Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
ya kwarara uban ihu, ai kuwa sai gaba dayan dakarun nasa ma suka zare nasu takubban sukayi koyi dashi wato suma suka kwarara uban ihun. Nan fa ihun nasu ya cakude da na abokan gabarsu, suma sai suka zaburi dawakansu suka rugo izuwa garesu.. Wohoho, tashin hankali ba'a sama rana haka kuma masifa batada dadi domin wanda bai san ta ba shi yake fatan ta. Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin wadannan rundunoni biyu sai ya zamana cewa an kasa gane abinda ke wakana domin babu abinda idanu ke gani face shawagin jini da sassan bil'adama na kowanne bangare a sararin samaniya yana zubowa kasa tamkar ruwan sama. Kunnuwa kuwa bayajin komai sai ihun mazaje da kururuwarsu a lokacin da jini yaci gaba da tartsuwa da fallatsi kuma yana kwarara a kan kasa tamkar teku ta balle. Kai saboda masifa ta kai masifa babu mai gane wani in ba don bambancin launin irin kayan yakin da ya bambanta. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 3 Lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin wadannan rundunoni biyu sai ya zamana cewa an kasa gane abinda ke wakana domin babu abinda idanu ke gani face shawagin jini da sassan jikin bil'adama na kowanne bangare a sararin samaniya yana zubowa kasa tamkar ruwan sama. Kunnuwa kuwa basa jin komai sai ihun mazaje da kururuwarsu a lokacin da jini yaci gaba da tartsuwa da fallatsi kuma yana kwarara a kan kasa tamkar teku ta balle. Kai saboda masifa ta kai masifa babu mai gane wani in ba don bambancin launin irin kayan yakin da ya bambanta ba. Kalmaru da sarki Daryan kuwa duk inda suka kutsa a cikin abokan gabarsu sai dai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona kowannensu jikinsa ya rine da jini, hatta fuskarsu ma sai ya sa hannu ya share jini sannan yake iya ganin gabansa. Kai hatta takubbansu ma sun rine da ruwan jini kuma dada ragargazar maza suke tamkar ba zasu taba gajiyawa ba. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face sai da aka shafe sama da sa'a ukku ana yin wannan masifaffan yaki amma ko sau daya kalmaru da sarki Daryan basu yi gaba da gaba ba, kowannensu ya bace a cikin yawan dakaru dake cikin filin yaki da turmutsutsu. Abu na biyu da zai kara baiwa mutum mamaki shine yadda dakarun sarki Daryan suka kasa kararda dakarun kalmaru alhalin sun ninkasu yawa sau dari, ba komai ne ya janyo hakan ba face tsananin iya yaki da kuma sababbun dabarun yaki wadanda kalmaru ya kirkiro kuma ba'a taba ganin irin su ba. Wani irin salon yaki suke yaki sai a sami adadinsu a bayansu a tsaye basa yakin amma da zarar sunga na gabansu sun fara gajiya sai su karbesu su shige gaba su kuma su dawo bayansu , kaga kenan a wannan lokaci su abokan gaba zasu ci gaba da yaki ne da masu rashin gajiya don haka cikin kankanin lokaci za'a ga sun rafkesu. Lokacin da sa'a uku ta cika sarki Daryan ya lura da yadda duk jikinsa ya rine da jinin abokan gabarsa kuma yaga cewa bai san iya adadin rayukan da ya dauka ba na abokan gaba sai ransa yayi dadi wani irin farinciki ya lullubeshi don haka sai ya tarwatsa dakarun dake gabansa, ya juyo ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa domin yaga irin gagarumar nasarar da suka samu a yakin, nan take hankalinsa ya dugunzuma ainun, wani irin gagarumin bakin ciki ya mamaye zuciyarsa. Adaidai wannan lokaci ne ya hango mahaifinsa sarki saumir a can gefe daya yana ta ragargazar dakarun su kalmaru, duk inda yasa gabansa maza ne ke zuba kuma yaki yake cikin wani irin zafin nama na ban al'ajabi sai ci gaba da yin mummunar barna yake an rasa wani jarumi da zai iya tsaida shi domin komai yawan abokan gabar idan suka yanyameshi suka yi masa rudugudu sai dai kaga ya tarwatsasu ya rugurguzasu sun zube kasa filla-filla Yana cikin yin wannan mummunar barna ne kalmaru ya ankara dashi kuma ya lura da irin mummunar barna da yake shi kansa kalmaru sai da ya razana domin bai taba ganin dattijo mai tsantsanin jarumtaka ba irin wannan kuma gashi musaki mai hannu daya, Koda kalmaru yaga hakan sai ransa ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka sai ya zaburi dokinsa da baya da gudu da nufin ya kai ya kai inda sarki saumir ketayin barna, Ai kuwa sai wani Badakare daga cikin abokan gaba ya tsire dokin nasa da mashi a wuya, take dokin kalmaru yayi tutus dashi suka fadi kasa tare, dokin ya kama shure shuren mutuwa, shi kuwa kalmaru sai ya mike tsaye zumbur ya daka tsalle sama ya kama gudu akan kawunan jama'a ya durfafi inda sarki saumir yake, Ai kuwa koda dakarun sarki Daryan suka ji kalmaru yana dira akan kawunansu sai suka rinka kaiwa kafafunsa sara da takubbansu amma sai ya rinka gocewa dukkan harin nasu ya zama kamar tsuntsu mai fukafuki,shi kansa kalmaru sai da yayi mamakin yadda akayi yayi irin wannan gagarumar bajinta,domin dama mahaifinsa ne ya Koya masa irinta amma sai gashi yayi abinda ma ya wuce wanda aka koya masa din. A haka yaci gaba da durfafar inda sarki saumir yake, yana cikin hakane kuma ya hango sarki Daryan yaga ashe mummunar barna da yake yiwa dakarunsa harma tafi wacce sarki saumir keyi domin a cikin dakiku kadan yake batarda kimanin dakaru goma. Nan fa hankalin kalmaru ya rabu gida biyu ya rasa inda zai fara zuwa, Shin juyawa zai yi da baya yaje ya tari sarki Daryan ko kuwa kokari zaiyi yaje ya tari sarki saumir, A dai-dai wannan lokaci ne kalmaru yaga wadansu zakwakuran dakarunsa guda ukku wadanda yake ji dasu sun afkawa sarki saumir da nufin su hallaka shi farat daya bisa ganin irin barna da yake yiwa 'yan uwansu, koda suka afka masa da sara da suka sai yayi wata irin katantanwa a tsakiyarsu yana mai sunkuyawa kasa ai kuwa sai gashi ya yanki kowannensu a kirji, jini yayi tartsuwa daga cikin kirazan nasu sukayi tsalle da baya suna masu kwala ihu gami da faduwa kasa, Koda kalmaru ya hango abinda ya faru ga wadannan dakarun nasa guda ukku wadanda yake matukar ji dasu a filin yakin. Shi azatonsa ma zasu iya jagorantar yakin koda babu shi, Shi azatonsa ma zasu iya jagorantar yakin koda babu shi, Sai ransa ya baci ya daka wawan tsalle daga inda yake ya kaiwa sarki saumir wawan sara a wuya da nupin ya cire masa kai, inba don sarki saumir yayi wuf ya sunkuya ba da tuni aikin gama ya gama amma duk da haka sai da karfin takobin kalmaru ya zabtaro wani sashi na gashin kan sarki saumir kuma ya sami nasarar dukan kirjinsa da kafa, Sarki saumir ya dan ja da baya yayi taga taga amma sai ya tsaya kyam kamar giwa, Adaidai wannan lokaci ne kalmaru ya duro kasa bisa kafafunsa suka kama kallon kallo, Kada sarki saumir ya kurawa kalmaru idanu tswaon yan dakiku sai Ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta, a hakan duk abokin gabar da yazo gaban kalmaru ko saumir sai kaga sunyi masa kwaf daya ya zube kasa matacce. Sarki saumir ya nuna kalmaru da dan yatsa yace kai yaro tsaya iya matsayinka domin kana zartawa zaka zama tarihi, Ka sani cewa na gwazba da mahaifinka ma bai ji da dadi ba, Tabbas Nayarda cewa kai jarumi ne Domin tunda aka fara wannan yaki kai ka dai ne ka sami nasara iya taba jikina kuma ka cire wani abu daga cikin gashin kaina Tabbas kana kama da mahaifinka kuma ka gado shi a jarumtaka amma ka sani cewa yau ka taka sawun barawo. Ba kai nakeso na gani ba a gabana, ubanka nakeso ya tareni domin na dauki fansar abinda yayi mini amma ni duka hannayen nasa biyu nakeson na sare maimakon nawa guda daya dana rasa kuma na kamashi a raye na tsareshi kurkuku yayi ta kunar bakin ciki har ajalinsa amma tunda yaji tsoro ya kasa fitowa yakin kuma ya turoka ka wakilceshi, lallai akanka zan dauki wannan fansa. Koda sarki saumir yazo nan a jawabinsa sai kalmaru ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai tsohon azzalumi kayi sani cewa kunyi sake dan zaki ya girma kuma karen bana shike maganin zomon bana, Inaso ka sani cewa mahaifina ba ma tsoraci bane domin har gobe ruwa na maganin dauda, Babu yadda baiyi ba akan ya fito wannan yaki amma sai sarkinmu ya hanashi to ni gashi na fito amadadinsa kuma Shima yana da buri ya cika aikinsa ya kaika lahira, don haka nine zan cika masa wannan aikin, Koda jin haka sai sarki saumir ya bushe da dariyar a karo na biyu sannan ya turbune fuska ya dubi kalmaru yace ai kuwa sai dai mahaifin naka yaga gawarka ba dai cikar burinsa ba. Sarki saumir na gama fadin hakan sai ya daka tsalle sama daga kan dokinsa ya doki kirjin kalmaru da gwiwar kafarsa ta dama saboda karfin dukkan sai da kalmaru yayi baya da gudu tamkar an janyeshi da majaujawa ya fada can jan mayaka Yana mai yin aman jini amma sai ya mike zumbur cikin zafin nama da juriya ya daga takobinsa sama ya riketa da hannu biyu yana mai gyara tsayuwa. Koda ganin haka sai sarki saumir yayi masa wani dan guntun murmushi na mugunta irin wanda jaruman kwarai sukeyi sannan ya taho gareshi da sauri yana mai buda hannunsa mai rike da garkuwa, koda ganin haka sai shima kalmaru ya rugo izuwa gareshi suna haduwa suka kacame da azababben yaki, ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta, Koda aka fara wannan artabu kalmaru yasha mamaki kuma ya gane cewa tsohon kashi da sabo ba daya bane Abinda ya daurewa kalmaru kai shine ta yaya wannan tsohon mai hannu daya jal yake iya tare duk hare-harensa kuma yake maida martani, Harma nashi sara da sukan sunfi nashi zafi, kai inba don ma kalmaru yanada matukar juriya da zafin nama ba da tuni sarki saumir ya gama dashi. Sai da suka shafe kusan dakika dari uku da arba'in suna wannan bakin gurmuzu dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba, Al'amarin da ya fusata kowannensu kenan kuma duk wannan abu da ke faruwa sarki Daryan bai sani ba domin yana can yana ta ragargazar dakarun birnin zamar. Shi dai kalmaru mamaki ne ma ya ishe shi akan yadda tsoho mai hannu daya ya zame masa alakakai. Bisa dole duk su biyun suka dan ja da baya kadan suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru. Kowannensu acikin zuciyarsa yana tunani da nazari hanyar da zai bi ne ya sami nasara gamawa da dayan, Kowannensu acikin zuciyarsa yana tunani da nazari hanyar da zai bi ne ya sami nasara gamawa da dayan, Kamar hadin baki sai suka rugo izuwa kan juna a lokaci guda kowannensu yana ihu da karaji, suna haduwa suka sake kacamewa da azababben yaki amma wannan karon sai sarki saumir ya sauya salon yaki ya hada da naushi da bugu da hannu da kafa, Da yake yafi kalmaru zafin nama sai ya shammace shi ya doki kashin gwiwar kafarsa ta hagu take kashin ya goce daga jikin dan uwansa, kalmaru ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zojin da yaji, Kafin yayi wani yunkuri saumir ya sake kawo masa wawan sara a ciki da nufin ya farkeshi, cikin zafin nama ya da baya amma duk da haka sai da ya kawo masa suka da tsinin takobi a gefen kirjinsa na hagu,take takobin ta lube acikin kirjin, kalmaru ya sake kurma uban ihu kuma yayi sauri ya rike takobin da hannunsa guda a lokacin da saumir ke kokarin danna takobin domin ta lume gaba daya ta faso gadon bayansa, Kalmaru ya dage iya karfinsa ya hana sarki saumir ida nufinsa kuma gashi jini na kwararowa daga cikin kirjin nasa, gashi a durkushe ya kasa mikewa sakamakon gocewar kashin gwiwar tasa, Hakika duk wanda yaga halin da kalmaru ke ciki a wannan lokaci dole ne ya tausaya masa yasan cewa ya cika zarto kuma jarumin kwarai, Adaidai wannan lokacin ne sarki saumir ya fara kyalkyalar dariyar mugunta sannan ya dubi kalmaru yana mai ci gaba da kokarin danna takobin a cikin kirjinsa yace ai na gayamaka cewa sai dai mahaifinka yaga gawarka ba dai ya cika burinsa ba, Kwatsam ba zato ba tsammani kafin saumir yagama rufe bakinsa sai yaga kalmaru ya zare takobin da karfin tsiya daga cikin kirjinsa, jini yayi wata irin tartsuwa yayi 'yar dungure a kasa gaban saumir kafin saumir ya leka kasan nasa takobin kalmaru ta soke masa tasa takobin a makoshi take takobin kalmaru ta nutse a cikin wuyan saumir ta bullo ta keyarsa nan fa ya kama mata gungun a tsaye yana mai kwalawa dansa kira cikin ihu wato yana mai kiran sunan sarki Daryan Sarki Daryan na cikin ragargazar dakarun birnin zamar sai ya jiyo sautin murya mahaifinsa acan bayansa, A dimauce ya juyo da dokinsa baya ya tarwatsa abokan gaba kuma ya kutsa ta cikinsu da karfin tsiya yana kai sara da suka ta damansa da hagunsa ya samarwa kansa hanya ya durfafi inda ya juyo sautin murya mahaifin nasa a lokacin da zuciyarsa ke daka bisa zargin cewa lallai ba lafiya ba, Ai kuwa tunda daga nesa kadan ya fara hango kalmaru tsugune a kasa ya kasa mikewa,amma ya zubo masa idanu fuskarsa na ya tsine, Koda ya dubi gefen kalmaru yaga gawar mahaifinsa kwance a kasa sai ya takarkare ya kwarara uban ihu wanda ya razana gaba dayan mayakan dake filin dagar aka jujjuya da baya aka daina yakin aka zuba masa idanu a lokacin da ya karawa dokinsa kaimi ya sukwanoshi da gudun tsiya izuwa kan kalmaru yana mai sakin linzamin dokinsa da sake zaro wata takobin a gadon bayansa wato ya hada takubba biyu a hannunsa, A wannan lokaci komai yawan dandazon mayaka idan suka hango sarki Daryan sai sun firgita sun watsar da makamansu sun arce saboda tsananin kwarjininsa da kuma muguwar fusatar da yayi, Idanunsa sun kada sunyi jajur tamkar garwashin wuta da ya ruru ainun, Kuma gashi dama duk jikinsa da takobinsa guda sun rine da jini Kuma gashi dama duk jikinsa da takobinsa guda sun rine da jini Koda kalmaru yaga yadda sarki Daryan ya durfafoshi cikin tsananin fishi da mugun nupi sai ya tabbatarda cewa lallai idan ya riske shi haka yadda yake a tsugune kuma a galabaice tamkar gurgu, farat daya zai yi masa kissan gilla cikin tsananin juriya irin ta manyan mazaje kalmaru kalmaru ya kama kashin gwiwar kafar tasa ya durguzashi wato ya maidashi dai-dai yadda yake da saboda tsananin zafin da ya ji bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba, Ya fadi kasa, sa'adda kwallah wuya ta cika masa idanu, yaji kamar sare kafar tasa akayi. Adaidai wannan lokaci ne sarki Daryan ya iso daf dashi ya kawo masa wawan sara da takubbansa biyu cikin nufin guntule masa kai, Cikin bakin zafin nama kalmaru ya sunkuya takubban suka sari iska suka hadu da junansu wani irin tartsatsin wuta ya tashi kalmaru ya wurgina sau uku a kasa can gefe daya, Kawai sai gani akayi ya mike tsaye zumbur yana layi sakamakon jini dake zubawa daga cikin kirjinsa, cikin kuzari kalmaru yasa hannunsa guda ya yage rigar jikinsa ya toshe ramin raunin nasa kuma ya daure raunin tamau da ragowar tsumman rigar tasa don kada cikon ya cire jini yaci gaba da zuba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 4 Kawai sai gani akayi ya mike tsaye zumbur yana layi sakamakon jini dake bulowa daga cikin kirjinsa, Cikin kuzari kalmaru yasa hannunsa guda ya yage rigar jikinsa ya toshe ramin raunin nasa kuma ya daure raunin tamau da ragowar tsumman rigar tasa don kada cikon ya cire jini yaci gaba da zuba. Koda ganin wannan jarumtaka da kalmaru yayi sai sarki Daryan ya duro kasa daga kan dokinsa ya tsaya cak Sa'adda tazarar dake tsakaninsa da kalmaru bata wuce taku biyar ba, Koda ya sake duban gawar mahaifinsa a karo na biyu sai hawaye ya subuto masa kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda bakin ciki, Bai san sa'adda ya kwarara uban ihu ba sannan ya dubi kalmaru fuskarsa nayin gantsin wutar tsana da gaba na ruruwa a cikin idanunsa, Yace, na rantse da kaunar da nake yiwa Mahaifina ko ni ko kai a filin yakin nan, Bazamu daina yaki ba har sai dayanmu ya kashe daya, Yana gama fadin haka ya zaburo da gudu izuwa kan kalmaru, shima kalmaru sai ya zaburo izuwa kansa, Suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki kamar zasu cinye junansu danyu, Ai kuwa sai sauran dakarun ma suka dada kacamewa.... Yaki ya dawo sabo kuma danye tamkar ma a sannan aka farashi yazamana cewa ihun mazaje da karafkiyar karafa ta cika dajin gaba daya ta razana duk wani abu mai rai dake bisa doron kasa da karkashinta. Sai da sarki Daryan da sarkin yaki kalmaru suka shafe Sa'a daya da rabi cif suna kaiwa junansu sara da suka amma ko sau daya babu wanda ya sami nasarar yiwa dan uwansa rauni koda bille kuwa, Al'amarin da ya fusatasu kenan duk su biyun, don haka babu shiri suka yi ja da baya suka tsaya suna haki da hararar juna kamar yadda akayi dazu tsakanin kalmaru da sarki saumir, Ko hutun dakika ashirin basu yi ba, suka sake kacamewa da sabon azababben yakin gaba, kamar zasu ci naman junansu danye, Wannna karon Sai labari yasha bam-bam domin sun sauya salon fada domin sun hada da tsalle-tsalle da kwance- kwance a kasa gamida kai naushi da bugu. Ai kuwa nan take labarin yasha bam-bam domin sun fara yiwa junansu rauni duk da cewa kusan karfinnsu yazo daya sarki Daryan ne ya fara samun nasarar yankan kalmaru a kafadarsa ta dama. Kafin ya kara kai masa wani harin tuni shima ya samu nasarar yankarsa a kafadar hagu, Haka dai suka cigaba da samun nasarar yiwa junansu rauni har sai da kowannensu ya sami rauni bakwai a jikinsa ya zamana cewa jini na zuba a jikinsu amma saboda naci gamida tsananin juriya basu fasa cigaba da yaki ba, Kamar ma a sannan suka fara yakin. Al'amarin gimbiya lazima kuwa wacce ke zaune a cikin keken doki a tsakiyar dakarun birnin zamar sa'adda aka fara wannan bakin masifaffen yaki an barsu ne a can baya bisa tsaron dakaru dubu arba'in, Batada ikon barin wajen sai dai ta hau saman keken dokin ta hango abinda ke faruwa acan filin yakin sannan ta rubuta acikin wani littafi wanda tazo dashi. Tsakanin inda take da sansanin yakin akwai tazara ta kimanin taku dari hudu da saba'in da shidda don haka tana hango mutane da ke can sansanin yakin ne y'an mini mini saboda nisa. Bisa wannan dalili ne hankalinta ya dugunzuma ainun kuma ranta ya baci saboda batada halin ganin ainihin abinda ke faruwa a filin yakin sai dai in angama yakin wadanda suka tsira da rayuwarsa su bata labari. Nan fa gimbiya lazima ta koma cikin keken doki nata tayi zamanta ta shiga tunani hanyar da zata bi ta sulale taje cikin sansanin yakin ba tare da an ganeta ba. Tana cikin wannan tunani ne wata dabara ta fado mata kawai sai tayi kiran sunan daya daga cikin dakarun dake tsaronta. Huzen ya yaye labulan keken dokin ya leko da kansa yana mai risinawa cikin biyayya yace,ya shugabata meye bukatar ki? Lazima tayi murmushi mai taushi ga Huzen tace, ina son ka shigo cikin keken dokin nan ka zauna tare da ni domin ka debe mini kewa da tsoron da nake fama dashi bisa jiyo ihun mazaje da nake ji daga can sansanin yaki. Koda jin wannan batu sai mamaki da tsoro suka kama sadauki Huzen ya dubeta cikin alamun matukar damuwa yace , ya shugabata kina so sarki yasa a tsirani ne idan ya sami labarin cewa na kadaita dake a cikin keken dokinki. Lallai wannan laifi ne mai girma a wajen sarki, Kiyi hakuri bazan iya ba. Koda jin haka sai fuskar gimbiya lazima ta juye izuwa tsananin fushi tayi wuf ta zare wata wuka mai tsananin kaifi da tsini daga kugunta ta dorata akan makoshin Huzen har wukar ta dan tsireshi jini ya fito sannnan tace ko kayi abinda na umurceka ko kuma na kasheka sannan na kashe kaina in yaso raina ya rataya a wuyanka Mahaifina ya kama iyalinka da daginka gaba daya ya kashe su. Duk wannan zance dake wakana tsakanin gimbiya lazima da sadauki Huzen babu mai jinsu domin cikin karamar murya suke maganganinsu. Cikin tsananin tsoro jikinsa na karkarwa ya kunna kai ya shige cikin keken dokin A wannan lokaci sauran dakarun basu lura da shigarsa ba don sai da ya faki numfashinsu a matsayinsa na shugabansu wanda basa sa masa ido. Huzen na shiga cikin keken dokin sai gimbiya lazima ta shammace shi ta gabza masa wawan naushi a kuibin kasan kunnensa na hagu, nan take numfashinsa ya dauke yayi suman tsugune, zai fadi kasa kenan sai tayi sauri ta tallafoshi ta ajiye shi kasa a hankali, Cikin sauri ta tube kayan jikinta tayi musanya dana Huzen sannan ta kishingidar dashi tamkar barci yake yi. Hatta hular karfen dake kansa sai da ta cire tasa akanta, Shima sai ta rufe fuskarsa da irin kyallen da ta rufe fuskarta Lazima ta fito daga cikin keken dokin a hankali yadda ko motsinta ba'a ji ba Kawai sai ta dubi mataimakin huzen tayi masa inkiya da zataje can sansanin yakin ta gano halin da ake ciki. Ba tare da ta jira taji abinda zai ce ba sai kawai ta falfala da gudu ta nufi inda sansanin yakin yake. Cikin alamun tsananin damuwa mataimakin huzen ya dubi daya daga cikin dakarun yace,amma fa Huzen yayi babban ganganci domin bisa dokar sarkin yaki ba zai taba gusawa daga nan inda aka umurcemu da tsayawa ba face ya tabbatarda cewa muke samun nasara a wannan yaki kuma gashi babu wanda yasan halin da ake ciki. Koda jin haka sai Badakaren yayi ajiyar numfashi yace, kwarai kuwa abinda ka fadi gaskiya ne To amma inbanda abinka ta yaya zai iya gane hakan idan baije kusa da sansanin yakin ba. Badakare ya gyada kai yace hakane to amma dai ai sarkin yaki yace komi ake ciki zai aiko mana da umurni bisa abinda ya kamata muyi, Mataimakin huzen yace to idan kuma yakin ya rincabe fiye da yadda ake zato ya zamana cewa shi sarkin yaki ya rude ya manta damu da gimbiya gaba daya fa?" Ai wani lokacin sai anyi kundunbala sannan ake samun abinda zaifi, ina ganin fa ya kamata ka leka cikin keken dokin nan domin mu san halin da gimbiya lazima ke ciki don tun dazu da ta leko waje a karo na uku bata sake lekowa ba. Mataimakin huzen yace maganarka gaskiya ce, nan take ya yaye labulen keken dokin ya leka, Ai kuwa sai yaga gimbiya a kishingide alamar tana barci. Cikin tsananin mamaki ya juyo da baya da kansa da sauri ya dubi Badakaren yace ai barci take yi. Koda jin haka sai gaba dayan dakarun dake gadin keken dokin suka zazzaro idanu, Badakaren ya dubi mataimakin huzen yace, ta yaya gimbiya zata iya yin barci alhalin muna cikin wannan mugun tashin hankali na yaki, Daga nan ma tana jiyo ihun mazaje da karar haduwar makamai? " MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 3 PART 5 Koda jin haka sai gaba dayan dakarun dake gadin keken dokin suka zazzaro idanu, Badakaren ya dubi mataimakin huzen yace, ta yaya gimbiya zata iya yin barci alhalin muna cikin wannan mugun tashin hankali na yaki, Daga nan ma tana jiyo ihun mazaje da karar haduwar makamai? " Sa'adda mataimakin huzen yaji wannan tambaya sai ya gyada kai yace ai kasan wani lokacin tashin hankali yakansa mutum yasha maganin da barci zai daukeshi don kada razana tasa ya fada cikin wani mugun hali Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya kwanta Akayi tsit babu wanda ya kara yin magana ko cewa wani abu. Al'amarin gimbiya lazima kuwa lokacin da ta durfafi cikin sansanin yaki a cikin shigar sadauki Huzen sai ta zare takobinta taci gaba da falfala gudu har ta iso inda ake yakin. Koda ta iso da nufin ta tsaya a gefe daya tayi kallo kuma ta rubutasu abinda take gani sai ta kasa domin hankalinta ne ya dugunzuma ainun bisa ganin yadda ake ta ragargazar dakarun sarkinta duk da cewa kuwa suma suna kashe abokan gabar ta hanyar amfani da sababbin dabarun yaki da kalmaru ya koya musu, Babu abinda ya firgita gimbiya lazima face ganin tsananin yawan abokan gabar tasu akan nasu dakarun. Gashi dai kashesu akeyi amma kamar matattun nasu ne suke kara tasowa, Koda ganin wannan al'amari sai zuciyar gimbiya lazima ta kama tafarfasa, Take taji dukkan tsoro ya kau daga cikin Zuciyarta, Ta tuna cewa itama fa tun tana yarinya karama mahaifinta sarki Barham Ya koya mata yaki a sirrance ba tareda kowa ya sani ba har izuwa girmanta amma dai bata taba jarraba hazakarta da kokarinta kuma bata taba halarta yaki ba sai wannan karon. Nan take taji kishin al'ummata ya kamata kawai sai ta kutsa da karfin tsiya izuwa cikin turmutsutsun yakin ta hau dakaru da sara da suka. Nan da nan ta rinka dauka rai kai kace dama can tsohuwar jaruma ce wadda ta saba gurmuzu a filin fama, Ita kanta sai mamaki ya turnuke ta bisa ganin irin tsananin zafin namanta da jarumtakarta saboda ganin yadda take tarwatsa abokan gabar da karfin damtsenta tana gididdibasu da ratsawa ta tsakiyarsu tamkar tana sassabe a gona, Koda dakaru suka ga Huzen ya shigo cikin filin daga anci gaba da yaki da shi sai suka cika da tsananin tsoro gamida mamaki saboda zaton ko an kaiwa gimbiya lazima hari ne a can inda take amma kuma da suka ga jarumtakar huzen ta wuce yadda suka santa sai kansu ya kulle don haka sai ya zamo tamkar ya kara musu kwarin gwiwa ne, Suma sai suka kara zage damtse, Haka dai gimbiya lazima taci gaba da kutsawa cikin sansanin yakin har ta iso tsakiyar yazamana cewa itama gaba daya cikinta ya rine da jini, su kansu abokan gabar da suka ga sabon mayaki daga cikin dakarun birnin zamar ya shigo cikin wannan sansanin yana ta ragargazar jama'arsu sai suka firgita suka rinka yi masa rubdugu amma duk a banza domin bankesu yake yi yana ci gaba da ragargazarsu, kai kace wutace ta kama karmami, Kai da yawa daga cikin dakarun ma cewa sukayi wannan ba mutum bane, aljani ne kawai yayi basaja A can bangaren sarki Daryan da sarkin yaki kalmaru kuwa al'amarin ya sake muni domin sun sake yiwa junansu rauni guda bakwai bakwai, jini dake zuba a jikinsu yafi na da har takai cewa jiri na dibansu amma saboda bakin nacinsu sun ki faduwa kasa babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda karfin damtsensu da iya yakinsu yazo kunnen doki kai kace 'yan biyu ne su a komai. Shi dai sarki Daryan yana yin wannan yaki ne da dukkan karfinsa da zuciyarsa don ganin ya dauki fansar ran mahaifinsa saumir don haka yana kaiwa kalmaru hari yana ihu da kururuwa bai fasa ba, Shi kuma kalmaru yana kare kansa gamida maida martani, Saboda tsananin bakin ciki dake ran sarki Daryan sai ya zamana cewa taurin ransa yafi na kalmaru don haka sai yaci gaba da Kaiwa kalmaru mahaukacin hare-hare ba sassauci Kafin kalmaru ya kai masa hari daya shi ya kai masa uku. Nan da nan ya kuntata kalmaru har ta kai cewa da kyar kalmaru ke iya tare hare-haren nasa kai har ta ma kai cewa karfin saran Daryan da Nauyinsa suna sawa kalmaru na durkushewa kasa amma saboda juriyarsa da

Chapter 6 of 10