Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
dakin nan da tagogin dake dakin yadda babu wanda zai ji abinda za mu tattauna. " Da jin haka sai kalmaru yaje ya rufe kofa da tagogi cikin sauri ya dawo suka zauna akan gefen gado tare da sarki suka fuskanci juna. Sarki Barham ya numfasa yace, ba zuwa nayi domin muyi shawara ba, zuwa nayi kawai na baka umurni domin tuni na gama yin shawarar Abinda zamuyi. A gobe zan aika takarda raddi ta yaki ga sarki Daryan na birnin musab. Ina so daga yanzu a cikin wannan dare ka fara shirye-shiryen yaki kuma duk yadda zakayi ka tabbatarda cewa ka kammala baiwa dakarunmu horon yakin da kake so su koya a cikin kwanaki bakwan nan kafin mu soma wannan yaki. Na yarda da hikimarka da basirarka kuma na ji a jikina cewa zaka iya jagorantar wannan yaki yadda za'a akai ga nasara. Da wannan furuci nake yi maka sallama sai gobe da safe zamu hadu a fada. Koda gama fadin hakan sai sarki Barham ya mike tsaye da sauri ya fice daga cikin dakin. Koda ganin haka sai shima kalmaru ya kama shiri ya sanya kayan yakinsa sannan ya kira daya daga cikin dakarun dake gadinsa a waje ya bashi umurnin ya kwashi dakaru talatin su bazama cikin gari su tattaro sauran dakarun yakin kasar a hallara gaba daya a cikin gidan sarauta in da ya basu horon yaki. Nan da nan kuwa wannan Badakare yaje ya cika umurni. Kamar yadda sarki Barham ya tsara haka al'amura suka kasance, wato kashe gari da safe sarki Barham yasa aka rubuta wasikar raddi ta yaki aka tashi manzo ya tafi da ita izuwa kasar sarki Daryan wato birnin musab. Al'amarin da yai matukar razana fadawa kenan kuma yai matukar basu mamaki domin basu taba tsammanin cewa sarki zai iya yin kundunbala yace zai tari sarki Daryan bn saumir ba da yaki, Tunda kura ma tasan gidan mai babbar sanda kuma ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin kaza. Shi kuwa sarkin yaki kalmaru tun a daren jiya yaci gaba da baiwa dakarun sababbin horo na dabarun yaki kamar yadda ya fara. Bayan sarki Barham ya gama taro da fadawansa a dakin ganawa Ya tabbatar musu da cewar yaki zai yi da sarki Daryan kuma ba gudu ba ja da baya sai gaba dayansu suka nuna rashin goyan bayansu akan yakin. Suka nuna tsananin tsoronsu saboda suna ganin cewa lallai idan akayi wannan yaki baza a sami nasara ba. Al'amarin da yai matukar fusata sarki kenan ya rufesu da fada kamar zai sa musu duka kuma ya gaya musu cewa duk wanda yake ganin zai iya tsayarda wannan yaki sai dai ya zare takobi ya fara yakin da shi na cikin gida. Yana gama fadin hakan ya fice daga cikin dakin ya shiga izuwa cikin gidan sarautarsa. Sarki Barham na shiga cikin turakarsa ya iske gimbiya lazima a zaune tana jiransa. Koda ganinta sai ya cika da tsananin mamaki ya dubeta yace, yake yata menene ya kawoki cikin turakata har kika dade haka kina jiran dawowata? Gimbiya lazima ta mike tseye ta tari sarki Barham ta kama hannayensa ta rike sannan ta kaishi izuwa kan wata kujera suka zauna tare tace, Ya kai Abbana na sani cewa babu wani gata wanda baka nuna mini ba a cikin wannan duniya tun daga ranar da mahaifiyata ta kawoni duniya kawo izuwa yanzu. Kuma ka sani cewa baka taba bani wani umurni ba na ketareshi dai-dai da dakika guda. A iya zamana da kai ban taba budar baki ba na nemi wata alfarma koda guda daya ce a wajenka, Haka ne?" to ka sani cewa a yau gani gareka ina mai neman wata alfarma guda daya rak a wajenka wadda nake son ka amince kayi min ita. Koda jin wannan batu sai sarki Barham ya sake kamuwa da tsananin mamaki, ya dubi gimbiya lazima yace, yake 'yata ke kuwa wacce irin alfarma ce haka kike son nayi miki?" Maza ki fadeta in dai ina da ikon yi miki ita sai nayi, Koda gaba dayan abinda na mallaka zai kare." Gimbiya lazima tayi ajiyar numfashi sannan tace, Ya kai Abbana ba wani abu nake bukata ba face ka yarje mini a tafi wannan yaki da za'a yi da birnin musab tare da ni, saboda inason naga irin jarumtakar sarkin yaki kalmaru a filin daga.ka sani cewa ban taba halarta yaki ba sai a cikin littatafan tarihi nake jin yanayin yaki, Lallai inason naga yadda maza suke faduwa kasa da idanuna, kuma inason naga yadda kaifi da tsini ke ratsa jikin bil'adama. Inason naga yadda jini yake fantsama yana malala akan doron kasa, Inason naga mazan kwarai wadanda komai gumu basu gudu a filin daga. Kuma basa baiwa abokan gaba baya. Inason nagani a zahiri abinda na karanta a littattafai domin na dawo gida na rubutasu da hannuna a cikin sabon kundin tarihin kasar nan. Koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai hankalin sarki Barham ya dugunzuma ainun ya dubeta alamun matukar tsoro da damuwa ya ce Haba yake 'yata hakika inda kinsan menene yaki da bazaki taba sha'awar ganinsa ba da idanunki ko fatan faruwarsa. Yaki bala'i ne wanda an san farkonsa amma ba asan karshensa ba. Yaki GUGUWAR ANNOBA ne mai share rayuka da dukiya. Yaki masifa ce mai ruda yaro da babba, mace da namiji , har yasa mutum ya gwammace rayuwar kabari akan ta doron kasa, Yaki jaza'i ne mai haddasa talauci, fatara,yunwa da kirshirwa wacce kesa zubar hawaye ba adadi. Yake 'yata kiyi sani cewa ni kaina gani nayi bamu da wata mafita wacce tafi ayi wannan yaki, Domin idan muka ki yinsa muka cika umurnin sarki Daryan tamkar mun mika kasar mune da jama'ar mu a hannun makiyanmu. Ina mai tabbatar miki da cewa wannan yaki da zamuje shine yaki mafi hadari da za'a yi a nahiyar nan wanda za'a yi asarar miliyoyin rayukan da ba'a taba yiba. Banida tabbacin zan iya kare kaina yayinda aka fara wannan yaki bare har na samu tabbacin kareki. Ina mai rokonki da ki janye wannan alfarma da kika nema a wajena. Da dai kije filin wannan yaki a kashe ki a can gwara ace an ci ni da yaki an shigo har cikin birnin nan an kamaki a matsayin baiwa. Ko ba komai nasan ba za'a kashe ki ba saboda kyawunki. Kinga kenan zaki tsira da rayuwarka ya zamana cewa zuri'ata bata gushe ba a doron kasa, tunda ke kadai kika rage mini a cikin wannan duniya " Sa'adda sarki Barham yazo nan a jawabinsa sai gimbiya lazima ta dubeshi cikin murmushi tace, Haba ya Abbana ai idan har kayi imani da abinda masana da matsafa suka fada akan bayyanar sabon sarkin yakinka ka tabbatarda cewa ba zan mutu ba a wannan yaki da za'a yi. Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai jikin sarki Barham yayi sanyi ya sunkui da kansa kasa yana tunani baice komai ba. Daga can sai ya dago kai ya dubeta yace, shikenan na Amince za'a tafi wannan yaki tare da ke!" * * * * Al'amarin waziri kuwa, lokacin da aka watse daga dakin taron bai zame a ko ina ba sai a kurkuku wajen Attajiri yunaru. Da zuwansa kofar dakin da aka kulle yunaru sai ya kori masu gadin dake bakin kofa dakin ya dubi yunaru yace, "Ai wannan mahaukacin sarkin namu yayi watsi da gargadin sarki Daryan ya zabi muyi yaki dashi. Koda jin wannan batu sai yunaru ya bushe da dariyar farinciki yace, Ai shi kenan lokacin cikar burin mu yazo. Hakika yau na gano cewa sarki Barham dakiki ne mai tosasshiyar kwakwalwa kuma ya cika mahaukaci. In banda mahaukaci waye zai yarda yayi yaki da sarki Daryan, mutumin da yake da mayaka sama da guda miliyan dari bakwai? "kuma zakwakurai balle shi kadai ma fasa taro ne. Ina mai yi maka albishir cewa da zarar sarki Daryan ya kai sarki Barham kasa kaine sarkin mu, sai ka baiwa dana takobinsa ta zinare. Gimbiya lazima kuwa da karfin tsiya zamu aurar da ita ga Hamsaru. Inason ka sa a kamo dan uwana Ridwan a kwantar dashi a kasa a daure da hannuna zanyi masa yankan rago domin na gusar da kishirwar kiyayyar dana ke yi masa ta tsawon shekara da shekaru." SHIN ATTAJIRI YUNARU DA WAZIRI ZASU SAMI NASARAR CIKA WADANNAN BURIKA NASU?" WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'A YI TSAKANIN BIRNIN MUSAB NA SARKI DARYAN DA BIRNIN ZAMAR NA SARKI BARHAM? " SHIN SOYAYYA ZATA KULLU KUWA TSANANIN SARKIN YAKI KALMARU DA GIMBIYA LAZIMA? " YAYA KARSHEN LABARIN 'YA'YAN KALMARU ZAI KASANCE TUNDA AN FARA WANNAN LITTAFI NE DA LABARINSU SA'ADDA 'YAN HARIN SUMAME SUKA KAWO FARMAKI KAUYEN DA SU KALMARU SUKE?" SHIN SHUBAIRU ZAI MUTU NE KO KUWA ZAI ISA GIDA YA RISKI DAN UWANSA HUZAIRU? " Mu hadu a Littafin MAZA SUN FADI kashi na (3) don jin cigaban wannan labari. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 1 Lokacin da attajiri yunaru yaji wannan batu na waziri sai ya bushe da dariya yayi ta kyalkyatawa kamar ba zai daina ba. Shima waziri yana tayashi da dariyar lokaci guda kuma sai duk su biyun suka tsuke bakinsu sukayi shiru suna masu kurawa juna idanu sannan waziri yace, ai kamar yadda kake da wannan buri Nason hallaka dan uwanka sarkin yaki kalmaru haka nima nake da burin yanka dan uwana sarki Barham saboda tun muna yara nake kunshe da bakin cikin yadda sarauta kasar nan ta kufce daga gidanmu ta koma gidansu alhalin fiye da shekaru talatin baya a gidan namu take. Koda jini wannan batu sai yunaru ya jinjina kai yace, tabbas nasan kana dauke da wannan takaici kuma kakanku ku ne ya janyo muku wannan babbar hasara a yadda naji tarihin al'amarin. Ya kamata lallai ka gyara wannan tarihi ka dawo da bara bana. Waziri yayi murmushi mugunta yace, ai dama lokaci kawai nake jira kuma gashi yanzu yazo. Tabbas bokaye na sun tabbatar mini da cewa a wannan yaki da za'a yi ne kadai zan sami babbar damar da zan cika gurina na zama sarkin kasar nan. Ya kai wannan attajiri yanzu wace damara ya kamata mu sake daurawa a cikin wannan kankanin lokaci domin cika burin mu da kuma kare duk wata matsala wacce zata iya kawo mana mishkila.?" Koda jin wannan tambaya sai attajiri yunaru ya yafito waziri da hannu yayi masa rada a kunne, koda waziri yaji abinda yunaru ya rada masa sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariyar farinciki saboda ya tabbatarda cewa indai wannan tuggu da suka shirya ya tafi dai-dai babu abinda zai hanasu cika burinsu. Nan fa waziri ya rungume attajiri yunaru yana ta sunbatarsa saboda farinciki. Kashe gari da sassafe dakaru suka taru a kofar fada a cikin shigar kayan yaki Wasu akan dawakai dauke da guzurinsu Wasu kuma a kasa sunyi sahu sahu layi-layi amma gaba dayansu adadinsu bai wuce miliyan ukku ba da dubu dari biyu da Arba'in. Bayan wadannan dakaru sun shafe kusan dakika dari da ashirin tsaitsaye suna jira sannan aka busa algaita kuma aka buga tambari sai ga sarki Barham ya fito daga cikin gidan sarauta, sarkin yaki kalmaru na take masa baya, koda suka iso gaban wannan runduna sai suka tsaya cak suka fuskancesu. Ai kuwa sai gaba dayan dakarun suka risina suka kwashi gaisuwa ga sarki Barham. A sannan ne kalmaru ya dubi dakarun a cikin nutsuwa yace ya ku dirkokin.wannan birni namu mai albarka inaso ku sani cewa wannan yaki da zamu fita yanzu yaki ne na rai ko mutuwa. Yaki ne na kwatar 'yanci da kare lafiyarmu, iyalanmu, dukiyarmu da rayukanmu. Ku sani cewa idan bamu yi nasara ba a wannan yaki matayenmu, 'ya 'yenmu da jikokinmu zasu zamo bayin mutane birnin zamar kuma dukiyoyinmu zasu zamo ganimar, don haka ya zama wajibi a garemu mu kawar da makiyanmu ta kowane hali idan munason mu kare martaba mu. Da dai mu dawo gida babu nasara gwara gaba dayanmu mu zamo gawarwaki a cikin filin yaki. Inason mu jajirce kuma mu zage damtse iya karfinmu da iyawarmu don tabbatarda nasararmu. Kamar yadda na gayamaku da farko cewar kada yawan abokan gaba ya razana ku ko firgitaku domin zuciyar da ta kekashe ga barin tsoron mutuwa bata faduwa. Indai muka rike wannan a cikin zukatanmu kuma kukayi duk abinda na umurceku dayi sai mun sami nasara a wannan yaki. Koda gama fadin hakan sai kalmaru ya daga hannunsa sama kuma ya wangame bakinsa ya kurma uban IHU irin wanda dakaru keyi ai kuwa sai gaba dayan dakarun suka kwarara uban ihu cikin hada baki. Sautin ihun nasu ya cika birnin gaba daya da amsa kuwwa yadda ko mutum a cikin rijiya yake sai ya jiyo. Nan da nan aka fara shirin tafiya yaki ana loda guzuri da makamai a kan dawakai,rakuma da alfadarai. Adaidai wannan lokaci ne aka ga gimbiya lazima ta fito daga cikin gidan sarautar a cikin kasaitacen ado mai tsantsanin kyau, nan fa gaba dayan mutanen dake wajen suka rude suka dimauce kai kace lu'u lu'u ne guda daya jal aka jefa a cikin bakin ruwan tabo saboda irin haske da kyalkyalin da gimbiya lazima take. Shi kansa sarki Barham bai san sa'adda murmushin farinciki ya subuce masa ba. Saboda yasan cewa Allah ya bashi kyakkyawar 'ya ta gaban kwatance kuma abar misali. A cikin keken doki lazima ta fito kuyanginta guda bakwai na biye da ita bisa ingarmun fararen dawakai kuma duk fararen tufafi suka sanya.kuma ita kuwa gimbiya lazima koren tufafi ta sanya masu duwatsun lu'u lu'u hatta takalmin dake kafarta kore ne hakama mayafin da ta lulluba a kanta. Kai duk da namijin da yayi arba da gimbiya lazima a wannan lokaci sai yaji kamar ya saceta ya gudu da ita koda kuwa samun damar kallonta kadai zai samu na dakika ashirin bare ya yi dace ace zai kalleta ne a lokacin da take yi masa murmushi, murmushin da ka iya wanke bakin ciki shekara dubu kuma ya kawar da damuwar da ta hana rai sukuni. abinda ya daurewa mutane kai shine ganin yadda gimbiya lazima ta fito a cikin shirin tafiya wannan yaki mai mugun hadari haka. Kai tsaye lazima ta karasa wajen sarki Barham suka rungume juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata ya sumbaci goshinta ya dubeta a cikin wani irin yanayi mai nuna tsantsar damuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah kamar zai fashe da kuka yace, yake yata kin sani cewa bamu taba rabuwa ba sai yau. Naso ace nima zanje wannan yaki domin ya kasance bamu nisanta da juna ba kuma ya kasance zan taimaka wajen baki kariya duk da cewar kina daga bayan filin yaki kuma nasan cewa sarkin yaki zai iya baki duk irin kariyar da zan iya baki. Na sani cewa Kinada son kallo don haka ki tsaya a baya baya kada ki kuskura ki bari dakarun birnin musab suyi tozali dake. Koda jin wannan batu sai gimbiya lazima tayi murmushi tace ka kwantar da hankalinka ya kai Abbana lallai na tabbatarda cewar babu abin da zai sameni a wannan yaki zan dawo gida lafiya. Sarki Barham yayi murmushi yace nasan da hakan amma dai duk hakan zan mikaki amana a hannun sarkin yaki kalmaru inaso ki sani cewa tsakanin ke da sarkin yaki tamkar bawa ne da mai gidansa.lallai ki ja mutuncinki da darajarki kada ki kuskura ki fara nuna soyayyarki a gareshi kuma kada ya nuna miki tasan kema kija ajinki kuma kijashi a kasa kafin ki karbi soyayyar tasa. Wannan wani karatu ne da ya faru a baya akan mahaifiyata nake biya miki shi domin ki kare martaba ki da darajarki. Sa'adda gimbiya lazima ta ji wannan batu sai murmushi ya subuce mata tace, lallai kuwa zan kiyaye bisa duk wadannan Abubuwa daka zaiyana mimi. Koda jin haka sai farinciki ya lullube sarki Barham ya kama hannun lazima ya jata izuwa wajen kalmaru suka tsaya daf dashi yadda babu wanda zai ji abinda zasu tattauna. Sarki ya fuskanci kalmaru yace, ga 'yata nan na baka amanarta. Ka lura da lafiyarta, mutuncinta da rayuwarta kamar yadda mahaifinka ya kasance mai biyayya da rike amana a garemu. Koda jin wannan batu sai sarkin yaki kalmaru ya tsuguna kasa bisa guiwoyinsa gaban sarki Barham kansa na sunkuye yace na rantse da darajar gemun ubana zan kula da lafiyar 'yarka, mutuncinta da rayuwarta kamar yadda zan kula da nawa. Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube sarki Barham ya kama kafadun kalmaru ya tasheshi tsaye suka rungume juna sannan yayi masa rada a kunne yace, Ba a zama sarki a banza sai ka saka wadansu matakai guda ukku, wannan yaki da zaka jagoranta shine mataki na farko kuma samun nasararka a yakin shine hayewarka matakin. Sauran matakan guda biyu kuwa kai da kanka zaka gansu da idanunka ayayin da kake ganin cigaba a kan matattakalar benen rayuwarka. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 2 Ba'a zama sarki a banza sai ka saka wadansu matakai guda ukku, wannan yaki da zaka jagoranta shine mataki na farko kuma samun nasararka a yakin shine hayewarka matakin Sauran matakan guda biyu kuwa kai da kanka zaka gansu da idanunka ayayin da kake ganin cigaba a kan matattakalar benen rayuwarka. Lokacin da sarki Barham yazo nan a zancensa sai mamaki ya turnuke kalmaru kuma kansa ya daure saboda ya kasa fahimtar abinda sarki ya gaya masa. Abinda ya fara Tambayar kansa shine ya za'a yi ya zama sarki alhalin bai gaji sarauta ba? " Nan dai sarki Barham da gimbiya lazima da sarkin yaki kalmaru suka yi bankwana kowa yaje ya hau dokinsa kalmaru ya jagoranci mayaka mutum dubu dari takwas da sittin kadai suka fice daga cikin birnin gaba daya suka nausa daji suka yita tafiya ba sassauci. Tunda aka fara wannan tafiya kalmaru bai yarda ya gusa daga kusa da keken dokin gimbiya lazima ba kuma a duk inda aka yada zango gimbiya ko kewaye zata yi don kawar da bukatarta shi yake rakata kuma sai ya caje ko ina a duk inda zata shiga ya tabbatarda cewa babu wani mugun abu a wajen sannan baya yarda a sami tazarar da tafi kamu goma a tsakaninsa da ita a duk inda take sai dai kawai ya juya mata baya tayi abin da zatayi sannan ta fito su koma cikin sansaninsu. A cikin wannan tafiya kalmaru yayi wadansu dabaru wadanda suka baiwa kowa mamaki domin tabbatar da tsaro. Duk sa'adda akayi 'yar doguwar tafiya ta Kimanin sa'a daya sai a tsaya cak a tura dakarun leken asiri suje su gano lafiyar hanya kuma su binciki karkashin kasa da saman bishiyoyi ko abokan gaba sun binne tarkuna ko kuma sun buya don shirya mugun hari. Ai kuwa a hakan sai da aka gano mugayen tarkuna kimanin guda arba'in na irin dakarun birnin musab kuma sai da aka kashe dakarun birnin musab kimanin mutum dubu uku wadanda suka bubbuya a cikin duhuwar bishiyoyi. Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon kwana ashirin ana tsallake mugayen hare-haren abokan gaba cikin nasara ba tare da an rasa ko da Badakare daya ba na birnin zamar har aka iso bakin wani daji wanda aka yiwa lakabi da Hajarul maut. Shi dai wannan daji na Hajarul maut an mai dashi tamkar filin yaki na nahiyar gaba daya. Duk kasashen da zasu yi yaki to Hajarul maut ne mahadarsu don haka ko yaushe ba'a rasa kwaran gwalolon bil adama a cikinsa kuma baya rabo da ungulaye da aljanu masu shan jini. Lokacin da rundunar yaki ta birnin zamar ta iso bakin dajin Hajarul maut sai sarkin yaki kalmaru ya daga hannu yana mai bayar da inkiyar a tsaya Nan take kuwa kowa yaja linzamin dokinsa aka tsaitsaya cak. A wannan lokaci keken dokin gimbiya lazima yana can tsakiyar rundunar kuma kalmaru yasa wadansu zakwakuran mayaka guda dubu biyu sun yi masa kawanya ta kowanen bangaren dan bata kariya. A cikinsu har da masu manyan garkuwowi, kwari da baka, masu da takubba amma in mutum ba'a cikinsu yake ba babu yadda za'a yi ya gane cewa suna aikin tsaron lafiyar gimbiya. Bayan rundunar ta tsaya cak sai aka yi tsit, in banda sautin numfashin dakaru dana dawakai babu abinda kunne keji. Sai da kalmaru ya zuba ido a bangaren da makiya zasu bullo kuma ya kasa kunne har tsawon dakika dari uku da sittin ko da yaji shiru sai hankalinsa ya dan tashi domin ya fuskanci cewar abinda yake gudun faruwa shine zai faru duk da cewa kuwa yayi tanadi akan hakan amma yasan cewa ba a bari a kwashe dai-dai. Kawai sai aka ji sarkin yaki kalmaru ya bayarda umurnin cewa kowa ya tsuguna kasa ya rufe jikinsa da garkuwarsa, nan da nan kuwa kowa yabi umurnin, hatta keken dokin gimbiya lazima sai da aka lullubeshi da wadansu irin manyan hijabai na karfe. Faruwar hakan ke da wuya sai ga ruwan kibiyoyin wuta a sama daga can bangaren da abokan gaba suka fito, saboda yawan kibiyoyin a sararin samaniya sai mutum yayi zaton cewa tsuntsayen duniya ne kaf! Suka taru suke shagalin biki Kaico, masifa bata da dadi, nan fa kibiyoyin wutar suka rinka zubowa akan garkuwoyin dakarun birnin zamar amma saboda yawansu sai da wadansu kibiyoyin suka rinka sukan dakarun a kafafunsu, kai wasu ma garkuwoyin karfen suka rinka hudawa suna soke dakaru suna mutuwa gashi babu damar a mike a mai da martani. Kafin a ankara abokan gaba sun kashe sama da dakaru dubu biyu nasu kalmaru, Al'amarin da yayi matukar fusata kalmaru kenan ya kwarara uban IHU yana mai yin inkiya ga dakarun nasa na musamman masu bakaken kaya. Nan take kuwa kasa ta tsage sai dakarun suka shige cikinta kimanin su dubu uku suka bace bat a cikin karkashin kasa basu baiyana a ko ina ba sai a can gaba kimanin nisan tafiyar sa'a guda inda rundunar su sarki Daryan take kawai sai gani akayi sun taso sama daga cikin karkashin tsakiyar abokan gaba sunyi sama tamkar daga cikin baka aka harbosu sun luluka kafin su dawo kasa sai suma suka rinka jeho mugayen wukake da kibiyoyi suna kashe dakarun da suke harba wadannan kibiyoyin wuta ga rundunar su kalmaru. Nan fa abin al'ajabi ya faru domin kuwa cikin kankanin lokaci suka kashe kaso biyu cikin kaso uku na dakarun masu kibiya. Koda ganin abinda ya faru sai sarki Daryan ya fusata ainun shima ya kwalawa nasa dakarun masu bakaken tufafi kira, ai kuwa sai gasu suma sun ratso kasa sun taso sama sun afkawa nasu kalmaru suka ruguntsume da azababben yaki a sararin sama tamkar tsuntsaye. Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai aka fara karkashe dakarun su kalmaru. Koda shugaban su ya ga ana yi musu barna sai ya busa wani kaho, take shida yaranasa suka yo kasa suka nutse a cikin kasa. Har dakarun sarki Daryan masu bakaken tufafi sun yunkura zasu bisu izuwa cikin karkashin kasar sai sarki Daryan ya hanasu yana mai daka musu tsawa sannan kuma ya kece da dariyar mugunta yace, ai fada da gudu tsoro ne, Na tabbatarda cewa kibiyoyin wutar da muka harba musu dole ne muyi musu mummunar barna, ko ba komai mun karya lagonsu don sai sun firgita damu bare kuma yanzu mu karasa garesu suga wannan tsananin yawa namu tunda mun ninkasu sau dari. Yanxu zamu karasa bakin dajin Hajarul maut inda za'a yita ta kare. Koda sarki Daryan yazo nan a zancensa sai mahaifinsa sarki saumir ya kyakyale da dariya yace, da kyau dana nima na sani cewa wannan shiri da mukayi bana wasa bane, Kasani cewa a wannan yaki ne zan cika burina na daukar fansa a kan tsohon sarkin yakinsu Ridwan. Koda jin wannan batu sai sarki Daryan ya dubi saumir yace, ya kai Abbana kayi sani cewa babu yadda zakayi ka dauki fansa a kan sarkin yaki Ridwan face idan mun shiga har cikin birnin zamar saboda Ridwan bai fito wannan yaki ba bisa rahoton da 'yan leken asirinmu suka kawo mini, shima sarki Barham bai fito ba. Wanda yake jagorantar mayakan birnin zamar ba wani bane face tsohon abokin fadana kalmaru saboda sarkin yakinsu wanda suka yi gasar matsayinsa da Hamsaru dan attajiri yunaru. Koda jin wannan batu sai mamaki da takaici ya kama sarki saumir yaji kamar ya fashe da kuka saboda ya dade yana shiri akan yadda zai rama abinda sarkin yaki Ridwan yayi masa wato shima ya sare masa hannu, ashirin sama duka hannayen biyu yake so ya sare masa kuma bayason ya mutu, so yake ya kamashi a hakan ya tsareshi a kurkuku har izuwa karshen rayuwarsa yana kunsar bakin ciki da takaici iri-iri Cikin tsananin fishi sarki saumir mai murabus ya dubi sarki Daryan yace haba ya kai dana me yasa tuntuni baka gaya min wannan al'amari ba sai yanzu?" Ridwan yace, yadda nasan irin burin da kaci a wannan yaki idan na sanar da kai ba karamin bakin ciki zaka yi ba amma tunda yanzu ka sani ina rokonka da ka hakura ka koma gida saboda ina mai tabbatar maka da cewa wannan yaki da za muyi yanzu ban taba yin mai hadarinsa ba da muninsa a wannan nahiya. Abba banason na rasaka don haka zai fi kyau ka koma gida. Ina mai tabbatar maka da cewa mune zamu sami nasara a wannan yaki saboda zamu sami hadin kan wasu daga cikin birnin zamar kasan kuwa ance da dan gari akanci gari, ka sani cewa muna da goyan bayan wazirin sarki Barham da attajiri yunaru. Akwai wani makirci da suka shirya mana wanda shine gudunmuwarsu kuma sai bayan su sarkin yaki kalmaru sun iso nan dajin Hajarul maut sannan za'a kulla makircin a can cikin birnin zamar, Ina nufin su kalmaru suna nan suna yaki za'a yiwa sarki Barham juyin mulki, tuni an gama duk wannan shiri harma an shigar da dakarun sojojin haya wadanda zasu taimakawa waziri ayi wannan yaki kuma suna yin nasara za'a fito da attajiri yunaru daga kurkuku. Koda sarki Daryan yazo nan a zancensa sai farinciki ya lullube saumir yace, ya kai dana hakika kwakwalwarka tana ja sossai kuma yanzu na gamsu cewar lallai mune zamu sami nasara a wannan yaki koda kuwa anci galabarmu a nan filin yaki. Kayi hakuri ya kai dana bazan iya komawa gida ba tunda har nayi damara na fito wannan yaki har sai takibina tasha jinin abokan gaba mai yawa. Koda jin haka sai idanun sarki Daryan suka ciko da kwallah saboda yasan halin mahaifinsa indai yayi magana baya sauyawa. Ba komai ne yasa idanunsa suka ciko da kwallah ba face bokayensa sun gaya masa cewa lallai a wannan yaki zai rasa wani babban masoyinsa. Da farko yayi tunanin cewar a cikin manya abokansa ne zai rasa daya wadanda suna daga cikin manyan dakarun yakin kasar wadanda ake takama dasu amma da yaga mahaifinsa ma ya fito wannan yaki sai zuciyarsa ta kama wasi-wasi yana mai zargin cewa anya kuwa ba mahaifinsa zai rasa a wannan yaki ba?" Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan, Kawai sai ya zare takobinsa ya kwarara uban IHU, suma sauran miliyoyin dakarun nasa sai suka zare takubbansu suka kwarara uban ihun nasu ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa ya firgita komai da kowa domin har sai da kasa ma tayi girgiza tamkar duk abinda ke kanta zai rufta cikinta. Hatta su kalmaru dake can bakin dajin Hajarul maut sai da suka jiyo wannan ihu kuma suka firgita ainun amma saboda suna da tsananin Kishin kasarsu Gamida da kekashasshiyar zuciya sai suka dake suka tsaya cak a inda suke ko motsi basuyi ba har sai da aka hango abokan gaba sun taho a cikin azababben gudu sun ta da kura suna wannan ihu da kiraji har dudufniyarsu ta haddasa karamar girgizar kasa saboda yawansu. Duk wannan kwarjini nasu baisa dakarun su kalmaru sun razana ba. Sai da ya rage tazarar kimanin zira'i arba'in a tsakanin rundunonin biyu sannan kalmaru ya zare takobinsa shima

Chapter 5 of 10