Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
ya ganni nafito daga dakinta a daidai lokacin data mutu me kake tsammani? Kanajin yan sanda zasu yarda da karyata cewa maganin ciwon ciki nazo karba a dakinta na taradda ita a mace? Na saba jakata a kafada sannan na dubeta nace da ita ina dan makullin motarki ko kuwa kin baro shi a dakin? A'a gashi nan tace dani ta miko min dan makullin na jefa a aljihuna sannan nace tashi mu tafi ta dauki jakarta mai taya ta biyo ni zuwa kofar dakin cikin mamaki da rashin fahimtar al'amarun dake gudana duk da yake dai nasan tasan babu lafiya amma bazan taba hakura na fada mata ba sai mun fice daga cikin otel dinnan . Bani jakar taki saiki rike wannan na ce da ita ayayin dana mika mata tawa jakar ni kuma na karbi tata akwatin ita dai batayi min musu ba ko kuma tambaya kawai dai tana bina kamar kumama mun kawo hawan benen na karshe kenan sai naga dan motsatstsen tsohonnan yana kokarin shigewa wani daki nayi sauri na matsa kusa dashi da farko nayi niyyar na manta dashi amma sai nayi tunanin me yiwa ya leka dakin yaga abindake ciki don hakane yake kokarin bace min sa'adda ya hango ni babu mamaki ma yanzu yan sanda suna kan hanyarsu zuwa otel din Na rarumi kwalarsa na hada shi da bango kafafunsa da kyar suke taba kasa sannan nace dashi cikin fushi ka manta da duk abunda ya faru dazu ka gane ko? Na buga matsa tsawa ko da anzo ana tambaya to amsar ka itace banga kowa ba in ka sake ka kara cewa wani abu daga nan ba na saina na fada maka ba na sake shi yafado akan tsintsiyar dake hannunsa yaso yabani tausayi amma dana tuna da masoyiyata badura da bala'in da take cki saina dake zuciyata na sake buga masa harara ka jiko? Nace dashi Toh ya amsa cikin irin muryar da zakaji yayin da ka shake zakara abinda nake nufi nace dashi koda yan sanda zasu tambaye ka kokaga wanda ya shiga daki mai lamba uku ko ya fita to amsarka itace BAN GANI BA toh yasake amsawa ban damu ba nasan ko ya leka ko kar ya leka dole ne nan da awa daya a sami gawar zainab dan tsurkun tsohonnan kuma dole ne yace ya ganni amma yanzu nasan nayi maganin na dan lokaci . Badura na rabe ajikin bango jiki na rawa batace dani komai ba na duba agogona dakyar naga karfe nawa ne yanzu sainaga babu shi babu labarinsa na juya nakama hannun badura dake tsaye kamar gunki muka nufi kasa nasan na maka ban damu dana koma dakin badura ba domin duba agogo na tabbata tataba anan na yada shi ko yake nasan agogo ba wani abu ne ba dan yan sanda sun sami agogo wannan wani abu ne da bai shafeni ba domin kuwa ba ni kadai ne mai sa agogo ba tunanina ya katse ayayinda naji wani abu kamar kukan jiniya na fizgi hannun badura mukayi kasa da gudu muka fice ta kofar baya yi sauri ki kaimu inda motarki take nace da ita batayi min gardama ba sai kawai ta wuce gaba da gudu nima na bita a halin yanzu ta fara gane lamarin bata bata lokaci ba duk da yake batasan meke faruwa ba amma nasan ta san muna kokarin kaucewa yan sanda ne kafin na karaso inda motar take tuni ta fada ta tashi motar tayi baya kadan zuwa saitin da nake banyi wata wata ba sai kawai na bude gidan gaba na fada na jawo na rufe duk wannan ya faru ne acikin dakika talatin. Badura ta fizgi motar da gudu kamar walkiya muka nufi kofar otel din dake baya don kuwa nasan yanzu yan sanda sun cika daya kofar wata mata ta dauki kara ayayinda motarmu tayi kan danta dake wasa a tsakiyar titin otel din badura ta dauke kan motar tsakanin tayar motar da kafan yaron baifi takun hannu daya ba duk da haka bamu tashi ba kaga da laifi ya karu kenan muna isa kofar otel din dake baya sai naga sai naga maigadin kofar da wayar tarho a hannunsa nan da nan kwakwalwata ta fada min cewa babu mamaki yan sanda ne sukayi masa waya ya hana mu wucewa kafin na gargadi badura ita har ta yanke hukunci ta nufi kofar da gudu kamar harsashi maigadin ya tsaya cak yana kallon ikon Allah yana baiwa kansa shawarar ya bude ko kar ya bude daga karshe dai ya ga in yaki budewa su zasuyi asarar kofarsu domin kuwa mu bamuda niyyar tsayawa ya bude kofar yayi tsalle yakoma gefe guda mu kuwa muka wuce kamar walkiya na jua baya na kalli otel din. Sai naga duk mutane sun leko ta tagogi suna kallon mu In ka dauke matar nan da muka kuskure danta da taku daya ta dora hannunta akan danta wanda ke rungume a kirjinta tana kukan murna badura ta kara take totur din motar muka harba kan titi kamar kibiya dana duba malekin motar sainaga ya nuna muna tafiyar kilo mita....... Dana Duba malejin motar sai naga ya nuna muna tafiyat kilo mita dari da shirin a sa'a guda na jingina kaina akujerar motar na rufe idona sannan nafara me kake jin zai faru idan taya ta fashe awannan lokaci? Lallai muna bukatar addu'a . ******* ****** ******* ******* ******** . Agogon dake jikin motar ya nuna karfe shida ta rabi na safe a daidai lokacin da muka kawo mararrabar da zata fitar damu wajen gari har yanzu bamu yanke inda zamu nufa ba kokari na dai kawai shine mu fice daga kaduna in yaso daga nan sai muyi shawarar inda zamu a yanzu dai kilo mitar mu biyar da barin kaduna Badura ta rage gudu sannan ta dauke kan motar muka shiga wata yar siririyar hanya wacce ta shiga cikin daji muka wuce ciki da gudu hakika badura tana kokari domin ki ni nake tuka motar da kyar ne in zan iya irin gudun hadarin da takeyi batareda gabana ya fadi ba saida mukayi gudun kilo mita daya da rabi acikin dajin sannan muka isa wani waje mai yawan bishiyoyi manya manya da kuma koren gayayyaki ko ina tayi kwana ta motar ta shiga cikin sarkakkiyar bishiyoyi da ganyayyakin har saida ya zamanto bazaka iya ganin mu ba idan kanadaga waje sannan ta taka burki ta tsaya ta kuma kashe motar sannan duk muka fito daga motar. Ta juyo muka kalli juna sai tayi min murmushinta mai sanyaya zuciyar masoyi a karo na farko kenan tun lokacin dana sami gawar zainab, sai naji raina ya danyi sanyi. . Me ke faruwa? Tace dani daidai lokacin data hau bakin motar ta zauna nikuma ina zaune akan wani reshen bishiya dake kasa kasa ya kamata ka bani labarin tun daga farko. Tace dani sannan taci gaba da cewa ni duk ban gane abinda ke faruwa ba Na gyara zama sannan nace da ita zainab ta mutu tayi min wani irin kallo kamar wadda take zaton kaina ya tabu. Me kake nufi ta tambaya a rufe abinda nake nufi shine na sami zainab a kwance akan gadonki matacciya sannan naci gaba da cewa in duk wannan bai ishe ki ba to hadda ramin harsashin bindiga a kirjinta Badura ta dafe kirji ta lumshe idanu nayi saurin dirgo daga kan reshen da nake zaune na nufi inda take da sauri na tare ta a yayinda ta fara gangarowea daga gaban motar sumammiya. Na kwantar da ita akan koriyar ciyawar dake shimfide a ko ina cikin dajin sannan na bude motar na dauko kwalbar ruwan yankarin dana saya tun kafin mu bar cikin kaduna nafara zuba mata a fuska ina dan jijjigata can bayan kamar mintuna biyu ta farfado ta bude idanunta kadan sannan ta sake rufe su. Na sunkuya na ciccibeta nasata a bayan motar sannan na gyara mata kwanciya hakika tana bukatar hutu ahalin yanzu na bar kofar motar a bude domin ta sami isashshiyar iska sannan na koma gaban motar na zauna ina tunanin abinda ya kamata na farayi a halin yanzu hakika muna cikin bala'in da bansan karshensa ba sannan tambayar nan guda daya ce wai shin wacece take son kashe BADURA? Kuma akan me? Ya zama dole nayiwa badura wasu yan tambayoyi kafin mu bar dajin nan domin ina bukatar sanin labarnta dana iyayenta da kuma sunan unguwar datake a kano . Agogon motar ya nuna karfe bakwai na safe wato munyi kimannin rabin sa'a kenan a dajin dajin yayi tsit bakajin komai sai kukan tsuntsaye dana kananan namun daji akwai alamar hadari a garin har yanzu ga kuma sanyi saboda ruwan da aka kwarara duk da yake dai ruwan da akayi a dajin bai kai na cikin garin kaduna yawa ba. Na kunna rediyon dake gaban motar kade kaden hausa dana turawa sai tashi suke daya bayan daya mintuna uku suka shude batareda naji abinda nake jira ba JAMA'A GA WATA SANARWA...... A daidai lokacin duk wani kade kaden dake tashi a rediyon ya tsaya cak. Sannan sai naji mai sanarwar yaci gaba da cewa JAMA'A KUYI HANKALI DA YA'YANKU SABODA AN SAMI WANI SAURAYI WANDA BA'A TABBATAR DACEWA SHIN MAHAUKACI NE KO MAI HANKALI BANE Wannan saurayi ya harbe wata ma'aikaciyar daba otel nan kaduna sa'o'i uku da suka wuce don haka yan sanda suna rokon jama'a duk wanda ya hangi inda ya nufa to ya sanar dasu ganin karshe dai da akayi masa yana tare da wata yarinya wacce a dakinta aka kashe ma'aikaciyar otel din ana kuma tsammanin yarinyar ma da suke tare rayuwarta tana cikin hadari domin kuwa yan sanda suna zaton yarinyar ta ganshi a yayinda ya kashe ma'aikaciyar otel din ya kuma kamata a matsayin garkuwa don Allah Jama'a a taimaka fari ne dogo dan kimanin shekaru ashirin da daya yarinyar kuma dake tare dashi itama fara ce yar shekaru goma sha takwas dukkansu suna cikin bakar mota 505 lambar motar shine KN 0912 NS kuyi hankali dashi domib ana zaton bashida cikakken hankali....... . Na kashe rediyon jikina na bari sansassayan iskar dake shawagi a lokacin bata hanani gumi ba sai yanzu ne kara fahimtar irin bala'in dana sami kaina aciki hakika duk wanda ya biyewa mace saita batar dashi yana kuma tare da mummunar rayuwa Da ace na manta da badura na fitar da sonta daga zuciyata na kuma ki karbar ta alokacin datazo dakina a otel din daba da duk wannan bata faru gareni ba gashi yanzu laifin ma ni kadai ya shafa . Tunanina yakatse a daidai lokacin danaji kamar motsi a bayan motar da farko na dauka tsuntsaye ne suke motsa ganyeyyakin bishiya amma daga baya sai naji kuma sawun mutum yana taka ganyayyakin nazaro kafata na fito daga gaban motar da niyyar naga abinda ke faruwa sannan na kalli madubin motar gashin jikina ta tashi. Da farko na dauka iccen bishiya ne ya zunguri kuguna amma daga baya sai tunanin bindiga ya fado min azuciya kada ka motsa aka gargadeni daga baya. Kamshin turaren danaji shekaranjiya a dakina shi ya bani damar gane ko wanene ke bayana madubin motar ne ya nuna min shi haryanzu yana sanye da farin wandonsa da koriyar riga hancin bindigarsa a kuguna . Numfashina ya tsaya cak a daidai lokacin da bindigar mutumin ke barazana yin ruwan harsashi a kuguna. Kada ka sake ka motsa mutumin yace dani cikin wata murya irin wadda zakaji a yayin da kayi magana acikin hujajjiyar lasifika. kayi kuma duk abinda na umarce ka ya ci gaba da cewa idan kuma kayi kokarin yin wani abu daban wannan shine zai zama motsi na karshe da zakayi a duniya. Abinda yafi bani tsoro shine badura bayan motar a kwance sumammiya na tabbata in har yasan tana nan to babu abinda zai hana ya karasa ta. Nasan a halin yanzu kowa yake yiwa aiki na riga ya yardamma kansa cewa an kashe saidai kuma abinda na kaa fahimta anan shine shin me ya kawo wannan mutumin nan? Kuma yaya ma akayi yasan muna nan? Duk wannan tunanin nayi shi ne cikin dakika ashirin mutumin yasa hannunsa daya acikin aljihun wandona dana rigata ya lalube ni ko ina a tsammaninsa ina dauke da bindiga ko wani makami hannunsa dayan kuma yana rike da katuwar bindigar dake kokarin yimin raunin da bana tsammanin harsashinta zaiyi min. Na tsaya nan yanata lalube ni kamar wani barawo bayan dan lokaci kadan ya tsame hannayensa daga aljihuna na gane hannayensa manya ne ta hanyar ganinsa danakeyi ta jijkin madubin motar. Ya tsaya nan yana kallona kamar wata sabuwar halitta gabana yanata faduwa saboda tunanin abinda zai faru har yasan Badura tana motar don na tabbata baisan tana bayan motar ba yawun bakina ya kafe saboda abinda na gani BADURA na zaune a bayan motar tana kallon bayan mutumin shi kuma duk hankalinsa ya tattaru a kaina nayi kokari na yi mata alama da idanuna domin ta koma ta kwanta amma hakan ya gagara ga dukkan alamu ita bata ma san abinda ke faruwa ba. . Adaidai lokacibn ne ta juyo fuskar ta wajen madubin muka hada ido da ita ta madubin babu alamar data nuna cewa ta damu da bindigar dake barazana a kuguna nasan taga mutumin ta kuma ga bindigar amma hakan bai ko chanza kamannin fuskarta ba tana zaune kamar mutum mutumi tana kallona sannan cikin abinda baifi dakika biyu ba sai kyawawan labbanta suka fadada izuwa murmushin da bai kai ido ba hantar cikina da hanjina suka dankare a waje guda saboda tsabar kaduwa da abinda na gani. Hakika badura ta chanza min kama cikin dan kankacin lokaci ta taso ahankali ta fito daga motar banga alamar mutumin dake bayan yayi koda motsi ba shi dai kawai bindigarsa ya ajiye a kuguna yana shirin harbawa kada ka sake ka motsa mutumin ya sake gargadina har yanzu murmushin yana fatar bakina gushe ba. Wani kamar juwa ya fara daukata kamar zan fadi kaduwa da tsoro da kuma mamakin abin dake shirin faruwa agareni suka cika min kwakwalwata kada kayi zaton murmushi da takeyine kawai ya bani tsoro a hannunta na hagu tana rike da damin igiya sannan hannunta na dama tana rike da yar' karamar bindiga mai kama da ta wasan yara ko kadan ban zolayi kaina ba na tabbata bindigar bata wasan yara bace. . ME KAKE JIRA DASHI NE? badura tace da mutumin naga giftawar gindin bindigarta cikin madubi kamar walkiya nayi kokari na goce kaina amma ina na maka gindin bindikar ya daki tsakiyar kaina sannan rana ta bayyana a idanuna taurari masu haske suka maye gurbin ranar sannan duhu ya maye gurbin su gabaki daya abu na karshe danaji shine maganar badura tana ceewa 'Daure shi sosai don kasan kakkafar ne sannan ta kyalkyale da dariya. ** Bansan iya tsawon lokacin dana dauka sumamme ba nidai kawai na farka na sami kaina a daure kamar damin gero acikin awani dan kankanin daki nake da baifi na tattabaru ba yana dauke da taga daya da kuma wata katuwar kofa wacce tafi dakin kwarjini gadon dasu badura suka kwantar dani dan kankani ne na katako yana dauke da wata latsatstsiyar katifa mai kamar silifa a duk lokacin dana motsa sai naji gadon na kokarin rabewa na fado kasa tsakar dakin na mamaye da wani rubabben kilishi wanda ga dukkan alamu zai sami shekaru uku rabonsa da yaga ruwa in ka dauke wasu dagargazazzun takalma dake daf da kofar dakin dakuma karzan sigari guda daya akan tagar dakin babu komai sai tsabagen zafin dake kokarin dafani da raina Tagar dakin a rufe take kada kayi tsammanin kuma za'a bar kofar a bude wannan shine ya hanani gane shin yanzu dare ne ko kuwa rana? Duk motsin da zanyi sainaji kamar gabobin jikina zasu ruguje saboda tsabar dauri na dan dago kaina sainaga gaban rigata a rine da bushshan jini alokacin ne kwakwalwata ta fara aiki SOSAI....... . Alokacin ne kwakwalwata tafara aiki sosai abubuwan da suka faru sun bayyana a fili a zuciyata. . Ko kadan banyi mamakin abinda Badura tayi min ba domin kuwa wannan kadan ne daga yaudarar mata tarko ne dai na riga na fada za'a iya kiransa tarko mai kofa uku biyu daga cikin kofofin a bayyane suke sai dai babu halin fita kofar farko yan sanda sun tsareta kofa ta biyu kuma su Badura sun tare ta. Kada ka yi tsammanin su Badura sun kawo ni nan ne kawai don jin dadi hakika nasan zasu bukace ni da wani abu shin toh menene toh dalilin kamani? . Ya zama dole na samu kofar nan ta uku wacce na tabbata itace zata fitar dani daga bala'in dana fada a halin yanzu. Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji muryar Badura a kofar dakin. Har yanzu bai farka bane? Baduta tace ina tsammanin tana magana ne da bakin mutumin nan wanda har yanzu na kasa fahimtar sunansa. Bai farka ba mutumin yace da ita kaduba shi dazu ne? Badura ta tambaye shi Sa'o'i biyu da suka wuce kenan yace da ita daman ai na ce maka ka dake shi kadan kai kuma ka doke shi da karfi, meyasa bakayin abinda aka sa ka sosai ne ? Kaga shekaranjiya ma haka kaso ka bata mana shirin da mukayi wata shida munayi. Ance kazo da wuri amma saida ka bata lokaci yanzu daya sa mun fice daga dajin yaya za'ayi ka same mu? Kaga fa wahalar da ka bani badon Allah yasa dabarar yin suman karya ta fado min ba da yanzu shirin ya baci. Kiyi hakuri mutumin yace da ita Badura kinsan dajin ne wahalar ganewa ne dashi kuma ke kanki kinsan da wahala a kai mutum cikin wannan dajin da daddare ya gane shi da rana don haka daman na ce ki kaini da rana kika ki to..... Kada ka dame ni da surutu badura ta katse masa hanzari in kasan bazaka iya aikin ba gara tun wuri ka fada mu sami canji kada kiji komai mutumin yace da ita daga yau bazan sake yin kuskure ba bari na shiga naga ko ya tashi Yi sauri toh badura tace dashi zaka same mu a babban falo. . Jikina na rawa na koma da sauri na rufe idona kamar ina barci a daidai lokacin da kofar dakin ta bude mutumin ya shigo dakin yana tafiya kamar baya so haryanzu yana sanye da kayansa na gado kora da fari ga dukkan alamu mutumin yana tsananin kishin tutar Najeriya tafka tafkan hannayensa masu kama da mahuci suka dafa kirjina sannan ya kama kwalar rigata ya jijjigan na bude idanuna na kalle shi ya kalle ni jajayen hakoran suka fara wani abu dashi yake tunanin murmushi ne. Barka da zuwa dan tsako yace dani daga yanzu sai abinda aka sa ka shi zakayi haushi ya kamani na daga kai na tofa masa yawu a bakar fuskarsa mai kama da ta biri nan da nan idanunsa suka kada sukayi jajur kamar garwashin wuta ya daga hannunsa ya sharara min mari wani abu yabi ta kwakwalwata sannan ya gangaro ta babban dan yatsan kafata da farko na dauka kunne na ya fita banajin kome sai irin karar dazakaji ayayinda ka kara kunnen ka a kan titin motoci hakika ba'a taba yimin mari irin wannan ba. Bayan nayi kokari na dawo da numfashina sai na sake tofa masa yawu amma wannan karon sai na kasa jajayen idanunsa suka tsoratani suka kumayi min kashedin cewa yanzu fa in na sake kara marina toh kurumcewa zanyi sai kawai na koma kan gadon na kwanta har yanzu akwai murmushin mugunta a fuskarsa wuka ta fado hannunsa daga bako ina ba don ko ni kaina bansan daga inda ya zato ta ba nayi tsammanin fede ni zaiyi amma daga karshe sai na ga ya kama igiyar dake jikina ya fara yankewa. . In ka sake kokarin tofa min yawu ya gargade ni sainayi maka marin da uwarka bazata gane ka ba. Gara ma ni inada uwar nace dashi kai taka uwar ma ba a san ta ba. Idanunsa suka sake kaduwa amman wannan karon bai kawo min mari ba sai yawai yaci gaba da tsinke igiyar bayan jiran danayi kamar shekara awurina daga karshe na sami kaina ya warware igiyar sannan ya kama wuyan rigata ya tashe ni tsaye naji kamar kafata bazata iya daukana ba kwana biyu a daure baci ba sha ba wasa bane saura kadan na fadi amma sai kore da farin ya taro ni ya kama hannayena yana jana kamar mai koyon tafiya Muka fita daga dakin muka shiga wani da bai fi wanda muka fito yanzu kyau ba daga gefen hannun dama akwai kofofi guda biyu sai mutumin nan kore da fari yace dani shiga kayi wanka ina nan ina jiranka ka kuma shiga taitayinka ya gargade ni na lallaba na shiga bandakin ta hanyar dafa bango naja kofar na rufe bandakin yafi dakin da aka daure ni girma da kadan yana dauke da kwamin wanka irin na turawa guda biyu kowannensu yana dauke da famfo daya da kuma shaya daya akwai katon madubi a manne a jikin bangon bandakin daga kudu na dubi fuskata ajikin madubin sai naga duk ta fada lallai naji jiki ciwon dake kaina yanzu ya daina zafi sosai na lallaba na tube kayan dake jikina sannan na kunna shaya na shiga karkashinta ruwan yana kwarara akaina ni kuma ina wanke busashshen jinin dake kaina Lokaci yayi da yakamata na nunawa baki mai kore da fari cewa nima fa ba matsoraci bane nima fa ba karamin shaidani ne in dai har mutum ya biyo dani da hanyar shaidancin to zan nuna masa na fishi. . Bayan na wanke jikina tsaf na kuma shafa mai sai na sa kayana sannan da daki kofar bandakin da kafata ta bude na fito ina muzurai wai dan ya gane cewa to yanzu babu wasa mutumin ya dago ya kalle ni a yatsine a hannunsa na dama jakata ce wacce na dauko daga hotel din mu shekaranjiya lokacin da muke shirin gudu, Yi sauri kasa kayanka suna can falon suna jiranka yace dani. Sannan mutumin ya jefo jakar saitin fuskata da farko nayi niyyar na kauce dan kada jakar ta sameni a fuska amma dana tuna da halin danake ciki yanzu bana tsoro bane sai kawai na tsaya waje daya ina jiran jakar ta karaso nasa hannun hagu na cafe ta na girgiza ta a gabansa sannan nace dashi. Kaje kacewa uwarka badura ta jirani minti biyu fuskarsan ta canja kala daga baki zuwa toka toka na kalle shi na fashe da dariya matsoracin mata nace dashi karka dauka ni ma tsoranta nakeji kamar ka hannayensa suka dunkule ya fara matsowa inda nake tsaye in yana tsammanin zan tsaya ya dakeni to lallai yana bukatar sake sabon tunani naja da baya ina duban ko ina cikin dakin ko zanga makami. Can sai na hango wani manjagara a jingine a kofar bandakin daga hannun hagu nayi sauri cikin dakika biyu saiga manjagaran ya fado hannuna dakin yayi shiru bakajin komai sai karar disar ruwa a bandakin dake gefenmu. . Kada kayi fada shi SALMAN muryar badura ta ratsa shirun dake dakin mutumin yaja da baya jiki na rawa sannan ya daka min harara ya juya ya fuce daga dakin yanata faman hadiyar zuciya. . A karo na farko tun ranar da aka danamin tarkon sai na gane sunan mutumin nan mai koren wando da farar riga SALMAN bantaba jin suna irin wannan ba mukayi ido hudu da badura tana tsaye a kofar dakin wacce nake tsammani zata kaini babban falon sannan sainaji gabana ya fadi kofar dakin ta bude wata kuma Badurar ta fito Al'amarin zai baka mamaki idan nace maka na kasa banbancewa tsakanin yan matan biyu da suke kallona kamar a majigi suna sanye da bakaken riguna dogaye anyi musu adon fari a wuya muryarsu iri dayace kamar su daya babu banbanci ko kadan tsawon su daya kalar jikinsu kuma daya ce idan aka hada su su biyun zaka iya kiransu BADURA waccan badura dana sani amma hakika ayanzu bazan iya cewa wannan ce Badurar dana sani ba. . Muna son magana da kai idan kagama shiryawa sannan daya badurar ta ce. Badura da amira shine sunayenmu idan ka shirya muna jiranka a falo sannan sukayi min murmushi iri daya suka juya suka nufi dakin nayi kokarin gane banbancinsu amma nakasa tafiyarsu iri daya sannan na tambayi kaina tambayar da zata fitar dani daga tarkon dana fada shin WACECE BADURAR ? WACECE KUMA AMIRA ? Na tabbata daya daga cikinsu itace ta harbe zainab. Amira kenan? Na tambayi kaina wacece to Amira daga cikinsu duk abinda yafaru tun daga farko har zuwa yanzu sai ya zama kamar mummunan mafarki agareni kiran da Salman ya kwada min shi ya tabbatar ba mafarki nakeyi ba. ** Ahaka na shiga dakin a rude na tsaya a bakin kofar farlon kato ne mai dauke da kujeru goma sha shida kowanne bango na dakin yana dauke da kujeru hudu kyawawan kilishin mai taushin gaske ya mamaye dakin a kusuwar dakin dake bangaren gabas akwai katuwar kanta mai dauke da littattafai sama da dari bakwai kamar dakin Al'huda huda bana tsammanin gidansu ne sai dai in na wani ne suka ara koma na wanene zan iya cewa dakin ya tsaru daidai misali . Shigo ka zauna mana badura tace nashiga cikin dakin a hankali tattausan kilishin da ya mamaye dakin yana barazanar shanye kafata iya idon sawu na zabi kujera daga bangaren arewa na zauna ina fuskantar su Badura ta Amira suna zaune a kujera guda idan har kasan sunansu shine Badura Da Amira to zaka iya kiransu cikakkun yan biyu idan kuwa baka san sunayensu ba zaka iya kiran Badura inuwar Amira kokuma Amiran inuwar Badura. Da gangan suke komai iri daya domin kawai su rikita min kwakwalwa Salman na zaune acan jikin bango a kusan kantar nan mai dauke da tarin littattafai muka hada ido dashi akaro na farko tun da muka hadu dashi sai yayimin murmushin daya kai har idonsa. FADIL daya daga cikin su tayi kiran sunana lokaci yayi daya kamata kasan duk abinda ake ciki.... Me ya shafeni? Na katse mata hanzari kwarai kuwa ya shafeka tace dani in zaka bani dan lokaci yanzu kuwa zakaji abinda ya shafeka sannan taci gaba da cewa kasan KANAL MUKHTAR ? Nayi shiru na dan lokaci babu alamar razana a fuskata amma daga cikina har zuwa kwakwalwata sun daina amfani alokacin. . Tun ranar dana farko kano sai yanzu ne na tuna da AMINA Yarinyar datake matukar sona amma haryanzu Allah baisa min sonta ba magana ma inayi mata ne don kar tace na wulakantata duk da cewa bansan abinda wannan yan biyun ke nufi ba murmushin dake yawan bayyana a fuskarsu bana sonsa murmushine irin na mugunta nakuma kasa gane abinda suke nufi idan baka sani ba bari nafada maka ko wanene Kanal Mukhtar . Fari ne dan gajere kakkaura mai yawan tarin gashin baki tsohon sojane wanda ahalin yanzu shekararsa goma dayin ritaya daga aikin soja mutane da dama suna jita jitar cewa shekarunsa saba'in a duniya wasu kuma... . Mutane da dama suna jita jitar cewa shekarunsa saba'in a duniya wasu kuma sunce ya kusan tamanin Allah ne kawai da mahaifiyar Kanal Mukhtar suka san yawan shekarunsa a duniya

Chapter 2 of 9