Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
Abu daya ya rage masa jin dadi shine bashida 'da ko daya a duniyar nan sai Agolansa daya tal wacce yake mutuwar so kamar ransa wannan Agola tasa ya dauke take ne kamar yar da ya haifa AMINA itace Agolan Kanal Mukhtar. . Dakin yayi shiru bakajin komai sai motsin gayayyaki da furannin fulawa dake ta gugar tagogin gidan hakika yanzu ne na fahimci sabon salon danake shirin shiga duk da cewa kuwa bansan abinda su badura ke nufi ba da ambatar sunan Mukhtar. Na dago kaina muka hada ido dasu sannan nace da ita Menene to idan na san shi? Batareda ta dubeni ba sai taci gaba da cewa . Shekaru biyar da suka wuce mahaifinmu Alhaji Ahmad ya rasu a sakamakon hadarin jirgin saman daya rutsa dasu in zaka iya tunawa yana daya daga cikin manyan masu kudin dake kano yana kuma daga cikin manya manyan marubuta littafi na kungiyar RAINA KAMA munyi bakin ciki da mutuwarsa duk da yake yana nuna mana bambanci tsakaninmu da yan uwarmu ya mutu yabar mata biyu daga cikinsu akwai mahaifiyarmu Hajiya binta dake zaune a unguwar tarauni cikin birnin kano sai kuma kishiyar babarmu Hajiya Asma'u sannan ta dubeni tace dani Hajiya Asma'u itace mowar babanmu yafi sonta akan kowa daga ita sai yarta sai abinda suka fada shi akeyi agidan idan baka manta ba babanmu ya rubuta wasu littattafai guda biyu tun kafin ya rasu littattafan da suka daga karshen bahaushe aduniya sun sami karbu acikin najeriya gaba daya harma wadanda basa jin yaren hausa sunyi kokarin koyonta domin su sami damar karanta littafin Akwai kasashen waje da dama da sukayi murna da fitowar littafin musamman ma dayake yana taimakonsu wajen koyon harshen hausa an gabatar da littafin shekaru biyar da suka wuce tun kafin mutuwar mahaifinmu ya samu kyaututtuka da dama daga manyan mutane dake cikin birnin kano daya daga cikin kyaututtukan itace wata SARKAR ZINARIYA wacce wani kwara ya baiwa babanmu shi wannan kwara yana matukar son yaren hausa kuma ya koyi yaren hausa ne saboda yin hulda da hausawa wajen cinikayya mutumin daya koya masa hausa shine BABANMU Don haka lokacin da aka gabatar da littafin sai kwaran ya tafi kasar waje a can yasa aka kero masa wannan sarka ta zinare ajikinta an rubuta kalmar R.K da ruwan daiman wato ma'anar kalmar R.K shine RAINA KAMA Dalili kuwa shine littafin yafito ne ta karkashin Kungiyar Raina kama kano. . Atakaice dai mahaifinmu ya raba gadonsa tun kafin rasuwarsa da wata daya mun sami dukiya mai tarin yawa saidai kuma abinda ya bakanta mana rai shine baiyi rabon gado da sarkan nan ba da ya tashi sai yayi son kan nasa ya baiwa yar lelen yarsa sarkar wato yar gidan hajiya Asma'u kenan kada kayi tsammanin sarkat tanada wani kudi ne mai yawa sam sam kudinta bai wuce naira milliyan biyu ba da dubu dari biyar. Fadil' badura takira sunana cikin wata murya wacce taban tsoro. Inason sarkar nan ta dawo wajena Ta yaya zata dawo wajenki? Na tambayeta ta dubeni sannan tace dani haryanzu baka gane abinda nufi ba in baka gane ba to bari na karasa ma labarin bayan mutuwar babanmu hajiya asma'u tayi aure bayan shekara daya mutumin data aura kuma shine Kanal Mukhtar yanada gida sultan road cikin jihar kano in baka sani ba kuma na bari nafada ma duk cikin jihar kano in ka dauke gidan Gwamna babu inda yakai gidansa tsaro. Anan ne kuma nake so kaje ka samo min sarkar shiga gidan wata sabuwar duniyace amma shiga gidan yafi shiga hannun yan sanda awajenka ko har yanzu baka gane abinda nake nufi ba? Sannan ta kyalkyale da dariyar mugunta kada kayi tsammanin shiga gidan kanal mukhtar kamar shiga gidanku ne amma duk da haka gara masu gadin gidan su harbeka da ace yan sanda sun harbeka acikin Jama'a me nayi yan sanda zasu harbeni na tambayeta 'baka ma sani ba kanajin zaka KASHE ZAINAB A BANZA NE ? . Kayi a hankali Fadil badura tace domin dole ne kayi abinda nasaka domin itace hanya mafi sauki agareka itace hanyarka daya Tal da zaka iya tsira idan ka kawo sarkar kudin da zamu baka ya isheka kabar kasar nan kaga ka tsira kenan. . Hakika yanzu daidai nake dana shaqe wuyan badura na karyashi saboda rashin kauna sannan na dubeta nace da ita 'idan nace bazanyi ba fa me zakiyi ? Kada ka batawa kanka lokaci Fadil tace dani sannan ta mike tsaye ta bude wata loka ta dauko wasu fararen takardu masu dauke da rubutu ta jefo minsu hade da wata jarida sannan tace dani ni zan tafi sai kayi kokari ka san yadda zakayi ka isa birnin kano sannan tayi min murmushi tace dani. Bakada mafita dole ne kayi abinda nasaka babu damar kaucewa kasan daman hausawa sunce KIBIYAR AJALI FALKE BAYA KAUCE MATA. Sannan ta tura kofa ta juyo ta kalli su Salman da daya yarinyar da nake tsammanin itace Amira Kuzo mu tafi tace dasu suka bita kofar dakin adaidai lokacinne amira ta juyo tace dani mu hadu a daula otel kano idan kayi nasara idan kuma bakayi ba sai nace mu a hadu a filin sukuwa wajen harbe rufe kofar dakince ta tabbatar min cewa sun tafi na dubi takardun nan da bansan abinda suke nufi ba ya zama dole na duba su don haka sai na gyara zama na buda jaridar an rubuta cikin manyan haruffa kamar haka WANI DAN BINDIGA DADI YA HARBE MA'AIKACIYAR DABA OTEL KADUNA . Guntu labarin kuma basai na fada maka ba yansanda sunata nemansa ruwa a jallo an kuma rufe kowace hanya da zata fita daga jihar kaduna.... Babu motar da zata fita batareda yan sanda sun yi mata bincike ba. Abin dayafi bani tsoro shine dan tsohon nan motsatstse ya bada shaidar cewa ya ganni na fito daga dakin da zainab ta mutu akaryarsa cewa yayi wai har da bindiga a hannuna wannan shaida ita zata kara tabbatar da badura daga zargin ko bakinmu daya da ita . HUDU 4 Lallai Kibiyar Ajali hakika yanzu nasan kibiyar da badura ta harben da ita ta sameni a makogoro samun da ta yi min ina tsammanin shine zai zamo ajalina duk da yake har yanzu inada damar da zan zare kibiyar daga jikina batareda tayi sanadiyyar ajalina ba saidai kuma damar kadan ce. Mintuna biyar suka shude kamar wasa haryanzu kwakwalwata bata fara aiki ba aduk lokacin dana fara tunani sai tunanin abinda badura tace dani ya ruguza tunanina kamar yadda ruwa ke ruguza tubalin yashi 'inason sarkar nan ta dawo wajena idan kayi nasara ladan da zamu bakaya isheka kabar kasar nan kaga ka tsira kenan..... Wannan sune maganganun da suke rikita min kwakwalwa. Hakika badura taso kanta tayi amfani da rashin imaninta wajen ruguza rayuwata acikin zabin data bani babu wani mai sauki kamar yadda tace wai idan nayi nasara zan bar kasar wannan kuma wani abu ne da ba zai yu ba idan na bar kasar wajen wa za ni shin kuma ni da sake haduwa da yan uwana sai a lahira kenan? Duk wannan mai sauki ne a kan shiga satar sarkar gidan kanal mukhtar abinda na tabbatar ma kaina shine kwanana yazo KARSHE. Badura ta bani zabin shaidan dolene na kira shi da zabin shaidan domin kuwa babu mai sauki daga cikin biyun idan nayi nasara nabar dangina yan uwa da abokaina kenan har abada? Idan kuma banyi nasara ba to wannan ba sai na fada ma ba na mutu kenan dolene na samu zabin kaina na uku idan har kuwa inason tsira ya kuma zama dole na rama abinda badura tayi min sai kuma na samo wanda ya kashe zainab in har ina raye wannan shine alkawarin dana daukarwa kaina lokacin da nake zaune acikin gidan nan wanda bansan ko awacce unguwa yake ba. . Abinda yafi damuna yanzu shine hanyar da zanbi naje kano na farko dai ko wace hanya acike take da masu jajayen idanu suna nemana gashi kuma banida mota bakuma kudi to idan ina da mota ma ta ina zanbi? Kuma wajenwa zani idan na isa kanon domin na tabbata yanzu yayana yasan halin danake ciki ahalin yanzu nayi alkawarin bazan taba tunkarar gidanmu ba sai na abinda ya turewa buzu nadi. . ******** ***** ******* ********* ******* . Sa'o'i biyu suka wuce batareda nasami wata kwakkwarar shawara ba don haka sainaga zama bazaiyi min ba nan da nan na tashi na nufi kofar dakin danake tsammanin zata fitar dani har farfajiyar gidan na bude kofar ga mamakina sainaga wani makaken lambu mai dauke da kayan marmari iri iri ya zagaye ginin dakin danake ciki Lambun yana zagaye ne da wata makakiyar katanga wacce bana tsammanin zan iya tsallakata saidai idan nayi amfani da tsani ya kamara na dan zagaya naga tsarinsa don haka saina rufe kofar dakin na fito waje kafafuna babu ko takalmi nabi wata yar siririyar hanya wacce nake tsammanin zata kaini tsakiyar lambun. . Koda na juya na kalli dakin dana fito daga ciki sai naga ya zama dan kankani acikin tafkeken lambun sannan naci gaba da tafiya ahankali nabi wata yar siririyar hanya wacce bishiyoyi sukayi mata inuwa tako wanne bangare saida na wuce bishiyoyin nan sannan na hango wata tafkekiyar kofa wacce nake tsammanin zata iya fitar dani daga lambun batareda danayi tunani sau biyu ba sai kawai na na nufi kofar da sauri tun kafin na isa kofar na fara jin karar motoci suna ta wucewa ta kofar lambun katuwar hanyace motoci sunata zirga zirga dada can kuma tsallaken titin manya manyan kantuna ne wasu ana saida kayan masarufi wadansu kuma ana ta ciniki iri iri daban daban wata katuwar mota ta wuce kamar guguwa adaidai lokacinne na hango wani shago wanda ganinsa yasa gumi ka karyo min katon shagone a shafe da fentin an zagaye kofar da wasu bakaken karafuna wani inyamuri kato fari mai kaurin wuta yana zaune a kofar shagon yanata girgiza kai kamar kadangare ga dukkan alamu dai yana sauraron turawane a gefen hadun dinsa kuma wani katon katako ne fari yana dauke da rubutu cikin harshen turanci EMAKA BUSINESS CENTRE daga kasan katafon kuma anyi zanen wani mutum da wayar talfo a hannunsa ko banfada maka ba zaka iya tunanin cewa wannan shine mataki na farko da yakamata na dauka domin fita ta daga kaduna batareda na bata lokaci ba saina juyo aguje na nufo dakin ina zuwa na bude shi na shiga da sauri batareda na rufe kofar ba agogon bangon dakin ya nuna karfe goma sha biyu na rana na bude cikin jakata na dauko wata rigar sanyi mai hade da wuya nasa har na juya zan fita daga dakin sai Har na juya zan fita daga dakin sainaga wani katon bakin tabarau akan tebur nayi tsammanin na salman ne nan da nan na dauka nasa na dubi fuskata a mudubi nayi murmushi abinda nagani a mudubi shiya bani dariya zaka iya kirana da Uche ko kuma chinedu na zama kamar inyamuri duk wannan abin yafarune acikin abin da bai gaza minti biyu ba. . Da gudu da sassarfa na isa kofar lambun ina fata dai bazaka iya mamaki ba da irin shigar danayi wani abune daka sani kusan kowa ahalin yanzu yasan halinda ake ciki a kaduna yakuma san kamannina a hoto to amma yanzu zaiyi wahala ka ganeni in dai har kayi la'akari da hoton dake jikin jarida banyi mamaki ba danaga na tadda kofar lambum a bude kofat tayi kara kirr a daidai lokacin dana maida ita na rufe bayan nayi jira kamar na dakika talatin na samu na tsallaka titin. Tun kafin na karaso shagon sainaga inyamurin ya shiga shagon ni kuma nabishi abaya katon shagone wanda ke dauke da manya manyan kujeru uku bangon dakin a lullube yake da takarda ruwan gwal kana shiga dakin zakuyi ido hudu da kayuwan talfo biyar uku daga cikinsu jajaye ne biyun kuma farare duk wannan na kula dashi ne cikin abinda bai wuce dakika hudu ba. Menene lambarka? Inyamurin ya tambayeni cikin harshen turanci na zaro biro da da wata guntuwar takarda daga aljihuna na rubuta masa lambar talfon din yayana dake kano sannan na mika masa zauna acan ya nuna min daya daga cikin kujerun da take fuskantar fararen kayukan din nan guda biyu banyi cikakken minti daya da zama ba sai ya miko min kan talfon, tun kafin na karasa da kan talfon kunnena sai naji muryar hajara tana cewa wanene? Nine fadil nace da ita hajara matar yayana ce dake kano kuma a wajenta na girma tun lokacin da iyayenmu suka rasu a samakaon hadarin mota sai babban yayanmu ya daukeni yakaini wajenta alokacin shekararsa uku dayin aure tana matukar sona musamman ma dayake taga banida kiwa da rashin jin magana fadin kana ina? Tausayinta ya kamani saboda sheshshekar kuka data farayi kada ki damu nace da ita kedai ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada miki batareda najira tasake tambaya ba sainaci gaba da cewa don Allah hajara kiyi maza ki tafi gidan kanal mukhtar ki sami amina idan kin sameta kice mata ni na aiko ki kice mata ina tudun wada kaduna kuma ina bukatar taimako da gaggawa domin ya zama dole nabar kaduna yau dinnan kuma kice mata wannan itace damata ta karshe ko na fice daga kaduna yau ko kuma yansanda su kamani kinaji na hajara? . Na tambaya naji shiru na dan lokaci sannan sainaji hajara tace dani fadil nace na'am ta sakeyin shiru jikina ya fara rawa hajara nayi kiranta yaya naji kinyi shiru in wani abu ne ya faru ai saiki fada min ba sai kin boye min ba kinsan dai wannan abu kaddarace kuma dole ne ta faru akaina amma abinda nake so ki gane shine bani nayi kisanba sharri akayi min ko kin yarda kasheta ? Wannan magana danayi ita ta dawo da hajara cikin hankalinta haba fadil tace dani daidai rana daya ban taba zaton zaka iya kashe akuya da ranta ba balle mutum abinda abinda yasa kaji nayi shiru shine aminar da kake fada bata nan tun jiya da muka sami labarin abinda ya faru tazo gidan nan da jarida wacce ke dauke da hotonka tana kuka tace dani zata tafi kaduna wajenka ko nasan inda zata sameka? Nace mata wallahi bansan inda zata sameka saboda kaima bakasan kowa ba shine tace ita dai saita tafi nemanka don tace wai akwai gidan yan uwansu a kaduna batace dake ga inda zataba? Na tambayi hajara Nima wallahi bata fadamin ba shikenan to nace da ita saura kuma abu daya don Allah Hajara idan yaya yadawo karki ce masa na bugo waya saboda banason hankalinsa yatashi kema kuma kar hankalinki ya tashi kinsan..... ta katseni da cewa to fadil yaya zakayi ka tsira daga wannan sharrin? Kuma tayaya zaka fice daga kaduna? Babu komai nace da ita ke kedai kitayani da addu'ar nasara saina samo wanda ya kashe zainab nakaiwa yan sanda shi a hannu. Tayaya fadil? hajara ta tambaya haba hajara kin sanni fa ban taba cewa zanyi abu na kasa ba hajara ta fara kuka fadil don Allah karka yadda su kamaka kaga in sun kama ka.....na ajiye wayar talfon din bazan iya jure kukan da hajara takeyi ba domin zai iya karya min zuciya basai an fada ma ba kai kanka kasan bana bukatar karayar zuciya ahalin yanzu. ** Motsin wani abu da bansan ko menene ba shi ya tashe ni daga nannauyan barcin danakeyi na tashi firgigit saura kadan na fado daga kan benin danake kwance magariba tayi duhu ya mamaye ko ina cikin lambun inka dauke wani farin kyandir daya haskake kofar dakin dasu badura suka kawoni. nayi mamakin yandda akayi bacci ya daukeni a lambun tun lokacin dana dawo daga wajen talfon nan saina koma daki na sako karamar riga na dawo cikin lambun na fara tunanin abinda yakamata nayi shawarar da na yanke itace idan dare yayi saina sulale nabar gidan tunda a lokacin duhu bana tsammanin akwai dan sandan da zai iya kamani hanya daya dana ga zata fitar dani itace naje wajen wanzami ya aske min kaina gaba daya nasa kaya masu datti Idan duhu ya karayi sai naje tasha na shiga motar katako irin wadanda suke safara daga kano zuwa kaduna nasan in ba tsautsayi ba da wahala su kamani domin wadannan motocin anfi bincikar kayan da suke dauke dashi sama da mutanen cikinsu yanke shawarar keda wuya sainaga ina bukatar hutu kuma gashi inuwar dake lambun tana da sanyi sai kawai na kwanta. . Motsin danaji yabani tsoro na duba sai naga dakin a bude da kuma tabbata a rufe na barshi lokacin dana fito dadin da dadawa kuma sai naga dakin gauraye da haske hakane ya tabbatar min da cewa akwai wani acikin dakin dan da nan na mike tsaye na nufi dakin da sanda ta hanyar boye jikina abayan bishiyoyin da furannin da sukayi layi a lambun taku ashirin daidai yakaini kofar dakin sannan sai na tsaya cak ina sauraron wani abu dayasa tsigar jikina ta tashi in dai ba kunnena ne ya fada min karya ba toh naji kamar jiniyar yan sanda kafin na karasa tunani tuni duk zagayen unguwar da lambun yake ta gauraye da kukan jiniya ko ina kudu da yamma harda arewa bakajin komai sai kukan jiniyar yan sanda batareda sanin hakikanin abinda zanyi ba saina dare wata bishiya dake kofar dakin na hau can samanta na mike tsaye ina hangen bayan lambun Tafaru ta kare nace cikin zuciyata abinda na hango ya kada min hantar cikina yansanda sun zagaye lambun kamar kasa ahalin yanzu kukan jiniyar tayi sauki bakajin komai sai kwat kwat din gudun yansanda a iya hangena ina iya ganin kudu arewa da yamma amma bana iya ganin gabas saboda manyan benayen da sukayi shinge a bayan lambun ta bangaren gabas da suka zagaye lambun. . Karar Bindiga ya cika min kunne ina tsammanin yan dadi bindiga ne suke gargadina da cewa sunzo harsashin ya daki gilas din tagar dakin dake kasana wani radadin zagi ya mamaye hannuna na dama dake rike da reshen bishiyar dana ke kai na shafa sai naji danshi a hannuna raina ya baci dana tuna da badura duk abinda akayimin ita ta janyo min kada kayi tsammanin zan tsaya su kamani kamar mace ni ma fa ba karamin shaidani bane idan aka takura min duk da yake nasan ko wanene ni dole ne in tsorata ni dai har kaga yawan yansandan da suke jirana awaje. . Tunanin badura ya sake fado min in dai akwai yadda zanyi dolene nayi kokarin tserewa yansandan nan ko ta halin kaka inaso ace koda sun kamani to ya zama na rama abinda badura tayi min na tashi tsaye na hangi cikin lambun sainaga kamar yansandan sun fara shigowa ga wanda baisan me ake kira yaki ba idan yaga yawan yan sandan da suke jirana sai yayi zaton wannan shine farkon yakin duniya na uku batareda na sake tunanina sau biyu ba sai na saki reshen bishiyar nayi kasa na tabbata ko wanene ke cikin dakin badan sanda bane yakuma zama dole naga ko wanene kafin nayi shirin gudu abu daya dayake bani kwarin gwiwa shine yansanda bazasu motso kusa dani cikin gaggawa ba domin suna tsammanin inada bindiga Na daki kofar dakin da kafata ta bude na shiga ina dube dube banga kowa ba kofar wani dake fuskantata a bude take na nufi kofar da dan sanda tun kafin na karasa sainaji kamar mutum ne ke numfashi sama sama a dakin na tura kofar ahankali na shiga. . Tana kwance a gadon da suka daureni tasha dauri da igiya kamar damin gero tana numfashi daidai jajayen kayan data zo dasu dakina a otal din daba sune ke jikinta saidai yanzu duk sun yayyage alamun tasha wuya awajena mukayi ido biyu da badura sai tayi min murmushi. Ina fatan ka gane abinda nake nufi da KIBIYAR AJALI ? Tace dani abinda kawai ya rage yanzu shine suzo su sameni a kwance shi kenan kai kuma kazo hannu . Kina nufin kice bazasu yarda da cewa ni na daureki? Nace da ita. Ba sai an fada musu ba shin menene amfanin jaridar dana baka? A tsammaninsu kayi niyyar kashe ni ne kenan bakada mafita idan suka sameni to na tsira kenan abu daya da bazan sake na musu ba shine inda gidanku yake a kano wannan wani abu ne da zasu nema da kansu na kalleta cikin haushi sannan nace ita kina tsammanin ni mahaukaci ne zan nufi gida ahalin yanzu badura tayi murmushi fadil tace dani karka batawa kanka lokaci kayi kokari ka tserewa abinda ke jiranka waje damarka ta karshe kenan sannan taci gaba da cewa idan kana ganin ba wani abu ne yansanda su san gidanku ba to bari nafada ma ba abin wahala bane na fadawa yan sanda cewa yayanka yasan inda kake kaga zasuyi tsammanin shi ya boyeka ta danyi shiru sannan ta sake murmushin mugunta bazaka so ace an azabtar da yayanka ba saboda kai kada kuma kayi tsammanin idan yan sanda sun saki yayanka zai sami cigaba da aiki agidan redio ba abun kunya ne ace ma'aikacin gidan rediyo ya boye mai kashe jama'a da gangan kawai don saboda dan uwansa ne idan muka bi ta fuskar siyasa wannan zai janyo abin kunya da maganganu ga gidan rediyon. Nayi shiru ina tunani lallai yarinyar nan ta gama sanin sirrina ciki da waje haushi ya kamani nayi taku guda na gaggawa na kifa mata mari don karin haushi maimakon tayi kuka sai ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma sai ta kwalla ihu kamar wacce ake zarewa ido cikin dakika uku na gane abinda ke shirin faruwa na fadi rub da ciki adaidai lokacinLokaci guda kuma saita kwala ihu kamar wacce ake zarewa ido cikin dakika uku na gane abinda ke shirin faruwa na fadi rub da ciki adaidai lokacin ne aka fara ruwan harsashi ta cikin tagogin dakin in danayi sa'a sai harsashi daya daga cikin dubun harsashen da ake zubowa dakin ya daki katuwar fitilar dake like a bangon dakin fashewarta keda wuya sai dakin ya zama kamar kabari saboda duhu na manta da zancen badura yanzu ta kaina nake duhun dakin shi ya bani damar yin wani abu naja ciki ina laluben jakata zakaga wawanci na idan kaji cewa ina neman jakata cikin wannan lokaci maganar yayana ita nabi lokacin da zan taho kaduna sai ya bani wata jaka baka yace dani duk inda zaka katafi da jakar ka kada ka sake kuma ka bata bansan abinda yake nufi ba amma nasan akwai ma'anar yin hakan. Bayan dan lokaci na sami jakar na rataya ta abayana nayi amfani da wasu igiyoyin roba dake jikinta na daureta a bayana lokacin gudu yayi nace cikin zuciyata na tashi cikin sanda na leka tagar dakin dake gabas banga motsin komai ba cikin lambun banyi tsammanin daman zanga motsin wani abu ba amma bangaren kudu da arewa nasan yanzu ya zama tarkon mutuwa nayi shiru tunanina ya katse wata katuwar murya na magana cikin bututun magana tana cewa FADIL FADIL FADIL Munsan kana ciki ka ajiye bindigarka kafito hannunka a sama. . BIYAR 5 Mun san kana ciki fadil muryar ta sake cewa kafito a hankali hannunka a sama muna so ka fito ta kofar dakin zaka hadu da mutanen mu guda uku mun baka mintina biyu ka fito in kuma bahaka ba to zamu sa yaranmu su kamo ka da rai ko babu rai gidan yayi shiru bakajin komai sai jefi jefin motsin yan sanda abayan gidan na lalubi bangon gabas na tashi tsaye naja tagar dakin kadan kadan har ta bude wata sassanyar iska ta bugi fuskata sama tayi bakikitin da hadari anata walkiya iska na kada rassan bishiyoyin dake lambun na kurawa cikin duhun lambun ido ina kokarin ganin motsi sassanyar iskar dake lambun tattare da duhunsa suka kara razana daren da barazana mai ban tsoro kada kayi tsammanin hakan zai hanani dirga cikin lambun ko kusa yanzu babu alamar tsoro a tare dani raina yagama baci. Bayan idona ya tabbatar min da babu kowa kusa saina kama karfen tagar na dafe ajiki na dago kafafuna biyu na zurasu waje kaina na ciki sannan na juya kaina na kalli inda badura take nace ita sai gani na biyu amma kada kiyi tsammanin kinyi nasara ba'a gane jarumi sai yaki ya kare batareda najira wani abu ba saina dirga cikin lambun ganyayyakin bishiyoyin lambun su suka hana yan sanda suji sautin dirgata cikin lambun duk inda ka taka cikin lambun ganyayyaki ne sun lullube kasar wajen kamar siminti ga dukkan alamu yayi shekaru rabonsa da shara. Badura ta kwalla kara kara ne irin wanda zakaji daga bakin wanda ake azabtarwa adaidai lokacin ne naji katuwar muryar nan taci gaba da magana ta cikin bututun magana Fadil haryanzu kanada sauran minti daya kada ka sake ka taba yarinyar nan ta wajenka idan ka tabata harbinka zamuyi na tsaya cak a inda nake wani motsi agabana shi ya dauke min hankali bayan dakika uku sai naga wani tsamirmirin dan sanda yana sanda yanufo gindin bishiyar na rabe abayanta na godewa Allah dayasa bakar rigace ajikina na tabbata bai ganni ba baya kuma zaton ina wajen ayanda yake tafiya da gadara yana tsammanin ina cikin dakin ne dan sandan ya matso kusa dani tsakaninmu dashi bai wuce taku daya ba bantaba ganin tashin hankali irin wannan arayuwata ba dan sandan ya fara sanda a tsammanina bayaso naganshi ne domin yana tunani a kwance nake a tsakar dakin indai haka yake tunani to lallai yana bukatar sake sabon tunani numfashina ahalin yanzu sama sama ne dan sandan ya leka tagar dakin ahankali ta hanyar sunkuyar da kansa kasa kasa ya dan karkatar da kunnensa yana sauraron ko zaiji inda badura ke kara banjira wani bata lokaci ba saina takura na daka tsalle cikin abinda bai wuce dakika daya ba sai gani akansa muka fadi rikica akan matattun ganyayyakin bishiyar abinda yaso ya bani dariya domin lokacin dana fada kansa nayi zaton zai fadi da gwiwowinsane amma abin mamaki sai naji kamar na fada akan karmami muka mirgina sau biyu a kasa nayi wuf na rufe bakinsa adaidai lokacin dayake shirin ihu na dunkule hannuna na kirba masa naushi a muka miki yayi wani irin kuka mai ban dariya nataka ruwan cikinsa sai ya tashi zaune kamar sifirin dana dauke kafara kuma daga ruwan cikinsa sai ya koma ya baje da farko na dauka na kashe dan tsamirmirin sandansan nan amma dana taba kirjinsa sai naji yana bugawa. Ahalin yanzu an fara ciga da yayyafin ruwan na kama kafar dan sandan na jashi kamar buhu har karkashin wata bishiyar goba mai yawan ganyayyaki akalla zai kai sa'a guda kafin a same shi ya isa haka wata siririyar murya irinta matsorata tace daga bayana ka ajje bindigarka ka daga hannayenka sama kada ka manta muryar tace dani daidai nake dana harbeka a gadon baya amma abinda mukafi so shine mukama ka da ranka motsin yaudarar daya daga gareka zai zama shine motsinka na karshe aduniya . Aka fara iska da ruwan sama hancin bindigarsa a tsakiyar gadon bayana indai har na samu damar zillewa dan sandan dake bayana to ina da cikakken kwarin gwiwar cewa zan iya ficewa daga lambun amma abinda yafi damuna

Chapter 3 of 9