Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
ba, amma tun ina yarinya karama nake jin labarin irin jarumtakar da kayi a daji sa'adda kuka fita farauta kai da mahaifinka. Tun a lokacin nake kwadayin na ganka amma saboda nayi alkawarin sai na girma na zama cikakiyar budurwa sannnan zan yarda ka ganni shiyasa ban nemi a kawoka gareni ba. Lokacin da gimbiya lazima tazo dai-dai nan a zancensa sai sarkin yaki kalmaru ya kamu da tsananin farinciki kuma nan take yaji ya kamu da tsananin son gimbiya lazima. Abinda ya fara burgeshi game da ita shine, jin yarda ta dade a cikin jiran ranar da zasu hadu. Abinda kuma ya bashi mamaki shine yadda ta saki jiki dashi suke ta hira tamkar dama can dade tare. " To wai shin ma menene ya burgeta a game dashi har ta tsaya take hira dashi haka?" Nan take zuciyar kalmaru ta kamu da wasi-wasi yana mai zancen zuci a ransa yana cewa; Anya kuwa gimbiya zata iya bani wani gurbi acikin zuciyarta har muyi soyayya? Don ta saki jiki dani muna hira tana yi mini murmushi bai zama dole ba ta soni kamar yadda naji inasonta yanzu. Zaifi kyau na gaggauta cire sonta daga cikin Zuciyata domin babu yadda za'a ma na aureta a matsayinta na yar sarki ni kuma sarkin yaki bawan mahaifinta. ***** A can gidan attajiri yunaru kuwa, lokacin da suka koma gida shida dansa Hamsaru, Sai suka sa aka kawo musu giya tulu guda suka yita zubawa a kofi suna dirka saboda bakin ciki, har sai da suka bugu ainun suka kama sumbatu irin na wadanda suka zautu. Suna cikin wannan hali ne wani babban hadimin Hamsaru ya shigo cikin turakar ya risina yana mai duban Hamsaru yace, ya shugabana yau dai gashi can gimbiya lazima ta fito filin fada har ta zauna a kusa da sarkin yaki kalmaru suna ta yin hira. Koda da jin wannan batu sai Hamsaru ya kurma uban IHU ya naushi tulun giyar dake gabansa ya fashe, ruwan giyar ya zube kasa. Zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Daga can sai ya fashe da kuka ya dubi mahaifinsa yunaru yace, Ya kai Abbana yanzu gashi kanaji kana gani na rasa kujerar sarkin yaki, Babban burina na farko a duniya. Shin haka zaka zuba ido kuma na rasa gimbiya lazima maccen da tun ina yaro karami na kamu da tsananin sonta. Koda jin wannan batu sai yunaru ya kama rarrashinsa yace, Ka kwantar da hankalinka ya kai dana, kayi sani cewa indai ina numfashi a doron kasa sai na karbo maka takobin zinare daga hannun kalmaru, kuma sai ka auri gimbiya lazima. Inason ka kwantar da hankalinka ka sani cewa nan da cika wani lokaci zan shirya tuggun da kalmaru zai rasa kujerarsa ta sarkin yaki. Sa'adda yunaru yazo nan a jawabinsa sai hankalin Hamsaru ya kwanta ya kamu da tsananin farinciki ya dubeshi yace, ya kai Abbana kayi sani cewa na yarda da dari bisa dari saboda nasan cewa duk abinda kasa a gabanka sai kaga bayansa, baka faduwa Daga yau zanci gaba da dogoro da kai akan wadannan burika nawa. Amma fa ka sani cewa idan na rasa takobin zinare kuma na rasa gimbiya lazima zan iya rasa hankalina ko kuma na rasa rayuwata gaba daya. Attajiri yunaru ya sake kankame Hamsaru a jikinsa yace, "muddin ina numfashi bazaka taba rasa wadannan Abubuwa biyu ba. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 3 Attajiri yunaru ya sake kankame Hamsaru a jikinsa yace, muddin ina numfashi bazaka taba rasa wadannan Abubuwa biyu ba. Tunda safe aka fara wannan walima ta karshe a fada sai da rana ta fadi gari ya fara duhu sannan aka watse. Tsawon wannan lokaci sarkin yaki kalmaru da gimbiya lazima suna tare suna ta yin hira basu rabu ba. Kuma ko kadan basu lura cewar lokaci yayi nisa haka ba. Koda suka ga sarki ya sallami jama'a yana sallama da manyan bakinsa sai hankalinsu ya dugunzuma ainun domin ko kadan basu son rabuwa saboda jin dadin hirar da suke yi da kuma kasancewarsu tare. Kai inda za'a kyalesu zasu iya kwana a wajen suna hira. Nan dai filin fadar ya dade da watsewa ya zamana cewa babu kowa a wajen daga sarki da gimbiya lazima sai sarkin yaki kalmaru da dakaru masu tsaron gidan sarautar. A sannan ne sarki Barham ya taho gaban kalmaru sa'adda yake tsaye daf da gimbiya lazima, ya dubesu cikin murmushi yace, Ga dukkan alamu matasan nan biyu suna jin dadin wannan haduwa da sukayi a yau ta bazato." Koda jin haka sai kunya ta kama lazima da kalmaru suka sunkuyar da kawunansu kasa. Sarki Barham ya dafa kafadar kalmaru ya dubeshi cikin alamun matukar damuwa yace, ya kai jarumin jarumai kayi sani cewa yanzu ka taka wani matsayi na musamman a cikin masarautata don haka dole ne ka sami makiya da yawa. Daga yau ka zama makusancina kuma abokin shawarata saboda haka rayuwarka da lafiyarka suna da matukar muhimmanci a gareni. Dole ne duk inda kake ya zamana cewa akwai dakaru masu tsare lafiyarka walau a gida, a hanya ko a nan fada. Ka sani cewa yanzu bazaka tafi gida ba sai bayan munyi taro da dukkan dakarun yakina anan cikin gidan sarauta bayan munci abinci. Domin ka gansu gaba daya kuma ka gana dasu ka raba musu ayyukansu. Na sani cewar mahaifinka ya baka cikakken horo akan yadda zaka tafiyarda ayukanka don haka baza ka fuskanci wata matsala ba. Koda gama fadin hakan sai sarki Barham ya kira sarkin gida ya umurceshi da ya kai sarkin yaki izuwa bangaren da ake saukar manyan baki, Domin ya huta kafin lokacin cin abinci dare yayi. Nan take kuwa sarkin gida ya yiwa sarkin yaki kalmaru jagora izuwa wani bangare dabam a gidan sarauta. Sarki Barham da gimbiya lazima kuwa suka nufi nasu bangaren. Lokacin da sarki Barham da gimbiya lazima suka iso wata mararraba inda zasu rabu,shi ya nufi turakarsa itama ta nufi tata turakar, sai ya dubeta cikin alamun damuwa yace, akwai bukatar ki nutsu sossai kuma ki kare kanki domin yanzu ne zaki shiga wani sabon babi na rayuwa wanda baki taba tsintar kanki a ciki ba. Tuni na dade da yanke shawarar bisa cewar ba zan aurar dake ba face ga gwarzon jarumi wanda nasan zai iya kula dake ko a bayan raina. Tabbas na dade da sanin abinda kika gani a cikin bincikenki na littatafan da kika karanta. Sama da shekara goma shabiyar baya nasan cewa kalmaru ne zai zamo sarkin yaki na kuma shine wanda zaki aura, Jarumin da zai gawurta a wannan nahiya. Kuma nan gaba zai haifi dan da zaiyi abin bajintar da tafi tasa, amma sai nabar wannan al'amari a cikin Sirri domin saninsa a wajen fadawana ba karamin hadari bane. Sannnan kuma akwai wani babban Sirri da baki ganshi a cikin binciken da kikayi ba wanda shine Babban abin bakin ciki ga rayuwata wanda zai ruguje dukkan farin cikina. " Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lazima ya dugunzuma ainun ta dubi sarki cikin alamun tsananin damuwa tace, Ya kai Abbana menene Wannan Sirri wanda ni ban ganshi ba a cikin bincikena? " Koda jin wannan tambaya sai sarki ya gyada kai yace, kada ki damu zan sanar dake ko menene idan lokacin da ya dace ki sani yayi ." Koda gama fadin hakan sai sarki ya wuce izuwa cikin turakarsa itama gimbiya lazima sai ta wuce izuwa cikin tata turakar jikinta a sanyaye, Kuma hankalinta a dugunzume kamar zata fashe da kuka. Lokacin da sarkin gida ya kai sarkin yaki kalmaru cikin turakar da ake saukar manayan baki yaga yadda aka kawata dakin da kayan alatu gamida shimfidu na alfarma, ya kwatantata yadda suke tafiyar da rayuwarsu shida mahaifinsa sai ya ga ashe suna cikin talauci ne da kunci na rayuwa. Tabbas sarakai da attajirai sune suke rayuwa mafi dadi da kwanciyar hankali a duniya. Duk da cewar suma ba talakawa bane kuma sun rabi sarauta. Kalmaru na cikin wannan tunani ne aka fara kwankwasa masa kofa.kalmaru ya tambaya yace, Wanene nan?" Sarkin gida ne" Kalmaru yayi masa iznin ya shigo, ya bude kofar ya shigo ya dubi kalmaru yace, ranka ya dade sarki da gimbiya suna jiranka a dakin cin abinci. Da jin haka kalmaru ya mike tsaye yace, "muje ka kaini garesu" Nan take sarkin gida ya juya ya fice daga cikin dakin, Shi kuma kalmaru ya bishi a baya. Nan fa suka yi ta kutsawa cikin gidan dakaru suna risinawa suna gaishe shi. A sannan ne ya tabbatarda cewa ya zama sarkin yakin birnin zamar. Sa'adda suka shiga dakin cin abinci sai kalmaru ya iske sarki da gimbiya a zaune bisa kujerun dake karkashin wani katon benci wanda akansa an dora abinci iri-iri sama da kala dari amma ko fara cin abincin basu yiba. Nan take sarkin gida da ya rako kalmaru ya juya ya fice daga cikin dakin. Take sarki ya umurci kalmaru da ya zauna suci abinci tare. Ba tareda fargaba komai ba kalmaru ya zauna suka kama cin abincin. Har suka gama cin abinci babu wanda yace kala, Amma gimbiya da kalmaru suna ta satar kallon junansu har suka kasa kawar da kansu. Sarki yaga halinda suke ciki, kawai sai yayi murmushi kuma yai shiru baice komai ba. Bayan sun gama cin abinci sai suka mike suka fice daga cikin dakin cin abinci suka tunkari wani katon fili a cikin gidan sarautar. Suna isa filin suka yi arba da dakarun yaki sama da mutum miliyan ukku a tsaitsaye cikin shigar yaki rike da makamai. Koda dakaru suka ga sarki tare da sabon sarkin yaki sai gaba dayansu suka risina suka kwashi gaisuwa. A sannan ne sarki ya gabatar da kalmaru a garesu duk da cewa da yawansu sun sanshi tunda sun halarci taron gasar da akayi a filin fada ya karbi takobin zinare. Sarki yaja kunnen dakaru akan lallai su zamo masu ladabi da biyayya ga wannan sabon shugaban nasu. Kuma su bashi dukkan hadin kai domin yaji dadin gudanar aikinsa lafiya cikin nasara. Bayan sarki ya gama nasa jawabin sai ya kama hannun gimbiya lazima ya jata suka koma can gefe daya suka zubawa kalmaru idanu a lokacin da ya fara nasa jawabin ga dakaru. Nan take kalmaru ya fara rabawa dakarun horo na dabarun yaki kala-kala Al'amarin da yai matukar daurewa sarki kai kenan domin ko mahaifin kalmaru Ridwan bai taba zuwa da sababbun horon yaki ba irin wadannan. Sai da kalmaru ya shafe sama da sa'a daya da rabi yana koyawa dakarun sababbin dabarun yaki na ban al'ajabi Duk abinda ke faruwa sarki Barham da gimbiya lazima na kallo suna jin dadi. A lokacin ne sarki Barham ya dubi gimbiya lazima yace, hakika koda banyi irin binciken da kika yi ba a yanzu dana ga irin hikima da basirar kalmaru dole ne na gamsu cewa shine jarumin da zai yi gagarumin abin al'ajabin da babu wanda ya taba yin kamarsa a wannan nahiya tamu." Bayan sarkin yaki kalmaru ya gama baiwa dakarun yakin horo sai ya zabi dakaru guda hamsin kacal wadanda zasu rinka tsaron lafiyarsa a duk inda yake, Sannnan yayi wa sauran dakarun sallama akan gobe zai dawo yaci gaba da basu wadansu sababbin dabarun yaki. Nan take dakarun suka cika da tsananin mamaki domin su a tunaninsu basirar kalmaru ta kare amma kuma sai sukaji yace gobe ma idan ya dawo wadansu sababbin dabarun yaki zai basu. Nan dai kalmaru ya baro wajen dakarun yaje inda sarki Barham da gimbiya lazima suke. Wadannan dakarun guda hamsin na take masa baya. Kalmaru ya risina ga sarki yayi sallama ya juya zai tafi ba tare da Yayiwa gimbiya lazima sallama ba, kawai sai yaji gimbiya ta kirawoshi da ainihin sunansa. Cikin mamaki ya juyo ya dubeta a lokacin da sarki ya tafi ya barsu a wajen Gimbiya lazima ta dubi kalmaru cikin wani irin murmushi na musamman tace, laifin me nayi maka zaka tafi bakayi min sallama ba? Koda jin haka sai kalmaru yayi murmushi yace, ki gafarceni ya shugabata, kiyi sani cewa in dai kina tare da sarki Inajin nauyin na kalleki ma bare na iya yi miki magana. " Lazima ta gyada kai tace, na yarda da duk kalamanka. Ina mai sanar da kai cewa daren yau shine daren farko a rayuwata da zanyi barci mai dadi wanda bantaba yin kamarsa ba, ba don komai ba sai saboda na sami natsuwa da kwanciyar hankali. Na tabbatarda cewa wannan birni namu ya sami jarumi da zai iya kareshi daga dukkan abubuwan fargabar da nake tunanin zuwansu" Da jin haka sai kalmaru yayi murmushi yace, godiya a gareki ya shugabata kuma ina fatan abinda kike zato a kaina zai tabbata gaskiya. Lazima tace. Ai abinda ma nake zato ya wuce hakan, da sannu zan sanar da kai wani abu mai matukar muhimmanci wanda bazaka taba mancewa dashi ba Na barka lafiya, sai mun sake saduwa. Koda gama fadin hakan sai gimbiya ta juya ta nupi cikin Gidan sarauta tana waigensa. Shima sai ya tafi yana waigenta yana mamakin irin kalaman da gimbiya ta fada masa wadanda suka jefashi cikin wasi-wasi da rashin fahimta. * * * Lokacin da gari ya waye attajiri yunaru na zaune tare da dansa Hamsaru a turakarsa suna yin kalacin safe, Sai ga sarkin yaki kalmaru tare da dakaru sun shigo har cikin gidan Kalmaru na rike da wata takarda mai dauke da hatimin sarki a jiki Cikin fushi yunaru ya dubi kalmaru ya daka masa tsawa yace, menene ya kawo ka cikin gidina har da za ka shigo har cikin turakata tare da dakaru don muzantawa?" Kalmaru ya risina cikin alamun girmamawa yace. Ka gafarceni ya kai kawuna, kayi sani cewa nazo gidanka ne akan aikina bisa bin umurnin sarkina. Idan baka manta ba ranar da akayi gasar kujerar sarkin yaki kunyi alkawari da sarki cewar idan boka hizainu ya fadi cewar banyi amfani da sihiri ba bisa nasara dana samu zaka tafi kurkuku na tsawon wata shidda.? To yanzu nazo ne na tafi da kai izuwa can kurkukun bisa umurninsa. Koda jin wannan batu sai Hamsaru ya mike tsaye zumbur! Cikin tsananin fushi ya zare takobinsa ya dubi kalmaru a fusace yace, idan har kaga ka tafi da mahaifina sai idan ka kasheni. Koda gama fadin hakan sai yunaru yai sauri ya sha gaban Hamsaru yace, kada ka damu ya dana, Ai wata shidda kamar yanzu ne amma nayi maka alkawari sai kalmaru ya mika maka takobin zinare da hannunsa. Kada ka zargeshi da laifin komai akan aikinsa yake umurni yake bi kawai. " Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru ya juyo ya dubi kalmaru yace, muje ka cika aikinka. " MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 4 Gama fadin hakan keda wuya sai yunaru ya juyo ya dubi kalmaru yace, muje ka cika aikinka. " Nan take kalmaru yasa dakarunsa suka sawa yunaru sarka aka tusa keyarsa gaba aka fice daga cikin gidansa. Hamsaru yaga an tafi da mahaifinsa a gaban idanunsa yana ji yana gani, kuma babu abinda zai iya yi Sai ya kamu da tsananin bakin ciki, ya kwarara uban IHU ya kama saran komai dake falon har sai da ya tarwatsa komai sannan ya zauna a kasa ya fashe da kuka. Kwana biyu da kai attajiri yunaru kurkuku wasika tazo daga wata kasa da ake kira MUSAB. Birni musab na karkashin mulkin wani gawurtaccen jarumin sarki wanda ake kira SADAUKI DARYAN Sarki Daryan ya tara manyan zakwakuran mayakan da babu kamarsu a nahiyar gaba daya a yawa da iya yaki. Bisa wannan dalili ne gaba dayan sarakunan dake nahiyar suke matukar tsoronsa. Sarki Daryan ya kasance azzalumin sarki mara imani da tausayi ko kadan, Kuma a rayuwarsa babu abinda yake so sama da kudi da son tara dukiya. Gashi kuma birninsa cibiya ce babba ta kasuwanci a nahiyar gaba daya, amma sai ya sanya haraji mai tsantsanin yawa ga yan kasuwa yadda duk irin ribar dazasu samu sai sun biya harajin da ya fita yawa. Attajiri yunaru aminin sarki Daryan ne,saboda shine bafatake da yafi kowa biyansa haraji mafi tsoka idan yazo yin fatauci birninsa. Ban da ma haraji da yake biya. Yakan debo wadansu kudaden masu dumbin yawa ya baiwa sarki Daryan. Lokacin da aka kawo wasikar sarki Daryan cikin fadar sarki Barham gaba daya yan majalisarsa na nan, Shima sarkin yaki kalmaru yana zaune a gefe daya. Koda aka ji cewar wasikar ce daga sarki Daryan sai hankalin kowa ya dugunzuma domin an san cewa ba wasika bace ta alheri. Nan dai sarki Barham ya umurci maga-takarda da ya karanta wasikar a fili kowa yaji abinda ta kunsa. Nan take maga-takarda ya bude wasikar ya fara karantawa kamar haka... " wasika daga hannun sarkin sarakuna, Daryan ibini saumir mai mulkin kasar musab, Zuwa ga sarki Barham na birnin zamar "Ya kai wannan sarki kayi sani cewa labari yazo mana bisa irin rashin adalcin da kayi a masarautarka na bayarda sarautar sarkin yaki ga mutumin da bai dace ba, Wanda yai amfani da karfin sihiri wajen lashe gasar da akayi ya sami nasara. Sannan kuma kasa aka daure mahaifin wanda ya lashe gasar bisa gaskiya Ina mai gargadinka da ka hanzarta karbe takobin zinare daga hannun kalmaru ka mika ta ga Hamsaru dan yunaru kuma ka gaggauta fito da attajiri yunaru daga kurkuku ka bashi matsayi babba a fadarka daga nan zuwa cikar kwana bakwai. Idan har ka saba wannan ka'ida zamu yake ka domin mu tabbatarda adalci acikin kasarka" Lokacin da maga-takarda yazo nan a karatun wasikarsa tuni jikin sarki Barham ya kama karkarwa saboda tsananin fishi da takaici. Kawai sai ya mike tsaye zumbur! Ya kwace wasikar daga hannun maga-takarda ya yayyagata ya kama huci yana muzurai. A dai-dai wannan lokaci ne waziri da sauran fadawa suka zube kasa gaban sarki suna cewa, "zuciyarka tayi sanyi ya mai birnin zamar " sai da suka fadi hakan har sau uku sannan waziri ya mike tsaye ya fuskanci sarki yace, "ya shugabana inason ka bi al'amarin nan a hankali domin idan muka ce mu ketare umurnin sarki Daryan babu abinda zai haifar mana face mugun yaki wanda zai janyo asarar dumbin rayuka da dukiya. Kasani cewa sarki Daryan ya fimu yawan dakaru da karfin mayaka ba zamu taba samun nasara ba akansa kuma idan ya cimu da yaki kaima bazaka tsira da rayuwarka ba" Koda gama fadin hakan sai gaba dayan ragowar fadawan suka sake hada baki sukace, Abinda waziri ya fada gaskiya ne a tsaya ayi nazari da tunani kan haka. Koda jin hakan sai sarki Barham yai ajiyar zuciya cikin tsananin takaici sannan yace, Baza muyi gaggawa yanke hukunci ba bisa wannan al'amari don haka a bani zuwa gobe nayi tunani tukunna. Na sallami kowa ina bukatar na kadaita. Gama fadin hakan keda wuya sai fada ta watse kowa ya kama gabansa. A wannan lokaci sarkin yaki kalmaru yaso ace sarki ya kirashi sun kadaita domin suyi shawara amma daya ga sarki baice masa uffan ba sai ya tafi gida cikin damuwa. Kalmaru yana isa gida ya iske mahaifinsa Ridwan wato sarkin yaki na zaune a turakarsa tare da Zulaima suna hira cikin nishadi suna ta dariya. Koda suka ga kalmaru ya shigo jikinsa a sanyaye kuma fuskarsa cike da alamun matukar damuwa sai suma hankalinsu ya dugunzuma. Ridwan ya mike da sauri ya kama hannayen kalmaru ya zaunar dashi suka fuskanci juna yace, "Bani labari ya kai dana, menene ya faru a yau a fada ka dawo gida fuskarka na cike da alamar damuwa?" Koda jin wannan tambaya sai jarumi kalmaru yaja dogon numfashi sannan ya kwashe labarin duk abinda ya faru a fada ya zaiyane masu dangane da abinda wasikar sarki Daryan ta kunsa da kuma irin shawarar da fadawansa su ka bayar. Koda jin wannan batu sai Ridwan ya kyakyale da dariya, al'amarin da yai matukar ba wa Zulaima da kalmaru mamaki kenan. Daga can sarkin yaki Ridwan ya hade fuskarsa ya dubi kalmaru yace, ya kai dana idan ba ka mance ba a shekarar da nayi yaki na karshe Na umurceku ku ya'yana ku duka ku bini izuwa yakin. Gaba daya yan uwanka mutuwa sukayi a wannan yaki, kai ka dai ne ka dawo gida a raye saboda tsananin juriyarka, Nacinka da karfin damtsenka. A tarihin kasar nan ba'a taba yin matsainacin yaki ba irin wannan kuma yakin ya faru ne tsakanin kasar nan tamu da kasar musab, Kuma a wannan lokaci mahaifin sarki Daryan ne akan karagar Mulki. Hakika munyi bakin gurmuzu a wannan yaki kuma mun sha tsananin wuya mu da dakarun kasar nan ban taba tsammanin zamu sami nasara ba. Da kyar da sidin goshi na kai sarki saumir kasa na sare masa hannunsa na dama. Ina shirin zan kashe shi ne dansa Daryan yai wuf! Ya sureshi daga gabana ya dorashi akan doki suka janye yakin. Koda Ridwan yazo nan a zancensa sai nan take tunanin abinda ya faru a lokacin ya fadowa kalmaru. Duk da cewa a zamanin da akayi yakin kalmaru baifi shekara goma sha bakwai ba sai gashi yana tunowa da al'amarin tamkar a sannan abin ke faruwa. Abinda ya fara fadowa kalmaru a rai shine, Yadda filin yakin ya hargitse aka bude kasuwar dauka rayuka. Mazaje suka rinka faduwa kasa sa'adda sara da suka ya yawaita, ihun mazaje ya cika dodon Kunne, Sannan jini ya rinka fallatsi yana fantsama. Komai kallon kurillar mutum a wannan lokaci bai isa ya iya tantace bangaren da ke samun nasara ba a yakin domin kare jini biri jini akeyi. Duk da cewa kalmaru yaro ne sai gashi yana ta kutsawa ta cikin abokan gaba yana ta sara da suka, Duk inda yasa gabansa sai dai kaga maza na zubewa kasa. Yana cikin yin wannan mummunar barna ne tsulum! Yaga wani matashin saurayi sa'ansa daga cikin abokan gaba yasha gabansa, nan fa suka fara sabon azababben yaki shi da wannan sarauyi amma sai ya zamana cewa karfinnsu yazo daya, Domin sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna kaiwa junansu sara da suka amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba har ya zamana cewa takubbansu sun dakushe. Ba shiri suka yadda takubbansu suka kaure da fadan hannu suna masu naushi da bugun juna. Nan da nan kuwa suka hadawa kansu jini da majina tun suna da kuzarinsu har sai da ta kai cewa sun galabaita ainun suna maye a tsaye kamar sun sha giya sun bugu. Amma saboda naci da taurin zuciya basu fasa bugun juna ba. Suna cikin wannan hali ne sukaji an busa kahon janye yakin daga bangaren kasar musab. Bisa dole suka ja da baya cikin tsananin takaici suna huci da haki da hararar juna A sannan ne wancan jarumin saurayi ya bushe da dariyar mugunta yace, "Sunana yarima Daryan "da" ga sarki saumir mai birnin musab. Nine DODON MAZA kuma mai kai maza kasa. Yaro kayi arziki da aka tsaida wannan yaki.amma da sai na kaika barzahu." Koda jin wannan batu sai shima kalmaru ya bushe da dariya yace, "kai.yaro ai jiki magayi ne, ina mai tabbatar maka da cewa nine jarumi kalmaru" da" ga sarkin yaki Ridwan na birnin zamar. In ba don an busa kahon tsayarda wannan yaki ba da tuni MAZA SUN FADI amma nayi maka alkawari komai daren dadewa nan da shekaru dari idan muka sake haduwa a filin yaki sai na kaika kasa kuma na kashe ka. Da jin haka sai Daryan yayi kaki ya tofar da jini sannan ya dubi kalmaru yace, shikenan mu zuba mugani ai lokaci shine maganin gardama, Ni da kai zanga wanda zai cika Alkawarinsa, lokacin da yazo dai-dai a tunaninsa ne yaji mahaifinsa Ridwan ya dafa kafadarsa. Nan take yayi firgigit! Kamar wanda ya farka daga barci. Ridwan ya dubeshi yace, ya kai dana lokaci yayi da duniya zata sanka, ina mai tabbatar maka da cewa dole ne muyi yaki da birnin musab a karo na biyu. Kuma kaine zaka jagoranci wannan yaki Babban takaicina shine, ni yanzu na tsufa bazan iya fita yaki ba. Ga kuma lalurar dake damuna mai alaka da sihiri, amma da sai na fita yakin nan na karasa aikin dana fara." Koda jin wannan batu sai kalmaru ya dubi Ridwan cikin mamaki yace, "ya kai Abbana me kake nupi da ka karasa aikin da ka fara? Ridwan yayi murmushi sannan yace "A wancan yakin danayi na karshe na sarewa sarkinsu hannu daya. Zanso ace yanzu zamu sake haduwa mu fafata na kaishi kasa gaba daya, ina nufin na kashe shi domin na huce takaicin da ya cusa mini acikin Zuciyata. Inaso ka sani cewa mahaifin Daryan wato sarki saumir ya dasa mini bakin ciki da har abada ba zai kankare ba daga cikin Zuciyata face naga na kashe shi da hannuna domin a wancan yakin ne na rasa dukkan ragowar ya'yana yan uwanka su biyu wadanda suka kasance yayyenka. Koda Ridwan yazo nan a zancensa sai ya fashe da kuka a lokacin da itama Zulaima ta fashe da kukan. Al'amarin da ya jefa tsananin tausayinsu kenan a cikin zuciyar kalmaru shima ya kama kukan. Daga can sai Ridwan ya dago kai ya dubi kalmaru yana mai share hawayen idanunsa yace, ya kai dana abinda nake so da kai shine, idan har sarki ya kiraka ya nemi shawararka bisa wasikar da sarki Daryan ya aiko, Ka gaya masa cewar kawai a aika masa da amsar wasikar raddi ta yakin. Ina mai tabbatar maka da cewa wannan yaki da za'a yi shine yakin farko da sunnanka zai shahara ko ina a wannan nahiya. Kuma shine yakin da zaka kawo babban ci gaba a kasar nan. Kuma ina san ran cewa zaka karasa abinda na kasa karasawa. Ka cire tsoro da fargaba komai daga cikin zuciyarka kamar yadda na sanka da dakakkiyar zuciya irin ta manyan mazaje tun kana yaro karami. Koda jin wannan batu sai kalmaru ya mike tsaye zumbur! A lokacin da jikinsa ya kama tsuma ya dubi Ridwan yace, Ya kai Abbana nayi maka alkawari komai rintsi da tsanani sai na cika wannan aiki naka kuma sai na ga bayan dukkan makiyan sarki da makiyan wannan kasa tamu mai albarka. Koda jin haka sai farinciki ya lullube Ridwan shima ya mike tsaye ya rungume kalmaru yana mai yi masa jinjina da godiya. Nima a lokacin na mike tsaye na rufe littafi na wuce izuwa masallaci. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 2 PART 5 Sarki Barham bai nemi sarkin yaki kalmaru ba har sai da dare ya raba sannan ya taso da kansa a sirrance ba tare da kowa ya sani ba yazo gidan sarkin yaki Ridwan. Koda masu gadin gidan suka ga sarki Barham yazo da kansa sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa sannan suka yi masa iso har izuwa cikin dakin kalmaru. A wannan lokaci Ridwan da baiwa Zulaima tuni sun dade da yin barci basu san abinda ke faruwa ba. Kalmaru na tsaye a cikin dakinsa yana kai kawo yana tunani da zullumi bisa wannan al'amari da ya taso sai kawai yaji an turo kofar dakin an shigo. Cikin zafin nama ya zare takobinsa domin a zatonsa makiya ne suka kawo harin shammace. Kwatsam! Sai ya ga ashe sarki ne da kansa yazo, cikin tsananin mamaki ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dubi sarki yace, Ya shugabana menene ya kawoka gidan mu a cikin wannan tsohon dare?" Ai kamata yayi ka aiko nazo, bai kamata kazo da kanka ba, ana cikin irin wannan hali domin rayuwarka ma abar farauta ce a wajen makiya. Koda jin wannan batu sai sarki Barham yayi murmushi yace, ai shi makiyi kullum a cikin kawo harin shammace yake don haka dole ne kaima ka rinka shammatarsa, idan kanason ka tsira daga sharrinsa. Babu wanda zai taba tunanin cewa zan fito daga cikin gidan sarauta ni ka dai a cikin wannan dare, shi yasa ma kaga banzo ba tare da dakaru. Kasani cewa makiyanmu suna jikinmu don haka dole ne muyi taka tsan-tsan a cikin duk abinda za mu kulla ya zamana cewa muna da cikakken Sirri. Yanzu inason ka rufe kofar

Chapter 4 of 10