Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
yaki da mukayi har da kake cewa yanzu muka fara yaki dashi alhalin kai bakaje filin yakin ba?" Koda jin wannnan tambaya sai sarki Barham yayi murmushi yace, ai faduwar babbar giwa ba wasa bace, inda sarki Daryan ya fadi to da ajikinama sai naji alama, Baya ga haka bisa binciken da nayi sarki Daryan ba zai mutu ba a wannnan yaki domin akwai wadansu abubuwa da aka kaddara masa yinsu kafin ajalinsa kuma har yanzu bai gabatar dasu ba, Koda Kalmaru yaji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi kuma hankalinsa ya tashi ya dubi sarki Barham cikin alamun damuwa yace, ya shugabana to ni kuma me kasani akaina bisa bincikenka? Sarki Barham yayi murmushi yace Lokacin da ya dace kasan amsar wannan tambaya taka bai yi ba saboda haka ka kara sauraro. Ya kamata ace kun tambayeni ko akwai matsala anan gida bayan Tafiyarku Koda jin wannnan batu sai gimbiya lazima ta matso gaban sarki tace ai tabbas mun san cewa akwai wani abun da ya faru amma zaifi kyau yanxu mu karasa gida, inyaso bayan mun huta sai mu zauna sossai a tattauna, Da jin haka sai sarki Barham yayi murmushi yace da kyau 'yata inda kike matukar birgeni kenan kina da tunanin ya kamata, Nan sarki ya juya ya kama dokinsa ya hau,shima Kalmaru sai mayarda takobin daraja cikin rigarsa ya kama dokinsa ya haye itama lazima ta hau nata dokin sannnan aka dunguma gaba daya a juya aka koma cikin birnin zamar. Ana isa cikin gari sai dakaru da Kalmaru suka raka sarki har kofar gidan sarauta, sannnan suka yi masa sallama kowannensu ya nufi gidansu domin iyalinsa su ganshi, Da yawa daga cikin iyalan dakarun da suka tafi wannan yaki sun zo sunyi dafifi a kofar gidan sarautar tunda labarin yazo cewar gasu nan sun dawo suna daf da karasowa saboda tsananin damuwa da kaguwar son tabbatar da sun rayu ko sun mutu a can filin daga amma da dakarun suka gama isowa gaba dayansu duk maccen da bata ga mijinta ba ko 'yan uwan da basu ga dan uwansu ba sai kaga sun kama kuka, Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda wadanan iyalai ke kuka saboda rashin da sukayi dole ne ya tausaya musu. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 5 Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda wadanan iyalai ke kuka saboda rashin da sukayi dole ne ya tausaya musu. Shi dai jarumi Kalmaru ana isowa kofar gidan sarautar bayan an yiwa sarki sallama bai tsaya duba mahaifinsa Ridwan ba da kuma baiwar mahaifinsa wacce ya dauketa a matsayin uwa saboda dama a ranar da sukayi bankwana Ridwan ya dubeshi yace ya kai dana na yarda da kai dari bisa dari kuma naji a jikina cewar duk irin tsananin da xaka fuskanta a wannan yaki sai ka dawo gida a raye don haka duk ranar da kuka dawo bazamu fito ba taryar ka ba sai dai mu jiraka a gida, A Lokacin da Kalmaru yaji wannan batu daga bakin mahaifinsa sai yayi murmushi ya rungumeshi a kirjinsa yace,ya kai abbana nima nayi maka alkawarin cewar komai rintsi da tsanani zan dawo gida a raye ko don na cika maka burinka nason ganin karshen sarki saumir sai dai idan bai fito wannan yaki ba, Koda jin haka sai Ridwan ya kamu da tsananin farin ciki sannnan yasa masa albarka suka yi bankwana, Lokacin da jarumi Kalmaru ya baro kofar fada ya tunkari gida cikin murna da dokin ya isa gidan domin ya sadu da iyayensa, Sai kawai yaji tunanin gimbiya lazima ya fado masa, take ya rinka ganin fuskarta a Lokacin da take yi masa murmushi sannnan kuma yayi ta tuno da duk abubuwan da suka faru tsakaninnsu da ita tun daga ranar da aka tafi wannan yaki kawo Izuwa dawowarsu kuma yana tuna cewa in ba don ita da tuni yanzu ya dade da shekawa barzahu, Lallai tana binsa bashi a rayuwa, bashin da bai san da abinda zai biyata shi ba, haka kuma sai ya tsinci kansa yana mai mamakin irin jarumtakarta wacce har ta iya cetonsa daga shairin sarki Daryan A takaice dai shi yaji ya kamu da tsananin sonta a cikin zuciyarsa amma sai ya kudiri niya cewa zai danne soyayyarsa a cikin ransa muddin ba ita ce ta nuna masa tana sonsa, haka dai Kalmaru yaci gaba da wannnan zancen zuci har ya iso gida, A kofar gidan ya iske mahaifinsa da mahaifiyar tasa a tsaye sun kura masa idanu sunata murmushi. Koda Kalmaru ya hangosu sai ya kasa hakurin ya karaso akan doki don haka sai ya duro kasa ya rugo da gudu Izuwa garesu suka rungumeshi duk su biyun kowannensu na kwalar farin ciki, tsawon yan dakiku suna kankame da juna sannnan suka janye yakinsu daga cikin nasa, Koda ta dubi jikin Kalmaru taga ya cika da tabon raunuka da dinki sai ta fashe da kuka saboda tausayinsa da kuma kaunarsa. Koda ganin haka sai Ridwan yayi murmushi ya kawar da ita gefe ya dubi Kalmaru yace kada ka damu da kukanta kasan su mata zuciyarsu tana da rauni amma ni ko kadan banji tausayinka bisa wadanan raunikan dake jikinka, Abinda nake bukata daga gareka kawai shine naji irin nasarar da ka samo a wannan yaki? " Koda jin wannnan tambaya sai Kalmaru ya kama yin murmushi yayi shiru kamar ba shida Abin fada, hakan ce tasa Ridwan yayi fushi ya daka masa tsawa yace idan baka da Abin fada ai sai kayi magana baka tsaya kana yi mini murmushin banza ba, Yana gama fadin Hakan sai ya juya ya nufi kofar gida zai shiga wani irin haske da yaga ya dallare bangon gidan nasa ne yasa ya juyo da sauri, Take yayi arba da takobin daraja a hannun Kalmaru har ya zarato daga cikin kufenta, nan take idanun Sarkin yaki Ridwan suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro, mamaki da kuma farin ciki ya rasa abinda zai yi tsakanin kuka da dariya, kawai sai ya rugo Izuwa kan Kalmaru ya rungumeshi yana ta sumbatar goshinsa, Daga can kuma sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna sossai a Lokacin da hawaye ya zubo masa ya dubi Kalmaru cikin nutsuwa yace ya kai dana hakika ka sami babbar nasara wacce ta gagareni tunda har ka iya kashe babban makiyina sarki saumir Tsananin farin ciki ne bisa wannan nasara taka ta haifar da zubar hawayena amma kuma na kamu da tsananin bakin ciki gamida tsananin tashin hankali bisa ganin wannan takobi a hannunka, Akan wane dalili ka dauko wannan takobi? " Kashe saumir kadai ya isheka abin alfahari ba sai ka dauko takobinsa ba domin wannan takobi tafi komai da kowa muhimmanci a wajen sarki Daryan ina mai tabbatar maka da cewa sarki Daryan zai ci gaba da farautar rayuwarka da lafiyarka kamar yadda mai fama da yunwa da kishirwa ke farautar abinci da ruwa. Babbar matsalar itace bazaka iya mayarda wannan takobi ba gareshi sai dai shi da kansa ya karbeta da hannunsa da karfin tsiya, zaman wannan takobi a hannunka ba karamar masifa ce ba gamida da babban tashin hankali kuma duk wanda ma ya rabeka yana cikin bala'i mara misaltuwa kuma a koyaushe zai iya rasa rayuwarsa da lafiyarsa. Koda Sarkin yaki Ridwan yazo nan a zancensa sai mamaki ya turnuke Kalmaru ya dubi Ridwan cikin alamun rashin fahimta yace saboda me kace ba zan iya mayar masa da takobinsa ba? " Ridwan yace haka sirrin takobin yake kuma duk iya kokarin da zaka yi wajen mayar da ita ba zaka iya ba don ko ka kaita can wajensa ba zai iya riketa ba sai ta dawo da kanta wajenka, Yanzu dai mu karasa cikin gida domin ka zauna ka huta kuma kaci abinci, ba tare da gardamar komai ba kuwa Kalmaru ya bisu Izuwa cikin gidan. Bayan Kalmaru ya huta kuma yaci abinci sai Ridwan ya shigo cikin dakinsa inda ya iskeshi a kishingide yana kallon rufin dakin alamun tunani, koda ganin haka sai Ridwan ya zauna a kusa dashi sannnan ya dafashi, kamar wanda ya farka daga mafarki haka Kalmaru yayi firgigit ya mike zaune, Ridwan ya bushe da dariya yace kai dana hakika nasan cewa ruwa baya tsami banza, Lallai tunanin da kake yi yanzu na musamman ne, Ba tunani ne na tashin hankali ba, tunani ne irin na ma'abota soyayya. Koda jin wannnan batu sai mamaki ya turnuke Kalmaru yace ya kai abbana shin kana samun labarai ne daga wajen aljanu?" Ridwan ya sake bushe da dariya yace A'a ko kadan bana samun labarai daga wajen aljanu tsabar sanin rayuwa ne da kuma lura da irin yanayin da na ganka a ciki saboda nima na taba shiga irin yanayin dana ganka yanzu, sa'adda na kamu dason mahaifiyarka. Koda yazo nan a zancensa sai nan da nan idanunsa suka kada suka ciko da kwalla don haka sai yayi sauri ya kau da kansa ga barin kallon Kalmaru yace bayan Tafiyarku yaki Izuwa dajin hajarul maut, waziri da Hamsaru da yunaru sunyi yunkurin juyin mulki,inba don cewa nayi zargin hakan zata iya faruwa bana sanar da sarki da tuni an cimu da yaki acikin gida. Koda jin wannnan batu sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubi Ridwan cikin mamaki da tsoro yace me yasa sarki bai bamu wannan labari ba dazu sa'adda muka iso?" Ridwan yayi murmushi yace ai saboda bayason hankalinku ya tashi ne kuma yasan cewa zaku sami labari a gari, Kalmaru yayi dogon ajiye numfashi sannnan yace ina fatan dai an kashe Hamsaru da waziri? " Ridwan ya girgiza kai yace ai sun sami nasarar guduwa,.hakan kuma shine babban tashin hankalinmu saboda nasan cewa babu inda zasu je face birnin sarki Daryan domin su sake hada kai dashi, Babbar illar itace sun san sirrin birnimu kuma kusan cewa da dan gari akan ci gari. Kalmaru ya gyada kai cikin alamun tsananin takaici sannnan yace haka ne amma babu komai zamu canja gaba dayan hanyoyin tsaron garin nan sannnan kuma ina son ka sani cewa dole ne mu kara matsanancin tsaro a kurkuku saboda a koyaushe su Hamsaru zasu iya kokarin kawo harin kubatar da mahaifinsa yunaru saboda shine kadai garkuwarmu a garesu. Ridwan yace kwarai kuwa dana hakika kana da basira sossai da hangen nesa shiyasa nake alfahari da kai, amma fa inaso ka sani cewa yanxu fa ba yunaru ne kadai abin farautarsu ba har da kaima. Kai ina tabbatar maka da cewa ma hankalin sarki Daryan sai yafi karkata a kanka tunda kana tare da takobinsa ta daraja sannnan kuma zuciyarsa tana ruruwa da wutar son daukar fansa a kanka bisa kashe mahaifinsa da kayi, Bisa wannan daliline nake son na baka wani taimako yanzu ina zuwa. Koda da gama fadin Hakan sai Ridwan ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin ya tafi Izuwa tasa turakar, jim kadan sai gashi ya dawo dauke da wata laya wacce akayita da jaf fata, nan take ya daurawa Kalmaru layar A wuyansa sannnan ya dubeshi cikin murmushi da murna yace daga yau komai gumu, duk wuya duk tsanani kada kayarda wannan laya ta fita daga wuyanka koda kuwa wanka zakayi har sai a ranar da ka tabbatar da cewa munga bayan makiyinmu, Ina mai tabbatar maka da cewa in dai kana tare da wannnan laya babu wani Aljani da ya isa ya dosheka da niyar cutar da kai kuma babu wani sihirin tsafi da zai iya tasiri a kanka. Koda jin wannnan batu sai Kalmaru ya kama layar daga jikin wuyansa ya kalleta da kyau kuma ya sumbaceta sannnan ya yunkura zai cireta daga wuyan nasa sai Ridwan yayi sauri ya dafe hannunsa yace saboda me kuma kake yunkurin cire ta alhalin na gayamaka muhimmancinta? " Cikin alamun matukar damuwa yace ya kai abbana nafison kai ka kasance tare da wannnan laya saboda rayuwarka tafi tawa muhimmanci a wajena, Lallai Banason na rasaka kamar yadda na rasa mahaifiyata ta ainihi. Koda jin wannnan batu sai Ridwan ya kamu da tsananin tausayin Kalmaru gamida tsananin kaunarsa, Nan take hawaye ya zubo masa sai suka rungume juna suna kuka har Izuwa tsawon yan dakiku sannnan Ridwan ya janye jikinsa daga cikin nasa ya fuskanceshi yace ya kai dana kada ka damu da rayuwata a kan taka saboda ni yanzu babu wani buri nawa a duniya wanda bai cika ba tunda naga girmanka kuma naga Lokacin da ka gajeni sannnan gashi ka kashe babban makiyina a duniya, kai kuwa yanzu ne ma ka taka matakin farko na rayuwarka ka tuna cewa idan fa baka rayu ba ka sami magaji shi kenan sarautar Sarkin yaki birnin nan ta bar gidanmu har abada. Ina mai tabbatar maka da cewa ni zan iya kare kaina daga dukkan shirin abokan gaba. Inda kuwa ba zan iya ba da ban kawo yanzu ba don da tuni sun gama dani,saboda haka sai ka kwantarda hankalinka, gobe da safe ka shirya mu tafi Izuwa gidan sarki zamuyi zama na musamman tare da manyan amintattun 'yan majalisarsa domin mu tattauna akan matakan da ya kamata mu dauka don kare birninmu daga shairin abokan gaba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 6 Ina mai tabbatar maka da cewa ni zan iya kare kaina daga dukkan shirin abokan gaba. Inda kuwa ba zan iya ba da ban kawo yanzu ba don da tuni sun gama dani,saboda haka sai ka kwantarda hankalinka, gobe da safe ka shirya mu tafi Izuwa gidan sarki zamuyi zama na musamman tare da manyan amintattun 'yan majalisarsa domin mu tattauna akan matakan da ya kamata mu dauka don kare birninmu daga shairin abokan gaba. A can birnin sarki Daryan kuwa bayan an gama bikin binne gawar sarki saumir da kamar bayan sa'a daya da rabi sai ga su Hamsaru tare da wazirin sarki Barham sun iso garin, ana ganinsu aka bude musu kofa suka shige ba tare da anyi musu wani bincike ba, Kai tsaye suka wuce har cikin fadar sarki Daryan anan ne suka tsaya har sai da aka je aka sanar da sarki isowarsu Nan da nan kuwa sai ga sarki Daryan ya fito, ko da yayi arba dasu Hamsaru a tsaye kawunansu a sunkuye kuma babu wani annuri a kan fuskokinsu sai jikinsa yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma domin ya fuskanci cewa lallai basu sami nasarar yiwa sarki Barham juyin mulki ba, Sarki Daryan ya dubi waziri da Hamsaru yayi musu nuni da inda zasu zauna sannnan shima yaje ya zauna akan karagarsa ta mulki, bayan sun zauna gaba daya ba tare da ya sake kallon fuskokinsu ba sai yace, wace irin matsala kuka fuskanta wacce ta hanaku samun nasara? " Koda jin wannnan tambaya sai Hamsaru yayi gyaran murya ya dubi sarki Daryan a cikin nutsuwa yace ya shugabana babban abinda ya kawo mana matsala shine sarki Barham yayi hasashen cewa zamu iya shirya masa wannnan juyin mulki don haka ashe bai saki jikinsa ba a wannnan dare dasu Kalmaru suka fito yaki saboda yasan cewa manyan zakwakuran dakarunsa basa nan, idan aka kawo masa harin sumame za'a iya gamawa dashi farat daya, bisa wannan daliline yayi bad kama a cikin dare ya fice daga cikin gidan sarautar kuma yaje ya hada runduna ta mayakannsa a wajen gidan sarautar, Sai bayan mun sami nasara shiga gidan sarautar mun kashe gaba dayan dakarun dake tsaron cikin gidan sannnan shi da rundunar tasa suka shigo suka ritsami, Mun fafata kazamin yaki dasu amma cikin kankanin lokaci suka kashe gaba dayan wadanan dakaru namu na sojan haya, Koda muka ga zamu hallaka idan muka ci gaba da yakin nida waziri sai muka tsalleke katangar gidan sarautar muka ruga da gudu dama can mun boye dawakanmu a wani waje, Muna zuwa wajen muka hau dawakanmu muka fice daga cikin birnin gaba daya muna masu tsala gudu amma duk da haka sai da dakaru yan kubau suka biyo mu suna ta harbo muna kibiyoyi da kyar da 'yan dabaru muka bace musu muka tsira da rayuwarmu, Sa'adda Hamsaru yazo nan a zancensa sai sarki Daryan yayi ajiyar zuciya sannnan cikin tsananin takaici sannnan ya dubi waziri da Hamsaru yace mu ma bamu sami nasara ba a yakin da muka gwabza dasu Kalmaru kuma a yakin nayi babban rashi guda biyu, Koda jin haka sai idanun su waziri suka zazzaro, zuciyoyinsu suka buga da karfi Cikin rawar murya waziri ya dubi sarki Daryan yace ya shugabana wadanne abubuwa kenan ka rasa?" Sarki Daryan ya sake yin ajiyar zuciya a karo na biyu yace na rasa takobin daraja koda jin haka sai mamaki da tsoro ya kara turnuke waziri da Hamsaru, Ba zato ba tsammani sai suka ga sarki Daryan ya bushe da mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma sai ya tsuke bakinsa ya turbune fuska yace hakama mun dauki abokan gabarmu da wasa shiyasa muka sami wannan matsala duk da cewa mun yi gagarumin tanadi akansu. Ko a mafarki ban taba zaton cewa zan kasa murkushe dakarun birninku ba a cikin kankanin lokaci, lallai an shammaceni. Inaso ku sani cewa yanxu ne zamu daura damarar yin yaki na biyu amma zamu fara ne da yakin sunkuru. Abu na farko tuni na tura da kwararrun 'yan leken asirin kasa domin su gano mini inda Kalmaru yake a cikin birninku da inda yake ajiye takobina ta daraja. Kuma zanyi amfani daku wajen cika wannan aiki, Burina shine nayi kicibis da Kalmaru a Lokacin da yake tare da takobin tawa na kashe shi na karbi abata, ku sani cewa muddin wannan takobi bata dawo hannuna ba banida sauran kwanciyar hankali kuma ba zamu taba samun nasarar yaki ba akan sarki Daryan. Inaso na kashe sarki Barham da tsohon Sarkin yakinku Ridwan wato mahaifin Kalmaru domin na dauki fansar ran mahaifina amma na sani cewa abune mai wuyar gaske yin hakan saboda dole ne yanzu a tsananta tsaro a birnin naku fiye da koyaushe amma duk da hakan bayan 'yan leken asirina sun kawo mini rohoto bisa binciken da na turasu suyi nima zanyi bad da kama nasan yadda nayi na shiga birnin don cika burina, masu iya magana sunce da dan gari akan ci gari. Don haka ina bukatar na zauna tare daku ku sanar da ni sirrin duk hanyoyin shiga birninku dana fitowa da kuma zuwa gidan su Kalmaru. Bayan duk wadanan abubuwa idan har ban cika burina akan Sarkinku da Kalmaru to ku sani cewa kuma baku da sauran amfani a wajena. Daga yanxu har Izuwa wannan Lokaci zan ci gaba da baku mafaka ku ci ku sha daga da dadan irin abinda nake ci kuma ga Kuyangi da barori da zasu debe muku kewa. Duk abinda kuke bukata najin dadin duniya ba zaku rasa ba. A karshe in dai babu nasara ku hada naku inaku kubar mini kasata inba haka ba kuwa zaku rasa rayuwarku domin babu abinda ganinku zai kara mini face tsananin bakin ciki da tsanarku. Yanxu babu abinda zamu gabatar har sai na sami rahoto daga bakin 'yan leken asirina. Koda gama wannan jawabi sai sarki Daryan ya mike tsaye ya bar su Hamsaru a tsaye suna masu binsa da kallo cikin kaduwa da mamaki har ya fice daga cikin fadar gaba daya. Nan dai suma suka fice daga cikin fadar suka tafi Izuwa masaukinsu. Wannan shine abinda ya faru tsakaninn su waziri da sarki Daryan bayan sun sami nasarar guduwa daga birnin zamar a Lokacin da suka yi yunkurin yin juyin mulki amma basu sami nasara ba. A can birnin zamar kuwa, Al'amarin da gimbiya lazima kuwa bayan ta shiga gida ta ci abinci sai ta shiga turakarta ta kwanta da nufin tayi bacci domin ta huce gajiyar tafiya da ta yaki amma sai idanunta suka soye taji ko kadan bata jin barcin. Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan kuma ya bata tsoro saboda bata taba tsintar kanta ba a cikin irin wannnan hali. Ashe ba wani abu bane ya hanata yin wannnan barci ba face tunanin jarumi Kalmaru. Duk sa'adda ta runtse idanunta sai ta rinka ganin fuskarsa, kai ko bude idanun nata ma tayi sai ta rinka ganinnsa yanayi mata gizo a cikin dakin yana baiyana yana bacewa. Sai da ta shafe sama da rabin sa'a a cikin wannan hali, Al'amarin da yasa taji cewar ba zata iya jure rashin ganinsa ba kenan amma kuma sai taga cewar ai ba kimarta bace yanzu ta tashi ta tafi gidansu Kalmaru. Idan ma taje din me zata ce ya kawota, haka kuma sai ta tuno da shawarar da sarki Barham ya bata cewar taja muruncinta da kimarta a wajen Kalmaru har sai idan ya baiyana mata tasa soyayyar karara a gareta sannnan itama ta baiyana mata tasa soyayyar tata. Koda ta tuno da wannnan batu sai hankalinta ya kara dugunzuma ainun fiye da koyaushe saboda ta fuskanci cewar rashin ganin Kalmaru zai iya haddasa mata wani ciwon. Da dai lazima ta ga bata da wata mafita a wannan Lokaci sai ta dauko wani maganin barci mai karfi wanda likitanta ya bata tasha da yawa fiye da yadda ma aka ka'idance mata. Ai kuwa tana gama shanye maganin ta baje akan gado sai barci ya saceta. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 7 Kuma na karshe Da dai lazima ta ga bata da wata mafita a wannan Lokaci sai ta dauko wani maganin barci mai karfi wanda likitanta ya bata tasha da yawa fiye da yadda ma aka ka'idance mata, Ai kuwa tana gama shanye maganin ta baje akan gado sai barci ya saceta, Al'amarin 'yan leken asirin da sarki Daryan ya aika Izuwa birnin warzas domin su hada kai da dakarunsu na can wato yan uwansu yan leken asiri sai da magarib ta kawo kai sannnan suka iso birnin na warzas. Birnin warzas ya kasance wata 'yar karamar kasa wacce gaba dayan jama'ar dake cikinsa ma basu wuce adadin miliyan daya da rabi ba. Sarkinsu kuwa wani mashahurin dan caca ne wanda babu abinda yakeso a rayuwarsa sama da kudi, indai zai samu kudi to fa babu abinda ba zai iya ba. Ya kware a kasuwanci, kai yana da yara ma wadanda suka kasance mashahuran barayi. Bisa wannan daliline yake da kwararrun dakarun 'yan leken asiri a birninsa wadanda suke gano masa inda za'a sami dukiya mai yawa. Shi dai wannan sarki na birnin warzas ana kiransa da suna murzalu. Duk irin tsananin son kudin sarki murzalu bai taba tunanin kai wargi ba a kasar zamar da birnin sarki Daryan ba don komai ba sai don kura ma ta san gidan mai babbar sanda. Shugaban dakarun leken asirin da aka tura birnin warzas sunansa zilla kuma ya kasance sadaukin gaske wanda bai san tsoro ba. Lokacin da sadauki zilla tare da yaransa mutum tara suka iso birnin warzas sai suka wuce kai tsaye Izuwa gidan sarki murzalu. Cikin tsananin farin ciki da mamaki sarki murzalu yayi musu tarba ta karamci yasa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka kimtsa. Bayan nan ne ya dubesu yace ya ku wadanan baki masu daraja wane sako kuka kawo mini daga wajen Sarkinku? " Koda jin wannnan tambaya sai zilla yayi gyaran murya sannnan ya janyo wata katuwar jaka da suka zo da ita ya budeta sai ga dinare acikinta mai yawan gaske. Koda ganin wadanan kudade sai sarki murzalu ya dimauce, idanunsa suka zazzaro, bai san sa'adda yawu ya dalalo daga bakinsa ba yace, wannan dukiyar fa ta mecece?" Ko da jin wannnan tambaya sai sadauki zilla yayi murmushi yace, wannan dukiya sarkina ne yace a kawo maka bisa wani gagarumin aiki da yake son ka aiwatar masa. Yayin da sarki murzalu yaji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi ya dubi zilla cikin alamun tsananin damuwa yace ina fatan dai Sarkinka baso yake na baku gudunmuwar dakarun yaki ba a kan yakin da kukeyi da sarki Barham? Koda jin wannnan tambaya sai zilla yayi murmushi yace, Ya shugabana ba haka bane, amma dai bukatar taso tayi kama da hakan. Abinda yake da bukata kawai shine ka zabo kwararrun 'yan leken asirinka ka hadasu damu domin mu shiga cikin birnin zamar saboda mu gano sirrin hanyoyin shiga birnin dana fita da kuma hanyoyin shiga gidan sarautar su da gidan tsohon Sarkin yakinsu domin a zuba ido a kan jarumi Kalmaru asan inda ya ajiye takobin daraja ta sarki Daryan. Koda sadauki zilla yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki murzalu ya dugunzuma ainun domin ga bikin zuwa ne amma babu zanin daurawa. Sarki murzalu ya dubi zilla kamar zaiyi kuka yace, ya kai wannan manzo kayi sani cewa wannan aiki da Sarkinku yake so nayi masa yanada matukar sauki a wajena tamkar cire sillin gashi daga cikin tandun mai amma kuma hadarinsa dai- dai yake da mutum ya tafi farautar ajalinsa. Abinda yasa na fadi haka kuwa shine idan har sarki Barham ya gano cewa akwai sa hannuna a cikin wannan aiki da za'a yi zaizo birnina ne a dare daya ya murkushemu. Koda zilla yaji wannan batu sai ya bushe dariya sannnan yace ai tuni sarkina yayi tunani akan hakan kuma ya samar da dabarar da zata kawar da faruwar hakan. Dabarar kuwa itace daga cikin zakwakuran mayakanka masu tsananin juriya da naci, kuma dole ne su shiga a cikin shiga da siffar da baza a taba gane cewa daga birninka suka fito ba. Mataki na karshe kuma shine dole ne. su tafi da shirin cewar da zarar sunga asirin su zai tonu a kamasu dole ne su kashe kansu kafin suje hannu bisa wannan daliline ma ya aiko maka da miliyoyin wannan dinare domin ka baiwa dakarun da zasu yi wannan aiki dukiya mai yawan gaske wacce zasu iya siyar da ransu akanta kuma duk da haka kaima sai ka sami rarar kudin masu yawan gaske. Sa'adda zilla yazo nan a zancensa sai sarki murzalu ya bushe da dariyar farin ciki ba don komai ba sai saboda yasan cewa tabbas ya sami mafita. Nan take ba tare da bata wani lokaci ba sarki murzalu ya tura aka kirawo masa wadansu zakwakuran dakarunsa mutum goma. Shida daga cikinsu wadansu kyawawan 'yan mata ne na gaban kwatance kuma sun kasance sadaukai, gwanayen iya yaki, juriyar wahala gamida nacin tsiya. Babbar cikinsu ana kiranta da suna Rizaila. Sauran mutum biyar din kuwa wadansu matasan samari ne majiya karfi masu takama da karfin damtse gamida jin samartaka. Lokacinda wadanan jarumai guda goma suka gabata gaban sarki murzalu sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa sannnan suka mike tsaye suka koma gefe daya suka jeru a layi. Zilla ya karewa dakarun kallo cikin alamun raini sannnan ya dubi sarki murzalu yace haba ranka ya dade yanzu har da mata zaka hadamu a cikin wannan aiki, lallai kuwa ashe ba zamu taba samun nasara ba. Koda jin wannnan batu sai sarki murzalu yayi murmushi sannnan ya dubi Rizaila yace yake Rizaila fito tsakiyar fada Nan ki tsaya,take Rizaila tabi umurni ta taho tsakiyar fadar ta tsaya tana mai gyaran tsayuwa. Sannnan ta zare takobinta sarki murzalu ya sake yin murmushi ya dubi zilla yace na yarda ka umurci gaba dayan yaranka su yaketa, idan suka sami nasara a kanta ka dauke jakar kudI nka ku tafi ka gayawa Sarkinka cewa na kasa. Koda jin wannnan batu sai sadauki zilla ya dubi sauran yaransa su duka suka bushe da dariya kuma yayi musu inkiya, take dakarun nasu su tara suka zare takubbansu suka ruga da gudu Izuwa kan Rizaila aka kacame da azababben yaki, nan fa gaba dayan jama'ar dake cikin fadar suka fara ganin al'ajabi dakarun guda tara suka yiwa Rizaila zobe suna kai mata sara da suka ta sama da kasa amma sai ta rinka kare duk hare haren nasu kuma tana maida martani. Ai kuwa sai gashi tana tarwatsasu da karfin tsiya da kuma tsagwaron iya yakinta, sai da aka shafe dakiku masu yawa a haka amma an rasa mutum daya

Chapter 9 of 10