Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 10
shiga bashi baki sannnan ya dawo cikin haiyacinsa amma duk da haka sai da ya yunkura ya mike zaune ya sake yunkurawa zai mike tsaye yana mai cewa akaishi wajen gawar mahaifinsa, A wannan Lokacin kansa a kumbure yake sumtun kuma gaba dayan jikinsa ya dume da zazzabi, Kwatsam sai ga likitansa ya shigo da sauri cikin tantin da zuwansa sai ya dubi sarki Daryan ya duddubi ko ina a jikinsa cikin alamun tashin hankali yace ya shugabana jinin jikinka ya zuba da yawa dole ne ka kwanta muyi maka aiki sossai mu baka magani kasha, inba haka ba kuwa zaka iya rasa rayuwarka, Koda jin wannnan batu sai bakin ciki ya kara turnuke sarki Daryan a Lokacin da hawaye ya zubo masa sannnan ya dubi Sarkin yakinsa wanda ake kira da suna Balwaz yace ayi shirin komawa gida domin muje mu binne mahaifina bisa al'ada da addininmu kamar yadda aka saba. Sarkin yaki Balwaz ya risina yace an gama ya shugana, nan take Sarkin yaki Balwaz ya juya ya fice daga cikin tantin shi kuma sarki Daryan sai ya koma ya kwanta akan shimfidar tasa likitoci suka kama aikinsu. Bayan likitan Kalmaru ya gama yi masa aiki an dinke raunikan dake jikinsa an shafa masa magani kuma an bashi wadansu magunguna kusan kala shida yasha sai idanunsa suka fara lumshewa alamar cewar barci zai yi don haka sai kowa ya fice daga cikin tantin aka barshi shi kadai domin ya sami nutsuwa yin barcin sossai. A can gaban sansanin nasu kuwa gimbiya lazima ce a tsaye tare da dakaru sun zuba ido Izuwa can sansanin abokan gaba ko zasu ga an taho kawo musu sabon hari, tsawon kusan rabin sa'a shiru basuji motsin kowa ba don haka sai gimbiya lazima ta tashi dan leken asiri guda daya tace dashi yaje ya gano musu halin da abokan gaba ke ciki nan take kuwa wannnan dan leken asiri yayi wata irin shiga wacce ta saje da kalar kasar dajin ya ruga Izuwa inda sansanin abokan gabar suke. Jim kadan sai ga dan leken asirin ya dawo a nutse cikin kwanciyar hankali, da zuwansa gaban lazima sai ya risina yace ya shugabata ai tuni abokan gaba sun hada nasu da nasu sun juya sun nufi birninsu. Koda jin haka sai wani babban badakare ya dubi lazima cikin murna yace ya shugabata ai wannan wata babbar dama ce muka samu da zamu bisu a baya mu kai musu harin bazato mu gama dasu cikin abinda bai wuce sa'a biyu ba, Koda jin haka sai gimbiya lazima ta dubi badakaren a fusace tana mai daka masa tsawa tace tabbas bakada hankali kuma bakada wayo, Ashe baka san cewa ba a tsokanar mahaukacin kare ba, shin ka manta ne cewa yanxu sarki Daryan yana cikin tsananin fushi da bakin ciki bisa rashin mahaifinsa, Idan kuma wani tarkon ya shirya mana fa ta hanyar nuna sun janye yakin? Ni 'yace kuma nasan irin zafin da zanji idan na rasa mahaifina, yana da kyau a kyale sarki Daryan yaje gida ya binne mahaifinsa cikin nutsuwa domin Hakan zaisa zuciyarsa tayi sanyi, Idan yana zaton zai iya gamawa da mu farat daya yanzu ya gane ba haka bane mu ma kuma mun gane cewa karo dashi ba wasa bane,tunda dai yanxu mun tabbatar da cewar abokan gabarmu sun janye daga filin yaki muma sai mu gaggauta kwashe namu inamu mu juya domin mu koma kasarmu da wuri muga halin da take ciki. Ba tare da gardamar komai ba kuwa dakaru sukabi umurnin gimbiya lazima aka kwashe komai daga filin yakin aka kama hanyar zuwa birnin zamar. Wannnan karon dai Sarkin yaki Kalmaru akasa a cikin keken dokin gimbiya lazima kuma itace taci gaba da jinyarsa ko tari yayi sai ta tambayeshi ko akwai wani abu yake bukata, Kai hatta su kansu likitocin basu kaita yi masa hidima ba, Kalmaru bai soma jin kwarin jikinsa ba har sai da kwanaki biyu suka shude,sannnan ne ya fara iya mikewa tsaye daga kwance amma tafiya ma baya iya yinta har sai lazima ta taimaka masa ta dora hannunsa a kafadarta ta talabi kugunsa a haka take rakashi inda zai je ya kawarda bukata, Al'amarin da ya daurewa dakuru kai kenan suka fara zargin anya kuwa babu soyayya tsakanin Sarkin yaki Kalmaru da gimbiya lazima? Ba komai ne ya sasu wannan zargi ba face ganin cewa ita fa gimbiya lazima 'yar sarkinsa ce wadda babu kamarta a fagen kyau a gaba daya birnin zamar kuma babu wani da namiji da ya taba kusantarta haka sai shi Kalmaru barema har jikinsa ya taba nata amma gashi ita da kanta take kusantarshi tana hada jikinsa da nata a matsayin mai jiyarsa bisa rashin Lafiya. A ranar kwana na uku a yada zango a bakin wata korama cikin wani daji mai yawan ni'ima sai Kalmaru ya mike tsaye yana mai dogara wata santa ya nufi inda karshen karamar take ya baro inda gimbiya lazima take tare da sauran dakaru, a wannan Lokaci an baje abinci ana ci amma shi Kalmaru ko loma daya baiyi ba ya tashi ya bar abinci. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, koda ganin haka sai gimbiya lazima ma ta mike tsam ta baro nata abinci a cikin tantinta ta nufi inda Kalmaru yake inda suka nisanta da sauran dakaru, Koda Kalmaru yaji motsi a bayansa ya waigo da sauri don ganin mai zuwa,sa'adda yaga ashe lazima ce fuskarta cike da annuri da murmushi mai dimauta da namiji sai yaji zuciyarsa ta baaQquga da karfi, nan take yaji ya kamu da tsananin sonta fiye da koyaushe, Kawai sai ya risina da nufin ya kwashi gaisuwa,cikin hanzari ta karaso gareshi ta rike kafadunsa ta tasheshi tsaye tace haba ya kai dirkar birnina ai yanxu kuma ka wuce matsayin ka rinka risina mini tunda kai ne na uku a cikin majalisar birnin zamar tunda daga sarki sai waziri kuma sai kai. Koda jin haka sai Kalmaru yayi murmushi yace ai duk da haka kina gaba dani tunda ke yar sarki ce, nan gaba zaki iya zama sarauniya ta kuma dole ne nayi bauta da biyayya a gareki, Ya shugabata naji dadi da kika zi nan inda zan iya isar da sakon godiyata a gareki bisa ceton rayuwata da kikayi daga hannun sarki Daryan, tabbas kin bani mamaki kuma kin baiwa duk dakarunmu mamaki domin babu wanda ya taba zaton cewa kema jarumace haka, Nayi matukar farin ciki da kika boye kanki ga abokan gabarmu amma kuma banso jama'armu suka san cewa ke jaruma ce ba saboda wani abu da zai iya faruwa nan gaba bayan mun koma gida. Cikin mamaki lazima ta dubi Kalmaru tace wane abu ne kuma zai biyo baya saboda sanin matsayina na iya yaki?" Kalmaru ya numfasa yace kiyi hakuri ba zan iya gayamiki amsar wannan tambaya ba taki a yanzu amma idan kika zuba ido zaki ga amsar da idanunki, ya shugabata inaso ki sani cewa na yi matukar bakin ciki mara adadi bisa rashin samun nasararmu a wannan yaki a matsayina na Sarkin yaki kuma a matsayin farkon fitowata yaki, Tabbas kunya da bakin ciki zasu addabi zuciyata har Izuwa ranar da zan wanke gazawata na ciyo nasarar wani yakin, Ko kadan ban taba zaton cewa zan fuskanci wannan matsala ba. Lokacin da gimbiya lazima taji wannan batu sai ta bushe da dariya, Al'amarin da yayi matukar baiwa jarumi Kalmaru mamaki kenan yace menene kuma ya baki dariya? " Lazima ta dubeshi cikin nutsuwa sannnan tace ai kai ne kuwa ka sami babbar nasara a wannan yaki tunda har ka cika babban burin mahaifinka ka kashe tsohon makiyinsa wato sarki saumir mahaifin sarki Daryan, bisa wannan daliline ma nayi maka wani babban tanadi wanda ka manta dashi kuma wannan tanadi abune mai darajar gaske domin a duk fadin kasar su sarki Daryan da fadin mulkinsa babu abinda ya fishi daraja. Cikin tsananin mamaki ya Kalmaru ya sake duban lazima yace wane abune kuwa wannan wanda ban sanshi ba? Koda jin wannnan tambaya sai lazima ta zaro wata kyakkyawar takobi daga cikin rigarta, ita dai wannan takobi kufen ta ma da zallan lu'u lu'u akayi shi, ita kuma takobin anyita ne da zallar farin karfen lu'u lu'u. Masana kyalkyali da makeran duniya sun tabbatar da cewa ba a taba yin takobi mai kyau, daraja da tsadar wannan takobi ba, Bakowane keda mallakin wannan takobi ba face marigayi sarki saumir. Kalmaru ya karbi takobin yana mai kura mata idanu cikin tsananin al'ajabi harma ya zarato daga cikin kufenta, take haskenta ya dallare masa idanu kuma ya haskake gaba dayan wajen da suke tsaye. Lazima ta dubi Kalmaru tace a cikin bincikena da karance karancena na samo tarihin wannan takobi kuma asalinta ta Sarkin farko ce wanda ya fara mulki a birninsu sarki Daryan, ance babu mai mallakar wannan takobi face jarumin da zai sami daukakar da babu kamarta a zamaninsa kuma dole ne ya kashe mai mallakar takobin Kafin ya iya amfani da ita, Ita dai wannan takobi sirrinta shine in dai mamallakinta yana raye kuma yana tare da ita koyaushe a jikinsa to har abada baza'a ci birninsa da yaki ba, kaga kenan yanzu idan sarki Daryan ya nemi wannan takobi ajikin gawar mahaifinsa ya rasa hankalinsa zai dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya shiga farautarka dare da rana, Duk wanda ya mallaki wannan takobi dole ne yayi nisan kwana a duniya bisa wannan daliline sarki saumir ya shekara Dari da Ashirin da uku a duniya sai a wannan yaki ne ka zare masa ruhin numfashinsa. ** ** ** MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PArt 3 Duk wanda ya mallaki wannan takobi dole ne yayi nisan kwana a duniya, bisa wan nan daliline sarki saumir ya shekara Dari da Ashirin da uku a duniya sai a wannan yaki ne ka zare masa ruhin numfashinsa. Koda gimbiya lazima tazo nan a zancenta sai hannun Kalmaru ya kama karkarwa yayi sauri ya mika mata takobin yace ungo rike ta bazan iya ajiye taba a wajena, Cikin mamaki lazima tace saboda me ba zakaka iya ajiye ta ba a wajenka?" Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannnan yace ina tsoron kada a dalilin wannan takobi dake hannuna mutane da yawa su rasa rayuwarsu, Na sami labari cewar babu abinda sarki Daryan bazai iya ba akan bukatarsa,tun muna yara da ya kullaceni har yanzu wannan gaba mai tsanani tana nan a ransa kuma koda anyi sulhun yaki tsakanin kasarmu da tasa, ba zai daina gaba dani ba face yaga karshen kiyayyar tamu, Ni bana tsoronsa ko shakkarsa amma ina tsoron abinda zai sami duk wanda ya rabeni, Yayin da lazima taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai tunda kasan da hakan dole ne yanzu ka tsananta tsaro a kanta da duk makusantanka, Inaso ka sani cewa babuwanda zai iya ajiye wannan takobi ta ajiyu face kai domin duk wanda ya barta a wajensa har tayi sa'a goma sha biyu takobin ce zata zamo ajalinsa kuma ta bace bat ta koma hannun mamallakinta in yana raye in kuma baya raye sai ta koma wajen wanda ya kasheshi, Kaga dai kenan baka isa ka guji wannan takobi ba , ko kana so ko kana ki a duk inda kake sai ta bika babu mai iya rabaka da ita face sarki Daryan domin a sirrin da aka yiwa takobin jinin gidansu ne kadai zasu iya mallakarta su zauna Lafiya, Abinda yasa na dauko maka wannan takobi daga jikin gawar sarki saumir shine idan har kajewa mahaifina da mahaifinka ita sukayi arba da ita zasu yi farin ciki marar misaltuwa tunda kayi abinda ya gagaresu tsawon shekara da shekaru zasu ji tamkar ka ciyo nasarar wannan yaki ne kuma zasu kara girmamaka su sallamawa jarumtakarka don ba a taba zaton cewa akwai jarumin da zai iya kashe sarki saumir ba. Lokacin da gimbiya lazima tazo nan a jawabinta sai jikin Kalmaru yayi sanyi sossai ya karbi wannan takobi daga hannunta saboda yayi imani da abinda ta gaya masa a kan takobin sannnan ya boye takobin a cikin rigarsa yayi shiru bai kara cewa uffan ba. Nan dai suka baro inda suke tsaye yana dogara sandar dake hannunsa suna tafiya a hankali har suka dawo inda suka bar dakaru, kowannensu ya shige cikin tantinsa. A can birnin sarki Daryan kuwa Lokacin da ya dawo gida tare da rundunarsa ta yaki sai mutanen gari da fadawansa suka taru taru a fada akayi jugum jugum saboda bisa babban rashin da akayi wato mutuwar saumir mahaifin sarki Daryan, Tun kafin rundunar ta iso gari jikin jama'a yayi sanyi saboda angane cewa lallai ba lafiya ba, Dalilai kuwa shine duk sa'adda aka dawo daga yaki tun daga can wajen gari za'a ji ana buga tambura kuma ana busa algaita alamar cewar an dawo cikin nasara ko kuma anyi ragas, Wannan karon kuwa ko da rundunar ta kusanto gari sai akaji ana buga gangar bakin ciki guda daya jal. Duk sa'adda akaji sautin wannan ganga na tashi to dole ne cikin abu uku daya ya faru,kodai wani babban mutum ya mutu ko kuma an fadi yaki ko kuma anyi asarar dukiya mai yawan gaske. Koda aka budewa rundunar yaki kofar gari suka shigo babu abinda mutane suka fara yi arba dashi face gawar sarki saumir, Ai kuwa nan take garin ya kaure da koke koke, babu wanda zaka tausayawa a wannan Lokaci sama da sarki Daryan domin kuka yake yi tayi kashirban kamar ransa zai fita, Kai har sai da ma ya rinka shidewa numfashinsa na sarkewa. Koda likitansa ya lura da halin da yake ciki sai yayi sauri ya bashi maganin bacci, Ko dakika biyar ba'ayi ba barcin ya saceshi, sai akayi sauri aka saukeshi daga kan dokinsa aka darashi akan wata karamar karaga aka shige dashi cikin gidan sarautar, Sarki Daryan bai farka daga bacci ba sai da ya kwana ya yini yana bacci, yana farkawa ya tsinci kansa a gado. A firgice ya mike zaune kawai sai yayi arba da likitansa zaune a gefen gaddon daf dashi ga abinci iri iri da ruwan magani, Abinda ya fara fitowa daga bakin sarki Daryan shine ina gawar mahaifina? " Yana gama fadin Hakan sai ya mike zumbur da nufin ya fice ya tafi wajen gawar a Lokacin da hawaye ya zubo masa, Cikin hanzari likitan ya sha gabansa ya dubeshi yace ya shugabana shin bakason ka dauki fansa ne akan wanda ya kashe maka mahaifinka, so kake kaima kabi mahaifin naka?" Koda jin wannnan tambaya sai jikin sarki Daryan yayi sanyi ya koma ya zauna a kan gadon yaci gaba da zubarda hawaye, A sannnan ne likitan ya tafa hannayensa sai ga wata amintaciyar kuyanga mai suna Afila ta shigo cikin turakar, take likitan yayi mata inkiya ta zauna kusa da sarki Daryan ta shiga bashi abinci yana ci har sai da taga ya koshi sannnan kuma ta bashi ruwan wadanan magunguna ya shanyesu duka faruwar hakan keda wuya sai sarki Daryan yaji karfin jikinsa ya dawo tamkar bai taba wata jinya ba, Nan take ya tura aka kirawo wani babban hadiminsa ya bashi umurnin yaje yasa a fara shirye shiryen bikin binne mahaifinsa, Nan take hadimin ya fice da sauri yaje ya cika aiki, ai kuwa sai aka fara busa wani irin kaho mai karar tsiya wanda ba'a busashi face idan sarki ne ya mutu a garin, kuma nuni ne da cewar za'a fara bikin binne gawar Sarkin, Shi kuwa sarki Daryan sai ya shiga kewaye ya kwanta a cikin bahon wankansa, Kuyangi suka yi masa wanka sannnan ya fito ya sanya bakaken tufafi ya nufi wani babban fili dake tsakiyar gidan sarautar inda kabarurrukan sarakunan da suka shude suke, Yana isa wannan wuri ya iske an kawo gawar sarki saumir a cikin wata akwatin zinare an ajiye akan wani gini mai tudu, wadansu makadan gargajiya sun kewaye gawar suna ta kida, a gefe daya kuma mata da maza da bokayen kasar sun taru suna ta tika rawa kowannensu na rike da ganyen wata bishiya a hannu, wasunsu suna tayin bori, har kumfa na fita daga cikin bakunansu suna ta suratai na ambaton aljanunsu iri-iri, ta cikin tsakiyar dandazon wadanan mutane sarki Daryan ya kutsa ana ta buda masa hanya yana wucewa har ya isa inda akwatin gawar taken, Tun daga nesa ya kurawa fuskar gawa idanu ya fara zubarda hawaye, da ya iso kan gawar sai ya fada kanta ya rungumeta kuma ya fashe da matsanancin kuka, Sai da ya shafe kusan rabin sa'a a cikin wannan hali sannnan ya tuno da batun takobin daraja,nan take ya zura hannunsa cikin aljihun gawar ya kama lalube amma sai yaji shiru, take ya tuno wani abu da ya faru a filin yakin sa'adda ya hango gawar mahaifinsa baje a kasa kuma rigarsa ta Bude babu takobin daraja a cikinta,yana gama wannan tunani sai ya dago kansa ya juyo da baya ya dubi jama'ar dake wajen sannnan ya kwarara uban ihu gamida kiran sunan takobin daraja, Nan fa kowa ya gane dalilin ihun nasa kuma ba komai bane face batan takobin daraja, Cikin tsananin fushi sarki Daryan ya kwalawa Sarkin yakinsa kira ya rugo Izuwa gabansa ya zube kasa, sarki Daryan ya dubeshi yace maza kaje ka zabo manyan dakarun leken asirinmu guda goma suje su hada kai da wasu dakarun leken asirin birnin warzas su shiga birnin zamar suyi bincike su gano wanda ya sacewa ubana takobinsa ta daraja, Abu ne mawuyaci idan ma ba Kalmaru bane ya sace wannnan takobi ba domin shi kadai ne zai iya ajiyeta har Izuwa wannan Lokaci, inda wani ne daban da tuni takobin ta hallaka shi ta dawo da kanta nan. Sa'adda Sarkin yaki yaji wannan batu sai ya mike tsaye da sauri yace an gama ya shugabana sannnan ya bar filin bikin binne gawar gaba daya, Nan dai aka ci gaba da bikin binne gawar amma sai da dare ya raba sannnan aka binne gawar sannnan kowa ya kama gabansa aka watse. Al'amarin birnin zamar kuwa sarki Barham na zaune a fada kan karagarsa ta mulki sai ya mike tsaye ya kama kai kawo cikin alamun tsananin damuwa da kaguwa, Ba komai ne ya jefashi cikin wannan hali ba face rashin dawowar dakaru masu kibiya wadanda aka tura su kashe sadauki Hamsaru da waziri. Suma fadawan na sarki Barham hankalinsu a tashe yake kuma basu da burin da yafu suji ance ankawo su waziri ko kuma an kashe su,saboda cin amanar kasa da suka yi da kuma janyo sanadin asarar dubunnan rayuka. Ana ckin wannan hali ne aka ga wadanan dakaru 'yan kubau sun dawo sun shiga cikin fadar da sauri,da isowarsu sai shugabansu ya zube kasa gaban sarki Barham ya risina cikin biyayya yace, Ya shugabana kayi sani cewa munyi iya kokarinmu wajen ganin mun riski su waziri amma mun kasa duk da cewa muna ta harba musu ruwan kibiyoyi saboda sun bamu tazara mai yawa da kyar ma muke iya hango kurarsu, sannu a hankali kuma sai muka fara amfani da sawayen dawakansu, sa'adda muka iso dajin Sahara sai sawajen dawakan nasu ya bace bat muna muka nemishi muka rasa, duk da haka bamu daina nemansu ba har sai da....... Kafin ya gama fadin abinda ke bakinsa sai sarki Barham ya tari numfashinsa yana mai daga masa hannu yace ya isa ba sai ka karasa bayaninka ba domun na fahimci cewar waziri da Hamsaru sun yaudareku sun buya a cikin daji kuma sun boye dawakansu ta hanyar amfani da tsofaffun dabarun yaki. koda gama fadin Hakan sai sarki Barham yasa aka shirya masa doki ya hau, tsirarun dakaru suka yi masa rakiya basu zame ko inaba sai kurkuku. *** **** Mu hadu anjima da dare don jin cigaban wannan kasaitacen labari na maza sun fadi kashi na hudu MAZA SUN FADI!!! LITTAFI NA 4 PART 4 Koda gama fadin Hakan sai sarki Barham yasa aka shirya masa doki ya hau, tsirarun dakaru suka yi masa rakiya basu zame ko ina ba sai kurkuku. Attajiri yunaru na zaune a cikin dakin da aka kulleshi cikin tsananin farin ciki da murna domin zatonsa saura 'yan dakiku kadan ya fice daga cikin wannan kurkuku, Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga sarki Barham ya durfafoshi tare da tsirarun dakaru suna take masa baya kuma fuskarsa cike da murmushi, Nan take zuciyar yunaru ta buga da karfin gaske ya tabbatar da cewar hakansu bai cimma ruwa ba, Sarki Barham ya iso daf da kofar tagar dakin da yunaru ke ciki suka yi kallon kallo na taawon yan dakiku sannnan sarki Barham ya sake yin murmushi a gareshi a karo na biyu sannnan yace ya kai yunaru babban Attajiri kayi sani cewa ramin da kuka haka kai da danka da kuma dan uwana waziri yayi zurfi da yawa don haka ba zaku iya fitowa ba daga cikinsa kaga kenan ci gaban da kuka samu iri daya ne dana mai hakan rijiya. Koda jin wannnan batu sai fuskar attaji yunaru ta juye Izuwa tsananin damuwa amma sai ya dubi sarki Barham cikin nutsuwa yace, wace irin nasara dakarunku suka samu a filin yaki? Sarki Barham yace ai kamata yayi ka fara tambayata irin nasarar da kuka samu a nan birnin a kokarin yi mini juyin mulki kafin kaji wacce muka samu a filin yaki. Attajiri yunaru yayi dan guntun murmushi mai nuna alamun rashin karayar zuciya yace ai na sani cewa shirinmu na juyin mulki ya tarwatse saboda inda bai tarwatse ba da yanzu ba zan ganka ba a raye amma kuma na tabbatar da cewa Baka dana da waziri ba kuma baka kamasu ba domin ina da yakinin cewa baza ka taba samun nasarar hakan ba a kansu, ko kasheni kasa akayi yanzu banida sauran nadama muddin baku ne kuka yi nasara ba a filin yaki domin na tabbatar da cewar sai sarki Daryan ya shigo har cikin garinan ya kasheka ya baiwa waziri karagarka ,a sannnan ne nima zan kamo dan uwana tsohon Sarkin yakinka na danneshi na yanka don na kawar da tshohon bakin cikin daya dasa mini a zuciyata, Lokacin da yunaru yazo nan a zancensa sai sarki Barham ya bushe da dariya yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba, daga can kuma sai ya tsuke bakinsa ga barin yin dariya sannnan ya dubi cikin tsananin fushi yace, ya kai tsohon abokin gaba kuma maci amanar kasa kayi sani cewa bambanci dake tsakanin haske da duhu a baiyane yake don haka har abada adali yana kan azzalumi, Na yarda da Sarkin yaki Kalmaru dari bisa dari don haka na tabbatar da cewa ba zai taba bani kunya ba a wannnan yaki don haka ka saurari dawowar su zakaji bakin labari mai daci wanda zai kona zuciyarka da ranka gaba daya har sai kaji kamar gwara mutuwarka da rayuwarka, Danka Hamsaru da waziri sun sami nasarar guduwa amma ka sani cewa zanci gaba da farautarsu dare da rana bazan gaji ba har sai na cafkesu kuma kaima bazan yanke maka hukuncin komai ba har sai ka gama wa'adin kwanakin da aka diba maka a cikin kurkukun bisa alkawarin dana dauka a gaban jama'a. Koda gama fadin Hakan sai sarki Barham ya juya ya fice daga cikin kurkukun gaba daya yana mai kyalkyala dariyar farin ciki har yana gwara kansa akan sandunan karfen dake jikin tagar dakin kuma yana kwarara uban ihu kai kace wata azaba akeyi masa mai radadin gaske. Da yammaci sakaliya rundunar yaki ta dawo birnin zamar, Tun kafin rundunar ta iso labari dawowarsu ya riski sarki Barham don haka sai mike da sauri yayi shiri tare da manyan fadawansa domin taryar su Kalmaru, Nan da nan su sarki Barham suka yi hawa suka fice daga cikin birnin zamar. Tafiyar da sukayi bata kai ta rabin sa'a ba suka hango rundunarsu Kalmaru, nan take farin ciki ya kama sarki ya bayar da umurnin a tsaya a jirasu Kalmaru su karaso, Take kowa yaja linzamin dokinsa aka yi cirko cirko kuma aka zuba idanu akan hanya ana jiran karasowarsu Kalmaru, Lokacin da rundunarsu Kalmaru ta kusanto sai fuskar sarki Barham ta sauya yanayi daga walwala Izuwa damuwa, Ba komai ne ya haddasa hakan ba face hango 'yarsa gimbiya lazima a cikin shigar yaki bisa doki ta jero da Kalmaru sannnan kuma ya lura da cewa akwai dinkin raunika da yawa a jikin Kalmaru Al'amarin da yasa ya gane cewa lallai ba karamar wahala Kalmaru yasha ba a wannnan yaki kuma lallai akwai alamun nasara amma Abin tambaya shi ne akan wane dalili lazima ta sanya kayan yaki alhalin taje yakin ne da niyar kawai ta rubuta duk abinda tagani, haka dai zuciyar sarki Barham taci gaba da wasuwasi gamida zargin abubuwa da yawa har su Kalmaru suka iso, Nan take Sarki Barham ya sauko daga kan dokinsa itama lazima sai ta sauko daga kan nata dokin ta ruga Izuwa gareshi suka rungume juna bisa farin ciki saduwa a Lokacin ne shima Kalmaru ya sauko daga kan nasa dokin ya tsaya yana kallonsu cikin murmushi, Nan fa shima yaji yana sha'awar ace yayi aure kuma ya sami 'ya ko da wanda zai kaunaceshi kamar yadda sarki Barham da gimbiya lazima ke tsananin kaunar juna. Sai da sarki da lazima suka shafe yan dakiku masu yawa a kankame da juna sannnan ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace hakika gani ya kori ji domin tunda na ganki sanye da kayan yaki nasan cewa ba karamar masifa akayi ba a filin daga, Tabbas yanzu kinga amfanin koya mike yakin danayi tun kina yarinya karama Banason naji labarin komai daga bakinki sai daga bakin Sarkin yakina. Koda gama fadin Hakan sai ya juya ya fuskanci Kalmaru, Kalmaru ya taho ga sarki da sauri ya zube kasa bisa guiwarsa guda ya kwashi gaisuwa, sarki Barham ya sunkuya ya kama kafadun Kalmaru ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna sossai yana mai murmushi a gareshi sannnan yace ya kai dirkar birnina ina matukar alfahari da kai saboda nasan cewa ba zaka taba bani kunya ba yanzu wane albishir kazo mini dashi bisa wannan yaki da kikayi? " Sa'adda Kalmaru yaji wannan tambaya sai ya sunkui da kansa kasa yai shiru cikin alamun karayar zuciya sannnan yace ya zura hannunsa cikin rigarsa ya fiddo takobin daraja ya mikawa sarki Barham da hannayensa biyu kansa na sunkuye sai da sarki Barham ya dan ja da baya cikin alamun razana da tsananin mamaki sannnan kuma fuskarsa ta kama murmushi. Sarki Barham ya matso daf da Kalmaru ya dafa kafadarsa cikin matukar murna yace ya kai jarumin jarumai tabbas yau ka sharewa mahaifinka hawayensa kuma kayi abinda babu wani mahaluki daya taba yinsa a wannan nahiya tunda gashi ka kashe sarki saumir har ka dauko takobinsa, Ka sani cewa banida ikon karbar wannan takobi daga hannunka saboda kai kadai ne zaka iya riketa ka zauna Lafiya to amma fa ka sani cewa ka tsokano tsuliyar dodon da zai tada hankalin duniya domin kuwa zaman wannan takobi a hannunka dai-dai yake da tsokano yakin duniya gaba daya. Ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu ka dauko gunguma gunguman itatuwa ka zuba a cikin wutar gabarka da sarki Daryan tunda ka kashe masa mahaifi kuma ka rabasu da takobin daraja, Takobin da a halin yanxu duk duniya babu wata takobi wacce ta fita daraja Ya zama dole musa ido a birnin nan namu kuma mu tsananta tsaro fiye da koyaushe domin sarki Daryan sai yabi kowace irin hanya don ganin ya mallaki wannan takobi ta koma hannunsa kuma yaki tsakaninmu dashi yanzu aka fara Yakin da kuka je tamkar sharar fage ne. Sa'adda sarki Barham yazo nan a jawabinsa sai Kalmaru ya dubeshi cikin mamaki yace, ya shugabana yaya akayi kasan cewa sarki Daryan bai mutu ba a wannnan

Chapter 8 of 10