Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 10
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAZA SUN FADI Part 1 RANA ta take kuma tayi zafi sossai, Amma hakan bai hana mutane cigaba da Harakokinsu ba a cikin birnin kowa ka gani sha’anin gabansa yakeyi, har a cikin kasuwa kuwa ana ta kai kawo ana saye da sayarwa. Kwatam sai aka hango wani matashin saurayi wanda ba zaifi shekara goma shabiyar ba, ya ratso kasuwa yana tafe yana layi sakamakon jini dake zuba a jikinsa har idanunsa suna lumshewa, kai da ganinsa kasan cewa yasha fama gudu sai haki yake, Rigar jikinsa kuwa ta jike sharkaf da jini, nan take ya kife kasa da rub da ciki a tsakiyar kasuwar. Al'amarin da ya matukar razana mutane kenan domin ba'a san yadda wannan saurayi ya shiga wannan hali ba. Nan da nan mutane suka taru suka kewaye wannan saurayi amma aka rasa wanda zai taimakeshi, Sai wani tsoho ne yayi sauri ya tashe shi zaune ya daura masa ruwa a baki yasha, Koda tsohon ya dubi fuskar saurayin sai ya tsorata ainun ya dubeshi cikin dimauta yace ya kai SHUBAIRU waye yayi maka Wannnan karen aiki?'' Cikin matukar karfin hali shubairu ya dubi tsohon ya bude idanunsa da bakinsa da kyar yace, ''kowa yai sauri yayi gudun ransa domin wadansu yan harine suka biyoni da gudu da kyar na guje musu na iso nan, Ina gaya muku cewa suna da tsananin yawan gaske Idan suka iso cikin garin nan sai sun kashe kowa kuma su debe mana dukiyoyinmu '' Koda jin wannan batu sai gaba daya kasuwar ta yamutse mutane suka fara guje-guje da iface- iface masu kokarin kwashe hajojinsu nayi,wasu na bangaje wasu a lokacin gudun, maza da mata yara da manya, nan da nan labari yakai har cikin gari. Shi kuwa wannan tsohon ko juyawa izuwa cikin rumfarsa baiyi ba, sai yai sauri ya tashi shubairu tsaye ya kaishi inda dokinsa yake ya dorashi akai yace, dashi ''maxa ka ruga izuwa gida ka sanar da dan uwanka HUZAIRU halin da ake ciki kuma ka gaya masa ya hanzarta dinke maka raunin dake bayanka domin sara da akayi maka mai zurfi ne'' Koda jin haka sai hawaye ya zubowa shubairu yace, ''Yakai Abbana Yaza'ayi na tafi na barka anan yan sumame su kasheka?'' Tsoho KALMARU ya dubi shubairu a lokacin da shima kwalla ta cika masa idanu yace, ''idan na bika muka tafi tare, Biyu babu za'a yi sbd dokin nawa bashida issashiyar lfy ba xai iya daukarmu mu biyu ba. Dolene na tsaya na tari 'yan harin nan nayi iya kokarina na bata musu lokaci don ka isa Gida da wuri, ku sami damar guduwa kai da dan uwanka huzairu, Na sani cewa dan uwanka huzairu yanada taurin zuciya zai iya cewa sai ya dawo nan ya ceceni to ka gaya masa cewa ko! idan har ya biyo bayana ya karya alkawarin da ya daukarwa mahaifiyarku. Na cewa komai rintsi zai rayu domin ya dauki fansar ranta. '' Gama fadin hakan keda wuya sai hawaye ya zubowa tsoho kalmaru ya yiwa shubairu kallon karshe mai nuna bankwana, dan ya san cewa baxa su sake saduwa ba. Nan take kalmaru ya doki bayan dokin da tafin hannunsa nan take dokin ya zaburi shubairu da gudu izuwa cikin gari. A Wannnan lokaci tuni kasuwar ta dade da watsewa, babu mutum koda guda daya jal a cikinta face tsoho kalmaru. Kawai sai kalmaru ya ruga izuwa cikin rumfarsa ya dauko takobi da garkuwa sannan ya fito ya hau kan wani dogon mumbari dake tsakiyar kasuwar ya tsaya cak!'' yana kallon hanyar da yan harin zasu shigo. Kallo daya mutum zai yiwa tsoho kalmaru ya tabbatarda cewa ya kasance tsohon Sadaukin Jarumi, domin da gani babu tambaya sbd ya kasance dogo mai murdadden jiki, duk da kasancewar shekarunsa a yanzu sun haura saba'in (70) kasancewar akwai sauran kuzari a tare dashi, kuma komai takamar Jarumi zai yi shakka yayi masa shiga farat daya, saboda kwarjininsa. Bayan tsayuwar tsohon kalmaru da kamar tsawon dakika dari da ashirin sai ya jiyo sukuwar dawakai babu adadi sun durfafo kasuwar. Duk da cewa kalmaru yanada dakakkiyar zuciya irinta manyan maxaje sai da tsoro ya darsu acikin zuciyarsa, Ba wai tsoro bane na mutuwa ko irin fafatawar da xaiyi ba, tsoro ne na takaicin irin barna da wadannan dakarun sumame zasu yi idan suka shigo wannan karamin kauye nasu. Shi dai wannan kauyen nasu tsoho kalmaru ana kiransa da suna HIDAIMAT mutanen kauyen gaba dayansu masu sana'ar kera jirgin ruwa ne, kasancewar kauyen yana bakin teku Asalin kauyen tsoho kalmaru ne ya kirkireshe domin shine ya fara zama a bakin tekun, tun kafin matarsa ta haife masa ya'yansa guda biyu, SHUBAIRU DA HUZAIRU Kafin tsoho kalmaru yayi aure ya kasance mataimakin sarkin yakin birnin zamar kuma sai da ya shekara ashirin da biyu yana yiwa sarki Barham bauta. Duk sa'adda kalmaru Ya jagoranci yaki sai an sami nasara ba'a taba samun akasi ba, Al'amarin da ya janyo kishi kenan tsakaninsa da sarkin yaki HAMSARU sbd shi kuma duk sa'adda ya jagoranci yaki anfi yin RAGAS ba'a cika samun nasara ba, Wani babban abun takaici shine sarkin yaki Hamsaru da kalmaru sun kasance 'yan uwan na jini domin dan wa da dan kane suke, Mahaifin Hamsaru ne yayan mahaifin kalmaru, Tun sa'adda kalmaru da Hamsaru suka taso da kurciya ya xamana Cewa ana basu horon yaki a gidan sarautar zamar, kasancewar a wannan lokaci mahaifin kalmaru ne sarkin yaki, Burin mahaifin kalmaru shine dansa ya gajeshi amma sai ya zamana cewa Hamsaru yafi kalmaru tsagwaron karfin damtse da iya yaki, Shi kuma kalmaru sai yazamana cewa yafi Hamsaru sa'a gamida taurin zuciya. Komai hadarin yaki da yawan abokan gaba kalmaru baya ja da baya. Lokacin da tsufa ya riski mahaifin kalmaru sossai har ya zamana cewa baya iya zuwa fada bare yaje yaki sai kalmaru da Hamsaru ne suke walkitarsa sai sarki Barham yasa aka kirawoshi suka kebe inda ya dubeshi yace , ''ya kai dirkar birnin zamar kasani cewa kai yanzu tsufa ya riskeka har ta kai cewa ka kasa ruke mukaminka, sai ya'ya'nka ne suke kula dashi, sbd haka inason a cikin ya'yan nan naka ka zabi daya daga cikinsu wanda kake ganin cewa shine mafi cancanta daya gajeka, Lokacinda sarkin yaki yaji wannan batu na sarki Barham, sai hankalinsa ya dugunzuma ainun sbd shi baxai iya zabar daya daga cikinsu kalmaru ba. Duk da cewa a zuciyarsa yafi son dan cikinsa kalmaru ya gajeshi sbd bayason wani abu da xai kawo sabani tsakaninsa da dan uwansa wato mahaifin Hamsaru. Sarkin yaki yai shiru yana tunani har izuwa tsawon wani dan lokaci sannnan ya dago kai ya dubi sarki Barham yace, ''ya shugabana kai da kanka ka sani cewa Hamsaru yafi kalmaru tsagwaron karfin damtse da iya yaki, Amma kuma kalmaru yafi Hamsaru sa'a da taurin zuciya da naci. Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi wanda zai gajeni ba daga cikinsu ba. MAZA SUN FADI!!! Part 2 Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi wanda zai gajeni ba daga cikinsu. Kamata yayi kai da sauran yan majalisa ku zauna kuyi tunani kuyi zabin da kanku bisa wanda kuke ganin yafi cancanta, Kasani cewa idan na zabi dana kalmaru zan sami matsala da dan uwana mahaifin Hamsaru wato YUNARU,har zumuncin mu ya raunana '' Sa'adda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai sarki Barham yai shiru yana nazarin al'amarin. Daga can sai ya dago kai ya dubeshi yace, ''ya kai dirkar birnin zamar hakika na karbi uzurinka, Amma baza mu zabi magajinka ba Nida yan majalisata kadai ba, Abinda zamuyi kawai shine, zamu shirya gasa ta jarumtaka tsakanin kalmaru da Hamsaru, su yaki juna a tsakiyar fada agaban alkalan gasa, 'yan majalisa da mutanen gari. Wanda da duk yasami nasara kai wani kasa daga cikinsu shine zai gajeka, Koda jin haka sai mamaki da tsoro ya kama sarkin yaki ya dubi sarki Barham cikin tsananin damuwa yace, '' haba ya shugabana ai bai kamata ayi hakan ba tunda kowa ya san cewa Hamsaru yafi kalmaru karfin damtse da iya yaki. Sarki Barham yai ajiyar zuciya yace, ''ya kai abokina kasani cewa kai aminina ne kuma tun muna yara muka taso tare, Bamu taba rabuwa ba, Ko ayanzu daka tsufa har takai cewa baka iya zuwa fada, bana shafe kwana 2 bankai maka ziyara ba har gidanka, Wannan tsufa naka da rashin kuzari a jikinka yanada nasaba da asirin da dan uwanka yayi maka yasa maka rashin lfy sbd bakin cikin kasami sarautar sarkin yaki shi bai samuba, Ka sani cewa duk fadin kasar nan ni Kadai ne na san wannan Sirri kuma bantaba gayawa wani ba. Ta yaya kake tsammani cewa zanso dansa ya zama sarkin yakina? '' A koda yaushe ciwon dake jikinka xai iya zama ajalinka, Idan har ka tafi ka barni zanso ace na rinka ganin danka akusa dani tunda kammaninku iri daya ne sak tamkar an tsaga kara, tunda idan ina ganinsa zan samu saukin kewarka. Lallai zanso ace kalmaru ya gajeka, Zan iya amfani da karfin kujerata na tabbatarda cewa kalmaru ya gajeka, To amma idan nayi hakan jama'a zasu ce nayi son zuciya sbd ansan kusancina dakai. Nayarda da sa'ar danka kalmaru gamida da nacinsa don haka nayi imani cewar zai iya lashe wannan gasa'' Lokacin da sarki Barham yazo nan a zancensa sai idanun sarkin yaki suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa yace,, ''yakai abokina nasani cewa kana son ka kasance dani da zuri'arka har karshen rayuwaka to amma dole mu rungumi kaddara domin hakan baxai taba yi yuwa ba. Na yarda batun wannan gasa da kashirya kuma ina yiwa mai sa'a fatar samun nasara '' Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki Yayiwa sarki Barham sallama ya mike tsaye da kyar! Sbd laulayin rashin lfy da tsufa ya fice daga cikin dakin dasu ka gana. Tafiyar sarkin yaki ke da wuya sai sarki Barham ya kira wani babban hadiminsa wanda ake kira zilla ya umurceshi da yaje yasa ayi shelar wannan gasa da za'a yi a fada a gobe kuma ana gayyatar kowa da kowa birni da kauye. Nan take kuwa zilla yaje ya cika umurni, Lokacin da mutanen gari suka ji wannan shela sai aka cika da tsananin mamaki domin a tarihin masarautar ba'a taba shirya gasa ba akan zaben sarkin yaki. Kawai sarki ne yake duba cancanta ya zabarwa kansa sarkin yaki, Lokacinda kalmaru yaji ansa gasa tsakaninsa da dan uwansa Hamsaru akan takarar kujerar sarkin yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun don haka sai ya shiga cikin turakar sarkin yaki ya sameshi kuwa a zaune yayi tagumi yana tunani. Kalmaru ya xauna daf da sarkin yaki ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa yace,, ''ya kai Abbana saboda me kana raye da lafiyarka kuma kanaji kana gani zaka bari a aiwatar da abinda zai haddasa gaba tsakanina da dan uwana Hamsaru kuma ya lalata zumuncin dake tsakanika da dan uwanka?'' Ina mai rokonka daka hanzarta komawa yau wajen sarki ka nemi alfarma a janye wannan gasa, Ni kam na hakura na baiwa dan uwana Hamsaru wannan kujera. Shin ka manta ne da halin mahaifin Hamsaru? '' Akan Hamsaru ya mallaki wannan matsayi babu abinda baxai iya ba koda kuwa sai ta kai cewa an hallakani ko kai an hallaka ka'' Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaki, ya dubi kalmaru yace,, ''ya kai dana kayi sani cewa bakin alkalami ya bushe. Domin babu abinda zanyi wanda zai sa sarki ya janye batun wannan gasa, Hakika so sone amma son kai yana gaba da komai , Babu yadda za'ayi naso wani ya gajeni face kai, Kawai kaje ka fara shirye-shiryen wannan gasa da za'a yi gobe, Wanda keda rabo a cikin ku shine zai gajeni,, Daga yanzu zuwa gobe ka tsare kanka domin za'a iya yunkurin cutar dakai ko kuma a hallakaka. Na sallameka kuma banason naji wani korafi daga bakinka, Cikin alamun tsananin damuwa kalmaru ya juya ya fice daga cikin turakar sarkin yaki. ****** AL'AMARIN Hamsaru kuwa lokacin da yaji cewar sarki ya shirya gasa tsakaninsa da dan uwansa kalmaru akan zaben sarkin yaki bisa cewar duk wanda ya kai wani kasa shine zai sami mukami sai ya kamu da tsananin farinciki sbd yana ganin cewa tunda yafi kalmaru karfi da iya yaki dole ne ya sami nasara lashe gasar sarkin yaki. Kai tsaye Hamsaru ya wuce izuwa cikin gidansu fuskarsa cike da walwala da annuri, Yana isa turakar mahaifinsa sai ya iske mahaifinsa da mahaifiyarsa a zaune sunyi jugum- jugum kamar anyi mutuwa. Al'amarin da yai matukar baiwa Hamsaru mamaki kenan ya dubesu cikin damuwa yace,, ''yaku iyayena menene kuma ya faru haka na ganku acikin yanayin damuwa? Dajin wannan tambaya sai mahaifiyarsa ta dago kai tace,, ''ya kai Hamsaru sbd me ba zamu kasance a cikin tsananin damuwa ba alhalin mun kwallafa burin mu gaba daya akan gasar da za kayi gobe kuma gashi bamuda tabbacin cewa zaka lashe gasar, Koda jin haka sai mamaki ya sake turnike Hamsaru yace, Me kike nupi da cewar burinku yana kan wannan gasa da zanyi kuma sbd Me kuke shakkar nasarata alhalin kunsan cewa nafi kalmaru karfi da iya yaki, Dajin haka sai YUNARU mahaifin Hamsaru ya numfasa ya dubeshi yace, Kai yanzu kana ganin cewa zaka iya kai kalmaru kasa ne da karfin damtsenka da iya yakin ka?" To ka sauya tunani tunda wuri domin kuwa idan bamuyi amfani da yaudara ko ha'inci babu yadda za'ayi ka sami nasara akan kalmaru sbd ya fika naci da juriya, Ina mai tabbatar maka da cewa zai iya jure duk irin wani sara da sukan da zaka rinka kai masa gami da naushi da bugun hannu da kafa har izuwa lokaci mai dan tsawo sa'adda zaka gaji ya sami nasara akan ka. MAZA SUN FADI!!! Part 3 Na fuskanci cewar har yanzu kana shakkar abinda nake fada maka, Shin kun taba yin gurmuzun da ya kai na rabin sa'a kai dashi a yayin da kuke baiwa juna horo? " Koda jin wannan tambaya sai jikin Hamsaru yayi sanyi yace, Ai bamu taba yin gurmuzun da yakai na tsawon dakika dari biyu ba ni dashi, YUNARU yayi dan guntun murmushi yace, Shiyasa ba zaka taba fahimtar bam-bamcinka dashi ba, ai kallon kitse kake yiwa rogo. Na rantse da darajar iyayena bazaka iya kai kalmaru kasa ba domin ya gado kakanmu a tsananin juriya da naci, Hatta yanayin jikinsa da sifofin jikinsu duk iri daya ne, Har kakanmu ya bar duniya ba'a taba samun jarumin da ya kai shi kasa ba kuma komai yawan dakaru shi kadai yana iya tarwatsa su, Hakika MAZA SUN FADI!!! Inda ace kakanmu har yanzu yana raye a doron kasa a wannan zamani kuma yana cikin koshin lfy da rashin cutar tsufa irin wacce ta kama dan uwana sarkin yaki a yanzu da zai iya mulkar duniya Gaba daya, abu daya nake tsoro. Wani boka ya tabbar mini da cewa idan har kalmaru ya yi aure to zai iya haihuwa dan da zai sami gagarumin karfi irin na kakanmu kuma xai iya mulkar duniya Gaba daya. ''Ya kai dana kayi sani cewa dole sai idan ka lashe wannan gasa akan kalmaru sannan zamu iya hanashi yin aure bare har ya haifi dan da zai mulki duniya." Sa'adda YUNARU yazo nan a zancensa sai kan Hamsaru ya sake daurewa yace,, Ta yaya zaka iya hana kalmaru yin aure ta hanyar amfani da karfin kujerata ta sarkin yaki? " YUNARU ya sake yin murmushi a karo na biyu yace,, "kada ka damu zaka sani nan gaba idan ka hau kan kujerarka. Abinda nake da kai shine , ka kwantar da hankalinka tuni na gama tunani akan yadda zaka sami nasara akan kalmaru ka kaishi kasa kuwa a daren yau zangama shirina, Kaje kayi kwanciyarka kasha barcinka, Kada ka wahalarda kanka wajen kokarin baiwa kanka horon yaki a yau sbd gasar ta gobe, Dajin haka sai Hamsaru ya mike tsaye ya fice daga cikin fallon ya tafi izuwa dakinsa yana mai mamaki zullumi gamida tunanin irin abin da mahaifin nasa xai shirya don tabbatarda samun nasararsa a Wannnan gasa, Har izuwa wannan lokaci Hamsaru bayajin shakkar komai a cikin zuciyarsa bisa fuskantar kalmaru, Abin da Hamsaru baisaniba shine, Kalmaru baya sakin jikinsa da karfinsa gaba daya a duk sa'adda zasuyi gurmuzun sbd yana girmamashi Amatsayinsa na yayansa wanda ya girmeshi a shekara ***** LOKACIN da kalmaru ya isa turakarsa sai ya iske mai kula da abincinsa wata baiwa mai suna ZULAIMA ta shirya masa abincinsa akan tebur ta kawo ruwan inibi acikin tulu ta ajiye, Zulaima tsohuwa ce wadda shekarunta sun haura saba'in, Tun kalmaru baifi shekara shidda ba a duniya Zulaima take rainonsa sakamakon mutuwar mahaifiyarsa har kalmaru ya girma bai san uwarsa ba sai Zulaima domin itace take masa komai kamar yadda kowace uwa keyiwa danta, Kalmaru da Zulaima sun shaku ainun kuma sun yarda da juna ainun, Shi kansa sarkin yaki ya yarda da Zulaima dari bisa dari domin tun tana budurwa ya siyeta a matsayin baiwa har yazo ya 'yantata amma wani abu bai taba shiga tsakaninsu ba domin ya dauketa tamkar 'yar cikinsa, Duk da cewa ya yantata sai ta kasa tafiya ta barshi, tayi alkawarin zata zauna tare dashi har izuwa karshen rayuwata tana yi masa bauta gami da kula da dansa guda daya jal! Wato kalmaru, Lokacin da sarkin yaki yaji wannan batu na Zulaima sai ya cika tsananin mamaki yace, yake Zulaima kiyi sani cewa ni tunda nake ban taba ganin bawan da aka yanta shiba amma ya ki karba 'yancinsa ba sai ke. Sbd me kika zabi ki karar da rayuwarki a cikin bauta? " Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Zulaima tace,, ''ya shugabana kayi sani cewa tun inada shekara tara a duniya 'yan hari suka shigo birninmu suka kashe iyayena da dukkan mutanen garinmu, A sannan ne aka kamani a matsayin baiwa aka tafi dani aka siyar dani a can wata Nahiyar daban, Haka akayi ta yawo dani kasa-kasa har aka kawoni nan birninku na ZAMAR ka siyeni, Bani da kowa a yanzu kuma bani da komai sai kai. Na daukeka tamkar mahaifina domin kaine ka debe mini kewar iyayena, haka kuma gashi na shaku da danka kalmaru ina kallonsa tamkar dan cikina duk da cewa ni ban taba yin aure ba bare ma na haihu, Idan na tafi na barku da wa zan ci gaba da rayuwa wanda xai aminta dani kamar yadda kuka aminta dani?" Koda Zulaima tazo nan a zancenta sai tausayinta ya turnuke sarkin yaki har kwallah ta cika masa idanunsa ya rungume Zulaima yana mai Cewa ni kaina idan kika tafi kika barni zan zamo acikin tsananin takaici bakin ciki da tunani domin kin zama tamkar jinina" Daga wannan rana Zulaima taci gaba da zama a gidan sarkin yaki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Kamar yadda Zulaima ta saba a koda yaushe lokacin da taga kalmaru ya shigo cikin turakar sai tayi masa barka da zuwa kuma ta janyo masa kujera daga karkashin tebur domin ya zauna yaci abinci, Cikin sanyi jiki kalmaru ya zauna a kujerar, Koda ya dago kai ya hada ido da Zulaima sai yaga idanunta sun kada sunyi jawur kuma sun ciko da kwallah, Al'amarin da yai matukar bashi mamaki kenan kuma ya dugunzuma hankalinsa ya dubeta yace,, '' yake Zulaima menene ya faru da a gareki har naga kwallah a idanunki?" Kamata yayi yau ace kina cikin tsantar farin ciki bisa abinda xai sameni gobe idan na lashe gasar da za'a yi tsakanina da dan uwana Hamsaru." Koda jin wannan tambaya sai jikin Zulaima yyi sanyi ta zauna akan kujerar dake fuskarta kalmaru tace, ya shugabana kayi sani cewa tun kafin mahaifiyarka ta rasu ta damka amanarka a hannuna, Amma yanzu gashi inaji ina gani bazan iya kare rayuwarka ba tunda gobe zakayi wannan gasa mai mugun hadari wacce zaka iya rasa rayuwaka." Koda jin haka kalmaru yayi dariya yace, haba Zulaima ai indai dan Wannnan dalilin ne kika tashi hankalinki to ki cire dukkan damuwa, Ina mai tabbatar miki cewa babu abinda zai sameni koda kuwa Hamsaru yakaini kasa, Sa'adda kalmaru yaxo nan a jawabinsa sai Zulaima ta fashe da matsainacin kuka ta mike tseye zumbur ta ruga da gudu izuwa cikin dakinta ta turo kofa ta rufe, Cikin tsananin tashin hankali kalmaru ya mike tsaye ya ruga izuwa kofar dakin na Zulaima ya rinka kwankwasa kofar yana kiran sunanta kuma yana rokonta akan ta bude kofar amma sai taki bude kofar kawai taci gaba da rusa kuka. Al'amarin da yai matukar baiwa kalmaru mamaki kenan kuma ya jefashi a cikin zullumi, ''To wai shin anya kuwa babu wani boyayyen al'amari dake shirin faruwa wanda Zulaima ta boye masa?" MAZA SUN FADI!!! Part 4 " To wai shin anya kuwa babu wani boyayyen al'amari dake shirin faruwa wanda Zulaima ta boye mini? " Amsar da kalmaru ya kasa baiwa kansa kenan, Ya Juya ya koma izuwa kan tebur ya zauna ya cigaba da cin abincisa har sai da yaji koshi sannnan ya zuba wannan ruwan inibin a cikin kofi har ya kai bakinsa xai kurba sai ya fasa sakamakon ganin sauyin yanayi acikin ruwan inibin, Wannnan karon launin ruwan inibi ya dan sauya, Kalmaru yai shiru yana tunani yace a ransa, " yau kuma me Zulaima ta kara acikin ruwan inibin nan?" To menene ma zan damu tunda na tabbatarda cewa babu yadda za'ayi Zulaima ta cutar dani ko kuma a hada baki da ita a cutar dani. Yana gama fadin hakan sai yasa kofin a bakinsa ya kama sha. Nan da nan ya shanye kofin guda ya sake karawa har sai da ya shanye kofi shidda sannan mike tsaye ya shige cikin dakinsa ya baje akan gado ya kama barci. Kashe gari da sassafe sarkin yaki ya tashi ya kimtsa domin yanason ya raka kalmaru izuwa fada domin ayi wannan gasa agaban idanunsa, Yana shiga cikin dakin kalmaru sai ya cika da mamaki domin ganinsa yayi a kwance yana ta faman sharar barci. Cikin fushi sarkin yaki ya daka masa tsawa da karfi, Afirgice kalmaru ya farka firgigit! Ya mike zaune yana mai bude idanunsa da kyar! Yana mika. Kawai sai yaji wani irin rashin kuzari a jikinsa wanda bai taba jin irinsa ba, Sarkin yaki yace, " Baka da hankali ne da zaka kwanta kayita sharar bacci gashi har rana ta fito Alhalin kasan cewa yau ne zakayi gasar neman kujerata? " Cikin alamun damuwa kalmaru ya dubi sarkin yaki yace, " ka gafarceni ya kai Abbana ni kaina nayi mamakin ganin yadda akayi na makara kuma yanzu ma dana tashi sai naji Inajin muguwar kasala." Koda jin haka sarkin yaki ya dubi kalmaru cikin firgici da tsananin damuwa yace, "shin kafin ka shigo gida wani ya baka wani abu ne kaci? Kalmaru yace " ai ban yarda naci komai ba sai da nazo nan gida sbd na kiyaye gargadin da kayi mini." Sarkin yaki ya gyada kai yace, shi kenan maza kaje ka kimtsa zan jiraka a falo kazo muyi kalaci tare sannan mu tafi fada. Na tabbatarda cewa yanzu haka fada ta cika makil, Banason muje a makare bayan sarki ya fito domin laifi ne babba." Dajin haka sai kalmaru ya sauko daga kan gadonsa da sauri ya shiga kewaye yayi wanka. Har kalmaru ya gama wankan ya sanya kayan yaki ya dauki takobinsa da kufe bai daina jin wannan rashin kuzari ba a jikinsa, Sai ya dangana al'amarin da yunwa tunda jiya da daddare ma bai tsaya yaci wani abinci ba mai yawa ba, da wannan ruwan inibin ya cika cikinsa, Yana zuwa ya iske sarkin yaki a zaune ga abincin kalaci bisa tebur a gabansa, Kalmaru yaje ya zauna akan kujerar dake fuskarta ta mahaifin tasa suka bude kwanukan abinci suka fara ci. A daidai Wannnan lokaci ne Zulaima ta kawo musu shayi a cikin buta bisa kan faranti dauke da kofuna biyu, Zulaima ta a ajiye farantin shayin a tsakiyarsu sannnan ta juya zata koma cikin dakinta, Sai sarkin yaki ya kira sunanta ta waigo, ya dubeta yace, "yake Zulaima wai shin menene yake damunki ne jiya cikin dare na jiyo shesshekar kukanki daga cikin dakina. Yanzu ma da kika zo gabana naga alamun kinsha kuka da safen nan domin ga idanunki nan sunyi jawur. Yanzu ashe har akwai wani abu da zai dameki ki kasa sanar dani?" Sarkin yaki ya dubi kalmaru yace, ko kai ta gayamaka abinda ke damunta?" Kalmaru ya gyada kai yace , bata gaya mini komai ba. " Koda jin haka sai Zulaima ta sunkai da kanta kasa tace, Tun jiya da naji za'ayi wannan gasa ne hankalina ya tashi na rasa sukuni harma jiya cikin barcina sai da nayi mafarki mai ban tsoro. Dajin haka sai sarkin yaki yai murmushi yace, "in dai don wannan ne ki kwantarda hankalinki babu wani abin damuwa, Ina mai tabbatar miki da cewa kalmaru zaije yayi wannan gasa lfy kuma zai dawo gida lafiya cikin nasara. Maza kije kici gaba da yan

Chapter 1 of 10