Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
nacinsa Daryan kasa hallakashi. Ana cikin haka ne Daryan ya sami nasarar buge takobi guda daga hannun kalmaru ta fadi can gefe daya. Kafin kalmaru ya ruga inda takobin tasa take ya daukota tuni Daryan ya gabza masa wawan dundu a gadon bayansa, take kalmaru yaji kamar kashin baya nasa ya karye bai san sa'adda ya kife kasa ba da rub da ciki yana mai rusa uban ihu, kawai sai Daryan ya daga takubbansa biyu sama da nufin ya tsira gadon bayan kalmaru, A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya lazima ta hango abinda ke shirin faruwa ga kalmaru kawai sai ta falfalo da azababben gudu daga inda take, saboda karfin gudun har tashi sama take tana tsallake mutane amma da zarar kafarta ta taba kasa sai kaga ta sake yin sama, kafin takubban sarki Daryan su caki bayan kalmaru tuni gimbiya lazima ta doki kugun sarki Daryan da kafafunta biyu , Saboda karfin dukan sai da yayi sama fuskarsa ta gwaru da garkuwar wani Badakare, Take hakorinsa guda yayi fitar burgu daga cikin bakinsa ya fado kasa tim kuma magashiyan amma sai ya yunkura ya mike tsaye ya juyo ya dubi inda kalmaru ke kwance kawai sai ya hango gimbiya lazima ta sunkuya ta dauki kalmaru ta sabashi a gadon bayanta tamkar ta saba silin kara, Kawai sai ta juya da baya taci gaba da gudu kuma kuma tana saran abokan gaba, A sannan ne filin yakin ya dada kacamewa fiye da ko yaushe, Aka ci gaba da asarar dubunnan rayuka ba adadi. Cikin tsananin fushi sarki sarki Daryan ya kurma uban ihu yayin da bakinsa ke yoyon jini kuma kansa ya fara kumbura jini yaci gaba da dibarsa amma duk da haka sai ya yunkura da nufin ya ruga ya iske jarumin da ya dauke kalmaru amma sai dakarunsa suka yi wuf suka rike shi. Adaidai wannan lokacin ma karfinsa gaba daya ya kare ya sulale kasa sumamme. Koda kowanne bangare suka ga shugabansu na cikin mugun hali sai aka shiga busa kahon janyewa daga filin yaki, Nan da nan kowacce runduna taja da baya aka daina yakin, kowanne bangare suka koma sansaninsu ya zamana cewa filin yakin ya watse babu kowa sai gawarwaki dake kwance a kasa fululu ba adadi sai kuma jini da ya malala yana ta gudu akan kasa, kai kace idaniyar ruwa ce a dajin Hajarul maut inda aka fafata kazamin yaki tsakanin dakarun birnin zamar da dakarun birnin sarki Daryan, A can birnin zamar kuwa bayan sarkin yaki kalmaru ya kwashi dakaru yaki sun fice daga cikin birnin, Magariba nayi sa'adda gari yayi duhu sai ga wadansu dakarun sojojin haya kimanin su dubu dari sun zo a cikin siffar fatake dauke da hajoji bisa dawakai, rakumai, da alfadarai, Ashe a cikin buhunhunan can kasan hajojin akwai makamansu na yaki a boye, Kowanne Badakare yayi shiga irinta bafatake, babu yadda za'a yi a gane cewa shi ba bafatake ne ba. Da isowar wadannan fatake sai ga Hamsaru dan attajiri yunaru yazo daga cikin gari. Nan take ya gabatar da fataken a wajen masu gadin kofar yasanar dasu cewa ai bakin mahaifinsa ne kuma dama an san da zuwansu Ba tare da anyi musu wani kwakkwaran bincike ba sai a ka bude musu kofa suka kado ababan hawansu, Suka shigo cikin gari, maimakon Hamsaru ya kai wadannan fataken inda suka saba saukar bakinsu sai ya hadasu da wani hadimin gidansu suka bi wata barauniyar hanya suka tafi izuwa wani gida dake can bayan gari nesa da mutane sossai, Shi dai wannan gida mallakin wazirin sarki Barham ne kuma gidan gona ne inda ake kiwon dabobbi kuma ana ajiye amfanin gona, Gidan yana da girma sossai don haka zai iya daukar sama da mutum dubu dari uku ma. Da isar wadannan dakarun sojojin haya sai suka iske tuni an shirya musu abincinsu don haka sai suka yi murna. Nan take suka zauna suka cika cikinsu sukayi hani'an kowannensu ya sami wuri ya kwanta yana huce gajiya. *** *** *** Har yanzu akwai sauran rina akaba domin kuwa akwai sauran asarar rayuka kawai kuyi hakuri ku biyoni izuwa gobe. MAZA SUN FADI!!!! LITTAFI NA 3 PART 6 Da isar wadannan dakarun sojojin haya sai suka iske tuni an shirya musu abincinsu don haka sai suka yi murna. Nan take suka zauna suka cika cikinsu sukayi hani'an kowannensu ya sami wuri ya kwanta yana huce gajiya. Al'amarin Hamsaru kuwa bai zame ko ina ba sai gidan waziri inda suka kebe a cikin turakarsa ta barci, Bayan sun rufe kofofin dakin da tagoginsa don kada wani yaji abinda zasu tattauna sai suka zauna suka fara magana a acikin karamar murya tamkar masu yin rada, A sannan ne Hamsaru ya dubi waziri cikin murmushin farinciki yace ya shugabana na sami nasarar shigowa da dakarun mu na sojojin haya ko kyakkyawan bincike ba'a yi ba a kansu. Koda jin wannan batu sai waziri yai shiru fuskarsa na nuna alamun damuwa yana tunani, Hamsaru ya dafashi yace ya shugabana me ya faru? " Shin kana ganin cewa asirinmu zai tonu ne?" Waziri ya kawo gauron numfashi ya ajiye sannan yace, Nayi mamakin da kace ba'a yi kyakkyawan bincike ba akansu alhalin sanan cewa yanzu dole ne sarki yasa a tsananta tsaro tunda manyan dakarun mu na yaki wadanda ake takama dasu basu nan sun fita yaki. Hamsaru yayi murmushi yace karka ka damu ai tunda yammacin jiya na siye gaba dayan masu gadin kofar birnin, Domin babu wanda ban baiwa albashinsa sau uku ba, A yau dinnan kuma na nuna musu ne cewar hajar da aka kawowa mahaifina riba ce mai, kuma na kara baiwa kowa albashinsa sau biyu, Shiyasa suka gamsu suka ki yin kwakwaran bincike tunda sun san cewa basu taba samun kudade masu yawan haka ba. Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariya yace to yanzu naji zance. Ai inda ba kayi wannan dabara ba da sai nace sarki Barham tarko ya haka kawai jira yake mu fada cikinsa ya maida kasa ya rufe, Yanzu na gamsu cewa mun tsallake matakin farko a cikin shirinmu, saura mataki na biyu yaya zaka shirya shi? " Hamsaru ya numfasa yace,a yanzu haka nasa a lura da duk motsin sarki a cikin gidan sarautar har izuwa lokacin da dare zai raba domin musan acikin dakin da zamu riskeshi muyi masa kisan farat daya, Waziri yayi murmushi yace wannan ma yayi dai- dai,Mataki na uku fa? Hamsaru ya mike tsaye yayi 'yar tafiya taku uku sannan ya juyo ya fuskanci waziri yace mataki na uku yayin da dare ya raba, Zan jagoranci wadannan dakarun sojojin haya namu na tafi dasu izuwa can gidan sarauta, Kasani cewa dama inada mutanena acikin dakarun dake cikin gidan sarautar don haka da zarar munje kusa zamu harba kibiyar wuta sama domin su gane cewa mun iso. Sune zasu kashe masu gadin kofar gidan sarautar su bude mana kofar mu fada ciki. Kafin muje zan nunawa dakaru namu taswirar hanyoyin gidan sarautar gaba daya da duk inda dakaru ke tsaitsaye don haka muna shiga zamu fara amfani da harba kibiyoyi mu kawar da dukkanin dakarun dake sama bisa benaye da wadanda ke kan kwanoni. Sannu da sannu cikin sauri da daukar numfashi zamu yi ta yiwa dakarun gidan kissan mummuke, Kafin su ankara mun kashe kaso biyu cikin ukun su kaga kenan ko fito na fito mukayi da sauran dakarun gidan zamu iya gamawa dasu cikin kankanin lokaci, Kasan dai babu yadda zaiyi damu tunda sarkin yawa yafi sarkin karfi barema ko ni Kadai ma ina ganin zan iya dashi, Koda jin haka sai waziri yayi caraf yace kada ka kuskura kace zakayi wannan ganganci, Duk wannan jarumtakar taka da kake gani ba komai bace akan ta sarki Barham, An gayamaka cewa ana zama sarki ne a banza? " Kada kamanta da alkawarinmu cewar ni da kaina zan kashe sarki dan haka kada dayanku ya kuskura ya kasheshi kamar yadda mukayi alkawari cewa mahaifinka ne zai kashe dan uwansa sarkin yaki Ridwan da hannunsa lallai nima haka nake so na kashe dan uwana sarki Barham da hannuna, Koda jin wannan batu sai Hamsaru ya bushe da dariyar mugunta yace,kwantarda hankalinka ya shugabana yadda duk ka tsara haka za'a yi, Dole ne mu yiwa sarki Barham juyin mulki ko don na sami damar mallakar gimbiya lazima ta kowane hali. Lallai ne a wannan karon maza zasu fadi kasa ina nufin dole ne sarki Barham ya zama gawa dashi da babban makiyina kalmaru, Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar mugunta yace ai kama daina batun kalmaru domin yanzu tuni ya dade da faduwa kasa, Tunda na tabbatarda cewar babu yadda za'ayi yasami nasara yaki akan sarki Daryan don ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza, Hamsaru ya kyakyale da dariya yace zancenka dutse ne, Kamar yadda su waziri suka tsara haka duk al'amarin ya kasance wato lokacin da dare ya raba sun sami nasarar shiga har cikin gidan sarautar kuma sun kashe sama da dakaru dubu arba'in masu tsaron gidan sarautar, kai sai da suka sami nasarar shiga har cikin turakar sarki Barham ta barci. Nan take suka kewaye gadonsa koda suka yaye mayafin da yake lullube dashi sai suka ga babu komai face tulin tsumman kara, Al'amarin da yayi matukar razana su kenan, idanunsu suka zazzaro, waziri ya dubi Hamsaru yace, duk yadda akayi sarki yayi tunanin cewa zamu shirya mada juyin mulki amma duk yadda akayi yana nan a boye cikin gidan nan don haka muyi sauri mu bazama nemansa tun kafin ya nemo agajin dakaru daga cikin gari, in ba haka ba kuwa gaba dayan shirinmu zai wargaje. Gama fadin haka keda wuya sai suka fito gaba dayansu daga cikin turakar sarki Barham suka rarrabu suka rinka shiga daki daki sako da logo da lunguna na gidan sarautar ko ina da ina suna neman sarki Barham, Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce in zaka haka ramin mugunta to ka ginashi dai- dai da kai, Abinda su waziri basu sani ba shine tun kafin su sarkin yaki kalmaru su tafi sai da sarki Barham yayi tunanin cewa lallai su waziri zasu iya amfani da wannan dama su yi yunkurin juyin mulki bisa wannan dalili ne shima yayi nasa shirin a boye ya tanadi mayakansa sama da dubu dari biyu a wajen gidan sarautar suka yi kwanto a cikin wani rusasshen gida wanda yafi shekara dari da rugujewa kuma ba a shigarsa, Lokacin da dare ya soma sai sarki Barham yayi shiga irinta dakarun dake tsaron gidan sarautar ya sulale daga cikin dakinsa ya fice daga cikin gidan sarautar yaje ya iske wadancan dakaru nasa dake cikin rusasshen gidan, Dama daga cikin rusasshen gidan ana iya hango duk abinda ke faruwa a kofar gidan sarautar, Don haka su sarki Barham na nan labe suka hango an harba kibiyar wuta wato su Hamsaru sun iso kenan suna yiwa jama'arsu inkiya, har aka budewa su Hamsaru kofar gidan sarautar suka shiga su sarki Barham basuyi wani Yunkuri ba sai da suka bari sun dan jima da shiga sannan suka fito daga inda suke boye suka nufi kofar gidan sarautar, Da zuwa sai suka iske kofar a rufe, kawai sai sarki Barham ya kwankwasa kofar Badakaren dake bakin kofar a sannan yana daga cikin irin yaran waziri don haka sai ya tambaya yace wanene yake buga mana kofa?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Barham yayi irin murya waziri yace nine. Cikin sauri Badakaren ya bude kofar, koda su sarki suka shigo yayi arba dasu sai ya firgita ya yunkura da nufin ya ruga da baya amma sai sarki Barham ya cakumoshi ya soko masa Wuka a makoshinsa yai jifa da gawarsa kuma ya tofawa gawarsa yawu yace wannan shine sakamakon masu cin amana. Nan take sarki Barham ya juya ya dubi gaba dayan dakarun dake bayansa yace to ku shirya yanzu ne muma zamuyi namu gagarumin yakin kamar yadda su kalmaru keyin nasu a can dajin Hajarul maut, Yana gama fadin haka ya raba dakarun izuwa kaso hudu, Kaso daya ya turasu suka tsare gabashin gidan sannan sauran kason biyun suka tare yamma da kudu shi kuma sai ya jagoranci kaso na karshe suka durfafi arewacin gidan sarautar. Su sarki Barham suka durfafi hanyar da zata kaisu inda turakarsa take,ai kuwa suna isowa wani babban fili sai suka yi kacibis dasu Hamsaru nan fa aka tsaya ankayi cirko-cirko ana kallon kallon, Hamsaru ya dubi dakarun dake bayansa su dubu dari yace, maza ku karkasu izuwa kowanne bangare na gidan domin ansamu a tsakiya, Kowannenku yayi yaki iya ransa kada ku bari a kamaku a raye sai dai gawarku, Nan take dakarun suka rarrabu wadanda suka rage a bayansa basu fi su dubu ashirin ba, Koda ganin haka sai sarki Barham ya bushe da dariya. Lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubi Hamsaru a fusace yace ya kai Hamsaru dan yunaru kayi sani cewa ko zaki ya fadi yafi gaban wargi, An gayamaka cewa ana zama sarki a banza ne?" Ai na sani cewa da dadewa mahaifinka Yanason ya gaji karagata amma bai sami damar da xaiyi mini juyin mulki sai a yanzu da wannan yaki ya taso tsakanina da sarki Daryan, Dama na sani cewa zai iya hada kai da shi don ganin bayana bisa taimakon mahaifinka wanda yanzu yana tsare a gidan kurkuku, To ka sani cewa bana bukatar na kasheku kai da waziri dan uwana maci amana da kuma mahaifinka yunaru, So nake kuje ku taya yunaru zama a kurkuku har izuwa karshen mulkina bisa wannan babban laifi da kuka aikata domin ya zamo babban abin bakin ciki ga rayuwarku, Koda sarki Barham Yazo nan a zancensa sai Hamsaru ya bushe da dariya yace kai wannan sarki kayi sani cewa kada mage ba yanka bane, ka bar ganin cewa dakarunka sun kewaye mu a cikin gidan nan, hakan ba zata hana mu cika burinmu ba akanka, Idan har kaga a yau dinnan waziri bai hau karagar Mulkinka ba to bana numfashi a doron kasa kuma ka sani cewa ko mu bamu sami nasarar kawar da kai ba da zarar sarki Daryan ya gama dasu kalmaru acan dajin Hajarul maut babu inda zai doso sai anan tare da miliyoyin dakarunsa yazo ya cika da yaki har gida, kuma ya fito da mahaifina daga kurkuku, Kafin Hamsaru ya gama rufe bakinsa tuni sarki Barham ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace karyaka tasha karya yaro ga maza nan bisa kanka, Yana gama fadin haka ya daga takobinsa sama su Hamsaru sai suka daga nasu takubban aka rugo izuwa kan juna aka ruguntsume da masifaffan yaki Adaidai wannan lokaci ne gaba daya gidan sarautar ya hargitse da ihun mazaje gamida karafkiyar karafa, matan da ke cikin gida suna barci ba shiri suka farka a firgice suka rinka neman ma maboya, Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi nan da nan aka kashe gaba dayan wadannan dakarun sojojin haya wadanda su Hamsaru suka zo dasu ya zamana cewa saura mutum biyu kacal ana ta faman gurmuzu dasu kuma ba wasu bane face Hamsaru da waziri. *** *** *** Karshen dadi karewa!!! ~~~~~~~~~~~~~~~ Shin wanene zai samu nasara a cikin wannan yaki da akeyi a gidan sarauta tsakanin sarki Barham dasu Hamsaru da waziri? " Mu hadu a Littafi na hudu don jin cigaban wannan labari. Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 1 Shi dai waziri ya rufe jikinsa da fuskarsa gaba daya, idanunsa ne kadai a waje kuma yana da bakaken tufafi yana ta ragargazar dakarun sarki ya zame musu alakakai an rasa yadda za'a yi dashi acan wani bangaren daban na gidan sarautar, Shi kuwa Hamsaru an rasa wanda zai kusanceshi sai sarki kuma sai da suka shafe sama da sa'a guda suna gurmuzu amma dayansu ya kasa samun cutar da dayan, Al'amarin da yayi matukar baiwa Hamsaru mamaki kenan domin shi a zatonsa zai iya gamawa da sarki farat daya, nan fa hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya fahimci cewar lallai dukkan shirinsu ya lalace kuma idan ya tsaya yaci gaba da wannnan yaki da sarki komai zai iya faruwa, ko dai karfinsa ya kare, sarki ya sami logonsa ko kuma ya rasa rayuwarsa gaba daya Abu daya ne ya dan kara masa kwarin gwiwa kuma ba komai bane face jiyo karafkiyar karafa a can wani bangaren daban na gidan sarautar, Hakan ne ya tabbatar masa da cewa waziri na raye kuma da shine ake ta yin wannnan karafkiyar, tunda shima ya kasance tsohon gwarzon jarumi mai dakawa maza gumba a hannu. Koda aiyana Hakan sai Hamsaru ya shammaci sarki da dukkan dakarunsa ya daka tsalle sama ya dira akan rufin dakunan gidan sarautar ya kama gudu a kansu ya nufi can inda yake jiyo sautin karafkiyar karafa, Ai kuwa shima sarki Barham sai ya daka tsallen sama ya dira a kan rufin dakunan suka kasa tsere. Lokacin da ya iso inda ake fafatawa da waziri yaga yadda dubunnan dakaru sukayi masa rubdugu sai hankalinsa ya kara dugunzuma saboda ya tabbatar da cewa shuma nan da dan wani lokaci karfinsa zai kare a cimmasa, Hamsaru ya waiga bayansa yaga sauran kiris sarki Barham ya cimmasa kawai sai ya yunkura kamar zai daka tsalle ya dira a inda ake gurmuzu da waziri amma kuma sai ya juyo cikin zafin nama da shammace ya doki kirjin sarki Barham saboda karfin dukan sai da sarki yayi baya a sama tamkar an jamyeshi da majajjawa ya fada kan rufin wani dakin, hannunsa na hagu ya bugu har kashinsa ya tsage ya fado kasa a matukar galabaice. Kafin ya mike tsaye tuni Hamsaru ya juya ya daka tsalle ya dira a tsakiyar dakarun da suka lullube waziri ya tarwatsasu da sara da suka, Damar da yasamu kenan ta tsayawa daf da waziri yace, dashi shirinmu fa ya watse dole ne mugudu inba haka ba sarki da jama'arsa zasu sami nasara a kanmu kuma na fuskanci cewar sarki so yake a kamamu a raye yadda zai iya cin mutuncinmu. Kafin Hamsaru ya gama rufe bakinsa sai suka juyo takun sawayen sarki Barham a kan rufin dakuna ya durfafo inda suke ba shiri suka sake tarwatsa dakarun dake zagaye dasu suka kutsa ta cikinsu da karfin tsiya suna masu falfalawa da fudun tsiya, Kawai sai suka sake daka tsalle sama a tare suka dira akan rufin dakunan suka ci gaba da gudu a kasa suka nufi inda katangar gidan sarautar take. Koda sarki ya hangosu sai ya bisu suka kasa tsere a sama kuma a Lokacin ne dakarun masu kibiya suka fara harbawa su Hamsaru kibiyoyi amma cikin sa'a ko kibiya daya ba ta samesu ba. A haka dai da kyar da sidin goshi suka isa inda katangar take suka sake daka tsalle a tare suka haye katangar suka dira kasa, Ashe dama tuni sun tanadi dawakansu a wani sako dake bayan gidan sarautar Don gudun faruwar bacin rana, don haka suna dira a kasan suka sake rugawa da azababben gudu Izuwa wannan soko suka kwance dawakansu suka hayesu gamida da zaburarsu da gudu, A dai-dai Lokacin ne sarki Barham ya duro kasa gaban katangar gidan sarautar ya hango su Hamsaru bisa dawakai sun tada kura, cikin tsananin fushi sarki Barham ya kurma uban ihu har sai da kwallar bakin ciki ta zubo masa, domin a sannnan ne ya tuna cewa yayi babban kuakure da bai yi tunanin toshe duk wata hanya ba dasu Hamsaru zasu iya guduwa, Nan take sarki Barham ya kwallawa dakaru masu kibau kira ya umurcesu dasu hau dawakai su bi bayan su Hamsaru suyita harbinsu har sai sun hallakasu sannnan suzo masa da gawarsu. Nan take kuwa dakarun sama dasu dubu talatin suka hau dawakai suka zaburesu da gudu suna masu bin sawun dawakansu Hamsaru, A dai-dai wannnan lokaci ne sarki yaji hannunsa yayi masa nauyi da yawa. Koda ya dubi hannun sai yaga ya kumbura suntum sakamakon tsagewar da kashin ya samu, nan take ya kwalawa likitansa kira, nan da nan dakaru suka rugo da gudu dauke da karaga aka dora sarki a kai aka shiga dashi cikin gidan sarautar, likitansa na biye dashi, Wannan shine abinda ya faru a birnin zamar yayin dasu waziri suka yiwa sarki Barham yunkurin juyin mulki amma basu sami nasara ba. Al'amarin su gimbiya lazima kuwa Lokacin da ta saba Kalmaru a bayanta ta falfala da gudu dashi bata tsaya a ko ina ba sai a can inda suka kafa sansaninsu ta shige dashi cikin tantinta, ashe tun sa'adda sarki Daryan yayi masa wannnan wawan dundu a gadon baya ya suma kuma har Iyanzu bai farfado ba. Koda gimbiya lazima ta shimfida Kalmaru akan shimfida taga babu alamun numfashi a tare dashi sai ta rude kuma kuma ta dimauce, a dai-dai wannnan lokaci ne taji dakaru sun fado cikin tantin sun ritsata da makamai saboda ba'asan ko wacece ita ba, dalili kuwa shine a can cikin keken dokinta an iske huzen a kwance sanye da tufafinta Koda lazima taga dakaru sun kewayeta rike da makamai kuma ga Kalmaru kwance a kasa cikin mugun yanayi sai tayi sauri ta cire hular karfen dake kanta Kyakkyawan dogon gashin kanta ne ya fara zubowa kasa. Koda dakaru sukayi arba da kyakkyawar fuskarta sukaga itace sai dukkaninsu suka zubarda makamansu suka zube kasa cikin biyayya da tsananin mamaki. Adaidai wannnan lokaci ne likitocin dakarun yaki suka shigo cikin tantin suka shiga duba Kalmaru suna kokarin ceto rayuwarsa, Koda gimbiya lazima taga likitocin sun shafe yan dakiku masu yawa a kan Kalmaru amma ko motsi baiyi ba sai sai hankalinta ya dugunzuma ainun, nan take idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya subuto mata bata sani ba, Cikin sauri ta juyawa jama,a dake cikin tantin baya don kar suga zubar hawayen nata, Kwatsam sai aka ji Kalmaru ya farfado yana mai dogon numfashi gamida furzar da wani irin gudan jini daga bakinsa, Kalmaru ya yunkura zai mike zaune amma sai likitoci suka mayar dashi kwance babban likitan ya dubeshi yace, ya kai dirkar birnin zamar kayi sani cewa kashin bayanka ya bugu sossai kuma ba karamar sa'a kayi ba da bai karye ba sannnan kuma inba don gimbiya lazima ta ceci rayuwarka ba da tuni sarki Daryan ya hallaka. Koda da jin wannnan batu sai Kalmaru ya fara kallon mutanen dake cikin tantin a sannnan ne ya hango lazima tsaye can gefe daya ta juya baya. Cikin tsananin mamaki Kalmaru ya dubi shugaban likitocin yace,ban gane abinda kake fada ba, ta yaya gimbiya lazima ta ceci rayuwata alhalin tana can bayan sansanin yaki a cikin keken dokinta, Kai huzen meye ka juya mini baya ko ka sabawa umurnina ne shiyasa baka son mu hada ido?" Koda jin wannnan tambaya sai lazima ta juyo sukayi arba ita da Kalmaru, cikin tsananin mamaki Kalmaru ya kurawa gimbiya lazima idanu ya kasa cewa komai, Koda ganin haka sai gimbiya ta dubi likitocin da sauran dakarun dake cikin tantin tace ku fita ku bamu wuri. Nan take kuwa dakarun da likitocin suka fice gaba dayansu. A sannnan ne gimbiya lazima tazo ta zauna a gefen shimfidar da Kalmaru ke kwance ta dubeshi cikin murmushi mai taushi tace, tabbas nice na ceci rayuwarka daga shairin sarki Daryan a Lokacin ya kaika kasa yana shirin soke gadon bayanka da takubbansa, ni kuwa sai na dako tsalle daga inda nake na doki kugunsa, naga Lokacin da yayi sama kansa ya bugu a kan garkuwar wani badakarensa har hakorinsa guda ya fita daga cikin bakinsa, ina mai zaton dai shima ya suma kamar yadda ka suma, ya kai dirkarbirnin zamar nasan cewa. Kayi matukar mamaki bisa jin wannnan labari daga bakina to ka daina mamaki domin tun ina yarinya karama mahaifina yake koya mini yaki a boye har Izuwa girmana ba tare da kowa ya sani ba Ba don komai ya koya mini yaki ba sai saboda irin wannnan rana, Lokacin da aka fara wannan yaki ina can bayan sansani a cikin keken doki sai na fito na hau saman keken domin na hango abinda ke faruwa a filin yakin na rubuta a cikin littafina kamar yadda burina ya kasance amma sai naga bana iya hango abinda ke faruwa, Al'amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na fara tunanin hanyar da zan bi naje daf da filin yakin yadda zan iya ganin duk abinda ke faruwa, Tunda dakaru da yawa sun tsareni kuma ka basu umurnin kada subar wani abu yazo kusa dani kuma kada a barni naje ko ina, Nan take dabara ta fado mini na ribaci huzen na sumar dashi a cikin keken dokin nayi musayar kaya dashi na fito daga cikin keken dokin ba tare da dakaru sun shaudani ba, Lokacin da na iso sansanin yakin da nufin na kalli abinda ke faruwa na rubata sai na hango kana kwance kasa sarki Daryan na shirin hallakaka shine na falfala da gudun tsiya na ceci rayuwarka wannnan shine iyakar abinda ya faru, koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun tsananin damuwa yace kinyi babban kuskure da baki hallaka sarki Daryan ba a wannnan lokaci tunda kin samu dama. MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 2 Koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun tsananin damuwa yace kinyi babban kuskure da baki hallaka sarki Daryan ba a wannnan lokaci tunda kin samu dama. Lazima tace ai inda kuma na tsaya kokarin hallaka sarki Daryan kai kuma zaka iya rasa rayuwarka gaba daya Kalmaru yace ai in dai sarki Daryan zai rasa tasa, rayuwar tawa ba a bakin komai take ba, Ki sani cewa hankalina a tashe yake sossai saboda ina tunanin cewa zamuyi biyu babu, Abinda nake nufi shine yanxu gashi a nan munyi ragas dasu sarki Daryan tunda babu bangaren da suka sami nasara a wannan yaki kuma inaji a jikina cewar wani mugun abu na faruwa acan birnin zamar. Shin bakiyi tunanin cewa Hamsaru da waziri zasu iya shiryawa sarki wani mugun tuggu ba tunda ni da dukkan manyan mayakan kasar bama nan mun fito yaki?" Koda Kalmaru yazo nan a zancensa sai hankalin gimbiya lazima ya dugunzuma ainun bata san sa,adda ta dafa kafadar Kalmaru ba tace ya kai jarumi Kalmaru yanxu menene matakin da ya kamata mu dauka? " Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannnan yace,bai kamata muyi gaggawar dauka wani mataki ba tunda bamu san abinda abokan gaba ke shirin yi ba, bamu sani ba ko zasu ci gaba da wannnan yaki ba ko baza su ci gaba ba tunda mu dasu kowa na sansaninsa. Yana gama fadin Hakan sai ya kwallawa shugaban likitocin kira, likitan ya shigo cikin tantin da sauri ya zube kasa gaban Kalmaru, Kalmaru ya dubeshi cikin nutsuwa yace tsawon wane lokaci zan iya mikewa na ci gaba da yaki? Likita yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar zuciya yace ya shugana a kalla kwana biyu,koda jin haka sai hankalin Kalmaru ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe, kawai sai ya tura aka kirawo manyan dakarun yakinsa, da zuwansu sai ya dubesu yace daga yanxu gimbiya lazima ce shugaba a wannan yaki itace zata baku umurni kubi, idan kuma abokan gaba sun janye sun bar sansaninsu mu ma sai mu janye amma yanxu inason a tashi manzo ya tafi Izuwa can birninmu domin yaje ya gano halin da garin ke ciki domin ina zargin cewa akwai abinda ke faruwa. Nan take dakaru suka durkusa a gaban lazima suna masu yin mubaya'a a gareta sannnan kuma aka tashi manzo da sauri ya tafi Izuwa birnin zamar, Acan sansaninsu sarki Daryan kuwa Lokacin da aka shigar da sarki Daryan cikin tantinsa aka shimfideshi bisa shimfida a matukar galabaice sai ya fashe da matsanancin kukan bakin ciki ya kama ihu da shure shure har saida dakaru suka danneshi aka

Chapter 7 of 10