Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
da ruwa na markada likui-lukui,sannan na tace da matacin yadi mai laushi. A tukunya na zuba uwan gyadan,sannan na dumtso yar shinkafa babu wacce ba'a zubawa ta tuwo ko ta dafawa,amma ni da ta tuwon nayi amfani.Na dora a wuta na ce"Grace zo ki ringa motsawa idan ta taso kada ta zube"ta ce "TO" Da sauri.Fridge na nufa,dadi ya kamani da naga akwai abin da na je nema,woato hanta.Na debota da dama na wanke,sannan na yankata kanana- kanana sosai na zuba a tukunya.Kyan miyar a gefe na wanke su tas! su ma na yankashu kanana,amma ita albasar da yake ta fi yawa sai na yankata slice da fadi sirrin -siri.Na zuba ruwa kadan na dawo mai shi ma dai-dai na zuba yadda bazi yawa ba.Na san maggi onga guda daya da dan gishiri na rufe,na dora a wuta minti ashirin ruwan sun kafe na dan kara rabin kofi,sannan na zuba maggi star da cuury na kara rufewa.Nan dai gida ya rikide da kamshi.lokacin kunun gyadan ya dahu sai tashi yake yi gwanin dadi.Na saukesu atre da farfaesun hantar,kunun na fara zubawa a katon kwano na sa madara peak ta gwangwani har biyu da sugar sannan na zuba masa na shi a flask na sa nawa a cup su kuma na mikia masu nasu.Haka farfesun na shi a cookler,nawa a filet na sa a tunkunya su gane.Duk da abin da ya yi mini jiya wai na kasa jin haushinsa,ji nake kamar na shekara ban ganshi ba,a gurguje na yi nawa ganin har karfe tara kada ya fito ban shirya table ba,tsaf na hade wurin na kame a kujera inda na saba zama ina jiran fitowarshi.kuri ma yi wa kofafin biyu ko wacce zai bullo? ina nan zune har karfe sha daya da rabi,ko motsin bude kofar yasa na hanzarta maida hankalina wurin. Wani sanyin dadi ya ziyarci zuciya ta,fuskar nan washe ya kara kyau,kwarjininsasa ya fito fili.Ya hadu hundred percent(100/)na fada a hankali.jallabiya ce yar madina fara da irin hular nan tasu karama mai raga ta zagaye kansa idon sa manne da farin glass.jikin yayi lakwas lokacin da ya jefan da wani shu'umin kallo,anya ba makasata yake nema ba?kafin na lalubo amsa ya karaso ya zauna.I'm ready (na shirya) ya fada a hankali, duka da ya saba fadin haka kullum yau sai naji jikina ya dauki rawa, saboda yanayi yadda ya furta kalmar yau. ya tsareni da ido ko wane motsi nayi tana biye shi kenan na bani yau.Da kyar na gama hada masa.Na zauna ina son kallonsa,amma da na dago sai naga idanunsa na kai na har ya gani. kullum shi ke cewa Na gama"amma yau shiru ga shi ina son zuwa na dora na rana.Abin mamaki na kasa tashi daga wurin.Na saci kallosa,sai naga ya maida hankali a tv na kuwa ware idanu na ci gaba da kallonsa, ban san me yasa ba,ina son kallon fuskarsa,yana kara mini nishadi.So!lallai so babbar cuta ne.kafar muka hada ido,ya yi murmushi,kina jin dadin zama wurin ne?saboda na gama tuni"kunyar duniya ta rufeni na mike zan kwashe kayan,ya ce Ba fa korarki na yi ba,tambayar.... "Ban san ka gama ba,daman zaman da nake kenan.Ina jinsa lokacin da na wuce yana yar dariya,karfe biyu ya shigo kitchen ina harhada abincin a kuloli,zan je airport ki hada komai na mutum biyu,zan dauko babban bako ne"Da kyar na ce "To" saboda kasala.wannan matsala Allah ka yaye mini ita,mutum da ya yi magana shi kenan ya tafi da duk wani karfi?Gaskiya ba haka naji mutune na fadin so ba.Na kawata wurin gwanin ban sha'awa,ga abinci ya fi kala shidda.banda drinks na kwali da na gida sanye nake ciki farin material mai kwalliyar flower ruwan ganye,ina gyara daurin kallabi na ya leko ba tare da ya shigo ba,"ki fito ku gaisa da bakon". Bai jira na yi magan ba,ya koma.Haushi da ya turnikeni ban san lokacin da bakina ya furta, ka kaisu in kaya ne" ba.Ina fita na ware ido,wa zan gani? yaya Abdullahi ya hade cikin wasu track suit ya yi jawur,ga uwar kiba.Haba ban san lokacin da na sa a guje ba.na rikeshi,ina tsalle,kada ki kadani, don Allah" ko saurarnsa banyi ba.Sai da na gaji don karin kaina,me ya faruk zai mana ba dariya ba?A haka muka zauna ya ci abince,ya faruk ya mike,zan fita,bari na barku ku gana yan 'uwan juna.kada akai da fara nuna mini yan ubanci"Na shareshi nasan ni yaek wa habaici.Na zumbuure baki bayan fitar sa,shine tun da ka tafi ko waya?"Meena kenan,kina cikin wanan rikitaccen hali bazan iya kiranki ba,saboda kina iya kara rudewa ki tada mini hankali.yanzu kuwa da alama kamoi,zazzabi kawai nayi.ina labarin salma?kuna waya da ita ko?ya yi murmushi,yaya bai fada miki an sa rana ba last month? Da gaske kake ko wasa?" Na girgiza kai,Uhm-uhmwata nawa aka sanya?ya ce "hudu".yauwa lokacin muna hutun session kenan.ka hado lefenka daga can ko?ya bushe da dariya,wane lefe ga dan makaranta,in ba cin shirmen ki?"Anyo mana tsarba dai ko?"jakarrki daban ta na nan waje,tafi kowane girma.har kin saba da yaya ko?ya kikaji don Allah,wai ya faruk mijinki?Bari kai dai Allah yayi babban kwabo"Duk muka juya munakallonsa,har ya dawo.ya sosa keya,malam kaje ga kayanka can an kai maka daki ka shirya"Ni kuwa kunya ce ta koreni da karfi tsiya.Da daddare ya shigo mana da tsarabobi kowa tsalle,ba kamar merry uwar son kyauta.Ni kuwa kasar ce kawai ba ataho mini da ita ba,saboda katuwar jakace cike da kaya kala kala.yau ma ni kadai na kwana,damuwar yau ta fi jiya,saboda karancin baccin da na samu.karfe bakwai ya Abdullahi ya shigo ya ce,idan yaya ya tashi ace ya tafi Garhi daga can zai wuce kano,gobe jibi zai dawo.na ce,to a gaida Abba. Miskilancin yau ya fi na jiya,bakwai da rabi ya fito da shirinsa tsaf na zuwa office.sai wani basarwa yake yi,yana kalaci. hakan ya kara burgeni,aji sai mai shi.Mai makon yace,na gama 'yau din ma sai kawai ya miki,Na bishi da idanu ya waigo,"OFFICE".Na yi murmushi,ya maido martani yafice.iokn Allah yau kuma yanga ake ji"office".kawai aka fada tare da nuna kofa da yatsa,"ka hadu" Na fada a hankali.yau sha biyu na gama abince,na tura merry gidan maryam ta amso mini lambar wayar ta.ina lamba ta dawo,Aunty tace zata zo anjima" Tsawa na daka mata,"ke da na ce ki amso mini.....""Wall ahi na fada mata,lokacin da na je har ta fito get shi ne ta ce,zata biyo idan ta dawo".Na ce"Oho, i though shirme kika yi mini,je ki na gode".Har karfe uku bai dawo lunch ba,hankalina ya tashi,raina ya baci,wannan azaba da ya faruk ke gana mini ta isa.Wato tunda ya gane cewa, na kamu da ciwo sonsa ya ke garani kamar kallo,sai ma kara kaurace mini yake yi,kwalla suka zubo mini.A haka maryam ta yi sallama,cikinta ya fito sosai.Ganin halin da nake ciki yasa ta jani muka koma daki."Me ya faru kuma? kuka dai kullum abun daya ba canji? kani farau aure dole Meena?"kukana ya karu, "Maryam ba wannan ne matsalata ba yanzu" ta yi shiru,ki goge hawayen,yaushe zan fahimceki kina kuka haka? ya akayi kuma?kin gane......Na bata labarin abin da ya faru,sannan na ci gaba da cewa,tun daga ranar abubuwa suka canza mini,shi kuma ya fahimce ina son sa yanzu shi ne ya ke guduna,yanzu haka yau bai dawo cin abince ba.Abin haushi sai naga ta kama yi mini dariya.sai da ta yi mai isarta,sannan tace,yanzu me ne shawara? Duka na kai mata,don ta gama kuleni,idan ina da shawar zan kiraki ne?" Allah ya baki hakuri,ni a gareni kawai anjima ki bishi dakin sa..."Wallahi bazan iya ba maryam,wannan zubar da.....""a'a ke fa ce kasa,dole ki bi"."Don Allah canza mini sata,bazan iya wannan ba".:ki bari sai ranar asabar lokcin yana gida sai ki yi karyar ciwo ciki....."yau ma ina iya yi idan ya dawo".Na fada ina washe baki."period,kinga lokacin dazai rude,sai k kuma ki fara kukan shagwaba,ko ya ce zai kaiki asibiti kada ki yarda,ki san hanyar da zaki jawo hankalinsa,ki ce ya dinga messaging cikin zaki sami sauki,daga nan......"Ta ban hannu maka kashe muna dariya."maraym so babbar cuta ne.wallahi kinga kwan bakwai duka na tfara fita haiyacena.:. tun daxu naso shigowa amma network ya hanani yanxu ma da kyar na samu ya hau.... ada Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤13¤¤ Ta yi murmushi "shi kuwa nasa ya fi shekara sha wani abu" Na langwabe kai, "Bawan Allah".Ta kyalkyale da dariya,"meenar soye wa....""Maryam kin fa dameni"."Iye!!! sakayyar kenan?Da an soma miki mafita ko? zan kamaki,bani jakata".Haba mutuniyas bamu haka""ko zan hakura sai kin bani hakuri sau goma"Ba musu na bata,ta yi dariya,"Baekanki.Muje ki rakani kada maigidan ya dawo ya same ni nan""To me ye?"Na fada ina hararanta."ke ba zaki so ba,saboda kina fara lambo zan yi dariya.kinga ya gane plan ne abin"."fita-fita".Na turata waje muna dariya.Na saka mata ledar da na fito da ita bisa kujera,atamfa ce super wax kayan kwalliya,sai gyale kalar atamfar."kin san daga yau bazan kara amsar tarkacenki ba,ni kullum sai dai na zo a bani,amma ba ataba zuwa ind nake ba". Na sassauta murya."idan komai ya dai dai ta oga zaikawoni"muka tuntsire da dariya,ke nibani number kada ki manta"Ina gama rubutawata figi mota muna daga wa juna hannu.Anya bazai yi sauri dagoni ba? Marar lafiya an ci kyalli,kamshi ta ko ina? Riga da wando na saka cikin tsarabar ya Abdullahi,ruwan ganye (Lemon green) sun amshi jikina sosai.Na gyara kaina da man(morgans),kamshi kawai ke tashi.Ban yafa gyalen ba na bazo gashin bisa kafaduna,wani juma kwance bisa baya.Nasan duk duminiyarsa ya isa fitowa yanzu, ilai! zaune ya ke bisa kujera remote a hannunsa yan kallon labaru.Dan milki yau falo ake son cin abincin kuma? Na zuba farfesun kajin da yar soyayyar doyar exotic da robar ruwan kawai na rabe na dauki tiren.sai yatsina fuska nake yi,wai marar lafiya.kawai ya ci gaba da aiki abinci a ciki,idonsa kan tv,wannan mutumin wannan mutumin Allah ya yi maugu.Ganin ba shi da halin kallona yasa na fara na nishi a hankali ina rike ciki.ya dan waigo a kasale,what's wrong""cikina". Na fada har da matso kwallah.Daman kina samun wanan matsalar?Na girgiza kai."ya kike ji? Haushi ya fara kamani,amma na daure na ce."murdawa yake yi""sosai?"ya bukata Na ce,"Eh".kin ci abince kuwa?""Na ce mana".Na fada a hasale,zai tsareni da tambayoyi bazai zo ya kamani ba.:Dauko gyalenki muje asibiti""A'a,ba sai munje ba".Na fada ina 'yan duke duke."Ban gane ba sai mun je ba,haka zaki zauna da ciwo? Ai da an daddana mini cikin zan sami sauki".ya yi murmushi,"ke da baki taba irin wannan ciwon ba ya aka yikika san idan an danna zaki sami sauki?Na yi tsuru-tsuru,dabara ta fado mini,na ce,Na taba karantawa a wani litafi""ciwon cikin?"Na ce,Eh""To ni ban yarda ba,dole mu je asibiti"Na langwabe kai,Allah yaya da anyi mini zan war ke"Dariyar da yake guntsewa ta kubuce ya ce,jeki daki ina zuwa.LOKACIN TASHI YAYI SAI ANJIMA IDAN NA FITA DAGA SECOND OFFICE DIN NA. Dadi ya kamani, na dan gyasa da kyar da kyar nashiga daki, nayi saurin canza rigar bacci na kara turare a jiki na kwanta, gabana sai faduwa yakeyi tawa ta sameni yau, ga dadi ga tsoro, a hnkl naji an bide an shigo, na runtse ido ina yan juye juye alamar ciwon na damuna. Kamar daga sama naji wata siririyar murya na fadin, "Aunty" ni tsoro ma yasa na ware idanuna duka, merry ce tsaye da daurin gaba alamar bacci takeyi aka tadota, na ce, me ye? Oga ne yace nazo na danna miki cikinki, na tashi zaune, me? Ta maimaita, bansan lkcn da na sirfa mata zagi ba, kamar itace tayi mini laifin ba shi ba. Sannan na daka mata tsawa" will you get out from here b4 i break your leg or not?" a guje ta fice tana fadin sorry aunty. Shin da wannan bakin cikin zanji, ko da tsananin sonshi dake damuna zan ji? Abu kamar wasa komai sai habaka yakeyi. daren nan na ci kuka kamar raina zai fita, kafin safe idanuna sunyi luhu luhu, da safe naki hada kalaci, lkcn da zai shigo na fada toilet nayi zamana, ya gaji da jira ya fice inaji yana basu grace sako, idan na fito ace ya tafi office, sbd tsoro babu wacce ta tunkareni da mgnr, na kira maryam ina kuka na zayyana mata duk abinda ya faruk yayi mini kiyi hkr zan shigo da daddare mu sake shawara nace toh. Dadi ya kamani,na dangyasa da kyar na shige daki.Na yi saurin canza rigar bacci na kara turaren a jiki na kwanta.Gabana sai faduwa yake yi,tawa ta sameni yau,ga dadi ga tsoro.A hankali na ji an bude an shigo,na runtse ido ina ;yan juye-juye alamar ciwon na damu na.Kamar daga sama naji wata siririyar murya na fadin,Aunty!"Ni tsoro ma yasa na ware idsnuna duka,merry ce tsaye da daurin gaba alamar bacci ta ke yi aka tadota,na ce, me ye?"Oga ne ya ce na zo na danna miki cikin"Na tashi zaune,"Me? Ta maimaita,ban san lokacin da na surfa mata zagi ba, kamar ita ce ta yi mini laifin ba shi ba.Sannan na daka mata tsawa, "Will u get out from here before i break ur legs or not ?"A guje ta ficetana fadin "sorry Aunty".shin da wannan bakin cikin zanji,ko da tsananin son shi da ke damuna zan ji?Abun kamar wasa, komai sai habaka yake yi.Daren nan na ci kuka kamar raina zai fita,kafin safe idanuna sunyi luhu-luhu.Da safe na ki hada kalace,lokacin da zai shigo na fada toilet na yi zamana.ya gaji da jira ya fice ina ji yana ba su Grace sako,idan na fito ace ya tafi office.Saboda tsoron babu wacce ta tunkareni da maganar.Na kira maryam ina kuka na zayyana mata duk abin da ya faruk yayi mini."kiyi hakuri zan shigo da daddare mu sake shawara"Na ce,"To" karfe goma ya Abdullahi ya dawo,ke kuma me ya same idon ki? Ban san dalili ba,bana iya fada mishi tsakanina da ya faruk,kunya nake ji."ciwo suke yi"Na fada kaina kasa,da kyar na maida kwallan da ke barazanar zubo wa."ki na murzarsu ne halan?"Nace,"kai kayi naji shi ya sa""To" ga ya nankinje sun kumbura"ya miki,Bari na amso miki magani"Da kyar na iya furta,yaya ya sowa mini,na sanya kuma akwai na sha"kin tabbata? ya tsareni da ido,kamar bai gasgataabin da na fadi ba.Na ce,"Da gaske ne Allah""ok,sanya a kawo mini break yunwa nake ji" Na ce "To" Na mike.yana gama kalaci ya ce zai je gidan su salma ya dawo.Na yi murmushi,a dowa lafiya.Alkubus na yi da rana miyar kaji,mai kunshe da ganyen alayyahu.ina gama shirya table din na yi komawa ta daki.zuciyata ciki da son ganinshi.amma na daure.gabana ya ci gaba da faduwa lokacin da na ji higo war motarsa.wato yau an gama damar zuwa kan lokacin duk abin da zai yi sai dai ya yi bazan serving dinsa ba.wayata ta fara rero wakar mtn ce,ko ban tambaya ba nasan shi ne,saboda.... ta i gaba da ruri Na dauka a fusace.Hello" ya kwantar da tashi cikin wani irin salo,Ranki ya dade azo a bani abinci". kafin inyi wani yunkuri ya kashe.Na kalli wayar na yi murmushi, shu'umi kenan". Zaune ya ke ya bada baya cikin bakaken jacket da wando,ko kallonsa banyi ba,na ci gaba da zuba masa ina tura mishi gabansa har na gama Na juya zan bar falon,ya mike,idan baki dawo ba,zan bar miki abincin kin nan na koma office"Inda ne ko ance ya fadi haka bazai fara ba,amma yanzu da yake ya gani bakin zaren shi ne zai mini wata barazana.Ni ban zauna ba,ban kuma tafi ba,ga ni nan tsaye shi ma haka,ina zama ya zauna na kaalleshi.ya sadda kai yana cin abincin fuskarsa kunshe da murmushi.""wann an murmushi wai ne me ye ma'anar sa?idan ya ganoni me zai hana ya basar mu ci gaba da rayuwamu, amma don mungun ta kullum daga dariya sai murmushi."kana wahalar da ni ya faruk don Allah....."ya dago ido muka hada, na kawar da nawa,"wannan kallon ai sai ki sanya na kware" ya fada.Murmshi nayi,"Ni ba kai nake kallo ba.wancan frame din nake kallo na bayan ka"yar dariya kawai yayi.ya ci gaba da cin abincisa,na kara tsareshi da idanu ina kallon yadda ake cin abinci da yanga kamar wani mace.kai wannan mutuni akwai kankanba da feleke."ina labarin ciwon ciki? ya na raina mini wayau banda wulakanci da ya yi mini bazai ce ya jiki ba,sai ina labari? Na daure fuska,yana cikin redio kasan shi labari a redio aka fi jinsa ni kuwa...."Na ciwon ciki na ce ni ba wani......""ok yana hannu merry" ya mike,Allah ya baki hakuri,ba fada ba ne abun zan koma office""A dawo lafiya" Na fada ina kallon kujera da ya tashi. . Lallai, meena karki bada mata!!! Sadin Ma. a Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤14¤¤ Ya mike ok Allah ya baki hkr,ba fada bane abun zan koma office. A dawo lafiya. Na fada ina kallon kujerar daya tsh. Na bishi da kallo yadda ake wani rangwada da kasaita kmr wani sarki, wannan mutum sai dai a barshi inda yake. Krf 7:30 maryam tazo, naji dadi kwarai, ya kike ganin zan bullo wa wannan matsalar maryam? Ta tallabe habarta da hannu daya tana kallona, abun ba krm bane meena, sbd babana ya fhmc kin kamu da mugun sonsa,shine yake garaki,bawai donki wahala ba,a'a kawai yana son garkuwa mai amfani cikin zuciyarki.... Bai mini adalci ba wlhy,abinci wannan bana iya ci kullum tunani, ke ni abinda yafi damuna kallon da nake yawan yi masa,wanda bana iya dauke idanuna a kansa dai dai da second idan muna tare. Shi kuma dizgi,ga kuma wani hali daya tsiro na ko'in kula. Kin jahilceshi,ba haka yake nufi ba,shifa ya gama tasa whlr ko ince aikin,wannan ya rage naki yanzu. Banza! Kina da wannan sirrin kike wahalar da kanki? Nayi murmushi matsalata kananan kayane, bani da ko1 kuma da kyar zai barni naje kasuwa, nawa duk inna ta rabar dasu koma wata garhi. Turare fa? Ta bukata, ina da su kala kala na bata amsa, to ki fara, nikuma zan kawo miki english wears next week idan aunty sun dawo daga turai, karfe tara na rakata ta tafi, na dawo yana zaune falo remote a hannunsa, daman tun da zamu fito maryam ta sa na canza kaya, material riga da skirt sun matseni kamar zasu tsage komai nawa ya fito fili, ga wani kamshi da ke tashi ko ina, falon duk ya hade, ko kallabi babu a kaina, ina dawowa na wani fada bisa kujerar dake kallon tasa wato 2sitter, gashina ya watso a fuskata, yayi wal! Da ido cikin wani asirtaccen kallo, nayi saurin maido masa martani, nan da nan ya dafe kai tare da runtse ido, kamar na kurma ihu dan dadi, haba mlm yau kai zaka kai ni daki, zanyi baccin karya ne dole a tadani daga nan zan fara gigin bacci me hade da shagwaba, karaf zan kamaka a tarko, na kwanta cikin salon yaudara kaina kaina bisa hannun kujerar, idona bisa silin, ya bude ido na dan kalleshi, yayi saurin maida nasa a tv, haka muka zauna yanayi yana satar kallona, nima haka, daga nan na runtse ido ina saukar da numfashi kamar dai mai baccin gaske, shiru shiru naji ya tashi, har baccin gsk ya saceni, matsanancin sanyin da ke ratsa jikina yasa na bude ido ina laluban bango, saura kadan na fado kasa, da sauri na mike ina 'yan waige waige, falon dundum an kashe fitila da kyar na lalubo ma kunni ina mamaki ko shima nan.... Wayam ba kowa lkcn da haske ya gauraye ko ina, tsoro ya kamani naruga daki, dole na hkr da ya faruk ko shi ne autan maza, wannan wulakancin ya isa haka, baccin da ban koma ba kenan, har aka kira sallar asuba. Abu kamar wasa, duk wata hanya da nake tunanin zan bullo wa ya faruk nabi, amma ba wani cigaba, aikina kenan ya basar ko yayi pretending bai gane ba, kaina ya dauki caji sosai, kullum tunaninsa, ga ciwon sonsa dake damuna,kullum sabo yake komawa, krt ya tasoni gaba yau saura kwana ashirin daidai mu fara exams, bikin ya Abdlh kuma saura kwana 30 daidai, kamar kullum mun fito daga lectures, maryam na ciki tana ba idris nono, wanda ake kira babawo, hassana hassan ta karaso inda muke zaune ni da surayya lawal albaba, wai Allah ya taimakemu m2mnan yayi covering, Aisha sani saulawa tayi murmushi, bari ke dai daman shi kadai ya rage mugun, jinsu kawai nake yi amma sam hnkln yana ga ya faruk, Allah ka yassaremin wanan wahala, abnd nake ta nanatawa kenan, Aminatu zo mu wuce hostel sai exams kenan ko? Na dan ritse ido alamar tunani kafin ince " may be na shigo krt" ok idan maryam ta fito kice mun wuce ba matsala na fada ina 'yar dariya. Suna wucewa naci gaba da tunani, aure har mun kusa shiga wata shidda ace ba...... Thinker meye kuma? Nayi saurin mikewa ina dariya, na karbi babawo da ke faman miko mini hannu yana dry alamar in daukeshi, na koma na zauna, itama ta raba kusa da ni, meena kin cika girman kai, ki dubi ramar da kikayi duk kin lalace sbd mugun tunani, kinsa wa kanki tunani, kinsa wa kanki damuwa, nayi murmushin karfin hali, idanuna sukayi jawur alamar bacin rai "maryam kenan kina ganini laifinane while ni a wurina banda shi? Kinsan Allah ko mutuwa zanyi, sai dai na mutu, amma bazan taba kai kaina ga ya faruk ba kamar yadda ya ke tunani, yana sona shima takura yake, amma sbd tsabar rainin hnkl ya kasa tunkararta, na kalleta idanuna sun kara rikicewa maryam shi namiji ya daure sai ni mace? Duk miskilancimsa da jiji da kai, wlh na fishi. Baki ma san wani abun haushi ba, ynz daya fahimci ina son zama falo idan yana nan, kawai sai ya fara waya da 'yan matansa har wani i miss you, yake fada, don ya maidani..... Thinker meye kuma? Nayi saurin mikewa ina dariya, na karbi babawo da ke faman miko mini hannu yana dry alamar in daukeshi, na koma na zauna, itama ta raba kusa da ni, meena kin cika girman kai, ki dubi ramar da kikayi duk kin lalace sbd mugun tunani, kinsa wa kanki tunani, kinsa wa kanki damuwa, nayi murmushin karfin hali, idanuna sukayi jawur alamar bacin rai "maryam kenan kina ganini laifinane while ni a wurina banda shi? Kinsan Allah ko mutuwa zanyi, sai dai na mutu, amma bazan taba kai kaina ga ya faruk ba kamar yadda ya ke tunani, yana sona shima takura yake, amma sbd tsabar rainin hnkl ya kasa tunkararta, na kalleta idanuna sun kara rikicewa maryam shi namiji ya daure sai ni mace? Duk miskilancimsa da jiji da kai, wlh na fishi. Baki ma san wani abun haushi ba, ynz daya fahimci ina son zama falo idan yana nan, kawai sai ya fara waya da 'yan matansa har wani i miss you, yake fada, don ya maidani..... "mts" ta ja tsaki.kada ki bani kunya. Be a wise mana,makircin maza kuma? Yanzu haka ke ya maida waya,ko an taba bugowa? Nace "a'a, kullum shi yake kiransu" Makircin ne yana son ki nuna kishi akansa ne, a tunanina yana jarabaki ne yana auna irin son da kike mashi" "ya kuwa ganewa idonsa,don kuwa jiya tsakin da na ja ai da ya tsorata shi, nabar falor afusace. Don wulakanci ko yi hakuri maganar kenan. " you see,amma bari na baki shawara, ki dan ringa tura masa txt masu dadi, kamar Guudmorni,gud nyt, hav a pleasant day da sauransu. "zan kwatanta amma da kamar wuya" "jst try" Nayi murmush "zanyi insha Allah" har mun mike zamu tafi,na rikota" maryam ina cikin matsala, ya faruq na gasani." Tayi yar dariya, " wata rana sai labari,idan da laifinsa kema da naki." nayi saurin wucewa ina fadin, "zan zo mu yi discussion course din Doctor" "ba matsala" ta bani amsa. Karfe biyar da rabi na isa gida, nayi kicibus da Ya Abdallah shima ya taso daga wurin aiki, muka karasa tare. " Ango ka sha kamshi"na fada inna dariya lokacin ina kulle motata. Ya kyalkyace da dariya,"Amarya,matar yaya,aunty meena." Na galla masa harar"a'a inna ba aunty ba" "oh sorry inna meena". Ya maimata cikin zolaya. "kai dai kaisu in kaya ne". Muka wuce ciki tare ana raha. Zaune ya ke bisa table yana shan fruits salad daga shi sa vest da wando three quater dukkansu farare. Ya yi kyau har ya gaji. Yadda muka shigo muna fara'a shima ita yake yi, da alama tamu ce ya ara. Ya yi rangwadar da kai zai yi magana,manya sarakan feleke kai ya faruq da mace ne wallahi da an bani dan yanga, magana ma sai an yatsina fuska, idan abinci za a ci ana kilbibi. " lafiya kuke ta washe hakora kamar 'yan talla makilin" Yadda ya fadi maganar yasa ni yin dariya,ya bina da ido cike da sha'awa, "gulmamme" na fada a rai. Wai don na kirata anty shine ta ce ,ba inna ba? Ka ji fa?. " a ina ta zama aunty?" ya bukata idonsa na kaina. " saboda matar yaya ce" ya abdallah ya fada yana dariya." "girman kanta da zurfin ciki ya hana ta zama aunty har yanzu"." ni kadai na gane inda ya dosa. Kuwa ya abdallah sai cewa yayi"kyaleta, duk abinta aunty zance,idan kuma inna take so sai mu fada. Yadda ya fadi maganar yasa ni yin dariya,ya bina da ido cike da sha'awa, "gulmamme" na fada a rai. Wai don na kirata anty shine ta ce ,ba inna ba? Ka ji fa?. " a ina ta zama aunty?" ya bukata idonsa na kaina. " saboda matar yaya ce" ya abdallah ya fada yana dariya." "girman kanta da zurfin ciki ya hana ta zama aunty har yanzu"." ni kadai na gane inda ya dosa. Kuwa ya abdallah sai cewa yayi"kyaleta, duk abinta aunty zance,idan kuma inna take so sai mu fada." Da gudu na fada daki ina jin ya faruq na fadin, "meena kena", daga ji yadda yake maganar ta fito na gane dariya yake yi. Toilet na shiga, na yi tsugunne lallai maganr maryam ta fito,ni kadai yaya ke jira. Dole in bi shawararta............ Kaman ya? Na tambayi kaina. Dabara ta fado mini, na yi wanka na fito,ina gama shiri na yi tafiya ta gurin su grace muna hira. Sai sha daya na dawo. Karfe 12:15 na gama nafilfilun da na ke yi ko wane dare kafin na kwanta. Ina hawa bisa gado na lalubo wayata a hankali na fara tsara txt kamar haka. "Salam, bacci kake yi?" Ko in tura masa? Na tsaya tunani,wata zuciya ta ce. Eh,wata kuma a'a. Kawai na rutse ido na tura. Abin mamaki ba a fi minti 1 ba,ya maido amsa "ido na biyu." na kara tura masa "me ya hana ka bacci?" sai ga amsa "kin ban dariya, ke me ya hanaki?" " ka fata amsa tambayat" na mayar masa " To saurara, abinda ya hana ni bacci shi ne tunani, tunanin abubuwa da dama. Hope kin gamsu, ke kuma fa?" ya tambaya. "maganarka ce ta dame ni." nayi saurin tura masa "wace magana kenan?" "wanda kace wa ya Abdallah, girman kaina da zurfin ciki sun hana ni zama aunty." "meena baby! Kin bab dariya har da kyalkyatawa. To sai me don na fada haka? Baki da girman kan ko kuwa baki da zurfin ciki?" " gaskiya bani da su, don ba hali na bane" na ba shi amsa " na fahimce ki, to ki yi hakuri amma idan har da gaske kike don Allah zan miki yan tambayoyi?" na ce "ba matsala, go ahead". "mene ne SO?" Na zaro ido,lallaiwannan mutumin. Me yake nufi????????????????? Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤15¤¤ Ya kara turo mini da" ke nake jira,marar zurfin ciki da saukin kai." Nayi dariya,"So abu ne mai wuyar fasarawa,saboda duk wanda ya fada wannan tarkon zan iya kiransa'SORRY' ina turawa. Ya maido mann " ban gamsu

Chapter 7 of 9