Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
Allah yaya baka ckn tsarin mazan da nake so in aura ta fannin kyau, kudi, ko wani abu wanda ya shafi wannan bangaren, sai dai kawai kullum nakan yi maka addu'ar Allah saka maka da alkhairi bisa ga rikon da kayi mana ni da dan uwana, ta hnyr ba mu ilimi da tarbiyya mai kyau kasan a rayuwa... Babu tsammani muka jiyo sallamar ya mukhtar. Kafin hafsa ta rufe bakinta wurin amsawa ya kunno kai a dakin, ganin yadda mukayi tsaitsaye fuskarsa ta nuna alamar tsarguwa. Hannu kawai suka ba wa juna ya juya ya bar dakin. Da yake ba kwana yaya mukhtar ya yi ba a ranar ya koma, amma kafin ya tafi sai da ya kara jamin kunne da na bi a hankali sosai, to ka wai na bishi dashi, ya faruk kuwa bamu qara ganinsa ba sai dare, misalin karfe takwas muna kwance daki na ji Baba na kwallan kira, da hanzari na fito a rude, kila wani abun ya kulla, abin da kawai zuciyata ke bani kenan har na iso tsakar gida inda ya ke zaune bisa tabarma yana cin tuwon dawa miyar lalo. Baba na gani na fada tare da tsugunna wa gabansa, ina ta zaro ido kansa sunkuye yana lomar tuwon ya ce Faruk ke kiran ki a waje, ki amso sako.na danyi shiru lkcn ne ya dago muka hada ido, ko baki ji abinda na fadi bane? Naji Baba na fada a sanyaye, tare da mikewa nayi waje, da man akwai yar karamar hijabi a wuyana. Ko da ta isa gurinsa, ya tsareta da. Idanunsa kamar zaiyi kuka, ya ce ki taimaka ki ceci rayuwata, wallahi ina matukar kaunarki, ta amsa masa da cewa gaskiya yaya kayi hakuri, ba zan iya zama da kai amatsayin mata ba, ina, ba zai yiwu ba, ya sunkuyar da idanunsa yana hawaye, can kana ya mike ya goge hawayensa ya ce, na gode kanwata, Allah Ya baku zaman lpy da shi wanda ki ka ce kike so... Kawai ya fice hawaye na cigaba da zubo masa. Nan ta ji tausayinsa ya kamata, da ta koma tunowa da Yaya Mukhtar inta, sai tayi murmushi ta shige ciki. Akwana atashi ba wuya, ana ta shirye shiryen bukin Mukhtar da Meenah.. Sai murna suke, amarya da ango, shi ko farukh bai kara ko lekowa gidan ba sai ana saura kwana 1 da daurin aure, ya zo mata da kudi masu yawa cikin enbelop, ya ce gudumuwarsa, sannan da kayan daki ma duka shi yayi.... Ranar daurin aure yazo, aka daura aure..... Amarya sai lokacin ta danji hankalanta ya dan kwanta, manya da iyaye duk suka ja mata kunnuwa da zaman hakuri gidan miji, ta hakura da dukkan abunda ya shige mAta ta fawwalawa ubangiji mai kowa mai komai, sannan kowa dai ya fadi bakinsa, kamin a dauki amarya akai gidan miji.... Ahaka aka tafi da amarya da a lullube har aka kaita aka baro dakinta, tana lullube.a hakan tana jin kirjin ta na bugawa, ko maiye dalili ta kasa tantancewa, da ta tuno yanzu yayaMukhtar ne Angonnata sai ta dan ji sauki, amman bugun kirjin yaki tsayawa.. Can ta ji anshigo, ta kara nokewa cikin lullubinta ta na jin kunya, ko da ya zo kusa da ita kanshin tularensa ta shaka ta lumshe ido, tana fadi cikin ranta, yau kuma irin tularen Yaya yasa... Kawai taji ya bude lullubin a hankali, ya sa hannu ya daga habrta, ta lumshe ido, sai cewa yayi, Ina farin cikin zamanki amatsayin mata a gari, ina son..... Kawai ta bude ido, ta ce Yaya Farukh me kake yi a dakina?????? da Hada Hausa Book stories GIDA BO KOSHI BA ¤¤10¤¤ Ai kuwa, ta rude shi kuwa sai murmushi ya ke, ta soma tunanin rabonta da sa Yaya mukhtar a idonta tun ranar da ya ya gargadeta da karta yarda Yaya farukh ya rudeta da kalamansa, nan ta tuna ko shirye shiryen bukinma awaya suke magar, kullun ya ke cikata da kalamansa na soyayya, can sai ta ce, ko dai bakinsu daya da yayafarukh..... tunanin me kike haka? Maganar sa ce ta dawo da ita hayyacinta! Ya ce ni Farrukh ni ne mijinki ba mukhtar ba! Nan da nan ta soma matsanancin kuka, tana fadin ba na sonka, ba na sonka, kuma ba zan taba sonka ba, ka cuceni ka ci amanata, kuma ba zan taba yafe maka ba, kuma dole ka sallameni ya...... Ba ta karasa ba ya rufe mata baki da tafin hannunsa, kawai ta galla mai uban cizo, nan ta rapka mishi kyawawan mari ba adadi..tana kara kai masa duka a kirji tana kuka, sai da ya bari tayi mai isarta sannan ya rungumeta yana kokarin lallashinta, kawai ta tureshi sai da ya bugu sosai kamar ba mace ta turashi ba, ya durkusa yana kuka kaman wani mace, yana bata hakuri, meena kiyi hakuri, ki min kowace wulakanci, amman ki daina ambaton saki,,,,, nan ta yi shiru tace ka fitarmun daga daki ban son ganinka... Kaman wani soko yace tom ya fice, a haka kowanne ya kwana da takaici.(Daren farko) Akwana a tashi gurin Allah ba wuya, yau watanninsu shida da aure, wulakancin yau daban na gobe daban, shi ke mata komai, kai wani sa'in har sashi girki ta ke shiko yana biye mata saboda so da kauna, a hakan ta soma makaranta, en wajen aikinsa ma duk sun san yadda ya ke ji da ita, ita kuwa ko a jikinta. Abu daya ya daure mata kai har yau bata kara jin motsin yaya mukhtar ba tun wancan lokacin. Wata rana tana dawowa daga makaranta, ta samu go slow. Dai dai cikin go slow din wata mota ke kusa da taa ta, wani ta hango kaman yaya mukhtar yana washe baki da wata kusa da shi, zance suke akan zai aureta, abin ya daure mata kai, nan yake cemata kema kin san ke zan aura, er uwarcan tawa ma ba wani sonta nake ba tun lokacin balle ma da yanzu na huta tayi aure tuni!!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un abunda kawai take ambato ke nan, can ta kwala masa kira Mukhtar!!! Ya juyo, ko da ya ganta, be wani damu ba, sai suka cigaba da tafiyarsu.... Ita kuwa da kyar ta kai gida, kanta na mugun sarawa ta ji zazzabi ya lullubeta, kawai ta kasa daurewa ta kira layin hafsa ta zayyane mata komai... Nan hafsa ta soma kwantar mata da hankali, ta ce ai daman halinsa kenan amma, Ki dai kwantar da hnklnki,ki kuma kama mijinki,wlh meena kowa sai cewa yakeyi,kun dace da juna, kuma kinyi sa'ar miji. Dangi kmr su cinyeku da mgn. Ngd hafsa. Na fada a sanyaye na kashe wayar. Na rasa me zanyi,kuka ko me? Hnklna idan yayi dubu tashe yake,kafin kace me? Zazzabi ya dawo,jiki ya fara rawar sanyi ga matsanancin ciwon kai. Kudundune nake cikin bargo,jikina kuwa kmr mazari rawa kawai yakeyi. Haba shi yasa ya mk baya zuwa saina roka,shima a gurguje zan gnsh,duk dadin bkn da yake yi mini wato yaudara ce,lallai maganar yaya ta fito, da ya ce cikakken dan duniya ne. Yana da wacce yake so zai aura a legos,ni haukan banza nakeyi kenan? Kullum hnklna yana kansa,na damu kaina akan ya shiga wnai hali,kokarina kullum ya faruk ya hkr ya sallameni, kai jama'a ashe ya manta da ni yana can ya rungumi budurwarsa ta gsky. Wai ko ya aureni daman ya making mind dinsa sai ya aureta,kenan ni dole na zame masa ba don yana sona ba.ita ce yake wa son gsky. Kwalla suka zubo mini,ina zan kai hakkin ya faruk? Mutumin da yasan ciwon kaina,yake kaunata kmr ransa,shi yasan cina,shana,sutu ra,lafiyata da kuma ilmina, bai taba gajiya da ko daya ba kullum kara nuna min kauna yake ina gwasale shi. Yau kadai ta isheni ishara,da gayya nace, Fura zan sha. Amma ya tafi ya nemo mini, don na bata masa rai naci indomie kada furar ta samu shiga,bai nuna damuwa ba,dukda wannan bai yi fushi ba,dai da ya tmbyni me nake marmari. Na ci kuka kmr raina zai fita,ciwo kuwa ya karu musamman ciwon kai,sbd uban kukan da nake faman ruzga. Ina nan kwance har aka kira sallar azahar,krfe 1:30 naji karar shigowar motarsa,lkcn nakai makura a galabaita. Ji kake jim jim ana ajiye kaya lkcn daya shigo. A tunaninsa bacci nakeyi,ina jin ya zauna bkn gado yayi shiru. Nishin da nake yi ya jawo hnklnsa,da hnzr ya hawo gadon tare da yaye bargon, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Meena jikin ne haka? Cak! Ya daukeni bisa kirjinsa kmr wata 'yar yarinya,turarensa ya kara rikitan kwalwa. Gudu gudu haka ya fito dani ya saka mota,kmr wanda ke shirin tseren motoci ya figeta a guje mukayi asbiti. Yan aikin gidan kowa yayi cirko-cirko, kamar mahaukaci ya daukieni da gudu yana fadin, Doctor! doctor! doctor!" fitowar likitan yasa shi yin shiru, "please duba mini ita, jikinta yayi zafi da yawa,ta galabaita doctor taimaka""kwantar da hankalinka yallabai,komai zai zama normal muje wancan dakin". muna shiga ya kwantar da ni bisa gado, na dan kalleshi a galabaice na maida idona na rufe ciki da matsanancin tausayisa.Babu bata lokacin likita ya fara aikinsa,ya sanya mini karin ruwa da allurai,daga nan bacci yayi awon gaba da ni.Ban farka ba,sai wajen biyar na marecce,zaune yake bisa kujera daga gaban godan ya tallabe fuskarsa da hannuwa yana kallo na.Ganin na bude ido ya sauke hannun tare da matsowa,"yaya dai meena? jikin da sauki ko akwai matsala?" "da sauki,jikin ne dai kawai ba karfi""Dole ne wannansai a hankali zai koma normal.Ga furarki na dauko miki,ko ice-cream din zaki fara sha? "zan sha furar"Na fada a hankali.ya tallaboni ya jingina mini filo,sai da ya bani ruwa da roba na kuskure baki na,sannan na sha furar wadda shi ne ke bani ita a baki.Na kura masa ido ina kallon sa ciki da tausayi, idona yayi narai-narai alamar kwalla.yayi murmushi,"ya ya dai ?tsikar jikina ta tashi,na ji wani abu yana ratsa jikina kamar an tsikaran allura."Me ne ne? ya kara fada a hankali, nayi saurin sunkuyar da kai ina murmushi."surpr ise!!"ya fada a hankali.Na dauke kaina alamar na koshi, ice -cream din fa,na miko? Na dago kai alamar "Eh".Duka robar na shanye yaji dadi haka,sannan ya maidani na kwanta,"Bari naje gida na dawo kinji? Nace to.A hankali. Ya yi dariya tare da girgiza kai, ya fita yana dan waiwayena,ko mamakin kallon da nake yi mishi yake yi?Na tambaye kaina.kawai na sami kaina da jin wani irin nishadi da annashuwa na nemi ciow na rasa,kawai matslata rashin karfin jiki.Na lallaba na sauko na shiga toilet na yo alwala,ina sallame sallar la'asar naji motsin bude kofar. Merry da Grace ne gaba su Emmanuel na binsu a baya,rike da ledoji.Grace ta ajiye ta hannunta,wadda ke dauke da kula katama da babba, sai mercy ta rabe tata lemu ne da ayaba, apple da kuma inibi a ciki.Su Emmanuel kuwa lemuke ne da kayan tea a cikin tasu. "Sannu Aunty" Nayi murmushi,tare da mikewa ina linke hijabin,yauwa merry,ya gida?Ba ta amsa ba,su Emmanual suka fara,"SannuAunty,Allah ya baki lafiya". Nace,Amin". "Oga ne ya kawo mu yace,ki yi hakuri zai je ya dawo yanzu,bazai dade ba" Nace "ba matsala" "Ga abince nan yace mu baki kice,kafin ya dawo"."Me ne ne? Na bukata ina da yatsina fuska,don ba kamai nake son ci ba."Farfesun koda ne soyayyen dankali,akwai kuma yamballs a ciki" Na fadada murmushina,"Amma kun kyauta,kamar kunsan abin da nake son ci kenan".Grace ta cabe,Oga ne yace ayi miki,wai shi ne best food din k""Zuban na ci bada yawa ba" Na yi hakan don kada zuciyata ta samu nasarar nazarin wani abu.Naji dadi abincin nan sosa,saura kadan na karasa cinyewa suka turo kofa,Alhaji Habibu ne da Aunty Asiya, sai Alhaji Garba da Aunty Hadiza matarsa,shi Oga ne karshen shigowa.Very good,taci abincin ko merry?"Ta rusunar da kai "yes Oga.ya zauna bakin gado, sannu meena,ya kike ji yanzu?.Duk kunya ta kamani yadda ya wani shige mini,na kasa magana, Alhaji Habibi ya ce,Malam ka fa takurata......"Me ye takura anan Habibu? Alhaji Garba ne ya katse,duk suka matso bakin gado suna fadin,sunnu Amin".A hankali nake fadin yauwa"Aunty Hadiza ta kara matsowa, "Wata nawa ne Aminatu? "Sam ban fahimci tambayarta ba,nayi tunanin ko maganar hutun makaranta ne takeyi,nace sati uku aka bamu" Duka suka kyalkyale da dariya.ya faruk ya dafa kafadata,"wai cikin suke magana,wata nawa.......""Wallahi bani da ciki"suka kara yin dariyar.Nan da nan na kule,wannan wane irin wulakanci ne,me suke nufi da ina da ciki,ko na zama yar'iska a nufinsu?Rainin hankalin yayi yawa,a gabansu Merry za'a ci mini fuska?"Na fada musu ba ciki gare ki ba,amma sun ki yarda"ya kalli Aunty Hadiza,"kun yarda yanzu ko? Ni idan nayi karya ita ba zata yi ba ko?.Ai duk bakin ku daya".Alhaji Garba ya fada.Na sunkunyar da kai na saki ajiyar zuciya a hankali,sai yanzu na fahimcesu.Basu bar asibitin ba sai bayan isha'i,nayi ta mamakin irin rudewar da yayi akan ciwon nan,har da tattaro su Aunty.Da zasu tafi ko wane ya ajiye mini rafar kudi. Alhaji Habibu ya ce,"mun dai zo wannan da tsiya tunda tashi na kamaka aka yi mana,da bamu zo ba mun shiga uku".suka kyalkyace da dariya.yaushe zaka dawo ta arziki tunda wannan ta tsiya ce?Gobe zamu koma gida yau din ma don likita ya dage shi yasa na hakura,amma gobe tara a gida zata yi mun". Ma same ku gidan gobe".Alhaji Garba ya fada.muka yi sallama suka tafi,har sun kai kofa Aunty Asiya ta dawo,kayan nan da na baki ki dai na shansu haka nan,kinji?"ko kallonta banyi ba,ta juya ta fice da sauri.ba tasan cewa,ko tabasu ban yi ba,tunda ta bani,ko drower ban taba budewa ba balle na taba su.Karef takwas ya maida su Grace, ina nan kwance na saka wancan na kwance wannan,har ya dawo daga kaisu.Daga shigowar sa har zamansa akan idona,wai ashe haka yake da kyau?Dazun suna magana da su Alhaji Habibu baka taba cewa,abokinne kamar yayyensa ne.ya kalleni,sai naga yayi murmushi ya dauke kai.Ban so hakan da yayi ba,har dan kara gyra kwanciya nake yi yadda zan ganshi sosai."wai me ne ne meena? ya fada yana 'yar dariya,kumatunsa ya lotso point din ya bayyana,kunya ta kamani,na snkunyar da kai ina murmushi.Kokina bukarta wani abu n, kin kasa fada?"ya kara tambayata yana ci gaba da yar dariyansa wadda na fi komai so a tare da shi,idan ya yi ta tana kara wa funkrsa kyau fiye da in yayi murmushi."Uhm-uhm" Na fada a hankali.to kallon na mene tun dazu na lura da ke,ko mosti nayi idon ki na kai na"Kamr na bude kasa na shige don kunya,Allah ba komai"Na fada ina yan kame-kame.Haka ake so aji,ba wani abun".ya miki,ni kuma na gyar kwanciyata,ma'a na na matsa inda zai kwanta yau kawai na tsinci kaina da son jinsa kusa da ni.Idona kansa ya gama shirin kwanciya,abin haushi,sai na ga ya dauki filo ya kwanta bisa kafet.Na bishi da kallo na takaicr,ya dago ido muka hada ido,na yi saurin dauke kaina,Good night'ya fada yana murmushi. Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤11¤¤ Ban san lokacin da na harareshi ba.sai naga ya bushe da a,ya maida kansa a filo tare da rufe idanu,yana fadin tuba nake,mu kwana lafiya"Don karfin hali,ni ma sai na maida idanuna na rufe wanda nasan yaudarar kaina kawai nayi,babu wani alamun bacci a tare da ni.Ba'a fi minti talatin da kwanciyasa ba,na ji yana fitar da nufashi a hankali,alamar ya samu bacci.Zaune na tashi na tsura masa ido.lallai Abba yayi gado,shi ma haka yake barcinsa,ya kududune wuri daya kamar karamin yaro,kana hango murmushi a fuskarshi,idona ya kai ga hannunsa,yatsun hannunsa zara-zara ga dogayen akaifa an yankesu dai dai,sunyi kyau abinka ga fari.Wannan tsafta ta yaya daman likita ne.Kafarsa na birgeni da gani zata yi taushi,ko ita kadai ta isa ka gane yana hutawa a rayuwarsa.Nayi murmushi,"miskili ya faruk. jan class kiri-kiri yau ya kasa bacci kusa da ni,saboda ya lira ina son haka shi ne za'a ja mini aji shiga miskili"Yau kadai zan hakura,gobe dole......motsawar da yayi yasa na kwanta da sauri,abin haushi ashe ba tashi zaiyi ba,juyawa yayi.Ban sa ya bani baya ba,na kalli kansa,sumarsa liya-liya kwance bisa wuya ta sha gyara,yana da girma,amma ba kato ba ne,gashi moderate {tsakiya).maganar maryam faruk ta fado mini a rai,"Ina sonki da babana"Haka ta ke kiransa, saboda sunan babanta ne,ko ni a gabanta sai dai nace yaya kawai,ba dai ya faruk ba."Meena kinyi sa'ar miji wallahi sweety(haka ta ke kiran mijinta) yake fada mini a office dinsu babu wanda bai san yana son ki ba.Ashe tun kina yarinya yake sonki,har zolayarsa General Director ke yi,yana ce masa,angon Amina,baban Amina sannan kuma yayanta.lokacin da kika fara sanar da ni baki son sa,ban yi bacci ba,kawai ina tausaya masa.sweety kuwa kamar zaiyi kuka don bakin ciki,wallahi sai an sha wahala,ga kyau,kudi,takama,kasaita,sanna jan aji,kin san irin wadannan mazan tsada suke yi yanzu.Ina anfanin shegen surutu ga namiji kamar aku?tun ana fadin gaskiya har a kai ga karya?Amma na miji na basarwa yana takama shi ne mini mai class,ki gode wa Allah,wallahi kada ki butulce masa meena.....ke bana son ji.Wannan kalma ita yasa ta yi shiru ban mantawa fushi tayi lokacin koda muka fito lecture tafiyata tayi.Dai-dai lokacin da ya kwants rigingine,kansa na kallon silin,wani bugun zuciya ya zo mini da sauri.Anya ba son ya faruk ke damuna ba,abun fa ya fara wuce misali.Murmushi nayi,don na gan amsar,lallai sonka nake yi ya faruk,har cikin raina.kwalla suka zubo mini,tausayinshi ya kamani,Na yi kamar na koma bisa kafet din don tsannanin begensa.Ban taba jin abin da nake ji ba,ko daman ba son ya mukhtar nake ba da farko?wannan yanayin sam daban yake da wanda naji baya a kansa. Shin ko maganar mutane zata tabbata ne da suke ce,ina son sa?yaushe nake sonsa?ya aka yi suka gane ni na kasa fahimta?ya taba fada mini cewa,Meena kina sona,kawai tsabar kishina da son zuciya......."Lallai na kusa yarda da maganarsa,saboda akwai lokacin bana mantawa,muna zaune a filo Aunty zata wuce ya kamo hannunta yana fadin,come my love...."Na banka masa harara,wadda na dade da tuhumar kaina ko me yasa?Amma ban gano amsa ba,anyi hak ba sau daya ba,ba sau biyu ba.Duk da masifarsa a duk lokacin da haka ta faru sai dai naga ya yi dariya ko murmushi.Na dafe kai na,lallai akwai matsala,in haka ne ya faruk ya ganoni yanzu shi yasa ya basar,to me ye ma'anar dariya ko murmushi da yake yi? Maganarsa ta fado mini,Ni faruk zan baki mamaki, in don ni ne,sai kin nema da kanki"To fa yanzu meye abin yi ni Aminatu? Na ja wani guntun tsaki,haba lokacin dazai kawo kansa me nawa ya gani?ni fa mace ce.Da kyar bacci ya dauke ni,waien hudu saura.Don haka ban jima ba naji yana tashina na tashi nayi sallah.Abu biyu ya fado mini a rai,lokacin da na gama sallah.shin in gaidashi ko in kyale?Ba tare da ba yanke ani hukunci ba,na durkusa a hankali na furta, ina kwana?"Murmushi yayi tare da tsareni da ido,ni kaina sai da naji wani banbarakwai,na sunkuyar da kai cikin jin kunya.Sai da ya mila,sannan yace "ya karfin jikin?""Alhamdulillahi!"Na ba shi amsa a gajarce.Da kansa ya hada mini tea na sh da cake shi kumasauran frur jiya naga ya kara wa ruwa ya shanye.ko me yasa ya ki bani da kansa? tambayar da ta dade a raina,har muka gama.Shiru babu wanda ya ce wa kowa kala,wai me ye haka ya ke neman canza mini ? ko yan tambayoyyin da yake mini ya kiya.Me ya hanaki bacci jiya? kamar daga sama naji tambaya,nan da nan na dimauce,sai kama-kame.da ke fa nake,na ce me ya hanak bacci jya,ko kona tunani bani ba ne?. Nan da nan na kara diriricewa,kai wannan mutumin shu'umi ne,kafin na bashi amsa likita ya turo kofar.ya kallemu yana \yar dariya,ya nufoni da file rungume.please Doctor taimaka mini ka dubata,ta wahala da yawa"duk mukayi dariya,wato yana kwaikwayon yaya jiya da ya dauko ni a rude.Duk dokin sallama ne yasa ba zaka yi wanka ba?A'a idan mun je gida ma yi,ko meena?Na yi saurin dauke kaina.Ni kaina na fara jin haushin kaina,ni wannan mayen kallon da nake yi masa har ya kai ga ganewa.Takwas da rabi ya sallame mu,da yake abonki ne da shi aka tayami tatara kayan.Na kama yaye zanen gadon da bargo,yaya yace,madam ba namu bane wannan,ajiye" abu har kamshi suke da shi.Tsohowar asibitinsa da na sani, sam ba ta kai haduwar haka ba,lallai ci gaba da dadi a rayuwa, Bas barni na dauki ko cokali ba, motar ma yaya ya bude mini na shiga muka tafi,abin mamaki ko kallona bai yi ba,ya maida hankalinsa a titi ni ke satar kallon sa kamar munafuka. Na fito ina 'yar miki ya kalleni cikin murmushi,"ki je ki yi wanka".Na langabe kai,"kayan fa?" ya guntse dariyarsa,"zamu shigo da su yanzu".Na feso wanka na bata fiye da awa daya ina tsafatce ko ina,shafar kanta yau ta dabance,jikina ya dinga wani irin kamshi,saboda hadin da na yi masa na body fantasies apple, resberry,da kuma vanilla.Wani sabon leshi na dauko sky blue dinkin riga da skirt ya yi matukar karbata leshin,duka sawata daya,tun cikin wadanda ya yi mini ne lokacin da na gama makaranta.Das! ya zauna jikina don ma na yi dan wuya ba kamar da ba,farin gazar kawai na shafa masa,turai 'yar'adu'wa shi ne daurin kallabina na yau ya fi na kullum,saboda gashina na fiddo kwance bisa goshina,ya lankwafa ta cikin daurin.Na yi murmushin mugunta,duk miskilancinka na tabbata......miyau ya sarkeni lokacin da ya shigo babu zato.Bai taba yi mini kyau irin yau ba.kananan kaya ne jikinsa,bakin jeans mai tambarin butterfly a baya,sai T shirt round neck,sky blue,rubutun jikin rigar ya dau hankalina,an rubuta,Tm waiting.Na kalli kwayar idonsa,shin ko haka ya ke nufi a zuciyarsa,gayya ce ta sanya.....Kin tsareni da ido,ke ba ki amsa sallamata ba,baki kuma bani izinin shigowa ba,kin barni tsaye kamar dogari".kunya ta kamani,kwakkawaran motsi wannan dizgi ya fara isata,idan yaga haka me zai hana ya basar,amma don tsabar raini....."Daman chocolate da biscuit dinki zan baki,ga su nan a kwalaye,ko wane hurhudu ne,naga sabbin shigowa ne shi yasa,idan sun miki dadi sa ki yi magana a karo miki"Wai ina ya yi wanka? Na tambayi kaina,dariyasa ta katseni, wannan wace irin tambaya ce Meena?"kinyi tambaya kin kuma basar da ni.A dakina nayi ko ba kya so?"Don taikaici sai na bar dakin wannan shi ne nade tabarmar kunya da hauka.Na shiga kitchen na tabbata ko shirmen merry ya mantar da ni,sai dai na makaro,ko zama banyi ba,na ji sallamar su Alhaji Habibu da Aunty Asiya.Raina ya baci,bawai zuwansu ya bani haushi,a'a zama na kasa da shi na tabbatar idanuna ba zasu daina kallonasa ba,na dafe kaina,"Ni Meena tawa ta magana" Ina haka ya shigo,"Meena Asiya na magana".Na runtse idona, Ina zuwa" Na ba shi amsa a gajarce.Tunanina ya fita na saki ajiyar zuciya da karfi,Grace ta matso,Aunty head ache?(ciwon kai)" Na girgiza kai kawai tare da mikiewam bude idon da zanyi naga mutum tsaye nan da nan jikina ya kama rawa,Na rabashi zanwuce yayi saurin rada mini,control your self.Da sauri na fice gabana sai ya fadi,wannan na sani tuna ina yarinya,kullum maimakon raguwa sai karuwa ma kaomai ke yi,ga rawar jiki,wanan kuma kwana biyun nan ya sameni.yawan kallonsa kuwa na barshi a cewar,asiri yayi mini Zauna suke bisa lumtsa- lumtsan na falon baki,ya wani rungumota ko kunyata ba sa ji."salamu alaikum"Aunty ta yi karaf,"wa'alaikumus salam"shi kuma na amshe,"Amarsu ta ango mai dadin tuwo".Na yi murmushi ciki da zolaya kamar yaron goye.Na zauna kujerar da ke kusa da tasu,"ya karfin jiki?" "Alhamdulillah" "Ba ki dai amai ko?" Na daure fuska, "Wai ke Aunty wa ya fada miki ciki gareni.......?""kyaleta Meena,ciki ma gareki sai me?Kafin ki fara yi ita ta rigaki".Ya salam! jikina ya bada wani dam!!!! kunya ta lullubeni,su kuwa abin takaici dariya naga suna yi."Gaskiya bazan dauki managar ban...."Grace ce ta shigo da katon tire,Merr na binta a baya..suna ajiyewa na shiga serving dinsu,ina satar kallonsa,mamaki kawai nake bashi.kowa ya yi kat!!Ni kaina nan na ci nawa,Aunty ta kalleni,"mu shiga ciki,mu yi gulma zaki ce malama"ya faruk ya fada yana dariya.Ni kuwa har da tuntube nake yi don sauri.Mun dade muna hira,wani abin har kunya Aunty ke bani idan ta fada,muna cikin cin abincin dare Alhaji Garba ya zo banda Aunty Hadiza.A nan ne nake jin wani sirri a ban taba jinsa ba,"kasan Allah bazan maidata ba,idan kuka dameni kuma zan cika dayan sakin ya koma uku.Yanzu haka iyayenta sunyi fushi da ita,maganar mutane ma ta isheta, karuwanci abu ne mai kyau? kawai na kawo wa kaina cuta? yanzu haka zuwana test biyu, Allah ya tsirar da ni,sai na kai kaina? yarinyar na sha kamata gidan dan iskan nan Alhaji Naziru donta maidani sakarai ce mini ta yi kawunta ne,kuma harka banza jiya bistoriya kawarta ke shaida mini ta tafi saudiyya,itada su nananduwa da dubulle shi yasa na kai Abba kano hutu,ko zai dawo Abuja sai nan da wata uku."karuwanci? Innalillahi wa'ina ilaihi raji'u,lallai biri ya yi kama da mutum,nasan wannan mutumin,shi ne wanda na taba rakata gidan Aunty Hauwa sada muka biya, wai zata gaida kawunta, ta barni a mota fie da awa daya da rabi.sannan ta fito ko jikina ya bani Aunty bata da gaskiya,saboda hakan da na karanta a fuskanta,sai kame kame ta keyi. yana tsaye bisa bene sai faman daga mata hanun yake yi,ta maida masa tare da yi mini yake,wanda a lokacin na yi tunanin dariya ce.Kash! Aunty ba ta kyuata wa kanta ba wallahi.Bawan Allah ya faruk duk sai da na kara jin tausayinsa.Har mota muka rakasu,muna dawowa na shige daki,na tsak wanka,ranar farko da na saka rigar barci fara yar guntuwa duka iyakarta gwiwa,kamshi ko ta ina,yau zan ba shi mamaki na haye gado ina jiran shigowarsa ciki da fargaba. Karfe goma tayi shiru,sha biyu kai har wajen daya da rabi banji ya shigo ba,Nan da nan raina ya baci,na lallabo a hankali na bude kofa.wayam folan ba kowa,na kara sadadawa na leka na baki shima ban ganshi ba.Na yi turus! Akwai matsala,wato dakinsa ya tafi,me yake nufi?Na bi shi can?Na girgiza kai, Never"Ciki da takaici na koma na kwanta,duk wannan gayun nayi sa a banza kenan?lallai ya faruk ya cika dan wulakanci.karfe shidda na bude idona na hanzarta gabatar da sallah,na fito kitchen cikin wata matsiyaciyar sadda kalar kwaiduwar kwai.Na fere dankali na dafashi batare da na datsashi ba,na ajiye gefe don ya huce,sannan na dafa nama na nikashi, daman na soya kayan miya na hade da naman na kara ba su tsoro tare da zuba spices da maggi.Na dauko dankalin nan na dinga debe saman sannann na kwakware tsakiyarsa in debo kayan miyan nan da suka ji nama da kayan hadi in ciki ramin,na maida murfin na rufe,har na gama sannan na kada kwai na dinga tsoma dankali ina soyawa a mai. Sadiq Halima mai kaunar ku akoda yaushe... -Hada Hada Hausa Book stories GIDA BAI KOSHI BA ¤¤12¤¤ Na gama kenan Grace ta shigo na ce,yauwa muna da gyararriyar gyada? tace,"Eh Aunty an cire jan kwafasar ta koma fara?" tace,kwarai" yauwa debo mini kofi hudu" ta washe baki,Aunty kunun gyada zaki y mana? "uhm!"Na fada a gajarece.Tana kawowa na wanke ta tas tare da fiddo ragowar bawo ta koma fara kal.Nasa a blender

Chapter 6 of 9