Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 10
Ridwan fiye da dukkanmu?" Sa'adda mahaifinmu da Ridwan suka ji wannan tambaya sai hankalinsu ya dugunzuma ainun, a lokaci guda duk su biyun idanunsu suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masu. Mahaifin namu ya dubeni kamar zai fashe da kuka yace, Kafin na baku amsar tambayarku nima zanyi muku wadansu tambayoyi guda ukku rak. Tambaya ta farko itace, acikinku nan ku arba'in da biyu waye ya taba jinyata ta tsawon kwana ukku rak a duk sa'adda na kwanta rashin lfy ko kuma na sami babban rauni a daji wajen yin farauta? " Dajin wannan tambaya sai mu duka muka sunkui da kawunanmu kasa aka rasa wanda zai ce kala. Mahaifin namu yace, ga Ridwan shine kankanin cikinku amma wasu shekarun baya sa'adda na fafata kazamin yaki da wani sihirtaccen zaki na sami rauni mai yawa a jikina sai da ya shekara ukku yana jinyata. Dare da rana yana tare da ni Baya gusawa daga kusa dani Ko tari yaji nayi sai ya tambayeni ko inada bukatar wani abu A wannan lokaci sai da raunikan jikina suka zamo gyambo suka rinka wari Gaba dayanku Ku ka daina shigowa turakata don kada wannan wari da nake yi ya cutar daku, Shi kuwa ridwan a cikin warin yake kwana da yini. Haka zan turashi daji ya tafi neman saiwoyin bishiyoyin da zai hada mini magunguna. A tafarkin hakan ne ya rinka shiga garari da masifu iri-iri amma dai-dai da rana daya bai taba tsorata ba ko gajiyawa ba Sai da yaga na sami lfy na warke sumul a cikin wadannan shekaru ukku. Tambaya ta biyu a gareku itace, " Acikinku wanene ya taba sallama rayuwarsa don ceto tawa? Duk sa'adda na shiga daji farauta tare daku da zarar kunga wata muguwar dabba wacce zata iya hallakani duk sai ku gudu Ku barni Shi kuwa Ridwan bai taba guduwa ba Akwai rana da na fafata da wani katon gwaggon biri mai tsantsanin karfin tsiya, kuma wanda sihirin tsafi baya tasiri akansa. Koda Ridwan yaga birin yayi mini wawan duka na zube kasa magashiyan kuma birin ya yunkura zai hallakani Sai ya kwarara uban IHU ya fito daga inda yake boye. Koda birin yayi arba da Ridwan sai ya fasa hallakani ya nupi inda yake, A lokacin ne Ridwan ya kalleni yana mai zubda hawaye Mai nuna alamar bankwana kuma yayi mini inkiyar na tashi na gudu domin na tserar da rayuwata, Kawai sai gani nayi Ridwan ya durkusa a gaban wannan birin yana jira kawai ya kashe shi. Cikin tsananin fusata na mike tsaye zumbur! Na kwarara uban ihu mai firgita maza Ai kuwa sai birin ya juyo gareni ya falfalo da gudu Nima sai na falfala da gudun tsiya izuwa gareshi Muna haduwa muka ruguntsume da azababben yaki na ganan kwatance, A wannan lokaci yaki nake da dukkan raina da jikina Kona mutu Kona rayu Bisa mamaki wannan karon sai naga na sami azababben zafin nama don haka sai na rikirkita birin Yazamana cewa baya ma iya kawo mini harin sai kokarin kare kansa yake kawai Gashi dai ina saran sassan jikin birin Amma Takobin bata yi masa lahanin komai saboda karfin sihirin dake jikinsa, A hakan ne kuma birin ya rinka samun damar kawo mini mugayen Hare-hare ina kaucewa Ina cikin wannan gurmuzu ne da birin kawai sai naga Ridwan ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan birin Yana zuwa daf dashi sai ya daka tsalle sama ya sokawa birin wuka a tsakiyar kansa. Ai kuwa sai wukar ta nutse izuwa cikin kan birin Jini ya kama tsiri a sama A dai-dai lokaci Ridwan ya duro kasa bisa kafafunsa Nan take birin ya kama ma-ta gungun daga tsaye yana ruri da kururuwa. Daga can kuma sai ya sulale kasa matacce. Lokacin da mahaifin namu yaxo nan a labarinsa sai gaba dayan mu kunya ta kama mu Muka sunkui da kawunanmu kasa Shi kuma Ridwan sai ya kama kuka yana mai Cewa, Ya kai Abbana ka daina fadin wadannan kalamai." MAZA SUN FADI!!! Part 9 Lokacin da mahaifin namu yaxo nan a labarinsa sai gaba dayan mu kunya ta kama mu Muka sunkui da kawunanmu kasa Shikuma Ridwan sai ya kama kuka yana mai Cewa, Yai kai Abbana Ka daina fadin wadannan kalamai. Mahaifin namu ya sake Duban mu duka yace, "ya kai Ridwan ka kyale ni na fadi bakin ciki dake Zuciyata Domin idan ban amayar dashi ba Zai iya cutar dani Tambaya ta ukku wadda itace ta karshe A gareku. A cikinku ku arba'in da biyun nan waye in hanashi da barin abu yake bari ko kuma in na umurceshi da yayi yake yi?" Mu duka sai muka sake sunkui da kawunanmu kasa Aka rasa wanda zai ce kala. Kawai sai ya kamo Ridwan ya rungumeshi a kirjinsa a lokacin da hawaye ya zubo masa yace, "Tunda Ridwan ya taso bai taba ketare umurnina ba. Komai tsananin son da yake yiwa abu indai nace ya barshi, ya bar abin nan Har abada. Saboda me zaku ga laifina akan na kaunaci Ridwan fiye daku na fifitashi? " Inaso ku sani cewa duk irin kiyayyar da kuke nunawa Ridwan na santa Kuma kunsha kokarin hallakashi amma bakwa samun nasara. To ku sani cewa daga nan har mutuwarku baza ku iya cutar da Ridwan ba Domin na kareshi da dukkan Sirrinkan tsafina. Daga wannan rana mahaifinmu yaci gaba da fifita Ridwan akanmu Mu kuma bamu daina nuna kiyayyarmu a gareshi. Abinda ya hana sarki ya baiwa mahaifinmu sarautar sarkin yaki shine, Sarkin yaki na wannan lokaci dan uwan sarki ne na jini domin yan maza zur suke. Amma duk da haka sai sarki ya yiwa mahaifin namu alkawarin cewar indai sarkin yaki ya tsufa ko ya mutu shi zai baiwa sarauta. Idan kuma baya raye a sannan to zai baiwa dansa Ridwan. Lokacin da muka sami labarin wannan alkawari wanda sarki Yayiwa mahaifinmu sai muka kamu da tsananin bakin ciki muka sake daura damarar ganin bayan Ridwan. Wannan shine Asalin gabarmu da Ridwan, Kuma gashi har yanzu mun kasa ganin bayansa. Amma abinda nakeson ka fahimta ya kai dana shine, Komai rintsi da tsanani sai na tabbatarda cewa, Wannan kujera ta sarkin yaki ta dawo hannunmu. Koda jin wannan batu sai Hamsaru yai ajiyar zuciya yace, " ya kai Abbana kayi sani cewa Nayarda da kwarewarka gamida tuggunka Amma inaso ka sani cewa, Muna cikin tsaka mai wuya akan burinmu Domin idan har boka hizainu yace, Babu tsafi a cikin nasarar da kalmaru ya samu Yanzu shikenan fa munyi asara. Kuma sai ka tafi kurkuku tsawon wata shidda. Koda jin wannan batu sai yunaru ya bushe da dariya yace, Sau nawa zangaya maka cewa, "kada mage ba yankawa bane?" Ko ina tsare a kurkuku kuma koda kalmaru ya hau kan wannan kujera sai nasan hanyar da nabi na rabashi da kujerar. " Acan bangaren sarkin yaki Ridwan da dansa kalmaru kuwa, Suma sun kebe gefe daya kusa da karagar sarki sun zauna suna tattaunawa. Sarkin yaki ya dubi dansa kalmaru a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace, "ya kai dana yanzu wane mataki ya kamata mu dauka akan baiwa Zulaima? Tabbas taci amanarmu domin na fahimci cewar dan uwana YUNARU ne ya hada baki da ita ta zuba maka sinadarin kashe jiki acikin ruwan inibin da kasha Wanda ya cire maka kuzari ya saka maka tsananin kasala domin Hamsaru ya samu nasara akan ka. Ina ganin kawai mu kasheta." Koda jin haka sai kalmaru ya zazzaro idanu ya dubi sarkin yaki Ridwan cikin alamun tsananin tsoro yace, Haba ya Abbana ka tsaya fa kayi tunani, aduk iya tsawon shekarun da kayi da Zulaima bata taba ha'intarka ba ko cin amanarka ba. Ni kam ina ganin cewa abinda zai sa taci amanarmu ba karami bane Abune wanda yafi karfinta Ni yanzu ma hankalina a tashe yake domin bamu san a irin halin da take ciki ba. Don na tabbatarda cewa tana cikin tsananin damuwa bisa abinda ta akanta. Kayi mini iznin na koma gida dan na ganota." Sarkin yaki Ridwan yace, To idan kuma ka tafi su waziri suka dawo fa yanzu Ya zamana cewa gaskiyar mu ta tabbata sarki zai baka takobin zinare? " Ai kaga idan baka nan sarki da jama'a baza su ji dadi ba. Ni ya kamata na koma gida domin naga halin da Zulaima ke ciki. Idan sarki ya nemeni ka gaya masa cewa zan dawo nan bada jimawa ba." Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki Ridwan ya mike ya kutsa ta cikn taron jama'a ya fice daga cikin fadar gaba daya. SHIN WACE IRIN AMSA BOKA HIZAINU ZAI BAYAR?" SHIN TSAKANIN KALMARU DA HAMSARU WAYE YAKE ZAMA SARKIN YAKI BIRNIN ZAMAR KUWA? " Mu hadu a maza sun fadi kashi na biyu don jin cigaba... MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 1 Al'amarin su waziri kuwa saida suka shafe Sa'a guda cur! Suna tafiya akan dawakai sannan suka iso bayan gari inda gidan boka hizainu yake. Da isowarsu kofar gidan sai suka iske wani hadimin boka hizainu tsaye a kofar gidan wanda ya kasance gajeren mutum mai dogon gemu tamkar wada Amma ba wada bane Yana da manyan idanu masu dauke da gashin gira mai kauri. Ko kadan babu alamar annuri akan fuskar mutumin. Ga wadanda suka san tarihin wannan mutum Ance ba'a taba ganin dariyarsa ba ko murmushinsa. Har ma mutane suna yi masa lakabi da wakilin bakin ciki. Nan take wakilin boka hizainu ya risina ya gaishe dasu waziri cikin girmamawa kuma yai musu barka da zuwa. Waziri ya dubi hadimin yace, "ya kai zunnaru maza kaje ka gayawa maigidanka cewa sarki ya aikiomu bisa wani sako na musamman wanda yake bukatar amsarsa yanzu- yanzu" Koda da jin wannan batu sai zunnaru yace, ya shugabana ai tuni maigidana yasan da zuwan ku kuma yasan sakon da kuke dauke dashi har ya gayamini na shaida muku cewa lallai kalmaru ya lashe wannan gasa babu sihiri. Kuma yace a gayawa sarki ya tabbatarda cewa an baiwa kalmaru takobin zinare Idan kuwa akayi kuskure aka baiwa waninsa birnin zamar zai fuskanci annoba da masifu iri-iri. Koda jin wannan batu sai waziri da sauran wadannan yan majalisa mutum ukku suka kama kallon junansu suna muzurai. Kawai sai waziri ya dubi zunnaru ya daka masa tsawa yace, "shin baka ganin cewa wannan aike da sarki yayi mana sako ne mai muhimmanci wanda ya kamata ace munji amsarsa daga bakin boka hizainu da kansa?" Ta yaya kake tsammani sarki zai yarda da mu idan muka ce kaine ka sanar damu wannan batu? " Har zunnaru ya budi baki zaice wani abu sai kawai suka ga boka hizainu ya bayyana tsulum a gabansu fuskarsa cike da alamun damuwa. Kawai sai ya dubi waziri yace, "Abinda bawanmu zunnaru ya fada muku gaskiya ne Lallai ku isar da wannan sakon dana gaya muku dai-dai idan kuka kuskura kuka fadi wani abu sabanin nawa zancen Karshen wannan birnin namu yazo, domin duk wani babba walau basarake ko attajiri sai ya mutu " Boka hizainu na gama fadin hakan sai ya bace bat daga wajen tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen. Koda faruwar hakan sai daya daga cikin yan majalisar yaja waziri gefe daya suka kebe yadda babu wanda zaiji abinda zasu tattauna. Dan majalisar mai suna Raziyan ya dubi waziri yace, ya shugabana yanzu yaya zamuyi kenan " Kasan yadda muka rabu da attajiri yunaru ya bamu dukiya mai dimbin yawa domin mu murda wannan al'amari domin tabbatar da dansa Hamsaru akan wannan matsayi, Gashi kuma boka hizainu yace idan ba'a baiwa kalmaru kujerar sarkin yaki ba manya da yawa zasu mutu a garin nan. Shin menene mafita akan wannan al'amari? " Waziri yai ajiyar zuciya cikin sanyin jiki yace, ai sawun giwa ya take na rakumi. Dole ne mu kawar da bukatar attajiri yunaru gefe daya don ba zamu yarda wake daya ya bata gari ba" Koda gama fadin hakan sai waziri ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya. Cikin hanzari Raziyan da sauran abokan tafiyarsu suka zaburi dawakansu suka rufa masa baya. ***** Lokacin da sarkin yaki Ridwan ya sulale ya bar filin fadar yaje ya hau dokinsa ya zubureshi da gudu ya nufi gida. Yana isowa cikin harabar gidan sai hadimin dake kula da barga dawakai ya rugo da gudu ya rike masa ya sauka. Sarkin yaki Ridwan na sauka sai ya dubi hadimin yace, shin kaga motsin Zulaima kuwa a gidan nan?" Hadimin ya risina yace, ya shugabana tunda kuka fita kaida kalmaru ko motsin Zulaima a yau ban jiyo ba daga cikin gida kamar yadda ta saba a kullum. " Koda jin haka sai hankalin sarkin yaki Ridwan ya dugunzuma ya ruga da gudu izuwa cikin gidan ya wuce kai tsaye izuwa turakar Zulaima. Da zuwa sai ya taba kofar dakin yajita rufe daga ciki. A dimauce ya kama kwankwasa kofar yana kwalawa Zulaima kira, amma sai yaji shiru bata amsa ba, kuma bata bude ba. Sarkin yaki ya zagaya bayan dakin ya leka ta taga don yaga abinda ke faruwa Kwatsam! Sai ya hango Zulaima ta daura igiya a jikin rufin dakin wacce zata rataye kanta tana kokarin taka wata kujera ta zarga igiyar. Koda tayi arba da sarkin yaki yana lekenta ta cikin tagar sai hawaye ya zubo mata tayi masa kallon karshe. Sarkin yaki na ganin haka sai ya daka mata tsawa yace, waye ya baki iznin ki kashe kanki alhalin kina matsayin baiwata?" Dajin haka sai hawaye ya sake zubowa Zulaima tace, Ka gafarceni ya shugabana ka tuna cewa ka dade da yantani ni ba baiwarka bace, kawai dai ina zaune tare da kai ne sbd kauna da shakuwa. Abinda yasa na yanke hukuncin kashe kaina shine, banga amfanin rayuwata ba tunda na zama maci amana na kawo karyewar darajar gidanan kuma na dakushe ci gaban kalmaru Ina mai neman gafararka data kalmaru bisa wannan mummunan aiki dana aikata wanda nayi shi bisa dole, saboda dan uwanka ne yunaru ya gayamini cewa idan ban zubawa kalmaru sinadarin kashe jiki ba a cikin abin shansa zai kasheka. Ni kuwa naga da na rasaka gwara na rasa tawa rayuwar kuma na janyo rushewar mulkin gidanan. Tunda har na aikata wannan laifi babu wani hukunci da zaifi dacewa dani samada mutuwa. Koda gama fadin hakan sai Zulaima ta yunkura da sauri ta taka wannan kujera ta mike tseye ta kamo wannan igiya ta shake wuyanta ta fara kakarin muruwa. Cikin tsananin dimauta sarkin yaki ya ja da baya ya rugo da gudun tsiya yasa kafa ya doki tagar dakin da dukkan karfinsa da kafarsa. Take tagar da ginin dakin suka burma ciki. Sarkin yaki ya fada cikin dakin sannan ya daka tsalle sama ya sare igiyar data daure wuyan Zulaima da takobi ta rikito kasa bisa tafin hannayensa a sume. A guje sarkin yakin birnin ya fito da Zulaima rungume a kirjinsa yana ihu yana kuka domin a zatonsa ma ta mutu. Yana isowa tsakar gidan sai ya shimfideta a kasa ya kura mata idanu yana mai zubda hawaye kuma yana sambatu. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai yaga Zulaima ta farfado tana mai yin tari cikin tsananin farinciki sarkin yaki ya kamo Zulaima ya rungumeta a kirjinsa ya sake fashe da kukan murna. Daga can sai janye jikinsa daga cikin na Zulaima suka fuskanci juna yace, Yake Zulaima kiyi sani cewa rayuwarki tafi tawa muhimmanci, tunda ni duk abinda nake nema a duniya na samu kuma dana kalmaru bashi da wata uwa a doron kasa wacce ta fiki. Yaya kalmaru zai kasance idan yazo ya riski gawarki?" Kiyi sani cewa da farko nayi matukar bakin ciki dana gane cewa kin zubawa kalmaru wani abu ya sha a cikin abin shansa kuma har na yanke miki hukuncin kisa bisa cin amanarmu, amma kuma sai kalmaru ya bani shawarar kada na kasheki tunda baki taba amanata ba a tsawon shekarun da kika shafe tare dani. Ki kwantarda hankalinki ki sani cewa burin dan uwana yunaru ba zai taba cika ba. Domin bazai iya kashe ni ba kuma ba zai iya hana kalmaru karba takobin zinare ba. Ina fatan nima zaki gafarceni bisa zargin dana yi miki akan wannan laifi wanda bayin kanki bane" Sarkin yaki Ridwan ya share hawayensa yace, ni kaina a yau ne na gane cewa irin son da kike yi mini ya wuce ma irin wanda nake yiwa kaina. Yanzu ki tashi mu tafi izuwa fada domin ina son ki gani da idanunki yadda danki kalmaru zai karbi takobin zinare a hannun sarki. Koda jin haka sai Zulaima ta mike cikin farin ciki, ba tare da bata lokaci ba suka fice daga cikin dakin. Suna fita sarkin yaki Ridwan ya kira babban hadimin gidan ya umurceshi da yaje ya kira magini ya gyara dakin Zulaima. Bayan nan sai suka je suka hau dawakai biyu suka garzaya fada. Acan fada kuwa mutane sun kagu dasu ga dawowar su waziri domin a kawo karshen wannan mahawara tsananin jarumi kalmaru da jarumi Hamsaru a baiwa dayansu takobin zinare. Shi kansa sarki Barham sai da ya gaji ya kosa da jira duk da cewar ana debe masa kewa da kade- kade da raye-raye Kwatsam! Sai aka hango dawowar su waziri sun durfafo filin fadar. Nan take dakaru suka bude hanya mutane suka dare, Su waziri suka iso gaban sarki. Nadeen Da isowarsu sai suka risina ga sarki gaba dayansu sannan waziri ya dago kai ya dubi sarki a lokacin da fadar tayi tsit! Tamkar babu wani mahaluki mai numfashi acikinta saboda kowa so yake yaji bayanin da waziri zai yi. Attajiri yunaru da dansa Hamsaru kuwa sai suka kama murmushin murna domin suna ganin cewa dole ne ma bukatarsu ta biya tunda waziri nasu ne. Kuma shine ya jagoranci wannan karbo sako daga wajen boka hizainu. Waziri yayi gyaran murya sannan yace ya shugabana mun karbo sakon ka ga boka hizainu kuma ya gaya mana cewa nasara da kalmaru ya samu a wannan gasa babu sihiri a cikinta. Kuma yace Lallai ka damka takobin zinare ga kalmaru idan kayi sabanin haka kuwa gaba dayan masu mulkinmu da attajiranmu na kasar nan zasu zama gawa. Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da shewa aka kama yiwa jarumi kalmaru jinjina. Attajiri yunaru da dansa Hamsaru kuwa Sai suka fashe da kukan bakin ciki. Kawai sai yunaru ya kama hannun Hamsaru ya janye shi suka fice daga filin fadar gaba daya. Nan take sarki Barham ya cika da tsananin farinciki ya mike tsaye aka miko takobin zinare ya karbata da hannu biyu sannan ya mikawa kalmaru. Shima ya karba da hannu biyu. Ai kuwa sai fadar ta sake rudewa da shewa har sai da sarki ya daga hannu sannan akayi tsit! Koda kalmaru ya juyo da baya ya fuskanci jama'a dake filin fadar sai hango mahaifinsa sarkin yaki Ridwan tare da Zulaima tsaye acan gefe daya sun zubo masa idanu suna ta murmushin farinciki bisa ganin takobin zinare a hannunsa. Take kalmaru ya sake kamuwa da tsananin farinciki mara misaltuwa musamman da yaga Zulaima a raye cikin koshin lfy. Sarki Barham ya dubi jama'a yace, Ya ku al'ummata kuyi sani cewa daga yau kalmaru ya gaji mahaifinsa ya zama sarkin yakin kasar nan na saba'in da bakwai. Ina fatan gaba dayan mu zamu bashi goyan baya da dukkan taimako domin ya sami damar gudanar da aikinsa kamar yadda ya kamata. Kuma saboda taya kalmaru murna wannan matsayi da yasamu zansa a shirya gagarumar walima anan fadata har tsawon kwana ukku " Nan take mawaka, makada da maroka suka shigo cikin fili fadar suka fara baje kolinsu. Sarakai da attajirai kuwa suka kama likin dinare da dirhami ana nuna farinciki ana bushasha. Kamar yadda sarki Barham yayi alkwari haka al'amarin ua kasance, Wato sai da aka kwana ukku anyin walima a fada irin wacce ba a taba yiba a kasar domin sai da abinci da abinsha suka wadata har ya zama almubazzaranci. Sarki Barham yanada wata 'ya budurwa guda daya mai suna LAZIMA Lazima ta kasance daban acikin mutane, Domin ra'ayinta da yanayin rayuwata ya fita dabam da na sauran mutane, tamkar ma bata kasance bil'adama ba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 2 Sarki Barham yanada wata kyakkyawar 'ya budurwa guda daya mai suna LAZIMA. Lazima ta kasance daban a cikin mutane, domin ra'ayinta da yanayin rayuwata ya fita dabam da na sauran mutane, tamkar ma bata kasance bil'adama ba. Dalili kuwa shine, duk irin abinda mutane suka sabayi, to fa ita sai tayi nata dabam. Abu na farko, tunda ta taso daga kurciyarta zuwa girmanta bata taba cin abinci sau uku a rana ba. Kullum sau daya take cin abinci da hantsi, Kuma bata cin abinci mai nauyi sossai daga ganye sai zuma da nono sai kuma naman tsuntsaye, Bata cin naman rago ko na akuya bare na rakumi da sauran manyan dabobbi. Idan taci wannan abinci da hantsi, to fa ba zata sake cin komai ba har dare sai ruwan shayi kawai ko ruwan inibi. Kuma kullum kara lafiya take, jikinta yana yin kyau tamkar na jaririya. Abu na biyu shine, kullum bata da aiki sai karanta littattafai iri-iri na adddinai dana tarihin masarautu da jaruman duniya. Sai lazima ta yini tana karatu da nazari, sai idan ta gaji sannan take dan yawatawa a cikin gidan sarautar ta mike kafafunta, Kuma ta shiga cikin lambun sarki ta zauna tana hutawa, tana kallon furanni da tsuntsaye. Tunda aka haifi lazima bata taba fita ba daga cikin harabar gidan sarautar, bisa wannan dalili ne mutane da yawa a kasar basu santa ba sai labarinta kawai suke ji. Idan har mutum bai zamo babba ba cikin masu sarautar birnin ba, to bai isa yaje inda ma zai ga gimbiya lazima ba. A ranar da za'a ayi walima karshe ta bikin sarautar kalmaru ta sarkin yaki gimbiya lazima na zaune a cikin turakarta tana nazarin wani littafi na tarihi sai taga kuyanginta gaba daya sun ci ado sunzo gabanta sun durkasa. Kawai sai shugabarsu ta dubi gimbiya lazima tace, Ya shugabata muna neman izini a wajenki ki amince mana muje mu halarci walimar karshe da za'a yi yau ta murna bikin nadin sarautar sarkin yaki. " Koda jin wannan batu sai idanun Gimbiya lazima suka zazzaro ta dubesu tace, Yanzu ashe har an nada sabon sarkin yaki a garin nan amma baku bani labari ba?" Shugabar kuyangin ta sukui da kanta kasa tace, "ya shugabana ai kinsan cewa kin hanemu gaba daya da gaya miki abinda ya shafi harkokin sarauta shiyasa bamu sanar dake ba. Lazima ta gyada kai tace, Acikin jerin sarakan yaki na kasar nan wannan shine na nawa?" Shugabar kunyangin tace, naji sarki yana cewa kalmaru shine na saba'in da bakwai. " Koda jin haka sai gimbiya lazima ta mike tseye zumbur! Cikin tsananin farinciki tace, Ku shirya mini fita izuwa fada. Lallai inason na gana da wannan sabon sarkin yaki. Koda jin wannan batu sai gaba daya kuyangin suka tsaya suna noke-noke Cikin fushi gimbiya lazima ta daka musu tsawa tace,wai shin ba kwa ji nane, maza ku tashi kuje ku shirya mini fita zuwa fada. Cikin hanzari kuyangin suka mike tsaye suka je suka fara shirye-shiryen tafiya. Ita kuwa gimbiya lazima sai ta shiga cikin turakarta ta cabo ado na kure adaka. A can filin fadar kuwa, a yau mutane sunfi cika fiye da kullum saboda yau ne rana ta karshe a bikin sarautar, don haka duk inda mutum ya duba sai dai yaga mutane fulufulu babu masakar tsinke. Sarki Barham tare da yan majalisarsa na zaune acan sama bisa wani gini mai tudu. A hannun daman sarkin yaki kalmaru ne, a hannun hagunsa kuwa sarkin yaki ne na da, wato Ridwan mahaifin kalmaru. Waziri da mukarrabansa na gefe daya suna surutunsu na gulma. A wannan lokaci ana ta raye-raye da kade-kade a tsakiyar fadar don debewa mutane kewa, manyan baki suna ta shaye-shayensu suna kyalkyala dariya. A kusa da sarkin yaki kalmaru baiwa Zulaima ce itama ta caba ado saboda farinciki har idanunta na cika da kwalla saboda murna. Kwatsam! Sai akaji an buga tambari alamar cewa wani babban mutum zai fito daga cikin gidan sarautar. Al'amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan sbd an san cewa in banda sarki babu wanda ake bugawa wannan tambari, tunda shi kadai ne yake fitowa daga gidan sarautar. Shi kansa sarki Barham sai ya bude idanu yana kallon kofar gidan sarautar domin yaga wanda zai fito. Ba zato ba tsammani sai sarki yaga ashe gimbiya lazima ce ta fito, kuyangi da dakaru na take mata baya, ta caba ado na gaban kwatance, tana taku dai-dai tamkar toron dawisu. Wohoho! Nan fa gaba dayan jama'ar dake filin fadar suka kura mata idanu akayi tsit! Tamkar mutuwa ta kawo ziyara. In banda sautin sawun gimbiya da na masu take mata baya babu abinda kunne keji, Saboda ganin tsananin kyawun gimbiya lazima, Mutane da yawa basu san sa'adda suka wangame baki ba suna dalalar da yawu tamkar mayunwaciyar kura ta ga nama. Wasu mutane kuwa sai suka dimauce suka kama sumbatu. Shi kuwa sarki Barham bai sa'adda ya mike tsaye ba daga kan karagarsa yaje ya tari gimbiya a lokacin da itada kalmaru suka kurawa juna idanu ko kiftawa basa yi duk da cewa basu san juna ba. Bata san cewa shine sarkin yaki ba, sai bisa ganin takobin zinare a hannunsa. Shima kuma labarinta kawai yake ji a gari, amma bai taba ganinta ba. Koda sarki ya tari gimbiya lazima sai ya dubeta cikin matukar mamaki yace, Yake 'yata menene ya fito dake wajen gidan sarauta, alhalin baki taba fitowa ba?" Hakika kin rugaza mini shirina domin banso jama'a suka ganki ba a yanzu, So nayi sai a ranar da zan gabatar da gasar neman aurenki sannan zan bayyanaki kowa yaga wannan tsananin kyawun naki. Koda jin wannan batu sai gimbiya lazima tayi murmushi tace , "ya kai Abbana kayi sani cewa a cikin Karance-karance na da kuma bincikena a littattafai na tarihi wadanda masana da matsafa suka yi hasashe naga cewar wannan nahiya za'a sami wani sarkin yaki wanda zaiyi gagarumar jarumtakar da ba'a taba yin kamarta ba, Kuma zai auri yar sarkinsa. Bincikena ya nuna cewa wannan sarkin yaki shine na saba'in da bakwai a cikin jerin sarakan yakin kasarsa, kuma zai fito ne daga birnin da babu kamarsa a girman kasa da karfin arziki. Ya Abbana wannan sarkin yaki da ka nada tabbas ance shine na saba'in da bakwai, sannan kuma ka sani cewa a gaba daya nahiyar nan babu wata kasa mai girman tamu da karfin arzikinmu. Idan har hakane kuwa ashe wannan sarkin yaki daka nada shine zai zamo mijina. Kaga ashe banyi laifi ba don na fito domin naga mijin da zan aura." Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a jawabinta sai sarki Barham ya cika da tsananin mamaki kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubi gaba daya kuyangin dake bayan gimbiya lazima wadanda sunji duk abinda ta fadi yace, Duk wanda ya furta wannan zance ga wani daga cikinku a bakin ransa! " Koda gama fadin hakan sai sarki ya dubi gimbiya lazima yace, Yake 'yata daga yau ki guntse bakinki domin idan kika furta wannan zance 'yan majalisata suka ji zai iya haifar da tashin hankali da fitina wacce ba'a san karshenta ba. Gama fadin hakan keda wuya sai sarki ya kama hannun gimbiya lazima yajata izuwa inda karagarsa take. Har jarumi kalmaru ya mike tsaye zai baiwa gimbiya lazima kujerarsa ta zauna sai ta dubeshi cikin murmushi mai taushi tace, "Yi zamanka ya kai mai kai maza kasa, dirkar birnina. Kawai sai gimbiya ta zauna a kujerar dake kusa data kalmaru suka kama hira Ta fara da yimasa barka da samun nasarar gasar da akayi tsakaninsa da dan uwansa Hamsaru. Koda jin haka sai kalmaru ya dubeta cikin mamaki yace, dama kin san dan uwana Hamsaru? " Lazima tayi murmushi sannan tace, dan uwanka Hamsaru shine sarauyi na farko wanda ya tareni gaba da gaba ya bayyana mini sirrin zuciyarsa bisa yadda ta kamu da tsananin kaunata. Amma kuma ni dai-dai da dakika daya ban taba jin inasonsa ba. Na sani cewa duk garin nan babu wani attajiri mai yawan dukiyar mahaifinsa, Hatta mahaifina kuwa sarki. Gaba dayan sarakai da manyan kasar nan suna shakkar attajiri yunaru kuma suna girmamashi, sarki ne kawai baya shakkarsa amma yana shakkar tuggunsa. Kai kuwa ban taba ganinka

Chapter 3 of 10