Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
haka nake ta jiranka har kasa na fara tunanin ko wani abune ya faru? Kada ki damu nace da Amina adaidai lokacin data tuka motar mukaci gaba da tafiya dogon zagaye nayi don haka kikaga na dade banida tabbacin cewa amina zata yarda da abinda nake fada mata hakan ya samo asali ne daga irin kallon da naga amina nayimin kallon da takeyi min ba kallo ne irin na so ba saidai zan iya kiransa da kallon an daukeni makaryaci . Fadin amina ta kira sunana batareda na amsa ba saitaci da cewa akwai wani abu dana fahimci kana boye min kuma sanin kankane bai dace ace kana matsayin masoyina ba amma kana boye min matsalarka sannan ta dubeni duba irin na SO indai har da gaske kake kana sona to ka sanar dani gaskiyar labarinka tun daga lokacin daka bar kano har zuwanka kaduna Amina tayi shiru na dan lokaci tana sauraron abinda zai fito daga bakina. Bai kamata ba ace Amina tasan gaskiyar labarin domin yin hakan yana iya jefata cikin hadarin da nake ciki idan kuma na sake na fada mata cewa sharrin da akayimin yana da alaka ne da yan uwanta Badura da Amira to tana iya yin abinda ni zan kwana aciki domin idan taji gaskiyar al'amarin tana iya zuwa ta fadawa babarta hajiya Asma'u ita kuma Hajiya Asma'u tana iya fadawa mijinta Kanal A. Mukhtar ya kai maganar kotu duk yadda aka juya ni zan kwana ciki saboda babu wanda zai yarda bani na kashe zainab ba hakan shi yasani yanke shawarar cewa zan sake shiryawa Amina karya bazan sake tasan gaskiyar labarin ba domin data sani gara na shiga gidan Kanal A. Mukhtar din na sato sarkar idan da kwanana agaba to dole ne na wuce koda kuwa ana ruwan wuta ne tattausan murmushin shirin yin karya ya bayyana a fuskara adaidai lokacin da Amina ta dan juyo daga tukin motar da take ta fuskance ni sannan nace da ita. Amatsayinki na masoyiyata ina zaton ya kamata ki yarda da abinda nake fada miki koda kuwa karyane saboda shi so hana ganin laifi ne ya masoyiyata ruwan raina mai taimakona..... Dakata. Amina tace dani basaika kurarani ba fadi abinda kake son fada zan yarda dashi koda kuwa ba gaskiya bane sannan taci gaba da cewa nasan daman fadin son danakeyi ma yafi wanda kakeyi min amma ni na gode Allah akalla dai yanzu kana saurarona akan da, wanda ada ko hira bakaso kayi dani sai gashi yanzu da bakinka kana cewa dani Masoyiyarka hakika wannan kalma ta masoyiyata da kake kirana da ita itace kalma mafi dadi da kunnuwana suka jiye min tunda nazo duniya in har kana ganin rufe sirrinka agareni shine mafi soyuwa agareni farin cikin ka shine abin sona rayuwarka itace abar begena sannan taci gaba da cewa Ka sani Fadil duk abinda kake so to nima zuciyata dolene ta karkata zuwa kaunarsa koda kuwa ada batayi amanna da shi ba. Idanuwan Amina suka cicciko da kwalla wanda hakan yasa da kyar take tuka motar so sartse ne fadil amina taci gaba dacewa da kasan irin son da nake ma da baka boye min abindake damunka ba idan da ka daure ka sanar dani gaskiyar labarinka toh a shirye nake na mika rayuwata wurin ceton ranka. Domin rayuwata batada amfani idan har ka kasance cikin kunci amma tunda kana ganin rufe sirrin naka shine yafi alheri to shikenan bana bukatar ka sanar dani saboda sanar dani din wani abune da zai bakanta ma rai ni kuma duk abinda zai bakanta ran abin begena to ina gaba dashi daga nan Amina ta karawo motar wutar muka nufi birnin kanon dabo bata ko jira kwakwalwata ta gama nazarin abinda tagama fadamin ba duk da haka saida kwakwalwata ta sake gargadina. Kada ka sake ka fada mata idan kuwa ka fada mata to kaine ruwa tsundum kasan kuwa laifin wani baya shafar wani. Misalin karfe goma sha dayan dare muka iso kano. ** Kamshin furannin fulawowi ya bugi hancina a sakamakon bude tagar dakin danayi na leka kaina ina nazarin farfajiyar gidan wacce ke haske da wutar lantarkin dake gidan bayan hanci na ya gamsu da irin kamshin furannin dake farfajiyar gidan sai na juyo da kaina na sake nazarin falon a tsanake cike kuma da mamakin irin son da Amina takeyimin duk da yake ran Amina ya baci a sakamakon yan maganganun da suka tsakaninmu a hanya amma hakan bai hanata yi min abinda tayi niyya ba lokacin da mukazo gidan talabijin na kano CTB sai Aminta ta juyo ta kalleni murmushin karfin hali a fuskaa sannan tace dani zankai ka gidanmu dake tarauni ka zauna acan kafin yan sanda su sassauta nemanka nasan da wahala yan sanda suyi tunanin nemanka agidan domin gidan sabone ba a ko taba zama acikinsa kaine na farkon zama acikinsa kwanaki hudu da gama gininsa mahaifina ya rasu na kumayi gadonsa daga wajen mahaifina sannan Amina ta danyi shiru ta dubeni tayi murmushi sannan tace idan kana bukatar abinci zaka tarar da komai acikin firji zan dawo gobe da rana domin mu sake tattaunawa sannan ta juya ta nufi kofa ta barni ina bude baki cike da mamaki kafin hankalina ya dawo jikina Amina ta fice daga dakin abu na karshe da kunnena ya sanar dashi shine karar tayar da motar Amina wacce ta fice da gudu ta nufi kofar gidan alamace dake nuna cewa haryanzu bata Huce ba. ** Karar kararrawar Agogon dake nane ajikin bangon dakin ita ta tasheni daga nannauyan baccin da ya daukeni tun karfe tara daidai na safe agogon ya nuna na tashi zaune ina mutsutstsuka idanona hasken rana ya fara bayyana a sarari yau garin babu alamar hadari sai dai idan iska ta kada hancina yakan shaki kamshin Damina. Saura kadan na fado daga kan gadon saboda tsoro wata ajiyar zuciya akayi a bayana wacce ta tsoratani a iya sanina ni kadaine a dakin tsoro ya hanani juyawa naga wanda ke ajiyar zuciyar abayana ina zaune kamar an zare min laka kuma kowanne lokaci ina tsammanin naji bindiga ta zunguri kuguna can kuma sai naji wata zazzakar murya ta kyalkyale da dariya nan da nan na dago kaina sannan na ganta a zaune akan kujerar dake gaban gadona fuskarta cike da annuri da walwala tana sanye da doguwar riga fara wacce akayi mata ado da bakaken duwatsu masu kama da zinare ta lullube kanta da bakin kyalle farin ciki ya kamani har na manta da halin da nake ciki. Wallahi Amina kin ban tsoro nace da ita. Amina ta dubeni tana murmushi daman nasan zaka tsorata tace dani tun karfe takwas da yan mintuna nazo ganin kana barci ne yasa na kyaleka saika tashi. Kuma shine kika tsoratani? Kodai ka tsorata kanka amina tace dani tana kallona haryanzu murmushin bai bar fuskarta ba sannan ne na lura da kurtun zuba shayi akan wani tebur dake gabana agefensa kuma wani kwano ne na azurfa (Silver Plate) wanda bansan ko menene aciki ba amina ta matsa kusa da teburin sannan ta bude kwanon ganin abinda ke cikin kwanon yasa cikina ya fara salati sai yanzu ne na gane cewa inajin yunwa kwanon yana dauke da toyayyiyar wainar kwai da biredi da kuma hanta, zan tafi makaranta saina dawo ma sake tattaunawa Amina tace dani yaushe zaki dawo? Na tambayeta duk da yake kuwa bana son rabuwa da ita Amma tafiyarta ita zata bani damar tunanin yadda zan fuskanci gidan Kanal Mukhtar wajen sato sarkar zinaren da Badura ta sani. Amina ta dago kai tana murmushi sannan tace dani ai ba dadewwa zanyi ba yanzu ma wani aiki ne da aka bamu tun kafin na tafi nemanka kaduna nake son nakai musu ina kaiwa zan dawo kada ka damu kaji My Darling. Ahaka muka rabu da amina ba don naso ba sai bayan da ta tafi ne nagane cewa Amina ta karance takardar da badura tabani domin ni a aljihun wandona nasata amma dubawar da zanyi sai naganta a wandon aljihun rigata tun da bata nuna min alamar komai ba nace cikin zuciyata to ya kamata nayi shiru na manta da ita. . Amina bata dawo ba sai misalin takwas da rabi na dare hankalina yayi matukar tashi badan neman yansanda keyimin ba to dana bita makarantar ina ta faman safa da marwa a farfajiyar gidan tun hudun yammacin wannan ranar har takwas da rabi ina shirin yanke shawarata karshe kenan sai naji karar mota ta nufo kofar gidan Aminace bayan munyi yan mintuna muna hira takuma fada min abinda ya tsayar da ita sai mukayi sallama saboda tace ita bata dadewa awaje kasan yadda gidansu yake mukayi sallama da ita akan yarjejeniyar cewa gobe zata zo ta tayani zama domin ba zata makaranta ba bayan na rakata har gindin motarta ta tafi sai na juyo da niyyar na shiga daki anan ne to NA FARA GANINTA. . Tun kafin na shiga dakin naji wani kamshin kakkarfan turare ya daki hancina ina tsammanin zai iya bugar da mutum hakan ne ya tabbatar min akwai mutum a dakin na dai lallaba na shi tana zaune akan kujerar dake fuskantar gadona katuwar mata ce kakkaura zatayi shekaru hamsin aduniya ta lullube kanta da bakin hijabi hakika bansan ko wacece ba. Fadil tace dani kana mamakin ganin bakuwar mace a dakinka ko? To karka damu yanzu zaka san ko ni wacece idan har kana bukatar sanin koni wacece din to nice mahaifiyar BADURA. . TAKWAS 8 Kece wa? Na sake tambayarta cikin kaduwa da mamaki Nice Hajiya binta babar badura tace dani haryanzu ina tsaye a kofar dakin banshiga ba. Abinda badura tayimin yasa duk wani wanda yake sona da yan uwantaka dashi na tsane shi don haka kallo daya nayiwa mahaifiyar badura naji na tsaneta bakuma nason zama a dakin muddin tana ciki akwai wani abu a tattare da hajiya binta dake bani tsoro irin kallon da takemin dakuma irin yadda take murmushi tana kuma bata rai alokaci guda shi ya sani na fara tunanin ba kanta daya ba sabanin 'yarta Badura ita hajiya binta bakace mai jajayen idanu can cikin loko kamar kwankwalati duk lokacin data dubeni sai ta zazzaro minsu alama ce ta mahaukata don haka sai na toge daga kofa ina shirin shekawa da gudu aduk lokacin da bukatar hakan tataso idan akwai abinda zanyi harta bar dakin to zanyi shi domin zamanta agidannan hadari ne yana iya kawo karshena shin wai me yakawota ma gurina? Kuma tayaya akayi tasan ina nan? Duk yadda kuma akayi akwai wani da yasan ina nan bayan.. Duk yadda kuma akayi akwai wani da yasan ina nan bayan ita. . Me yakawo ki nan? Na tambayeta yakamata ka shigo ka zauna tace dani ki tashi ki fice daga gidannan nace da ita domin banga hujjar da zatasa ki shigo min gidaba batareda dansani ba hajiya binta ta kyalkyale da wata irin dariya dariyar data sa tsigar jikina ta tashi gashin jikina ya mimmike gurmi ya karyo min hakika yanzu na tabbata mahaukaciya ce cikin lokaci kankani kuma saita murtake fuska sannan tace dani kai yanzu baka jin kunya kace nan gidanka ne gidan Amina kuma sai ya zama naka? Ta sake kyalkyalewa da dariya ko ka taba ganin saurayi yaci gadon budurwarsa ? Fadil ya kamata kasan halinda muke ciki domin ina son sanar dakai wasu muhimman batutuwa danake tafe dasu ko kanaso kuwa ko baka so. Me yasaki tsammanin zaki iya sani na saurare ki dole? Na tambayeta, saboda nasan muddin ina tare dakai dolene ka saurareni domin idan ka gudu ma baka da wurin zuwa ko kanadashi Fadil? Ta tambayeni nayi shiru duk da yake nasan ba kanta daya ba dole ne na yarda da abinda ta fada yanzu tabbas banida wurin zuwa to ki fada ina daga nan nace da ita kana tsorona ne? Ta tambayeni to idan tsorona kakeji saika zaba tsakanina da yansanda wa zaka saurara fadil na gaji da bata lokaci tace dani idanuwanta masu kama da kwankwalati suka juya sukayi jawu idan baka shigo ba tace dani tana murmushi irin na wadanda kansu ya tabu to zanyi ma irin abinda NAYIWA ZAINAB..... na rike numashina cikin tsoro da kaduwa, kina nufin kice kece kika kashe zainab? Tayi dariya sannan tace. Banda ma kashe zainab danayi akwai wasu abubwaunda duk zan sanar da kai yanzu kuma dole ne ka saurara na juya da niyya na fita da gudu domin na tabbata mahaukaciya ce. Gudunka bazai ka ga komai ba sai halaka tace dani gargadin da yafito daga bakinta shi yasa na sake juyowa na fuskanceta sannan ne naga wani abu kamar karfe ya turo kanta ta cikin bakin lullubin da tayi idan ka gudu zan harbe ka Fadil shigo ka zauna in kuma bahaka ba kaima kabi zainab lahira kan bindihar ya bayyana a fili na kuma tabbata ina motsawa zata harba dole kanwar naki ce tasani na nufi cikin dakin kamar kazar da kwai ya fashewa aciki na nufi kan gado kusa da inda jakar da yayana ya bani take na zauna koda na zauna sai nace da ita menene wannan kiketa faman nuna ni da ita tunda na zauna, Hajiya binta tayi dariya sannan tace KIBIYAR AJALI ce maganin yara masu taurin kai irinku idan bakayi min shiru ba da tambayoyin rainin wayo daka saba to ka ayyana azuciyarka tsakaninka da mutuwa baifinida kai din nan ba. Ai daman duk mai rai matacce ne nace da ita don Allah kuma bari nayi miki tambaya shin da wannan bindigar kika kashe zainab......? Kafin ta bani amsa sai kofar dakin ta bude sannan ya shigo hannunsa sanye cikin koren wandonsa akwai alamar datti ajikin farar rigarsa SALMAN ne. Taurin kai zai nuna miki ne Hajiya? Yanzu na dan tausasa shi yace da ita yana murmushi fice daga nan shashasha wayace ka shigo kafin ta rufe bakinta tuni salman ya bace daga dakin kamar aljani. ** Ina son sarkar tazo hannuna gobe da misalin karfe biyu na dare tace dani wacce sarka kike nufi? Na tambaya duk da cewa kuwa nasan sarkar da take nufi Sarkar da na dade ina burin mallaka tace dani na kuma jefa rayuwata cikin hadarin gaske domin ganin na cimma burina kada kaja min rai Fadil nasan kasan matsayinka agurina yanzu idan baka sani ba to bari na fada maka Sannan taci gaba da cewa kai yanzu kana matsayin karan farauta tane yakuma zama dole kayi duk abinda na saka domin idan kaki bin umarnina to bazan saurara ba wajen ganin na bakanta rayuwarka kamar yadda baka daumin sarkar nan ba zaka bakanta tawa rayuwar ina kuma yi maka tuni da cewa duk abinda ya faru akanka ba laifin kowa bane sai laifina don haka ina fatan bazaka zargi 'yata badura ba akan duk abinda ya faru itama ta taimaka min wajen hadama tarkon ne don takura mata da nayi da kuma tsorona da takeji inason ka sani Fadil taci gaba da cewa cikin daga murya in da ta badura ne to da yanzu baka cikin halin da kake ciki yanzu hakika badura ta dade da Kamuwa da sonka idan baka manta ba lokacin da kake Otel dinnan ta kaduna kunyi da badura cewa zatazo da yamma ta sameka wannan alkawaru da tayi ma tayima shine ran da kuka fara haduwa dakai a lambun otel din wanda daga karshe baka samu damar ganinta ba sa a daren wannan yammacin inda tayima karyar cewa wai wani na barazana ga rayuwarta inason kasan cewa rashin ganin badura da bakayi ba awannan rana ya samo asaline da rashin son da takeyi ka fada cikin Bala'i ina kuma fada maka duk wadannan abubuwa ne domin kasan cewa badura batada laifi kuma masoyiyarkace ba dole bane ka yarda amma zaka gane nan gaba Ina fatan duk ka gane abinda nake fada? Hajiya binta tace dani daga karshe kuma ina son snaar dakai cewa nice Ummul Aba'isin duk abinda ya faru agareka nice kuma na kashe zaina na sake maimaitawa NI NA KASHE ZAINAB Ni na kashe zainab na sake maimaitawa ni na kashe zainab don ganin na cimma burina kuma kaima ma na jefa cikin Bala'i badon komai ba sai don na bakantawa Amina Rayuwa. . Sanin kanka ne amina na mutuwar son nasan kuwa jefaka cikin bala'i kamar jefa Amina ne domin nasan zata iya yin duk wani abu don ganin ta kubutar dakai sannan hajiya binta ta kalleni ta kyalkyale da dariya. Hakan shi ya kara tabbatar min da cewa ta gama zarewa sai kayi hankali kuma tace dani na sami labarin akwai yansandan ciki akalla guda uku suna nemanka an kuma turo sune daga Durba hotel kaduna a iya sani na kuma ba'a taba samun gwanayen yan sandan ciki kamarsu ba na tabbata kuma muddin suna nan ba jimawa zasu kamaka muddin kuma kana kasar nan don haka ma nake baka shawarar ka sato min sarkar gobe mu kuma hadu a daula otel karfe biyu na dare sannan taci gaba da cewa banyi ma alkawari ba amma idan kayi sa'a zan iya baka isassun kudin da zasu fitar da kai daga najeriya ko kuwa me ka gani? Idan kuma kana ganin zaka koma gidan yayanka to bismillah kana komawa zan bugawa yansanda waya in sanar dasu cewa yayanka ne ya boye ka kasan kuwa sai sun wahalar dashi ko kuwa kana son yayanka ya wahala akan ka ta tambayeni tana zazzare idanu har yanzu ban saki jikina da ita ba domin a shirye nake na ruga da gudu aduk lokacin data taso min saidai kuma abin da yafi damuna shine bindigar dake hannunta hakika ko ban fada ma ba kai kasan ba abinda yafi kome hadari irin ace mahaukaci ya tsare ka da bindiga da dutse ma yaya ballantana kuma da bindiga zan tafi Fadil kakkausar muryar tace ta dawo dani daga tunanin dana fara tana tsaye akaina tana muzurai har yanzu bindigar na hannunta tana kuma saitin kirjina cikin murya mai dauke da tsananin gargadi tace dani ina fatan gobe warhaka kana can kana dauki ba dadi da sojojin kana Mukhtar kuma gobe warhaka ina daula otel ina jiranka ka kawo min sarkar sannan ta zazzare min idanu tace dani idan har karfe biyu da rabi tayi ban ganka ba to zanyiwa yan sandan waya na fada musu cewa nasan inda wanda ya kashe zainab yake zan kuma sanar dasu cewa nasan yarinyar data tserar dakai daga kaduna daidai nake kuwa don ayi musu bayanin kamannin Amina nasan bazaka so ba ace budurwarka ta wahala saboda kai ko zaka so Fadil? Ta tambayeni akwai alamar gajiya da surutu a muryarta, abu na karshe kuma fadil tace dani adaidai lokacin da hannunta ke kokarin kaiwa ga kunamar bindigar gumi yafara tsatstsafowa daga goshina domin nasan tana iya harbawa tunda ba cikakken hankaline da ita ba kafin ta sake cewa wani abu tuni har nayi kalmar shahada cikin carbi azuciyata domin cikin yan dakikun nan ni ina tsammanin tawa ta kare na rufe idona ina jiran naji harsashi yasami matsugunni akirjina. Kada ka tsorata fadil tace dani duk da yake nasan ka fara tunanin ko ba kaina daya ba amma hakan ba zaisa na harbeka ba domin harbinka yanzu na nufin ni da mallakar sarkar(kishiyata hajiya Asma'u) har abada kenan na tabbata babu mai iya sato sarkar idan ba kai ba ko banza dai kai Jarumine. Haka kuma da kake tunanin koni mahauciya ce banga laifinka ba domin kuwa lokuta da dama tun bayan rasuwar mijinmu na fara tunanin cewa kaina ya tabu inasonka kasani cewa babu abinda ya haukatar da kwakwalwata sai tsabar tunani da bakin cikin son kan da mijinmu ya nuna wajen rabon gado kuma kishi da son ganin na mallaki sarkar nan shi ya kara lalatar da al'amarun har kaima najefa cikin Bala'i Amma duk da haka taci gaba da cewa da ace nabarwa Hajiya Asma'u sarkar nan gara nayi sanadiyyar hallakar mutane dubu acikinsu har da kai Allah kayi mana tsari da tabin hankali nace cikin zuciyata yanzu na kara tabbatarwa da cewa wannan matar dake barazana ga rayuwata ta haukace saboda tsabar son zuciya kishi da kuma rashin tawakkali ga ubangiji idan karfe biyu da rabi tayi ban ganka ba zan baiwa salman izini da ya harbeka domin banga amfanin zamamnmu aduniya ba saboda in har bakayi nasara ba to banga amfanin rayuwata ba ban iya rayuwa da bakin cikin kishiya kuma.... Ga mamakina sai naga hannunta yayi sanyi bindigar ta fara rawa ahannunta kamar zata fadi sannan sai hawaye ya fara kwaranyowa ta kan manya manyan kumatunta masu kama da kwallon kafa dakin yayi shiru na dan lokaci ita a tsaye nikuma a zaune ina ajiyar zuciya bakajin komai sai sheshshekar kuka daga hajiya binta acan wani bangare na gidan ana ta danna hon din mota yayi wata kara fom fom har sau uku kafin akara na hudu hajiya ta fice daga dakin kanta a sunkuye bayan na bari takai tsakiyar furannin dake farfajiyar gidan sai na mike na biyo bayanta da gudu gudu ina zuwa kofar gidan, direban hajiya binta yayi ribar wane to direban na tambayi kaina salman ne ko kuwa ? Nan da nan zuciyata taki Na'am da tunanin da ta farayi ba salman bane saboda salman kato ne mai fadin kafada kamar kofar garejin mota wannan kuwa dake tukin motar dan tsatstsama ne duk kuma da yake duhun cikin motar bai bani damar ganin fuskarsa ba nasan fuskar matsoratace dashi to wanene kuwa? Kamar anso a bani amsar tambayata sai direban ya....... Kamar anso a bani amsar tambayata sai direban ya kunna fitilar dake cikin motar cikin zafin naman da ya bani mamaki sai hajiya binta tayi sauri ta sake kashe fitilar duk motsin da sukayi ya dauki abinda bai gaza dakika hudu bane jikina ya dauki rawa zuciyata ta fara bugawa da sauri direban motar ne ya sani rawar bakuma wani bane sai DAN TSOHON NAN MAI FUSKA KAMAR MATSATSTSEN LEMON TSAMI mai aiki a durba otel idan baka manta ba lokaci na karshe da muka hadu dashi shine a durba otel lokacin dana shake shi a jikin bango ina gargadinsa da cewa kar ya sake yacewa yan sanda ya ganni. Yau kuma gashi tare da hajiya binta motar taci taya kuuu sannan ta hau titi da gudu. ** Zuciyata cike da tunani da kuma matsanancin mamakin ganin dan tsohon nan ahaka na nufo daki jikina kamar anyimin duka kwanaki biyu da suka wuce nasha yiwa kaina tambayar cewa yaya akayi har wani mahaluki zai saci jiki ya shigo kasaitacciyar otal kamar durba ya kuma kashe mutum batareda jami'an tsaron otel din sun ganshi ba wannan yana bani mamaki to amma yanzu na daina mamaki domin na samu amsar tambayata yanzu kam na tabbata wannan dan matsatstsen tsoho dashi hajiya binta ta hada baki harta sami damar halaka zainab saboda nasan kudi yana iya sa mutum yayi komai koda a dane ballanata ayanzu to amma abinda yake bani mamaki haryanzu shine menene hadin hajiya binta da dan tsohonnan da har zai zama direbanta? Kuma shin yabar aikin otel dinne kokuwa. gaskiya fa naga dan tsohon nan ya dage tsakaninsa da Allah yana baiwa yan sanda bayanin kamannina a jarida ashe saye shi akayi aka kuma shirya tuggun jefani bala'i taredashi to Allah ya toni asirinsa. Na nufi gado nayi zaman yan bori akai alokacinne naji wani abu ya danyi kabarbar a cikin aljihuna gaban rigata nasa hannu na zaro takardar ahankali manta sam sam da ita na bude takardar na fara karantawa kamar haka takardar da Badura tabani tun ina Kaduna. . TSARIN GIDAN KANAL MUKTAR. Fadil inason kasan cewa wannan takarda na rubuta tane don na sanar dakai wani abu dake cikin duhu wanda kai baka sani ba na farko dai inason ka sani cewa duk abinda yafaru akanka ba laifina bane ba kuma laifin yar uwata Amira bane ko kusa babu laifin kowa acikinmu babarmu hajiya binta ita ta takura min don na yaudareka kafada tarkonta ni masoyiyarka ce Fadil kuma ina tayaka bakin cikin abinda yake faruwa akanka ina kuma fatan Allah ya taimakeka yakuma tsallakar dakai sharrin mahaifiyarmu, ina kuma son na sanar dakai cewa mahaifiyarmu ba kanta daya ba tun lokacin data dauki ranta ta kwallafa akan sarkan nan ta gadonmu haka nan sai duk Al'amuranta suka canza son zuciya da sharrin shaidan suka rudeta ta fara tunanin mallakar sarkar ko ta halin kaka. Fadil da farko na dauka wasa take min daga baya sai naga abin yafi karfin wasa ka yafeni Fadil badon ni ba wallahi duk abinda nayi ma a da takura min akayi saboda mahaifiyarmu tace idan ban yaudareka saita harbeni nikuma danaji haka sai tsoro yakamani saboda ina gudun ta harban matukar banyi abinda tace ba to tana iya halakani domin kuwa ba kanta daya ba, tun farko dana fahimci cewa kwakwalwarta ta tabu naso naga na sanar da hukuma to amma saina tuna da cewa muddin na sanar dasu cewa mahaifiyata tana barazanar kasheni to gidan mahaukata zasu sata kasan kuma yadda gidan mahaukata yake ba a basu kyakkyawan kulawar daya kamata saboda an ga yawancinsu talakawane da marasa gata kuma koda ana basu kyakkyawar kulawar ma bazanso ace mahaifiyata tana cikin gidan mahaukata ba bayan haka kuma Fadil zakaso kaji inda muka sami Bindiga har muke wasa da ita akan rayuwarka bindigogin dai su uku ne kuma na baban mu ne tun yanada rai mahaifiyata ta sace su an neme su har an gaji bani na sake ganinsu ba sai bayan da mahaifiyarmu ta fara shirin tsunduma ka acikin bala'in nan sannan ta fito dasu ta dauki daya ta baiwa Salman daya nikuma ta bani daya amma ni bantaba amfani da tawa ba kada na cikaka da surutu ni dai inason kasancewa ni masoyiyarka ce kuma duk abinda kaga nayima har dukan da salman yayi ma acikin dajin nan na kaduna nabar shi ya dake ka ne don babu yadda zanyi dashine domin ina nuna alamar raina ya sosu salman zai fadawa mahaifiyarmu domin shi ta dauko shi haya ne domin yana kula da duk abinda nake aiwatarwa akanka saboda ta lura da cewa tun lokacin data nuna min kai amatsayin saurayin da zata tsunduma cikin bala'in don ganin ta cimma burinta ta gane cewa na kamu da CIWON SONKA. Kamar yadda nace abaya inason na sanar dakai wasu abubuwa masu hadari guda uku dake tattare da gidan kanal mukhtar na 1 farko dai inason kayi hankali idan ka shiga saboda akwai karnuka masu cin naman mutane 2 na biyu kuma gidan yana dauke da kofofin shiga har guda goma sha biyu kowacce kofa akwai kosassun karnuka guda uku da kuma sojoji masu jajayen idanuwa guda hudu idan kayi jimla zaka sami karnuka talatin da shida kenan sojoji kuma arba'in da takwas ban da kuma na kofar farko wacce ke dauke da sojoji goma shabiyu kowannensu kuma bai dauki ran mutum abakin komai ba.Sai kuma abu na 3 uku wanda shima yanada muhimmancin gaske sarkar da mahaifiyarmu take son ka dauko mata tana cikin wani gilas ne mai dauke da wata irin fitilar lantarki mai tsananin haske babu kuma wanda ya isa ya je kusa da gilas din sai inuwarsa ta fada kan gilas din

Chapter 5 of 9