Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
inuwarka kuma tana fadawa wata na'ura wacce ita da inuwa take aiki zata dau kara don haka nake shawartarka amatsayina na mai kaunar karka sake ka kusanci gilas din da sarkar take har saika kashe duk fitilun dakin dakin kuma zaka same shi a karshen kofar gidan ta goma sha biyu daga hannunka na hagun idan kuma zaka shiga gidan karka sake ka shiga ta kofa koda yake basai na fada maba nasan kanada kwakwalwar da zata iya fitar dakai Allah ya taimake ka Masoyina. Daga Masoyiyarka BADURA Mai neman Gafara agareka. . Acan wani bangare na cikin gidan kararrawar agogo ta fara kuka wannan shine yake nuna alamar karfe goma sha biyu tayi na linke takardar na mayar aljihuna na nufi gado na kwanta amma na kasa barci na sake zaro takardar naci gaba da karantawa kafin gari na ya waye na karanta takardar yakai sau SITTIN 60 . TARA 9 Na duba agogona sainaga karfe goma sha biyu saura minti daya nan da nan na tashi tsaye na sakala jakar da yayana ya ce karna rabu da ita sannan na fito daga dakin na rufe gidan na jefa dan makullin a aljihuna sannan na kama hanya ina rarrabewa acikin duhu kamar barawo Tafiya ta tafi kenan ko na dawo ko kuwa sojoji su harbeni babu mamaki kuma na zama abincin karnuka abin ya zame min gaba siyaki baya damisa idan na dawo banyi nasara ba hajiya binta tayi alkawarin aikawa dani barzahu idan ma nayi nasara abiyu nake kona bar kasar kokuma yansanda su kamani karshe kuma a dora min laifin kisan zainab a rataye ni idan kuma duk wannan ma bata faru ba idan nayi kuskure wajen shiga gidan Kanal Muktar to nan ma dai na lalace wannan shine zabin Shaidan ko ina Halaka bayan tafiyar minti goma sha biyar ina bin bango kamar kadangare na karaso Sultan road kirjina yana dakan uku uku titin sultan a haskake take kamar rana akwai kwayeyen wutar lantarki sama da tamanin anan tun daga nesa na toge ina tunanin ta inda zan lallaba na karasa gidan kanal batareda ana ganina ba amma hakan yaci turo saboda babu damar nayi taku biyar cikin titin sultan sai sojojin sun hangoni na duba bangaren kudu na titin ga mamakina sai na hango wani kangon gida wanda a tsammanina babu kowa acikinsa kuma tsakaninsa da gidan Kanal muktar gida dayane wanda shi naga alamar akwai mutane na sake duban gidan tsakanin kangon nan da gidan kanal sai naga biyu daga cikin tagogin dakin dake fuskantar iya gajeriyar katana agidan abude suke daga inda nake tsaye ina sauraron lallausan sautin turawan dake tashi agidan hakanshi ya sani tunanin in har zan iya shiga gidan ta baya to da wahala masu gadin suji shigata saboda kidan dake tashi bai iya barinsu suji komai bayan haka ma kuma ai daye yayi babu mamaki ma mutum dayane kawai ya rage baiyi bacci ba agidan kuma koma wanene ina tsammanin saurayine dan haka batareda dana barzuciyata ta sake min tunani ba sai na nufi katangar kangon nan na dare kamar barawo kafin na dira ciki sai da na hanga kofar gidan kanal muktar wacce ke cike da yan mazan jiya. . Abin mamaki kofar hidan kanal muktar kamar rana sojoji sun rarrabu har kashi uku kashin farko mutum ne suna tsaye suna muzurai kowannensu rikeda zungureriyar bindiga a hannu suna jiran koda kudane su harbe kashi na biyu kuma mutum ukune suna hira biyu daga cikinsu suna rike da karan taba abakinsu dayan kuma yana wasa da hancin bindigarsa kashi na uku kuma mutum hudune suna wasa da karta daga can gefen su kuma wani katon sojane mai nadadden gashin baki yana zukar sigari katon takalminsa na kafar dama yana barazanar fashewa ga dukkan alamu dashi sojan yaje yakin duniya na daya sojan ya kai kimanin shekaru saba'in ina kuma tsammanin shine mai fada aji agurin na tabbatar da hakan adaidai lokacin da wani dogon soja ya fado wajen kamar daga sama sojan na sanye da hular malafa mai kamar gare gare sojan ya kame agaban katon sojan nan Morning Sir (barka da asuba) yace dashi cikin harshen turanci katon sojan ya daga kansa sannan yaci gaba da zukar zigarinsa shi kuma daya sojan sai ya zauna wajen masu wasa da katin adaidai lokacin na dirga cikin kangon gidan nan. . Akan wani abu lallausa na dira takalmina ya bada wani kara cus na tsayye gefe guda cikin razana sannan naji wani irin wari ya daki hancina nayi sauri na zaro yar karamar fitila cucila na haska akan abinda na taka cikin kaduwa saiga mushen wani katon kare mai dauke da farin kyalle awuyansa abinda zuciyata ta raya min shine wannan daga cikin karnukan Kanal muktar ne ya mutu aka jefo shi nan na godewa Allah da yasa ba akan mai rai na dira ba nayi wa karen kallo daya sannan nayi gaba da sauri ina haska cucilar kangon an fara ginashi amma ginin baiyi nisa ba hakan ne ma yasa ciyawa ta fara yiwa farfajiyar tsohon kangon kawanya gidan yayi shiru kamar makabarta bakajin komai sai sautin bugun zuciyata naci gaba da tafiya ina sanda na. Gidan yayi shiru kamar makabarta bakajin komai sai sautin bugun zuciyata naci gaba da tafiya ina sanda na nufi katangar gidan nan da yake makwabtaka da kangon ina tafiya ahankali tare kuma da zagaye duk inda wata duhuwar ciyawa take aduk lokacin dana dan taka sahuna da karfi akan ciyawar sai baraye da jabaye su fita da gudu su nufi ramukansu wasun su kuma cikin karkashin wani tarin katako suke shigewa katakon tari gudane kuma a zaube yake agindin katangar gidan wacce ita nake kokarin kaiwa domin na samu damar shiga daya gidan na kusa dashi. . Koda na matsa kusa da katakon da niyyar na takashi na kama katangar sai naji motsin wani abu a saman katangar tsohon ginin nan motsin yaso ya razana ni amma dana tuna da cewa gidan fa a cike yake da beraye saina dake da farko har naja da baya na makale ajikin katangar amma da tunanin beraye ya fado min sai zuciyata tace dani babu komai kaidai kayi hankali kar shegen tsoronka yasa har ka dirga daya gidan da karfi su jika don haka sai kawai na nufi katakon da sauri takun farko nayi shine da kafata ta dama kafin kuma na dago kafata ta hagun sai naji wani abu ya fado akan kafata ta damar abin lallausane kuma ina tsammanin yana da tsayin gaske na gane hakan ne ta hanyar nannade kafata da abin yafarayi cikin dan lokaci kankani sai naji kaina yayi min nauyi dim tsoro da fargaba suka hanani motsi abu na farko daya darsu cikin zuciyata shine Maciji ne ya nannade ni nayi karfin hali na zaro fitilar cocilata daga aljihuna na haska kan kafata domin naga abinda ke Faruwa Abinda hasken fitilar ya dauko min yasa numfashina daukewa yakumasa gumi ya fara zuba daga fuskata zuwa wuyana kamar ruwa alokaci guda kuma ya sani tunanin mutuwa Innalillahi Wa'inna Ilaihi Rajiun Nace cikin zuciyata wani dogon macijine wanda nake tsammanin yayini a tsaye idan har baifini tsawo ba to ni kuwa bazan fishi ba bakine kakkaura wani abu mai kama da dan kunne dake makale a kunnensa na hagu shi ya kara fito da siffarsa ta masifa da kuma razanarwa na lumshe idanuna ina jira ya sare ni na huta daga inda nake tsaye inajin sautin kidan bandirin dake tashi a daya gidan dake makwabtaka da ni da kuma Maciji. ** Bansan iya tsawon lokacin danayi a sume ba nidai na farka naji wani abu yana gugar kafata na haska cocilaya cikin tsoro da fargaba nida a tunanina rayuwata tazo min karshe amma yanzu sainaji kamar macijin yabar kafata na tabbatar da hakan alokacin da hasken fitilar ya dauko min katon macijin nan a kwance gefe guda hakika idan akwai abinda yafi mutuwa to shi wannan macijin yayi domin kallo daya nayi masa na tabbata bashida rai an kuma farayi masa rami aciki na juya hasken fitilar wajen kafata don ganin abinda ke lasar kafata anan ne to na gane abinda ya cinye macijin nan hasken fitilar ya dauko min idon wata katuwar jaba mai dogon baki kamar asuwaki tana lasar kafata ga tsammaninta nima ko macijine nayi zunbur na mike tsaye sannan cikin zafin nama na nufi katanga da gudu ina nayi tsalle na kama katangar ta hanyar taka tarin katakon nan dake yashe agindin katangar beraye da jabaye da kuma sauran ire iren kwarin da suka saba zama cikin tsohon ginin wasun su kuma suka nufi cikin ciyayin da sukayiwa gidan kawanya koda na lura sainaga jaba tafi yawa fiyeda bera agidan. * Nayi kimanin mintuna biya ina zagaya cikin gidan kamar barawo ina tafiya da sanda kamar gajimare kamar yadda nayi tsammanin sautin kidan dake tashi shi yabani damar tsirga gidan batareda wani ya jini ba ginin gidan ginin gidajen gwamnatine kamar dai yadda sauran gidajen suke awannan titin angina shine a tsakiyar farfajiyar gidan wannan shi ya bani damar zagayawa ko ina cikin gidan. Daya daga cikin abinda na lura shine katangar gidan data raba gidan kanal mukhtar da gidan tanada tsayin gaske akan katangar kuma kusoshi ne da miyagun kwalabe masu barazana ga hannun duk wanda yayi kokarin kamawa abu na biyu kuma dana lura na kuma gargadi kaina shine gidan danake ciki akwai maigadi na gane hakan ne saboda ganin wata yar rumfa akofar gidan acikin rumfar na lura da wani kasko na kasa cike da garwashin wuta jajawur wannan alama ce dake nuna cewa maigadin tsohone don haka cikin gadara sainaci gaba da zagayawa batareda fargabar komai ba. Haryanzu sautin na tashi acikin dakin saidai kuma wannan lokacin an canza kaset din daga bandiri zuwa na turawa zanso ace nasa kowanene acikin dakin tuni zuciyata ta fara zargin wanda ke dakin shin me ya hanashi barci? Wannan tambayar ita tasani na nufi tagar dake bangaren gaba da gidan wacce kuma itace take fuskantar katangar gidan kana muktar nayi sa'a na sami tagar a bude take banjira wani abu ba saina fara bude ta ahankali har dai na sami yar kofar da zan leka to a sannan ne na sake ganinta tana zaune akan kujera tayi tagumi a kusa da ita kuma dan tsohon nan ne mai fuska kamar matsatstsen lemon tsami yana gyangyadi bangama mamakin abinda nagani ba sai naji wani na taba bayana na juya cikin razana sannan mukayi ido hudu da Salman yana murmushi daman nasan tanan zaka biyo yace dani .Daman nasan tanan zaka biyo yace dani . Kada kayi mamaki da ganinmu anan Fadil. Salman yace dani wannan alamace da take kara tabbatar da maganar uwargidata kuma shugabata hajiya binta inda take cewa duk inda kake ina biye dakai kuma wannan gidan ma daka ganmu aciki ni na bada shawara akama shi haya waya daya kenan yanzu tun lokacin da hajiya binta ta dauko hayata. Nayi shiru cike da mamaki lokaci guda kuma ina kallon tagar dakin dasu hajiya binta suke kar wannan ta dameka salman yace dani sun riga sun san kana cikin gidan domin tunda ka shigo titin nan nake biye dakai duk kuma zagaye zagayen da kakeyi ina kan soron dakin nan ina kallonka don haka nake kara gargadinka da cewa kayi kokari kaci nasa idan kuma harkay kuskura ka fadi to ka lissafa kanka cikin matattu bita can ka tsallaka da fatan zakaci nasara kafin na bude bakina salman ya zagaya ya shige dakin koda na lura da inda salman ya nufa sainaga wani dogon tsani jingine. ** Abu na farko da ya fara yiwa idona maraba shine manya manyan karnukan dake zagaya gidan suna gurnani kamar saci babu kamar yadda badura ta sanar dani cikin wasikarta kofofi goma sha biyu ne reras kowaccensu tana fuskantar yar uwarta idan ka fita daga wannan sai ka shiga waccan daga kan katangar da nake makale rib da ciki ina iya hangen kowace kofa dauke da sojoji masu gadinta guda huku kamar dai yadda badura ta sanar dani ina iya kuma hangen karnuka uku uku akowace kofa tsoro ya dada kamani nayi matukar tsorata da karnukan nan hakan nema yasa na fara tunanin abinda yafi hadari cikin abu uku na farko dai soja na biyu bindiga na uku kuma karnukan duk da yake nasan bindiga farat daya zata hallaka mutum amma hakan baisa zuciyata ta amince da cewa bindiga tafi kare hadari ba nasan dai bindiga bata harba kanta san an harbata haka shima soja sai yaga abin harbawa zai harba din to amma kare fa? Na sunkuyo da kaina kasa na sake nazarin gidan nayi sa'a saboda daidai inda nake saitin kofa ta karshe ne daga nan babu wata kofa saidai kawai mutum ya tsinci kansa tsakar gidan wacce a haskake take tsakar gidan nayi karo da kare saidai kuma in har abinda badura ta fada gaskiyane to da wahala naci karo da kare ko kuma maigadi tunanin haka shi ya baiwa zuciyata damar raya min cewa nayi kunar bakin wake na fada tsakar gidan amma duk da haka saida na dan saurara akalla mintuna biyar ina sauraro tare kuma da kallon tsakar gidan duk tsawon lokacin nan banji komai ba bankuma ga wani abu da zai sani shakkar shiga gidan ba. A cikin dan lokacin danake jiran ko zanji motsin wani abu daban ne sai tunanin Amina ya fado min wacce rabona da ita tun safe data kawo min abinci takuma ce zata dawo da daddare amma bata dawo ba wanda a karshe na godewa Allah dayasa bata dawo ba saboda zuwan nata yana iya kawo min bata lokaci wajen fitowa neman sarkar sanin cewa yanzu fa tsakanina da Amina baifi taku kadan ba shi ya jefo da tunanin ta zuciyata daman ance rashin sani yafi dare duhu don na tabbata da Amina tasan irin hadarin da nake ciki yanzu to da takawo min sarkar har gida to amma bata sani ba nima kuma banason ta sani din domin rashin sanin nata shi yafi alheri agareni. Wani zakara yayi kuka na duba agogona karfe daya da minti daya alamune da suke nuna cewa gari ya kama hanyar wayewa nan da nan nayi tsalla na dira tsakar gidan nayi sa'a ba'a kan dandamali na fado ba saboda gindin katangar a zagaye yake da koriyar ciyawa tattausa ina dirga sai mukayi arba da juna wani daki mai kyakkyawar kofa ta gilas saidai kuma gilas din kamar madubi yake idan na lekada niyya kaga abinda ke cikin dakin saidai kaga fuskarka. Na matsa ahankali ina sanda zuciyata kuma tana bugawa tsakanin hakarkarina kamar dai yadda badura ta fada dakin daga bangaren hagu yake tsakanin dakin da kofar gidanta goma sha biyun zaikai kimanin sawu na dogon mutum ashirin daga nake tsaye ina iya jin gurnanin mugayen karnukan dake gadin kofar idan kuma har ba hancina bane ke fada min karya to ina iya shakar warin tabar da masu gadin ke sha. Good Morning Sir wani soja yace da dan uwansa acan daga bangaren na gidan abinda yabani mamaki don na lura da cewa shi soja bashida dare bashida rana ko yaushe safiya ce na matsa kusa da kofar dakin gabana ya fadi wannan ya samo asaline saboda sanin cewa tsakanina da sarkar data jefa ni cikin bala'i baifi taku uku ba saidai kuma ba anan gizon ke sakar ba kofar ta gilas ce shafaffiya babu alamar gurin budewa ajikinta. Ina na taba ina tsoron kada na jangwalo wani sabon bala'in to idan ma na taba din tayaya zan budeta? Nayi kimanin mintuna biyu ina zagaya dakin daga karshe ne na gano wata taga abayan dakin daga bangaren yamma tagar yar karama ce itama kuma a rufe take da gilasai saidai ita tana da wajen budewa ina jan wani karfe mai ruwan azurfa sai tagar ta bada wata yar kara ta bude sannan na leka cikin dakin kamar yadda badura ta sanar dani a zaune a tsakiyar gilas din wanka ke kan wani katon tebur mai ruwan gwal sarka ce tana kyalkyali kamar walkiya hakan yanada nasaba ne da irin matsanancin.. . Sarka ce tana kyalkyali kamar walkiya hakan yanada nasaba da irin matsanancin hasken dake zagaye da sarkar wanda kuma badura ta gargadeni da cewa kada na sake na matsa kusa da gilas din saina kashe wutar dakin gaba domin kamar yadda tace wai akwai na'urar kararrawa mai aiki da inuwa kuma itace ke gargadin sojoji dakuma karnukan gidan cewa gida babu lafiya . Na dada bude tagar sannan na zira kafata cikin dakin zan dago kafata ta hagun kenan sai naji wani abu ya mari fuskata ya kumayi sama da wani irin kuka da zaka tsaga jikina alokacin ba zaka sami jini ba don tsoro nayi kikam ko cikakken numfashi bana iya yi kafata daya aciki daya awaje sai bayan dana dubi tsakar gidan ne sannan abin ya ban haushi ya kuma bani dariya a zaune akan katangar gidan wani kyakkyawan aku ne shida matarsa yana kallona yana wani irin kuka ban ko kara komawa takansa ba na fada cikin dakin ta tagar dumi ya bugi fuskata saboda matsanancin zafin dake gauraye a dakin sakamakon kwayeyen wutar lantarkin da suka zagaye dakin a kalla goma sha uku na dubi gilas din da sarkar ke ciki sannan na dubi hasken dake zagaye da dakin sannan ne nafara gaskata maganar badura zaiyi wuya ko kuma ince bazai yu ba ka gane cewa gilas din da sarkar ke ciki a jone yake da na'ura mai kararrawa saidai ko an fada ma ko banza dai badura ta taimaken tanan wajen duk da yake kuwa har yanzu ban amince da ita ba ni aganina duk zakin bakin datayi na yaudarane. . Shawara ta kasa yankuwa agareni na duba dakin sama da kasa banga wajen kashe kwan ba sai bayan danayi minti gudane ina dube dube sannan naga abin kunnawar (swich on/swich off) su na gani a rubuce ajiki cikin harshen turanci wajen kunnawa da kashewa kenan sai dai kuma abin mamaki ko kuma ince abin bakin ciki wai aka rasa inda za'a ajje abin kunnawar sai akan teburin nan inda gilas din da sarkar ke ciki da farko har na matsa da sauri domin na kashe cikin dana fara nufar wajen sai kwakwalwata ta fara yi min ihun gargadi kai wawa baka ganin dabara ce aka hada don kama marasa gaskiya irin ku baka ganin kana matsawa kan teburin inuwarka zata fada akai bayan kuma an fada ma na'urar ce keyiwa sojojin gidan nuni tana aiki kuma ne da inuwar wanda yazo kusa da ita nayi turus na tsaya koda na dubi inuwata sai naga tsakaninta da gilas din baifi takun hannu ba nayi sauri naja da baya to a daidai lokacin ne kuma kaddara tayi halinta. . Ba zato ba tsammani sai ga dan tsuntsun akun nan ya fado dakin kamar daga sama ashe nine nayi kuskure ban rufe taga dana shigo ba cikin kankanin lokaci kwakwalwata ta fara min gargadi da irin aika aikar dake shirin faruwa nan da nan na kaiwa akun nan cafka yin haka shi ya tsorata akun shi kuma ya nufi kan gilas din yana fuffuka da fika fikansa atake anan Al'amaru suka watse inuwar akun tayiwa gilas din rumfa alokaci guda kuma sai duk naji gidan ya dauki kukan jiniya mai firgitarwa TA FARU TA KARE nace cikin zuciyata ina amfanin badi ba rai tunda abinda nake gudu ya faru me kuma zanji tsoro atake anan na nufi wajen gilas din da gudu haryanzu jiniyar bata daina kuka ba saboda karin inuwa da aka samu akan gilas din na ina zuwa saina bude gilas din na dauke sarkar na jefa a aljihu sannan na kashe wutar dakin gaba daya na nufo kofar dakin da gudu na manta da cewa ashe a rufe take ina zuwa sainaci karo da kofar gilas din ya tarwaste ni kuma na fado rub da ciki adaidai lokacin naji gudun sojoji sun nufo kofar gidan ta goma sha biyu gidan ya rufe da hayaniyar sojoji daga daukar sarkar zuwa ga fitowata naji harbin gargadi da bindiga yakai dari. . Nayi sauri na mike sannan nayi cikin gidan da gudu da nufin na sami gurin buya amma abin yaci tura filin gidan har yanzu a haske yake da lantarki kuma babu wajen buya dana lura da bangaren hagu sai naga wata yar siririyar hanya wacce bangon gidan da wani ginin daki suka kirkireta da gudu na shige kwanar da niyyar na sami wajen buya ina zuwa sainaga ashe hanyar wani daki take fuskanta abubuwa suka taru suka rikice min can kuma sojoji sai harbe harben iska sukeyi adaidai lokacin ne kuma naji ana bude kofa ta karshe wacce take fuskantar gidan ina tsammanin da katuwar sarka suka daureta don haka suka sami tangarda wajen budeta na duba sama da kasa ko zanga wajen buya amma babu nasan kuma ko wanne lokaci daga yanzu sojoji ne zasu shigo farfajiyar gidan na kuma dubi katangar sai naga duk tsallen danayi bazan kamo ta ba idan kuma nayi nasarar kamota ma to na tabbata ba zan dira da yatsuna ba domin kaifafan kwalabe ne da kusoshi akan katangar suna kuma maraba da hannun duk wanda yayi kokarin tsallaka katangar wau wauhn amsa kuwwar haushin karnukan ta dako dodon kunnena haushin karnukan kamar duka da guduma ne a kirjina idan akwai abinda nafi tsoro bai wuce karnukan nan ba da ace karnukan nan sun kamani gara ace da bindiga aka harbeni. Kofar da sojojin ke kokarin budewa ta fara yi yowa gaba gaba tsoro ya sake kamani saboda ganin irin yadda karnukan ke dukan kofar da jikinsu tun kafin ma sojojin su bude su har sun kosa su shigo. . Fadil... Wata siririyar murya tayi kirana kofar dakin dake fuskantar siririyar hanyar dana biyo ta bude tana sanye da doguwar riga ta barci kanta babu dankwali AMINA CE shigo nan tace dani adaidai lokacin ne kuma ta kama hannuna muka shige dakin sannan ta maida kofar dakin ta rufe duk da yake ta rufe dakin hakan bai hanani jin gurnanin karnuka a kofar dakin ba. . 11 Haba Fadil Amina tace dani cikin sheshshekar kuka me yasa zakayi min haka? Yanzu tsakanina dakai har akwai wani abu da zai sameka ka boye min in daka fada min kace sarkar kake so me zai hana na baka ita cikin ruwan sanyi katuna fa irin son da nakeyi ma kafi karfin sarkar awajena amma kuma...... Ta kasa fadar kalmar da take son furtawa saidai kuma na gane abinda take kokarin fadi tana son tasan dalilin da yasa na hauro gidan ne idan kuwa har bani da hujjar hauro gidan to suna daya ya dace dani BARAWO. Ba laifina bane Amina nace da ita wallahi tilasta min akayi aka kuma fi karfina haryanzu amina bata daina kukan ba amma jin cewa tilasta min akayi sai naga nan da nan ta dago kai ta dubeni duba na nutsuwa sannan cikin tattausar murya ta tambeyni Wanene ya saka ka shigo gidan nan daukar sarkar? Wadanda suka doramin laifin kisan kan da akayi a kaduna na amsa mata kai tsaye kana nufin kace duk akan sarkar ne aka dora ma sharrin? Akanta ne aka kashe zainab na karashe mata. Amina tayi shiru na dan lokaci sannan ta dago kai tace su wanene Fadil? Ina bukatar jinsu yanzun nan bana bukatar wani noke noke kuma. Sunada yawa nace da ita amma shugabarsu itace kishiyar mahaifiyarki hajiya binta yayarki kuma badura itace ke taimaka mata ita da wani dan ta'adda salman sannan..... Nayi shiru cikin kaduwa kallon da amina keyimin shi ya sani rawar jiki kallone da zan iya fassarashi da kallon tsana tunda nake da Amina ban taba ganin tayi min irin kallon ba. Ci gaba mana tace dani cikin kakkausar murya akwai daya yar uwar taki Amina sai kuma wani dan tsoho da bansan ko wanene shi ba nace da ita, da wa kuma? Ta sake tambayata. Sukenan na tabbatar mata. Karya kake tace dani cikin kukan takaici sai wa kuma ka rage guda daya idan bazaka fada ba bari na fada ma dayan Fadamin to nace da ita bakina na rawa KAI NE tace dani wallahi daman tun farko saida nayi zaton haka nasan Hajiya binta daman ba kaunar mu take ba bayaga haka ma..... Ta fashe da kuka ka cuceni Fadil wallahi ka cuceni an hada baki dakai domin acuci mahaifiyata sannan tayi min wani irin kallo sannan tace. Fadil ta kira sunana muryarta a dusashe Na'am na amsa muryata na rawa Meyasa ka yaudareni ta tambaya ba yaudararki nayi ba na amsa mata Haba fadil tace dani na fa karanta takardar da badura ta aiko ma ta soyayya wacce acikina ne har take fada ma sirrin gidan nan kaci amanata ka kuma cuceni tunda kaso yar uwata sanan kuma ka amsa min wai kana sona. Ni bance ina sonta ba nace da ita amina kin kasa fahimtata wallahi ba laifina bane kuma takardar da kika karanta baki karantata har karshe bane da kin fahimci gaskiya kaima kasan bazan iya karanceta ba saboda irin kalaman da badura keyin amfani dasu wai tana kaunarka wallahi zuciyata bazata iya daurewa kuma...... Muryarta ta sake dusashewa ta fara kuka sannan ta dago kai muka hada ido da ita. Babu abinda zakacemin na yarda dakai Fadil tun lokacin dana sami takardar da badura ta rubuto ma nake tunanin irin bakin cikin da zan fada in har abin yazama gaskiya sai gashi kuma ya zama din wai fadil da kanka da kuma hankalinka aka hada baki dakai don acuci mahaifiyata ko? Wato wannan shine sakayyar irin soyayyar dana nuna mak? Tun da nake dakai Fadil bantaba nuna ma rashin kauna ba ban kuma taba cutar ka ba duk da yake ma nasan daman can kai ba kaunata kake ba.... Kada ki fadi haka amina nace da ita ke kanki kinsan da bana kau..... Karka bata bakinka tace dani alokaci guda kuma ta miko min siraran kyawawan yan yatsunta na hannu. Bani sarkar da ka dauka tace dani nima ina sonta kamar yadda hajiya binta take sonta da farko nayi niyyar kin bata amma nasan hakan bai yiyuwa domin alokacin daidai take data kwala ihu sojoji su cika dakin. . Mukayi shiru na dan lokaci muna kallon juna ko kiftawa bamayi na dubi Amina babu alamun kauna a fuskarta sai alamun tsana dakuma zargi da suka fito karara a kyakkyawar fuskarta na danyi jim sannan na tura hannun nawa a aljihu na zaro sarkar na mika mata amina ta karbi sarkar ta buda rigar mamanta tajefa ta ciki sannan tace dani. Bace min da gani saboda me Amina na tambayeta saboda bana kaunar ganin mayaudari kuma makiyin mahaifiyata ta amsa min me yasa ki tunanin ni mayaudarine kuma makiyin mahaifiyarki na sake tambayarta. Saboda an hada baki dakai domin ganin an cuci mahaifiyata kuma ka yaudareni ta hanyar hada soyayyata data yar uwata badura naji na yarda tunda idan ma nayi miki bayani bazaki gani ba nace da ita. Saidai kuma kina ganin duk wannan yakai ace kin koreni zuwa ga halakata? Na tambayeta maganar tayi tasiri akanta saboda ganin irin yadda tayi kasake tana kallona kuma tana wasi

Chapter 6 of 9