Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
aiyukanki. Cikin sanyi jiki Zulaima ta juya ta nupi waje, Koda ta isa bakin kofar fita daga falon sai ta juyo tayiwa kalmaru wani irin kallo wanda yai matukar dugunzuma hankalinsa domin kallo ne mai nuna alamun cewa bazasu sake saduwa ba. Abinma da ya kara dugunzuma hankalin kalmaru da sarkin yaki suka hanzarta gama cin abinci nasu sannan suka fito kofar gida inda suka iske wani hadimin gidan a tsaye rike da dawakai kosassu guda biyu. Nan take sarkin yaki da kalmaru suka kama dawakan suka hau suka zaburesu da gudu izuwa gidan sarauta. Suna cikin tafiya ne kalmaru yaji jiri ya fara dibarsa kuma yaji wata irin tsananin kasala ta shigeshi irin wacce yaji tun daren jiya kawai sai sarkin yaki yaji kalmaru ya fado kasa tim! Daga kan dokinsa. Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalin sarkin yaki kenan yaja linzamin dokinsa yai turjiya ya sauko da sauri ya kama kalmaru ya tasheshi tsaye sannan ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da fargaba yace, "ya kai dana mai yai faru gareka haka?" Yanzu ashe dama bakada lfy amma ka boye mini baka gaya mini ba? " Kalmaru ya girgiza kai yace, "Haba ya Abbana yaya za'ayi nasan banida lfy amma na boye maka. Tun a jiya naji sauyin yanayi a jikina bayan naci abinci nasha ruwan inibi da baiwa Zulaima ta bani. Kuma ba wani abu naji ba face tsananin kasala. A yanzu kuwa Inajin kasalar fiye da wadda naji a jiya domin ina ganin ma cewa bazan iya sarrafa takobina ba." Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kuma ya kamu da tsananin bakin ciki ya takarkare ya kurma uban IHU! Kuma ya fashe da kukan bakin ciki. MAZA SUN FADI!!! Part 5 A yanzu kuwa Inajin kasalar fiye da wadda naji a jiya domin ina ganin ma cewa bazan iya sarrafa takobina ba " Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kuma ya kamu da tsananin bakin ciki ya takarkare ya kwara uban ihu a lokacin da zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, Kuma hawayen takaici ya zubo masa yace, "ya kai dana kayi sani cewa tabbas Zulaima taci amanarmu domin ko shakka babu itace ta zuba maka sinadarin da yasa maka kasala domin kada ka lashe wannan gasa da za'ayi. Duk yadda akayi dan uwana YUNARU ne yasa ta aikata wannan mummunan aiki sbd kawai Hamsaru ya sami nasara akanka. Koda jin wannan batu sai kalmaru ya dubi sarkin yaki cikin tsananin mamaki yace, "ya kai Abbana Yaza'ayi Zulaima taci amanarmu alhalin shekaru tana tare da kai tun kafin a haifeni kuma ko sau daya bata taba cin amanarka ba. Sarkin yaki ya gyada kai yace, "Ai mutum bashida tabbas ako yaushe yana iya sauya tunani." Koma dai menene da Zarar mun koma gida zansa takobi ta na sare Zulaima karshen zamana da ita yazo. Dajin haka sai kalmaru ya fashe da kuka yace, haba ya Abbana saboda me zaka kashe wadda take a matsayin mahaifiyata matar da ta dauki dawainiyata tayi rainona har na girma na zama mutum? " Sarkin yaki ya numfasa yace, "bani da wani zabi wanda yafi na kasheta yanzu domin idan na barta nan gaba kuma rayukanmu zata nema nida kai tunda har aka iya hada kai da ita yanzu domin a cutar dakai a hanaka samun damar gadon kujerata. Shin yanzu kana ganin zaka iya tarar Hamsaru a haka yadda kake jin rashin kwarin jikin naka?" Maimakon kalmaru ya bashi amsa,sai ya ja da baya kadan yana mai fuskarta sarkin yaki yace, "jarrabani ka gani ya Abbana, Ta ko wanne hali bazan yarda Hamsaru ya kai ni kasa ba" Kafin kalmaru ya gama rufe bakinsa tuni sarkin yaki ya zare takobinsa ya afka masa da dukkan karfinsa yana mai kai masa sara da suka. Ai kuwa sai kalmaru ya kasa maida martani yazamana cewa da kyar ma yake kare harin, Kafin a jima kalmaru ya galabaita ainun kuma dama gashi ya hadu da tsohon hannu masanin sirrin yaki kuma gashi sadauki. Nan take sarkin yaki ya doki kirjin kalmaru da kafa, ai kuwa sai kalmaru ya zube kasa wanwar ya yunkura domin ya mike ma ya kasa, Al'amarin da ya kara dugunzuma sarkin yaki kenan yaji kamar ya fashe da kuka. Nan take hawaye ya zubowa kalmaru ya dubi sarkin yaki cikin takaici da damuwa yace, "ka gafarceni ya kai Abbana hakika ni kaina yanzu na gamsu cewar na fadi a wannan gasar, Sarkin yaki yai shiru kansa a sukuye yana mai fadawa cikin kogin tunani mai zurfi sannnan ya dago kai ya dubi kalmaru cikin murmushi yace, "ya kai dana kayi sani cewa mai rai baya kasa yin motsi kuma hanyar kashe makahon kare yawa gareta. Yanzu wata dabara ta fado min wacce in dai muka bita lallai zamu sami nasara amma fa dole ne ka tsuke bakinka ka bar Wannnan al'amarin Sirri tsakanina da kai har abada domin duk ranar daka kuskura ka gayawa wani sai ka rasa wannan kujera kuma dole ne ka bar garin nan kayi nisa dashi yadda har abada bazaka iya dawowa ba. Lokacin da sarkin yaki yazo nan a zancensa sai kalmaru ya cika da matukar mamaki yace, ya kai Abbana wannan kuwa wacce irin dabara ce tazo maka haka?" Sarkin yaki ya numfasa yace, "Abinda za'a yi yanzu shine musanya kaya wato ka bani kayan yaki dake jikinka na sanya, Kaima ka sanya nawa kuma duk mu rufe fuskokinmu sannnan mu karasa fada. Muna zuwa ka wuce kusa da sarki ka zauna akan kujerar da aka tanadar mini. Kayi gaisuwa ga sarki amma kada ka kuskura ka budi baki kayi magana dashi yaji muryaka, Ni kuma zan shiga tsakiya fili na tari Hamsaru nayi wannan gasa dashi a madadinka tunda kai yanzu bakada kuzarin da zaka iya yin wannan gurmuzu. Wannnan ce kadai hanyar da zamu iya bi mu tabbatarda cewa sarauta sarkin yaki bata bar gidanmu ba kuma wannan ne kadai abinda zan iya yi maka na karshe a rayuwata domin gyara rayuwarka ta nan gaba. Lokacin da sarkin yaki ya zo nan a zancensa sai hankalin kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa yace, "ya kai Abbana ka tuna fa cewa kai yanzu ka tsufa, Hamsaru kuwa saurayi ne mai tashen kurciya da karfi ta yaya zaka ce ka tunkare shi,ina tsoron kada ya cutar dakai." Koda jin haka sai sarkin yaki yayi murmushi yace, ai faduwar mazan kwarai ba karamin aiki bane. Ina mai tabbatar maka da cewa har yanzu jarumtakata tana nan tunda acikin jini take a nono nasha. Hakika zan baka mamaki kuma zan nuna maka cewa kafin MAZA SU FADI sai anyi BAIKIN ARTABUN da yafi tunanin mai tunani. Maza ka cire kayanka ka bani kamar yadda na umurceka, Kafin ma kalmaru ya fara wani yunkuri tuni sarkin yaki ya fara cire nasa tufafin. Nan take sukayi musayar kaya ya zamana cewa shi sarkin yaki ya sanya kayan yakin kalmaru shi kuma ya sanya na sarkin yaki kowannensu ya rufe fuskarsa ya zamana cewa idanunsa kadai ake gani sannnan suka hau dawakan suka durfafi fada. Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce barewa bata gudu danta yayi rarrafe. Kalmaru da sarkin yaki suna matukar kama da juna tamkar an tsaga kara kuma tsawon jikinsu da kaurinsu duk yazo daya. Lokacin da sarkin yaki da kalmaru suka iso filin fada sai suka iske filin ya cika makil da jama'a babu masakar tsinke kuma kowa ya hallara hatta jarumi Hamsaru wanda za'ayi gasa dashi yana tsaye a tsakiyar fili cikin gagarumar shigar yaki rike da takobi da garkuwa, jama'a suna ta yimasa jinjina anata shewa. Makada da maroka kuwa sun bude nasu shafin kasuwanci, Sarki ne kawai bai fito ba. Nan take su kalmaru suka ratso cikin filin fadar ai kuwa ana hangosu sai dakaru suka bude musu hanya da karfin tsiya suka wuce izuwa tsakiyar filin. Sarkin yaki na isowa inda Hamsaru ke tsaye sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya ya sauka aka janye dokin nasa daga cikin fili, Shi kuma kalmaru sai ya wuce kai tsaye izuwa inda karagar mulki take wacce fadawa suka kewayeta. A wannan lokaci YUNARU dan uwan sarkin yaki Ridwan na zaune acan gefe daya cikin fadawa. Koda ya hango dan uwansa sarkin yaki ya taho inda suke zaune fuskarsa rufe sai ya cika da mamaki domin baiga dalilin da zaisa ya rufe fuskarsa ba, Wani abu da ya kara daure masa kai shine a iya saninsa da sarkin yaki ko yaushe yana tafiya ne cikin sauri da kuzari kamar zai tashi sama amma kuma yau gashi yana tafiya a hankali harma yana dan yin layi kamar wanda ya sha giya ya bugu. Nan take tunani ya fadowa YUNARU yace, acikin dukiyarsa anya kuwa sarkin yaki da kalmaru ba sauyin kaya sukayi ba yadda shi sarkin yakin zai yi wannan gasa a maimakon kalmaru. Ina ganin ma cewa saboda haka ne suka rufe fuskokinsu. MAZA SUN FADI!!! Part 6 "Anya kuwa sarkin yaki da kalmaru ba sauyin kaya sukayi ba yadda shi sarkin yakin zai yi wannan gasa a maimakon kalmaru. Ina ganin ma cewa saboda haka ne suka rufe fuskokinsu, Amma idan ma haka ne ai zan gane da Zarar an fara wannan gasa domin sinadarin da na baiwa Zulaima ta zubawa kalmaru a cikin ruwan inibin da yasha dole ne ya kasa yin wannan gurmuzu tunda ba zai taba samun kuzari da karfi ba a jikinsa. Ana fara yin wannan gasa dana Hamsaru zai kaishi kasa, To idan har zargina ya zama gaskiya to yaya zan iya wannan gurmuzu na tona musu asiri alhalin ni ba kowa bane daga cikin Alkalan gasar kuma in dai aka fara gasar babu damar a dakatar da ita har sai an kare" Koda yunaru yazo nan a tunaninsa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, Cikin rudewa ya mike tsaye domin ya karasa inda manyan fadawan sarki ke zaune gamida alkalan wannan gasa domin ya sanar dasu abinda yake zargi amma sai wani Badakare daga cikin dakarun sake tabbatarda Tsaro a wajen ya daka masa tsawa ya umurceshi daya koma wajensa ya zauna. A dai-dai-dai wannan lokaci ne akaji an fara buga tambura ana busa algaita alamar cewa ga sarki nan ya fito. Nan fa kowa ya mike tsaye har saida sarki ya shige cikin filin fadar tareda dakarunsa masu take masu baya ya isa kan karagarsa ta mulki ya zauna sannan kowa ya zauna. A wannan lokaci ne wazirin sarki ya mike tsaye ya fuskanci al'umma yace, "yaku jama'ar Birnin zamar kuyi sani cewa yanzu ne za'a fara wannan gagarumar gasa don samar da sabon sarkin yakin mu tunda namu lokacin yin murabus dinsa yayi. Tabbas wannan gasa da za'a yi yanzu za'ayi ta ne tsakanin jarumi Hamsaru da jarumi kalmaru wanda aka tabbatar da cewa a halin yanzu duk fadin garin nan babu wadansu jarumai wadanda suka fisu karfin damtse da iya yaki. Don haka yanzu ba tare da wani bata lokaci ba za'a fara wannan gasa. Koda gama fadin hakan sai waziri ya dubi mai buga tambari, take ya buga wani katon tambari, wanda ya cika filin fadar gaba daya ta amsa kuwwa.. Faruwar hakan ke da wuya sai sarkin yaki da Hamsaru suka gyara tsayuwar su kuma suka fara kewaya juna, kowannesu na tunanin yadda zai bullowa dayan. Kawai sai suka rugo da gudu izuwa kan junansu suka kacame da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya gamida naci. Hatta sauran jama'a gari da suke kallon wannan gurmuzu sai da hankalinsu ya dugunzuma ainun domin gani suke a koyaushe jaruman biyu zasu iya hallaka junansu. Koda aka sami tsawon kamar dakika dari uku da fara Wannnan artabu sai labari yasha bam-bam domin nan take sarkin yaki ya fara samun lagon Hamsaru ya zamana cewa Hamsaru baya iya maida martani sai kare kai. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan domin a saninsa duk sa'adda suke yiwa kansu horon yaki shida kalmaru suna shafe rabin sa'a ma suna gurmuzu kafin daya daga cikinsu ya fara samun lagon wani, Amma gashi yanzu daga fara wannan gurmuzu har kalmaru ya fara jigatashi. Su kansu 'yan kallo ma cika sukayi da tsananin mamaki musamman yunaru wanda hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da na kowa ya kara tabbatarda abinda ya ke zargi yaji kamar ya fashe da kuka saboda bakin ciki. Babban abinda yafi daurewa mutane kai shine kowa yasan irin tsananin karfin damtsen Hamsaru da jarumtakarsa amma yau gashi cikin kankanin lokaci an nuna masa cewa ruwa ba sa'an kwando bane. Haka dai Hamsaru yaci gaba da yin iya kokarinsa don ganin cewa baije kasa ba amma duk sa'adda sarkin yaki ya kawo masa sara ya kare sai yaji kamar katon dutse aka bugo masa har layi yake kamar zai fadi kasa amma sai ya cije yaki yarda yaje kasan. Ana cikin haka ne sarkin yaki ya shammaci Hamsaru ya gabza masa duka da kafa a kirji, saboda karfin dukkan sai da Hamsaru yai baya da gudu tamkar wanda aka janye da majaujawa sannan yayi wanwar a kasa. Ai kuwa sai filin fadar ya rude da shewa mutane suka rinka ihu suna cewa , MAZA SUN FADI " Saboda tsananin bakin ciki bisa da abinda ya faru sai yunaru ya kurma uban IHU kuma ya fashe da kuka sannan ya yunkura ya mike tsaye ya ruga inda jarumi kalmaru yake ya kwaye fuskarsa don ya tona masa asiri. Kwatsam! Sai kawai Aka ga gari yayi dundum! Ko ina ya disashe da tsananin duhu yadda ko tafin hannun mutum bazai iya gani ba. Al'amarin da ya razana mutane kenan aka fara guje-guje da iface-iface kenan. Wannan ce damar da kalmaru da sarkin yaki suka samu suka sauyin kaya a cikin duhun. Kafin hasken gari ya dawo sarkin yaki ya koma can kusa da sarki, shi kuma kalmaru ya dawo tsakiyar filin dagar ya tsaya. Faruwar hakan ke da wuya sai wannan duhu na ba zato ya yaye, gari ya sake yin haske fayau! Tamkar wani abu bai taba faruwa ba. Ashe duk wannan abu da ya faru sarki da fadawansa basu motsa daga inda suke zaune ba , haka ma dakaru masu tsaro, mutanen gari ne kawai suka firgice. Koda jama'a suka ga gari ya dawo yadda yake sai kuma aka rinka dawowa fada a guje anaci gaba da yin shewa da jinjina ga kalmaru bisa ga wannan nasara da yasamu ta lashe gasar sarkin yaki. Makida da mawaka kuwa suka kama aikinsu, shikuma Hamsaru sai ya kasa tashi tsaye tun sa'adda yaje kasa yaci gaba da zama dirshan yana zubar da hawayen takaici. A dai-dai wannan lokaci ne mahaifin Hamsaru wato YUNARU ya taso daga inda yake zaune ya taho wajen Hamsaru ya tasheshi tsaye ya dubeshi yace, Daina kuka ya kai dana Kayi sani cewa yanzu take zansa a rushe wannan gasa domin kuwa anyi algus acikin gasar." Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru yaja Hamsaru suka isa har gaban sarki suka risina suka kwashi gaisuwa, a sannan fadar tayi tsit! Kowa ya zuba musu idanu yana sauraro don aji abinda zasu fadi. Sarki ya dubi yunaru yace. " ya kai abdul Hamsaru fadi abinda ke bakinka muji" Yunaru yayi gyaran murya yace, " ya shugabana inada korafi akan wannan gasa har guda biyu wanda na tabbatarda cewa an shirya algus da manakisa kafin a sami nasarar kai dana kasa." Koda jin wannan batu sai mamaki yakama gaba daya jama'a dake fadar. Shi kuma kalmaru sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi. Da ganin haka sai sarkin yaki ya dafa kafadar kalmaru yace, ka kwantar da hankalinka babu abinda zai taba wannan nasara da ka samu domin naga akamar cewar ubangijinmu ma yana goyan bayanmu akan wannan gasa. " Sarki Barham ya dubi yunaru cikin mamaki yace, muna sauraronka ya abdul Hamsaru fadi korafinka muji. " Nan take fadar ta sake yin tsit! A karo na biyu tamkar mutuwa ta gifta. Yunaru ya dago kai ya dubi sarki cikin natsuwa yace , ya shugabana wannan gurmuzu da akayi bada kalmaru akayi ba da mahaifinsa akayi kaga kenan an zalunci dana yayi fada da wanda dama yafi shi jarumtaka " Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da tsananin mamaki, filin fadar ya rude da hayaniya kowa yana fadin albarkacin bakinsa har sai da sarki ya daga hannu sannan akayi shiru. Sarki Barham ya dubi yunaru yace, ya kai abu abdul munji korafinka amma sai kazo muna da cikakiyar sheda wadda zata tabbatar Muna da zarginka. Yunaru yace, kwarai kuwa inada cikakiyar hujja. Idan har kalmaru ne yasami nasarar kai dana kasa dole ne ya zamana cewa har a yanzu yanada karfi da kuzari a jikinsa. Na yarda ni na tareshi a yanzu mu fafata Idan ya Kai ni kasa ya tabbata cewa shine ya kai dana kasa tunda dai kowa a garin nan yasan cewa ni ban kasance jarumi ba, asalima ban taba fita yaki ba. Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya dugunzuma saboda yasan cewa ko kadan babu kuzari a jikin kalmaru, koda karamin yaro suka fafata ba zai iya kaishi kasa ba. MAZA SUN FADI part 7 Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaki ya dugunzuma saboda yasan cewa ko kadan babu kuzari a jikin kalmaru, koda karamin yaro zasu fafata ba zai iya kaishi kasa ba, Shikuma kalmaru sai ya dubi sarkin yaki yayi masa murmushi yana mai yi masa inkiya da kada ya damu zai iya. Nan take sarki Barham ya dubi kalmaru wanda ke tsaye a tsakiyar fili yace, "ya kai magajin sarkin yaki kaji korafin da wannan dan uwan mahaifinka yazo dashi, shin zaka iya kare kanka? " Kalmaru ya gyada kai yace, zan iya ya shugabana. " Koda jin haka sai yunaru ya karbi takobi a wajen wani Badakare ya dagata sama ya ruga da gudu izuwa kan kalmaru cikin mugun nupi, kai da gani kasan cewa so yake kawai ya kashe shi. Kalmaru ya tsaya cak! A inda yake ko motsi baiyi ba, kuma baiyi wani yunkuri ba na nupin kare kansa ba ko kai hari. Da isowar yunaru daf da kalmaru sai ya kawo masa mugun sara a wuya da nupin ya cire masa kai, cikin zafin nama kalmaru ya sunkuya takobin ta sari iska kafin yunaru ya juyo ya kawo masa wani harin sai kalmaru yasa hannunsa ya doki bayansa, Nan take yunaru ya kife kasa da rub da ciki har bakinsa ya fashe yana zubar jini. Ai kuwa sai fadar ta sake rudewa da shewa. Hamsaru da mahaifinsa yunaru kuwa sai suka kara kamuwa da tsananin bakin ciki. Nan take sarki ya kirawo kalmaru yaje daf dashi ya tsaya, sarki ya mike tsaye ya karbi wata takobi ta zinare daga hannun wazirinsa wacce duk wanda aka baiwa ita ya zama sarkin yakin kasar. Dama takobin a hannun sarkin yaki take amma tun a jiya sarki ya tura a karbota. Koda sarki ya karbi takobin ya juya zai mikawa kalmaru sai kawai akaji yunaru yace, "A dakata" Cikin mamaki kowa ya zuba masa idanu, yunaru ya mike tsaye yana mai goge jinin bakinsa, sannan ya tako ya taho wajen sarki ya sake risinawa a karo na biyu yace, " ya shugabana inada korafi na karshe. " Sarki ya gyada kai cikin alamun damuwa yace, zan baka dama ka bayyana korafinka, amma idan ya zamana cewa baka da cikakiyar hujja kawai hassada ce tasa ka fadeshi zansa a tsareka a kurkuku tswaon wata ukku. " Yunaru ya gyada kai yace "na yarda " Sarki yace fadi korafinka muna sauraro" Yunaru yai gyaran murya sannan yace, ya shugabana a dazu sa'adda kalmaru Ya sami nasarar kai dana kasa , nan take gari ya disashe da tsananin duhu ta yadda mutum ko tafin hannunsa baya gani. Ina mai tabbatar maka da cewa ba kusafin rana bane, tsafi ne sarki yaki yayi domin kawai su sauya tufafi shi da dansa yadda mutane baza su gani ba. Amma tabbas bada kalmaru akayi wannan gasa ba da sarkin yaki akayi ta" Koda jin wannan batu sai jikin kowa yai sanyi a filin fadar. Sarkin yaki da kalmaru kuwa sai hankalinsu ya dugunzuma ainun domin sun tabbatarda cewa asirin su ya tonu. Sarki yai shiru yana tunani da nazari har tsawon 'yan dakiku sannan ya dago kai ya dubi yunaru yace, hakika wannan korafi naka abin dubawa ne kuma ta hanya daya kadai zamu iya tabbatarda gaskiya " Nan take sarki yace, " ina BOKA HIZAINU YAKE?" Waziri yace, " ranka ya dade ai boka hizainu bai zoba, dama ya aiko an gaya mini cewa ba zai sami damar halarta wannan taro ba saboda ya shiga halwar wani aiki mai muhimmanci. " Koda jin haka sai hankalin sarki Barham ya tashi ya sake yin shiru yana tunani a karo na biyu. Daga can sai ya dubi waziri yace, "Ba zamu tashi daga nan ba har sai mun tabbatarda gaskiyar abinda muke zargi. Ya kai waziri na umurceka da ka tafi izuwa gidan boka hizainu yanzu ka sameshi, kace dashi nace ya duba mana yanzu ya gano mana gaskiya al'amarin. Koda gama fadi hakan sai sarki ya dubi mutum ukku daga cikin fadawansa wadanda ya Aminta dasu ya tabbatarda cewa sun kasance masu gaskiya yace dasu, ku kuma kubi waziri a yi komai a gabanku domin ku zamo shaida. Sannnan inason dakaru dari suyi muku rakiya izuwa gidan boka hizainu domin tsaron lafiyarku saboda wannan sarauta ta sarkin yaki sarauta ce mai muhimmancin gaske a cikin mulkin kasar nan, Idan har aka bayar da ita ga inda bai dace ba za'a sami babbar matsalar da zata iya janyo rushewar mulkina." Nan take waziri da fadawa ukku suka mike tsaye aka kawo musu dawakai ukku suka hau sannan dakaru dari suka yi musu rakiya. Tafiyarsu ke da wuya sai wadansu kyawawan 'yan mata su goma sha daya cikin kyakkyawar shiga iri daya suka shigo cikin tsakiyar filin tare da wadansu Makada, Take makadan suka fara aikinsu na doka manya ganguna suna fitar da sauti mai dadi da sanyaya rai. Su kuma yan matan suka fara tikar rawa iri daya a tare mai kayatarwa domin debewa sarki da jama'a dake wajen kewa kafin su waziri su dawo daga gidan boka hizainu. A sannan ne kuma kuyangi suka rinka kawowa sarki da yan majalisarsa kayan shaye-shaye da ya'yan ita tuwa suna ci dasha. Ana cikin wannan hali ne Hamsaru da mahaifinsa suka kebe gefe daya suka zauna. Hamsaru ya dubi yunaru yace, ya kai Abbana jiya ka gaya mini cewa na kwantar da hankalina lallai ka aiwatar da abinda kake ganin cewa sai na sami nasara a wannan gasa ta ko wanne hali, Yanzu gashi kalmaru ya kaini kasa a gaban kowa. Tabbas idansu waziri suka dawo daga gidan boka hizainu da amsar cewa ba tsafi su kalmaru sukayi ba, shikenan fa damarmu ta kare kuma burin da yake gabanmu na hana kalmaru samun damar haihuwa ya rushe. " Sa'adda Hamsaru yazo nan a zancensa sai yunaru ya kyakyale da dariyar mugunta. Al'amarin da yai matukar baiwa Hamsaru mamaki kenan, yai shiru kawai yana kura masa idanu kawai........ Daga can sai yunaru ya hade fuska yai shiru ga barin dariyar sannan yace, " ya kai dana inaso ka sani cewa, kada mage ba yankawa bane. Koda ban sami nasarar doraka akan karagar sarkin yaki ba yanzu, nan gaba sai na sami nasara, kuma koda ina tsare a cikin kurkukun. Kada ka manta cewa a gaba daya kasar nan babu wani attajiri mai yawan dukiyata. Inaso ka sani cewa babu abinda kudi ba zai iya siya ba, ka sani cewa rabin yan majalisar sarki yarana ne, ko cewa nayi su jefa kansu a cikin wuta sai sun jefa. Shi kansa waziri na hannun damana ne, a cikin fadawa ukkun ma da aka turasu gidan boka hizainu yanzu akwai mutum daya nawa, Ina tabbatar maka da cewa koda boka hizainu yace ba tsafi akayi ba zasu iya sauya maganar su ce yace tsafi ne, " Koda jin wannan batu sai Hamsaru yai ajiyar zuciya cikin alamun damuwa yace, abu daya nake tsoro. Idan har boka hizainu ya taso da kansa yazo ya bayarda shaida da bakinsa anan fada agaban kowa shirin nan duk da akayi ya watse. Ni kuma babban bakin cikina a yanzu shine naga sarki ya mikawa kalmaru wannan takobi ta zinare ya zamana cewa bani ya mikawa ba. Koda jin haka sai yunaru ya gyada kai yace, Tabbas abinda ka fada yanzu zai iya faruwa, amma duk da haka kada ka damu ka kwantar hankalinka. In dai ina raye a doron kasa koda kalmaru ya zama sarkin yakin birnin nan sai na shirya tuggun da sarki zai saukeshi daga kan matsayin ya maye gurbinsa da kai. Sai na jefa rayuwarsa da ta mahaifinsa cikin mugun tsananin da kunci yadda zasu gwammace mutuwa akan rayuwa. Lokacin da yunaru yazo nan a zancensa sai Hamsaru ya dubeshi cikin mamaki yace, Ya kai Abbana ni kuwa na dade inason nayi maka wata tambaya tun-tuni,amma ban samu dama ba. Wai shin menene dalilin da yasa ka tsananta gaba tsakaninka da sarkin yaki da dansa kalmaru alhalin kuma sarkin yaki ya kasance dan uwanka na jini tunda mahaifinku daya? " Yayin da yunaru yaji wannan tambaya daga bakin dansa Hamsaru sai yai ajiyar zuciya cikin alamun tsananin takaici yace, Gabata da dan uwana sarkin yaki ta samo asali ne tun muna yara kanana sbd mahaifinmu ya kaunaceshi fiye da kowa a cikin ya'yansa duk da kasancewar mun kai mu arba'in da uku. Ba wani abu bane yasa mahaifinmu yake son sarkin yaki ba fiye da kowa a cikin mu sai saboda irin jarumtakar da yake da ita da kuma tausayi. Shi dai mahaifinmu ma farauci ne wanda ya shahara a fagen farauta, domin Shi kadai yana iya shiga daji ya kamo katon zaki ko giwa yazo dasu cikin gari a raye. Bisa wannan dalili ne ya sami dukiya mai yawan gaske a wajen sarkin dake mulki a wannan zamani wanda shine mahaifin sarki Barham na yanzu, Tun a wannan lokaci sarkin yaso ya baiwa mahaifinmu sarautar sarkin yakinsa sbd ya jarraba jarumtakarsa yaga cewa babu wani ma yaki kamarsa a gaba daya nahiyar wanda idan dakaru sama da dubu suka lullubeshi da sara da suka sai ya kaisu kasa. Acikinmu gaba daya babu wanda ya gado jarumtakar mahaifinmu face sarkin yaki Ridwan. Bisa wannan dalili ne yake fifitashi akanmu, kuma ko gidan sarki baya zuwa tare dayanmu sai da Ridwan kadai. Wannan dalili yasa mu duka muka tsani Ridwan muka fara tunanin hanyar da zamu bi mu rabashi da duniyar gaba daya. MAZA SUN FADI !!! Part 8 Wannan dalili yasa mu duka muka tsani Ridwan muka fara tunanin hanyar da zamu bi mu rabashi da duniyar gaba daya. Amma sai muka kasa saboda shi mahaifin namu ya kareshi da sihirin tsafinsa. Kai hatta Sirrinkansa na daji da sirrin farauta a dajin mahaifinmu ya baiwa Ridwan duka. Mukuma sauran yayansa babu wanda ya samu guda daya. Lokacin da muka ga munyi iya kokarinmu akan mu hallaka Ridwan mun kasa, sai muka taru gaba dayanmu muka je gaban mahaifin namu inda muka iske shi a cikin turakarsa tare da Ridwan a zaune suna cin abinci tare. Koda mahaifin namu ya ganmu mu duka mun shigo cikin turakarsa mun zauna sai jikinsa yai sanyi ya tsame hannunsa daga cikin akushin da suke cin abinci, Ya dubemu cikin alamun mamaki da damuwa yace, ya ku ya'yana yau kuma menene ya faru kuka taro kanku gaba daya kukazo wajena?" Koda jin wannan tambaya sai na nayi ajiyar numfashi nace, "ya kai Abbanmu zanyi magana da yawun sauran yan uwana a matsayina na babbansu, muna da bukatar ka bamu amsar wata tambaya guda daya wacce ta jefamu cikin wasi-wasi gamida da tsananin damuwa da tashin hankali a tsawon shekaru. Wannan tambaya kuwa itace, "menene dalilin da yasa ka fi kaunar

Chapter 2 of 10