Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
shine bansan iya yawan yan sandan da suke gadin bangaren gabas na lambun ba duk da yake dai nasan har yanzu gungun yan sandan basuda masaniyar abinda ke faruwa a bangaren gabas na lambun addu'a ta daya itace Allah sa na samu damar yaudarar dan sandan dake bayana tun kafin wani yazo ya tadda mu Kada ka sake ka motsa yace dani bansan abinda yake nufi ba amma zatona yana jiran ruwa ya tsagaitane mun jike shakaf amma ni duk da haka zafi nakeji akayi wata walkiya mai hasken gaske duk lambun ya haske sannan wata tsawa mai karar gaske ta biyo baya amsa kuwwar tsawar ta sake rikita lambun dan sandan dake bayana sai yayi zaton shi zata fadawa yana rawar jiki sainaji saitin bindigar ya kauce daga bayana banjira wani abu ba sai kawai na fadi rib da ciki nasa kafata na doke shi a kirji bindigar dake hannunsa ta fadi can gefe guda muka tashi lokaci guda muka shiga tsere kowa na kokarin daukar bindihar ruwa ya dada tsugewa da karfi santsin cabin ruwa ya kwashi dan sandan sai gashi a kasa kamar wanda aka jefo daga sama baiyi wata wata ba sai ya rike idon sawuna nima na fadi kansa muka shiga kokowa cikin cabin abinka da wanda ya manyanta kafin minti daya saiga dansandan yana numfashi sama sama nayi masa diban karan mahaukaciya na jefa shi bayana idona ya gama rufewa ahalin yanzu fada kawai nake kamar mahaukacin doki domin nasan idan sauran yan sandan sukazo to fa kashina ya bushe kenan. Dan sandan dana jefar gefe guda yayi kokarin tashi amma sai juwa ta dauke shi ya fadi sannan sai ya tashi naga ya dora hannu aka zaiyi ihu na duba inda bindigarsa ta fadi na raruma kafin ihun nasa yagama fitowa saina kwada masa gindin bindihar a tsakiyar ka yayi taga taga ya fada cikin cabin da fuska biyu kenan nace a zuciyata ** Ko kadan bana son fada da dan sanda ba don komai ba kuwa sai don dokace mai tsanani amma kuma irin halin danake ciki ya zama dole na kwaci kaina. Rigata ta jike sharkaf da ruwa bayan na dawo da numfashina daidai saina gyarawa jakar dake bayana dauri sannan na kama kafar dansandan dana dole na boye shi shima a karkashin bishiya lambun yayi shiru bakajin komai sai dirar zubar ruwa akan kwanukan gidajen jama'a dake bayan lambun sai kuma jefi jefin cabal cabal din ruwa danake ji na takalmin yan sanda acan bangaren arewa ina tsammanin sun fara tunkarar gidan saidai kuma ruwan da akeyi shi ya bata musu lamari domin duk takun da suke inaji har yanzu fa suna tsammanin inada bindiga. Nasa gabana gabas ina dansa ahalin yanzu na fara hango katangar gidan ta cikin wata bishiyar lemon zaki marar ganye da yawa saidai kuma kaiwa ga katangar shine yake da matukar hadari domin babu mamaki wani dansandan na nan a na gadin wajen kamar da bakin mala'iku sainaji nayi sama kamar karmamai sai bayan dana fada cikin cabalin ruwan da fuska sannan na gane cewa ashe fa wai kafafuna aka kwarfe na mirgina sau uku cikin cabin ruwan sannan nayi karfin hali na tashi zaune ina kokarin gane me ya faru katon dan sandan wanda zaka iya ganin jajayen idanunsa daga cikin duhun daren na tsaye a kaina jibgegen kakkauran mai fadin kafada kamar kofar gareji zaiyi wuya ka banbance tsakanin wuyansa da kansa da farko sai ka dauka mutum mutumi ne hannunsa daya yiwo kaina kamar harsashi shi ya tabbatar min da cewa ba mutum mutumi bane. Katon hannunsa mai kamar farantin waina ya cakumi kwalata ya dagoni safayau kamar biredin mahaukaciya kafata da kyar take taba kasa ya kwada min mari sau uku idona ya ganemin taurarin wahala kamar tarin yashi naji kamar saman kaina zai cire yafado. Sai ka san ka daki dan sanda yace dani daga yau ka sake kashe wani muryarsa mai kama da kwankwatsa kafafuna sai reto suke falau falau kamar bulala mai baki biyu cikin gigiya da takaici na kutufi hancin dan sandan alamun da ya nuna alamu ne na irin wanda aka doka da gudumar totuwa agadon baya kaje ka sake kwarewa a dambe dan sandan yace dani adaidai lokacin ne ya saki kwalata tareda dukan kirjina dukane irin wanda zai iya kayar da katangar bulon siminti na fadi rica.... Kamar wanda iskar gas ta doka hankalina ya fara fita daga jikina kuguna kamar zai fashe nayi kokarin tashi abin ya gagara dana yunkura sai naji kamar gini ya fado min. Dan sandan baya ko kokarin fito da bindigarsa domin yasan zaiyi wuya na tsira daga hannunsa ya yarda da kansa nafara tunanin daya naushe ni gara ya harbeni da bindiga akafata naushinsa yafi bindiga hadari don kuwa dukansa zai iya kashe mutum fatar daya kada kayi zaton abinda nake fade gaskiyane kai kanka kasan wahalace tasani tunanin haka. Cabal cabal naji karar dansandan nacewa ayayinda ya keto cabin ruwan dake tsakaninmu dashi nayi ta maza sai gani a zaune dolene yanzu nasan yanda zanyi na rage masa haukan karfin dake kansa in kuwa na sake yayi min irin dukan dazun toh nasan yau banida wajen kwana sai gidan DAN KANDEIn kuwa na sake yayi min irin dukan dazu to nasan yau banida wajen kwana sai gidan YARI . Ya matso kusa dani tsakaninmu dashi bai wuce takun sawu uku ba dabara ta fado min saina yanke jiki kafin kiftawa da bisimillah sai gani facal cikin cabin duk da yake babu cikakken hasken da zan iya ganin fuskar dan sandan sosai duk da haka zan iya cewa naga hakoransa suna murmushin mugunta a zatonsa sarewa nayi na fadi in har yana tsammanin zan kamu haka kamar wani jikakken zakara to yana bukatar sake tunani sau dubu acikin kowace dakika daya. Na harbo kafara kamar KIBIYAR AJALI jibgegen dan sandan yayi kokarin kauce tunbinsa amma ina ya makara gindin takalmina ya daki tumbinsa sainaji kamar na daki salkar ruwa dansandan yayi kara irin karar da zakaji daga bakin kwado da farko na dauka bazaiji dukan ba saboda ganin naushin danayi masa ya shanye shi kamar wanda na daki bango duk wannan rikicin ya farune cikin dakika biyar na sake yunkurawa gaba na sake dukan cikinsa sau biyu dansandan yayi baya taga taga kamar zai fadi sannan sai naga ya tsaya cak kamar mashi yana fuskantata katon cikinsa a hannu naji kamar motsin ganye abayansa wani dan siririn dansa ne yake matsowa ahankali cikin sanda walkiyar da akayi ita ta bani damar ganinsa kirjina ya fara dukan uku uku dole ne yanzu nayi wani abu na tabbata dansan bai ganni ba. Dan uwa me kakeyi hakane? Siririn sandan ya tambaya cikin harshen turan nan da nan nayi saurin na kwanta ahankali cikin cabalin na mimmike kamar fatalwa . Wayyo cikina ya kasheni kawo min taimako dan uwana nayi maganar ne cikin harshen turanci idan baka harbi katon nan ba kasheni zaiyi nasake cewa cikin harshen turanci karar harbin bindiga da hasken wutar data fitar daga bakinta da kuma aradun da akayi a daidai lokacin hade da walkiya sai suka hadu suka kurumta kunnen jibgegen dansandan yayi kuka Ka kashe dan uwanka kaiw awa yayi taku biyu gaba ya fadi da baya agabana cikin hasken walkiya sainaga jini na bulbulowa daga gwiwarsa ta kafar hagun nayi ajiyar zuciya akalla dai bai mutu ba nace cikin zuciyata. Karar bindigar da kuma aradun da akayi alokacin su suka hadu suka ruda matsoracin siririn dansandan nan da yayi harbin yana harbin sai ga bindigar ta kwace daga hannunsa ta fadi kasa a tsammanina bai taba harbi da ita ba sai yau cikin rudanin nan na tashi nayi kan dan sandan da gudu kamar kibiya yaga tahowata don haka sai yayi kokarin kai usir (abun busa) bakinsa idan na sake ya busa usir din to ni ina bukatar addu'a kenan domin nasan wajen na iya cika da yan sanda cikin minti daya nayi kokarin kai kutufo bakinsa adaidai lokacin da iskar bakinsa ta fara busa usir din naushin ya hada da iskar bakinsa suka bada irin karar da zakaji idan tayar da keke ta fashe dan sandan ya fadi wanwar hancinsa da bakinsa na tsiyaya ban koma ta kansa ba domin nasan an gama masa aiki saina harba da gudu na nufi takantar lambun. . Ruwan saman da ake tafkawa kamar da bakin kwarya ya fara tsagaitawa shirun dake kambun ahalin yanzu ta fara rayuwa da hayaniyar gudun yan sanda acikin ruwa daga can bangaren lambun usir mai karan gaske na tashi kamar algaita lallai ina ganin bala'i amma duk wannan kadan ne idan na tuna da sato sarkar gidan kanal mukhtar soja fa ba dansanda bane banbancinsu a bayyane yake. Nayi tsalle na kama katangar lambun sainaji an rike kafata wani dan gajeren dan sanda ne tsatstsama tsawonsa bai wuce takun kafa biyar ba ya fizgoni da wani irin zafin nama na mamaki santsin ruwa ya kwashe shi sai ya saki kafara ni kuma hannuna ya rabu da katangar na fado kan tsakiyar cikin dansandan sainaji kamar na fado akan kwallon kafa nayi tsalle gefe guda daidai lokacin ne dansandan ya tashi yayi yo kaina abinda da gajeren mutum tuni sai gashi acikina yayi sama dani ya hadani da bangon ya matse ni kamkam da kyar nake numfashi kamar daga sama sai naga wani abu kamar katako ya taho daga saman katangar dansan bai kula ba yanata kokarin fasa min ciki da matsa katakon ya daki tsakiyar kan dan gajeren dansan nan yayi yar dani ya fadi ko motsawa baiyi ba na dube shi na hada masa naushi a fuska kafafunsa suka mimmike sannan yai shiru kamar matacce . Kama nan Fadil wata siririyar murya tace dani daga saman katangar muryar sananniyace agareni saidai bazan iya tunawa ko ta wacece ahalin yanzu. Aka zuro min kafa sanye da takalmin ruwa baki na kama ta na yunkura sannan na kama saman katangar can kasan katangar wani siririn layi ne wanda ya ziro min kafar shi ya fara disa kasa ni kuma na bishi abaya ya kama hannuna muka mike cikin wani loko da gudu wasu yara suna karatun Islamiyya acikin wata rumfa suka zuba mana ido suna kallon mu bayan wani dan lokaci saigamu abakin titi motoci sunata zirga zirga saida naga mun nufi wata bakar mota fasfanda sannan na gane mai ja na yi sauri ka shiga AMINA tace dani rigar ruwan da tasa ita ta maida ita kamar namiji fuskarta na kyalkyalin farin cikin sake ganina . SHIDA 6 Aduniyar nan gaba dayanta banga wanda yafi masoyi ba lallai duk wanda yace yana sonka koda da wasa ne to ka rungume shi hannu biyu ada ban san haka ba sai da Aminatu ta tseratar dani daga hannun yan sanda sannan na fahimci cewa mai sonka shi yake bada rayuwarsa wajen ceton taka rayuwar Nayi tunani mai zurfi alokacin da Amina take zura gudu damu acikin motarta aduk cikin abokaina banga wanda zai iya min abinda Amina tayi min ba sai yanzu na gane irin son da Amina takeyimin sone na hakika SON UWAR YARA ba so irin na badura anuna ma so a lalata rayuwarka akaro na farko tun farkon haduwatarmu da Aminat sai naji kaunarta ta mamaye min zuciya cikin minti goma sha biyar saigashi ina nadamar kin karbar soyayyar amina da na yi hakika na wahalar da rayuwarta nakuma zalunci kaina domin nasan abinda tayimin tagama karya min zuciya ta sani na kamu da ciwon sonta batareda na shirya ba in da ace Amina zatace bata sona ahalin yanzu to da wahalar da zan sha sai tafi wacce tasha linkin ba ninkin. Tunanina ya katse adaidai lokacin da amina ta taka birki sannan ta sauka daga kan hanya ta tsaya tsakaninmu da kaduna yayi min biyar tun lokacin da muka shiga motar babu wanda yace da wani kala. Amina ta juyo ta fuskance ni tana murmushi sannan ta dafa kaina tace dani Sannu Fadil wallahi kasha wahala kalli duk yadda ka canza kamar ba kai ba yanzu da sun kashe ka ni yazanyi aduniyar nan Fadil danima karshen farin cikina yazo kenan. Kiyiwa Allah godiya dayasa har yanzu inada sauran numfashi nace da ita wata mota tazo da gudu ta wuce mu kamar walkiya cikin hasken fitilar motar sai Amina ta kula da hannuna inda gilas ya yanke ni tun ina kan bishiyar gidan nan mai lambu nan da nan ta kunna yar karamar fitilar dake cikin motar dana kula naga hannun ya kumbura haryanzu jini na zuba kadan kadan. Bari na daure ma Amina tace dani dame zaki daure? Na tambayeta. Bari ka gani mana tace dani sannan sai ta cire dan kwalinta gashin kanta ya bayyana yana sheki kamshin damina da kuma kamshin turaren dake jikin Amina suka hadu suka cika cikin motar suka bada wani irin kamshi mai faranta rai muka hada ido da ita sai kwarjininta yasa na dauke idona kaunarta ta cika min zuciya begenta ya mamaye kwakwalwata bansan lokacin data daure ciwon da kallabin taba. Kingazaki bata dan kwallinki da jini nace da ita haba fadil lafiyarka ai tafi komai agareni tasa siraran yan yatsunta masu taushi tana shafar saman fuskata kalli duk yanda fuskarka ta kumbuta na matsa kusa da tagar motar na dubi fuskata ajikin mudubi sai naga yan yatsun jibgegen dansan dan guda biyar a fuskata fatar bakina ma ta kara girma babu komai Fadil amina tace idan munje gida sai mu sami asibitin da zasu duba ka kada ki damu nace da ita kedai kiyi kokari mu tsira tukunna Fadil amina ta kira sunana hannunta acikin hannayena tana matsawa dana lura sai naji yan yatsunta suna rawa acikin tafin hannuna sannan taci gaba da cewa nayi ma tambaya zaka bani amsa? Allagh sa nasani nace da ita Fadil kana sona kuwa kamar yanda nake sonka? Muryar ta na rawa kada kace nayi rashin kunya wallahi sonka danakeyi yafi karfin na boye azuciyata kai kuma naga kamar baka damu dani ba fadil don Allah ina rokon arziki daya kafin muci gaba da tafiya ina son ka fada da bakin ka cewa kana sona koda da wasa ne. Sainaji dadin tukin da zan tserar damu daga sharrin makiyanka ya masoyina bana son ace kana kusa dani amma bansan matsayina azuciyarka ba. Mukayi shiru na dan lokaci na kalleta nace da ita AMINA kwanakin baya da suka wuce bana tunanin zan taba kaunarki amma ayanzu sonki da begenki sun zama ginshikin rayuwata wallahi Amina ina kaunarki bazan iya bayyana miki yadda nakejin sonki acikin zuciyata ba na baki amanar kaina sai yadda kikayi dani na zama naki Amina bansani ba ko kema kin zama tawa? Na tambayeta tayi min murmushin dana tabbatar na farin cikin jin kalamaina ne. Daman ni takace Fadil na gode da abinda naji daga bakinka koda kuwa baikai zuciya ba. Nima na saki murmushi kwatankwacin irin wanda tayi min kada kiyi shakkar abinda na fada ya masoyiyata abar kaunata kece tauraruwata ta shekara kauna so da bege agareki bazan taba dainawa ba muka hada ido da ita abinda ta gani a idona shi ya tabbatar mata da gaske nake kunya ta kama mu gaba dayanmu sannan ta lullube idonta da tafin hannayenta biyu wayyo rabin raina Amina tace dani cikin murmushi. Amina ta jijjiga kafadata na tashi firgigit tun lokacin da muka ci gaba da tafiya na fara yin barci saboda gajiya da kuma zazzabin dake damuna bayan Amina ta gane zazzabi na damuna saita dauko gyalenta daga cikin wata bakar jakarta ta rufeni dashi sannan mukaci gaba da tafiya bana tsammanin Amina zata tasheni daga barcin batareda wani dalili ba don haka batareda tambaya saina tashi zaune kallo daya nayiwa fuskarta na tabbatarwa kaina babu lafiya sannan na gansu acan gabanmu suna tsatstsaye cakare cakare abakin hanya ko wannen su sanye da bakar rigar ruwa da bindigoginsu a makale a kafadarsu Ko wannen su sanye da bakar rigar ruwa duk da yake kuwa an dauke ruwan da bindigoginsu a makel a kafadarsu. . Tun kafin mu karaso suka fara dallop mana fitila suna yi mana alamar idan munzo mu tsaya acan gefen hagu kuma na titin sun balbalawa tayar mota wuya tana ci a kusa da wutar ne idona ya gane min wani dan karamin katako ajikinsa an rubuta kamar haka cikin harshen turanci STOP POLICE CHECK Amina ta taka birki muka tsaya. Ka koma bayan motar ka kwanta banyi mata musu ba sai kawai na fada bayan motar na kwanta aminta ta janyo wani katon tamfal ta rufeni sannan ta juya ta nufi yansandan bayan mun danyi tafiya sai naji motar ta tsaya nayi mutuwar tsohuwa acikin tamfal din bana ko cikakken numfashi saboda tsoron kar ajini zazzabin dake jikina na riga na mance dashi ahalin yanzu inata kaina ne. Sannunki hajiya wani gwarin dansanda yace da ita yawwa sannunka da aiki Amina tace cikin dariya ya dukan ruwa? Dansan ya dan kyalkyale da dariya sannan yace haba hajiya kinajin zamu zauna ne anan ruwa yayi ta dukanmu ai kinsan zatayi wuya sannan yaci gaba da cewa da za'a fara ruwan ma yanzu da duk gida zamu gudu Don cika aiki ko? Amina ta tambaya cikin dariya abar maganar dan sanda yace da ita ina zuwane hajiya zanje kanon dabo amina ta amsa masa ko zamu iya duba bayan motar ki a'a bazaku iya ba Amina tace cikin dariya kai dan samari karka bata min lokaci kaje can ka nemo wanda yayi muku kisan kai amma banan ba ko kana tsammanin harkata harta kai ta wadda zan dauko mai kisan jama'a abayan motata? Kin cika surutu yan mata dan sandan yace oho wato yanzu an tashi daga hajiya kenan na koma yan mata to nima bari in kira ka yallabai idan baka yarda dani ba to je ka duba amma kada ka nuna ka sanni idan muka hadu dakai a kano watarana tunda sharri zakayimin haba hajiya yan mata abin har yazo da haka kada ki damu daman wasa nakeyi miki wanda muke nema ina tsammanin tuni yabar kaduna mu ma munayine don dole sannan dansan ya dan marairaice muryar yace da ita idan nazo kano a ina zamu hadu? A daula otel amina tace dashi cikin rada wa zan tambaya idan nazo dan sandan ya tambayeta kace kana neman BABY To shikenan sai nazo sandan yace zaki iya tafiya amina ta taka motarta mukayi gaba koda mukayi gaba sainaji karar wata katuwar mota abayanmu taja birki lallai sun batawa dansandan shiri nace cikin zuciyata. . ******** ******* ********* ******* . Tsakaninmu da kano yanu bai wuce mil ashirin ba mun wuce karfi da kadan tun da muka bar yansandan nan babu mai cewa komai aminatu tana ta maka gudu damu kamar zamu tashi tunda muka baro kaduna har zuwa yanzu banga motar data wuce mu ba lokaci lokaci amina takan dubeni tayimin murmushi murmushin shi yake sani nake dan manta halin danake ciki soyayya da dadi take agurin wanda ya samu mai sonsa. Duk rikicin da mukayi da yansanda jakar da yayana yabani tana bayana KADA KA SAKE KABAR JAKAR NAN TA BATA KATAFI DA ITA DUK INDA ZAKA... maganar da yayana yayita jaddada min kenan daya bani jakar alokacin da zan tafi kaduna na gyara daurin jakar dake bayana hannuna ya dunguri aljihun gaban rigata sai naji kabarkabar nazaro wata takardar daga ciki tasha ruwa har ta fara bushewa amma haryanzu rubutun jikinta bai goge ba na budata rubutun saman takardar shi ya tuna min ko ta mecece tsarin gidan Kanal Mukhtar ce shine abinda ke rubuce a jikinta takardar da badura tabanice hade da jaridan nan tun ina gida mai lambu na kaduna kada kayi zaton zan bar amina taga takardar don haka saina saye ta a aljihuna. . Saura kadan hancina ya daki gilas din gaban motar a sakamakon birkin da amina taja saida tayar motar tayi kara kuu can gaban mu motocine sama da guda biyar anfito da mutanen ciki anata bincike mukayi shiru na dan lokaci muna kallon abinda ke faruwa. Ya kamata ki kashe fitilar motar na ce da ita kwakwalwata ya fara tunanin mafita yansandan kano fa ba irin na kaduna bane idan Amina ta yaudari wani ya yarda toh wani bazai yarda ba sannan ne dabara ta fado min duhun gero ya rufe ko ina abakin hanyar na kalli amina nace da ita zan sauka nabita cikin gero ke kuma sai kiyi gaba idan sun gama binciken ma hadu agaba karki tsaya sai kin baiwa min daya baya sannan ki jirani nayi mata murmushin tabbatar mata da abinda na fada kada ki damu rabin raina nace da ita banjira wani abu ba sai kawai na bude murfin motar na dira amina ta bari saida na shige duhun geron sannan taja motar tayi gaba. Ruwan saman da akayi a kano baikai na kaduna ba amma hakan bai hana cikin duhun geron sanyi ba abin ka da mai jin zazzabi nan da nan saina fara rawar dari na daure naci gaba da tafiya cikin geron bayan yan mintuna saina fara jiyo hayaniyar yan sandan sunayiwa masu mota tambayoyi tsakanina dasu bai wuce taku shida ba amma duhun geron bazai barsu su ganeni ba na karaso wata duhuwar gero akusa da wajen akwai wata katuwar bishiyar kuka don haka sai nabita bayan kukar da nufin ci gaba da tafiya sannan ne nayi tuntube da wani abu na wuntsila gaba nazo da fuska a kan tushiyar gero da farko na dauka kututturen bishiyane ya tadeni amma karar razanarKIBIYAR AJALI 19 . Amma karar razanar danaji abayana shi ya tabbatar min ba kututture bane. . Kana motsawa ina harbeka dansandan dogo ne siriri yana rike da bindigarsa a hannun dama hannunsa na hagu kuma rike da wandonya yana barazanar sullubewa duk da yake ya tsorata saida abin yaso yabani dariya saboda ganin dan sandan fitsari yake nayi tuntube dashi na tashi tsaye ina rawar jiki hancin bindigarsa akan goshina babu mamaki ma kaine mutumin da yayi kisan kai a kaduna dansan yace cikin fushi me kakeyi anan ya daka min tsawa aikin da muka sashi yakeyi wata murya ta amsa masa tambayarsa daga baya idan baka aje bindigarka ba to saidai ku mutu tare kana harbinsa ina harbinka muryar tace daga baya dansandan ya saki bindigarsa kasa yana rawar jiki kamar mazari cikin razana sai ya saki wandonsa kasa yafado daga shi sai diras mutumin ya zagayo ya dauke bindigar dansandan cikin mamaki da razana saina gane ko wanene mutumin da ban taba zato zan gani ahalin yanzu ba duk da yake akwai duhun dare hakan bai hana ni ganin kayan jikinsa ba KOREN WANDO DA FARAR RIGA abinda ya dada razanani shine yadda akayi ya biyoni batareda na sani ba Salman na kra sunansa muryata na rawa . KASHI NA BIYU 2 . BAKWAI 7 Salman nakira sunansa muryata na rawa. Hakika al'amura sunata faruwa agareni kamar a majigi daga wannan sai wannan daya bayan daya kamar jan carbi nikam yanzu nafara fitar da rai da rayuwa musamman ma danayi la'akayi da irin bala'in dake samuna bi da bi kamar yayan carbi sai yanzu ne na yarda cewa duk wanda yakibin maganar na gaba dashi to lallai yana tare da nadama domin danabi maganar yayana nayi zamana a gida to da yanzu saidai nima na karanta irin wadannan abubuwa da ke faruwa agareni kamar yadda kuke karantawa ahalin yanzu duk wannan tunanin nayishine lokacin da salman ya dago kai ya dubeni yana murmushinsa irin maisa kananan yara mafarki dansandan dake gefenmu yayi sororo kamar mutum mutumi ga dukkan alamu yana tsammanin alburushin bindigar salman zai iya ratsa jikinsa akowane lokaci daga yanzu domin irin tsayuwar da dansandan yayi ba dan yana numfashi ba da sai ka iya kiransa matacce amma mutuwar tsaye kayi mamakin ganina ko? Salman ya ce dani na dago kaina dube shi da niyyar nayi magana amma tsoro da mamaki suka hana harshena fadin komai. Kada kayi tsammanin zamu barka kayita aiki batareda saninmu ba Salman yaci gaba da cewa dole ne mu sa ido aduk abubuwan da kake don ganin ka cimma nasara wajen sato sarkar saboda haka ko kana niyyar wata kurda kurda ko kuma wata yaudara don kin bin umarninmu to ka tabbata bazaka kai labari ba domin duk abinda ke faruwa tun daga kaduna ina nan kusa dakai sannan salman yayi dariya yace wannan umarni ne daga uwar gidata Badura kuma zanci gaba da binka abaya a baya har sai ran da naga kaci narasa wajen sato sarkar ka kuma baiwa badura sarkar kamar yadda muka tsara maka cewa daula otel ce wurin da zamu hadu ka bada sarkar idan kayi haka to sannan ne zan rabu dakai amma yanzu kam da kai Allah ya hadamu zanyita binka kamar yadda ajali ke bin rai zan kuma fada ma wani abu Fadil Salman yace dani bance dashi komai ba don haka sai yaci gaba da cewa masoyiyarka amina ni nayi mata talfon agidan data sauka na kaduna na kuma sanar da ita inda kake domin tazo ta kwaceka daga hannun yan sanda za kuma kayi mamakin ganin mun kyaleka kafita garin kaduna kai kadai amatsayin mai laifin kisan kai kuma ta cikin hadari iri daban daban to munyi hakane domin mu gwadaka muga jarumtarka to hakika yanzu muna sa ran cewa idan akwai mutumin da zai iya sato mana sarkar to kaine gumi sai kwarara yake daga goshina zuwa bayana tunda na fada cikin bala'in nan sai yanzu ne naga Allah ya budo min hanyar da zata fitar dani idan yansanda sun kamani idan baka sani ba to bari fada ma salman nata sharara labari bayako tunanin cewa gaban shaida mai kwari yake bayaninsa dansan dake gabana ya isheni shaida fatana daya shine Allah yasa Salman ya barshi da ransa wannan tunani shi yasa na fara tunanin cewa Salman ya tabu hakika mutum mai hankali bazai taba fadar laifin daya aikata agaban dansan ba. . Tunanina ya katse adaidai lokacin danaga salman yafara murmushin muguntarsa kirjina ya fara dakan uku uku domin murmushin salman yana bayyana ne aduk lokacin dayake shirin aikata tabargaza kafin na karasa tunanina salman ya daga bindigarsa ya daki kan sandan duke ne irin wanda zai iya jefar da ingarman doki dansan ya kifa da fuska da wani irin kuka mai kama da na karamin yaro bai ko shura ba a tunanina ya mutu idan kuwa ya mutu da kuwa damata ta karshe ta subuce kenan Allah yasa bai mutu ba nace cikin zuciyata yakamata ka kama gabanka salman yace dani a fusace Amina nacan tana jiranka kada ka sake kiran sunan Amina nace dashi bana son kusa ta cikin wannan rikicin nidai dana riga na shiga to na shiga amma ita ku barta waje guda. Ta riga ta sa kanta salman yace dani idan ma kuma da batayi saurin sa kanta ba to dolene anan gaba ta shiga saboda me kace haka? Na tambayi salman ka tambayi badura salman yace dani sannan yayi murmushi Saboda me kace haka? Na tambayi salman ka tambayi badura salman yace dani sannan yayi murmushi kafin na sake tambayarsa wani abu tuni salman ya sake bacewa acikin duhun daren da yafito kamar Fatalwa . *********** ******** ********* ********** . Rabin raina ina ka tsaya ne

Chapter 4 of 9