Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
tsini alburusan bindiga ne dan sandan ya rike numfashi sannan ya taba kafadata ya nuna min jikin bangon dakin bindigogi ne amakale suna reto akalla sun kai talatin da biyar yawan bindigogin shiya tuna min da labarin yakin duniya na biyu. ** Ka taba harba bindiga? Dansandan ya tambayeni na girgiza kai matsa nan kagani yace dani sannan ya fara nuna min yadda ake amfani da ita idan ka taba nan saika makala dan yatsanka ajikin kunamar bindigar saidai kuma wannan bindigogin tsohon yayice bari na zabo ma ta zamani dansandan ya sake nazarin bindigogin da suke makale ajikin bangon dakin sannan ya zabo wata yar gajeriya mai launin azurfa sannan ya bude gurin da ake jera harsasai sai da ya tabbatar babu komai aciki sannan yace dani idan ka rike kunamar ka taba nan saikaja kunamar ahankali rike ka gani yace dani na karbi bindiga jikina na rawa tunda nake bantaba rike bindiga ba ballantana ma harna harbata Ja kunamar to ahankali dansandan yace dani na rufe idona jikina na rawa sannan naja kunamar bindigar tayi wata yar kara Dass wannan shine ya zama karshen koyon bindigar abinda ya biyo baya shiya sani jefar da bindigar dake hannuna duk da yake da farko na dauka itace tayi karar to amma nasan zolayar kaina kawai nake karar bindigar ya ratsa sararin dajin daga dakin ina iya jin kukan namun dajin da suka watse da gudu aka sake harba bindigar wannan karon sau biyu aka harba ajere. . Sun dawo dansandan yace dani a rude tuni har bindigogi biyu sun fado hannunsa cikin minti guda kuma ya jera musu alburussai na juya a rude zan fice daga dakin saboda ganin badura na waje bankula ba kafar dansandan ta tade ni na fada da baya a tsakiyar dakin naji kamar kwankwasona zai fashe na rasa abinda yake min dadi domin nasan in har suka kama mu ba shiri to kashinmu ya bushe to amma ba haka abin yakasance ba. . Fadil muryar badura ta daki dodon kunnena a sanyaye rawar da muryarta keyi shiya tadani zaune zumbur kwankwasona kamar zai fashe don radadi ganin fuskarta kuma shi ya sani mikewa tsaye. Sun biyo mu nan Fadil ta wani kamar zatayi kuka na shiga uku Fadil bakaga irin bindigogin da sukazo dasu ba sannan hawaye ya fara kwarara akan kyawawan kumatunta. Su wanene? Na tambayeta duk da yake kuwa nasan ko su wanene din. Yansanda ne tace dani dan sandan dake kusa dani bindigogi biyu ahannunsa sai fuskarsa ta washe don jin cewa yan uwansa sun iso. Kaga munsami hanyar tsira kenan yace dani bai rufe bakinsa ba sai mukaji dirin mota gidan kuma motar ta nufo tana zuwa saita daki kofar gidan kofar tayi sama sannan ta fado a ratattake abin yayi matukar girgizani lokacin da motar tashigo a zatona zanga yansandan suna firfitowa kowannensu da harbi ka ruga ahannunsa amma maimakon haka sai naga yan fashin nan suna durowa daga cikin motar babbansu shi yafara dirgowa dif. Sannan sauran biyun suka fito da sauri kowannensu bindigarsa ahannunsa na karshen daya fito shi yasani na gane abinda ke faruwa yansandane suka biyo su yau rana ta baci lokacin daya fito daga cikin motar hannun rigarsa na dama rine yake da jan jini jajur yana tafiya yana tangadi bayan rigarsa ma arine yake. Duk abindake faruwa akan idonmu ke faruwa hakan kuma baisa yan fashin sun lura damu ba badura tayi sauri ta shigo cikin dakin. Rufe kofar dansandan yace dani nayi sauri na rufe kofar amma muna iya ganin abinda ke faruwa ta wasu kofofin dake jikin kofar kargen ba'a dade ba yan sanda suka shigo gidan da gudu acikin katuwar PATHFINDER irinta yan fashin tun kafin motar ta tsaya yansandan suka fara dirgowa suna boye kansu yansandan sun kai su ashirin hakan shiya tabbatar min da cewa bayan motar tasu babu kujeru atunanina kuma a tsaye sukazo saboda babu yadda za'ayi mota taci mutum ashirin in har da kujeru acikinta. Tuni sauran yan fashin sun shige cikin dakin nan mai kofar sama dayan da aka harbe ne kawai ya rage bai shige ba yana saman kofar ya zura kafarsa ta dama zai shige sai wani kurtun dansanda ya hango shi sannan ya daga bindigarsa ahankali yaja kunamar. Karar bindigar ta amsa kuwwa acikin dajin dan fashin yayi taga taga ya fada da fuska cikin dakin duk da yake banga sauran abinda yafaru gareshi ba nasan cewa YA MUTU babu wanda za'ayiwa harbi uku daya a hannu wani abaya sannan a kirji sannanya rayu zaiyi wuya. ** Bakajin komai a sararin dadin sai amsa kuwwar karar bindigogin yansanda da yan fashin suna musayar wuta wani dan siririn dansanda fari wanda nake tunanin bai dade da shiga aikin ba yafito daga maboyarsa ya budewa dakin yan fashin wuta cikin lokaci kankani yayiwa wani bangare na dakin katakon kaca kaca dankararen dan fashin ya leko dansandan na kokarin lodawa bindigarsa harsashi abinka da sabon shiga maimakon ya sunkuya a maboyarsa sai ya tsaya kerere atsaye shi a zatonsa yan fashin sun tsoratane don haka suka daina harbi dan fashin ya saita kan dansandan sannan yaja kunamar bindigarsa dansandan yayi sama ya fado sannan cikin abinda bai wuce dakika biyar ba jini ya rufe fuskarsa baiko shura ba inajin lokacin da dansandan dake kusa dani ya rike numfashinsa cikin razana shima yaga abinda yafaru Badura na gefe guda tana kuka. Ya kamata na fita na taimaka musu dansandan yace dani. Kana jin zaka iyayin abinda ya gagari mutum ashirin? Na tambaye shi bazan iyaba yace dani kuma bazan iya tsaiwa anan ba inaji ina gani suna kashe mana yan uwa don me yasa ake biyana? Kafin nayi kokarin yin wani abu tuni dansandan ya bankeni ya bude kofar ya fita lokacin daya banke ni sainayi sauri nakai idona wajen yar kafar dake jikin kofar domin leken abinda dansandan zaiyi baiyi cikakken taku biyu ba saiga kan dan fashin nan ya leko sannan kan bindigarsa ya leko. Zai harbeka na gargade shi cikin karaji amma na makaro karar bindigar dan fshin ta sake ratsa sararin dajin dansandan yayi taku biyu gaba sannan yafadi da baya BAI KO SHURA BA. . Jin na kwallawa dansandan kira shiyasa badura ta nufi inda na leka itama ta leka akan idonta aka harbe shi. Fadil ta kira sunana tana kuka don Allah kayi min wani abu mana ina tunanin kuma abin shine zai zama karshe. Menene? Na tambayeta cikin mamaki da tausayin halin data shiga Fadi mana badura banason naga kina kuka wallahi kukanki shi yake dada karya min zuciya inason naji wata kalma daya ta fito daga bakinka Fadil tace dani. Wacce kalma ce? Na tambayeta. Inason kace KANA KAUNATA DA BAKINKA sannan kuma inason kace ka YAFE MIN DUK ABINDA NAYI MAKA ABAYA DON ALLAH FADIL ka taimakeni ka fada karka bari na mutu da ciwon sonka ban samu cikar burina ba. . Haba badura kidaina fadin haka wayace zaki mutu ? Na yafe miki badura. Nace da ita na kuma gane cewa ba laifinki bane laifin mahaifiyarki ce bakida laifi agurina Badura har abada ina rokon ubangiji kuma ya tserar damu MASOYIYATA na yarda da kaunar da kikeyimin Badura. Tunda kika sadaukar da rayuwarki gurin ganin kin tserar dani INASON KI BADURA INASON KI KECE ABAR BEGENA HAR ABADA RABIN RAYUWATA. . Badura tayi ajiyar zuciya bayanta yana fuskantar kofar dakin ni kuma bayana yana fuskantar cikin dakin kowannenmu yana kallon abin kaunarsa soyayyar badura ta motsa cikin zuciyata sannan na dubata sai ta sunkuyar da kai tana zubar da kwalla bansan ko kukan farin ciki bane ko kuma bakin ciki ba. Fadil.... Ta kira sunana cikin sassanyar muryarta mai daukan hankalin ma'abocin bege muryarta da bazan taba mantawa da ita bace har abada arayuwata bata karasa fadar kalamin dake bakinta ba sai yansandan dake waje suka budewa Kofar dakin da muke ciki wuta. Babu mamaki gargadin dansandan nan danayi shiyasa suka san da wasu acikin dakin harbin kuma shi ya shuka bakin ciki mara Misaltuwa acikin rayuwata aduk lokacin dana tuna da mutuwar Badura sainayita zubar da hawaye ruwan harsashin bindigogin yansandan duk abayan Badura suka sami matsugunni ta kwalla kara sannan ta fado kirjina. Wayyo Fadil.. Wayyo Fadil.. Amira Amira sannan tayi shiru ahaka ta mutu ajikina bazan taba mantawa da ranar ba har abada. . 16 Bayan da suka harbe yarinyar data mutu tana begena sai suka tsaya da harbin a zatonsu sun gama damu gaba daya sannan sai naji sun budewa daya dakin yan fashin wuta kasancewar kofar dakin damuke ta zama kamar rariya saboda ruwan alburusai da akayi mata saina sami damar ganin abinda ke faruwa badura rungume ajikina ina kuka ban motsa daga gurin ba bana kuma tsoron mutuwa bandamu ba na mutu kona rayu sai bayan da badura ta mutu sannan nagane irin matsanancin son da nakeyi mata sannan ne kuma na gane cewa duk da yake itace asalin fadawata acikin bala'in dake faruwa akaina amma hakan bai hana nafi sonta fiyeda da Amina ba mutuwar badura kamar wata fitilace aka kashe ya arayuwata. . Fadil.. Amsar kuwwar kalaminta dana ji akaro na karshe shiyaketa kururuwa a kunnena akoda yaushe nakan tuna irin yadda take kiran sunana aduk lokacin dataso sanar dani wani abu don haka tun farkon labarin nake cewa (Muryar da bazan taba mantawa ba) . Gawar badura a rungume ajikina ina leke ta kofofin da harsashi yayiwa kofar hawayena na kwarara akan kumatuna lokacin da yan fashin sukaga ruwan harsashin.. Lokacin da yan fashin sujaga ruwan harsashin yayi musu yawa sannan suka ga halaka karara sai suka rude suka fara fitowa ba'a ko taba kasa ba aka dasu babbansu ne na karshen hancin bindigarsa ne yafara fitowa sannan barin wutar yabiyo baya nan da nan duk yansandan suka koma maboyarsu suka buya hakan shiya bashi damar fitowa fili haryanzu yana barin wuta wani dan gajeren dansanda baki kakkaura ya leko da bindigarsa sannan ya harba harsashin ya wuce takan danfashin lokaci guda kuma danfashin yaja kunamar bindigarsa harsashin ya sami dan sandan a goshi nan take ya shure baiko matsa ba alburushin kuma daya kashe dansandan shine ya zama harsashi na karshe acikin bindigar danfashin lokacin dayaja kunamar bindigar sai bindigar taki tashi ba'a jima ba da faruwar hakan yansandan dake boye suka gane abinda ke faruwa nan da nan danfashin ya kwalla kara cikin razana. Kada ka harbeni yace cikin karaji saidai ya dan makaro wani kurtun dansanda tuni ya auna kafarsa barinsa kuma yaga asarane don haka sai yaja kunamar bindigarsa dan fashin ya kwalla kara mai tsanani duwatsu da koramun da suke zagaye dajin suka amsa kuwwa sannan danfashin ya fadi da fuska wannan shine yakawo karshen musayar wutar da akeyi tsakanin yan fashin da suka kama mu da kuma yansanda mintuna biyu da harbe shi sai yansanda suka fito daga maboyarsu suka daure danfashin sannan suka masa ankwa ahannayensa. ** Na Ajje gawar badura ahankali ina kuka lokacin yansandan suka fara warwatsuwa ko ina cikin gidan menene abinyi? Na tambayi kaina shin bari zanyi su kamani ko kuwa me ma zanyine? Nace ahankali muryata na rawa sannan ne na kalli cikin dakin sosai ga mamakina sai naga dakin yana da tsayin gaske da zan yi sa'a dakin yana bullewa ta cikin wani to da sainabi tanan in zurare to idan na gudu ma ina zani awannan kungurmin dajin? Na tambayi kaina sannan ne dabara ta fado min tunda yansandan basa tsammanin akwai wani mai rai agidan me zai hana na buya awani lungun idan sun gama abunda zasuyi sun tafi saina fito nasan dai da wahala ace sun tafi da motocin yanfashin gaba daya saidai..... Tunanina ya katse adaidai lokacin ne idona ya hango min wani teburi acan karshen bangon dakin ba tebur dinne ya dauki hankalina ba abinda bantaba tsammanin zan gani bane a dakin nagani akan teburin a ajiye abayan mazauninsa kan talfon ne hakika shine abu na karshe da nake tsammanin zangani agidan nayi mamakin abinda yan fashin sukeyi da talfon. Cikin doki da kaguwa saina matsa kusa da talfon ne harna dauka saina tuna da cewa kofar dakin a bude na barta kuma nasan kowane lokaci daga yanzu yansanda zasu iya shigowa dakin don haka saina koma batareda na dubi inda Badura take kwance ba bayan na rufe kofar saina koma na dau kan talfon din sannan akaro na biyu tun sa'ar dana fada cikin masifar saina bugawa yayana waya. . Wane ne ? Aka tambaya acan daya bangaren gabana yafadi danaji muryar yayana ce da kansa, nine fadil nace dashi muryata na rawa. Fadil yayana ya kira sunana muryarsa na rawa. A ina kake? Ya tambayeni me kuma ke faruwa? Batareda bata lokaci ba saina bayyana masa duk abinda yafaru a gurguje tun daga farko har karshe sannan nace dashi ga halin danake ciki kuma Badura ma gata nan agabana sun harbeta yayana yayi shiru sannan yace dani saurara Fadil da farko ina son nayi maka albishir dacewa ka kusan fita daga sharrin da akayi maka. Ban gaskata abinda naji ba. Me kake nufi? Na tambaye shi kwana biyu kenan da kama hajiya binta mahaifiyar su badura sannan salman ma an kama shi dukkansu tare da tsohon nan ma'aikacin Durba otel. Amira fa? Na tambaye shi cikin doki. Amira batada laifin komai itada yar uwarta badura. Yaya akayi aka gane basuda laifi? . Ranar Talata din data wuce wasu jami'an bincike na yansandan ciki dake aiki a daba otel kaduna suka zo da shaidar da take nuna cewa hajiya binta itace tayi Ummul Aba'isin faruwar komai sannan abin mamakin ma shine ita wannan yarinyar ba'a cikin otel din aka kasheta ba saceta akayi ta hanyar hada baki da dan tsohon nan mai aiki a otal din bayan da suka kasheta ne suka shigo da ita cikin dare tare da taimakon dan tsohon nan suka kwantar da ita lokacin dakaje dakin mai Lamba 3 daman kusan abin a shirye yake.... . Kana nufin kace ba'a cikin otal din aka kasheta ba? Na tambaye shi. Ko kusa ba'a ciki bane kasan fa irin matakan tsaron dake otal din bazaka taba yin wani abu na rashin gaskiya ba batareda an kama ka ba itama wannan bindigar dan tsohon ne ya shiga da ita saboda hanyar da ma'aikatan otel din sukebi babu na'ura mai kwakwalwa wadanda kuma itace take nuna duk wani abu da mutum ya shiga dashi otal din saboda haka dan tsohon nan shi ya shigawar da hajiya binta da bindigar ciki ita kuma ta shigo ta hanyar da kowa ke shiga ta kama daki a hawan bene na uku shine ta bari saida asuba ta hayo hawan benen ku ta harba bindigar domin ta saka kafito ka kuma fada tarkonsu. . Nayi shiru cikin mamaki to tayaya akayi kukasan wannan? Nasake tambaya. Su Jami'an tsaron otal din sunada na'ura mai kwakwalwa wacce take. Su Jami'an tsaron otal din sunada wata na'ura mai kwakwalwa wacce take daukar duk wani abun dayake faruwa a otal din ko waya aka buga saita dauka bakuma a binciken abinda ta dauka sai karshen wata to a irin binciken ne aka gane duk irin makarcin da aka shirya hatta ita badura da amira duk dakinsu daya anan otel din da kake zaune shima salman anan hajiya binta takama masa daki don haka duk lokacin da zasu tattauna sai hajiya binta ta tarasu a dakinta saidai kuskuren da tayi bata san da wannan na'ura mai kwakwalwa ba wacce duk abinda suka tattauna yana cikinta kaga kenan banajin akwai sauran wani abu da zakaji tsoro. To yansandan da suka ritsani anan yaya zanyi dasu? Zan bugo musu waya yanzu tunda suna da salula saimu sanar dasu abinda ake ciki sannan wani abin kuma yayana yaci gaba da cewa tare muke da kanal muktar yanzun nan yazo domin bai dade da zuwa ba ka bugo waya shima yazo akan maganarku da Amina dakuma yadda za'a tserar dakai to inayi masa wannan bayanin danayi makane ka bugo waya yanzu ma gashi nan akusa dani sannan ya danyi shiru. . Fadil ina jakarka take? Ya tambayeni gabana ya fadi sai yanzu na tuna da jakata da yayana yabani nayi shiru ina tunanin inda na yarda ita. Na manta inda.... Ya katse ni kafin in karasa. Shikenan yayana yace dani ta cikin talfon din jiya muka tsince ta acikin motar da kukayi hadari watakila zakaso jin amfanin baka ita danayi to dalilinta shine a kasanta akwai wata yar karamar rikoda mai dauke da maganganu sanin yaudarar masu aikata muggan laifuka ne yasa nabaka ita saboda tun lokacin dana hanaka tafiya ka nace sai ka tafi saina ga ya dace na baka ita domin nayi tunanin wani abu sakamakon haka zai iya faruwa akanka domin su daman yawancin mutane irin hajiya binta sunfi yaudarar yan yara samari kamar ka kuma jakar tana da muhimmanci domin tana daya daga cikin abinda zai fitar dakai a kotu kuma duk maganar da kukayi da badura hajiya binta da amira dakuma salman duk suka ciki wannan ma shaidace da zata iya fitar dakai daga karshe banason barka cikin duhu ita wannan jaka ta yan sandan ciki ce C.I.D yace dani. Kana nufin kai CID ne yaya? Banason irin wadannan maganganun ta talfon yace dani abin yayi matukar girgiza ni duk da yake bai fada min da bakinsa ba na tabbata yayana dansandan cikine CID Tab abin da mamaki. Gashi nan Kanal mukhtar yana buga musu waya waya muryar yayana ta sake ratso talfon din mintuna biyar dayin magana da yayana ta talfon sai abubuwa suka sake juyewa awannan karon daga bakin ciki da kuntata zuwa farin ciki abin kawai da ya rage farin cikin shine mutuwar Masoyiyata Badura aka kwankwasa kofar dakin banyi fargabar komai ba sai kawai na bude domin nasan su yayana sun gama aiki dansandan yana tsaye sauran yansandan kuma a bayansa. Zo mu tafi yace dani na juya nayiwa badura kallon karshe tana kwance lallauan gashin kanta mai kyalli ya rufe idanunta haryanzu badura kyakkyawace duk da yake kuwa ta MUTU wasu yansandan biyu suka shigo da gado irin na asibiti suka dora badura akai sannan suka dauketa suka tafi da ita na fara kuka saboda bakin cikin rabuwa da masoyiyata badura. Dansandan ya dafa kafadata ya jani har zuwa cikin mota muna zuwa ya tayar da mota sauran yansandan suka dane direban motar yaja mukayi gaba wata barewa da wani dan zaki suka shige dajin da gudu lokacin da daya sandandan ya harba bindigarsa sama na juyo na kalli gidan yanfashin bazan manta dashi ba domin nanne aka kashe MASOYIYATA BADURA. ** Wata daya kenan da rasuwar badura abar kaunata Yau lahadi daya ga watan janairu ina zaune acikin dakina dake gidan yayana amina na zaune acikin daya daga cikin kujerun da suke dakin tana zaune acikin daya daga cikin kujerun da suke dakin tana fuskantata fuskarta cike da haske dakuma farin cikin jin cewa yau saura kwana goma ayi bikinmu da ita shari'ar da akayi bata dauki tsawon lokaci ba saboda shaidun da nake dasu kuma itama hajiya binta ta fada da bakinta cewa ita ta kashe zainab daga karshe an kaita gidan mahaukata saboda an tabbatar ba kanta daya ba shikuma salman an yanke masa hukuncin shekara biyar agidan maza saboda taimaka mata dayayi shi kuma dan tsohon nan an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma sha biyar. . Aka kwankwasa kofar amina ta dubeni mukayi murmushi inajin hajara ce tazo ta tsokaneni tace dani babu mamaki nace ina murmushi. Shigo ko wanene amita tace gabana yafadi zuciyata tai kunci da farko na dauka Badura ce ta dawo amma nasan nida badura har abada wannan AMIRA CE. Ina kwananku? Tace damu lafiya kalau Amina tace. Sannu da zuwa amira nace da ita bata amsa ba saita miko min wani dan karamin akwati na roba sannan tace sai anjima tafice daga dakin Amina ta kalleni nima na kalleta sannan na bude akwatin kamshin turare ya daki hancina wata takarda ta fado daga cikin akwatin nan danan na dauka na fara karantawa.. . Daga Masoyiyarka BADURA. Lokacin da kake karanta wasikar nan banajin akwai abinda zaka iya min daya wuce addu'a ya Masoyina. Tun daga ranar da naga babata ta tsundumaka cikin bala'i saina yanke shawarar tserar dakai saidai kuma jikina yabani cewa da wahala na tsira da rayuwata shine naga ya dace na rubuta maka wasikar bankwana da msoyi don haka kaji nace lokacin da kake karanta wasikar to ni kam na riga ku gidan gaskiya masoyina abu daya nake so ka rike a rayuwarka Fadil shine duk abinda zakayi kada ka sake kabi son zuciyarka domin shi yake kawo dana sani. Daga karshe inason ka sani cewe na mutu da masifar sonka ina kuma baka shawarar ka auri yar uwata Amina domin ita ta dace dakai ina kuma rokonka idan kun haifi 'ya mace kasa mata sunan BADURA. domin ka rinka tunawa da wacce ta mutu domin tserar dakai. Daga karshe nake cewa Allah yasa ina cikin Matanka A Aljannah Amin. Daga Marigayiya Badura Abar kaunarka A Kullum. . Na aje wasikar a hankali hawaye na kwarara akan kumatuna sai hakuri Fadil.... Amina tace dani muryarta na rawa ita kanta tasan matsayin badura azuciyata sannan Amina ta dauko dan akwatin ta mika mini. Kaga abinda yake ciki Fadil tace dani abinda nagani acikin akwatin zobe ne na zinare yana kyalkyali wata kyakkyawar fulawa kuma acikin akwatin itace ke bada kamshin dake tashi. A rubuce ajikin ganyen fulawar sunana ne Badura ta rubuta DON'T FORGET WITH ME FADIL. fadil kada ka manta dani na dauki zoben nasa a hannuna sannan na fara juya fulawar a hannuna hawaye na zuba akan fuskata. . Bazan taba mantawa da ke ba Badura. Nace ahankali cikin zuciyata abinda nakasa baiwa kaina amsa shine Anya kuwa zan sake son wata 'ya mace kamar Badura ? Na Tambayi Kaina. . NAZIR ADAM SALIH (NAS). . KARSHE. . KIBIYAR AJALI Na Nazir Adam Salih Ebook creator Shuraih Usman 99% . Zaku iya downloading wasu da dama daga cikin ebook namu ta hanyar ziyartar babban shafin mu na Hausaebook akan wannan adireshin www.shuraih.waphall.com Wannan ebook din an sake shi ne A matsayin Happy Sallah ga daukacin Al'umman musulmai baki daya , Asha karatu lafiya An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9