Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
da kakanninku suka shafe shekara da shekaru suna faman wahalar mayarda shi maraya?" To ku sani cewa dan halak baya yarda aci zarafinsa dana iyalinsa ko dukiyarsa sai dai ya mutu akan kare kimarsa da martabarsa. Ku tsaya kuyi yaki, ku zubar da jininku don kare kimarku da mutuncinku. Koda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai gaba dayan dakarun nasa suka ji kamar an cire musu dukkan tsoro da fargaba daga cikin zukatansu. Nan take jikinsu ya kama tsuma suka ji ma babu abinda suke so sama da su ga karasowar abokan gaba a fara gurmuzu. Nan take suka kama kiran sunan sarki ARYAN cikin hada baki suna cewa ransa ya dade. A dai-dai wannnan lokaci ne rundunar sarki larbusa ta kara kusantowo wacce saboda tsananin yawanta har ba'a iya hango karshenta, kai kace ta tokare da sararin samaniya. Koda su sarki larbusa suka yi arba da rundunar sarki Aryan wadanda basu fi kaso daya ba cikin kaso ukun tasu rundunar, kuma suka gansu 'yan kanana a gabansu amma ko gezau ba suyi ba bare suji tsoronsu, har ma ihu suke yi suna yiwa Sarkinsu jinjina, sai suka cika da mamaki. Shi kansa sarki larbusa sai da ya tsayar da giwarsa ya tsaya cak! Suka kurawa juna idanu shi da sarki Aryan wanda ke kan dokinsa. A wannan Lokaci tazarar dake tsakaninnsu bata wuce taku Ashirin ba, Sarki larbusa ya karewa sarki Aryan kallo sama da kasa, ya lura da irin kirarsa ta karfi da sadaukantaka,ku ma ya dubi cikin kwayar idanunsa yaga cewa tabbas wannan sarki ya cika JAN GWARZO,wanda zuciyarsa ta kekashe. Lallai bai san tsoro ba, kuma da gani kasan babu tambaya domin indai akwai dan shi akan kasa to a karkashinta ma ba za'a rasa ruwa ba. Abin nufi anan shine lallai alamar karfi tana ga mai kiba! Duk da cewa sarki larbusa ya tabbatar da cewa yafi sarki Aryan karfi da iya yaki a zahiri, amma sai zuciyarsa ta raya masa cewa babu mamaki fa sakon da Sarkin yakinsa ya zo dashi ya tabbata. Koda sarki larbusa ya gama aiyana wadannan al'amura a cikin zuciyarsa sai ya sakarwa giwarsa kaimi ya nufi inda sarki Aryan ke tsaye shi kadai. Har wadansu manyan mukarrabansa sun yunkura zasu biyoshi sai ya daga musu hannu ya tsaida su. Koda sarki Aryan yaga sarki larbusa ya nufoshi gadan-gadan ba tare da zare makami ba sai shima ya sakarwa dokinsa linzami ya nufeshi suka tunkari juna har sai da ya zamana cewa tsakaninsu bai wuce taku uku ba sannnan kowannensu ya tsayarda abin hawansa suka sake yiwa juna kallon nutsuwa na 'yan dakiku kadan. Sarki larbusa ya dubi sarki Aryan yace, "Ban taba haduwa da sarki mai DAKAKKIYAR ZUCIYA ba kamarka! Kuma ban taba ganin jarumin da ya burgeni ba irinka! Saboda ko kadan baka da tsoro tun da gashi ka tabbatar da cewar anfi karfinka amma saboda kishinka akan mulkinka, jama'arka da kasarka kaki mika wuya. Inaso ka sani cewa kune jarumai na farko a nahiyar nan kaf wadanda suka sami nasarar kashe wasu daga zakwakuran dakaruna. Lallai ina bukatar GWARZON JARUMI irinka! Shin me zai hana ka yi MUBAYA'A a gareni na baka Sarkin yakina ko don ka ceto rayuwar matayenku, 'ya'yayenku da tsofaffinku. Idan har ka mika wuya a gareni digon jini daya ba zai zuba ba a cikin wannan birni naka. baza a rushe gidajenku ba,ko a konasu, kuma ba za'a karbi koda kwayar hatsi ba a wajen talakawanka da kai kanka. Sai dai kasarka gaba daya zata dawo karkashin ikona! Kuma wanda naso daga cikin jama'ata shi zan nada ya hau kan karagarka!!!" Lokacin da sarki larbusa yazo nan a zancensa sai ran sarki Aryan ya sosu ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, bai san sa'adda ya tari numfashin sarki larbusa ba a fusace ya daka masa tsawa yace, "kai tsohon azzalumi! Kayi sani cewa ba zan taba siyar da jama'ata ba da kasata ba saboda tsoron MUTUWA! Da dai na bari azzalumi irinka ya shugabanci jama'ata gwara a shafemu daga doron kasa. Tsakanina da kai sai ya yaki! Babu Aminci sai matsanaciyar gaba!! Kaifin takobine kawai zai rabamu ". Koda jin wannnan batu sai sarki larbusa ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariyar mugunta, lokaci guda kuma ya turbune fuska, har fuskar tasa ta kama yin gatsine ita kadai, ya kuma cewa, "Ai kuwa sai kayi babbar nadamar da zata zamo abin misali ga duniya gaba daya! Daga yau sai na kashe Duk wani da namiji a birninka wanda ya kai shekara goma a duniya!! Dukkan 'yan matanku da matayenku na aure sai anyi musu fyade! Kuma na maishe su bayina! Sai na tabbatar da cewa an yiwa gidajenku da kasar birninka ado da jini kafin a kwashe duk abin amfani a cikinta a koneta kurmus ta zama toka! Sai na baje wannan kasa yadda ko a tarihi baza a iya tunowa da wanzuwarta ba.... Kafin sarki larbusa ya gama wannan furuci tuni sarki Aryan ya sake tarar numfashinsa a karo na biyu yace, "Ni kuma nayi maka alkawari cewar kafin ka kasheni sai na fitar da jini a jikinka! Na bar maka tabon da har abada ba zai bata ba. Kuma sai na yiwa dakarunka mummunar barna da ba a taba yi maka ba. Inda babu kasa anan ake yin gardamar kokawa, mu zuba mu gani!!" Koda gama fadin Hakan sai sarki Aryan ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya nufi cikin tawagar dakarunsa da sauri ya bar sarki larbusa a tsaye bisa giwarsa jikinsa na tsuma da karkarwa saboda tsananin fushi. Ji yake kamar yabi sarki Aryan da gudu ya sareshi. Kawai sai aka ga sarki larbusa ya sauko daga kan giwarsa ya juyo ya dubi dakarunsa masu jiran umurni. Sarki larbusa yasa hannunsa na dama ya zare zabgegiyar takobinsa ya dagata sama ya zabga kururuwa gamida yiwa dakarun nasa inkiya a afkawa abokan gaba! Kafin su zare takubbansu da sauran mugayen makamansu na yaki tuni shi sarki larbusa ya juya ya falfala da gudu Izuwa kan rundunar sarki Aryan. Koda sarki Aryan ya hango sarki larbusa a tsiyace a fusace ya durfafosu sai shima ya ruga Izuwa gareshi domin ya tareshi da sauri, saboda ya san cewa idan bashi ne ya tareshi ba zai iya yiwa dakarunsa mummunar barna cikin kankanin lokaci. Ai kuwa suna haduwa sai suka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban al'ajabi da ban tsoro, domin suna kaiwa junansu sara da suka ne cikin tsananin zafin nama, juriya da jarumtaka ta musamman, irin wacce idanu bai saba gani ba. A wannnan lokaci ne sauran dakarun sarki larbusa ma suka rugo da gudu Izuwa cikin filin yaki suna ihu da kururuwa mai firgita mazaje. Ba tare da shakkar komai ba kuwa suma dakarun sarki Aryan sai suka ruga suka taresu aka ruguntsume da azababben yaki a filin gaba dai ya zamo babu abinda mutum zai iya ji face ihun mazaje da karafkiyar karafa. Wohoho! Bala'i ba a sa masa rana! Haka ma wutar masifa idan taxo babu mai yayyafa mata ruwa face Allah!! Inda ace mutum na tsaye a filin wannan yaki yana ganin yadda ake gididdiba jikin bil'adama tamkar yadda ake sarrafa nama a mahauta da komai rashin imaninsa sai yaji zuciyarsa tayi rauni. Idan kuwa yana da dan guntun tsausayi ko da baifi kwayar zarrah ba sai ya zubar da hawaye. Duk inda mutum ya hanga ko ya waiga sai dai yaga sassan jikin bil'adama a zube tsubi-tsubi cikin ruwan jini tamkar bolar yayi da takarda, ko kuma ya gansu a sama suna shawagi suna zubowa kasa, kai kace biki ake yi na tsuntsayen duniya. Abin dai babu kyan gani, babu dadi! Sai da aka shafe kusan sa'a uku cur! Ana wannan BAKIN ARTABU, amma sarki larbusa da sarki Aryan na ta fafatawa dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar jikin abokin gwaminsa ba. Al'amarin da yai matukar baiwa sarki larbusa mamaki kenan domin gashi dai a zahiri yafi sarki Aryan tsagwaron karfin damtse, amma sai zafin naman su ya kusan zuwa daya. Nan fa ran sarki larbusa ya baci ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, saboda shi yasan cewa shi kadai yake tarwatsa runduna guda ta manyan mazaje ababan tsoro amma yau gashi mutum daya jal! Yana neman ya zamo masa alakakai. Nan take sarki larbusa ya sauya salon yaki, ya rinka kaiwa sarki Aryan hari da makami biyu a lokaci guda da dukkan karfinsa, wato bayan takobin dake hannunsa kuma sai ya zaro wata lafceciyar adda yaci gaba da kai masa mugayen hare-hare. Saboda karfin saram na sarki larbusa sai sarki Aryan ya kasa tsayawa a gabansa, bisa dole ya rinka ja da baya-baya, kuma ya rinka zille-zille da kauce kauce. Inda ba don yanada zafin nama gamida juriya da kwarewa ta yaki da tuni sarki larbusa ya gama dashi farat daya! Duk da haka sai da ta kai cewa da kyar! Yake iya kare hare-haren da yake kawo masa har ta kai cewa ya fara kuntatashi. Kwatsam! Sai sarki larbusa ya sami nasarar yankar sarki Aryan a gadon bayansa take wajen ya dare jini yai tartsuwa. Sarki Aryan ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zogin da yaji Sai yai sauri yayi alkafira da baya sau uku, ya diro akasa a matukar galabaice a Lokacin da jini ke zuba a gadon bayan nasa, kuma ya fara ganin mutane dishi-dashi. A hakan ne ya dubi gabas da yamma kudu da arewa yaga abinda ke faruwa a filin yakin. Nan take hankalinsa ya sake dugunzuma ainun fiye da koyaushe, domin gani yayi kawai ana ta ragargazar dakarunsa tamkar ana sassabe a gona. Al'amarin da yasa zuciyarsa ta kama tafarfasa kenan ya tuno da alkawarin da ya dauka cewar kafin a gama wannan yaki sai ya fitar da jini a jikin sarki larbusa. A wannan Lokaci sarki larbusa yana tsaye kawai yana faman kyalkyala dariyar mugunta bisa ganin nasarar da yasamu ta yiwa sarki Aryan wannan mugun rauni a gadon bayansa. Duk sa'adda wani badakaren sarki Aryan ya gifta ta gabansa kuwa sara daya yake yi masa ya gama dashi. Nan take idanun sarki Aryan suka kada suka yi jawur tamkar gasa dan buda a cikin wuta saboda tsananin fushi. Kwatsam! Sai aka ga sarki Aryan ya falfalo da azababben gudu daga inda yake yana ihu yana kade dukkanin abokan gaba dake gabansa ya nufi inda sarki larbusa ke tsaye bada fargabar komai ba. Shi kansa sarki larbusa sai da ya yi mamakin irin wannnan azababben gudu da sarki Aryan keyi da kuma yadda ya tunkaro shi gadan-gadan ba da shakkar komai ba. Ai kuwa shima sarki larbusa sai ya yunkura ya ruga domin ya tareshi yana mai yin wata kururuwa mai tsananin ban tsoro, wacce ita kadai ta isa ta sa kananan dakaru su dimauce su kama sakin fitsari a wando. Irin gudun da suke yi su biyun a wannan Lokaci kai kace akan iska suke saboda karfinsa. Lokacin da ya rage saura bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama kai kace daga cikin baka aka cillasu, suna haduwa suka kaiwa juna mugun hari. Kawai sai gani akayi duk su biyun sun rikito kasa sun tsugunna kasa sun kasa mikewa tsaye, kuma kowannensu kansa na sunkuye, jikinsa na tsuma. Daga can sai sarki larbusa ya fara mikewa tsaye, sai ga jini na digowa kasa ta cikin gefen sulken yakinsa. Cikin tsananin fishi ya yar da Addar hannunsa ya yage sulken dake kirjinsa yai jifa dashi. A sannnan ne ya yi arba da raunin da sarki Aryan yayi masa. Ashe takobi ya soka masa a gefen kirjinsa, bangaren hagu. Wajen yayi rami, har a sannnan jini na dan bulbulowa. Koda ganin wannan rauni sai sarki larbusa ya sake kwarara uban ihu a karo na biyu fiye da wanda yai da farko, kuma ya kamu da tsananin bakin ciki da takaici fiye da koyaushe a rayuwarsa. Domin wannan ne karo na farko da aka taba yi masa rauni a rayuwarsa koda bisa tsautsayi kuwa. Adaidai wannnan lokaci likitan sarki larbusa ya rugo da gudu Izuwa gareshi ya fara kokarin tsayarda jinin dake zuba a jikin nasa. A sannnan ne shima sarki Aryan ya mike tsaye da kyar yana mai dafe gefen cikinsa inda jini ke zuba. Shima wani lacecen yanka ne a wajen da takobin sarki larbusa tayi masa. Tabbas in ban da sarki Aryan ya kasance gwarzon jarumi mai juriyar gaske bai isa ya iya mikewa tsaye ba da wannnan rauni a cikinsa, domin saura kiris! Yankan ya fasa fatar cikin gaba daya aga kayan cikinsa. Idanunsa kuwa sai lumshewa suke, jiri na dibarsa yana layi kamar zai fadi,amma saboda taurin rai sai yai wuf! ya yagi rigarsa ya daure cikin nasa tamau, jinin ya daina zuba, sannnan ya tsaya daram akan kafafunsa ya dubi sarki larbusa ya bushe da dariya yana mai nunashi da Danyatsa sannnan yace, "Ko yanxu na MUTU burina ya cika tunda na cika ALKAWARINA na fitar da JINI a JIKINKA kafin karshen wannan yaki. Ina mai dada yi maka ALKAWARIN cewar yanzu zan sake yi maka wani RAUNIN a inda zai zamo SHAIDA yadda sai dai ka MUTU dashi, don har abada ba zai bace ba a JIKINKA! " Cikin tsananin fishi sarki larbusa ya tari numfashin sarki Aryan yana mai daka masa tsawa yace, "Ni kuma nayi maka alkawari cewar yanzu nan zan yi maka kissan wulakanci da zarar mun sake haduwa!!" Koda jin haka sai sarki Aryan ya sake bushewa da dariyar karfin hali yace, "Ai ko ba ka yi mini kissan gilla ba nasan cewa mutuwa zanyi, don yankan da kayi mini a cikina yayi zurfi ainun, ba zan tsira ba. Dubi jama'ata duk mutuwa suke ta yi, kuma nasan dayansu ba zai tsira ba,amma dai nasan cewa ko a bayan wannan yaki sai ka kwanta jinya. Na yarda ka cini da yaki, ka kama kasata, dukiyata da jama'ata, amma ka sani cewa iyalina sunfi karfin duk irin wulakancin da kake shirin yi musu. Domin baza ka taba riskarsu ba a cikin gidan sarautata ba!" Koda gama fadin Hakan sai sarki Aryan ya daga takobinsa sama ya sake falfalawa da matsanancin gudu Izuwa kan sarki larbusa a karo na biyu. Har Izuwa wannan Lokaci likitan sarki larbusa bai gama sa masa magani ba akan wannnan rauni nasa na kan kirji. Koda sarki larbusa yaga sarki Aryan ya kusa isowa kansa sai yasa hannunsa ya mangare likitan nasa yai sama ya fadi can gefe daya kai kace janyeshi akayi da majajjawa. Cikin bakin zafin nama da bakar zuciya sarki larbusa ya ruga Izuwa kan sarki Aryan. Wannan karon ma sai suka sake daka tsalle a sama suka kaiwa juna mugayen sara, kawai sai ji akayi duk su biyun sun kurma uban ihu sun fado kasa a matukar galabaice sun kife bisa kasa da rub da ciki! Ko motsin kirki babu wanda yayi a cikinsu. A wannan Lokaci an kashe gaba dayan dakarun sarki Aryan babu mutum daya a raye sai dakarun sarki larbusa ne kawai a tsaitsaye cikin tsananin tashin hankali sun kurawa sarki larbusa idanu wanda ke kwance da rub da ciki ba tare da sun fahimci halin da yake ciki ba,kuma an rasa wanda zai je ya dubashi. A wannan Lokaci fillin yakin ya cika da gawarwaki a ko ina a kasa suna ta iyo a cikin ruwan jini kai kace teku ce ta balle. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 3 PART 3 NASEER SHEHU TEARLOW ***** A wannan Lokaci an kashe gaba dayan dakarun sarki Aryan babu mutum daya a raye sai dakarun sarki larbusa ne kawai a tsaitsaye cikin tsananin tashin hankali sun kurawa sarki larbusa idanu wanda ke kwance da rub da ciki ba tare da sun fahimci halin da yake ciki ba, kuma an rasa wanda zai je ya dubashi. A wannan Lokaci fillin yakin ya cika da gawarwaki a ko ina a kasa suna ta iyo a cikin ruwan jini kai kace teku ce ta balle Bayan kamar dakika dari da Ashirin sai aka ga sarki larbusa ya yunkura ya mike tsaye. Koda ya daga hannunsa na hagu sai aka ga babu babban dan yatsansa, don ya guntule, jini na ta bulbulowa ta cikinsa. Koda ya dubi dan yatsan nasa yaga ya guntule sai ya sake kwarara uban ihu ya ruga Izuwa kan gawar sarki Aryan. Koda ya kamo kan sarki Aryan ya daga sama sai yaga ashe ya tsarge Gangar jikinsa gida biyu, wato kugunsa ya rabu da cikinsa tamkar an sa wuka an yanka tuffa a tsakiya. Kawai sai ya jifa da rabin Gangar jikin sarki Aryan ya tofa mata yawu sannnan ya dubi wani babban badakare nasa mai suna ZILGUL YACE dashi, "maza ka tattara sassan jikin sarki Aryan kasa ayi masa kabari a kofar fadarsa, nan gaba kabarin zai yi mini amfani matuka. Nan take zilgul ya dauko daya rabin jikin na sarki Aryan ya hada da dayan ya saba a kafadarsa. Sarki larbusa ya nufi kofar shiga birnin LURHAJ. Da isarsa bakin kofar sai yasa kafarsa daya ya banketa. Duk girman kofar da kaurinta sai ya zamo na banza, ta fadi kasa rikica! Wata irin kura mai yawa da karfi ta tashi, kawai sai sarki larbusa ya bayar da umurnin a afka cikin garin a kashe dukkan tsofaffi, kuma a kame mata da yara. Nan fa dakarun nasa suka ruga Izuwa cikin birnin LURHAJ suka hau ta more! Kaico! Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda dakarun sarki larbusa suka rinka kashe tsofaffin birnin LURHAJ, sannnan suna kama matayensu da karfin tsiya suna yi musu fyade, sannnan su daddauresu da sarkoki.sai dai kzaji mata da yara suna Iface-iface da koke-koke dole zuciyar mutum tayi rauni har ya zubar da hawaye. A cikin kankanin lokaci aka yi kaca- kaca da birnin gaba daya da kuma mutanen cikinsa aka kwashe dukkanin dukiyoyinsu aka tare a waje guda. Lokacin da aka shiga cikin gidan sarautar sarki Aryan aka gama da dukkanin jama'ar dake ciki sai aka duba ko ina da ina amma ba'a ga matar sarki Aryan ba da jaririn da ta haifa. Al'amarin da yai matukar fusata sarki larbusa kenan, kuma yayi matukar bashi mamaki, saboda tun kafin a fara yakin yayi bincike a halar tsafinsa yaga matar sarki Aryan da dan da ta haifa a cikin gidan sarautar, har Ya kudiri ajiyar cewar ba zai kashe sarki Aryan farat! daya ba sai bayan ya galabaitar dashi ainun sannnan zai yiwa matarsa fyade a gaban idanunsa sannnan ya kashe jaririnsa yana ji yana gani, sai kuma ya karasashi. Hakika ba karamin bakin ciki sarki larbusa yayi ba da yaga babu iyalan sarki Aryan, kuma dama tun kafin su fara wannan gurmuzu shi da sarki Aryan ya shafi madubin tsafinsa ya ga babu su a cikin gidan sarautar. Nan fa sarki larbusa ya sa aka ci gaba da duba ko ina, a cikin akwatuna, rijiyoyi da boyayyun wurare inda ake tunanin ko matar sarki Aryan da jaririnta sun buya a ciki. Amma har dare ya raba ana ta wannan bincike amma ba a gansu ba. A sannnan ne sarki larbusa ya zauna a cikin tsakiyar turakar sarki Aryan likitansa ya shiga dinke raunin dake jikinsa, kuma yana sa masa magani. Fuskar sarki larbusa a murtuke take ko kadan babu annuri, saboda tsananin fushi, takaici da bakin cikin rashin ganin iyalan sarki Aryan. Nan fa ya shiga tunani. Kwatsam! Sai tunanin matarsa ZURAIHA ya fado masa. Yace a cikin zuciyarsa, " kash! Amma nayi babban kuskure dana baro zuraiha a can sansaninmu, domin inda tana tare dani yanzu, sai ta gano inda iyalan sarki Aryan suke tun da ta fini karfin sihirin tsafi". Koda gama aiyana Hakan sai sarki larbusa ya kirawo babban hadiminsa zilgul ya dubeshi yace, "maza ka shirya ka koma da baya Izuwa sansaninmu ka taho da matata zuraiha Lallai ina son ganinta cikin gaggawa ". Zilgul ya risina yace, "An gama ya shugabana ". Nan take zilgul ya juya ya fice daga cikin turakar yaje ya kimtsa sannnan ya hau giwarsa ya durfafi sansaninsu. Tafiyar sadauki zilgul keda wuya sai sarki larbusa ya kirawo gaba dayan fadawansa ya dubesu yace, "ya ku yan majalisata yanzu dai ga shi mun ci birnin LURHAJ da yaki, birnin da babu kamarsa a gaba dayan wannan nahiya a girma, yawan arziki da karfin dakaru. To amma fa ku sani cewa mun kashe maciji ne bamu sare kansa ba tunda matar sarki ta gudu tare da dan da ta haifa. Wannan da, da ta haifa kuwa ba karamin annoba bane ga mulkinmu,domin bincike ya tabbatar da cewa idan har ya rayu ya cika shekara Ashirin da biyar a duniya nan gaba sai yazo ya shafemu akan doron kasa, ya karbi mulkinsa da kasarsa. Bisa wannan daliline yanzu na tsayar da wannnan yaki don ruguje sauran kasashen nahiyar wadanda dama basu kai darajar tsinke ba akan idanunmu. Abinda ya kamacemu a yanzu shine, mu baza dakarunmu masu yawa Izuwa gabas da yamma, kudu da arewacin wannan nahiya Izuwa cikin dazuzzukan birane domin neman matar marigayi sarki Aryan da jaririnta a duk inda suke a kashe su a kawo mini gawarsu. Wannan ne kadai zai sa mu sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Kafin a gano inda suke din zanyi jinyar raunikan dake jikina domin na sami karfin jikin nawa sossai. Yanzu zan sa a rubuta wasika Izuwa ga sauran dukkan kasashen nahiyar nan wadanda bamu cisu da yaki ba mu sanarda su cewar mun kama birnin LURHAJ. Gama fadin Hakan keda wuya ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar sarki Aryan. **** Al'amarin zuraiha kuwa, bayan su Humairu sunyi mata Sallama sun tafi zuraiha ta juya ta nufi inda tantinta yake, inda ta kalli gawarwakin dakarun dasu Humairu suka kashe sannnan ta iso inda ragowar dakarun suke wadanda suka zauna a gaban wuta suna jin dumi. Har ta giftasu zata je ta shiga cikin tantin nata sai wani tunani ya fado mata a rai ta tsaya. Dama su dakarun basa ganinta saboda karfin sihirin tsafinta, kuma ba su ga sa'adda ta fito ba. Kawai sai zuraiha ta dubi dakarun taMB hura musu iskan bakinta. Nan take suka bingire a kasa suka kama barci, sannnan itama ta shiga cikin tantinta ta kwanta ta kama barci abinta cikin kwanciyar hankali tamkar babu wani abu da ya faru a sansanin. Kashe gari kuwa, har rana ta kwalle wadanan dakaru basu farka ba daga dogon barcin da ya kwashesu sakamakon iskar bakin da zuraiha ta buso musu. Kwatsam! Sai ga sadauki zilgul ya tunkaro sansanin bisa giwarsa yana tafiya cikin sauri da takama, sai huci yake kamar tsohon maciji, kai kace shi kadai ma zai iya baje kasashen nahiyar gaba daya. Tub daga nesa hankalin sadauki zilgul ya yi mummunan tashi bisa ganin sauyin yanayi a sansanin, domin ba kamar yadda suka bar sansanin yake ba a yanzu. Sansanin yayi tsit! Tamkar babu wani mai rai acikinsa. Babu dakaru masu sintiri don tabbatar da tsoro. Ai kuwa yana kara matsowa kusa sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske, ya tsorata ainun sakamakon ganin gawarwakin dakarunsu Kimanin mutum tara. Cikin dimauta da hanzari zilgul ya zare takobinsa ya tsayar da giwarsa ya dure kasa daga kanta, sannnan ya kama tafiyar sanda yana waige- waige da dube-dube. Koda ya iso inda dakarun nan masu jin dumi suke sai ya iskesu a kwance suna ta faman shara barci har suna yin minshari. Gashi wutar da suka kunna har ta cinye ta zama toka sai burbushinta da dan hayaki kawai. Al'amarin da yai matukar bashi mamaki kenan, kuma ya daure masa kai. Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace, "To menene yasa aka kyale wadanan dakaru ba'a kashesu ba alhalin an kashe sauran 'yan uwansu? " Bashida amsar wannan tambaya da ya yiwa kansa, kuma babu mai amsa masa a kusa. Maimakon zilgul ya tashi wadanan dakaru daga barci sai kawai ya wuce gaba ya iso inda bayi suke a cikin kejin Nan ma ya gansu a kwance kuma a daure cikin sarkoki suna ta shara barci abinsu. Zilgul ya tasamma tantin zuraiha matar sarki larbusa zuciyarsa na ta dukan uku-uku yana fargabar kada yaje ya tarar da wani abu ya sameta. Abinda ya kara bashi mamaki shine, ko kuyanga daya bai gani ba daga cikin masu yi mata hidima a bakin tantin. Zilgul na shiga cikin tantin gimbiya zuraiha sai ya isketa a kwance tare da dukkanin kuyanginta suna ta faman shara barci da munshari. Koda ganin haka sai zuciyar zilgul ta kama tafarfasa kamar zata kone, bai san sa'adda ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin karfi da firgitarwa ba. Cikin firgici da dimaucewa gaba dayan mutanen dake sansanin suka farka daga nannauyan barcin da suke yi. Gimbiya zuraiha ta mike tsaye zumbur! A dimauce tana rawar jiki. Koda taga ashe sadauki zilgul ne tsaye a gabanta kuma ta fuskanci cewar shine yayi wannan ihu sai ta daka masa tsawa, ta dubeshi a fusace tace, "menene ya dawo da kai nan sansanin, kuma akan wane dalili zaka shigo har cikin tantina ka kurma wannan uban ihu? " Koda jin wannnan tambaya sai zilgul ya durkusa kasa bisa guiwarsa guda ya sunkui da kansa kasa cikin biyayya yace, "Ya shugabana ki gafarceni dole ce ta sa nayi hakan domin sarki ne ya aikoni na tafi dake Izuwa can birnin LURHAJ wanda mun dade da cinsa da yaki. A yanzu dana iso cikin sansanin nan sai na iske an kashe dakarunmu da yawa, sai kalilan ne suka rage, kuma sannnan na iske na iske ku kuna ta yin barci mai nauyi. Lallai duk yadda akayi abokan gaba sun shigo mana baku sani ba. Babu mamaki sun kubatar da rayuwar wadansu fursunonin " Koda zilgul yazo dai-dai nan a zancensa sai idanun zuraiha suka zazzaro, alamun tsoro ya bayyana sossai akan fuskarta ta mike tsaye zumbur! Da sauri ta fice daga cikin tantin. ***** DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 3 PART 4 NA KARSHE NASEER SHEHU TEARLOW ****** A yanzu dana iso cikin sansanin nan sai na iske an kashe dakarunmu da yawa, sai kalilan ne suka rage, kuma sannnan na iske ku kuna ta yin barci mai nauyi. Lallai duk yadda akayi abokan gaba sun shigo mana baku sani ba. Babu mamaki ma sun kubatar da rayuwar wadansu fursunonin " Koda sadauki zilgul yazo dai-dai nan a zancensa sai idanun zuraiha suka zazzaro, alamun tsoro ya bayyana sossai akan fuskarta ta mike tsaye zumbur! Da sauri ta fice daga cikin tantin. A Lokacin ne kuyangin nata su ka fara mikewa tsaye a razane. Shima zilgul sai ya biyo zuraiha baya da sauri. Zuraiha ta cigaba da yawo a cikin sansanin cikin sauri da gudu -gudu tana kallon abinda ya faru. Bayan taga gawarwakin dakarun da aka kashe sai ta dubi tsirarun dakarun da suka farka daga bacci ta daka musu tsawa tace, kuna ina har abokan gabarmu suka shigo sansanin nan suka kashe 'Yan uwanku?" Koda jin wannnan tambaya sai dakarun suka kama duru-duru suna kallon juna aka rasa wanda zai ce tak! Sannnan shugabansu ya risina yace, "Ya shugabata jiya har dare ya raba muna nan a gaban wuta muna jin dumi muna hira ko motsin bera ba mu ji ba. Daga sannnan ba mu san abinda da ya faru ba sai yanzu da muka farka daga barci sakamakon ihun sadauki zilgul ". Ya yin da zuraiha taji wannan batu sai tayi sauri ta dauko madubin tsafinta ta shafeshi da hannun hagu ta kura masa idanu har Izuwa tsawon yan dakiku sannnan ta dago kai ta dubi zilgul tace, Wasu zakwakuran jarumai ne guda biyu daga cikin kauyen kasar nan wadanda baku kashe su ba suka biyo sawun iyayensu da masoyansu. Sune suka zo suka kashe dakarunmu suka sami nasarar kubatar da bayi hudu. Kuma sune suka sa mukayi wannan barci mai nauyi da karfin sihirinsu na tsafi. Koda jin haka sai sadauki zilgul ya takarkare ya kwarara uban ihu a karo na biyu, sannnan ya dubi wadanan tsirarun dakarun da basu mutu ba yace, "sai kuyi shirin karbar hukunci daga wajen sarki bisa sakakin da kukayi haka ta faru". Caraf! Sai gimbiya zuraiha ta tari numfashin zilgul tace, " Ba zan bari ayi musu wani hukunci ba, domin abu ne wanda yafi karfinsu tunda ni kaina yafi karfina. Kawai abinda zamuyi shine, ku tashi mu tafi Izuwa birnin LURHAJ yanzu, idan na riski sarki zamu tattauna musan abinda zamuyi " Nan take kuwa aka shiga shirye- shiryen tafiya, sannnan aka fito da bayi daga cikin kejina aka tusa keyarsu gaba aka nufi birnin LURHAJ. Wannan shine abinda ya faru a sansanin da aka bar gimbiya zuraiha bayan sadauki zilgul yazo da sakon sarki larbusa. **** Al'amarin su jarumi Humairu kuwa, tun da suka kama hanya suka yi ta gudu a cikin daji tare da iyayensu da masoyansu su Laila, basu yada zango ba a ko ina har sai da suka iso iyakar birnin LURHAJ da wata kasa da ake kira ZAITUN, sannnan suka tsaya. A sannnan ne Humairu da Hashlar suka tsugunna a kasa suna ta faman haki kamar ransu zai fita saboda tsananin gajiya, saboda sun shafe kusan sa'a tara kenan suna gudu basu huta ba. Sai da suka dawo cikin haiyacinsu sannnan suka sha ruwa, suma iyayen nasu da 'yan matan nasu suka fito da abinci aka ci aka sha. Dama a can sansanin su sarki larbusa sun samu sun debo guzuri. Bayan kowa ya nutsu sai Humairu ya mike tsaye ya dubi mahaifiyarsa da masoyiyarsa laila yace, "Ni anan zan rabu daku, dole ne na koma can birnin LURHAJ yanzu. Koda jin wannnan batu sai mamaki da tsoro ya kama mahaifiyar Humairu da Budurwаrsa laila. Mahaifiyar tasa ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace, "akan wane dalili zaka koma Izuwa birnin lurhaj yanzu

Chapter 7 of 9