Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
Aryan yazo nan a jawabinsa sai gaba dayan yan majalisar suka dada dimaucewa suka firgita ainun. Wazirin sarki ARYAN ya dubeshi a rude yace, Ya shugabana lallai muna cikin tsananin masifa domin babu wata runduna ta mayaka da zata iya yin wannnan barna face wannan bakuwar runduna wacce aka ce a halin yanzu ta kama kasashe dari biyu da arba'in da uku a wannan nahiya. Sai da sama da kasashe tamanin suka hada kai da dakarun taron dangi domin su kawar da wannnan BAKAR RUNDUNA amma suka kasa. Ance wannan bakuwar runduna ta wadansu irin mutane ce masu kirar mutanen farko. Ya shugabana bamu da wani zabi wanda yafi mu hada namu inamu kowa da kowa muyi hijira mubar kasar nan gaba daya. Lallai a gaggauta yin shela a birnida kauye a bayar da wannnan izini Koda waziri yazo dai-dai nan a zancensa sai sarki Aryan ya daka masa tsawa, bama shi waziri ba hatta sauran yan majalisar dake wajen sai da suka firgita Sarki ARYAN ya dubi waziri cikin tsananin fushi yace, wacce irin maganar banza kake yi ne haka? " Shin ka manta ne cewa wadanan abokan gaba ance sun iso har kauyen Garul Aswar, wane isasshen lokaci ne damu wanda har zamu iya gama shiri mu yi hijira basu zo sun riskemu ba?" Ko kuma kana so ne sai muna kan hanya suyi mana kofar rago su ritsamu suyi mana kissan kiyashi?" Dukkan namijin kwarai baya gudu ya bar mahaifarsa domin itace abar tutiyarsa. Anan aka haifi iyayenmu da kakanninmu wadanda suka bayar da jininsu don kare iyalansu da dukiyoyinsu har aka samemu ashe kuwa ya zama wajibi muma mu bayar da jininmu don kare bayanmu koda kuwa dayanmu ba zai tsira da rayuwarsa ba. Bisa binciken da nayi a yanzu duk kasashen dake bayanmu duk an kamasu, wadanda make gabanmu haka Mu kadai ne muka rage, wannan alama ce mai nuna cewa su kansu wadanan rundunar bakaken dakaru sun san cewa muna da karfi. Ya zama dole mu tsaya mu jajirce muyi iya kokarinmu ya zamana cewa kafin akar biri, biri yayi barna. Ka tuna cewa koda mun ce zamu yi hijira a yanzu abu ne mawuyaci mu tsira tunda duk kasar da zamuje a gabanmu ko a bayanmu tuni wadanan bakin dakaru sun kamata. Ta ina zamu bi mu wuce har mu iya barin nahiyar gaba daya? Gwara mu tsaya mu bar abin tarihi wanda ba za'a taba mantawa dashi ba. Abinda nake so da ku shine maza aje a bayar da shelar cewa kowa yayi shirin yaki ban daukewa duk wanda ke da kashin lafiya ba face kananan yara da tsofaffi. Wanda duk yayi kokarin guduwa ni da kaina zanbi sawunsa na zare masa ruhin numfashinsa. Koda gama fadin Hakan sai sarki ARYAN ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin taron. Humairu da Hashlar na biye dashi a baya. Ai kuwa suma yan majalisar sai suka mike tsaye gaba dayansu cikin sauri suka bisu a baya duu. Nan take aka bayar da shelar shirin yaki Nan fa dakaru suka yi ta tuttudowa daga cikin birane da kauyuka suna taruwa a kofar birnin akayi ta fito da makaman yaki gamida tarkuna iri iri har dama irin wadanda anfi shekara da shekaru ba'a sake yin amfani dasu ba. Kafin cikar kwana daya da yini daya kofar birnin LURHAJ ta cika da dakarun yaki sama da mutum miliyan Ashirin da biyar ga sunan tsubi tsubi, sahu sahu Wasu akan dawakai, wasu akan rakuma da Alfadarai wasu kuma a kasa. Yan baka dabam, masu takobi da garkuwa dabam, sai kuma yan masu da yan majajjawa. Kai komai yawan runduna da kwarjininta idan taga wannan ta mutanen birnin LURHAJ sai hankalinta ya tashi domin ta san cewa kawar da wannnan din ba karamin aiki bane. Sarki ARYAN ne ya zamo jagoran wadanan mayaka, Humairu da Hashlar na taimaka masa, kuma sune akan gaba rundunar mayakan sun zuba ido kawai suga ta inda abokan gabar zasu bullo. Dama an tura dakarun leken asiri gabas da yamma, kudu da arewa Izuwa dazuzzuka sunyi kwanton bauna akan bishiyoyi masu tsawo wadanda da zarar sun hango abokan gaba zasu ruga suzo su sanar. Idan mutum yaga su sarki ARYAN a cikin sulken yaki a wannan Lokaci dole ne yasan cewa maza sun fito da shirin ayi ta ta kare domin hatta Humairu da Hashlar sun rufe dukkanin jikinsu da kayan karfe hatta kawunansu kuwa sun sanya hulunan karfe idanunsu kadai ake gani. A ranar kwana da yini daya ne kuwa wani dan leken asiri da aka tura yammacin dajin ya falfalo da gudun tsiya Izuwa kofar birnin LURHAJ inda su sarki ARYAN suka yada sansani. Da isowarsa gaban sarki sai ya zube kasa yana haki ya kwashi gaisuwa sannnan ya dago kai ya dubi sarki ARYAN yace ya shugabana na hango wadannan dakarun sumame yanzun nan sun durfafo wannan gari namu bisa giwaye. Narantse da darajar iyayena ko a labari ban taba ganin mutane masu irin girmansu da kwarjininsu ba. Sarki ARYAN yace, nawa ne adadinsu? " Dan leken asirin yace, gaba dayansu basu fi su dubu daya ba yanzu haka sun ketare kwazazzabon Bamhar suna daf da isowa kwarin kusara. Koda jin haka sai sarki ARYAN yai murmushi yace, "kadan ne daga cikinsu kuma an turo su ne neman su Humairu domin tabbas labari ya riski Sarkinsu bisa dakarunsa guda uku dasu Humairu suka kashe, Koda sarki Aryan yazo nan a jawabinsa sai kuma ya dubi Humairu da Hashlar yace, ni da ku da kuma dakaru dubu kozo muje mu tari wadanan abokan gaba tun gabanin su iso nan kofar birnin, Ina son mu kashe su duka amma mu bar daya jal daga cikinsu wanda zai koma ya kai labari. Koda jin wannnan batu sai Hashlar ya dubi sarki ARYAN cikin alamun tsoro yace, ya shugabana anya kuwa zamu iya da mutum dubu na rundunar wadanan abokan gaba? " Ka tuna fa cewa da kyar muma muka kashe mutum uku kacal. Maimakon sarki ya baiwa Hashlar amsar tambayarsa sai ya dubi Sarkin yakinsa wanda ake kira BARDE HABWAN yace, wanda duk ya karaya ya koma da baya ba sai ya biyomu ba. Koda gama fadin Hakan sai sarki ARYAN ya zaburi dokinsa da gudu ya nufi cikin daji. Cikin sauri habwan, humairu da Hashlar suka rufa masa baya sannnan sauran dakaru dari tara da casa'in da tara suka bisu duu..... Kai kace yakin ne ya barke a sannnan, * * * Sarkin yaki garbuza da dakuru dubu na tafe bisa giwayensu suna bin sawun kafafun su Humairu da Hashlar sai suka iso wannan wuri wanda ake kiran kwarin kusara. Shi dai kwarin kusara wata yar sirriyar hanya ce wacce manyan dogoyen duwatsu suka sa ta a hanya. Tun kafin su garbuza su iso wannan wuri na kwarin kusara ashe su sarki ARYAN sun iso sun yi kwanton bauna akan saman duwatsun. Rabin dakarun da suka biyo sarki ARYAN duk yan baka ne kuma ya gaya musu cewa da zarar ya basu umurnin harbi su tabbatar da cewa sun harbi wuyan dakarun da fuskokinsu kada su kuskura su ce zasu harbesu a gangar jikinsu. Sarki ARYAN ya bayar da wannnan umurni bisa la'akari da labarin dasu Humairu suka bashi bisa gurmuzun da suka yi da wadannan samudawan. Sai da su Sarkin yaki garbuza suka iso tsakiyar wannan kwarin sai sarki ARYAN ya bayar da umurnin a bude musu harbi Nan take kuwa yan baka suka fara sakin harbi kafin dakarun garbuza su daga garkuwoyinsu su fara kare harbin tuni an kashe musu sama da mutum dari biyu. Da yake garkuwar tasu garbuza ta karfe ce sai ya zamana cewa da kibiya ta dira a jikinta kaga ta kare. Koda sarki Aryan yaga harbin bashida sauran amfani sai ya zare takobinsa ya kwarara uban ihu yana mai bayar da umurnin a afkawa su garbuza. Nan take kuwa Humairu da Hashlar da sauran dakaru suka zare takubbansu suka daka tsalle Izuwa kasan duwatsu suka dira akan su garbuza. Nan take wurin ya yamutse aka ruguntsume da azababben yaki. DUGUNZUMA..2!!! LITTAFI NA BIYU PART 2 NASEER SHEHU TEARLOW ****** Koda sarki Aryan ya ga harbin bashida sauran amfani sai ya zare takobinsa ya kwarara uban ihu yana mai bayar da umurnin a afkawa su garbuza. Nan take kuwa Humairu, Hashlar da sauran dakaru suka zare takubbansu suka daka tsalle Izuwa kasan duwatsun suka dira akan su garbuza. Nan take wurin ya yamutse aka ruguntsume da azababben yaki. Duk inda sarki Aryan, humairu da Hashlar suka durfafa sai dai kaga maza na zubewa kasa ratata tamkar sarki ya hana dawa tsayuwa. Haka kuma duk inda garbuza da sauran dakarunsa suka kutsa cikin dakarun su sarki Aryan sai dai kaga suma suna yin gagarumar barna. Al'amarin da ya matukar girgiza kowanne bangare kenan domin asarar rayuka ta shafesu su duka. Sai da aka shafe kusan sa'a ana wannan artabu ya zamana cewa babu abinda kunne keji face ihun mazaje da haniniyar dawakai da giwaye, Jini kuwa ya rinka fallatsi da famtsama sassan jikin bil'adama ya kama shawagi a sama yana zubowa kasa. Ana ckin wannan hali ne Sarkin yaki garbuza ya farga cewa idan aka ci gaba da yakin a haka za'a iya yin ragas. Koda fahimtar hakan sai garbuza ya kurma uban ihu yana mai baiwa dakarunsa inkiya akan su dan ja da baya nan take kuwa dakarun suka bi wannan umurni suna ja da baya kadan sai su Aryan suka ja da bayan aka tsaya akayi cirko cirko ana kallon juna. A sannnan ne aka fahimci cewar dakarun su garbuza basu wuce saura su dari uku ba, su kuwa dakarun su sarki ARYAN basu wuce saura su dari shida ba, alhalin dama can sau biyu suka ninka su garbuza. Kaga kenan dai babu bangaren da zai iya daga hannu yace ya sami nasara. Koda ganin haka sai Sarkin yaki garbuza ya nuna sarki ARYAN da takobinsa yace, Ya kai wannan takadarin jarumi kayi sani cewa idan muka ci gaba da wannnan yaki a haka jama'ata da jama'arka duk karewa zasu yi. Shawarar da zan bamu itace ni da kai mu kara wanda duk ya kashe a tsakaninmu ya zama shugaba sai yayi duk yadda yaso da sauran dakarun dake tsaye anan. Idan kuma baka son mu yi wannan fada nida kai ka bani ragowar jarumai biyu wadanda suka kashe mana wadansu dakaru namu guda uku acan wani kauye da ke can baya na tafi dasu Izuwa ga sarkinmu. Sa'adda garbuza yazo dai-dai nan a zancensa sai sarki Aryan yai shiru yana nazari da tunani. Daga can sai ya dubi garbuza yace, bazan baka wadanan jarumai biyu ba, don haka na yarda mu kara yaki ni da kai. Koda ka sami nasara akaina ina mai baka sako ga sarkinka ka gaya masa cewa nayi alkawari kafin a gama wannan yaki shima sai jini ya zuba daga jikinsa. Koda jin haka sai garbuza ya bushe da dariyar mugunta sannnan ya murtuke fuska yace, inda ka san ko wanene sarkina da baka fadi haka ba. Ina tabbatar maka da cewa a halin yanzu duk duniya babu sadauki ko kuma gwarzon mayaki kamar sarkina. Ya halarci yaki guda casa'in da shida a rayuwarsa amma ko digon jini bai taba diga ba daga jikinsa. Ba'a taba kaishi kasa ba, kuma duk abinda ya sa a gabansa sai sami nasara. Koda jin haka sai sarki Aryan yayi guntun murmushi yace, "ai shi tsautsayi bashida rana, kuma ba kullum ake kwana akan gado ba. Lallai wannan karon sai na rugaza tasirin jarumtakar Sarkinka. Koda jin wannnan batu sai garbuza ya fusata ainun ya ruga Izuwa kan sarki Aryan yana mai daga katuwar takobinsa sama yana kururuwa. Shima sarki Aryan sai ya rugo gareshi yana ihu, ai kuwa suna haduwa suka kacame da azababben yaki. Nan fa ragowar dakarun garbuza dasu jarumi Humairu suka ga abin al'ajabi irin wanda basu taba gani ba, domin ana fara wannan gurmuzu sarki Aryan ya zamewa garbuza alakakai ya kuntatashi. Tsananin zafin naman sarki ARYAN ya wuce tunanin kowa dake wajen. Gashi dai kiri kiri garbuza yafi sarki ARYAN girma da tsagwaron karfin dantse, amma kuma da yake sarki ARYAN ya fishi zafin nama da gocewa da iya sarrafa takobi sai gashi ya kuntatashi. Bugu da kari sarki ARYAN bai tsaya kai sara da suka kadai ba sai da ya hada da kai naushi da bugu hannu da kafa kuma ya rinka yin alkafira yana shawagi a saman garbuza kai kace ya kasance tsuntsu mai fuka- fuki. A haka ne ya sami nasarar yankar garbuza a fuska yayi masa wani katon bille akan kumatunsa kuma ya jera masa duka goma sha daya a kirji da kafafunsa biyu a sama. Tun garbuza yana yin baya baya yana taga taga har sai da ya fadi kasa, takobin hannunsa fadi can gefe daya ya baje a kasa magashiyan kafin garbuza ya yunkura ya mike tsaye tuni sarki ARYAN ya sake afkawa ragowar dakarun garbuza, cikin kankanin lokaci ya kashe su gaba dayansu su dari ukun. Wani irin mugun kisa ya rinka yi musu yana shaftare musu makogwaro da kaifin takobinsa a Lokacin da suma ya rinka shawagi a kansu. Dukkaninsu suka rikito kasa daga kan giwayensu suka zube kasa matattu. Koda garbuza ya ga abinda ya faru ga sauran dakarunsa sai ya yunkura cikin zafin nama ya ruga inda takobinsa ta fadi domin ya dauka amma sai sarki ARYAN ya dako tsalle daga inda yake ya doki bayansa ya kifa da rub da ciki. Kafin ya dago ya juya Aryan ya daka tsalle ya dira a gabansa ya dora kaifin takobinsa akan wuyansa. Garbuza ya waigo ya dubi sarki Aryan cikin tsananin fusata jikinsa na tsuma yace, me kake jira dani,ka kashe mana? A wannan Lokaci Humairu, Hashlar da sauran dakaru sun bude baki kawai suna kallon ikon Allah sun kasa koda motsi saboda tsananin mamaki bisa ganin wannan gagarumar jarumtaka da sarki ARYAN yayi. Sarki Aryan ya dubi Sarkin yaki garbuza ya yi murmushi irin na manyan jarumai wadanda suka yarda da kansu yace, bazan kashe ka ba, domin inason ya zamana cewa kai kadai ne ka koma wajen Sarkinku a raye domin ka isar da sakon da na baka gareshi. Tabbas idan yaga wannan rauni danayi maka a fuskarka kuma yaji cewa na kashe sauran dakarunka zai yarda cewa kafin a gama wannan yaki shima sai jini ya zuba a jikinsa. Lallai sai na rugaza tarihin jarumtakarsa a duniya. Koda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai garbuza ya mike tsaye cikin takaici ya ruga Izuwa inda giwarsa take ya daka tsalle sama ya haye kanta sannnan ya juya da baya ya nausa Izuwa cikin daji da gudu. Tafiyar Sarkin yaki garbuza keda wuya sai su Humairu suka rugo da gudu Izuwa inda sarki ARYAN yake suna masa jinjina. Maimakon suga sarki ARYAN yana murna sai suka ga idanunsa sun ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa. Al'amarin da ya matukar firgitasu kenan, hankalinsu ya dugunzuma ainun, Cikin sanyin jiki Humairu ya risina a gaban sarki ARYAN yace ya shugabana ina dalilin zubar wannan hawaye naka? Kamata yayi ka kasance mai fаrinсiki bisa wannan nasara da muka samu ta kashe dakaru Kimanin dubu na wadanan abokan gaba. Sa'adda sarki Aryan yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya yana mai share hawayensa sannnan ya dubi Humairu yace, ya kai jarumi mai sa'a da nisan kwana, kayi sani cewa wannan nasara da muka samu ba nasara bace. Gagarumin bala'i ne ga mutanenmu domin tamkar mun tsokano tsuliyar dodone a Lokacin da yake kwance yana barci. Wannan hawaye daka ga ina zubarwa kuwa bana komai bane face na hango halin da kasarmu zata koma. Tabbas sai an rushe dukkanin gidajenmu, an kone komai. Sai an kashe dukkanin mazajenmu Babu sauran masu tsira face kananan yara da mata Ya kai Humairu ka kasance mai rike alkawarin dake tsakaninmu Lallai ka kare rayuwar matata har Izuwa Lokacin da zata haihu lfy Kuma ka reni abinda zata haifa acan wata nahiyar dabam Komai daren da dadewa ina sa ran cewa dan da matata zata haifa zai dawo birnin LURHAJ ya karbi karagar mulkinsa. Yanzu ku tashi muyi sauri mu koma can kofar gari domin mu cigaba da shirin tarar abokan gaba domin da zarar garbuza ya kai sakona zasu taho gaba dayansu ayi wannan gagarumin yaki. Sa'adda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai jarumi Humairu yace, Ya shugabana ina mai neman alfarma guda daya. Inason yanzu nida Hashlar ka kyalemu mu bi sawun wannan badakare da ya tafi kaiwa sarkinsu sakonka domin muga inda sansaninsu yake mu ceto rayuwar iyayenmu mata da masoyanmu wadanda muke son mu aura anan gaba. Lallai zan kasance mai cika alkawarin dake tsakanina dakai, wato zan dawo domin na tserar da rayuwar matarka. Koda sarki Aryan yaji wannan batu sai ya dubi Humairu cikin alamun tausayawa yace, Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa ko ka kadan bana yin kokwanto bisa duk abinda kace zakayi. Na yarda cewa zaku iya Zuwa ku karbo iyayenku da 'yan uwanku, amma fa ku sani cewa koda kun karbosu abune mawuyaci ku dawo tare dasu har nan a raye domin na tabbatar da cewa sai abokan gaba sun kure muku gudu sun riskeku. Idan ma basu riskeku ba akan hanya ba, ko kun iso birninmu ai dai baza a fasa yin wannnan yaki ba kuma kuna ji kuna gani zaku rabu dasu. Ku daina tunanin akwai sauran rayuwa ga jama'armu a wannan nahiya har da kuke sa ran zaku auri masoyanku kuci gaba da zama. Ina tabbatar maku da cewa wadanan abokan gabarmu sai sun mamaye ko ina a wannan nahiya tamu sai ya zamana cewa an manta da irin zuri'armu sai tasu. Wanda duk yai saura a cikinmu ya gudu Izuwa wata nahiyar dabam shine kadai zai iya bayar da labarinmu. Bazan hanaku zuwa aiwatar da abinda ke ranku ba,don nasan kai mutum ne mai sa'a amma ina mai dada rokonka da kada ka karya alkawarin dake tsakaninmu. Laila kafin na fadi na mutu a wannan yaki inason naga Lokacin da zaka dauke matata ka fitar da ita daga wannan nahiyar gaba daya. Idan har ka cika alkawari ka dawo zan sanar da kai hanyar da zaka bi ka sulale daga cikin birninmu koda kuwa ana tsaka da wannnan yaki. Koda jin haka sai jarumi Humairu yace, tabbas zaka sameni mai cika alkawari. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA BIYU PART 3 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ******** Lallai kafin na fadi na mutu a wannan yaki inason naga Lokacin da zaka dauke matata ka fitar da ita daga wannan nahiyar gaba daya. Idan har ka cika alkawari ka dawo zan sanar da kai hanyar da zaka bi ka sulale daga cikin birninmu koda kuwa ana tsaka da wannnan yaki. Koda jin haka sai jarumi Humairu yace, tabbas zaka sameni mai cika alkawari. Nan take Humairu da Hashlar suka yiwa sarki ARYAN sallama sannnan suka juya da baya suka falfala da azababben gudu Izuwa cikin daji. Kaji manyan mazaje wadanda babu ruwansu da hawa doki domin sun saba da gudun kafa wanda ya kai tafiyar Zango dari. Sai da Humairu da Hashlar suka kule a cikin daji sannnan su sarki ARYAN suka kada dawakansu suka zaburesu da gudu suka koma birnin LURHAJ. Tun daga nesa dakarun yaki dake tsaitsaye a sahu sahu a bakin kofar gari suka ga dawowar su sarki ARYAN sai suka rude da shewa suna yi musu jinjina don sun tabbatar da cewa sun sami nasara a wannan fita da suka yi. Abinda ya daurewa kowa kai shine, ganin fuskar sarki ARYAN a murtuke babu wani sassauci. Cikin sauri aka budewa su sarki ARYAN kofa suka kunna kai. Da isarsu kofar fada sai ga wata kuyanga ta fito daga cikin gidan sarautar a guje fuskarta cike da annuri. Kuyanga ta zube kasa a gaban sarki Aryan tana haki tace,ya shugabana sarauniya ta haihu lafiya. Koda jin wannnan batu sai sarki Aryan ya kamu da tsananin farin ciki, nan take ya duro daga kan dokinsa ya ruga Izuwa turakar matarsa lushirat. Yana shiga ya isketa kwance akan gado ga kyakkyawan jaririnta a daf da ita lullube cikin mayafi yana barcinsa abinsa. Sarki ARYAN ya matso daf da lushirat fuskarsa cike da annuri ya sumbaci goshinta yana mai yi mata barka da haihuwa lafiya sannnan yace, Wane suna ya kamata a sawa wannan jaririn? " Koda jin wannnan tambaya sai hawaye ya zubowa lushirat tace, banida zabi bisa sunan da za'a sawa wannan yaro tunda abune mawuyaci ka rayu Izuwa ranar da za'a yi bikin radin sunansa. Koda jin wannnan batu sai jikin sarki Aryan yai sanyi ya dauki jaririn ya rungumeshi a kirjinsa, kawai sai idanunsa sun ciko da da har hawaye ya fara sartu bisa kumatunsa sannnan ya dubi lushirat cikin alamun tsananin tausayawa yace, tabbas ba zan ga ranar da za'a yi radin sunan wannan yaro ba abinda nake so dake shine, ki sawa wannan yaron sunana domin naji a jikina kuma bincikena ya tabbatar da cewa shine zai gajeni har ma sai ya fini jarumtaka kuma shine zai karbi karagar mulkin kasar nan a hannun wadanan abokan gaba namu. Koda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai lushirat ta fashe da matsanancin kuka ta mike tsaye ta rungume sarki tace, Ya kai mijina kayi sani cewa ba zan iya rabuwa da kai ba a yanzu. Lallai kazo mu yi sauri mu bar wannan nahiya gaba daya tun kafin wadanan abokan gaba su iso garin nan. Sa'adda sarki Aryan yaji wannan batu sai ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta cikin fushi yace, Ya ya kike tsammanin cewa zan iya guduwa na bar jama'ata a cikin masifa? Ta yaya kike tsammanin cewa zan iya barin karagar mulkina wacce na gada a wajen ubana saboda tsoron mutuwa? Idan nayi haka na karya tarihin iyayana da kakannina, domin a duk cikin zuri'armu ba a taba samun sarkin da ya mika wuya ba ga abokan gaba sai dai ayi yaki a kaishi kasa. Na rantse da darajar iyayena ba zan mutu rago ba sai dai na mutu jarumi. Ni ki kyaleni na tsaya na kare mutuncina da jama'ata amma ke da jaririnki lallai zaku bar wannan nahiya gaba daya domin kuje ku ci gaba da sabuwar rayuwa a wata nahiya dabam. Tuni na mika amanarku ga jarumi Humairu na kauyen Garul Aswar. Jarumin da bincike ya tabbatar da cewar sai ya rayu a wannan gagarumin yaki da za'a fafata. Laila kibi wannan jarumi Humairu bisa duk irin umurnin da zai baki domin na aminta dashi dari bisa dari. Koda sarki Aryan yazo nan a jawabinsa sai lushirat ta sake fashewa da kuka tana mai cewa, Yanzu shikenan wannan da dana haifa zai taso kenan a matsayin maraya kuma a cikin rayuwar wuya da rashin sanin makoma mai kyau. Cikin hanzari sarki ARYAN ya rufe bakin lushairat da tafin hannunsa yace, kada ki kara fadin Haka. Na gaya miki cewa wannan da, da kika haifa lallai komai daren dadewa sai ya gajeni saboda haka koda zaku sha wahala to fa wahalar mai wucewa ce, zaku sha dadi a gaba. Yake matata inason ki daukar mini alkawari guda daya. Alkawarin kuwa shine inason ki raini dana kamar yadda iyayena suka reneni wato ki koya masa dakewar zuciya irin tawa ya zamana cewa bai san tsoro ba sannnan kuma kisa a horar dashi koyon fada da yaki da yaki tun daga kurciyarsa har Izuwa girmansa. Duk irin wahalar da zai sha akan wannnan horo kada ki ji tausayinsa kiyi masa sassauci domin ba gata za kiyi masa ba. Wannan shine iyakar wasiyyar da zan bar miki kuma ina ganin cewa wannnan shine kalamina na karshe a gareki domin daga yanxu bana jin zamu sake ganin juna. Zanje mu ci gaba da shirye shiryen yaki domin a ko yaushe abokan gaba zasu iya isowa nan. Koda gama fadin Hakan sai sarki Aryan ya mikawa lushairat jaririn ta karba sannnan ya juya ya nufi kofar fita daga cikin turakar kai tsaye ba tare da Ya waigo ba. Koda ya kai bakin kofar yasa kafarsa guda daya a waje sai lushairat ta kwala masa kira ya tsaya cak. Lushairat ta ajiye jaririn nata akan gado sannnan ta ruga da gudu ta rungume Aryan tana mai fashewa da sabon kuka tana mai cewa, ya kai mijina kayi sani cewa rabuwa da kai ba karamar masifa bace a gareni domin ka sani cewa a halin yanxu banida kowa a duniya face kai da wannnan jaririn nawa. Idan babu kai waye zai ci gaba da bani kulawar dakeke bani?" Koda jin tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Aryan yai shiru bai ce komai ba kawai sai ya janye jikinsa daga cikin na lushairat ya fice da sauri. Sau daya ya sake waigowa ya dubi jaririn ya kau da kai ya tafi ita kuwa lushairat sai ta ci gaba da kwala masa kira tana ci gaba da kuka har sai da ya bace mata da gani. Wannan shine abinda ya faru a birnin LURHAJ bayan sarki Aryan da tsirarun dakarunsa sun koma gida, kuma sun sami nasara akan su Sarkin yaki garbuza. ****** Acan sansanin su sarki larbusa kuwa, Lokacin da sarki larbusa ya ga su Sarkin yaki garbuza sun dade basu dawo ba sai ransa ya baci, cikin tsananin fushi ya dubi wani bardensa wanda ake kira DAUJIN yace dashi, maza ya kamo giwarsa ya kawo masa domin ya hau kuma shi ka dai zai bi sawun su garbuza domin yaga abinda yasa suka dade basu dawo ba. Nan take daujin ya cika umurni yaje ya janyo giwar sarki ya kawota gabansa yasa ta durkusa kasa bisa guiwoyinta hudu har sarki larbusa ya yunkura zai hau kan giwar kenan sai aka hango Sarkin yaki garbuza shi kadai bisa giwa ya tunkaro sansanin a guje fuskarsa a yamutse babu annuri kuma ga katon bille na yankan takobi akan kumatunsa. Koda aka hango garbuza a cikin wannan hali sai kowa ya cika da tsananin mamaki. Shi kuwa sarki larbusa sai yaji zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fushi. Koda isowar garbuza daf da sarki sai ya ja tunga ya sauko da sauri daga daga kan giwar ya zube kasa a gabansa ya kwashi gaisuwa yana mai sunkuya da kansa kasa. Larbusa ya dakawa Sarkin yaki garbuza tsawa yace, ina sauran dakarun da na hadaka dasu kuma waye yayi maka rauni haka akan fuska?" Ba tare da garbuza ya dago kai ba ya dubi larbusa sai yace, ya shugabana kayi sani cewa kamar yadda ka umurcemu mun koma Izuwa wancan kauye amma bamu riski kowa ba a can amma mun ga sawayen mutum biyu." Nan take muka ci gaba da bin sawayen har sai da ya kaimu Izuwa wani kwaroro mai tsawo wanda dogoyen duwatsu guda biyu suka sashi a tsakiya. A dai-dai wannnan lokaci ne aka shammacemu kawai sai harbin kibiyoyi muka ji, kafin mu kare kanmu da garkuwoyi an kashe mana mutane da yawa kuma a sannnan ne abokan gaba suka fito daga maboyarsu suka zare makamai suka afka mana aka ruguntsume da azababben yaki. Daga cikin abokan gabar har da Sarkin birnin LURHAJ wanda ake kira Aryan. Ya shugabana ina tabbatar maka da cewa tunda nake fita yaki a rayuwata ban taba karo da sadaukin jarumi mai naci da zafin nama ba tamkar sarki Aryan. Kai kadai ne zaka iya dashi, cikin abinda bai wuce sa'a daya ba ya kashe gaba dayan dakarun da ka hadani dasu ya zamana cewa saura ni kadai, Nan fa muka shiga gurmuzu nida sarki Aryan, sama da tsawon rabin sa'a muna fafatawa amma na kasa koda lakutar jikinsa. A sannnan ne ya sami nasarar yankata a fuska kuma yai tsalle sama kamar tsuntsu ya rinka jera mini naushi a kirji da kafarsa har sai da ya kaini kasa. Na baje cikin matukar galabaita sai gani nayi ya dira a gabana ya sa min kaifin takobinsa a wuyana. A fusace na daka masa tsawa nace me yake jira dani, kawai ya kasheni. Koda jin haka sai sarki ARYAN yayi murmushi yace, abinda yasa ba zai kasheni ba shine yana son nazo na gayamaka cewa kafin a gama wannan yaki kaima sai ka zubarda jini... Kafin garbuza ya gama rufe bakinsa tuni sarki larbusa ya zaro wata gajeriyar wuka a kugunsa cikin bakin zafin nama ya sokawa garbuza a goshinsa. Take wukar ta lume ta fito ta keyarsa jini ya kama kwararowa kasa kai kace idaniyar ruwa ce ta balle kawai sai garbuza ya bingire kasa matacce. Al'amarin da yai matukar razana gaba dayan dakarun sarki larbusa kenan da sauran bayin da aka kamo dake daure cikin sarkoki. Sarki larbusa ya tofawa gawar Sarkin yaki garbuza yawu sannnan yace, "Girmanka da sadaukantakarka duk sun zama na banza tunda har kanaji kana gani aka kashe mana mutane kuma mutum daya jal ya zame muku alakakai " Koda gama fadin Hakan sai sarki larbusa ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda zai iya tarwatsa dakaru komai yawansu a filin yaki. Nan take sarki larbusa ya bayar da umurnin ayi shirin yaki a durfafi birnin LURHAJ. Mutum dari kacal ya bari a sansanin domin su bayar da tsaro ga matarsa da kuma bayin da aka kamo. Nan take sarki larbusa ya jagoranci dakarun yaki suka bar sansanin suka durfafi hanyar da zata kaisu birnin LURHAJ. Idan mutum ya dubi wannnan runduna tasu sarki larbusa dole ne ya firgita komai dakewar zuciyarsa saboda kwarjininsu da kuma irin tarin kayan yakin da suke dauke dasu. Tabbas in da sarki larbusa ya san abinda zai biyo baya da bai bar kowa a wannan sansanin ba. ******** ASHE duk abinda ya faru yanzu a sansanin su sarki larbusa jarumi Humairu da Hashlar na labe a cikin duhuwar

Chapter 4 of 9