Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
alhalin ka san cewa yaki akeyi acan? " Humairu ya gyada kai cikin alamun tausayi yace, na rigaya na yiwa sarki ARYAN alkawarin cewar zan kubatar da rayuwar matarsa da dansa. Don haka dole ne na koma birnin LURHAJ yanzu. Sarki Aryan ya nuna mini wata barauniyar hanya da za'a iya fita daga cikin gidan sarautarsa, kuma ta can bayan gari za'a shiga. Babu wanda yasan wannnan hanya sai shi kadai, sai kuma ni da ya nuna mini ita, don haka ina son ku kwantar da hankalinku. Nayi muku alkawari zan dawo gareku a raye ". Koda jin wannnan batu sai hawaye ya zubowa mahaifiyar Humairu da laila suka rungumeshi a lokaci guda suka kama kuka. Al'amarin da ya baiwa Hashlar, Huzaila da mahaifiyar Hashlar tausayi kenan suma idanunsu suka ciko da kwallah. SHIN HUMAIRU ZAI SAMU NASARAR KOMAWA GIDAN SARAUTAR YA KUBATAR DA RAYUWAR MATAR SARKI YA DAWO A RAYE? " YAUSHE SU HUMAIRU ZASU YI GAMO DA SARKI LARBUSA, IDAN SUN HADU MAI ZAI FARU? " Mu hadu a Dugunzuma 4 don jin ci gaban wannnan kasaitaccen labari. ****** Dugunzuma!!! LITTAFI NA 4 PART 1 NASEER SHEHU **** Lokacin da su jarumi Humairu kuwa, tun da suka kama hanya suka yi ta gudu a cikin daji tare da iyayensu da masoyansu su Laila, basu yada zango ba a ko ina har sai da suka iso iyakar birnin LURHAJ da wata kasa da ake kira ZAITUN, sannnan suka tsaya. A sannnan ne Humairu da Hashlar suka tsugunna a kasa suna ta faman haki kamar ransu zai fita saboda tsananin gajiya, saboda sun shafe kusan sa'a tara kenan suna gudu basu huta ba. Sai da suka dawo cikin haiyacinsu sannnan suka sha ruwa, suma iyayen nasu da 'yan matan nasu suka fito da abinci aka ci aka sha. Dama a can sansanin su sarki larbusa sun samu sun debo guzuri. Bayan kowa ya nutsu sai Humairu ya mike tsaye ya dubi mahaifiyarsa da masoyiyarsa laila yace, "Ni anan zan rabu daku, dole ne na koma can birnin LURHAJ yanzu. Koda jin wannnan batu sai mamaki da tsoro ya kama mahaifiyar Humairu da Budurwаrsa laila. Mahaifiyar tasa ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace, "akan wane dalili zaka koma Izuwa birnin lurhaj yanzu alhalin ka san cewa yaki akeyi acan? " Humairu ya gyada kai cikin alamun tausayi yace, na rigaya na yiwa sarki ARYAN alkawarin cewar zan kubatar da rayuwar matarsa da dansa. Don haka dole ne na koma birnin LURHAJ yanzu. Sarki Aryan ya nuna mini wata barauniyar hanya da za'a iya fita daga cikin gidan sarautarsa, kuma ta can bayan gari za'a shiga. Babu wanda yasan wannnan hanya sai shi kadai, sai kuma ni da ya nuna mini ita, don haka ina son ku kwantar da hankalinku. Nayi muku alkawari zan dawo gareku a raye ". Koda jin wannnan batu sai hawaye ya zubowa mahaifiyar Humairu da laila suka rungumeshi a lokaci guda suka kama kuka. Al'amarin da ya baiwa Hashlar, Huzaila da mahaifiyar Hashlar tausayi kenan suma idanunsu suka ciko da kwallah. Mahaifiyar Humairu ta janye jikinta daga cikin nasa suka fuskanci juna a Lokacin da itama laila ta janye jikinta ta sunkui da kanta kasa. Mahaifiyar Humairu ta dubeshi sa'adda hawaye ya subuto mata tace, "Ya kai dana tun da na haifeka duk abinda ka sa a gabanka kana samun nasara, ba'a taba samun akasi ba. Amma ka sani cewa wannan karon zuciyata tana rawa, domin na firgita da Al'amarin sarki larbusa da dakarunsa, ina ji a jikina kamar idan muka rabu ba zamu sake saduwa ba. Koda gama fadin Hakan sai ta sake rungume Humairu ta fashe da sabon kuka. Da kyar Humairu ya rarrasheta tayi shiru ya kara tabbatar mata da cewa lallai komai RINTSI DA TSANANI sai ya dawo gareta. Daga nan sai ya matsa gaban laila ya rike kafadunta, ita kuwa sai ta dago kai ta dubeshi cikin yake tace, "Baka taba yi mini alkawari ka saba ba, don haka wannan karon ma idan har ka karya mini alkawari kashe kaina zanyi domin ba zan iya rayuwa ba in babu kai. Ka tuna cewa an kashe uwata da ubana sa'adda aka kawo hari kauyenmu, Yanzu ba ni da kowa sai kai, kaine uwata kaine ubana. Lallai ta kowanne hali ka cika alkawari ka dawo gareni a raye domin muyi aure. Koda jin wannnan batu sai fuskar Humairu ta fadada da murmushi yace, Ai kuwa laila zan kasance mai cika alkawari a gareku keda mahaifiyata." Laila tace "Na baka kwana daya da yini daya jal ka dawo garemu kafin faduwar rana. Idan har rana ta fadi baka dawo ba sai dai kazo ka riski gawata, ko da kuwa ka tsira da rayuwarka." Koda jin wannnan batu sai hawaye ya zubowa Humairu yace, "kada kiyi gaggawa ya masoyiyata, lallai koda mutuwa zanyi sai munyi bankwana." Gama fadin Hakan keda wuya sai Humairu ya karasa wajen Hashlar ya tsaya daf! Dashi yadda har suna iya jin numfashin juna, suka tsaya suna kallon juna kawai har tsawon 'yan dakiku, sannnan suka rungume junansu. Daga can sai Humairu ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dubeshi yace, "Ya kai abokina ka sani cewa mu biyu ne rak! Muka rage daga cikin abokanmu don haka duk yadda za'a yi komai rintsi da tsanani inason mu rayu domin mu kai Izuwa zamanin daza muga dawowar kasarmu. Idan kun shiga cikin birnin zaitun ku batarda kamanninku kada ka bari a shaidaku, kuma kada ka bari a san masaukinku. Lallai gobe kuje tsakiyar kasuwar birnin nan a gabannin faduwar rana anan zan riskeku. Idan ka kiyaye hakan lallai zamu sake saduwa. Da wannnan furuci nake yi maka sallama sai gobe idan muna da rabon sake saduwa." Koda gama fadin Hakan sai Humairu yaje ya kama dokin dasu laila suka hawo yai tsalle ya haye kansa ya juya da baya ya zabureshi da gudu Izuwa cikin daji. Su kuwa su Hashlar sai suka bishi da kallo kawai cikin tsananin damuwa da tashin hankali tamkar su aza hannu aka su fashe da matsanancin kuka. Humairu yaci gaba da keta dazuzzuka akan dokinsa yana ta tsala uban gudu na gaban kwatance, amma ji yake kamar ya sauka daga kan dokin yayi gudun da kafafunsa saboda gani yake kamar dokin baya sauri. Sai da ya shafe sa'a uku cur! A haka har ta kai cewa dokin ya fara gajiya yana rage karfin gudunsa a hankali, kai har ma ya koma tafiyar sauri- sauri, gudu-gudu, sannnan ya koma sassarfa. Al'amarin da ya fusata jarumi Humairu kenan, domin yana cikin tsananin sauri ne, burinsa kawai shine ya isa cikin birnin LURHAJ kafin su sarki larbusa su sami nasarar fasa kofar birnin su shiga cikin gidan sarautar inda su gimbiya lushairat suke, wato matar sarki Aryan. Dama wani boka da ya riska a cikin wani daji wanda ya fito daga wata kasa dabam yayi masa bincike ya gaya masa cewar sarki larbusa zai karya kofar birnin lurhaj a dai-dai Lokacin da magariba ta doso. Humairu ya gama auna cewa zai iya isa bayan birnin lurhaj a cikin sa'a biyar dai-dai, a Lokacin da saura baifi rabin sa'a ba kenan magarib ta doso. Koda Humairu yaga gashi yanzu sa'a uku kadai da fara tafiyarsa amma har dokinsa Ya sare sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, Cikin tsananin fishi yaja linzamin dokin nasa yayi turjiya sannnan ya duro kasa ya falfala da azababben gudu Izuwa cikin dajin ko waigowa bai yi ba bare yaga halin da dokin nasa ke ciki. Humairu yaci gaba da tsala gudu ba sassauci, babu daga kafa, ba gajiya, tamkar jikinsa bana jini da tsoka bane na karfe ne, Sai da Humairu ya shafe sa'a daya da rabi yana wannnan gudu sannnan ya fara sarewa. Gajiya da haki suka isheshi gamida tsananin kishirwa, inda yaji makogwaronsa ya bushe kamar zai mutu. Bisa dole ya dakata ya zaro battar ruwansa ya kwalkwala. Hutun dakika talatin kawai yayi sannnan ya mike zumbur yaci gaba da falfala azababben gudu. Sai gifta bishiyoyi, duwatsu da kwazazzabai yake kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya. Saboda da karfi gudun nasa wani Lokacin ma har tashi sama yake yana tsalleke abubuwa. Bayan cikar rabin sa'a dai-dai ya fara juyo ihun mazaje. Nan fa yasan cewa ya kusanci birnin LURHAJ, kuma gashi a wannan Lokaci yamma tayi sossai hasken rana ya fara disashewa. Nan fa hankalinsa ya kara dugunzuma, ya kara kaimin gudun nasa. Wohoho! Kaga maza masu DAKAKKIYAR ZUCIYA! Wadanda basu san wani abu ba wai shi tsoro ko karayar zuci. Ko yaushe a cikin sa ran samun nasara suke. Lokacin da Humairu ya kara kusantar bayan birnin LURHAJ sai ya firgita ainun sakamakon hangen yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya a cikin tsakiyar birnin, kuma ya rinka jiyo Iface-iface da kururuwar mata da maza wanda ya cika daji da amsa kuwwa. Nan fa zuciyarsa ta kama bugawa da karfi ya fara tunanin cewa lallai ya makara, aikin gama ya gama, wato tuni a wannan Lokaci su sarki larbusa sun fasa kofar birnin LURHAJ sun shiga ciki. Duk da aiyana Hakan a zuciyarsa sai ya yanke hukuncin ya karasa yaga zahiri da idanunsa ko da kuwa shima zai rasa rayuwarsa domin mutuwarsa itace sauki akan kasa cika alkawarin da ya daukarwa sarki Aryan. Wani katon kududdufi ne a karshen bayan birnin LURHAJ. Koda ya iso bakin gabar wannan kogi sai ya daka tsalle ya fada cikinsa yayi nutso Izuwa karkashinsa ya kama iyo yana karawa gaba. Sai da yayi 'yar doguwar tafiya sannnan ya dago sama ya shaki numfashi ya sake komawa yaci gaba da iyo. Sai da yayi hakan sau uku sannnan ya riski wani dogon bututu na karfe wanda ya lume a cikin kasan ruwan. Ba tare da fargabar komai ba ya kunna kai cikin bututun sululu! Kamar tafiyar kifi, yayi ta tafiya a cikinsa sai gashi ya iso karshensa, ashe magudanar ruwan da ake amfani dashi a cikin gidan sarautar ne. Tsulum! Sai ga Humairu a cikin tsakiyar gidan sarautar sarki Aryan. Yana baiyana yaga ana fafata kazamin yaki, da dakarun sarki larbusa nata ragargazar dakarun sarki Aryan tamkar suna sassabe a gona. Cikin hanzari ya zare takobinsa ya ruga da gudun tsiya Izuwa inda turakar gimbiya lushairat take. Ai kuwa sai dakarun sarki ya suka hangoshi suka yi caa! Akansa da nufin su gididdibashi. Wohoho! Idan zuciya ta fusata sai tsoro ya kauce, kuma jarumtaka ta ban al'ajabi ta bijiro. Nan take Humairu ya zamo tamkar shaidani a cikin wadannan dakaru ya zamana cewa yana gudu a tsakiyarsu yana kaucewa saransu da sukansu, kuma yana mai da martani. Yarinka tsalle -tsalle tamkar dan biri akan bishiyoyi. Ai kuwa sai ya rinka saransu akai da wuya suna zubewa kasa yana kutsawa da karfin tsiya cikin azababben zafin nama na ban al'ajabi wanda shi kansa yayi matukar mamakin yadda akayi ya sami wannnan jarumtaka alhalin dakarun sun fishi karfin damtse da iya yaki. Shi dai jarumi Humairu abinda ya sani shine, yana yin wannnan yaki ne da dukkan karfinsa da ransa da jikinsa, ko yai rai ko ya mutu. Kafin dakarun su ankara tuni ya tsere ya basu tazara mai dimbin yawan gaske, ya rigasu zuwa inda kofar turakar gimbiya lushairat take. Tun daga nesa da dakarun dake tsaron kofar suka hangoshi kuma suka hango abokan gabar dake biye dashi sai suka yi sauri suka bude masa kofar,yana shigewa suka mayar da kofar suka rufe saboda dama sun san zai zo don sarki Aryan ya sanar da su. *** SUNA SHIGEWA NIMA NA MAYAR DA LITTAFIN NA RUFE, DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 4 PART 2 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ******* Shi dai jarumi Humairu abinda ya sani shine, yana yin wannnan yaki ne da dukkan karfinsa da ransa da jikinsa, ko yai rai ko ya mutu. Kafin dakarun su ankara tuni ya tsere ya basu tazara mai dimbin yawan gaske, ya rigasu zuwa inda kofar turakar gimbiya lushairat take. Tun daga nesa dakarun dake tsaron kofar suka hangoshi kuma suka hango abokan gabar dake biye dashi sai suka yi sauri suka bude masa kofar, yana shigewa suka mayar da kofar suka rufe saboda dama sun san zai zo don sarki Aryan ya sanar da su. Ita kuwa gimbiya lushairat bata san da zuwansa ba, tana can cikin kuryar dakinta ta rungume jaririnta tana ta faman rusa kuka, Kuyanginta na tayata kukan. Acan bakin kofar turakar gimbiya kuwa, dakaru na rufe kofar sai suma suka ruga da gudu suka tari abokan gaba aka ruguntsume da yaki. Duk da dai cewar anfi karfinsu amma saboda suna da zuciyar kare martabarsu da kishin kasarsu basa mutuwa farat daya sai bayan bakin gurmuzu. Lokacin da Humairu ya iso cikin tsakiyar turakar gimbiya lushairat a guje rike da takobinsa wacce ta rine da da jini, sai gimbiya lushairat da kuyanginta suka firgice suka kama ihu suna zaton ko abokan gaba ne suka karaso. Cikin tsawa Humairu ya dubesu yace, "Ni dan uwanku ne haifaffen wannan kasa. Yake gimbiya kiyi sani cewa nine jarumi Humairu wanda sarki ya umarta da ya kubatar da rayuwarki da ta jaririnki daga cikin birnin nan. Maza ki goya jaririn naki a bayanki sannnan nima na goyaki a bayana mu fice da gudu daga cikin gidan nan. Koda jin haka sai lushairat ta dakawa Humairu tsawa tace, " kai waye har da zan hada jikina da naka?" Bazan ci amanar mijina ba, duk da cewa nasan cewa ya mutu. " Humairu ya ruga Izuwa gaban lushairat da sauri yace, "Bamu da Lokacin gardama,ai lalura ce ta janyo hakan. Ki hanzarta yin abin da na umurceki da yi in ba so kike keda jaririn naki ku mutu ba!" Lushairat tace, "Ai gwara mu mutu tun da dai mijina ya mutu, bamu da sauran wani gata, babu mai ka re...." Kafin ta gama rufe bakinta tuni Humairu ya doki wuyanta da hannunsa, kawai sai ta Sulale zata fadi kasa sumammiya. Cikin zafin nama ya tallafota tare da jaririn na ta. Cikin dakiku kadan ya goyata a bayansa. Su kuma kuyangin nata suka daure masa jaririn nata a bayanta. Kawai sai Humairu ya juya da baya da gudu ya nufi inda ya fito rike da takobinsa. Yana isowa bakin kofar turakar yayi arba da dakarun sarki larbusa Kimanin su dari biyu, tuni sun gama karkashe gaba dayan dakarun dake gadin kofar. Ita kanta kofar sun ragargazata. Nan fa aka yi kallon-kallo tsananin dakarun da Humairu, suka gane cewa lallai matar sarki Aryan ce da jaririnta a goye a bayansa, kuma dama umurnin da aka basu shine duk inda matar sarki Aryan take da jaririnta a kamosu a kashesu a kaiwa sarki larbusa gawarsu. Shi kuwa Humairu abinda yazo masa a rai shine, dole ne fa ta kowanne hali ya kashe gaba dayan wadanan dakaru da suka yi arba dashi, in ba haka ba kuwa dayansu zai iya kai labarinsa inda su sarki larbusa suke azo a gama dashi. Nan take jikin Humairu ya kama tsuma yaji wani irin gagarumin sabon karfi ya shigeshi, Kawai sai ya ruga da gudu Izuwa kan dakarun tun kafin su afka masa ya kutsa ta tsakiyarsu yana kai sara da suka ta ko ina, suma suna kawo masa. Koda dakarun suka ga sauran kiris! Ya fita ta tsakiyarsu sai suka yi dabara suka yi masa kawanya aka ci gaba da azababben yaki, suna kokarin gididdibashi shi da wacce yake goye da ita da kuma abinda ita take goye dashi (jaririnta) Kaico! Lallai duk inda jarumi yake jarumi ne, wanda a kowanne lokaci jarumtarsa kan iya motsawa yayi bajintar da ba'a taba tsammani ba. Koda Humairu yaga MUTUWA muraran sai ya fara katantanwa a tsakiyar wadannan dakaru ya rinka kaiwa kafafunsu sara ya hanasu kusantarsa, kuma yaci gaba da kokarin matsawa gaba, ammma sai abu ya gagara, domin kara matse kowanne gurbi suke, kuma suna dada kai masa mugayen SARA DA SUKA. Inba don ma Humairu ya sami sabon gagarumin karfi ba da tuni wadannan dakaru sun yi gutsin- gutsin da sassan jikinsa dana gimbiya lushairat da jaririnta. A koyaushe kokarinsa shine ya kare jikin lushairat dana jaririnta, ko kadan baya son su sami ko kwarzane a jikinsu. Sai da aka shafe sama da dakika dari biyu da saba'in ana wannan bakin gurmuzu, dakarun sun kasa cutar dasu Humairu, shi kuma ya kasa fita daga tsakiyarsu. Duk tsawon wannnan lokaci lushairat na kwance a gadon bayan Humairu a sume bata farfado ba. A dai-dai wannnan lokaci ne hankalin Humairu ya sake DUGUNZUMA ainun, domin ya fahimci cewar idan aka sake kara bata wani Lokacin a haka tabbas zai gaji, da zarar ya gaji kuwa tasu ta kare, take za'a gama dasu tun da Sarkin yawa yafi Sarkin karfi. Bare ma karfin ma anfi shi, juriya ce da tsantsar sa'a a tare dashi. Koda gama yin wannnan tunani sai Humairu ya yanke shawarar yin wata dabara ta karshe wacce ko dai ya sami nasarar tsira ne ko kuma shi dasu lushairat din su hallaka. BAZATO ba tsammani sai dakarun suka ga Humairu ya zaro wata zabgegiyar adda daga cikin wadonsa ya hada da takobin hannunsa sannnan ya doki kasa da hannayensa biyu ya tashi sama tamkar daga cikin baka aka harbashi, sai gashi ya dira akan katanga. Ai kuwa sai ya kama gudu akan katangar tamkar akan turba yake gudun A dai-dai wannnan lokaci ne dakarun sarki larbusa dubunai suka sake tuttudowa cikin gidan, a cikinsu har da 'yan baka (Gwanayen harbin kibiya ). Koda suka hango Humairu akan katanga sai 'yan bakan nan suka fara zaro kibiyoyi suna harba masa. Kibiyar farko ta cakeshi a kaurinsa na dama ta fasa kafar. Humairu ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji, amma saboda tsananin juriya bai yarda ya fadi kasa ba, sai ya ci gaba da gudu akan katangar goye dasu lushairat, kuma ya rinka kade kibiyoyin da ake harbo masa da takobinsa da Addarsa ta gaba da baya, sannnan yana gocewa tare da yin tsalle-tsalle kibiyoyin na wucewa ba tare da sun sameshi ba. Su kansu dakarun sarki larbusa sai da suka yi tsananin mamaki yadda akayi ya iya yin wannnan gagarumar jarumtaka, amma sai suka bishi gaba dayansu duu! Da gudu har ya duro daga kan katangar yaci gaba da gudu Izuwa cikin wani surkuki mai siririn lungu cikin gidan sarautar. Adaidai wannnan lokaci ne gimbiya lushairat ta farfado daga dogon suman da tayi. Abinda ta fara ji a kunnenta shine kukan jaririnta wanda ke goye a gadon bayanta, gashi kuma ita ma a goye take a bayan Humairu yana ta tsala gudu dasu. Koda ta waiga baya ta ga dubunnan dakarun da suka biyosu da gudu rike da makamai, sai ta kwalla ihu cikin tsananin firgita da dimauta. Nan fa taga anci gaba da harbo musu ruwan kibiyoyi, amma sai taga Humairu ya ci gaba da kade kibiyoyin ta baya da makaman hannunsa ba tare da ya waigo ba,kuma gashi yana dada ci gaba da gudu. Nan take ta kamu da tsananin mamaki, domin a saninta mijinta ne kadai yake da irin wannan bakin zafin nama da gagarumar jarumtakar haka. Koda ta kalli kasa taga kibiya soke cikin Kaurin Humairu ga jini na zuba amma bai fasa gudu ba da kokarin ceton rayuwarta da jaririnta sai ta sake cika da tsananin mamakin dalilin da yasa wannnan jarumi ya sallama rayuwarsa haka don kawai ya kubatar da tasu ita da jaririnta. Hakika rashin sani yafi dare duhu! Ashe wannan siririn dogon lungu da Humairu ya shigo babu komai a cikinsa face danyen mai acikin ganguna. Shi Humairu ya san da hakan, amma su dakarun da suka biyoshi basu sani ba. Sai da ya bari dukkaninsu sun shigo tsakiyar lungun inda gangunan man suke a jibge, kawai sai ya cafe kibiya guda daya daga cikin wadanda ake harbo masa ya tsaya cak! Ya daina gudun. Al'amarin da ya sa gaba dayan dakarun suka tsaya cak! Suma suna mamakin tsayawarsa, kuma tazararsu dashi bata wuce taku goma ba. Alokacin ne dakarun suka lura da yawan gangunan man sun huje suna ta tsiyayar da mai har kafafunsu sun jike sharkaf a cikin man ba tare da sun ankara ba. Kawai sai dakarun suka sake yunkurawa da gudu da nufin su cimma Humairu suyi masa rotse. Cikin bakin zafin nama ya yagi tsumman rigar jikinsa ya nannadashi a jikin wannan kibiya dake hannunsa, kawai sai ya karci bangon da kibiyar. Take wuta ta kama tsumman dake jikin kibiyar,kawai sai ya wurgo kibiyar Izuwa inda gangunan man suke. Koda ganin haka sai dakarun sukai turjiya ta bazato, sannnan suka juya da baya a firgice domin su ruga da gudu su bar wajen. Kash! Masu iya magana sunce, idan ajali yayi kira dole a amsa koda babu ciwo.! Kafin dakarun su tsere tuni wannan kibiya mai ci da wuta ta dira a cikin gangunan man nan. Ai kuwa sai gangunan man suka kama yin bindiga suna tarwatsewa, wata irin gagarumar wuta ta kama ko ina a cikin lungun ta rinka babbake wadannan dakaru suna ihu suna faduwa kasa. Koda Humairu yaga wutar ta dawo da baya zata lullubesu sai ya juya ya falfala da azababben gudu, ita ma wutar ta bishi suka kasa tsere. Saura kiris! Wutar ta lasosu ya sake daka tsalle ya fada cikin katon bahon wanka na sarki Aryan wanda ke cike da ruwa. Ruwan bahon ya rine da jinin mutanen da aka kashe a wannan yaki, Ashe can kasan bahon hanya ce wadda ta hade da wannnan katon kududdufin dake can bayan birnin LURHAJ. Kawai sai lushairat ta ga sun taso saman wannan kududdufi,gashi tana daure a bayansa tamau ai kuwa sai nauyinsa ya rinjayesu suka sake nutsewa kasa. Koda lushairat taga numfashinsu ya fara daukewa ita da jaririnta sai ta yi ta maza ta zare wata wuka dake daure a cinyar Humairu ta yanke igiyar da ta daureta a gadon bayansa. Sannnan ta cafi rigar Humairu tayi iyo Izuwa saman kududdufin suka fito tare. Koda ta dago sama taga jaririnta bai mutu ba, yana raye cikin koshin lfy, wannnan karon ma baya kuka sai murmushi yake yi kawai sakamakon tsintar kansa akan ruwa, sai farin ciki ya lullubeta. Haka dai lushairat taci gaba da jan Humairu a cikin wannan ruwa wanda ke sume har suka iso bakin gabar wannan kududdufin. Koda ta kara hancinta dai-dai dana Humairu sai taji babu alamar numfashi. Nan fa hankalinta ya DUGUNZUMA ta shiga kokarin ceto rayuwarsa tana danna kirjinsa saboda zargin ko ruwa ne ya cika cikinsa,amma shiru bata ga ruwa ya fito ba ta cikin bakinsa ko hancinsa. Nan fa ta kara dimaucewa bata san sa'adda tasa bakinta ba a cikin nasa ta hura masa iska. Faruwar hakan keda wuya kuwa sai Humairu ya farfado yana mai yin tari. Koda bude idanunsa ya tsinci kansa a bakin gabar wannan kududdufin kuma yaga gimbiya lushairat tare da jaririnta a raye a gabansa sai ya bushe da dariyar farin ciki. Amma da ya yunkura don ya mike tsaye sai ya kasa sakamakon kibiyar dake cikin kafarsa. A wannan Lokaci kafar tasa ma ta kumbura suntum! Kuma bata daina zubarda jini ba. Kawai sai ya sake kama rigarsa ya yageta gaba daya sannnan ya cusata a cikin bakinsa. Nan take ya kama wannan kibiya dake cikin kafarsa ya dinga zareta yana ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da zogi. Tabbas in ba don ya toshe bakinsa ba da wannnan tsumma na rigarsa da har a cikin gidan sarautar sai an jiyo ihun nasa. Humairu yana gama zare wannan kibiya ya kare sumewa, kuma jini yaci gaba da bulbulowa ta cikin ramin da kibiyar tayi masa. ***** DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 4 PART 3 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ***** A wannan Lokaci kafar tasa ma ta kumbura suntum! Kuma bata daina zubarda jini ba, kawai sai ya sake kama rigarsa ya yageta gaba daya sannnan ya cusata a cikin bakinsa. Nan take ya kama wannan kibiya dake cikin kafarsa ya dinga zareta yana ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da zogi. Tabbas in ba don ya toshe bakinsa ba da wannnan tsumma na rigarsa da har a cikin gidan sarautar sai an jiyo ihun nasa. Humairu yana gama zare wannan kibiya ya kare sumewa, kuma jini yaci gaba da bulbulowa ta cikin ramin da kibiyar tayi masa. Cikin hanzari lushairat ta yage gefen rigarta mai tsada ta sarauta ta daure inda jinin ke zuba, tayi ta nannada rigar akan kafar har sai da taga jinin ya daina zuba sannnan ta kama yiwa Humairu fifita. Humairu bai farfado ba sai bayanp Kimanin dakika dari uku da arba'in. A dai-dai wannnan lokaci ne suka daina jiyo ihu da kururuwar mutane daga cikin gidan sarautar, amma hayakin wutar nan data tashi a cikin gangunan mai bai daina tsiri ba a sama cikin gajimare, hasken wutar na binsa. Humairu ya bude idanunsa da kyar ya dubi lushairat sannnan ya dubi kafarsa wacce har yanzu a kumbure take ya gyada kai cikin takaici ya sake duban lushairat yace, taimaka ki samo mini sandar da zan dogora muyi sauri mu bar wajen nan mu nausa cikin daji don dakarun sarki labarusa zasu iya zuwa bincike anan. Ba tare da gardamar komai ba kuwa lushairat ta mike tsaye da kyar ta ruga taje ta karyo reshen wata bishiya mai dan kauri ta kawo ya karba ya dogara ya mike tsaye da kyar, amma duk da haka sai ya kasa yin tafiyar. Koda ganin haka sai lushairat ta karbe reshen bishiyar daga hannunsa ta yi jifa dashi sannnan ta tallafo kugunsa da hannayenta biyu yana dingisa kafar tasa mara lfy suka nausa cikin dajin. Al'amarin da yai matukar baiwa jarumi Humairu mamaki kenan, yace a ransa. "Ya ya akayi matar da tace bazata hada jikinta da nasa ba amma yanxu ita ce ma take kama jikin nasa da hannayenta, kuma tana sane take aikata hakan? " Amsar da bai sani ba kenan. Ba tare da Humairu ya dago kai ya dubi lushairat ba sai yace, "Mu ci gaba da tafiya har Izuwa iya yadda zaki gaji sannnan mu nemi inda zamu buya mu kwana kafin gari ya waye." Lushairat tayi shiru bata ce komai ba, taci gaba da jansa suna tafiya. A Lokacin ne duhun dare ya mamaye dajin ya zamana cewa ko gabansu basa iya gani, sai Humairu ne yake gane musu hanya ta hanyar yin amfani da takobin hannunsa yana sare ciyayi da kayoyin dake gabansu. Haka dai suka ci gaba da tafiya har Izuwa tsawon sa'a guda sannnan suka riski wani kogon dutse. Da zuwansu bakin kogon dutsen sai suka zauna suna haki, sai da suka dan huta sannnan jaririn lushairat ya fara kuka. Cikin hanzari ta kwantoshi daga Bayanta sannnan ta juyawa Humairu baya duk da cewa a cikin duhun dare suke ta fara shayar dashi. Take jaririn ya yi shiru kuwa. Tsawon 'yan dakiku dayansu baice uffan ba. Daga can sai lushairat tayi gyaran murya tace, "Tsawon wane lokaci zamu bar wannan dajin? " Humairu ya numfasa yace, Da ina da niyyar mu kwana amma yanxu na sauya shawara. Zamu huta ne anan tsawon sa'a uku kacal sannnan mu tashi muci gaba da tafiya saboda ina zargin cewa sarki labarusa zai iya turowa a biyo sawunmu. Baya ga haka kuma na yiwa masoyiyata Alkawarin cewar gobe kafin rana ta fadi zan riskesu a can wata kasa da ake kira ZAITUN. " Koda Humairu yazo nan a zancensa sai lushairat ta ji zuciyarta ta buga da karfi, kuma wani irin kishi mai karfi ya shigeta. Al'amarin da yai matukar girgizata kenan, kuma ya bata mamaki, domin ba ta ga hujjar da za ta sa tayi kishi akan wani da namiji ba face mijinta marigayi sarki Aryan gwarzon jarumin da babu kamarsa a gaba daya Nahiyar a fagen Kyau, Jarumtaka, Arziki da daukaka. Tabbas sarki Aryan yasha gaban Humairu a komai, don haka babu hujjar da zata sa lushairat taso shi." Lushairat na cikin yin wannnan zancen zuci ne Humairu ya katseta yace, "Yaya naji kinyi shiru kina tunani, ko kina da wata shawara ne?" Lushairat tayi firgigit! Kamar wacce ta farka daga barci ta dubeshi da sauri tace, "Eh.....abinda nake tunani shine, ci gaba da tafiyarmu da wannnan rauni naka da kumburin kafar taka ba a zai yiyu ba dole ne na fara yi maka magani. Koda jin haka sai Humairu ya dago kai da sauri ya dubeta yace, "shin dama ke likita ce?" Lushairat tayi murmushi sannnan tace, ai duk matar jarumi dole ne ta san magunguna iri-iri, kuma dole ne itama ta kasance jaruma koda kuwa a zuci ne ba'a zahiri ba. Mijina ya koya mini yadda ake rayuwa a daji da yadda ake farauta. Kai har yakin ma ya koya mini na iya abinda na iya dai-dai gwargwado. Yanzu zan kunna fitilar ice naje na nemo wani ganye da wata saiwa wacce zanyi maka magani dasu." Tana gama fadin Hakan sai ta yunkura da nufin ta mike tsaye, cikin sauri Humairu ya ruko hannunta yace, Akan wane dalili zaki bata Lokacinki akan talakanki?" Shin kin manta ne cewar ke matar Sarkin lurhaj ce, kuma uwar Sarkin lurhaj na gobe? Ai ni talakanki ne " cikin sauri lushairat ta zare hannunta daga cikin na Humairu ta mike tsaye sannnan ta dubeshi tace, " Talakan da ya ceci rayuwata da ta dana ya sami babban mukami a zahiri da badini. Har abada masauratar lurhaj baza ta taba mantawa dashi ba, kuma dole ne ta girmamashi tayi masa sakayya" Humairu yayi murmushi yace, Ai har yanzu ban sami nasarar kubatar da rayuwarku ba har sai na ga mun isa cikin birnin zaitun. Yanzu na baki kankanin lokaci kije ki samo ganyen da saiwar. Amma ina mai shawartarki daki nemo ganyen bishiyar raihas da saiwar bishiyar julus, domin sune masu saukin samu a wannan daji, kuma sune zasu sa nayi saurin samun lafiya. Cikin mamaki lushairat

Chapter 8 of 9