Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
wane irin mutum ne da baya jin hakuri?na miqe tare da wurga masa wayar da ya sawo mani Allah ya qara baka hakuri,kuma ga wayar kanan nagode.amma aba wata ni bani bukata Zumbur ya miqe,ni kuma na kwasa da gudu dakina,ina shiga na rufe kofar da danmukulli,Allah ya taimakeni na yiwa kaina kiyamullaili,sa boda ina zare mukullin naji ya turo kofar ba tare da yayi magana ba na tabbatar da ban kulle ba,yau kashina ya bushe,kuka na saki da karfi,hankali duk ya tashi wannan wace irin rayuwa ce? Mutum kullun ckn neman fitina qarar danmukulli naji alamar za'a bude dakin wani tsalle nayi sai hani tsaye tsakar dakin ina zare eyes a hankali ya bude kofar ya shigo,sai kyarma nan da nan jikina ya dauki rawa,shi kansa ya lura da tsananin tsoro da tashin hnklin dana shiga don sai ya maida kofar a hankali ta rufe tare da tahowa inda nake tsaye.yanayn fuskarsa ya qara razana ni,nayi saurin zamewa qasa na tsugunna tare da makalkale jikina kamar wacce ya yiwa sabon kamu nayi kasaqe!! Ina jiran naji ya shaqoni ko kuma yasa qafa yayi kwallo dani,shiru har wajen minti 5 na dago kai inga ko fita yayi,saboda ko motsinsa bana ji,tsugunne yake gabana ya tsare ni da fararen idanunsa nayi saurin maida kaina a hankali ya fara magana,rashin kunya ko meena?ni faruk yau kikawi tsageranci don ki nuna mani cewa u r matured enuf,kema kin zama cikakkiyar mace toh bari kiji wlh,wannan ya zama na 1 kuma na karshe,kin san halina,,toh lallai kiyi notcn wannan ban magana 2,sannan am alwys streat 4wrd Kada mu fara haka dake saboda wahala zaki sha,ladabi da biyayya na sanki da su,to ku riqe kada ki bari su kubuce maki, maganar waya kuma ban fahimce abinda kike nufi ba..ina son ki sake maimaitawa nidai kayi hakuri,na fada ahankali bance kinyi man laifi ba,ina sin kiban amsar tambayata ai....ai ai me?kike wani korar tumaki kawai malama baki da hujja,ya jefoni da wayar idan baki so,kina iya yarwa,saboda bata gabana,sannan idan kika qara gigin irin wannan,Allah sai kin sha mamaki kaima yaya na kasa gane gaskiyar damuwar ka a kaina shiyasa kika jefan da waya na zaro ido wlh....kada ki rantse azumi zai hau kanki saboda jifata kikayi don ki nuna Allah ya baka hakuri bazan qara ba na katseshi ya dalle mani baki da yatsansa baba.sai son laifi,amma tsoro na biye bayansa,da son bada hakuri,kin bani hakuri yafi goma na murza labbana cikin jin zafin dallar da yayi mani ke bani son lambo ya fada haba yaya da zafi fa daman zafin nake son kiji..sabodanima kin wahalar dani kalamar tazo mani banbarakwai, nace na wahalar da kai kamar yaya maimakon ya bani amsa sai naga ya miqe tare da komawa bisa stool din madubi na,ya zauna tare da canza zancen da cewa Meena aure zanyi amman su baba sunce yarinyar bata yi masu ba,miye shawara hakuri nabashi amsa a gajarce nima na koma bakin gadona na zauna bazan iya hakuri da ita ba gaskiyar magana in kuwa haka ne wannan maganar tafi karfina..tunda bazan baka shawara ba kaki biyayya kada ki kware mani baya don ke kadai zaki iya taimako na a wannan auren wacece yarinyar na tambaye shi,maimakon ya bani amsa sai ya ci gaba da cewa alkawari daya nake son kiyi mani,ni kuma na yi maki alkawalin bazan qara baki miyau ba kisha.sannan zan kaiki germany ki zabi motar da kike so saboda zamani wlh duk tsadarta kin yarda? shan miyau a kuma na ganni ina tuka qatuwar motar kaina sanna ta zama mallakina ba tare da tunanin komai ba yaya yace zaki iya?kin fa san girman alkawari nace insha Allahu yaya zan iya koma menene very good ya fada tare da yin wani murmushi ina son gobe ian Allah ya kaimu na hada da uche ya kaiki garhi kin san hausawa hausawa na cewa gida bai koshi ba ba a bawa dawa ba don haka maganar muktar ki soke ta kice su baba NI KIKE SO KI AURA...... da Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤6¤¤ iyakar abinda naji kenan ***********salati na dinga ji ta ko ina,na bue idona a hankali biji biji nake ganin kowa sai dai da alama ina ganin duhun mutane wadanda bana iya cewa ko su wanene a hankali suka dan washe amman ba garau ba asibiti nake kwance bisa gao bakina da hanci na cikin abun qarin iska wato oxygn ga kuma qarin ruwa ana yi mani dr naji an kwada masa kira,tare da bude kofar tare da bude kofar aka fita da gudu ban gane ko wacce murya bace wannan haka ina jin muyoyi da yawa ana cewa sannu amina tambayar danaji wata muryar namiji yayi ita ta tuno mani da maqasudidn zuwa nan na wurin wai meye ainahin faruwar.....bai qarasa ba naji muryar mace na baa amsa..na iso kenan naga faruk ya fito da ita rumgume duk ta sandare,don wlh munyi tunanin ta rasu...jin an anbaci sunan yaya nasyasa naji numfashi na ya fara sama,na da nan naji ana ta salati wasu kuma dama kuka suke yi pls gt out,naji an fada lkcn da aka shigo daga nan ban qara sanin inda nakeshiga wannan karon koda na bude idanuna garau na gansu,babu wata alama da ke nuna bacci ko gajia a atare da da su.....an cire mani oxygn din dana gani din dana gani daga farko ,amma har yanzu akwai qarin ruwa a tare dani...lallai hanklina ya dawo jikina..kwana nawa nawa atare dani?bani da mai amsa mani tambayar nan ole na hakura...na rushe da kuka lkcn dana tuna da maganar yaya wannan waane irin balai ne? wai ni...shigowar wani lkita ne yasa ya tsaida mani tunani na amman har kkcn idanuna basu bar zubar da hawaye ba...ya kalleni ya qara kallona ya girguza kai ckn nuna alamar damuwa,sannan ya jawo wani dan qaramin tebur ya zauna gaban gadon daidai inda fuskata take ..muka hada ido hada ido yai mani murmushi tare da fadin wipe ur tears...banyi gardama ba na aikata hakan sai dai ko hannuna ban baro daga wurin ba wasu suka biyo baya .......amina kalleni da kyau ,sannan ki saurare ni tare da bani cikakkiyar amsar tambayoyin da zanyi maki da fatan kin fahimce ni.....na daga kai alamar eh..kin shirya mutuwa kibar abdullahi?..tambayar tazo mani a hargitse na rasa me zance masa saboda tashin hankali dana Ina nufin abinda na tambayeki,sbd a gsky kina kan hanya. Wace irin damuwa kika shiga haka da har zuciyarki ke neman bugawayau fa kwananki takwas ana,alluran da muka yi miki banyi tunanin dakin tashi zaki iya fada wa wani dogon tunani ba,kamar yadda na fahimta. Ya dan lumfasa,kiyi hakuri mu shawo kan matsalar ko,idan kika yi wasa zaki iya barazanar rasa rayuwarki. Ya fara lallashina a hankali tareda bani shawarwari ta hanyar tsorata ni sosai. Ya lura cewa na nutsu sosai,hankalina ya dawo jikina sannan ya fara jero mini tambayoyi. Mene ne matsalar data jefaki wannan tashin hankali? Zan fara magna kenan ya daga mini hannu,ban da kuka. Na goge idanuna,shigowar nurse yasa naki magana, tana fita ana kiran sallah,ya kalleni,bari na hada miki abinci kafin na dawo. Tea mai kauri ya bani da soyayyen dankali da kwai,yace in cinye kafin ya dawo. Yasa hannu ya cire mini karin ruwa,tas! Natada komai. Ina gamawa nurse na shigowa,ta taimaka mini na shiga toilet nayi wanka tare da alwala,don rama sallolin da ake bina.lokacin daya dawo,maimakon ya cigaba dayi mini tambayoyin sai naga ya canza zancen ta hanyar kunna mana wata tashar hoto mai dauke da wake wakensu masu kyau. A hankali a hankali harna fara sakewa cikin kwana daya,a kwana na 2 ne na fara damuwa naga ya abdullah. Dadi ya kama dr,yace shi ya hanasu zo sbd jikina amma inyi hakuri gobe za a sallameni kuma shi zai mayar dani har gida. Nace to. Washe gari ta kama juma'a,karfe 12 muka isa gida cikin motarsa,babu abinda gabana keyi sai faduwa. Duk iyakacin kokarin da naso inyi alokacin ganin hawaye basu zubo mini ba na kasa. Zubowa kawai sukeyi ba kakkautawa. Gaisuwa kawai akayi dashi yace zai koma yayi gargadin cewa a guji abinda zai kara tada mini hankali. Hankalina ya tashi ganin baban garhi,gwaggo maryam,baban kano,da kuma baba auta. Sannu kawai ake ce mani,ya abdullah kuwa ko motsi ya kasa sbd ni kawai yake kallo duk ya rame. Nida aunty muke zaune bisa kujera doguwa,gwaggo maryam na gefenmu bisa karama,ya abdulla na daga kasa da gwaggon,sai su baba dake bisa dogayen dake kallon tamu. Duk da yawan sannun da nake samu daga su bai hana zubowar hawayena ba, maimakon su ragu karuwa ma kawai suke. Banyi mamakin rashin ganin yaya ba,sbd ranar aikice. Baban kano ya gyara zama sannan ya fara magana, bazai yiyu ace mutum lafiyarsa lau har ya kamu da bugun zuciya ba,ke hajiya jamila iyakar abinsa kika sani kena? Tace eh baba,kaifa abdullah? Ya kalleni,a harabar gida na barta na fita,ko dawowa banyi ba yaya yayi mini waya,suna asibiti. Ganin halin da take ciki ne yasa nayi muku waya. Kukana ya karu baban garhi yace tsohuwa meya sameki ne?(da yake haka yake kirana). Cikin tausaya wa gwaggo tace goge hawayen kinji meke damunki? Na nisa zuciata tayi min zafi raina ya kara baci hankalina ya tashi matuka, ya faruk ne yace zai hadani da uche.........na rushe da kuka,aka dauki salati. Ya hadaki dashi kamar yay? Inji baban kano wai muje garhi wurinku,nace, shi.....shi.... wai shi.....kukan ya kuma karuwa cikin kidima gwaggo tace wai shi me? Wai shi nakeso zan aura....... Ya abdullah na gani da aunty jamila a kwance sun some. Wuri ya rude da tashin hankali.da kyar aka samu suka farfado,bayan sun sha watsa ruwa. Gwaggo kuka mu kuka su bab kuwa kowane idanunshi ya kada yayi jah!!! Wannan yaro,wannan yaro naiyi mana adalci ba,sannan ya tabbata kafaffe,marar jin magana abibda baba auta keta nanatawa kenan. Tun farko saida yaya hadiza tace hakan na iya faruwa,amma kowa yai burus da maganarta,maganar hausawa ta tabbata 'duk abinda babba ya hango,yaro koya hau dala....kun dai san karashen ehee'. Dakata maryam inji baban garhi,ya katseta,tsohuwa! Ya kira sunana,na daga kai na kalleshi,jeki hado kayanki duka. Ya kalli gwaggo dake shirin magana yace zata koma gidana na garhi da zama. Ya abdullah ya rushe da wani irn rikitaccen kuka mai ban tausayi. Sole kayi hakuri barinta nan hadari ne tunda harya bijiro da wannan rigimar,baban kano ya fada. Cikin zubar kwalla aunty ta kallesu tace akwai aure tsakanin su kenan? Kwarai kuwa. Inji baban garhi. Kirjina yayi wani irin dam! Ras!! Ras!!! Sbd faduwa,kaina ya sara kwarai da gaske. Na dafe kaina, wayyo baba na shiga uku,yau mun bani... Ke dakata bari jawo mana banuwa. Inji gwaggo maryam. Na kra rike kaina gam,don ji nake kamar har wuyana don azaba, baba waye bare cikinmu? Na fada cikin tsoro da fargaba. Babu bare cikinku,jininku daya. Da sauri ya abdullah yace ya dangantakar take baba,kuma menene dalilin hakan? Ya gyara zama,sannan ya fara magana a hankali wanda kwai ya fashemawa a ciki. Alhaji bara'u rano shine mahaifinsa. Mahaifiyarsa kuwa itace babba gidanmu,wato yaya saude (ina rabi'ah kinyi gsky). Allah ya jikan rai ta rasu wurin haihuwarsa,son ko ganinsa batayi ba. Duk gidanmu babu wanda jinisu yafi haduwa sukafi shakuwa sosai irin mahaifinku da ita,ko kamarsu tafi fitowa zar zar. Ta dade da aure bata sami haihuwa ba. Lokacin da mahifinku na karatu kano gidanta yake sauka. Kamar da kuke ganin kunayi da faruk,mahaifiya rsa ya dauko,ke kuma abbanki, to kinga kuwa babu wani banbanci. Shekarar da abbanki ya yi aure shekarar ne ta sami ciki,tun a lokaci tabar wasiccin don Allah kome ta haifa insha Allahu kada ranta ko babu ranta bishir ne zai reni yaron. Duk dangi sun san da haka,sbd ko ina ta zauna maganar kenan. Akwai lkcn da alhaji ya kawota gida don a kwatanta mata sbd yana ganin sambatun nata sunyi yawa,kodon ta dade bata sami ciki ba? Inna tayi mata nasiha irinta mata,amma daga karshe ta kafe cewar ita kadai tasan abinda take gani,da kuma irin mafarkan da takeyi,tunda Allah yasata sami cikin. Sannan tanaso a ba bishir abinda ta haifa ne riko,sbd ba a son irin matar da alhajin zai auro ba.sai bayn rasuwarta abubuwan sukayi ta dawo mana. Inna ta fara renon faruk,yanayin shekara da wata 5 abbanku yazo ya tafi dashi. To kunji dangartakarku,baban kano shine mahaifinsa,wato alhaji bara'u. Duk muka dago kai muka dubeshi kamr hadin baki. Baba shi yayan yasan haka? Inji ya abdullah. Kwarai kuwa,abinda ya bata mana rai shine bishir yayi garhadi kada a sake a nuna muku cewa bashine ya haifi faruk ba,mu kyaleku a haka. Tun bara yaje mana da maganar yana sonki muka kwabeshi tare da tsoratarshi na zan amshe ki daga wurinsa,matuqar bai janye maganar ba,kamar ya hakr sai kuma kamar wata 4 da suka wuce..yaje da auta na hadashi yayi masa tatas.wlh bamu taba tunanin cewa zai qara tada zancen ba,wato shine ya debota tun daga tushe,yayi maki wannan karam-da-rutsi, ba dole zuciar yrnya ta nemi bugawa ba toh da ayi aika aika ai qara na rabata da gdn dan banza miqewa anty tayi ta shige daki nima na miqe na nufi nawa dakn don hada komatsaina ina fitowa nace ya abdulahhi don Allah dauko mani dayar jakar,ko tsinke ban bari ba nawa,,sai gado da madubi karfe 4 saura muka bar garin abj baban kano ke tuqa motar.baban garhi na zaune kusa da shi..nida baba auta muke zaune a baya..tunani kawai nake abuna haba shiyasa da ina mkrnta butsu butsu naga yazo wai yazo ziyarar bazata,toh wai tun yaushe ma ya fara sona? Amman yayi wauta saboda sam shi ba irin mijin da nake so ba kenan tsarin rywta sam bana sonsa,na frko yana da mata,nafi son saurayi...kai jama'a kenan mahaifinsau daya da ya muktar,ya rasa wanda zaiyi kasayya da shi sai dan uwansa,sabda tsabar son zucia ga saurin hasala,ni kuma zucia toh ina kaga aure haka?..wlh na auri yaya ai naci baya don ya tsofe mani duk da yafi ya muktar kyau wlh shina ke so,don kyau ba hali muni,na fi son mai sanyayyar zucia da sauqin kai wayyo abba idan ya dawo skul bai ganni ba koya zaiyi Allah sarki anty tayi fushi dani ko ya za'ai naci amanar ta?kai amma yaya bai mana adalci ba ko ina wayata? Wato ya muktar yasan dangantarkar sa da shi? Haka naita tunane har muka iso zaria suka tsaya sallah misaln qarfe tara muka isa garhi..baban kano ko ckn daren ya tafi bai kwana ba inna dije ta rasa ina zata saka kanta don dadi ta qara mani dakin hafsa wadda take sa'ata ,itama bana ta gama skul Kwana yau 4 har na fara sakewa.saboda yadda baba ke dawainiyya da ni,komai na gdn ya canzo duk don naji dadi..ganin haka yasa na ware na saki jikina,kullum sai mun zagaya gdn yanuwa nida hafsa.daga qarshe mu zame gdn inna fira,,abinda ya bana mamaki yadda har yau baban bai qara yi mani mgnr yaya ba ko a tambayeni wani abu ranar fana cika sati 2 ina zaune ina karanta littafn rabo ne kwatsam naji muryar yaya abdullahi.da gudu na miqe na saki wata uwar qara murnar ganinsa..inna tayo waje da gudu tana fadin lafia?,,ina riqe dashi muna ta daiya,ta fito tace haba nidai nasan ba banza ba..muka zauna falo na zauna kusa dashi haba sai kuka..inna tace daga murna sai kuka? Ai tafia ma zanyi tunda kuka take nayi saurn goge hawayena nace nayi shiru ke zaman qauyn ma ya amshe ki..kinga yadda kikai far.inna tace amma fa akwai rama..hafsa na shrin magana yaya faruk yai sallam..inna tace abdullahi akwai shakiyyi shine baza kace tare kuke ba au bai fada ma inna?na tsaya muna gaisawa da su amadu mai rake?mun same ku lafia?ya fada tare da kallo na,nna dauke kaina gefe shiko ramar baiyi ba wato hnkln sa kwance yake sai mu..mgnr sa ta dawo ni..inna ya baqi?..ta dalla masa harara baqin daka koro ya zaro ido ni wlh inna baba ya taho mani da ita lo....kai rufe mani baki kafaffen wofi duk wa ya janyo? Tayi shigewar ta daki yayai dariya kawai..na miqe nima nai shigewata daki..yaya abdullh ya biyoni naji dadn hakan saboda dama akwai tambyr da zanyi masa ko zama baiyi ba nace ina anty da abba? Ya dan tabe baki,yace bari meena bayan tahowar ki rigima ta kaure.kinga yadda anty ke qasqanci? Wai damn ita aka maida sakarai saboda haka sai dai yaya ya zaba ko ita ko ke,shi kuma da ransa ya baci yace ya zabe ki idan ta ga dama ta zauna idan bata ga dama kuma tasan inda dare yai mata..toh yanzu tana gdnsu nayi nayi muje,ya rantsae yace ,idn har ba zat dawo ba,wlh tayi ta zama shi bazai jeba..kuma anso abba zaiyi..yanzu mgnr ki yazo yi baba tare da basu hakuri Hnkl na ya tashi,tausayn anty ya kamani,na kalli ya abdlh nacekasan Allah bana son yaya,kuma ban taba jin ina sonsa ba ko kadan a zuciata,don haka ka... Meena yaya yana sonki,ban gane hakan ba sai bayan kin bar gdnsa,ke in baki lbr....yaudara ce da son zucia kada ka saurare shi,muci amana wlh kaji tsoron... Shi muka gani a bkn kfa ba zato,ba tsammani,.gulmata kuke yi ko? Na tsuke fuska na dauketa gefe,ya abdlh yace a'a shawara nake bata o.k kaje inna na magana yana fita naga ya shigo,sai kawai na miqe zan fita,ya fizgoni na fada jkns,kada kice zaki ringa yi mani gadara komai a hnkli ake binsa,don haka ki koma ki zauna.mgna kawai zanyi dake na zame jkn na zauna bisa kujera,shima ya janyo dan qaramn tebir ya zauna.......... a Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤7¤¤ Meena ki tausaya mani don girman Allah.kada ki zalunci danuwnki,bana tunanin zan iya daina sonki daidai da sec 1 kayi hkr ni kuwa bana jin zan iya snk daidai da sec 1..wlh u r nt my typ idan na aure ka naci baya,ko alama ban taba jin kana brgni ba ya kalleni ckn bacin rai ni kike fadawa haka meena ckn haln ko in kula nace iyakr gsky ta na fada mak...kin fi son bare da danuwnk waye bare?na bukta ya dallo mani idanu.baki hada komai ba dashi illa kara,,ni kuwa... Yaya bana sonka kayi hkr mubar maganr nan ni meena?.ya fada ckn tashn hnkl..don Allah kiyi mani adalci..kefa kika dauki alkwali,,,na rashn sani ba? Abnda yasa kika a ina lallabaki,bana son nazo nayi wani abu kice na cuceki..amman zan baki assgnmnt nan da sati 1 don Allah ki fara sona,ni kuma nai makialkwln zan jiyar dake dadn da baki taba ji ba dunia kayi wa kanka kiyamullai yaya kaje ku sasanta da matarka nikam nafi karfn ka wlh sai yaya muktar saurayi sabon jini wani tsaki ya buga tare da wrgo mani wayata da charga yace zan baki mamaki wlh wato ke lallashi baya maki....ya juya zai fita ya juyo yace wlh sai na aure ki saboda ina sonki GIDA BAI QOSHI BA BA BAWA NA DAWA BA Ta fiddo ta fara latse latse kenan,wayata ta fara rngn,ya muktar ne naji dadin hakan hello na fada yayi ajiyr zucia me ya samu wayarki 2days. Nayi murmush,kwana 2 a kashe take,kasan ina garhi ita kuma na barota abj,sai da su ya... Wai da gaske ne?ya katseni,nace me fa? Magnr dake tsaknin ki da yaya faruk gaky ne amma yanzu komai ya daidaita na fada masa abnd baba ya kidanya,yayi ajiyar hrt,kin san Allah meena daman na zargi haka tun farko,ina gudn kada na fada maki wani abu ya faru uhm kawai nace,yayi tsaki irin na ban haushi,daman ina lura da shi tun kina skul a sati sai yayi zuwa biyar.ga wani munafukn kallo da yake maki haba yaya cool down komai ya wuce na fada ckn yaryanga da shagwaba uhm ke kike ganin haka,ni nasan waye faruk.tun baki da wayau,ki fa tuna idan naje abj idan mun kebe muna hira irin sintirin da yake yi duk ya kasa zaune ya kasa tsaye,haka kuma idan ina gidan nan komai kikai laifi ne,sai ya hauki da fada har ta shafeni Ko kin manta ranar da muna zaune falo duka gidan ana hira da daddare,kamar wasa ya janyoki jikinsa ya hada bakinsa da naki wai kisha miyau,sbd ya lura tunda ya zauna kike wani yatsuna dan ya tsirtar dashi? Duk mai hankali ya zai dauki hakan? Wane yaya kika ga yana yiwa kanwarsa irin wannan horon,in har da gske ciki 1 suka firo? Ko wannan kawai bai zama alamar tambaya babba ba meena? Ina tunaninki da hankalinki suka tafi a wancan lakacin? A lkcn nafi dora wa jamila laifi,sbd itace katuwar jaka,dakikiya mara tunani,p. Abinda yasa kika ga na fita daga falon,haushi naji sbd lkcn daya sakeki wani mayen kallo ya biki dashi,wannan mu maza kawai mukasan ma'anarsa..... Kabar tashin tashina,tunda baba..... Ke kike ganin haka,faruk baida mutunci amma barshi,idan yasan wata aibai san wata ba,zan zo ranar juma'ar nan muyi magana da baba,don na turo magabatana,kin amince? Na danyi murmushi,na amince yaya,ka zo kawai. Ngd meena,zan kiraki anjima,ok? Nace yes my dear. Tare da kashe wayar na dan kalli mutuniyar ta wutsiyar ido kamar ta daura hannu sama ta kurma ihi. Hafsa ta matso,wai meye naji kina ce mishi yabar tashin tashina? Na danyi murmushi,magulmata suka fada mishi rikicina da yaya,duk ya rude shine yake tada mini wasu abubuwan da suka faru abuja,sai nace ya daina, yanzu dai ya rokeni alfarma yana son na bashi izini yazo wurin baba suyi magana... Me kika ce mishi? Ta katseni ciki nuna farin ciki dajin dadi. Na danyi dariya, yazo kawai nace,koya kika gani? Kafin tayi magana,fatima tabar dakin. Muka kyalkyace da dariya,har da tafa hannuwa. Amma kin birgeni mutuniyar,saidai zan baki shawara daya amma ba yanzu ba, ki bari mu koma gida tukunna. Nace ba mtsala 'yar uwa. Wayata tayi 'yar kara alamar sako ya shigo. Ina dubawa naga an rubuta 'message from ya faruk' kinga kuma wani sako daga ya faruk,kai Allah ya raba mai rai da naci. Kin cika daukar abu da zafi,ki karanata mana, menene a ciki idan bai miki ba sai ki goge. Inba ke ba waza a kula yace naci? Ki dubi yadda suka bar garin nan,yanzu haka basu isa kaiwa ba,don ya damu.... Kai ya isa,kada a isheni,bari na karanta ko daman can ba cewa nayi bazan duba ba. Rayuwata!!! Ya muka barki? Meena ina fama da azaba a zuciyata kece rayuwata,rasaki na iya sanya wa na rasa kaina,ki dubi abubuwan da suka faru,meye laifina a ciki,kodon nace ke nake so? Ki tausaya wa dan uwanki,kada ki jefani cikin mawuyacin hali don Allah. Alkawarina yana kanki,kamar yadda zan cika naki a duk lokacin da kika shirya karba. Mukhtar dan uwana ne,ba naki ba. Na fiki sanin halinsa,sha'awarki kawai yake,baya sonki,ni ne masoyinki mai kaunarki............. Nayi saurin gogeshi duka,ba treda na karsa karantawa ba don takaici. Daga na gidan inna muka wuce sai dare muka koma gida. Muna cin tuwo ya mukhtar ya kira,mun jima kafin muyi sallama, kamar hadin baki,ina wanke hannuna ya faruk ya kira,nayi saurin zuwa na kashe wayar baki daya sbd nasan nacinsa. Muna zaune daki muna kallon wata drama da akeyi ta 'yan korea, mai suna heaven fates,nace yauwa hafsa wace shawara ce za a..... Ban mnta ba,son Allah bari a karasa wnn episode din,naga yadda za a kare. Kinsan Allah ki raba kanki da kallon dramas. Sbd me? Ta bukata hankalinta nakan tv. Ban sani ba na fada cikin jin haushi. Dai dai lkcn aka gama ta juyo,kin cika saurin fushi da yawa,wannan wasan yanda kyau don baki fara daga farko bane,shiyasa kike ganin rashin kyansa. Ke dai kika sani na fada ina murumushi. Kinsan shawarr da zan baki? Sai kin fada nace da ita ina kallonta. Akan mgnrki ce dsu ya faruk,kin san ita gsky 1 ce amina,kuma rayuwar duniya da kike ganinta wlhy abu ce mai hadari. Duk macen duniya budurwa kamarki,kullum addu'arta ba zata wuce Allah ya bata miji na gari wanda yasan mu2ncinta,iyaye nta da kuma 'yan uwanta ba. Maza da kike ganinsu kyal kyal na rariya ne,wanda kike hangen mtnci da soyayya gareshi zaki zo daga karshe ki gane ba hakan bane. Bance miki duka ba a wasu daga ciki kamar yadda muma matan muke. A yanzu zaman nan da ake amina baki da kamar ya faruk,sbd shi ya rikeki,ya kuma raineki,har ki....ke kada kiyi sabo malama,akwai mai rainon wani banda Allah?na katseta cikin bacin rai,don fara gano inda ta nufa. Tayi murmushi, bana nufin haka,sbd da taimakon Allah,kuma shi yabashi ikob komai. Da fatan kin fahmceni? Tacigaba da cewa a mkrnt idan ana lbrn aure da yawa nakanji kawayena na fadin sunfi son aure mai mata,sbd yawanci sunfi sanin darajar mace. Ranar nan jinki kawai nakeyi wai ba kya son mai mata,sai saurayi,idan kishi ne yaja ki fadin haka to kinyi kuskure kina iya auren saurayin,lkcn da kika gane dadin zama ke kadan yayo maki wata ya zakiyi? Ga mgnr tsufa,kiji tsoron Allah meena,duka yaya idan yayi gudun hohoho yayi shkra talatin da takwas zuwa da tara. Amma a fuska saiki rantse da Allah shkransa talatin daid ai. Haka naji su inna nayin wannan zancen rannan ita da baba. Yana da kyan jiki dana fuska,banga makusarsa ba,sbd wlhy yanzu idan ya jera da ya mukhtar sai ace shi ne kane ba wa ba. Kuma ko zabe akeyi,kin san sai an zabi....... Look! Hafsa ya isheni haka nan,bana son ji....ki rage wannan....i dnt want 2 hear d hell of nonsense. Na kara daka mata tsawa. No wonder naga an tuza miki kudi dazai tafi,ashe na campaign ne... Baki fahimceni ba meena.... Bazan kuma taba fahimtarki ba,gargadin dazan miki na karshe shine,ki iya bakinki,kada takai muyi wulakanci........ Da wa? Allah ya baki hkr,me yayi zafi haka meena? Nace bana so dai na fada miki,wlhy ki daina. Insha Allahu anyi na farko ai. Ta fada tana rike da haba,kmr wata tsohuwa. Ta bani dariya amma na kame don kada ta dauki maganata wasa. Baku da gsky,sbd kuminiyarku tayi yawa,wace wainar ake toyawa adakin da kuka ki fitowa, har karfe sha daya ta gabato,ko yau bama cin abinci ne a gidan? Hafsa ta mike,kai inna,yau fa ke ce da girki..... Au daman da gaske kuke mgnr jiya? To bazan girka ba,idan baku yi k.......inna babu ruwana, hafsa ce da wannan 'yan kakale kakalem. Na sani tsohuwa,kullum idan girkinki yazo,sai dai muji kamshi,amma ita sai..... Sallamar ya suleiman ta hanta karasawa. Ya akayi ne inna kike ta faman bambami,ana jinki da an shigo soro? Sallamr yaya muktar ta hana inna magana ko amsa bamu tsaya yi ba mykayi daki wane nake gani haka kamar muntari,baba ya fada yana dariya inna tace ai kaifa yanzu ka ganshi ko ai tun dazu ya zo ya durkusa har qasa suka gaisa ganin yadda yake ta yan sunne sunnen kai ne yasa inna tashi ta shige daki kallo daya baba yayi masa ya gane lallai akwai wani abu,shi a tunaninsa ya dauka ko mgnr fati ce yar wajen baba auta ya akayi ne muntari? Ya qara saddar da kai qasa yace,damn uhm uhm y dan sosa qeya kai bana son skrci ni din zaka yi wa boye boye? nace menene kamar zai nutse qasa dn kny haka nan ya daure ya fara mgn.dmn munyi mgn da amina ne,shine tace nazo wurinka,,yayi shiru baba yayi dan tsaki.kai ni ban fahimci bayaninka ba tace ne nazo na nemi izni idan ka amnc mgbtana suzo ayi mgnr aurenmu dawa? Baba ya tambya,,yace da ita aminar kake so? Ya qara tmbr sa eh baba tun yaushe gsky zamu yi shkr 3 naso zuwa nan amman ya faruk ya hanani ashe yana da wata manufa sai yanzu na gane tsohuwa!! Ba zato naji baba ya kwalan kira ina zuwa na durkusa nace gani baba,gabana sai faduwa yake mene alakar ki da muntari? Na shiga rudani sai kame kame..kin yi shiru?..nace sona yake yi kefa?tambyr razo mani a bazata nace nima kina sonsa?nayi shiru.yace kiyi mgn sbd ina son fita hkkn ki ne.kada a tauye maki kina sonsa kuwa? Nace eh baba ina sonsa yayi murmsh

Chapter 4 of 9