Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
kibiya na rufe idona ina addu'a alokacin ba fargabar kamani da akayi ba nake fargabar nake hade take da mugun tunani yanzu idan badura taci karo da babbar mota ya za'ayi kenan? Ba zamu ko motsa ba nace cikin zuciyata. ** Idanuna a rufe ina addu'a badura kuma tana kwarara gudu damu kamar zamu bar duniya abin yayi matukar girgizani lokacin dana bude idona hakika dazu dana rufe idona acikin birnin kano muke amma yanzu ga mamakina sai na ganmu muna kokarin fita wajen kano munata sheka gudu dansandan dake gaban motar ya dubi badura cikin fushi. Ina kike nufin kaimune? Ya buga mata tsawa ofishin yansandann jiha ko ba can kace ba yallabai? Ta tambaya babu isashshen haske a motar amma hakan bai hanamin ganin murmushin daya bayyana kyawawan lebban badura ba. Hantar cikina ta kada murmushin irin wanda tayi minne lokacin da salman ya dakeni da gindin bindiga acikin dajin kaduna inda na sume ita kuma ta bada umarnin a daureni bambancin kawai aka samu shine wannan karon bani take yiwa murmushin ba wanda ke dauke da barazana dakuma gargadi da wanda akeyiwa murmushin tabbas nasan wani abu badura ke shirin aikatawa bana kuma tsammanin abin zaiyi mana dadi gaba daya a matsayina na wanda yayi digiri akan halayen badura sai murmushin ya zame min kamar jar danja ce wanda ke nuni da cewa ga hadari nan tafe bangama tunanina ba sai kakkausar muryar dansandan ta sake cewa. Ki kuka da kanki yarinya tunda har kika sake kikayi wasa da hankalina sannan yaci gaba da cewa saina nuna miki iyakarki idan har badura ta dago ta kallenshi to dutse ma zai iya kallon ka idan kayi masa magana ta take totur din motar gaba daya ruwan saman da akeyi kuma ya wuce yayyafi ahalin yanzu domin tuni gaban gilas din motar ya jike da kyar badura take ganin gabanta irin gudun da badura ke shekawa shi yasa fuskar dansandan ta canza cikin lokaci kankani sai duk kamanninsa suka sauya idanunsa suka firfito saboda tsoro da fargaba ya juyo ya kalleni sannan ya juya ya kalli badura wacce tuni tayiwa kano nisa ni kaina bansan ko hanyar ina take bi damu ba ruwan saman da ake shekawa da kuma duhun daren su suka hadu suka juyar min da kwakwalwa dadin dadawa kuma ga ciwon dake hannuna shima ya tsananta. . Tsaya na sauka don Allah dansandan yace cikin tsoro da fargaba don Allah ki tsaya na sauka wallahi na tuba duk da yake hannuna na radadin zafi hakan bai hanani yin murmushi ba nayi kokarin yin dariya amma na kasa. Dansandan yayi matukar bani dariya wanda ke buga mana tsawa sai gashi yana Magiya. Ina zaki damu? Dansandan ya sake tambaya cikin rawar murya INDA BAZAMU DAWO BA badura tace dashi adaidai lokacin ne akayi wata tsawa mai karfi wacce tasa motar mu ta girgiza saura kadan matukin motar mu ta kwace daga hannunta akayi walkiya hakan shi ya sani ganin fuskar dansandan wacce ta hade sharkaf da gumi gashin bakinsa sai diga yake da gumi fuskarsa kuma ta koma launin gasashshen nama. . Ka nuna min kai dansanda ne badura tace dashi menene amfanin bindigar dake hannunka? Ta tambaye shi tana murmushi ko ka dauka ina tsoron zungureriyar bindigar kane? Zan kuwa nuna miki ni dansandan ne dansandan ya daga bindigarsa yayi saitin badura na rufe idona cikina na rawa cikin yan dakikun da abin ya faru na dauka harbawa zaiyi don haka sai nayi kalmar shahada na kuma runtse idanuna ina jiran naji karar bindiga abu daya na tabbatarwa kaina nasan in har ya harbi badura acikin wannan gudun da take da motar to muma rayuwarmu tazo karshe kenan hakan shi yasa wani irin sassanyar gumi barkowa daga goshina zuwa kan fuskata naci gaba da kalmar shahada domin na tabbata mu tamu tazo karshe tuni har zuciyata ta fara ayyanawa wai gani nan na mutu an daukoni amakara an nufi makabarta dani. . Minti guda ya shude banji karar bindiga ba bankuma ji motar ta hantsila damu ba don haka saina bude idanuna domin naga abinda ke faruwa ga mamakina sai naga dansandan ya maida bindigar hannayensa na rawa KA HARBA MANA TSORON ME KAKEJI YALLABAI? Badura kenan take cewa cikin zazzakar muryarta da ba zan taba mantawa da ita ba Ka tuna fa kai namijine acikin mazan ma kuma wai dansanda tunda nake bantaba ganin mace mara tsoro kamar badura ba na duba irin ruwan da ake tafkawa gami da iska amma duk wannan batasa ta rage gudun da takeyi da motar ba maimakon hakan saita kara take totur din motar gaba daya dansandan dake zaune agaban motar ya zama kamar mutum mutumi baya ko motsi saboda tsoron abindake shirin faruwa idonsa akan.. Dansandan gake zaune agaban motar ya zama kamar mutum mutimi baya ko motsi saboda tsoron abindake shirin faruwa idonsa akan sitiyarin motar ya bude baki kamar zaiyi magana sai yayi shiru babu mamaki gani yayi maganar tasa ma bazatayi tasiri ba dansandan ya lumshe idanunsa hakan shi ya bani damar tunanin cewa babu mamaki addu'a yakeyi can sai ya nisa yace da Badura. Ya kamata kisan abinda kikeyi bakisan wannan gudun da kike halaka zai kaimu gaba daya ba. Ina tsammanin halakar ita tafi dacewa damu badura tace dashi idonta akan titin da muke bi dazun nan fa kake shirin kai masoyina ga halaka kasan kuwa in har ina numfashi abayan kasa babu wanda ya isa ya hana min saurayi..... Wa yace zai halaka shi? Dansandan yace muryarsa na rawa lokaci lokaci kuma yakan kalli malejin motar wanda tuni an kureshi har karshe. Laifine ake zarginsa dashi don haka dolene na kama shi tunda na ganshi ba laifina bane wallahi yanmata don Allah ki tsaya na sauka ya fara magiya. . Kada kayi min magiya badura tace dashi ai kasan cewa idan ka kaishi hannun mutananku hukuncin kisa za'a yanke masa amma baka damu ba da rayuwarsa sai yanzu ne kuma kake tsammanin zan damu da rayuwarka? Sannan taci gaba da cewa rayuwata batada amfani agareni in har na bari aka hallaka min rabin rayuwata akan laifin da bashi ya aikata ba wallahi na gwammace ni na salwantar da tawa rayuwar akansa sannan ta dubi dansandan da kyau tace dashi Mahaifiyata da kuma taimakona suka jefa laifin kisan kan da bashi yayi ba akansa inason ka zama shaida kaima tace da dansandan duk da yake kuma lokaci lokaci motar takan dan kufce daga hannunta amma hakan bai hanata ci gaba da maganar ba nikuma ban dainayin addu'a ba domin ni a tsammanina kowanne lokaci dansandan na iya fushi yayi kokarin hana badura tukin sannan kuma sauran abinda zai biyo baya ba sai an bayyana ba. Na maimaita na sake maimaitawa da ace Fadil ya halaka garani na halaka a hanyar kare tasa rayuwar badura tace don haka nayi niyyar tserar dashi daga sharrin da akayi masa ban kuma ga wanda ya isa hanani tserar dashi din ba sai ko ubangiji mahalicci amma ba dai mutum ko aljan ko kuma mutanenku yansandan. Tace da dansandan cikin sassanyar murya haryanzu dansandan baice komai ba a tunanina banajin yana saurarer abinda take cewa ma babu mamaki shi tunanin hanyar da zai tsira da rayuwarsa yake domin gudun da badura take ya wuce kima mima kuma abin ya fara bani tsoro. Ya kamata ki dan saurara haka badura nace da ita akaro na farko tun lokacin da muka bari cikin garin kano. Haba Masoyina tace dani baka ganin idan muka tsaya anan ritsamu zai sakeyi da bindigarsa ya kama ka? Ni ban damu da kaina ba Fadil inda dan tanice to da saina barshi ya tafi dani amma kai a'a bazai taba yiwuwa ba indai kaga har na tsaya ya sauka to sai ya yarda da sharuddaina guda biyu ta dubi dansandan. Wadanne sharudaine? Fadi naji wallahi zan cikasu inhar zaki saukeni Sharadin farko shine ka jefar da bindigarka ta tagar motar nan na biyu kuma shine ka koma bayan motar ka kuncewa Fadil ankwar dake hannunsa Na yarda dansandan yace nan da nan ya sauke gilas din motar ya jefa bindigar kasa ta bada wata irin kara lokacin data hadu da kwalta sannan sassanyar iska hade da ruwa suka feso cikin motar saboda tagar motar da dansandan ya bude nan da nan yayi sauri ya rufe sannan ya juyo tsakanin kujerun gaban motar yace Miko Hannunka. Ban sami damar mika masa hannun ba saboda abinda na hango a gigice a tsakiyar titin muke bi wani gungumemen reshen bishiyane wanda kuma cikin dakikar dana ganshi kwakwalwata tasanar dani cewa yan fashine suka gindiya shi nayi mamakin ganin Badura bata ko rage gudu ba. Kalli Gabanki nace da ita cikin karaji dansandan ya rufe idonsa jikinsa na rawa badura ta take birki motar tayi kuli kulin kubura damu abu na karshe danaji shine karar dansandan nan cikin gigita lokacinne akayi jifa dani waje ta gilas din Motar. . 14 Na farka agigice sakamakon sassanyar ruwan sanyin da aka kwaramin a fuska bansan abinda ya faru garemu ba tun bayan lokacin da mukayi hadarin nayi kokarin bude idanuna amma abin ya gagara matsanancin ciwon kan dake addabata shiyake barazanar raba kaina gida biyu aduk lokacin danayi kokarin bude idona Na fara kokarin tunanin abinda ya faru a kanmu koda yake ban cimma nasara ba kwakwalwata ta daina tunanin komai sai juyawa kawai takeyi kamar yadda hannun agogona manunin dakika ke juyawa duk wannan bai tashi hankalina sosai ba sai bayan danayi kokarin dago hannayena domin na rike kaina wanda ke barazanar rabewa saboda tsananin ciwo gabana ya fadi danaji hannayena a daure sauke tamau abayana Alokacin wato kwakwalwata ta fara tunani sosai na gane cewa hadari mukayi amma daga nan ban iya tuna komai ba hakan shi ya tabbatar min da cewa suma nayi to idan suma nayi ina Badura? Kuma ina muke ? Na tambayi kaina kamar amsar tambayata sai aka zungure min kuguna da wani abu mai tsini tuni zuciyata ta ayyanamin cewa mashine sai bayan dana bude idanuna ne sannan na gane nayi Kuskure Yana tsaye akaina.. Yana tsaye akaina dan kerera ne wanda ganinsa ya tunamin da barbushe wanda na taba karanta labarinsa acikin (Kano Ta Dabo Ci Gari) yanada jajayen idanuwa kansa shan kwalan kafane kansa kuma aske yake tas yana kyalli kamar madubi ga mamakina sainaga idonsa fari tas kamar madara sabanin guntun ire iransu wadanda su idonsu jajur yake kamar garwashin wuta boye kammaninsa masu firgitarwa abinda kawai zan iya cewa sun kara masa shine sunfito da kammaninsa irin na kumurcin maciji kada kaji ance idanunsa fararene ka dauka kuma wai manya ne masu kyaun gani sabanin haka shi nasa kanana ne kamar da reza aka yankasu yana sanye da wando da riga bakake tafkeken sawunsa kuma sanye cikin takalmin karfe irin wanda kafiran da can sukayi yaki dashi. Hakan shiya tabbatar min kuskurena a fili na tunanin wai da mashi aka sokeni. Na dube shi babu alamar murmushi a fuskarsa murtuk yake kamar wanda aka sanar dashi adadin kwanakinsa aduniya na duba izuwa bangarena na hagun annne to na hango badura akan kujera suka zaunar da ita suka kuma hadata da kujerar suka daure mukayi ido hudu da ita idonta ya cicciko da kwalla abin mamaki kuma shine dagani har ita babu wanda yayi koda kwarzane daga hadarin daya faru akanmu. Sannan ne to na tuna da dansandan nan babu mamaki dansandan ya mutu sakamakon hadarin daya faru akaro na biyu saina sake gane kuskurena ban karashe tunani naba sai kofar dakin ta bude su uku ne suka fito dakin dauketa dansandan suma dankara dankarane koda yake banajin idan an hadasu duka ukun zasu kai girman shugabansu. Suka shigo dakin ahankali saidai kuma kowannensu yana muzurai suna zuwa sai sukayi jifa da dansandan ya gangaro ta matattakalar da fuska akan tsandaurin kataki hade da karar data razani zakayi mamakin jin cewa inata magana akan katako amma nasan baka gane abinda nake nufi ba to bari na baka hoton yadda dakin da muke ciki yake a bayyane da farko dai zan iya cewa bangon dakin da kuma kasan dakin duk da katako aka ginashi tangamemen dakine wanda keda taga daya da kofa daya saidai shi kofarsa da tagar ba daya take da ta sauran dakunan ba daka sani shi wannan daki tagarsa da kofat a sama suke don haka ko su yan fashin saita hanyar amfani da matattaka irin ta bene suke shiga dakin. Hakan shi ya sani tunanin to idan ana ruwan sama yaya zasuyi kenan? Nasan dolene ruwa ya cika dakin koda yake kuma banga alamar zubar ruwan sama a dakin ba. In ka dauke wasu yan tarkacen kayayyaki dake kusa da badura duk sararin dakin babu komai sai wasu kujerun katako guda uku biyu daga cikinsu a kakkarye suke mai dan kyan daga cikinsu itace mai kafa daya Faffadan bakinsa mai kama da saran adda ya fadada izuwa abinda shi yake tunanin wai murmushine sannan ne na gane cewa ashe bashi da hakoran gaba guda uku wawilon dake bakinsa shi ya tuna min da bakin kadangare. . Kayi mamakin ganinka anan ko? Ya tambayeni yana kallona tsigar jikina tayi yarr ko kadan bana son murmushinsa Nine DAWAYE yace dani sana'ata kuma shine fashi da makami abinda nafi kauna aduniya kuma shine na kwace kayan da ba halak dina ba sannan ya kyalkyale da dariyar mugunta kukan jaki yafi dariyarsa dadin ji na dubi badura jikinta na rawa kamar mazari dansandan kuma da suka jefo na kwance jini na fita da baki da hanci hakika yana cikin matsananciyar azaba kuma na tausaya masa. Nayi farin ciki da kamaku danfashin yace dani yana murmushin mugunta duk da yake kuwa bamu sami komai a gurinku ba amma akalla mun kama makiyammu ya nuna dansandan da takalmin karfensa mai tsini Makiyanmu ne dan fashin yace dani kune kawai da kuke neman halal kuke tunanin masoyan kune amma a zahiri makiyanku ne tunda yanzu ma babu mamaki yana shirin kulla muku sharri ne. Maganar dake fitowa daga bakinsa babu kai ba gindi su suka sa na fara tunanin ko mahaukaci ne domin agurina dansanda ba makiyi bane duk da yake kuwa suna nan babu adadi suna farauta ta nasan cika aikinsu sukeyi rashin sani ne kawai yasa suka kasa gane gaskiya. . Kamar yadda suke kama mu suna harbewa haka muma idan mun kamasu bazamuyi musu ta dadi ba zamu kashe duk wanda yazo hannunmu acikinsu har da abokin tafiyarku ya nuna dansandan dake kwance maganar tayi matukar girgizani nakuma zargi badura cikin zuciyata saboda ita tayi sanadiyyar kawo shi ga halaka duk da yake kuwa ni take kokarin tsewarwa. Acan ma daya bangaren badura nata zubar da kwalla jin cewa za'a kashe dansandan nan shi yasa jikinta ya sake daukar rawa. Kada ka damu danfashin yace dani yana dubana bazamu kashe ka ba amma zamu mai dakai yaronmu ita kuma yar uwarka mai dafa mana abinci sannan ya sake kyalkyalewa da dariyar mugunta babu mamaki gome zamu kashe makiyinm ya nuna dansandan bakuma kisan bindiga zamuyi masa ba kisan da zamuyi masa bana farat daya ne ba sannan danfashin ya sunkuyo inda nake kwance yana zazzare idanu daga inda nake ina iya jin hucinsa kamar giwa. Da'ayi maka irin kisan da zamuyi masa dan samari gara a harbe ka da KIBIYAR AJALI ka mutu lokaci guda. Sannan ya sake.. .Gara a harbeka da kibiyar ajali ka mutu lokaci guda sannan ya sake dosaro gashin bakinsa kusa da fuskata kasan irin kisan da zamuyi masa? Ya tambayeni ban amsa ba ni ko motsi bana iyayi don razana da farko zamu yanke kunnuwansa daya bayan daya sannan mu yanke hancinsa zakuma mu datsa hannunsa na dama da kuma na hagun sannan kafafunsa da haka zamu kashe shi. Badura ta kwalla kukan razana da maganar dayayi daya daga cikin yaran da suke tsaye a bayansa ya matsa gaba ya falleta da mari har sai da kanta yayi baya dakin yayi shiru na dan lokaci bakajin komai sai hucin katon shugaban yan fashin nan sannan ya dubeni yace dani kayi mata nasiha dan samari idan ta sake yi mana kuka anan itama haka zamu kasheta Bansan lokacin dana sami kaina ina amsawa ba. ** Idan ka dauke sheshshekar kukan badura da kuma numfashin dan sandan nan dake kwance babu motsin komai adakin minti biyar kenan da ficewar yan fashin basu kuma fice daga dakin ba sai da nima wani daga cikinsu ya falla min mari. . Dolene nasan yadda za'ayi na tserar da rayuwar dansandan nan koda kuwa idan na tserar dashi din zai sake kokarin buga min sai yanzu ne na tuno da ankwar da dansandan nan ya buga min a hannu nayi mamakin yadda akayi har yan fashin nan suka cire ta daga hannuna batareda na farka ba. . Na dubi dansandan dake kwance magashiyan akasa jini na fita ta baki ta hanci haryanzu kayan ruwan na jikinsa na yunkura zan tashi sainaji ko ina ajikina na ciwo hannuna inda aka harbe ni ya dada kumbura abin ya bani tsoro saboda idan ba magani na samu ba zan iya hasarar hannun sa'a daya nayi yan fashin nan basu daure kafafuna ba sabanin dansandan dake daure tamau kamar damin goro na sake yunkurawa zan tashi zaune sainaji juwa ta daukeni na koma na kwanta numfashina sama sama yake zuwa ba'a dade ba bakake da fararen taurari suka bayyana a idona. . Aka kwara min ruwan sanyi a karo na biyu wannan karon daya daga cikin yaran dan fashin nan ne yazo yana tsaye a kaina kofin ruwan sanyi a hannunsa ba'a dade ba sai kofar saman ta bude jibgegen shugaban yan fashin ne ya nufo inda muke ya tako ahankali takan matattakalar benen idona akan matattakar benen tuni na fara tsammanin kafar benen zata ruguje saboda nauyinsa amma ga mamakina saigashi ya sauko lafiya matattakala uku ta rage ya sauko sai yayi tsalle ya diro tsakar dakin baiko damu ya karasa sauran matattakalar benen ba danfashin baiyi magana ba ya dai tsaya ne kawai akaina yana muzurai. Kwance shi yace da daya dan fashin cikin muryarsa mai kama da kwarankwatsa kamar daga sama sai wuka ta fado hannun dan fashin wannan shi ya tabbatar min da kwarewarsa wajen iya fada ya nufi badura da wukar tsirara ahannunsa gabana ya fadi domin a zatona soketa zaiyi amma sabanin haka saiya fara yanke igiyar bayan dan lokaci saiga duk igiyoyin da aka daure badura akasa badura tayi mika sannan ta mike tsaye tayi taga taga saita koma kujerar ta zauna banyi mamakin hakan ba ko wanene ya kwana daya a daure baci ba sha dolene ya kasa tafiya danfashin ya yiwo kaina da wukar yana zuwa sai ya yanke igiyoyin da suke daure da hannayena sannan ya kama hannuna mai ciwon na runtse ido sannan na budesu adaidai lokacin ne mukaji motsi a kofar saman dakin daya daga cikin yan fashin ne yake tattakowa zuwa cikin dakin farantin kayan abinci a kansa ahannunsa kuma na dama kuttun zuba shayi ne FLASK yawuna ya tsinke cikina yafara salati sai yanzune na gane inajin yunwa. Zamu baku abinci kuci danfashin yace amma ba zamu baiwa abokinku ba domin shi yau da yamma nan zai bakunci lahira na dubi dansandan cikin tausayi da kyar yake numfashi na dubi badura itama ta dubeni sannan dan fashin yace dani idan kun gama cin abincinku ku bar kwanukan anan kuna kuma iya fita ta saman dakin domin kuga yadda gidan namu yake saidai bamason tabe tabe akwai gurin wanka kuma awaje kana fita zaka ga kofofi guda takwas a jere mai launin fanti kore itace kofar bandakin sannan ya zazzaro idanu yace dani cikin gargadi da barazana da kuma tsoratarwa. Karka sake ka zolayi kanka babu mamaki tunanin gudu zaizo kanka to idan zaka gudu Bisimilla amma duk abinda ya faru akanku karka zargi kowa ya kyalkyale da dariyar mugunta kayi shirin gudu idan zaka iya amma karka laifina idan ka samu kanka a kabari sannan yayi shiru na dan lokaci yana kallona. Idan kayi niyyar gudun ma dan samari to ka tabbata babu inda zaka kana cikin dajin falgore ne atsakiyarsa kuma kake tunanin tsunduma babu gida gaba balle baya babu kuma abokam hira sai namun daji idan ka sake ka fita daga dogayen katangun gidan nan banajin zaka sake taku biyar batareda damisa ko zaki sun afka maka ba macizai ma sun isheka kawai sauran muggan namun dawa kuwa kamar su giwa kura mugun dawa karkanda da dai sauransu duk wadannan wasu abubuwane da zaku ke gaisawa dasu duk safiya saidai kuma ina tsoron na gargadeka da cewa idan har kana son rayuwa aduniya to kayi zamanka anan idan kuwa ka gaji da zama aduniya to ga fili nan ga mai doki daman mun dade bamu baiwa zakunan wajen nan abinci ba. Babu mamaki. Babu mamaki garabasa zata saukar musu ku biyu kenan ya nuna dansandan dake kwance da kakkauran danyatsan hannunsa mai kama da Ayaba. . Idan mun gama dashi namun daji zamu jefawa su lumashe shi ya danyi shiru sannan yace nasan yace nasan zakayi mamakin ganin mun dauko ku daga wani dan gari kusa da kano mun kawo ku har nan to abinda nake son ka gane shine bamu fiye fashi akusa da gidan ba ka kiyaye dan samari mu zamu fita sai mun dawo suka fice ta saman dakin basu dade da fitarsu ba sainaji karar harbin bindiga babu mamaki ta haka ne suke korar namun dake gurin kafin su shiga cikin motarsu. . 15 Ya kamata mu bashi abinci badura tace dani kina nufin mu kwance shi kenan? Ta gyada kai idan suka dawo fa me kike zaton zai faru ? Na tambayeta ta kalleni tayi dan murmushin karfin hali abincin da mukaci da kuma ruwan da muka samu mukayi wanka shiya taimaka wajen dawo da kuzarinmu dukkan wata gajiya yanzu ta fita daga jikinmu abinda kawai ke damuna yanzu shine hannuna dake damuna da ciwo a kumbure yake sumtum. Idan sun dawo sai mu yaudare su mu doddoke su tace dani batareda ta dubeni ba. Kamar yaya mu daddake su ? Na tambayeta banjira ta bani amsa ba saina ci gaba da cewa kina tsammanin mu uku zamu iya doke karfafan yan fashi guda hudu? Ki duba ki ga yadda hannuna ya kumbura fa kuma koda lafiya lau hannuna yake sanin kanki ne ki mu uku muka hadu bazamu iya doke shugabansu ba kuma bayan haka ma har yanzu bamu da tabbacin ko su hudu ne kawai ko kuma sauransu na makale awani wurin badura tayi shiru na dan lokaci sannan tace Banajin sun wuce guda hudu domin da sun wuce haka babu abinda zai hanasu shigowa dasu nan in ma basa nan nasan zai iya sanar damu cewa akwai wasu a makale ko dan ya tsoratar damu amma abinda zamuyi shine mu fara kwance dansandan da farko sannan sai muyi shawara har da shi nasan dai baai dace ba ace munaji muna gani anyi masa kisan gilla ko kuwa me ka gani DARLIN? Mamaki yakamani saboda jin cewa duk iya surutun da suka faru tsakanina da badura abaya bata taba kirana da Darling ba sai yanzu da muke cikin hali na kaka ni ka yi ban bari ta gane cewa kalmar data fada ta girgizani ba sainaci gaba da cewa. . Na yarda da maganarki DARLI.... nayi shiru ina kallonta bansan yadda akayi bakina ya subuce ba badura na kallona tana murmushi fuskarta cike da farin cikin jin kalamin daya so ya fito daga bakina. Ta matso a hankali haryanzu murmushin na nan a fuskata tana zuwa saita duba igiyar da aka daure dansandan da ita na tashi nima ahankali kafata kamar ba zata daukeni ba hannuna sai radadi yake bayan mun dan dudduba igiyar sai mukaga ashe ba wani kwakkaran dauri sukayi masa ba bamu dade ba muka kwance shi dansandan ya dan matsa sannan yace ku bani ruwa bangane abinda yake cewa ba saidana kara kunnena kusa da bakinsa badura ta miko min ruwa cikin katon kofi na bashi yasha sannan na tashe shi zaune na wanke masa jinin dake fuskarsa sannan na cire rigar ruwan dake jikinsa na dauko sauran abincin da muka rage na bashi soyayyiyar wainar kwai ce da hanta dakuma alkubus da miyar DAGE- DAGE nayi mamakin ganin irin yadda yan fashin suka iya dafa abinci amma dana tuna da irin rayuwarsu sai naga ai dole ne ma su iya. Awa daya kenan da gama cin abincinsa na raka shi bandaki yayi wanka sannan muka dawo dakin muka fara tattaunawa badura ce ta fara magana Ina ganin abinda ya dace mufarayi shine mu zagaya cikin gidan ina zaton zamu sami makamai kamar bindiga kaga idan muka sami bindiga daidai muke mu ritsa su koda sun kai ashirin kuma koda bindiga ce ahannunsu zamu iya ritsa su tunda mu buya zamuyi kuma kaga bandakin daf yake da kofar fita sai mu shiga ciki kaga suna shigewa sai mu ritsa su ta baya idan sun ajjae makamansu kai Fadil saika daddaure su kuma sai mu ritsa su idan ka gama daure su saimuyi amfani da motarsu mu fice daga cikin dajin nasan hanya bazata bace mana saimubi sawun tayar motar nasan in Allah ya yarda zata kaimu kan hanya kunga daga nan mun tsira kenan to yaya kuka gani ? Ta tambayemu tana murmushi gaba dayanmu sai muka amince da shawarar da badura ta bayar dmin babu wata hanyar data wuce wannan amma da farko shine mu sami bindigogi idan kuwa bamu samu ba to kashinmu ya bushe. . Mukabi matattakalar benen da zatafitar damu kofar sama gaba daya muka fita tsakar gidan kana fita zaka yi ido hudu da kofofi guda takwas biyar daga cikin kofofin sunada launin fari biyu kuma launin ja saikuma ta karshen launin kore wato bandakin gidan gidan zagaye yake da doguwar katanga wacce akanta da wasu irin itatuwa masu karfin gaske a daure kuma itatuwan suke da wata irin waya mai tsini tsini ina tsammanin tsini tsinin shi yake hana damun daji haurowa daga bangaren arewa na gidan wani katon dakine mai wangamemiyar kofa a cikinsa motoci ne LANDROVER guda biyu da kuma PATHFINDER guda daya hakan shi ya tabbatar min da cewa dakin garejine nakumayi mamakin ganin motocin nan har guda uku kuma sababbi banda wacce ma suka tafi da ita. . Ina zamu fara shiga? Dansandan ya tambayeni mu balla jar kofar ina tunanin..... . Ina zamu fara shiga? Dansandan ya tambayeni. Mu fara balla jar kofar ina tunanin me yiyuwa anan ne suke aje makamansu dansandan ya sungumi wani mulmulallen karfe dake can kusa da katangar itatuwan nan yana zuwa sai ya fara dukan kofar dakin ba'a dade ba ta balle. Ku shiga ku duba badura tace damu Ni zan jiraku awaje inason leka waje ta kofar gidan tace damu kiyi ahankali na gargadeta babu komai darling tace dani sannan ne muka shiga dakin mai tsananin duhun gaske ne saida muka fara wangame kofar gaba daya sannan muka fara ganin kayan cikin dakin banyi taku biyar ba cikin dakin idona ya hango min wata katuwar akwatin katako ajikin bangon dakin da dukkan alamu komai agidan na katako ne nace cikin zuciyata na leka cikin akwatin shima sannan ne naji tsigar jikina ta tashi wani sassanyar gumi ya fara barkowa daga fuskata acikin akwatin reras suna kyalli kamar zinare kowannensu bakinsa da

Chapter 8 of 9