Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KIBIYAR AJALI Na Nazir Adam Salih Ebook creator Shuraih Usman 99% . Zaku iya downloading wasu da dama daga cikin ebook namu ta hanyar ziyartar babban shafin mu na Hausaebook akan wannan adireshin www.shuraih.waphall.com Wannan ebook din an sake shi ne A matsayin Happy Sallah ga daukacin Al'umman musulmai baki daya , Asha karatu lafiya Karar Abinda Ban taba zato ba ta ratsa kwakwalwata da farko na dauka karar aradu ce barcin da idona ya zama tarihi a halin yanzu na tabbata karar bindiga naji nan da nan na nufi kofar dakin da gudu a daidai lokacinne naga wani ya nufi kasan benen da gudu sanye da bakaken kaya. Cikin kaduwa na juya zan koma dakina sai naga daki mai lamba uku 3 a bude banyi wata wata ba sai na fada cikin dakin na lalubi makunnin lantarki na kunna sannan na ganta a kwance gaban farar rigarta ya rine da JINI. Babu Alamar tsoro a fuskarta duk da cewa ta mutu hakan bai hana ZAINAB yi min murmushi ba......... . KIBIYAR AJALI-01 . NAZIR ADAM SALIH (Nas) . KASHI NA DAYA Lamarin yafaru ne tun yammacin wata lahadi misalin karfe hudu da rabi bazan taba mantawa da lokacin ba domin kuwa lokacine da ya zamo wani bangare na tarihin rayuwata ina zaune a kofar gidan mu sai ga wani yaro fari siriri yana sanye da fararan kaya da bakar hula hana sallah a kansa yaron bai wuce shekaru goma sha uku aduniya ba ya jingine kekensa a jikin bangon gidanmu . "Ina wuni yaron yace dani lafiya lau na amsa wai kaine Fadil yaron ya tambaye ni eh nine na amsa ya miko min wata farar jakar wasika an zaneta da furanni tun kafin na buda na gane daga inda wasikar ta fito wannan itace wasika ta uku dana karba a cikin kwanaki biyu hakika ina tausayin rayuwar amina sai yanzu ne nagane irin son da take min amma ni haryanzu allah baisa min kaunarta ba ko kadan kada kayi zaton wai ko don ba ta da kyau ne shine yasa bana kaunarta ba kada kayi mamaki idan nace ma ina kyautata zaton tana daya daga cikin matan da zasu cinye gasar sarauniyar kyau da za'ayi anan kano. . Nafito da wasikar na karanta sannan nace da yaron kaje kace mata ina zuwa yanzu yace toh sannan ya hau kekensa yatafi tausayin rayuwarta ne ya sake dawo min amma badon inasonta ba kyakkyawar tafiyar minti ashirin takai ni unguwar gidan KANAL A. MUKHTAR yana daya daga cikin manyan gidajen dake sultan road kanal mukhtar tsohon soja ne wanda yayi ritaya shekaru goma da suka wuce ganin wasu sojoji biyar masu jajayen ido da tarin gashin baki shiyasa ni na kafe babur dina tun kafin na karaso kofar gidan na tako a kasa har na karaso kofar gidan na tsaya cak ina shawarar abinda zanyi shin sallama zanyiwa sojojin ko kuwa sannunku zance musu? Sannan kamar daga sama sai na ji anyi kiran sunana tana zaune akan wata farfanda nayi mamakin yanda akayui ban ganeta ba. . Sannu da zuwa tace dani naji ance gobe zaka tafi kaduna hutu shine nace bari na kirawo ka muyi sallama tausayinta yakara kamani akaro na farko kenan tun lokacin da muka fara haduwa da AMINA a wajen wani fati da akayi a unguwarmu sainaji ta fara karya zuciyata... ** Kina nufin kice wani yazo nema na? Na tambayi yarinyar adaidai lokacin da zan bude kofar dakina dake DABA OTAL kaduna kwanana biyu a cikinta kuma naji dadin zama babbar otel ce mai dauke da kayan jin dadin rayuwa ana jita jitar cewa duk najeriya babu irinta in ka dauke guda daya wacce basai na fada ma ba. Ke menene sunanki? Na tambayi yarinyar dake gabana tayi murmushi sannan tace sunana ZAINAB kuma ni ma'aikaciya ce anan otel din sannan ta sake yin murmushi na dubeta sannan nace don Allah kinsan abinda zakiyi? Tace a'a idan ya dawo kice masa yabar miki sunansa ko kuma ya jirani har na dawo. kamar yaushe zaka dawo in yazo na fada masa ? Zan dawo kamar kamar bakwai da rabi na dare. Nagode kinji ko don Allah menene sunanki? Kin fada min amma na manta na tambayeta, Sunana Zainab idan kuma kana son ganina zaka iya zuwa hawan benen nan na uku ofis mai lamba(6). Nagode nace da ita sannan ta tafi tabarni nan cike da mamakin wannan bako nawa wanda bana tsammaninsa yanzu haka ma bani Fadil din yake nema ba nace cikin zuciyata sannan na fitar da maganar daga raina na tura kofar dakin na shiga. . Sanyi ya bugi fuskata a yayin dana ga dakin babban daki ne wanda ke dauke da gado daya, kujeru biyar da kuma tebur daya mai dauke da wata karamar bidiyo da talabijin mai fadin fuskar da ta wuce fadin bangon sinima ba zaka iya kiran dakin aljannar duniya ko kuma in ce aljannar najeriya saboda tsabar tsaruwarsa nidai awajen hudu na kira shi. Duk zuwan bakon mutumin nan bai dameni ba har yanzu ni ina murna da hutuna dana fara anan jihar kaduna kullum fatana shine idan nagama makarantar gaba da firamare wato sakandire na tafi kaduna na kashe lokacin jiran da zamuyi na fitowar sakamakon jarrabawar mu. Yayana wanda nake wajensa acan jihar kano baiso na tafi hutun ba saboda babu wanda na sani a kaduna amma dana takura masa sai ya amince yakuma kama min wannan daki dakuma wa'adin wata daya zanyi bayan wata guda yace kada na kara koda kwana daya na koma gida. Na zage labulen tagogin biyu dake dakin sannan na cire rigata da wandona na daura kyallen tsane ruwa na shiga wanka bayan na fito na dubi agogo naga karfe hudu saura minti biyu sannan na buda akwatina na dauko wata riga baka marar nauyi mai budadden hannu na kuma dauko wani farin wando shima nasa na tsefe kaina na daura agogo na kuma na kwama takalmina na shiga duba littafina dana rubuta. Bayan lokaci kankani na gano inda na ajiye shi shida alkamin rubutuna sannan na fito na rufe dakin har zan tafi saina dawo da baya na sake budewa na shiga domin na tabbatarwa da hancina abunda ya shaka adaidai lokacin danake kokarin rufe kofar na mika kaina ina daga waje na shaki iskar dakin nidai nasan bansa turare ba nakumayi mamakin yadda akayi harna shigo nayi wanka banji kanshi ba saida nazo fita. Hakika wani yashigo dakin dazun bayan fitata na tabbatar da hakan ta hanyar kula da tsarin inda takalmana suke daga bangaren arewa amma yanzu sun dawo bangaren kudu Na tabbatar da hakan ne ta hanyar kula da tsarin inda takalmana suke daga bangaren arewa amma yanzu sund awo bangaren kudu na dakin akwatin kayana ma ba'a barshi a baya ba. . ******* ******* ******* ******* ****** . Idan ka dauke wajen danake zaune ko ina cikin lambun shakatawar otal din cike yake da mutane makil wadansu na wanka wasu kuma suna wasa da jajayen ya'yansu a bakin ruwa wannan shine daya daga cikin abinda yasa jama'a suke zaune a otal din na dauki birona da littafina na dora akan tebur sannan na jingina da kujerar na fara tunanin abinda zan fara rubutawa. . Idan baka sani ba yakamata ka sani nazo hutu kaduna ne da niyyar rubuta littafi akan soyayya kamar yadda abokaina keyi anan kanon dabo a duk lokacin danayi niyyar fara rubutawa sai naji duk na rasa ta inda zan fara wannan shine babban abinda yasa na nacewa yayana yabarni nazo kaduna hutu domin idan ina ni kadan zanfi bada kwazo da nutsuwa. Don haka ma danazo wajen shakatawar otel din sai na zabi bangaren arewa da lambun dana jikin katanga wacce zaiyi wuya ka gane cewa katangar bulo ce saboda korayen furannin da ganyayyakin fulawowin da suka yi yado akanta gaba da baya abin ba'a cewa kome domin duk inda ka taka a otel din kore shar yake da ciyawar nan mai kama da kilishi. Saura kadan biron dake hannuna ya kwace ya fado kasa a sakamakon firgitar danayi na tabbatar da cewa lokacin da na zauna babu kowa a kusa dani sai wata bishiya taku biyu daga inda nake to amma yanzu juyawar da zanyi sai naga wata yarinya tana zaune akan wata kujera mai kyaun gani da dukkan alamu ita tazo da kayarta . Sannunka tace dani cikin wata murya lallausa muryar da bazan taba mantawa da ita ba har abada. zuciyata da kwakwalwa ba zasu iya jure irin kyawun wannan yarinya ba. Yawwa sannunki dai kyakkyawa na amsa mata WANNAN SHINE FARKON RIKICIN sa'adda na juya na tafi daga wajen da duk wannan bai faru a kaina ba. Na mike tsaye yayinda tabar kujerar da take zaune ta matso kusa dani sannan sai tattausan lebenta ya fadada izuwa murmushi fuskarta na kyalkyali hakoranta kamar nono tana sanye da riga suwaita baka da kuma jan wando jeans da bakin takalmi kambos ta daure mararta da wani faffadan belt mai kyalkyali ga sarka mai kamar walkiya nata kyalkyali a wuyan. Sai bayan datayi murmushi ne na kula da wani digon baki a kumatunta na hagu wanda shi dai ba digashi akai ba halitta ce kawai. . Yan mata da dama suna da kyawawan fuskoki da kuma halittar da zaka dade kana sha'awarta ka kalle su sama da kasa ka gane wa kanka cewa lalle wadannan sune irin matan da duk wani saurayi ke burin mallaka sannan da zarar kun rabu saika manta dasu da dai kamar ba'a halicce su ba amma wannan yarinyar bazaka taba mantawa da ita ba kada ka tambayeni me yasa akwai wani abu dake tattare da kyawunta ita dai daban ce daga cikin mata kamar yadda kalanzir yake daban acikin ruwa . Kina bukatar taimako ne? Na tambaya cikin muryar dana kasa ganewa ko tawa ce ko kuma ta wani. Ta girgiza kai sannan tace A'a daman dai naga kai kadai ne shine nace bari nazo na debe maka kewa. Kasan nima ban cika son surutu da hayaniyar jama'a ba. Toh ai shikenan nace cikin rwar jiki ta janyo kujerarta tazo gaban tebur dina ta zauna a duk lokacin data kalleni sainaji kamar na dauketa na hadiye don kauna na tabbata yanzu na kamu da ciwon SO wanda bansan maganinsa in dai har yarinyar nan bataamince min ba. Menene sunanki Yan Mata ? Na tambaya sunana BADURA tace dani cikin lafazi tattausa hutu kake anan ne naga alamar kamar kai bako ne? Kwarai kuwa nace da ita yau kwanana biyu kawai anan kuma sunana FADIL Badura ta kalleni na kalleta mukayi shiru na dan tsawon lokaci wajen yayi tsit na dan tsawon lokaci wajen yayi domin alokacin mutane sun fara watsewa ta dan duba agogo ta mike tsaye zan tafi Fadil sai kuma yaushe kenan . Haba Badura tun yanzu nace, ki bari mana shida ta karasa yayinda nake bin ta da kallo akwai abunda zanyi ne gobe ma ranace zamu iya haduwa kamar wannan lokacin sannan nan da nan ta dafa kafaduna guda biyu ta kura min ido nasan ta gane na kamu ciwon sonta ta kuma san nima nasan ta kamu da ciwon SONA. . Fadil! Tace dani cikin rarraunar murya kamar zatayi kuka kar kaji komai don Allah idan na bata ma rai kayi hakuri zan dawo gobe kamar yau kaine mutum na farko da na fara jin son sa acikin zuciyata kafin na farga har ta saki kafaduna ta fada motarta taja kamar hayaki ta nufi kofar lambun. . ****** ****** ****** ******* ******* . Karfe uku tayi hudu tayi banga alamar Badura ba na tashi na fara hange hange amma ban hango kome ba sai masu hannu da shuni ne suda ya'yansu keta shagali a bakin ruwa tun misalin karfe biyu na sauko daga dakina zuwa lambun na zauna zaman jira amma har yanzu shiru kakeji biyar tayi shida tayi sannan na fitar da rai na tabbata yau ko bacci bazan iya ba, haka na kwana ina tunani jiya ga dukkan alamu yau ma haka zan kwana na mike na nufo kofar lambun ina dube dube shiru kamar na tsaya na sake dubawa sai dai na hakura na hau sama na shiga dakina na bude tagogin dakin sannan na kwanta amma barci ya kasa daukata Na duba agogona naga karfe goma saura kwata hakika tunani da begen badura sun mamaye duk wani sashe na zuciyata abin dayafi tsoratar dani ma shine yadda akayi har na kamu da ciwon sonta cikin dan kankanin lokaci a yanzu kam babu wani abu da bazan iya ba wajen ganin na mallaki abar begena badura kada kaga laifina abin da ido ya gani zuciya ta amince masa dole ne rai ya so shi. Na juya da niyyar na gyara kwanciyata sai naji kamar ana kwankwasa kofar dakin na yunkura na tashi tsaye cikin mamakin ina tunanin ko zainab ce ta kawo min abinci to amma kuma ai na sanar da ita cewa yau a waje zanci abinci na dai bude kofar. A tsaye a bakin kofar fuskarta tana walwali kamar madubi tana sanye da riga ruwan hoda da wondanta akwati mai taya baka a hannunta kanta babu kallabi BADURA CE. Cikin mamaki da kaduwa na matsa ta shige cikin dakin batareda ta ko dubeni ba abin dana tabbatarwa kaina shine wannan zuwa nata bana kwanciyar hankali bane na kara tabbatarwa da kaina haka alokacin dana kunna lantarkin dake dakin haske ya gauraye ko ina sainaga fararen idanuwanta sunyi jajur kamar ta wuni tana kuka ko kuma bata sami cikakken barci ba . Me yafaru badura nayita jiranki bakizo ba? Na tambaya lafiya kuma na ganki haka cikin wannan lokacin? Tayi ajiyar zuciya sannan ta dago kai muka hada ido Wallahi Fadil wani abune yake bani tsoro tace dani tun jiya da safe wani mutum yaketa bina abaya abaya duk inda nayi sai ya bini da farko nayi kokarin bace masa amma na kasa sai na hakura na kyale shi na dauka irin samarin nan ne masu bin yanmata agindi toh sai kuma jiya muna zaune a lambun nan naganshi yanata kallon yana muzurai nayi niyyar na fada maka sai tsoro ya hanani shine nace maka zan tafi kaga idan natafi sai ya bini domin bana son abinda zai tayar maka da hankali 'kamar yaya yake? Na tambaya cikin mamaki. Baki ne dogo kakkaura yana sanye da koriyar riga da farin wando' tsoro ya kamani cikina ya kada tun sa'ar data fara bani labarin sai yanzu ne na gane abinda take nufi mutumin kenan dayazo nemana bana nan shine yake bin Badura . Bayan wannan fa? Shi ya hanaki zuwa wajena? Na tambaya 'A'a ba hanani yayi ba nice dai na hana kaina domin bana so in jefaka a cikin bala'i gara in wani abu ne ma ya sameni ni kadai na tashi na matsa kusa da ita na kura mata ido. Kada kice haka nace da ita ni masoyinki ne kifada min duk abin dake damunki gobe zanyi maganinsa abinda nake fada nima kaina ya bani mamaki domin maganar da tayi ta dada tabbatar min da kaunar da take min. Jiya da daddare..... Taci gaba da cewa naganshi yazo hotel din nan a wata mota kirar Alfa Romiyo amma bai shigo ciki ba daga waje ya aje motar ya shigo da kafa danaga haka sainayi sauri na rufe dakina ina lekensa ta tagar dakina. Yana nan yana ta dube dube har sha dayan dare danaga haka saina kulle tagar dakina nayi kwance toh sai kuma can dare naji ana taba min kofar daki amma idan na leka saina rasa kowa da haka dai har gari ya waye da yamma tayi yau kenan nayi shiri domin na same ka a lambu sai na ganshi a hawa na daya benen nan yana jira na nafito don haka sainayi zamana har dare yayi ban fito ba shine yasa kaga banzo wajenka ba . A wanne daki kike? Na tambayeta daki mai lamba uku 3 nayi mamaki don jin cewa dakin a kusa da nawa yake amma ban sani ba daki mai lamba hudu shine nawa ta dago kai muka hada ido sai tace dani ina fata ban takura maka ba don nazo nayi ma bayanin abun da yafaru kaga jiya wallahi banyi barci ba tsoro kuma yau ma na kwanta kenan sainaji an fara gugar kofar dakina shine na ganka kana bude kofar dakinka shine nace bari nazo na kwana anan da safe saina tafi. . Ki tafi ina? Na tambayeta kano mana ai canne garinmu daman a kano kike nace da ita da sauri Eh mana zakayi mamakin yadda akayi ban tambayi inda take zaune ba a kano bankuma tambayeta abinda ya kawota kaduna bahakika al'amarin ne ya rikitar dani yakuma bani tsoro don hakan saina kyaleta ban kara tambayarta komai ba. Saiki kwanta da safe ma tattauna akan maganar nace da ita ban kuma ce mata nima dan kano ne ba . Ahaka muka kwanta tana gefena daga bangon dakin nikuma ina kwance a gabanta wato a bakin gadon karfe hudu da rabi na dare agogon bango ya buga otel din tayi tsit bakajin komai sai saurar ruwan sama ajikin tagogin dakin kamar da bakin kwarya idona biyu tun karfe goma sha biyu sai yanzu ne naji idona ya fara lumshewa na juya na zubawa abar kaunata ido ina kallon kyakkyawar fuskarta har dai barci ya daukeni. . Karar Abinda ban taba zato ba ta ratsa kwakwalwata na tashi firgigit! Na miko kafata kasa sannan na tashi tsaye barcin ya fice daga idona nan da nan kamar daman idona biyu da farko na dauka karar tsawa ce amma daga baya saina kasa gaskata hakan na tabbata karar BINDIGA naji nan da nan na nufi kofar daki da gudu na bude na leka a daidai lokacin danaga wani kokuma ince wata ta nufi kasan benen da gudu sanye da bakaken kaya zaiyi wuya ka gane mace ko namiji ne saboda rashin isashen hasken dake kwararon benen saida me gudun yazo shan kwanar da zata kai shi hawa na karshe.... Saida me gudun yazo shan kwanar da zata kai shi hawa na karshene na gane macece na tabbata ko wacece bata so a ganeta a matsayin mace . Cikin kaduwa na juya zan koma dakina sai naga dakin badura mai lamba 3 a bude banyi wata wata ba na kutsa kai cikin dakin na lalubi makunnar lantarkin na kunna dakin ya gauraye da haske sannan naganta a kwance akan gado gaban farar rigarta ya rine jawur da JINI tiriri na tashi daga ramin da harsashin bindigar yayi a kirjinta. Babu alamar tsoro a fuskarta duk da cewa ta riga ta MUTU hakan bai hana Zainab murmushin karshe ba. ** Mintuna biyu suka shude ina tsaye akan gawar zainab bana ko motsi kamar an dasani rigata ta jike shakaf da gumi duk da yake ana san danyi saboda ruwan da ake ta ketawa kamar da bakin kwarya A halin yanzu ruwan ya dan tsagaita nayi zaton karar bindigar zai tashi jama'ar dake kan benen otel din amma koda na mutum daya baizo ba na dan bude kofar dakin na leka sosai ko zan ga motsi amma banji motsin komai ba sannan na juya nayiwa zainab kallon karshe na fice daga dakin nakuma maida kofar na rufe nasa hannu zan tura kofar dakin kenan sainaji wata murya irin wacce zakaji idan kaje makabarta da ake fatalwa tace min . Barka da asuba nayi firgigit na jya a rude abinda idona ya gane min ya ban haushi dakuma dariya wani tsoho ne fari mai motsatstsiyar fuska kamar matsatstsen lemon tsami yana sanye da shudayen kaya a kirjin rigar an rubuta cikin harshen turanci (DURBA HOTEL) wato sunan hotel din da nake ciki kenan barka ka dai na amsa masa cikin wata murya da batafi tasa dadi ba girarsa mai kama da ta biri ta daga sama ayayinda yaga fuskata ta hadu da gumi Lafiya dai malam kobakajin dadi ne ya tambaya nayi murmushin da bai kai idanuna ba nace dashi wallahi wani abinci jiya kuka bamu a otel dinnan wanda ya rikita min ciki shine yake murda min ciki yanzu ma naje wajen makwabciyata ce ko tanada magani ta taimaka min dan yi shiru sannan ya kalle ni yace Allah sawwake nace amin . Har zan shige dakina sainaji yace zainab ta tashi kuwa ko har yanzu bacci take? Saura kadan in kifa masa mari fuskata ta chanza kala jikina ya dau rawa lallai in tsohon nan yasan zainab tana cikin dakin nan to kashina ya bushe domin babu abunda zai hana a dora min laifin Kisanta Malam kaga karka bata min lokaci nace dashi cikin fushi ni bansan wata zainab ba Badura dai itace mai dakin ita kadai kuma nagani aciki in babu sauran wani abu kuma ya kamata ka kyaleni da shegiyar tambayarka kaje kayi aikin da aka saka ka Allah baka hakuri mallam motsatstsan tsohon yace dani daman abinda yasa na tambaya jiyane kafin mu tashi daga aiki tace min idan aiki yayi mata yawa a daki mai lamba 3 zata kwana wai saboda idan dare yayi ba'a samun motar zuwa unguwarsu. . Jikina ya sake daukar rawa kamar anayi min kidan gangi awace unguwa take? Na tambaya A Unguwar shanu take yace dani menene aikinta a otel dinnan? Aikinta shine bada dakunan kwana dakuma kula da wadanda ke ciki sai anjima kaji ko nace dashi ba tare dana jira wata amsa ba sai kawai na shige daki na janyo kofar na rufe sannan nasa sakata . Badura na zaune akan gadonta tana shafa mai koda ganin fuskata saita tashi tsaye ta dafa kirji lafiya fadil na ganka haka duk ka canja nan da nan ? Kada iya kayan da kika san zaiyi miki amfani kisa cikin jaka nace da ita batare da na kalleta ba domin nasan kallonta alokacin zai iya kara tsoratar da ita nayi tsammanin zata tambaye ni wani abu amma saita bani mamaki nan da nan naga ta fara hada kayanta kamar yanda na umarceta na wuceta nabarta anan tana ta hada kayanta ni kuma na shige bandaki na duba kaina sama da kasa acikin madubin dake like a dakin abindana gani yaban tsoro fuskata tayi sharkaf da gumi kamar wanda yaga fatalwa karkayi mamaki dajin haka domin kuwa wannan shine karo na farko dana taba ganin gawa kiri kiri kasan kuwa ko jana'iza naje a lullube nake ganinta na dauke kaina daga madubin sannan naje gindin famfo na shekawa kaina ruwa ahalin yanzu bana bukatar wanka itama badura rashin sanin abinda ya faru ne yabata damar wanka shin data san da gawa a dakinta me kake jin zai faru? Na shashshare ruwan dake kaina da wani kyallee sannan na sake duban kaina ajikin madubin abinda nagani yanzu yafi na da kyaun kallo da kadan a kalla dai bazan tsorata yara ba na bude kofar bandakin na shigo dakin tana zaune akan kujera tana kuka menene kuma ya same ki na tambaya tayi ajiyar zuciya sannan ta dago kai muka hada ido da ita sannan tace fadil don Allah in laifi nayi maka saika fada min bai kamata ace kana korata don kawai kaga ina SONKA. . Banga laifinta ba domin kuwa ko kaine ka kwana dakin wani yazo yace maka ka hada kayanka batareda wani karin bayani ba dole ranka ya baci saidai kuma shirin shi yafi amfani ahalin yanzu ba sai na gaya ma ba halin mata ina fada mata zata rikice har tasa shirin da nake a halin yanzu ya ruguje ya zama dole na bar otel din kafin a sami zainab a mace. Kada ki damu masoyiyata nace da ita cikin kalami mai dadi idan munje gidan zan fada miki abinda ya faru sannan naci gaba da nade kayana tana zaune batace dani Uffan ba Na hada kayana masu amfani a jaka daya sannan na zuge nayi shirin gudu kenan ko ban fada maka ba zaka fahimci bala'in dana fada a halin yanzu gawar ma'aikaciyar hotel din dake ciki dakin masoyiyata kanajin idan aka same ta matacciya wa za'a fara nadewa? Masoyiyata badura kasan kuma ko ban fada maka ba bazan taba barin wannan ta faru a kanta ba sannan abinda ya dada dagula al'amarin shine idan yan sanda suka fara bincike matsatstsen tsohon nan zaice

Chapter 1 of 9