Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
kana mai yin bara kana cewa, "waye zai ciyar da kai yanzu ni kuwa na ciyar dashi iya rayuwarsa? " Tabbas wannan sarauniya zata sa a baka abincin da zaka koshi. Bayan nan ka tambayeta babban burinta na duniya, lallai zata zo maka da barun wani littafi wai shi TSATSUBA Lallai kai ne zaka yi jagora bisa tafiyar da za'a yi ta neman wannnan littafi. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA BIYU PART 6 MR NASSEER ****** Kada ka kuskura ka kwana a wannan gari da zarar ka koshi sai kayi harama ka sayi doki ka hau ka cigaba da tafiya. Ina mai tabbatar maka da cewa sai ka shekara arba'in da biyar kana wannan tafiya kana ta keta dazuzzuka da birane. A sannnan ne zaka cika shekara hamsin da daya a duniya, kuma a wannan Lokaci ne guzurin dake cikin jakarka zai kare, za ka iso wani babban Birni inda wata mashahuriyar sarauniya ke mulki. A sannnan ne yunwa zata gallabeka don haka ka nemi hanyar gidan sarauta. Kana zuwa fada ka wuce kai tsaye Izuwa gaban katangar mulki kana mai yin bara kana cewa, "waye zai ciyar da kai yanzu ni kuwa na ciyar dashi iya rayuwarsa? " Tabbas wannan sarauniya zata sa a baka abincin da zaka koshi. Bayan nan ka tambayeta babban burinta na duniya, lallai zata zo maka da batun wani littafi wai shi TSATSUBA Lallai kai ne zaka yi jagora bisa tafiyar da za'a yi ta neman wannnan littafi. Tabbas za'a samu wannan littafi har bukatar wannan sarauniya ta biya. A sannnan ne zaka sami lada mai tsoka daga wajen sarauniyar kamar yadda tayi alkawari zata bayar ga wanda duk ya samo mata littafin TSATSUBA. A cikin tafiyar da zaku yi ne zaka sami daukaka irin wacce babu wani boka da ya taba samunta har duniya ta shude baza a manta da kai ba a cikin tarihi. Amma ka sani cewa zaku sha tsananin ukuba a cikin wannan tafiya kuma zaku ga abubuwan al'ajabi da yawa. Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na cika da tsananin mamaki na dubeshi cikin alamun rashin fahimta nace, " ya kai abbana yanzu ni da nake malalaci, matsoraci, kuma dakiki ya za'a yi na iya jagora a cikin wannan gagarumar tafiya alhalin ma ban inda za'a je ba bare a samo wani littafi wai shi TSATSUBA? " Ya yin da mahaifina yaji wannan tambaya sai ya yunkura domin ya bani amsa amma sai tari ya sarkeshi yaci gaba da aman jini. Al'amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na dimauce naci gaba da matsanancin kuka ina mai kankame mahaifina. Daga can sai ya daina wannan kumallon sannnan ya janyeni daga jikinsa muka fuskanci juna sossai a Lokacin da idanunsa ke lumshewa yana budewa da kyar sai ya budi baki yace,"ya kai dana abin kaunata kayi sani cewa muddin kana tare da wannnan jaka ta guzurinka babu abinda zai gagareka kuma babu wani tsautsayi da zai sa ka rasa rayuwarka. Sai kun yi shekara daya da rabi sannnan zaku isa inda littafin TSATSUBA yake,kuma wannnan jaka taka itace zata rinka yi muku jagora. Baza ku sami nasarar zuwa inda wannnan littafi yake ba sai kun hadu da wadansu jarumai guda hudu uku mata ne,daya namiji ma'abocin wani addini da ake kira MUSULUNCI. Wannan jaka taka itace zata kaiku wajen wadanan jarumai guda hudu. Sa'adda naji wannan batu sai na kara cika da tsananin mamaki bisa yadda za'a ce jaka zatayi mana jagora a cikin wannan doguwar tafiya alhalin bata kasance abu mai rai ba kuma ba magana take yi ba. Har na budi baki zan tambayi mahaifina ta yadda wannan jaka zata yi mana jagora a cikin tafiyar sai naji gaba dayan jikinsa ya sandare kamar gunki,idanunsa kuwa suka kafe. Cikin dimauta na girgizashi amma ko motsi baiyi ba. Kawai sai na rungumeshi na fashe da matsanancin kuka. Cikin sauri na maida shi kan shimfidarsa na kwantar dashi sannnan na ruga Izuwa cikin turakarsa. Da shigata sai naje na dafa bakar akwatin mahaifin namu da hannun hagu faruwar hakan keda wuya sai akwatin ta Bude nayi arba da wata jaka wadda akayi ta da fatar damisa. Koda na dauki jakar sai naji ta da dan nauyi. Kawai sai na rataya jakar a kafadata na fita da sauri daga cikin gidan. Ai kuwa ina fita sai naga gidan namu ya kama nutsewa Izuwa cikin karkashin kasa har sai da ya lume gaba daya. A dai-dai wannnan lokaci ne hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shikenan na rabu da mahaifina, kasarmu da 'yan uwana har abada. Yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki. Kamar yadda mahaifina yayi mini jawabin tafiyar da zan yi da sharuddan da ya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba. Haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana. Hakika naga abubuwan al'ajabi da yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al'adu iri-iri. Gaba dayan rayuwata ta tsawon shekaru arba'in da biyar din acikin tafiya ta kare. Na shiga dazuzzuka iri-iri masu mugun hadari, amma duk bala'in da na shiga da duk masifar da ta tunkaroni sai na ga na tsira daga shairinta. Babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane face wannan jakar sihiri ta abbana. Sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar har ma nakan ji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face tarin wannan dinare. Haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani sauti a ciki. A ranar da na iso nan birnin ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa na tunkari wannan gidan sarauta sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirina. Kawai sai na bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zan ga komai ba. Bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin aljani mai rafkeken kai wanda girmansa bai wuce na fara ba. Cikin tsananin firgici na yarda jakar a kasa na ruga da gudu ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyana a gabana tsaye cikin iska. Cikin dimauta na yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam-gam na kasa koda motsa dan yatsan hannuna. Kawai sai naga wannan dan guntun aljani ya baiyana a hannuna yana mai kyalkyala mini dariya. Wani abin mamaki shine, mutane nata kai kawo a gabana amma basa iya ganin aljanin kuma basa jin dariyarsa. Daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace, "ya kai HUZAILATUL MARWASU kayi sani cewa yanxu kaine ubangijina tunda mahaifinka ya bar duniya. Lallai babu abinda zai rabani da kai face mutuwa. Sunana SUBAURATU IBNI KIMSASA, nine jikan Sarkin bokayen aljanu na farko na dari tara da casa'in da tara. Nine kadai na san inda littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta, kuma ni kadai ne na rage daga cikin zuri'armu gaba daya. Daga yau ka saki jikinka dani domin nine kadai zan sa ka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi, ka daina mugun cin abinci, kuma ka sami daukakar da ko mahaifinka bai samu ba. Yanzu sai ka mayar da ni cikin wannan jaka da hannunka domin idan na haura rabin sa'a a waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana." Koda gama fadin Hakan sai nayi sauri na dauke aljani subauratu da yan yatsun hannuna biyu ina karkarwar jiki na mayar dashi cikin wannan jaka sannnan na rataya jakar akan kafadata, kai tsaye na shigo cikin wannan gidan sarauta. Lokacin da huzailatul marwasu yazo nan a labarinsa sai sarauniya larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki. A karon farko a rayuwata sai ta kama huzailatul marwasu da hannayenta biyu ta rungumeshi tana mai cewa, "tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena. Sai da larbisa da huzailatul marwasu suka shafe sa'a bakwai suna hira a wannan rana tare ma suka ci abinci dare sannnan tasa aka kaishi masauki, Kuyangi suka yi masa wanka aka caba masa ado. Abinda ya baiwa larbisa mamaki shine, Lokacin da suka ci abinci loma daya jal huzailatul marwasu yayi yace ba zai iya cin komai ba. Sa'adda huzailatul marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitacen daki bisa kan luntsumemen gado na alfarma ga kyakkyawan Kuyangi suna yi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar mahaukaci sabon shiga. A wannan rana dai bai rintsa ba saboda tsananin farin ciki. Kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta. A sannnan ne kuma ta tura aka kirawo huzailatul marwasu. Koda aka je sai aka iske huzailatul marwasu yana ta faman shara barci bai tashi ba. Da aka Koma aka shaidawa larbisa sai tace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa har sai ya farka da kansa. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba'a taba ganin sauraniya larbisa ta girmama makaskanci ba. Haka dai larbisa da fadawanta suka ci gaba da jiran huzailatul marwasu har sai da ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa sannnan aka yi masa jagora Izuwa fadar. Koda shigowar huzailatul marwasu sai gaba dayan fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shi ba cewar shine wannan almajiri da yazo yai bara yana neman abinda zai ci. Cikin farin ciki larbisa ta mike tsaye ta taryo huzailatul marwasu ta jawoshi hae Izuwa kan karagarta ta zaunar dashi. Sannnan ta dubi 'yan majalisarta cikin nutsuwa tace," ya ku yan majalisar birnin daulatul luharus kuyi sani cewa wannan almajiri da yazo ya nemi abincin da zai ci a wajena shine wanda zai cika mini babban burina na duniya. Koda jin wannnan batu sai fadawan suka sake cika da tsananin mamaki. Larbisa taci gaba da bayani tana mai cewa, ya ku 'yan majalisata inaso ku sani cewa na taraku ne anan domin na sanar da ku cewa nan da kwana uku zanyi shiri ni da wannnan bako nawa mai daraja domin mu yi tafiya neman abinda zai biya mini bukatata. Saboda haka xan bar Amanar kasata a hannunku Kuci gaba da tafiyar da mulki kamar yadda nake gudanar dashi. Idan akwai wani mai korafi a cikinku bisa wannan hukunci dana yanke sai yayi yanzu naji. Lokacin da fadawan sarauniya larbisa suka ji wannan batu sai suka yi shiru suka kama kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala. Koda ganin haka sai larbisa ta sallami dukkanin fadawan nata suka fita suka barsu su biyu kacal ita da almajiri huzailatul marwasu Tsawon yan dakiku da fitar fadawan sai larbisa ta dubi huzailatul marwasu tace, ya kai dan boka mai daraja inason ka fito da aljani subauratu ibini kimsasa daga cikin jakarka ta sihiri domin ina da wadansu Tambayoyi masu matukar muhimmanci da nake son zanyi masa dangane da wannnan gagarumar tafiya da Zamuyi. Koda jin wannnan batu sai huzailatul marwasu ya fiddo jakar sihirinsa daga cikin babbar rigar jikinsa ya ajiyeta a gabansa sannnan ya bude ya zura hannunsa a ciki ya dauko aljani subauratu bin kimsasa ya ajiyeshi akan wani dan karamin tebir na zinare dake gaban sarauniya larbisa. Nan take subauratu yayi sujada ga sarauniya larbisa yana mai bude fuka fukansa ya kwashi gaisuwa sannnan ya yace da ita, Yake sarauniyar duniya, fadi irin Tambayoyin da kike son ki gabatar dasu a gareni koda kuwa adadinsu ya kai na yawan gashin dake jikin rago ko Tinkiya. Lallai zan baki amsoshinsu koda kuwa zamu kwana dubu a zaune inayi miki jawabinsu." Koda jin wannnan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da dariya sannnan tace, "Ai ni Tambayoyina guda uku ne kacal. Tambaya ta farko itace, naji huzailatul marwasu yace, abokan tafiyarmu Izuwa inda zamu samo littafin TSATSUBA su hudu ne. Kuma ukun cikinsu mata ne, na hudun kuma namiji ne. To wai shin menene amfanin kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya, kuma a wane garuruwa zamu riskesu?" Tambaya ta biyu itace, akan wane dalili wadanan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda suyi mana rakiya Izuwa wannan tafiya mai tsananin hadari? " Tambaya ta uku wacce itace ta karshe, shin kasan dalasiman tsafin da za'a karanta a lalata gaba dayan tsafin dake cikin littafin TSATSUBA? " Sa'adda aljani yaji wadanan Tambayoyin guda uku daga bakin sarauniya larbisa sai yai shiru yana mai kura mata idanu cikin al'ajabi. Ba wani abu bane yasa yai shiru ba kuma ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta daya dimautashi. Koda larbisa ta fahimci halin da aljani subauratu ya shiga sai ta daka masa tsawa tace, Shin zaka bani amsar Tambayoyina ne ko kuwa za kaci gaba kallona ne har sai ka gaji?" Nan take aljani subauratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa cikin nutsuwa yace, ki gafarceni ya shugabata kiyi sani cewa kinyi mini Tambayoyi ne masu matukar muhimmanci a cikin wannan tafiya tamu, kuma wadanda zasu dauki dagon lokaci ina yi miki bayaninsu. Da farko dai, abokin tafiyarmu wanda zamu fara tafiya nema ba wani bane face JARUMA SHUMAIRA 'yar mafarauci IMSHAL. A halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki wanda yafi shumaira ibn imshal sanin sirrin daji da iya farauta da kuma juriyar wahala. Kafin mu isa kogon KITABUL SIHIR inda aka ajiye littafin TSATSUBA sai mun keta ta cikin wadansu dazuzzuka guda uku. A cikin Daji na farko sai mun shafe wata shida muna tafiya sannnan zamu je karshensa. A cikin wannan daji wanda aka yiwa lakabi da SHAJARUL SHALJUMA akwai mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye wadanda kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu, haka ma tsafi baya aiki a kansu. Babu abinda zai ceci mutum daga shairrinsu face ya san sirrinsu kuma ya kware a iya farauta gamida da jurewa wahala. Lallai idan babu jagorancin jaruma shumaira bamu isa mu ratsa ta cikin dajin shajarul shaljuma ba a raye. Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba kowa bane face jaruma LARIFAT ma'abiciyar basira da hangen nesa. Daji na biyu wanda ke gaban dajin shajarul shaljuma ana kiransa da suna UJURUL MAJNAN.... Koda mahaifiyar Humairu tazo dai- dai nan a zancenta sai suka jiyo takun sawayen giwaye daga can nesa a guje an durfafo inda suke. A rude kuma a dimauce su Humairu suka mike tsaye zumbur suka dora iyayensu da masoyansu akan wadannan dawakai biyu suka kada dawakan suka yi cikin daji da gudu, suma suka bi bayansu cikin azababben gudu. Suna cikin gudun ne suka waigo sai suka ga ashe ragowar dakarun nan ne na sansanin sarki larbusa su goma sha biyar bisa kan giwaye suka biyo sawunsu. Nan fa Humairu da Hashlar suka kara kaimin gudunsu zuciyoyinsu cike da tsananin fargaba da tashin hankali saboda tsoron kada dakarun su riskesu su hallaka iyayensu da masoyansu. WANE IRIN MASIFAFFEN YAKI ZA'A YI A CAN KOFAR BIRNIN LURHAJ TSAKANIN RUNDUNAR SARKI ARYAN DA RUNDUNAR SU SARKI LARBUSA? " SHIN LAILA ZATA CIKA ALKAWARIN DAKE TSAKANINTA DA ZURAIHA MATAR SARKI LARBUSA? " SHIN SARKI LARBUSA YANA CIKAo BURINSA NA MALLAKAR NAHIYAR GABA DAYA? " WACCE IRIN JARUMTAKA DAN SARKI ARYAN ZAI TASO DA ITA, KUMA ZAI DAWO BIRNIN LURHAJ NE YA KARBI KARAGAR MULKINSA? " Mu hadu a littafin Dugunzuma kashi na uku don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Dugunzuma!!! LITTAFI NA 3 PART 1 Mr NASEER SHEHU ****** Lokacin da su Humairu suka ci gaba da falfala azababben gudu a cikin daji tare da iyayensu da masoyansu wadanda ke bisa dawakai, duk sa'adda suka waigo bayansu sai suga har yanzu wadanan dakaru na sarki larbusa su goma sha biyar na nan biye dasu sun kasa tsere musu kuma tazarar dake tsakaninnsu bata wuce taku goma sha ba, alhalin sun yi wannan tseren gudu na akalla tsawon sa'a guda. Nan take zuciyar Humairu tayi bakikkirin yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa domin ya fuskanci cewar gudu fa ba mafita bane, Domin idan aka kure musu gudun, biyu babu za'a yi wato za'a kashesu kuma a kashe iyayen nasu gamida da masoyan nasu. Koda gama aiyana Hakan sai Humairu yaja ya tsaya cak! Shima Hashlar yana ganin tsayuwar Humairu sai ya tsaya ya dubeshi cikin tsananin mamaki da kaduwa yace, "ya kai abokina me yasa kayi ganganci ka tsaya alhalin ka san cewa ba zamu iya ba da wadannan dakaru su goma sha biyar? " Humairu yace, gudunmu bashida wani amfani domin ba zamu iya tsere musu ba kuma idan suka riskemu biyu babu zamu yi, babu mu, babu iyayenmu da masoyanmu. Idan kuwa muka tsaya muka yaki wadanan dakaru kafin su kashemu iyayenmu da masoyanmu sun yi nisa a cikin daji sossai sun basu ratar da baza su iya riskarsu ba. Abinda nake so da kai shine, mu tsaya mu yi yakin nan da dukkan ranmu da karfinmu kuma da madaukakiyar zuciya yadda koda zasu kashemu muma sai munyi musu mummunar barna don haka kada mu taba cire tsammanin sa'a da nasara akan abokan gaba. Koda gama fadin Hakan sai Humairu ya zare takobinsa ya dagata sama yana mai kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda ya cika dajin gaba daya. Take shima Hashlar yayi koyi dashi. A wannan Lokaci wadannan dakaru guda goma sha biyar sun kara tunkarosu a sukwane kuma a fusace suna masu karawa giwayensu kaimi saboda sun gane dabarar dasu Humairu ke shirin yi tason su tserar da rayuwar iyayensu da masoyansu. Koda ya rage saura bai fi taku goma ba dakarun su iso inda suke sai Hashlar da Humairu suka yunkura cikin zafin nama suka ruga suna masu taryarsu. Kamar hadin baki sai duk su biyun suka daka tsalle sama Izuwa kan dakarun. Duk da cewa Hashlar hannu daya gareshi sai da yai amfani da daya hannun lafiyayye ya kaiwa dakaru uku sara da takobinsa a lokaci guda, a hammatarsa kuwa ta hagu bangaren da yankakken hannun nasa yake yana makale da dogon mashi. Cikin bakin zafin nama ya zabtare makogwaron dakarun biyu da kaifin takobinsa kuma ya soke wadansu biyun da mashinsa, duka su shidan suka rikito kasa daga kan giwayensu suka kama shure - shuren mutuwa. Shi kuwa Humairu yana sama ya kwashe rabin kwanyar dakaru uku da kaifin takobinsa kuma ya soki tsakiyar kawunan dakaru biyu da wata zabgegiyar wuka tasa, su biyar din a lokaci guda suka rikito kasa matattu ko shurawar kirki dayansu baiyi ba. A Lokacin Humairu da Hashlar suka duro can bayan dakarun kafafunsa suka doki kasa suna masu tayar da kura. Cikin tsananin mamaki da takaici ragowar dakarun bakwai suka yi tirjiya da giwayensu suka juyo suka fuskancesu suna tsuma da gurnani kamar namijin kure. A wannan Lokaci su kansu su Humairu sunyi tsananin mamaki yadda akayi suka yi wannan gagarumar jarumta wacce basu taba yin irinta ba. Abinda basu sani ba shine, ya yin da zuciya ta hasala kuma rai ya tari mutuwa, tofa gangar jiki zata iya aiwatar da abinda baza iya ba. Bayan anyi kallon kallo na 'yan dakiku tsakanin wadanan dakaru bakwai dasu Humairu sai dakarun suka sauko daga kan giwayensu suka daga makamansu sama suna masu gyara tsayuwa. A wannan Lokaci ne Humairu ya dubi Hashlar yace, "tunda dai kai hannu daya gareka ka barni da mutum hudu kai kuma ka kara da mutum ukun. Inason mu jajirce iya karfinmu da kokarinmu har sai mun ga iya inda karfinmu ya kare. Ka sani cewa bamu da sauran abin alfahari face mu ceci rayuwar iyayen namu da masoyanmu. Sannnan kada ka manta cewar ina da alkawari a kaina na kubatar da rayuwar matar sarki da dan da ta haifa don haka ta kowanne hali lallai inason mu tsira da rayuwarmu. Musamman idan munason mafarkinmu na sake kafuwar kasarmu ya tabbata. Koda Humairu yazo nan a zancensa sai ya dubeshi yana mai gyada kai yace, ai kuwa zan jajirce iya karfina don ganin mun cimma nasara. Gama fadin Hakan keda wuya sai Humairu da Hashlar suka yi kukan kura a lokaci guda suka falfala da azababben gudu Izuwa kan wadannan dakaru guda bakwai. Ai kuwa suma dakarun sai suka falfalo da gudu suka taresu aka ruguntsume da azababben yaki. Kaico! Wuya bata da dadi kuma tashin hankali ba'a sa masa rana. Lokacin da aka fara wannan kazamin yaki sai kowa ya gane cewa shayi ba ruwa bane. Domin babu wanda yake da tabbacin cewa zai iya tsira da rayuwarsa saboda karfi ya hadu da naci gamida juriya da zafin nama. Kiri-kiri gashi dai dakarun sunfi su Humairu karfi, girma da iya yaki, amma sai karfi yake naman zuwa daya domin sun zamewa juna alakakai, wato kowanne bangaren yana jin jiki. Wani abin mamaki shine, dakarun suna yakin ne da dukkan karfinsu kuma a fusace, su ma su Humairu haka. Nan fa suka ci gaba da kaiwa junansu sara da suka na hauka ba kakkautawa. Tabbas in ba don Allah ya baiwa su Humairu tsagwaron zafin nama ba da naci da tuni dakarun sun hallakasu farat daya saboda bambancin karfi da iya yakin a baiyane yake, kuma sannnan Salon fadan da dakarun keyi yafi nasu Humairu, saboda sun hada da kai naushi da bugu. Tabbas su Humairu suna iya kare saran dakarun da sukarsu, amma kuma sai suka kasa tare naushinsu da bugunsu na hannu da kafa. Nan fa suka fara hada musu jini da majina a baki da hanci, amma kuma basu sami nasarar sarar jikinsu ba sai dai ga dukkan alamu idan aka sake dan jimawa a hakan dakarun zasu sami nasarar hallakasu farat daya. Ana cikin haka ne wani badakare wanda yafi sauran dakarun karfi da zafin nama ya sami nasarar yankan Hashlar a gadon baya, take gadon bayan ya dare, jini yai feshi. Hashlar ya tsandara uban ihu ya yi baya taga-taga zai kife a Lokacin da dakaru hudu suka yi kansa da nufin su daddatsashi. Cikin bakin zafin nama Humairu yai wuf ya janyeshi Izuwa gefe daya takubban dakarun suka sari kasa, kasar ta daddare kai kace girgizar kasa a akayi. Damar da wannnan badakare mai karfi da zafin nama ya sake samu kenan ya sari Humairu a cinya, take cinyar ta dare, jini yai tartsuwa, amma saboda tsananin juriya irinta Humairu bai yarda ya fadi kasa ba sai ya juyo a matukar fusace yaci gaba da yaki da wani irin azababben karfi, duk da cewa jini na zuba a cinyarsa bai sare ba. Ba komai ne ya sa Humairu ya sami wannan gagarumin karfi ba face tunowa da cewar idan fa basu sami nasara ba a wannnan yaki lallai iyayensu da masoyansu ma sai sun zama gawa. Cikin sa'a kuwa Humairu ya shammaci dakarun yayi wata irin katantanwa a kasa a tsakiyarsu ya sassare kafafunsu suka zube kasa su taran a lokaci guda suna zubarda jini tare da tsandara uban ihu mai firgitarwa. Kafin su kara mikewa tsaye Humairu ya kara dankarawa kowannensu sara a tsakiyar kai. Duka su taran sai suka zama gawa, ya zamana cewa sauran su shida kacal. Kuma sai Hashlar wanda ke kwance a can gefe daya, bayansa yai kaca- kaca da jini yana ta faman numfashi kamar ransa zai fita. Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin Humairu da ragowar dakarun shida suna masu matukar mamakin yadda akayi ya sami wannnan gagarumar nasara har ya kashe musu mutum tara a lokaci guda, kuma suna shakkar su shigoshi. Shima Humairu duk da cewa ya sami wannan nasara sai yaji yana shakkar ya sake tarar ragowar dakarun shida a Lokacin, domin har jiri ya Fara dibarsa sakamakon raunin dake kan cinyarsa mai zubar da jini. Dan kallon kallon da aka tsaya yi ne ya bashi damar da yai wuf ya yagi rigarsa ya daure raunin dake cinyar tasa. Faruwar hakan keda wuya sai yaji ya daina jin wannnan jiri dake damunsa Amma da ya dubi dan uwansa Hashlar wanda ke kwance face-face cikin jini sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, jikinsa gaba daya ya kama tsuma saboda tsananin fushi saboda ya tuna cewa yanxu fa a cikin abokansa su bakwai su biyun ne fa kadai suka rage kuma idan bai gaggauta tsayar da jinin dake zuba ba a bayan Hashlar shima zai iya rasa rayuwarsa. Nan take Humairu ya wangame bakinsa ya takarkare ya kwarara uban ihu ya ruga Izuwa kan dakarun aka sake ruguntsumewa da sabon yaki. Wannan karon sai ya sauya salon fadan ya hada Da tsalle-tsalle da kwance kwance yana kai musu hari da gudu ta ko ina. Nan da nan kuwa ya fara samun lagonsu ya rikitasu har ya sami nasarar dukan kijirnansu sau uku da kafarsa a sama. Duk da sadaukantakarsu, karfinsu, juriya da naci irin na wadanan dakarun sai da suka yi baya taga- taga kamar zasu fadi amma kuma saboda naci sai su mike su ci gaba da kawo mishi sara da suka. Al'amarin da ya firgita Humairu kenan yana mai ci gaba da kare kansa gamida mayar da martani har ma yana hadawa da kai naushi da bugu. Duk da hakan sai yaga suma dakarun sun kara kaimi fiye da farko ma. A sannnan ne ya gane cewa lallai wadanan dakaru ne na musamman ne wadanda suka sami horo mai tsanani. Sai da Humairu ya dage sossai sannnan ya fara samun nasara akan su. Nan fa ya rinka saransu da yankansu yana bazar dasu a kasa, cikin kankanin lokaci ya kashe mutum biyar daga cikinsu. Ya zamana cewa saura mutum guda ya rage kuma ba wani bane face wannan badakare mai karfin damtse da zafin nama fiye da na sauran yan uwansa. Nan fa badakaren yaja da baya cikin dan alamun tsoro ya tsaya cak! Ya zamana cewa shi bai gudu ba kuma bai afka masa ba. Humairu ya sake waigawa ya dubi inda Hashlar ke kwance yaga har numfashinsa ya fara sarkewa, kawai sai ya juya ya nufi inda Hashlar ke kwance yayi kamar ma ya manta da wannnan badakare dake tsaye a bayansa. Koda ganin haka sai badakaren ya dubi gefensa ya hango wata kwari da baka a kasa, kawai sai ya nufi inda kwarin take yana waigen Humairu da nufin ya dana akan bakan ya harbeshi. Abinda bai sani ba shine, humairu na lura dashi, kuma yana kallonsa ta wutsiyar ido. Koda badakaren ya dauki kwarin ya dana akan bakan. Kafin ya dago sama ya harbawa Humairu kibiyar tuni shi Humairu ya zaro wata sirriyar wuka mai tsawo kaifi da tsinin tsiya ya wurgawa badakaren, nan take wukar ta nutse a makogwaronsa ta fito ta wuyansa. Kawai sai badakaren ya sandare a tsaye ya bingire kasa matacce ko shurawa bai yi ba. Cikin hanzari Humairu ya karasa kan Hashlar ya shiga kokarin tsayarda jinin dake zuba a jikinsa don ceto rayuwarsa. Da kyar da sidin goshi Humairu ya sami nasarar ceto rayuwar Hashlar ya farfado kuma ya dawo cikin haiyacinsa. Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube Humairu ya mike tsaye da sauri shima ya sawa raunikan jikinsa magani sannnan ya goya Hashlar a bayansa ya sake runtumawa da gudu dauke dashi Izuwa cikin daji domin su riski iyayensu da masoyansu. Wannan shine abinda ya ga su jarumi Humairu bayan sun yi mummunan yaki da dakarun sarki larbusa. * A can kofar birnin LURHAJ kuwa su sarki Aryan sun yi dafifi a cikin shigar yaki, sarki Aryan ne tsaye a gaban rundunar dakarun kowa ya zuba idanu yana kallon Ta inda abokan gaba zasu bullo. Sai da aka shafe sama sa'a uku a tsaye cirko cirko aka yi tsit! Ba'a jin sautin komai face na iskar dake kadawa. Kwatsam! Sai aka hango kura daga can nesa ta turnuke sararin samaniya. Daga nan kuma sai aka ji kasa ta kama rawa da kara tamkar za'a yi girgizar kasa. Ashe ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsananin yawan takun sawun dakarun sarki larbusa. Al'amarin da ya fara tayar da hankalin gaba dayan dakarun sarki ARYAN kenan zuciyoyinsu suka fara sarewa. Koda dakarun suka kara matsowa kusa Sai dakarun sarki ARYAN suka dimauce kuma suka firgita ainun, saboda ganin yawan dakarun, girman jikinsu da kwarjininsu, domin sun san cewa ko ba a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza. Nan fa dakarun sarki ARYAN suka fara ja da baya-baya. Suna kokarin komawa cikin gari. Koda ganin haka sai sarki Aryan ya fusata ainun ya daka musu tsawa mai karfin gaske wacce tasa suka kara firgicewa fiye da farko sannnan suka shiga taitayinsu kowa ya dawo inda yake ya tsaya. Sarki Aryan ya juya ya fuskanci dakarun nasa yace, "Ya kai ku dakaruna shin kuna ji kuna gani zaku bari ne a yiwa matayenku fyade a kashe iyayenku, kuma a kame 'ya ' yayenku a maishesu bayi?" Shin kuna ji kuna gani za'a kwashe dukiyoyinku ne kuma a kone gidajenku da birninku wanda iyayenku da kakanninku suka shafe shekara da shekaru suna faman wahalar mayarda shi maraya?" To ku sani cewa dan halak baya yarda aci zarafinsa dana iyalinsa ko dukiyarsa sai dai ya mutu akan kare kimarsa da martabarsa. Ku tsaya kuyi yaki, ku zubar da jininku don kare kimarku da mutuncinku. Koda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai gaba dayan dakarun nasa suka ji kamar an cire musu dukkan tsoro da fargaba daga cikin zukatansu. Nan take jikinsu ya kama tsuma suka ji ma babu abinda suke so sama da su ga karasowar abokan gaba a fara gurmuzu. Dugunzuma!!! LITTAFI NA 3 PART 2 Mr NASEER SHEHU TEARLOW ****** Koda ganin haka sai sarki Aryan ya fusata ainun ya daka musu tsawa mai karfin gaske wacce tasa suka kara firgicewa fiye da farko sannnan suka shiga taitayinsu kowa ya dawo inda yake ya tsaya. Sarki Aryan ya juya ya fuskanci dakarun nasa yace, "Ya ku dakaruna shin kuna ji kuna gani zaku bari ne a yiwa matayenku fyade a kashe iyayenku, kuma a kame 'ya'yayenku a maishesu bayi?" Shin kuna ji kuna gani za'a kwashe dukiyoyinku ne kuma a kone gidajenku da birninku wanda iyayenku

Chapter 6 of 9