa kafadata, kada kiyi kuka. Ga shawara daya, kawo kunnenki! Na zare ido, Allah? Kina wasa,ke dai sha kuruminki kafin nabar gidan nan,komai zai daidaita. Allah yasa hafsa ya faruk shu'umin mutum ne. Duk shu'umancinsa zai zo hannu,ke dai dole ki cire kunya idan kina son success.ba matsala hafsa,i will try my best. Karfe bakwai da rabi an hallara falo ana ta kwakwazo gidan gwanin dadi, wai waccan kilbabbar yarinyar wacece? Na tmby hafsa. Tayi tsaki, diyar kanen b.kano ce. Wane ciki? B.rilwanu. Wacce tayi kara2 london? Ita ce fa! 'Yar ji! Haka naji dangi na fada mata,kin san ita kadai ce 'yarsa. Shine aka shagwabata haka? Hafsa tayi murmushi, kadan kika gani,rannan y.mktr na zuwaa,zamansa ke da wuya ta haye masa cinya tana shagwaba,sai ya siyo mata ice cream. Waccan katuwar? Na fada tare da mamaki. Tayi dry, zancen kike so. Sallamar yaya ta maida hnln kowa gareshi. Inna tace harka dawo? Yace eh, an gama shirya maku ko ina. Yauwa bacci daman nakeji tashi mu tafi ko kuna nan? Ta tmby su gwaggo maryama da sauran yara. Gsky inna kuje boys qtrs din nan,ni a nan zan kwana nida su hafsa. Ke maryama don me? Inji g.hadiza. Sbd katifun bazasu ishemu ba,ni kuwa bazan iya kwana mu 2 ba. Sannu giwa wadandan kattin katifun yaushe za a matse? Maryam tace, dama kyaleta kukayi hadiza kuzo mu tafi. Tace to. Duk suka fice aka barni daga ni sai hafsa da gwaggo duk ba,u lura da 'yarji dake kwance cikin kujera ba. Meena zoki bani tea. Ya faruk ya fada. Jin haka hafsa da gwaggo suka koma dakina. Ina cikin hada masa ta taso cikin shagwaba,ga wata 'yar iskar riga dake jikinta mai hannu daya,siket din ya matseta,kiri kiri an wulakanta babban leshi mai tsada. Ya faruk nima zan sha tea din. Me zan gani? Tsaye take bayansa ta sagalo hannuwanta a wuyansa. Nayi kallon da hararar amma a banza ba tasan inayi ba,sai shine naga jikinsa yayi sanyi, ka ji zan sha. Ta fada tare da dora kanta bisa nashi na runtse ido na bude sunyi jawur. Bari to! Tsaya...... Ya fara 'yan kame kame da kyar ya iya furta, Zakiyya zauna a hada miki ko bakiga nima sai an bani ba? A'a kai nake so ka...... Chafka daya na yiwa wuyanta na hada da bango,nan da nan idanuwanta suka fito,a rude ya tako, Meena!.... Kada ka tabani wlhy zan kasheta idan kayi gign tabani. Meena ki taimaka kada kiyi kisan kai... Kabace min da gani. To sakarta zan wuce,amma saki wuyan don Allah. Ka tafi daki ya faruk. A guje ya wuce na tafi,don Allah saki 'yar mutane. Yana shigewa na saketa,nana da nan ta hau yin tari,ko alama ban tausaya mata ba,na fara bata lafiyayyun mari guda uku. Zatayi kara na toshe bakin, 'ke yar iska ce? Ba 'yarji kike ba,ko 'yar gani ne sunanki.wlhy kiyi nesa da mijina don ubanki. Shine zakiyi mini karuwanci a gida? Burum naji ya fito ko kallonsa banyi ba. Nacigaba da cewa,wlhy ko kallonsa kika karayi saina cire miki makogaro duk a huta da karuwa irinki,banza. Kwalla kawai ke zuba a idonta,fskrta kuwa tuni ta kumbura sbd mari. Ke meena? Haka kike da mugun kishi? Na balla mishi uwar harara, saura 'yar iskan karuwanka dake maka waya ina jin na fara samun daya. Na figeta na wurga waje, aje ayi bacci. Na jawo kofa garam! Ya ruko hannuna na fizge,ya kara na fizge sai kawai ya sureni ya yi dakinsa dani. "ina zaki gwaggo ta ganki cikin wannan tashin hankali,ki je mini?" ya dorani bisa gado,"ki kwanta ni zan kwana bisa kujera mu ga abin da goben zatayi" "kin dai ballon ruwa doon wannan wani sabon tashin hankali ne" na ja bargo kawai na kyaleshi ina fadin "wa ya ja?" Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤16¤¤ Babu irin tambayar da ba ayi wa zakiyya ta fadi me ya same ta a fuska ba,amma amsar daya ce"ba komai" har aka gaji aka kyaleta. Dagani sai ya faruq muka san gaskiyar magana. Koda yan daurin aure suka zo ma sunyi tambayar,amma sai ta ce "ba komai." sam tabar shigowa gidan daga boys quaters sai harabar gidan,cewarta ta fi son zama can. Kowa yana mamakin wannan sudden change. Muna tsaye akitchen ni da hafsa muna harhada take aways na party da za ayi yau. Tace"shegiyar diyar nan kila ya faruq ta yiwa iskancita ya bubbugeta,hakan nake zargi." Na kyalkyace da dariya" nice nan na yi maganinta" ta zaro ido"WHAT" na bata labarin yadda abun ya faru, "kin burge ni mutumiyar,kinga kinyi mini maganin yar banza da yanzu ta addabemu. "tausayi ta bani na so jiya na kara ja mata kunne,zazzabin da ta yi ya ceceta. Yanzu ga shi ta maida mini hannun agogo baya." "wannan ba matsala bane,daman ke ce mai fushi don na lura har yanzu hankalinki ba kwance yake ba, yana son ba ki hakuri kin ki ba shi fuska. A yadda na fahimta sam ba ya son bacin ran ki. "kyaleshi,sai na gara shi nima" ta kyalkyace da dariya " ku gara juna dai,ina kallace-kallacen fina-finan syy da karance- karancen ban taba ganin irin taku ba. Ko wani girman kan tsiya ,wallahi kamar kada na tafi kawai na tsaya don ganin irin rayuwar da zaku yi" murmushi kawai na yi. Karfe 4 duk an gama shiryawa,motata hafsa,gwaggo maryam da inna zan dauka kowa ya tafi sai mu kadai. Na dauko jakata ina lalubem makulli ya ce dauke ni inda kika aje. Inna ce ta leko" tsohuwa muna waje ki yi sauri" "to inna, kuje ina zuwa,makulli zan dauka." daga can kofar gidan na jiyo karar motar, na leka ta taga a harzance,uche na hango ya fice da ita.sugwaggo a ciki. Aguje na fito amma ina! A falo nayi kicibus da shi,ya ci uban gayu shi ma blue material ya saka,ya hadu iyakar haduwa. "ina zaki haka da gudu?" na tsaya ina shessheka, "wallahi Uche........... ......." "ni ne na ba shi makullin, saboda ina son tafiya da matata." yau ina na kalla na yi sallah? Na tambayi kaina ina murmushi,dadi kamar ya halakani,amma na dan basar na ce" haba ya za a yi kaje party babba da kai,wannan ai sai mu yara." "dalilin da yasa kuka sanya mishi family & friends shi zai kai ni,me ya hana ku sanya kids party?" gaba nayi ina dariya, haka ya biyoni muka taho ina shirin tsayawa dayan gefen na ji an jefoni da makulli, "waye direbanki?" banyi magana ba na duka na dauka. 180 na dinga gudu tuni na wuce su hafsa. Duk ya rude "please meena rage gudun" na dinga yi masa dariya. Muna isa yayi ajiyar zuciya"wash! Wannan shi ne wuya makarantar kare... Gurin ya kawatu,amrya da ango sunyi kyau sosai. Kiri-kiri ya faruq ya hana ni sakat,ina kallon ya muktar sai safa da marwa ake yi amma ba fuskar magan. Da yayan kakai suka gaisa,ni kuwa ko kallo,na lura wannan abun da nayi ba karamin dadi yayi wa ya faruq ba. Karfe 7 aka gama partyn,muka koma gida a gajiya. Washe gari karfe 11:30 aka daura aure. Ranan iyaye maza suka bar Abuja,mata kuwa washe gari misalin karfe 2. Allah ya taimaka su merry sun gyara ko ina, saboda ban baro gidan amarya ba sai bayan magariba. Ko ina sun kintsa har da tukuicin turaren kamshi nayi ta sanya masu albarka. Karfe 9 na fito wanka,kai tsaye gaban madubi dagani da tawul, kamar ance in kalli bayana,kawai naga mutun tsaye daga shi sai jallabiya fara. Ya kura min ido kamar wanda bai sanni ba, ni kuwa kunya kamar na bude drower na shige. Na daure na cije na kalleshi, "wani abu kake so ne yaya?" ya tako zuwa kusa da ni, nan da nan gabana ya ci gaba da harbawa da sauri da sauri, ya tallabo kuguna na fada jikinsa ta baya, a hankali ya ce" YES I NEED SOMETHING".... Yadda maganar ta ratsa cikin kunnuwana yasa tsikar jikna tashi yarrrrrrrrr. " nazo tayaki kwana meena! Ni na kawo kaina saboda na lura baza ki taba gane damuwata akanki ba?" wannan shi ake kira babu zato babu tsammani............ "i love u meena, and i'm in need of u! Don Allah ki ceci rayuwata, yau ki sadani da farin cikin da na dade ina mafarkin samu shekara da shekaru." na shiga uku! Na fada a hankali, ashe ya jini. " bari kira wa kanki banuwa, jst love me @ this nyt, son da nake gani a idonki, please ki nunan shi zahiri meena, don Allah meena save........... na runtse ido da karfi..kayi hlr yay kunya nakeji..ya janyo ni da karfi saura kadan tawul din ya balle na hanzarta rikeshi da hannuna...ya sunkuyo da fuskarsa suka hadu da tawa ahankali ya furta zan cire maki kunyan meena jst agree wt me........na dora kaina a kirjinsa nidai kunya nakeji ya kara rungumeni sosai haba ma blvd kodai bakya sona......ya dago fuska kina sona????.....ina sonka amman..ya sakeni daura zaninki dauro alwala muyi sallah.... babu abunda jikina keyi sai kerma..kallo daya zaka mani kasan cewa a rude nake....haka mukayi rakaa biyu tare da dafa kaina yayi wata addua sanna ya mike jallabiyya naga ya cire daga shi sai gajeran wando..com on swty azo aimin tausa innallihai na fada a hankali..ko sainazo na dauke kine????na mike kawai ba tare da nayi wata maganba gabana kawai ke fadi na dadde ina tunanin wannan rana yau gashi Allah ya kawu ta naji kamarta koma..wai nice yau zan kwana da ya faruq kwana irinta maurata... kuka na fara a hankali na isa bakin gado, "malama ki cire mini wannan hijabin kafin ki karaso." kai jama'a shi ko ajikin sa, sai ma wata annashuwa da yake yi, kuka na ya karu, ya sauko yana fadin" ke kwantar da hankalinki, wasa nake yi, yi shiru zolaya ce kawai zuwa nayi muyi kwana babu abinda zan miki." . Duk da haka ban yarda ba, sai daya ce "ke ma kin san da haka raina tun jiya zan kamaki ko?" na yi murmushi tare da cire hijabin ya koma yana dariya"matsoraciya" mun kwanta shiru!! Zuwa can na ji ya dan miko hannu, nayi saurin matsawa jikinsa, nasan hakan yake bukata, amma sai me?????????????? Dai dai ina! Na makaro da wayau da dabara ya faruq ya maidani cikkakiyar mace. NI KUKA, SHI KUKA NI DAI NASAN KO KUKAN ME NAKE YI,TO SHI FA????????????????? Karfe 6:30 na bude ido, babu kowa dakin na fashe d kuka,ashe dama cika baki ya faruk yakeyi mini yana sona. Mutumin dana ringa gamawa da girman Allah,amma kmr kara zugashi nakeyi? Da kyar nakai kaina toilet duk wani sirrin gyaran jiki Allah ya taimakeni maryam ta karantar dani. Daga zaune nayi sallah. Ina cikin lazimi ya shigo,na yi saurin kifa kaina a cinya,tare da sakin kuka a hnkl. Motsin shigarsa toilet naji ina daga kai naga an yaye bedsheet din an shimfida sabo. Ina nan zaune harya gama wankewa ya fito,ya shanya. Banji shigowarsa ba,sai dai naji mutum ya daukeni cak! Babu inda ya direni sai dakinsa tsakiyar gado. Ya fice,ba a fi minti 2 ba ya dawo da tea da soyayyen kwai. Kuka kawai nakeyi, baice mini komai ba,sai dai ya kamani na kwanta jikinsa a hnkl ya bani tea din da kwan nayi kat! Sannan ya dauko wasu magunguna ya bani nasha. Ya maidoni na kwanta. Shima ya kwanta kusa dani ya maido kaina a kirjinsa. Aminatu!!! Na ji wani yar!!! Bai taba kirana da wannan sunan ba, Allah yayi miki albarka.... Wannan kalma tun jiya nake jinta bakinsa... Na rasa kalmar da zanyi amfani da ita wajen gode miki,hakika kin shayar dani zuma mai dadi,wanda nasha mafarkin samu, Allah bai bani ba sai yau. Kin cika 'yar halas meena,i'm really proud of you. Na dade da wani ciwo a raina yau kece kika wanken,Allah ya biyaki da aljanna. Lkcn dana auri jamila yarinyar nan bata cika mace ba, da nayi mata magana sai cewa tayi,fyade akayi mata lkcn tana secondary skul cewarta 'yan fashi. Daga karshe na gane karya tai min. Na dagi kaina ina dubansa cike da tausayi,lallai ya faruk ya cika mai hkr. Meena kiyi hkr da halina,muyi zama jindadi,pls i love you meena,with all my hrt. Kai ni dai ban san yadda wadannan maganfanu suka tsaya ba,bacci yayi awon gaba dani. Ina bude ido najini garau babu sauran ciwon jiki,na kalleshi yana ta sharar bacci, hannuna rike da nashi. Bawan Allah duk sai naji tausayinsa ya kamani,kwalla suka zubo mini,yayi saurin bude ido,zo, menene, Matson ya akayi? Naki yarda mu hada ido sbd kunya. Ya tashi zaune, bana son wannan kunyar fa. Ya fada cikin shagwaba,har da turbune fuska irin yadda yara kanana keyi. Ban san lkcn da dariya ta kubuce mini ba. Ya sauka bisa gadon ya bude wadrop dinsa ya fara fiddo wasu irin manyan jikkuna guda tara sai 'yar karamarsu ta cikon gomar. Nayi galala ina kallonsa ya kamo hannuna, Lefenki ne zaki gani? Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA. Karshe... ¤¤17¤¤ Lefe kuma? Sai a lkcn na tuna she fa baiyi mini lefe ba. Lkcn da nake ganin kayan nan banso zuciyata ta tuna mini da na ya mktr ba,sbd saina hangosu kmr gwanjo. Akwatuna biyar kayan sawa ne super wax ce karama a ciki,qura kuwa tafi ashirin a ciki,leshi kuwa karami shine na dubu hamsin. Galiloli da materials kai kace a textile insustry kake. Ba anan take ba,saida muka bude jikunna biyu na gaba,rigunan bacci inner wears da gyaluluwa kusan kowanne kaya akwai gyalensu. Ashe abu na gaba sauran biyun takalmomi ne kawai da jikkunansu bila adadin. Na kyalkyace da dry,sai naga ya shaka. Au na manta. Wani katon akwati naga ya jawo muna budewa saiga english wears da wanduna hadaddu,ga kuma fakistan nan da riga da siket irin na indiyawa,suma kala kala. Ban san lkcn dana fada jikinsa ina murna ba. Yayi murmushi, saura karamar jakar bude da kanki,ita jiya na amsota banki,yanzu haka idan kin gani kin kuma dauki wadanda zakiyi amfani dasu,to bankin zan maidata alabarshi idan kina bukatar wata saiki ringa zuwa can kina canzawa. Na hanzarta budewa don ganin wadanne irin kaya ne haka da ajiyarsu sai ban..... Gaba daya numfashina ya nemi daukewa. Jakr nan shake take da gwalagwalai da diamond sarka da 'yankunne,'yan hannu,,zobbe kai harda sarkar kafa. Na dauko wanis etin diamond wanda yafi kowane girma,babu shakka na ganeta. Itace na gani a wani shagin balarabe lkcn da mukaje umrah cikin wani azumi ina aji biyar. Na dauki sarkar ina dubawa yadda take walkiya ta birgeni sosai, a tunanina fashion ce. Aunty jamila na kusa dani ya faruk kuma na bayanmu bansan me yake dubawa ba. Aunty kinga sarkar nan ta birgeni woh! Gsky ta hadu bari na sayeta. Ke set ce fa,kinga sauran agogo da 'yan hannu. Ta katseni tareda dauko 'yar battar. Don Allah malam nawa? Nas tmby balaraben da turanci ya fada man kudin aunty tace yayi mana combine da kudin naija. Da gudu muka bar shagon don firgita lkcn daya fada mana,miliyan tara da rabi kenan. Sayayyar da bamu karasa yiba kenan. Gida yaya ya samemu sai tsiya yake yiwa aunty wai munji kunya. Tana dry tace, eh munji kunyar.... Kin tunata ko? Ya katsen tunanina. Na snkyar dakai... Tun a lkcn na sai miki ita,wannan agogon fa kin tuno shi? Tun a lkcn nasai miki ita,wannan agogon fa kin tunoshi? Na kalleshi na gwal ne,wanda shi kuma cikon dubu goma ya hana na sayoshi duk a saudiyyar. Ya kara dauko mini wasu set na gwal guda 5 'yan dubai design'design,wadan nan fa? Na zaro ido, sune da mukaje dubai yace na tayashi zabe anbashi sautu ne,matar abokinsa. Har aunty na tambayarsa wace ce? Ban mantuwa ya gwasaleta yace,ina ruwanki dako wacece tunda bake na sanya zaben ba? Batayi fushi ba,amma tabar wurin. Nace, yaya kmr wa take? Sai cewa yayi,kmt take. A lkcn na dade ina mamakin ya abokinsa zai auri karamar yarinya kamata? Kin ganesu ko? Na fada jikinsa ina dariyar kunya,wato ni ya maida matar aboki? Na gode yaya, na gode...... Ya rufen baki da hannunsa, nine zan gode miki meena,Allah ya barmu tare. Nace amin. Yaushe zaki ban 'yan hudu? Da sauri na boye fuskata jikinsa ina dariya,ya dan doki bayana, SHY GIRL. Yana dariya shima. Munyi shiru babu mai cewa uffan,ya janyoni jikinsa na fada da karfi. Kai yaya wai mene ne haka? Na fada cikin shagwaba. Ya lumshe ido,kunya zan cire miki,tunanina ta fita,ashe da saurana.... Nayi saurin rufe fuskata a jikinsa, a ni meena da fa tsorona akeyi,don Allah baki mamakin ganinki kwance o jikina ba? Nayi murmushi, inayi ma sosai ma. Lallai ni kuwa na dade ina tunanin ranar dazan rungumeki na danyi kissing din karamin bakin nan. Keda abun ya dameni kwarai,sai dabara ta fado mini tunda kina kyamar tsartar da miyau da nakeyi,kawai nace zan dura miki shi baki. Ya tallabo fuskata na runtse ido sbd kunya,ina tsoron hada ido dashi ba tun yau ba,akwai wani abu dake cikin idanuwansa wadanda ke haifar mini da kasala ga faduwar gaba. Da frko nayi tunanin tsoro ne ke haddasan hakan.amma daga baya na gane matsananciyar kauna ce. To wai idan haka ne tun yaushe kenan na kamu da son ya faruk? Kar dai ace tun ina karama sonsa ke damuna,kai ba lkcn bane....to yaushe ne....? Ranar dana fara zuba miki yawu a hannu, sai na ji kamar kissing dinki na yi a bedroom(en uwa a kiyayi irin paruwar hakan sabida Shaidan la'ananne) dinki,wlhy meena saura kadan shaidan yaci galabata a kaina shiyasa kikaga na fice dakin da sauri. A tunanina hakan zai samar min sauki,amma abinda bansani ba nayi babban kuskure,na rantse da Allah meena,gaba daya hnklna ya gama tashi da kaunarki. Washe gari na tafi garhi idan baki manta ba harna siyo miki waya. To a kaduna nayi cinikinta. Wlhy kmr mahaukaci na dinga yiwa su baba kuka da hawayena,abin takaici sukaki amincewa wanda a lkcn zuwana ne na takwas da maganar. Wai Allah jikan abba yace kada a sake a sanar daku dangantakarmu. Ranar da nayo miki waya nace ki fito falo,ina son magana dake cikin dare,wlhy meena lkcn kallonki kawai nake sonyi,bana son zuwa dakinki sbd gudun rudun shaidan. Kika kife mini ciki ranar har kuka nayi,ga bakin ciki ana neman haramta mini ke,ga na jamila don tun lkcn bama kwana daki daya tuni na koreta ta koma nata, da yake munafuka ce ko a jkinta. Duk wani hali da kika shiga gidan nan a kaina,wlhy ina sane kawai i'm just pretending. Allah yaga zuciyata nayi hakan ne don kawai na jarrabaki sosai,kidan wahala donki gane muhimmancin sona. ya yi dariya,wallahi kinji na rantse? tun a tapiyarda mukayi na fahimci son da kike yi mini,kawai akwai wani abu da kika dora wa zuciyan a kaina,wanda a lokacin babu wanda ya isa ya kankare miki shi.Abdullahi ne mutumin farko da ya fara sanar da ni hakan,bayan na fahimce ki. wata rana da daddare na je dakinsa muna hira akan aure da nake son karawa ban di fada masa yarinar ba.Bana mantawa ya kalleni yana dariya,kasan wani abu yaya? Na girgiza kai,Akwai wani abu da na fahimta tsakanika da meena.....A lokacin ba ki ji yadda gabana ya fadi ba,tunanina ko ya gane ina son ki ?Amma sa na ji ya ce,wasa-wasa yarinyar nan kishinka ta ke yi,saboda rashin wayo lokutta da dama ina lura da ita,ba ta son kana shishige wa Aunty jamila,nan da nan sai ta daure fuska ko ta bar wurin,musanman idan ka tsakaniku ba,wata rana sai anyi karamin yaki gidan nan,tana iya furta maka so gaban Aunty jamila,ita ma ta rama abin da ta ke yi maka.kai kowa ina lura da ita ko magana ka cika yi wa Aunty sai ta harareta,wanda baka san tana yi ba.Kinji fa?tun daga ranar na saki da al'amarin Abdullahi,becau se i realized yaron he is very sharp and intelligent.sai dai na basar kawai tare da ce mishi bana son zargi.firar daga nan ta kaste ranar,maganarsa kuwa na yi wajen wata tana damuna.Baban kano kuwa ban sami matsalarsa ba,cewa kawai ya yi,naje duk yadda muka yi da su baban inyi biyayya.kallonki

Chapter 8 of 9