Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
ne ya kamashi ganin irin kular da ya muktar ke bawa karatu na ranar asabar muna zaune bisa kuheru nida ya muktar abba kuma nata guje gujensa mu kuma mun tsinke da labari sai ga ya abdulla.nima dai ya kamata na dinga zuwa ina daukar wannan darasai ya zauna yana ida maganar sa.duk muka kwashe da dariya nace wai ya maganar salma yaushe zamuje mata yawo?yayi saurin nuna bakinsa da yatsa shshshshshshs alamar inyi shiru ga yaya nan tafe nayi saurin bude littafi na kamar karatun nake da gaske.yace da kyau meena Allah dai yasa ki fito mana da nine As ya fada lokcn da ya jawo kujerar kusa da ya muktar ya zauna duk muka ce amin lokci guda..yayi dariya yace kaji masu yaruwa,muma dariyar mukayi,na mike zan koma ciki ya daka mani tsawa abinda na tsana yace ina zaki? Nan da nan jikina ya dauki rawa na dawo na zauna.ran ya muktar ya baci na gane hakan ne saboda kalaman da yake fadawa yayan gaskiya yaya ya kamata ka ringa sassauta wa yaran nan don banga amfanin matsa masu da kake ba saboda yanzu dey r all matured enough,amman idan ka bari girm... Look! look! Ya katseshi me nayi mata yanzu? kana ganin daga zamana zata mike ta fita,sun mayar dani kamar wani azrailu.ko shigowa nayi gidan nan idan suna falo zasu tashi subar wajen,amman idan kaga suna fira da jamila abun sai ya baka mamaki ya dan tsirtar da miyau yaci gaba da cewa..ko matsalolinsu sunfi karfin suzo su fada mani sai dai naji daga bakin jamila,ina amfanin haka ya raina bazai baci ba?to daman duk kule nake da su..ya dan tsirtar da miyau,na hade rai zai yi magana kenan ya muktar yace ni banga laifinsu ba,kaine tun farko ka maida kanka azrailun Ina mamakin yadda ya muktar sam bai shakkar datsa ma yaya ko wace irin magana yaga dama ba ya ci gaba da cewa sai kayi kokari ka jawosu jikinka amman abin da kamar wuya.sai da ya tsirtar da yawu sannan yace ai naga wanda zan kara zama wuri ya tashi ko kuma inji matsalarku a wajen jamila kuga yadda zanyi da ku ya muktar ya kyalkyace da dariya mai hali da halinsa a hakan zaka jawo su jikin? Ya ballo mani harara,ni kike ma wannan yatsinar saboda miyau gabana ya fadi,ya kuta wallh idan baki yi a hankali ba wata rana tabe bakinki zanyi in zuba maki naga ta kyama.zuciata ta tashi,naji kamar zanyi amai ku tashi ku rakani yawo,inji ya muktar.duka mukai zumbur,ni kuwa har dauko abba. Mts!mukaji yayan yaja wani dogon tsaki tafia muke yi,amma idona na kan ya muktar,ina kallonsa ta mirror sai naji yana birgeni sabda yana son yaga walwalarmu tantalizers ya kaimu kowa ya zabi abin da yake so,shi ya biya kudi.daga nan bamu zame koina sai gidan su salma budurwar ya abdulla.skul dinsu daya amma ita ajinta 2 yanzu sabanin shi da ya gama servc zai tafi ledojin da muka ga ya muktar ya ciko ashe duk tsarabarata ce, bamu dade ba muka koma gida tare da wata bakuwar mota muka shiga,duk tunaninmu ko bakin anty ne,haushi ya kamani don ban so muka dawo yanzu ba,naso ace sai dare ba kamar dana hango yaya zaune inda muka barshi fitowar kasaitaccen mutumin nan daga motarsa yasa yaya mikewa zumbur,ina cikin kwaso kayan da muka sawo ne,naji ya iso yana fadin barka da zuwa yallabai,bisimilla,ya nuna masa hannu alamar su shiga ciki ko alama banyi tunanin zuwansa na da nasaba dani ba,don haka sun rigamu shiga gida ina kokarin gittawa na wuce ciki yaya ya kirani Har kasa na durkusa don gaida mutumen nan.a gaskiya muna yin baqi a gidan nan iri iri saboda yaya mutumin jamaa ne,shi kowa nasa ne,amma bamu taba yin airin wannan ba babban mutun ne,don a qalla zai kai kimanin shakaru arbain da haihuwa,yana da tsari ga kwarjini duk da ba wani kyau ne da shi ba.sai dai wanda ba'a rasa ba,kallo daya zakai mashi kasan cewa akwai masu gidan rana tare da kwancitar hankali a tare da wannan mutum meena wurin fa yallabai yazo,yaya ya katseni nayi saurin dagowa na kalli yayan, ya wurga mani wani kallo mai nuna alamar zaki gane kurenki. Yaci gaba da gabatar da shi a gareni yana fadin wannan oganmu ne,mnstry dinsu na kallon tamu sunansa sir alh abubakar muhd shine chief contrller genrl na custm bgabana ya fadi,na shiga 3 shi kuwa alh abubakar irin dariyar manyan n yayi,sannan yace ai faruk anan kaine oga,ni matsayi na a office kawai ya ke,dole in kiraka sir saboda nazo neman iri,duk muka bushe da dariya hajia amina yaya nayi maki ko? Nidai ban san ya akayi ba sai kawai na tsinci bakina na fadin sai abinda yaya yace ke ban son sakarcin wofi,ko bakiji tambayar tasa....kuka na saki a rude subhanallahi,ya akayi ne meena inji alh abibakar maganar yallabai naji yana yi masa bayani,yallabai kasan iyayenmu da ke can kauye sun sanya mata dokar ita da fidda miji sai ta shiga jami'a and yanzu tana aji 5 ne kaga kwa dole hankalinta ya tashi mamaki ya kamani yadda yaya ya shirga karya bayan mu ya hanamu yinta,saboda wannan doka da ya ambata tasa ce babu ruwan su baba na garhi No problm naji ya fada.fatana kawai don Allah faruk ka sanar da maganata,ni kuwa insha Allahu zan jure don nan da shekara 3 ko 4 toh yallabai.Allah yasa rabonka ce, gabana ya kuma faduwa saboda na tuna wannan adduar irinta yayi wa ya muktar.ya fiddo bandir din yan dari dari guda 2 ya ajiye gabana yana fadin tunda ke tsoro na kike zan dinga zance da faruk a office. Suka kyalkyace da dariya ina nan zaune mun kurawa kudin ido nida yaya,anty jamila cike da fargaban balain da zan sha wurin yaya. Tare ya muktar suka dawo shida ya abdulla,suna shigowa ya nuna kudin da yatsa yace you see? kaga abinda nake gudu ko,kana neman ka maida dan iska ko? Ya kalli yaya muktar,sai naga ya dukar da kai kasa,shi kuma ya cigaba da fadin sai ka nemi karyar mani da doka ko?toh wlh kaji na rantse idan har ka kara yi mani wannan abun tubewa zanyi mu ware naga ko zaka iya tsintar wani a guna sai na barka kwance maganar fita da meena yawo na kasheeta,in bada jamila ba,ke kuma idan kika sake gigi ya jaki kika qara binsa kik bari har wani ya biyoki gidan nan wh aure zanyi maki kai kuma kaji abinda yallabai yace kuma ba zan shiga maganar ba tunda kai kaja,don haka babu ruwa na da gida,fuuuuu,ya wuce dakinsa mu kuma ya bar mu nan tsumu Abubuwa sun taso,komai ya canza,wanda yayi shekara 2 bai ganni ba sai na bashi mamaki ,duk wani abu da cikakkiyar ya mace ke taqama da shi babu wanda Allah bai mallaka mani ba, kyau na ya fito,fatar jikina ta gyaru kwarai...na miqe cike da murna na tafi bisa step don yin submittn din jarabawar wadda ta kasance itace ta karshe daga ita munyi bankwana da TURKISH. Ina fitowa na hango ya faruk shida anty jamila saboda tsabar murna da dadi na cafe abba da ya rugo da gudu sama na cillashi ina dariya suma dariyar suke shida anty...suka ce congrats suka fada tare..nace tnk u so much..anty ta qura mani ido duk karatun ne ya ramar da ke haka.murmushi kawai nayi,mun dauki hanya ya muktar ya kira ta layin anty daman ita yake samu na a gida idan munyi hutu saboda shi yanzu aiki yake yi a wani company siminti a legas...... dit History Al-Hada Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤3¤¤ Nasan wannan kiran naki ne amshi kwai,waye ne ya bukata? Tace kaima ai kasan ba zai wuce muktar ba,shima dai murnar ya tayani,ina ajiye wa yaya ya kalloni ta madubi,wai ke har yanzu kwarakar wayar kike yi ne?.kafin inyi magana anty tayi caraf tace ka sai mata mana.yayi murmushi,anty tace baka ce komai,yace toh me zance..kamata yayi yanzu ka...ya katseta idan har tana son waya,to tayi addua Allah yasa taci jarabawarta duka babu pass shi kadai na fidda da fail,ni kuma nayi mata alkawalin sabuwar waya ta yayi,tare da dalleliyar mota,ni zan ma koya mata da kaina haba! Inajin haka na maqale abba,ina murna,saboda ina mai tabbatar ma kaina insha Allahu wannan kyauta naci ta na gama. Haukan banza kike ta wata murna cewa nayi idan, wlh yaya ni nasan insha Allahu babu jarabawar da zan fadi,anty tayki karaf tace amin diyata..ya kyalkyace da dariya yace kaji mai diya maimakon naga mun dauki hanyar zuwa gida wato area 8 sai naga ya dauki hanyar da zata kaimu life camp,cikin raina sai murna nake wata qila sayayya zai yi mani ta murnar na gama skul wani qaton gida muka dumfara wanda tsoro ya kamani saboda haduwar sai get dinsa up white irin farin nan wanda baya da haske bau,muna danna kai na hango ciki gidaje 2 iri daya kowanne an zagaye shi da filawoyi iri daya.ina waigawa na hango wani dan gida gefe a raina nace BQ kenan,..sabbin motoci na gani cikin wata rumfa guda 6..kai gidan nan ya hadu ashe ba'a zuciata na fadi ba sai naji anty na cewa ai sai ma kin shiga..nace wai gidan waye?..anty tace sayar dake zamuyi..very good inji yaya....tayi gaba abinta,sai naga yaya abdulla ya fito daga dayan gidan wanda anty ta nufa yana fadin oyoyo sister congrats..nayi tsaye turus,kijina na dukan 3-3.duka na ga kowa ya fito har da yaya ana yi mani dariya tare da fadin suprise!!!and dis is our new home na buga tsalle ina murna tare da rugawa ciki da gudu (toh nidai bazan tsaya fadi maku irin tsarin gidan da aka fadi ba gaskiya,na tsallake) eheheee duk nafi murna da sabbin dinkunan dana iske cike da wardrop babu abinda ba'a saka mani ba najin dadi a dakina..haka ma toilet dina babu ce kawai bau.kai gaskiya komai ya hadu ina cikin shafa mai ne anty ta kwala mani kira inzo muci abinci.koda na fito sai da nabawa kowa dariya wai yaya llafiar guiwa wurin son gayu na dariya kawai nayi muka gama na kwashe kayan nakaima yan aikin anty,na dawo falon kowa na zaune ana fira ni kuwa sai qara kurara gidan nake..yaya yayi mumushi Allah yasa ki samu wanda ya fishi ina ma laifin kamarsa na fada ina yar dariya.ya abdulla ya karaf yace kaji rasa kunya beran masar..duka aka qara yin dariya yaya yayi dariya yace ai ni nama rasa wanda take so tsakanin muktar da yallabai don kowanne saurare take SO? Ni wlh bani son ko daya wakike so ya abdulla ya jefo mani wannan tambaya nace ohon maka. Ohon masa?inji yaya toh yau sai fadi mani wanda kike so in har kince su duka basu yi ba,nayi murmushi ni ai ba yanzu zan fadi ba,sai yaushe ?anty ta fada cikin dariya,na daure fuska ganin kowa ya maida ni sakarai nace nan gaba. Misalin karfe takwas da rabi na dare ina kwance dakina ina karatun wani ltattafi mai suna rabona ne wanda zainab wauwo ta rubuta,na jyo hayaniyar yaya shi da anty. Haushi ya kamani,ina amfanin fitina,shi dai kullum ba ya rabo da fada,bamu ba ba ita antyn ba,ina amfanin tashin hankali ace rigima kuma kwana 4.amman taqi ci taqi cinyewa,maimakon ta ringa lafawa kullum sai qaruwa take yi,tun muna jiqasa qasa har sun fara daga muryoyin su,wai to miye ya hada su ne? Ji nake yi rikica!alamar fashewar wani abu mai kama da tangaram,ko kuma an fada samansa, na fito a guje na tarar da anty riiqe da tabarya tana dukan dinning table duk ya farfashe,shi kuwa yaya sai kokarin amshe tabaryar yake yi amma ya kasa gudun kada ta kwada masa,shi kadai yaga fitowata.saboda ita ta bani baya tana ta rusar galsses din yana qara rarratsewa,nayi saurin fizge tabaryar na wurga ma uche nace yayi waje da ita,ta yunquro zata dakan kenan,yaya ya riqeta ta baya gam,..ni kuma na ruga da gudu dakin ya abdulla a BQ na kirawoshu..har na dawo yaya bai saki anty ba,gaskiya ina son takun ya abdullahi,saboda shi komai nashi cikin ruwan sanyi yake yinsa ba tare da wani tashin hankali ba A hankali ya karaso inda suke,ya ruqo hannun anty,sannan ya kalli yaya yace sakarta. Baiyi musu ba ya kyaleta kuwa.abin mamaki sai naga duk wannan haukan da take yi ta daina cikin raina nace,wasa ma ai wuri gareshi,yawan bobbatai daman bashi ne fada ba Daki ya nufa da ita,ni kuma ina biye zungui zungui,ya zaunar da ita bakin gado,sai ta fashe da kuka,hakan yasa ta bani tausayi,saboda nasan balin yaya,ina ma ganin kokarinta kwarai je ki kira mani yaya,,da sauri na fita,sai gamu mun dawo tare yana ta mazurai sai da ya zauna,sannan ya abdulla ya fara magana ita gaskiya daya ce yaya,kuma dole ne a dubata,zama idan akace maka wannan zama ne na aure,to fa ayi shi ne har abada. Ya kuma zama wajibi a ringa hakurin matsaloli ko wane iri ne,wadanda suke kunshe here n dere..baifa yiwuwa ace kullun laifin mutum daya ne..dole shima dayan nada nasa..kabar ganin takuramu tare da lankwasa mu ta yarda kake so ya zama dole mu bika saboda wata rana sai labari. Don kasan daga inda nayi aure ko meena tayi aure hukunci ya tashi daga kanka to sabanin matarka ita kuna tare har abada yanzu kaddara abba na gidan nan salma bata tafi dashi ba.me kake tunani?kuna ganin zaku qanqare wannan tunanin a ransa?shekarar sa 5 kenan bai sai komai ba kuke tunani? Anty ta fashe da kuka,duk ta qara bamu tausayi wacce irin rigima ce haka kusan sati 2 kenan ana yinta?kamar an daidaita sai kuma ta taso?mene wai ya kamata ku sani cewa mufa ba yara bane kamar yadda kuka dauka..yanzu haka ina iya riqe mata kamar yadda meena na iya zama da miji menene ya faru yaya? Idanunsa jawur ya dago kai,ka tambayeta mana,ai ita akayi wa laifi sai ta baku amsar bazan fada ba inji anty. Murmushi yayi irin na bacin ran nan mai quna kamar wuta a zucia zan fada,amma ban ce cikinmu ga mai laifi ba,don haka na barku ku yanke hukunci daga karshe idan kun gano mai laifi Yau shekarar mu ta 10 da aure kenan.idan kunyi lissafi,sannan abba shekarar sa biyar kenan.kuyi mani lissafi ko bayan haihuwar sa yara nawa ya kamata ace kannensa ne? Ya kalleni,sannan yaci gaba da cewa,lokcn dana kaiki garhi da zamu dawo wane yanayi kika ganni ciki?wlh tunda nazo duniya ba'a taba yi mani zagin dasu baba da gwaggo sukai mani ba a ranar,wai na maida kaina baya tunda bana son haihuwa. Muka je kano gaban ku baban kano ya ringa mani habaici gabansu muktar har na fadin insha Allahu muktar sai yayi 'yaya fiye da goma. Kowa ni ya ba laifi,ana tunanin cewar bana son haihuwa ne,har cewa ake yi abba ma Allah ne ya qaddara zuwansa duniya,amma badon naso ba ya dan lumfasa tare da hadiye wani gawuratccen miyau,kun ganta nan,ya nuna anty da yatsan sa,babu irin rigimar daba mu yi da ita ba akan haihuwa,amma dage ita gaskiya bata so wai don shine ita da hauka kada ta tsufa da wuri da kyar na samu ta haifi abba kuma tana haihuwarsa tasa aka cire mata mahaifar baki daya. A tsorace muka zaro idanu nida abdulla cike da al'ajabi cirewa yaya? Yace kwarai kuwa toh yanzu fadan su baba da gore goren da ake yi mani tare da wulaknci ya ishe ni,shine don nace zan qara aure take ta yin wannan haukan Kuma wlh na rantse babu fashi danayi tunda bani na aike ta ba taje ta cire mahaifar ba.ni kuma yanzu yaya nake so tace in sake ta,saboda haka baqinta nayi ba sai dai nace,muje gaban mahaifanta idan na gama zayyana masu duk abinda ya faru na yarda zan sallameta don kada suga cewar ,naci ma yarsu mutunci,amma tace sam ita bata yarda ba saboda haka ya kuke ganin za'a shawo ma matsalar nan.aure kam wajibi ne sai nayi shi wlh babu fashi innalillahi wainna ilaihi rajiun,kawai ke fitowa bakin abdullah,ya danyi shiru sannan yadan karkata ya kalli anty,,haba anty da hankalinki da wayonki tare da ilminki,duk kikayi wannan aika aikan?to a gaskiya wannan shariar tafi qarfina kawai abin da yafi shine bari naje na taho da su daddy(wato mahaifanta). Nan fa ta rude tana roqonsa,amman ina yace gaskiya anty sai dai kiyi hakuri kiransu daddy ya zama dole,ni kuwa kuka kawai nake yi na rasa ko na mene shin antyn nake tausayi ko yayan? Ya kai qofa ta rukoshi,toh zo ni kuma kaji bayanina idan baka gamsu ba na yarda ka dauko su jin haka yasa ya dawo ya zauna,inda yake yana mai fuskantarta ta fara magana a hankali cike da danasanin wautar data aikata maganar aure na amince,amma da sharadin ko wacece ita ma ba zata yi aiki ba kamar yadda ya hanani. Cikin hanzari yaya yace ba matsala nayi maki wannan alqawalin magana ta qare,ta fada tare da miqewa tabar dakin Zaune muke falo daga ni sai ya muktar gidan babu kowa anty tatafi sunan wata qawarta da ta haihu ya abdullahi ya tafi ya kaita...yaya kuma yana wurin aiki mun tsinke da labari ba ji ba gani,zuwa can ya jefo da wannan tambayar,ya maganar controller har yanzu yana zuwa kuwa?,nayi murmushi ko jiya yazo da dare..ya hade rai me ya ce maki? wai yanason turo magabatansa,yau she?.nan da sati2,sai kika ce me?,ya dakata,ba yanzu ba,sai yaushe?,,kai yaya wadan nan.....just answer me. Ya daka mani tsawa abinda bai taba ba.nace baka ganin ko jami'a ban shiga ba...yace dakata kada ki maida ni abkn wasan ki mana ko kina tunanin har yanzu shekara 3 kenan baki gama yawo ya da hankali na ba? Sai naga ya dawo ya zauna,ji nayi yayi qasa da muryar shi ,ya fara magana cikin wata irin siga pls meena save my life,,wlh idan na rasaki ina iya rasa rayuwata,nayi saurin dago kaina na dubeshi,ya daga kanshi amalar eh abinda ya fada har zuciar shi ne,,ya kamata ace kin gane manufata tun tuni wlh sonki nake kamar raina,saboda ke naso yaya ya samar mani aiki nan gari.amma ya qiya wai zan takura karatun ki...ya sauko ya tsugunna gabana kamar mai neman gafara.don Allah kicece rayuwar danuwanki meena am in love wt u jikina yayi sanyi na kasa dago kaina na kalleshi,nidai ya bani tausayi amma na rasa kalmar da zanyi amfani da ita wurin yi mashi magana..sai danaji ya cigaba da roqona sannan nace ya muktar hakuri zakayi kasan komai muqaddari ne daga Allah..wlh idan ni matarka ce ba makawa sai na aure ka nasan haka meena ,ina son jin shin kina sona ko kuwa..nayi smyln ya za'ai naki ka ai koba komai kai danuwa nane kawai sai naji yana ya riqe hannuna yana fadin nagode meena Allah yasa ke matata ce nace amin...bamu san ya akayi ba sai muka ga yaya tsaye a gaban mu..nayi saurin miqewa tsaye tare da fizge hannuna cikin fargaba. Cikin ikon Allah sai naga yayi murmushi..a'a kuci gaba da soyayyar ku ni ci zan shiga sam yaya yanzu ya rage yi mana fada komai sai dai nasiha magariba lis anty ta dawo.muna zaune falo ana cin kayan sunan da anty ta kawo.tace muktar din yazo kuwa nace eh har ya tafi. Haka ya iskeki da wannan shegan wandon da wannan figaggar rigar..nayi saurin kallon yaya ya kuwa ballo mani harara,da sauri na sunkuyar da kaina,ayi hakuri anty bazan qara ba,, tace a'a toh da kin kyautawa kanki,ko kanzil dai yaya bai ce ba da dare ana zaune falo ana hira,ana ta dariya,emmanual ya shigo wai controler na sallama da meena....ce ya shigo inji yaya....da gudu na tafi daki na azo after dress bisa kayan jikina,na dan gyara fuskata,ina fitowa nayi karo da yaya,wannan shegiyar rigar zaki sa?ko baki ga shara shara take ba.nayi baya da sauri duka kayan na canza na sako atampa,sannan na doro hijab har qasa wanda nake salla na fito. Ban tadda shi ba,sai da na isa falo na ganshi zaune sunci gaba da fira falon yaya na iskeshi,na sami kujera na zauna sai na hango ina fuskantar yaya gashi idanunsa na kaina,hararata kawai yake yi. Duk sai banji dadin zama wurin ba,gashi babu halin canzawa..ranki ya dade ya gida?,na dan sunkuyar da kai lafia lau ya aiki nazo ne maganar mu ko har yanzu ba'ayi shawar ba.. Nayi saurin dago kaina daidai lokcn da na qaara samun mugun kallo daga yaya controller baiyi mashi ba,abinda na ayyana ma raina kenan,ya fi son yaya muktar,saboda dazu sam bai nuna wata damuwa ba sai dai ma ya qara mana qarin gwiwa..lallai akwai abinda ya hango wanda ni ban hango ba,saboda shine yasan sa ciki da bbai Kinyi shiru ameenatu,ya katseni gabana ya fadi,saboda ina tsoron fadar masa maganar da zata hanashi dawowa,bazan so hakan ba kuma gaskia duk da ban taba jin ina sonsa a zuciata ba,toh haka ma babakiyayyarsa. sai dai tausayinsa da yafi yawa a zuciata, dabara ta fado mani,nace jiya na fada ma yaya tun da safe ya tafi garinmu,don sanar da su ainahin iyayenmu,yace sun nuna rashin amincewar su a yanzu sai dai a bari a ga kamun ludayin karatu na sannan. Maganar zuwa wurina kuma ance kaci gaba har zuwa lokacn da za'a baka damar turo magabatanka yayi murmushi cike da jin dadin kalamaina yace ba matsala,Allah dai ya tabbat mana da alkhairi nace amin muka yi dariya lokc guda,toh ni zan wuce daman abinda ya kawoni inji kenan,kin san mai iyali bai cika yin dare sosai ba,gudun kada a rufe masa qofa ya kwana waje,duk muka tuntsire da dariya nace yau kam sai kayi hakuri da rakiya saboda yaya yaa nan ba matsala ya fada tare da mikewa yana fadin zan ba emanual sakonki sai ya shigo maki da shi.nayi godia na wuce Nayi sum sum zan wuce daki,yaya yace zo nan dan ubanki ya nuna mani gaban kujerar da yake zaune daga qasa yace zauna ya dan tsirtar da miyau nace toh ai kaji kuma a raina ya kalli su anty,ku tambayeta abinda take nufi kamar me fa ya abdulla ya bukata wasan da take yi da hankalin mutane,ko baku lura ta maishe mu sakarkaru ba ita yar banza dazun na isketa da muktar makalkale da juna yanzu kuma...ya dan tsirtar da yawu,.ta gayyato yallabai wallahi yi mani shiru ko na harbar da ke,tunda aure kike so,shi zanyi maki marar kunya...ya qara tsirtar da miyau,na bata rai ya yunquro zai cafkonu,yana fadin wa kike yatsina ma fuska,nayi saurin yin baya na ruga,ya hayyako mani yana fadin,ai na rantse wlh sai na dura maki miyau a baki zan ga ta kyama Yau din ta kama asabar,wadda tayi daidai kwana 3 da shan fadan yaya,,wasan buya kawai muke yi da shi,ban yarda mu hadu,idan ka ganni falo,toh ya fita ne zaune nake gaban madubi ina gyara daurin kallabina,motsi naji nayi saurin juyawa,anty ce tsaye bakin qofa,ta qaraso cikin murmushi,kai kai kai wannan irin qamshi duk ya gauraye gidan,shiyasa turare baya maki auki,ke kullum yar sabtunsa ce,saboda ba'ayi masa arziki nayi dariya kai anty tace Allah kuwa,amma fa kinyi kyau ko baqo.... Bari yi mani fatan baqo anty ta dalla mani harar,wace irin magana ce wannan? ke idan kina warwarewa ki ware,wannan yayan naku ko auren bazai barku kuyi ba,ko baki ji yadda suka yi da abdullah ba?da yake shi yana da baki,dole ya shafa masa lafia tadanyi tsaki ni fita zanyi....ina zuwa anty.na katseta yayanku ya hana don ko abba ma zan barshi,saboda meetn zanje gida..kin san kuwa ko zan dawo sai dare yaya fa?na fada ckn tsoro..yana nan ai kin san wkend ne bai cika fita ba...ta dafa kafadata,Allah ya hada ku da wani irin yaya mai taurin kai,tunda ya rantse sai kin sha miyan sa kawai kiyi hakuri,iyaka idan ya zuba maki sai ki zubar babu dai dadi..amman ya kika iya..inda ma Allah ya taimakeki,d same mum n dad kuke dashi,,ai da yasha dake ta juya sai na dawo,na bita da ido kawai.na lallaba na shige kitchn nace,idan sun gama abinci sukai mana nawa daki na koma tare da kabbara sallar azahar Ina gama cin abinci na tattara kayan kaf na kai kitchn,ina son kwadawa abba kira,ina gudun kada yaya yaji..sai kawai na koma daki na hakura ina shirin tura kofa,shi kuma ya banko,nayi baya da sauri,,ina kwana wai ina wuni,,na fada duka dabarbace riqe yake da lemun kwali yana shaexotic orange..sanye da fararen kaya,dinkin rigar budadde ne,amma iyakar ta rabin cinya,sai dogon wando kansa ba hula..ya maida kofar ya rufe tare da banko mai wata uwar harara,daidai lokacn da yayi wurgi da kwalin alamar ya shanye,ki taso ki zo nan don ba zama ya kawo ni ba. Babau ko gardama na taso na iso inda yake tsaye don girman Allah yaya kayi hakuri wall... Zaki wahalar da kanki a banza,na farko zaki sha miyau na,sau goma,ko wanne minti 2 ne...zan rarraba maki shine ko kina iya daukar mintin goma? Ba tare da fargabar komai ba saboda na saduda nace zan iya..tare da tarba mashi hannuna alamar ya zubo cikin raina kuwa kira nake yi..tsakanina da kai Allah ya sakawa mai haqqi yayi yar dariya zaki iya mintin goman kin amince? Haushi ya kamani amman na daure ban nuna masa bacin raina ba nace eh zan iya.......... . wan nya..... Allah Ya kiyaye, a Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤4¤¤ Toh ni ba zan iya ba .ban san lokcn dana dalla mashi wanii kallo ba mai kamada harara,cike da ban haushi, nace shi iyakarka fiddowa ko toh zan iya tsayawa. murmushi yayi wannan karon bana son mu yawaita gardama..ki kalli agogo karfe nawa? Na harari agogo nace 2 saura kwata.yayi dariyar qeta toh kinga biyu saura minti 5 ne cikar lokaci na fashe da kuka..yace wlh ko na jini zakiyi yarinya kiyi amman babu fashi gaskiya ka tsaneni yaya..wannan abun fa bai halatta ba wani ya kalli kazantar wani..kinga ba wa'azi nazo kiyi mani ba.kin san hali na kada kikai ga bani haushi jikin kine zai yi tsami. Yaya! meena! shima ya kira sunana raina ya baci ga tsoro shi kuma da alama baya da niyyar yin hakuri dana ga babu Sarki sai Allah sai na sadaqas kawai rainin hankali watau duk yadda na dauki abun ashe shi ba haka yake nufi ba idanunsa jawur ya tsuran ido, sai na ga ya ficeda sauri, bancin ya gama zuba miyau a hannuna har na wasu mintuna..... Na daure ban ce komai ba! Yana fita, na goge hannu na, dan takaici na fada bisa gado amman na kasa kuka..sai dai ajiyar zucia....kai yaya balai ne abinda kawai zuciata ke ayyana mani kenan Ina cikin tunani abba ya shigo da gudu rike da littafinsa a hannu ya hawo gadon,yana ta dan rubutunsa har bacci ya kwashe shi,ashe nima ya kwashe ni...wai me kuka sha ne kuke ta bacci gidan anty ce ta tayar da ni...eh babu shakka don shima faruk na iske shi yayi daya daya bisa gado yana sharar baccinsa har da minshari..toh sai atashi don magriba tayi..ta dauki abba tayi waje da shi..na tashi na gabar da sallar magrib nayi ta lazimi har isha i tayi itama nayi. Ta kitchn nabi ,na tsaya daga tsaye na cika cikina da tuwn shnkfa miyar agushi.sai danaji nayi kat.sannan na wuce falo inda na jiyo hayaniyar su anty,wato hira tayi dadi kenan idan kaji ana irin wannan daga muryar koda anty ta hango ni,zungoro ya abdullahi da hannu tayi,yana waigowa duk sai naga sun kwashe da dariya, shi kuwa yaya ya dukufa latse latsen tashoshi a setlight.na karaso fuskana ba yabo ba fallasa na zauna yaya ga fa mutuniyar ka nan duk ta gama yan boye boyen ta fito tana tsoron shan miyau,,ya abdullahi ya fada tare da tuntsirewa da dariya bai dago ba balle ya tanka,ya ci gaba da yan latse latsen sa,na balla masa harara tare da wucewa wurin anty La! La! La! Yaya kagama hararar ka take yi murmushi kawai naga yayi an dai yi

Chapter 2 of 9