Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
ta dubi Humairu tace, " ta yaya akayi kasan wadanan abubuwa? " Humairu yayi murmushi yace, "Ni fa tsohon mafarauci ne wanda ya gudanar da rayuwarsa gaba daya a cikin daji. " Yana gama fadin Hakan sai lushairat ta juya ta sake goya jaririnta a baya wanda tuni ya dade da yin barci, sannnan ta lalabo duwatsu guda biyu ta karyi wani ice, ta hada kyastu ta kunna wuta a jikin icen ya zame mata fitila, ta kunna kai Izuwa cikin dajin. Amma kafin ta tafi sai da ta dauki Addar Humairu. Tun Humairu na hango lushairat har sai da ta kule a cikin dajin ya daina hangota. Tafiyar lushairat keda wuya sai ya fada cikin kogin tunani, inda ya rinka tuna duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninnsa da abokansa wadanda dakarun sarki labarusa suka kashe, da duk irin gwagwarmayar da suka yi shi da Hashlar da kuma yadda yayi rabuwar karshe da mahaifiyarsa da masoyiyarsa laila. Humairu ya tuno da yadda suka iske kauyensu bayan an kashe kowa an kone gidajensu. Koda yazo dai-dai nan a tunaninsa sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka. Yana cikin wannan hali ne yaji motsi daga can wani sako, alamar an durfafo inda yake. Cikin firgici ya lalubi inda takobinsa take yaji bai jita ba,ya yunkura da nufin ya mike tsaye ya nemi maboya, amma sai ya kasa saboda a wannnan lokaci kafar tasa ta kara yin tsami da kumburi fiye da farko, gashi dafin kibiyar data sokeshi yana yi masa tsananin zogi da radadi. Bisa dole Humairu ya saduda ya zuba ido kawai Izuwa inda yake juyo wannan motsi. Sannnu a hankali motsin ya rinka karuwa, kuma wani irin takun sawu ne mai karfi yake tunkaroshi. Kwatsam!m Ba zato ba tsammani sai ga wata narkekiyar kura mai tsananin muni da girman gaske ta bayana a gaban Humairu. Ita dai wannnan kura tafi shekara Ashirin a cikin wannan daji, kuma mafarauta sun dade suna kokarin kamata kosu kasheta amma abun ya gagara. An sha yin gangami a fito farautar wannan kura amma sai a kwana bakwai ana nemanta ba'a ganta ba. Duk bayan kwana talatin sai wannnan kura ta fito ta yiwa fatake ko mafarauta mummunar barna, ta kashe mutane da yawa. Har ma an canfa wannan kura da cewar iska ce ba dabba ba, musamman da akayi la'akari da siffarta. Dama Humairu ya dade yana jin labarin wannan kura,don haka a yanzu da yayi arba da ita sai ya firgita ainun ya tabbatar da cewar ajalinsa yazo. Kurar ta tsaya cak! A nesa kadan suka fara kallon kallo ita da Humairu tana nazarinsa. Koda ta lura da raunin dake kafarsa domin idanunta suna ganin komai sarai a dajin kamar ba dare bane. Koda kurar ta gane cewa Humairu ba zai iya tsinana komai ba sai ta yanke shawarar kawai ta daka tsalle sama ta turmusheshi tayi masa kwab daya. Ai kuwa sai ta daka wawan tsalle a sama zata dira akansa. Humairu ya kwarara uban ihu irin na wanda yaga mutuwa muraran! Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai yaji jini yayi tartsuwa akan fuskarsa, yana dago kai yaga an raba gangar jikin kurar gida biyu ta fado kasa matacciya. Yana kallon kasa yaga takobinsa na digar da jini, kuma ba wani bane ke rike da takobin tasa ba face gimbiya lushairat wacce ke goye da jaririnta. A daya hannun nata kuwa ganye ne da saiwar bishiyar da ta tafi nema. Bai san sa'adda ya wangame ba yana Kallon lushairat idanunsa a kafe kamar gunki. ******* DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 4 PART 4 ADVENTURE STORY NASEER SHEHU TEARLOW ******* Ai kuwa sai ta daka wawan tsalle a sama zata dira akansa. Humairu ya kwarara uban ihu irin na wanda yaga mutuwa muraran! Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai yaji jini yayi tartsuwa akan fuskarsa, yana dago kai yaga an raba gangar jikin kurar gida biyu ta fado kasa matacciya. Yana kallon kasa yaga takobinsa na digar da jini, kuma ba wani bane ke rike da takobin tasa ba face gimbiya lushairat wacce ke goye da jaririnta. A daya hannun nata kuwa ganye ne da saiwar bishiyar da ta tafi nema. Bai san sa'adda ya wangame ba yana Kallon lushairat idanunsa a kafe kamar gunki. Har sai da tazo ta tsugunna a gabansa ta fara kwance tsumman da aka daure raunin nasa dashi sannnan ya dawo cikin haiyacinsa yana mai yin doguwar ajiyar zuciya. Lokacin da lushairat ta gama kwance tsumman taga irin zurfin raunin nasa sai hankalinta ya dugunzuma ainun, Shi kansa jarumi Humairu sai da ya firgita da ganin raunin yaji kamar yace ta sare kafar gaba daya ya huta. Kawai sai lushairat ta sake yagar gefen rigarta ta cusa a cikin bakin Humairu ta dubeshi tace, ihun da zaka yi yanzu sai yafi wanda duk kayi a baya. Tana gama fadin Hakan sai ta mike tsaye taje ta saro wata danyar jijiyar bishiya doguwa tazo ta kama hannayen Humairu ta dauresu tamau a jikin bishiyar, sannnan ta kama daya lafiyayyeyar kafar tasa itama ta daureta tamau. Daga nan sai ta dake wannan ganyen bishiya data samo, dama busasshe ne, ya zama gari. Wannan saiwar bishiyar kuwa sai ta zubata a cikin wani dan karamin kasko data dora akan wuta ta shiga dafawa. Koda tazo ta sake zama a gaban Humairu ta debo wannan dakakken ganyen zata cusa a cikin ramin raunin sai ta dubi Humairu, shi kuwa sai yayi mata murmushi. Koda ta cusa maganin a cikin raunin a karo na farko sai Humairu yayi wani irin zallo, ya rintse idanunsa ba tare da yayi ihu ba. Al'amarin da yai matukar bata mamaki kenan, amma daya bude idanunsa sai ga hawayen wuya ya zubo masa. Haka dai taci gaba da cusa garin maganin yana ta mutsu-mutsu yana hawaye har ta gama sa masa magani. Tana gamawa sai ta dubeshi tayi masa jinjina, tace Mazaje da yawa wadanda suka sami irin wannnan rauni idan akazo ana sa musu wannnan magani mutuwa suke yi kosu suma, amma kai, yanzu gashi ka jure, tabbas ka cika GWARZON JARUMI mai juriya abin kwatance. Ina mai tabbatar maka da cewa nan da cikar sa'a guda kumburin kafar taka zai sace gaba daya, kuma zaka iya taka kafarka muci gaba da tafiya. " Koda jin wannnan batu sai farin ciki ya lullube Humairu ya dubi lushairat yayi mata godiya bisa yi masa wannnan magani da tayi. Koda jin wannnan godiya sai lushairat tayi murmushi tace, "Ai bai kamata kayi mini godiya ba tun da har yanzu banyi maka rabin abinda kayi mini ba nida jaririna. Ko anan na rasa rayuwata nida dana ka gama cika alkawarin da ka daukarwa mijina. Lallai kana bina bashi don ka sallama rayuwarka don ceton tamu rayuwar nida dana. Ina mai tabbatar maka da cewa RINTSI DA TSANANI daka shiga a can gidan sarautarmu ka shigo har ka sami damar fita a raye babu wani jarumi da zai iya ta iba Marigayi ba." Koda tazo nan a zancenta sai idanunta suka ciko da kwallah, hawaye ya subuto mata, nan take tausayinta ya kama Humairu, ya dubeta cikin alamun tausayawa yace, "ya shugabata hakika rayuwarki abar tausayi ce,tunda kin taso a cikin Daula, jin dadi da mulki, amma yanxu gashi kece a cikin daji kina rayuwa irin ta dabbobi wadanda basu da gidan kwana da abinci sai sun nema dare da rana. Lushairat ta gyada kai tace, "Ai ni da kai duk ababan tausayi ne tunda kaima an tarwatsa kauyenku da Danginku. An rabaka da abokanka, kuma aminanka wadanda tun yarinta ku ka taso tare kuma kuka shaku da juna ainun kamar hanta da jini. Haka dai Humairu da lushairat suka ci gaba da hira har Izuwa tsawon sa'a guda basu sani ba. Kamar da wasa Humairu yaga gaba dayan kumburin kafarsa ya sace,kuma ta daina zogi da radadi. Cikin mamaki ya yunkura ya matsa kafar, nan ma sai yaga ya iya takata har ma ya mike tsaye daram! Ba tare da ya dafa komai ba. Al'amarin da ya jefashi cikin dumbin farin ciki kenan mara misaltuwa. Bai san sa'adda ya kama yin tsalle da Rawa ba. Ita kuma lushairat sai ta bishi da kallo tana ta faman yi masa dariya. Suna cikin wannan hali ne suka jiyo sukuwar dawakai daga can nesa, cikin hanzari suka kashe wutar da lushairat ta dafa magani kuma suka kwashe komai nasu daga wajen suka baje kasa sannnan suka ruga Izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suka buya. Suna nan a boye sai suka hango wadansu mahaya Kimanin su arba'in sun durfafo inda suke a sukwane bisa giwaye. Duk sa'adda sawun giwayen ya bugi kasa sai kaji dajin gaba daya ya kama girgiza kamar sama zata dawo kasa. Ba wasu bane akan wadanan giwaye face wadansu zakwakuran dakarun sarki labarusa mafiya kwarjini da karfi. Sai da wannnan zuga ta iso dai-dai inda su Humairu ke boye sannnan suka ja tunga suka tsaya suka kama waige waige da kalle-kalle suna muruzai kamar zasu ci babu. Ga fitilun wutar ice nan a hannunsu suna haska gabas da yamma, kudu da arewa ko zasu ga wani abu, kuma sun kasa kunnuwansu ko zasu ji wani motsi komai kankatarsa. Sai da suka shafe dakika dari da Ashirin a haka sannnan daya daga cikinsu ya sauka kasa daga kan giwarsa ya sunkuya ya damki kasar wajen ya shinshinata. Kawai sai ya dubi sauran 'yan uwan nasa yace, tabbas bil'adama yazo nan bada jimawaba, mu bincika cikin duhuwoyin can babu mamaki wadanda muka zo nema sunji motsin zuwanmu sun ruga sun buya." Koda lushairat ta jiyo wannan batu sai hantar cikinta ta kada, ta kamu da tsananin tsoro jikinta gaba daya ya kama tsuma. A wannan Lokaci suna kwance a cikin ciyawa sunyi rub-da-ciki ita da Humairu, kuma suna daf da juna. Koda Humairu yaga jikin lushairat ya kama karkarwa har hakoran bakinta sun fara gugar juna, a koyaushe za'a iya jiyo motsinsu, sai yai wuf! Ya janyota Izuwa kan kirjinsa ya rungumeta kuma ya toshe bakinta da hannunsa guda. A hakan suka mike tsaye a hankali suka kara gaba suna tafiyar sanda, hannunsa guda na rike da sharbebiyar wukarsa. Kafin wadanan dakarun su iso cikin wannan duhuwar bishiyoyin tuni sunyi nisa har sun bar cikin duhuwoyin. Sai dai suna isa karshen bishiyoyin suka yi kicibis da wani Ruwa mai dauke da tabo, kuma babu wata hanya daza su iya bi su ratse wannan tabo. Saura kiris! Ma santsi ya kwashesu su fada cikin tabon, suka yi tirjiya suka kurawa tabon idanu cikin alamun tsananin tsoro, kuma a Lokacin ne suka jiyo takun sawun dakarun a can cikin duhuwoyin da suka baro. Humairu ya dubi lushairat cikin karamar murya yace, Ranki ya dade ba muda wani zabi face mu fada cikin tabon nan mu nutse a cikinsa mu buya kafin mutanen nan su iso nan. Cikin fishi da tsoro lushairat ta dubeshi tace, "Baka da hankali ne? "ai duk abinda ya fado cikin wannan tabo ba zai yi rai ba. Ni ban damu da rayuwata ba,amma na damu da rayuwar jaririna.... " Kafin lushairat ta gama rufe bakinta tuni Humairu ya shammaceta ya doki wuyanta da hannunsa, kawai sai ta Sulale zata fadi kasa, yai sauri ya rukota, kuma ya ciro jaririnta daga Bayanta ya rungumeshi a kirjinsa ya daka tsalle suka fada cikin ruwan tabon suka lume a cikinsa gaba daya. Suna lumewa ya zaro wani karan bishiya mai huda saman tabon don zukar iskar numfashi. Faruwar hakan keda wuya sai ga wadanan dakI'll aru na sarki labarusa sun rugo da gudu Izuwa wajen suna haska fitilun itatuwa dake hannayensu. Koda suka yi kicibis da wannnan kogin tabo sai suka yi tirjiya suka tsaya cak! Suka yi nazarin wajen gaba daya basu ga alamar sawun komai ba. Wani daga cikinsu sai ya dubi shugabansu yace, "Anya kuwa wadanan muke nema basa cikin wannan tabo?" Koda jin wannnan tambaya sai shugaban nasu ya daka masa harara gamida tsawa yace, baka da hankali ne?" Ai duk wani abu mai rai idan a cikin wannan kogi ya mutu kenan, kuzo mu garzaya Izuwa wancan bangaren, a can nake zargin sun buya. Nan take su duka suka ruga suka bar wajen. Sai bayan yan dakiku kadan da tafiyarsu sannnan Humairu ya dago Izuwa saman kogin tabon tare da lushairat wacce har a sannnan bata farfado ba daga dogon suman da tayi. Shi kuwa jaririn nata in ban da tabo da ya wanke masa fuska da sai kace dariya ma yake yi saboda wutsil wutsil kawai yake yi da hannayensa da kafafunsa yana ta gyada kai. Cikin hanzari Humairu ya jinjin a kirjinsa sannnan ya goya lushairat a bayansa ya daureta tamau. Koda ya juya da nufin ya ruga daya bangaren wanda bashi dakarun suka bi ba sai yayi arba da daya daga cikinsu a tsaye rike da sharbebiyar takobi a hannunsa yana tsuma. Ba wani bane face wannan badakaren wanda yace yana zargin cewa wadanda suke nema suna nan a cikin wannan tabon. Ashe dama shi kadai ne ya jiyo motsi a cikin duhuwar bishiyoyin, da yake shine akan gaba. Koda Humairu yayi arba da wannnan badakare ya dubi bayansa da gefensa ya tabbatar da cewar shi kadai ne ya tsaya, sauran yan uwan nasa sun yi gaba, sai kawai ya falfala da gudu Izuwa kansa. Ai kuwa shima badakaren sai ya rugo Izuwa gareshi yana mai daga takobinsa sama cikin mugun nufi. Yayin da ya rage baifi saura taku hudu ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama suka kaiwa juna mugun hari. Shi dai badakaren wawan sara ya kaiwa humairu a wuya da nufin ya tsinke masa kai, cikin bakin zafin nama Humairu ya sunkuya, amma duk da haka sai da kaifin takobin ya yanke masa wani bangare daga cikin gashin kansa. Shi kuwa Humairu tuni ya sokawa badakaren takobi a kasan wuyansa gefen kirjinsa. Takobin ta nutse a cikin kirjin badakaren ya kwarara uban ihu ya durkushe kasa. Ihun nasa ne ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa, har sauran yan uwansa dakaru suka jiyo ihun nasa daga inda suke, suka juyo da sauri a guje kuma a fusace. Suna isowa bakin gabar wannan kogin tabo sai suka iske gawar dan uwansu durkushe a kasa bisa guiwoyinsa. Koda suka ga sawayen Humairu sai suka sake bin sawunsa a guje har suka fara hango Humairu daga nesa goye da lushairat yana ta falfala masifaffen gudu. Nan fa suka kasa tsere dashi, duk da cewar su akan giwaye suke sai suka kasa cimmasa, domin karfin gudunsa ya shallake hankalinsu da tunaninsu. Kai inda ace mutum na nan a cikin wannan daji yana ganin irin azababben gudun da Humairu keyi zai yi zaton iska ce take kara masa karfin gudun. Kafin a jima da fara yin wannnan tsere tuni na gaba yai gaba, na baya sai labari, domin tun dakarun na hango Humairu sai da ya bace musu bat! Ya kule a cikin dajin. Amma saboda naci basu daina binsa ba har tsawon sa'a uku. A sannnan ne giwayensu suka gaji likis! Suka zube kasa tare dasu. ****** An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9