Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
bar mahaifata A Lokacin da nike daf da cika babban burina na duniya wato Lokacin da zan ga dana na cikina. Wanda kullum nake mafarkin ganinsa akan karagata. A koyaushe matata lushirat zata iya haihuwa, burina shine na dauki jaririn da ta haifa da hannuna na daurashi akan karagar mulkina. Idan naga wannan Al'amari na gama cika burina, ko a sannnan ma idan na mutu banida asara. Abinda yasa na hanaku baiyana zuwan wadanan mutane a fada shine, jama'ata zasu firgice su fara kokarin guduwa, a kokarin hakan kuma zasu iya rasa rayuwarsu da dukiyoyinsu a dazuzzuka Sakamakon arangama da 'yan fashi da mugan dabbobi. Ni yanzu abinda na yanke hukunci shine, Ni da Sarkin yakina zamu jagoranci gaba dayan dakarunmu mu fita mu tari wadanan mutane ko mu kosu, amma zaman gida ba namu bane, Kai da dan uwanka Hashlar na yarda da jarumtakarku kuma an san cewa zaku taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Saboda haka sai ku shiga cikin rundunarmu don kishin kasarmu. Ko kadan bana son hankalin matata ya tashi saboda wannan tsohon ciki da take dauke dashi. Shine dalilin da yasa bana son tasan da faruwar wannan yaki. Lokacin da sarki ARYAN yazo nan a jawabinsa sai Humairu da Hashlar suka dubi junansu sannnan Humairu ya dubi sarki ARYAN yace, ya shugabana ina son ka sani cewa yadda duk kake tsammanin wadanan mutane sun wuce haka. Ko mu fita mu taresu ko mu tsaya a gida bamu isa mu hanasu isowa nan ba. Idan kuwa sukazo duk yawan nan namu dakake gani sai gaba dayan mazajenmu sun fadi kasa. Ka sani cewa bamu zo gareka domin ayi shirin yin yaki da wadannan mutane ba,sai domin ka sanar da jama'a su gudu mai rabon tsira ya tsira." Kafin Humairu ya gama rufe bakinsa tuni sarki ARYAN ya daka masa tsawa wacce tasa duk su biyun suka firgita. A fusace sarki ARYAN ya zare takobinsa ya fuskancesu yace, ko kubi umurnina ko kuma nayi yaki daku a cikin wannan daki wanda duk ya sami nasarar kashe wani sai shawararsa tayi amfani. Koda jin wannnan batu sai Humairu da Hashlar suka yi tsuru-tsuru suka hau kallon juna. Nan take Humairu ya fada kogin tunani. Kimanin shekara uku baya da suka shude akwai wata rana sa'adda Humairu da Hashlar, ILsam, Zuraif, Hashim , Sahal, Kaimur suka zo fadar sarki ARYAN kowannensu ya saba katuwar dabbar da ya farauto a daji. Daga wanda ya kamo katon zaki sai wanda ya kamo katuwar damisa kura da sauran manyan dabbobin daji masu matukar hadari da ban tsoro. Nan take jaruman bakwai suka zube dabbobin a gaban sarki ARYAN A matsayin sun bashi su kyauta alokacin da maroka suka rinka yi musu kirari suna kodasu a matsayin manyan jarumai da babu kamarsu akasar. lokacin da sarki ARYAN yaji kirarin da ake yiwa su Humairu yayi yawa Sai ya daga hannu sama kowa yai shiru, fadar tayi tsit! kawai sai ya mike tsaye ya dubi jama'a yace, "Ni ban yarda da jarumtakarka wadanan samarin guda bakwai ba. Kuma ko sau daya basu taba birgeni ba saboda sun kamo wadanan mugayen dabbobin daji. "Yaku jama'ata zaku gasgata zancena bayan na jarraba karfin dantsena da iya yakina akansu ni kadai. Saboda haka yanzu ni kadai zan yakesu su bakwan. Na rantse da darajar karagata dayansu ba zai iya yi mini rauni ba, idan kuwa yayi mini, na yarda zan sauka daga kan karagata na bashi ya hau. Koda jin wannnan batu sai mutane suka firgita kuma suka cika da tsananin mamaki har wadansu ma suka fara tunanin ko sarki yasamu tabin kwakwalwa ne. Abinda ya janyo haka kuwa shine kowa a birninsa yasan irin jarumtakar wadanan mafarauta guda bakwai domin duk shekara idan akayi gasar jarumtaka sune suke lashewa. Shi kuwa sarki ARYAN bai taba shiga wannan gasa ba tunda shine mai shiryata. Abu na biyu a tsawon shekara goma sha uku da sarki ARYAN ya hau kan karagar mulki bai taba fita yaki ba da kansa. Duk sa'adda yaki ya taso sai dai sarkin yakinsa ya wakilceshi. To wai shin mutumin da bai taba fita yaki ba, kuma ba'a taba ganin jarumtakarsa ba shine yanxu zai tari manyan gwarzaye bakwai? " To wai shin menene takamarsa?" Tambayoyin da jama'a suka kasa amsawa kenan. Sarki ARYAN ya sauko daga kan karagar mulkinsa ya cire alkyabbarsa sannnan sai ya juya ya dubi matarsa gimbiya lushirat cikin murmushi. Itama sai ta maida masa da martanin murmushin fuskarta cike da annuri babu wata fargaba. Al'amarin da ya kara baiwa kowa mamaki kenan domin anyi zaton za a ga hankalinta ya dugunzuma. Sarki ARYAN ya zare takobinsa ya fuskanci zaratan jaruman bakwai wato su Humairu yace, "ku nake jira kuma bayan mun gama wannan yaki da makami na yiwa kowannenku rauni daya bayan daya zamu gwada karfin dantse dimin naga iyakar jarumtakar taku. Sa'adda su Humairu sukaji wannan batu sai suka kama dariya suna yiwa sarki ARYAN wani irin kallo cikin rauni domin sun san cewa ko ba a gwada ba ai linzami yafi karfin bakin kaza. Koda Sarki ARYAN yaga haka sai ya rugo Izuwa kansu ya fara kaiwa humairu wawan sara a wuya Cikin bakin zafin nama Humairu ya sunkuya takobin ta sari iska ya zaro tasa takobin suka ci gaba da artabu. Suma su Hashlar sai suka zare nasu takubbansu suka rufarwa sarki ARYAN. Wohoho! Wanda ya iya ya huta, tabbas jarumtaka da sadaukantaka baiwa ce, wanda duk Allah ya bashi sai dai a kyaleshi kawai domin yafi gaban wargi. Lokacin da aka fara wannan gurmuzu tsakanin sarki ARYAN da su Humairu sai hankalin kowa a fada ya dugunzuma domin su bakwan sun kasa koda lakutar jikin sarki ARYAN kuma ya zame musu alakakai duk da cewa suna kawo musa hari ko ina. Babu abinda yafi baiwa mutane mamaki face tsananin zafin naman sarki ARYAN da yadda ya kuntata jaruman bakwai kuma ya zamana cewa yana iya sara da sukansu ta kowanne bangare, gabas da yamma, kudu da arewa da kuma sama da kasa harma wata irin alkafira yake yi a kasansu ko a samansu yana tarwatsasu da karfin saransa. Sai da aka shafe rabin sa'a cur! Ana wannan gurmuzu an rasa mutum daya daga cikin jaruman bakwai wanda ya sami nasarar taba jikin sarki ARYAN. Nan fa fadar ta rude da shewa aka rinka yiwa sarki tafi ana mamakin irin wannnan jarumtaka tashi. Koda ganin haka sai sarki ARYAN ya sauya salon fada ya zama kamar tsuntsu mai fuka-fukai ya zamana cewa a samansu Humairu yake shawagi yana kai musu sara, kafin kafarsa ta raba kasa sai a shafe dakikoki masu yawa, ai kuwa bai dade da fara yin hakan ba ya dimautasu. A Lokaci guda ya sami nasarar yankar kowa daga cikinsu. Wani a hannu, wani a kafa, wani a kirji, wani a gadon baya. Duk su bakwan babu wanda bai yi masa rauni ba, kawai sai yayi alkafira a sama ya dira a can gefe daya nesa dasu ya mayarda takobinsa cikin kufe yana murmushi. Koda ganin haka sai gaba dayan jama'ar dake fadar suka rude da tafi aka hau yiwa sarki ARYAN jinjina cikin tsananin al'ajabi domin babu wanda ya san cewa yana da irin wannan jarumtaka. Su kuwa su Humairu sai suka cika da tsananin bakin ciki domin a tarihin jarumtakarsu tun daga kurciyarsu kawo Izuwa girmansu ba'a taba samun wani jarumi da ya taresu ba har ya sami nasarar akansu sai shi sarki ARYAN din Dukkaninsu sai suka kama tsuma cikin tsananin fusata musamman Kaimur wanda yake ji da tsagwaron karfin dantse yana ganin cewa idan ya matse sarki ARYAN sai ya kakkarya masa kasusuwan jiki ko kuma idan ya bangajeshi da kirjinsa. Bayan sarki ARYAN ya maida takobinsa cikin kufenta sai ya cireta gaba daya daga cikin jikinsa. Sannnan ya cire rigar jikinsa, sai ga damtsensa da kwanjinsa sun baiyana a fili karara, duk jijiyoyin jikinsa sun tashi sun kumbura sunyi burdin burdin. Babu wanda ya taba ganin sarki ARYAN a cikin wannan kama don haka sai aka cika da mamaki su kansu su Humairu sai da suka ji wani abu a jikinsu, domin Kaimur ne kadai mai irin siffar jikin sarki ARYAN. Nan take sarki ARYAN ya dubi su Humairu yayi murmushi yace, "Nasan ku mafarauta ne kowannenku yana tafe da magani a jikinsa. Maza ku yiwa raunikan jikinku magani, sannnan mu gwada 'yar kashi domin nafison mu kara a Lokacin da kowannenku yake da isasshen kuzari. Kuyi sauri ku tsayar da jinin jikinku dake zuba don kada ku rasa kuzarin. Ba tare da gardamar komai ba kuwa kowannensu ya buda jakar guzurinsa ya dauko magani yasa a rauninsa. Sai bayan 'yan dakiku sa'adda kowannensu ya sami nutsuwa sannnan sarki ARYAN ya dubesu yace, "To ku shirya ga namiji nan bisa kanku. Kamar hadin baki sai sarki ARYAN da Kaimur suka rugo da kan juna a Lokaci guda, ai kuwa suna haduwa suka bangaji juna da kirji, tamkar dutse da dutse ne suka hadu kirazan nasu suka ba da wani irin sauti duum! Kuma ko gezau dayansu baiyi ba, sai kallon juna suke kawai irin kallon nan KAR TA KAR. Hakika Kaimur yayi tsananin mamaki domin duk wani abu mai rai idan ya hada kirji dashi a saninsa sai wannan abu yaje kasa tunda ko bishiya ko dutse ragargazarsu yakeyi. Koyaushe yana alfahari da karfin kirjinsa. A fusace Kaimur ya sungumi sarki ARYAN ya dagashi sama ya damfarashi da kasa, sai kawai ya ga sarki ARYAN ya dire da kafafunsa shima sai ya sunkuceshi ya dagashi sama Maimakon ya damfarashi da kasa sai ya makashi a jikin bango. Take Kaimur ya fado kasa ya baje yana murkususu ya kasa mikewa tsaye. Nan fa fadar ta sake kaurewa da shewa gami da jinjina. Koda su Humairu suka ga abinda ya faru ga dan uwansu Kaimur sai suka fusata suka rugo gaba dayansu Izuwa kan sarki ARYAN sukayi masa rubdugu sunayi masa luguden duka ya zamana cewa sun lullubeshi har ya tsugunna kasa. A wannan Lokaci ne gimbiya lushirat ta firgice bata san sa'adda ta kwalawa sarki ARYAN kira ba cikin ihu da razana. Ai kuwa yana jin kiranta sai ya taso da dukkan karfinsa ya tarwatsasu ya hau su da naushi da bugu da hannu da kafa,sai gashi yana watsi dasu kamar yara na gara tamola. Kafin a jima duk su shidan ya hada musu jini da majina duk sun zube kasa a galabaice an rasa wanda zai mike tsaye daga cikinsu. Koda ganin wannan gagarumar jarumtaka da sarki ARYAN yayi sai gimbiya lushirat ta mike tsaye zumbur daga kan kijerarta ta rugo gareshi cikin tsananin farin ciki ta rungumeshi. Jama'a kuwa suka sake rudewa da shewa aka hau buga tambura ana busa algaita, mawaka na yiwa sarki ARYAN kirari. Lokacin da Humairu yazo dai-dai nan a tunaninsa sai ya dago kai ya dubi sarki ARYAN cikin matukar damuwa yace, "Ya shugabana kaima ka sani cewa ni din da dan uwana Hashlar bamu isa mu tareka da yaki ba domin ruwa ba sa'an kwando bane, don haka dole ne mubi umurninka. Amma fa ka sani cewa wannan hanya da kake shirin bi ba mai bullewa bace idan kuka bita kana ji kana gani za'a shigo har cikin birninka a cika da yaki. Koda jin wannnan batu sai idanun Sarki ARYAN suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo sannnan ya dafa kafadar Humairu yace , "na gani a cikin madubin Bokana cewar zakayi tsawon rai a duniya abinda nake so da kai shine, idan har matata ta haihu to duk abinda ta haifa na bar amanarsa a hannunka. Itama matar tawa na bar amanarta a hannunka. Ka tsare lafiyarta da rayuwarta komai rintsi da tsanani. Shin ka dauki wannan alkawari?" Cikin firgici Humairu ya dubi sarki ARYAN yace, ya shugabana saboda me Zaka dora mini wannan nauyin alhalin kasan cewa ba zan iya ba. Ka sani cewa a halin yanzu fa mahaifiyata da masoyiyata laila suna can a hannun wadanan samudawa na kasa tserar da rayuwarsu da lafiyarsu. Yaya kuma yanzu zaka sake dora mini wani nauyi?" Nifa ban taba yin imani da tsafi ba saboda mahaifina bashida addini face farauta. Saboda haka ni ban yarda cewa zan iya kubuta ba daga shairin wadanan samudawa ba. Gaskiya ba zan iya karbar wannan amana ba tunda nasan cewa kokarin da zakayi a wannan yaki ko rabinsa ba zanyi ba. Koda jin haka sai sarki ARYAN ya dakawa Humairu tsawa yace, dole ne ka daukar mini wannan alkawari saboda kana daga cikin kalilan mutanen dasu rayu bayan wannan yaki. Kai ne kadai xaka iya sake kafa tubalin wannan birni namu mai albarka. Fatana shine dan da matata zata haifa ya shugabanci sabon wannan birni. Dukkan burina yanzu ya rataya a wuyanka. Da wannnan furuci nake yi muku sallama sai ku fara shirin fita yaki. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA DAYA PART 6 LITTAFIN YAKI ******* Koda jin haka sai sarki ARYAN ya dakawa Humairu tsawa yace, dole ne ka daukar mini wannan alkawari saboda kana daga cikin kalilan mutanen da zasu rayu bayan wannan yaki. Kai ne kadai xaka iya sake kafa tubalin wannan birni namu mai albarka. Fatana shine dan da matata zata haifa ya shugabanci sabon wannan birni namu mai albarka. Dukkan burina yanzu ya rataya a wuyanka. Da wannnan furuci nake yi muku sallama sai ku fara shirin fita yaki. Lallai gobe da asuba zamu fita mu tari wadanan abokan gaba kafin su iso nan su riskemu. Koda gama fadin Haka sai sarki ARYAN ya juyo ya fice daga cikin dakin ya bar Humairu da Hashlar a tsaye cikin tsananin tashin hankali da damuwa gamida da matukar mamaki bisa yadda al'amuran suka kasance. Duk su biyun sai suka zauna suka sake yin tagumi suka yi shiru suna tunani har Izuwa lokaci mai tsawo. Daga can sai Hashlar ya dubi Humairu a Lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace, "ya kai abokina ka tuna cewa mun rasa abokanmu su ILsam, mun rasa iyayenmu mata da kuma masoyanmu wadanda muke da burin aurensu. Kauyenmu wato asalin mahaifarmu an baje shi an kona shi. Bamu da sauran wani farin ciki a doron kasa. Yanzu gashi mun zo nan domin mu kubatar da rayuwar miliyoyin jama'a amma sarki yaki bamu hadin kai yace, mu shirya muyi yakin da mun san cewa babu nasara acikinsa. Ya kai abokina na sani cewa muna da burin mu kwato iyayenmu mata da masoyanmu daga hannu wadanan samudawan amma fa burina na matacce wanda ko a farki ba zai cika ba. Zamu iya guduwa mu bar wannan nahiya gaba daya domin mu tsira da rayuwarmu amma menene amfanin mu gudu mu bar iyayenmu da masoyanmu acikin bala'i, kunci da bakin ciki mara tukewa. Mu maza ne kuma kowanne namiji an san shi da jajircewa akan gaskiyarsa da tsare mutuncinsa dana iyalansa da kuma na kasarsa wanda duk bashida kishin wadanan abubuwa uku bai cika mutum ba. Tabbas sarki ARYAN yayi gaskiya domin da dai mu mutu ragwaye gwara mu mutu mazaje, wata ran za'a yi labarinmu anan gaba har mu zamo abin misali ga mutanen baya. Abinda nake so da kai shine ba gudu ba ja da baya. Kawai mu tsaya ayi wannan yakin damu. Sa'adda Hashlar yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa Humairu ya rungumeshi duk su biyun suka fashe da kuka suna masu kankame juna kamar bazasu daina ba. Lokacin da sarki ya koma cikin gidan sarauta sai ya nufi turakar gimbiya lushirat fuskarsa cike da annuri tamkar babu wani abu dake damunsa a cikin zuciyarsa. Da shigarsa cikin turakar sai ya hango gimbiya lushirat zaune akan luntsumemen gadonta ta juya baya. Cikin sanda ya karasa daf da ita yasa hannayensa biyu akan idanunta domin ya rufe mata idanu. Kawai sai yaji ruwan hawaye akan hannunsa, a firgice ya juyo da fuskarsa ai kuwa sai ya ganta a jike sharkaf da hawaye, Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsa kenan ya dubeta cikin tsananin mamaki da kaduwa yace, ya ke abar begena wane ya bata miki rai har ya saki kuka haka? " Ki fada mini ko waye yanxu nan uwarsa ta haifi wani. Koda jin wannnan batu sai gimbiya lushirat tasa hannunta ta share hawayenta sannnan ta dubi sarki ARYAN cikin nutsuwa tace, ya kai mijina kayi sani cewa duk abinda ya faru tsakaninka da Boka KURHAS IBINI LAMRAS jiya naji kuma na gani don haka kadaina tunanin zaka boye mini wannan Al'amari. Hatta duk abinda ka tattauna dasu Humairu acan dakin baki na gani kuma naji. Tabbas bamuda sauran farin cikin rayuwa domin burinmu ya rushe, shawarar da zan bamu kawai itace mu kashe kanmu yanzu a cikin wannan daki mu huta da takaicin da zai zo ya samemu anan gaba domin tabbas za'a kasheka, ni kuma za'a dauke ni a tafi dani, Ta yaya kake sai zan iya rayuwa a doron kasa alhalin na san cewa babu kai. Ka sani cewa a duniya babu abinda nake so sama da kai kuma banida kowa sai kai. Ka tuna da alkawarinmu na cewar babu abinda zai rabamu face mutuwa kuma mutuwar ma sai dai ta daukemu a lokaci guda. Lokacin da gimbiya lushirat tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubowa sarki ARYAN ya rike kafadunta yace, Yake matata ke kuwa yaya akayi kika san abinda ya faru tsakanina da boka kurhas alhalin sanda na kadaita dashi a cikin turakata kuma sai da na kulle kofofi da tagogi kuma yaya akayi kika san abinda ya faru tsakanina dasu Humairu a dazu acan gani?" Lushirat tayi ajiyar zuciya tace, da farko dai a jiya sa'adda kuka shigo cikin turakarka kai da Boka KURHAS tuni ni ina cikin turakar baku sani ba saboda haka ina ganin shigowarku sai na fada karkashin gado na buya har Izuwa da kuka gama maganganunku kuka fita. Na dade ina kuka da bakin ciki a karkashin gadon sannnan na fito. Ina fitowa kuma sai nayi arba da madubin tsafin boka kurhas, ina ganin madubin na gane cewa lallai mantashi yayi saboda rudewa da fargabar abinda zai zo. Kawai sai na dauki madubin na tafi dashi turakata na boyeshi ba tare da kowa ya gani ba. A dazu ne na dauko madubin na shafeshi da hannun hagu kamar yadda naga boka kurhas yayi da nufin naga abinda zaku tattauna kai da su Humairu saboda tun a fada nayi zargin cewa ba komai zaku tattauna ba face irin maganar da kukayi kai da Boka KURHAS. Ai kuwa nan take naji duk maganganun da kuka yi, Al'amarin da ya kara jefani cikin matsanancin bakin ciki kenan na kama kuka shine ka shigo yanzu ka iskeni ina kuka. Koda gama wannan jawabi sai lushirat ta dago matashin kai ta dauko wannan madubin tsafi ta mikawa sarki ARYAN. Yana karbar madubin sai ya dokashi da kasa ya tarwatse, sannnan ya dubi lushirat a Lokacin da hawaye yaci gaba da zubo masa yace, "hakika tsafi bashida rana a gareni tunda ya kasa kawar da abinda zai kawo rabuwata dake kuma ya kasa hana tarwatsewar farin cikin rayuwarmu. Yake matata inaso ki sani cewa ina ji a jikina cewar lallai zaki haifi abinda ke cikinki kuma a bayan bama nan abinda kika haifa komai dadewa sai yayi mulki a wannan birni na LURHAJ. Kinga kenan mutuwarmu a yanzu dai-dai take da rushewar tarihin birninmu har abada. Idan kuwa kika haihu zamu bar baya. Sa'adda sarki ARYAN yazo nan a zancensa sai lushirat ta dubeshi cikin matukar damuwa yayin da hawaye keta sartu bisa kyawawan kumatunta tace, Menene tabbacinka cewar Humairu zai iya tserar da rayuwar abinda zan haifa domin naji ka bashi amanarsa da tawa?" Sarki Aryan yai ajiyar numfashi sannnan yace, "Boka kurhas ya tabbatar mini da cewa Humairu tun yana mutum ne mai sa'a da nasibi duk abinda ya sa a gabansa sai yai nasara. Bisa wannan daliline yanzu na dora dukkan burina a kansa. Koda jin wannnan batu sai gimbiya lushirat ta rungume sarki ARYAN ta sake fashewa da matsanancin kuka shi kuma ya shiga rarrashinta. * * * A can sansanin su sarki labarusa kuwa Lokacin da aka kai laila cikin tantin sarki aka daureta sai sarki labarusa ya shiga cikin tantin da nufin ya afka mata domin tun sa'adda ya kyalla ido yai arba da ita ya aiyana Hakan a zuciyarsa. Yana shiga cikin tantin sai ya iske matarsa zuraiha zaune daf da laila tana bata madarar shanu a koko tana sha. Cikin fushi sarki labarusa ya dubi zuraiha yace, saboda me zaki shayar da wannnan fursunar alhalin ta kasance mai wargi da raini a garemu? " Ba tare da alamar tsoro ko damuwa ba zuraiha ta juyo ta dubi sarki larbusa tace, bisa alkawarin dake tsakanina da kai har a gama wannan yaki baza ka afkawa wata 'ya mace ba haka ne ko ba haka bane? " Cikin alamun kunya sarki larbusa ya kau da kai sannnan yace, ai ban kawota nan domin wani abu ba sai domin inason nasa ayi mata azaba mai radadi saboda ta kuranta masoyinta a kaina, kuma ina son na yiwa masoyin nata kisan gilla a gaban idanunta. Zuraiha tayi murmushi tace, shin babu inda zaka sa ayi mata azabar ne sai anan cikin tantinka?" Kada ka manta cewa a cikin alkawarinmu akwai batun cewa bazaka azabtar da mata ba, kuma ba za'a yi musu fyade ba. Ba kai ba ko a cikin yaranka duk wanda ya karya wannan doka sai ya fuskanci hukunci domin doka ce wacce muka gada tun iyaye da kakanni a duk sa'adda muka fita yaki. Ka tuna cewa baka da wani buri wanda yafi ka mamaye wannan nahiya gaba dayanta ya zamana cewa dukkan kasashen nahiya suna karkashin mulkinka. A wannan nahiya kasashe dari biyu da arba'in da uku ne, A halin yanzu mun ci kasashe dari da tamanin da shida da yaki kuma a ko ina ka kafa jama'armu sunci gaba da mulki. Yanzu saura kasashe hamsin da bakwai kacal burinka ya gama cika. Kasar da muka durfafa a yanzu wacce ake kira birnin LURHAJ itace mafi girma da yawan mayaka daga cikin kasashen da suka rage mana. Ka taka a hankali kuma ka kiyaye alkawarin dake tsakaninmu domin idan ka saba daya daga cikinsu nida sauran matan jama'armu zamu iya yimuku bore mu bata muku dukkan shirinku. Yanzu zan dauki wannan fursuna na tafi da ita tantina bazan baka ita ba har sai ranar da ka kamo masoyinta in yaso ku fafata yaki kai da shi a gabana a gabanta domin muga iyakar jarumtakarsa tunda ta kodashi ta kurantashi akanka. Na sani cewa kayi yake-yake a rayuwarka sama da guda casa'in kuma babu wani da namiji wanda 'ya macce ta haifa wanda ya taba kaika kasa. Ina alfahari da wannnan daukaka taka ya kai mijina saboda haka xan zuba ido naga yadda zata kaya tsakaninka da saurayin wannan yarinya. .. Koda gama fadin Hakan sai zuraiha ta kwance laila daga jikin dirka sannnan ta ingiza keyarta gaba a cikin wulakanci suka fice daga cikin tantin suka bar sarki larbusa a tsaye sororo kamar yaro mara wayo zuciyarsa a kufule yana mamakin yadda wannan mata tasa ta dade tana yi masa kama karya a cikin harkokinsa kuma gashi ta zame masa alakakai sai juyashi take kamar waina a kasko alhalin duk duniya babu wanda ya isa ya daga masa dan yatsa face ita. Wannan ya samo asali ne sakamakon wani babban sirri dake tsakaninnsu don haka zuraiha ta zame masa kadangaren bakin tulu. Har dare yayi gari ya waye sarki larbusa bai rintsa ba sakamakon tunani da damuwa bisa rashin ganin dawowar su Sarkin yaki garbuza. Nan take jikinsa ya bashi cewa lallai ba lafiya ba. Don haka sai ya fara tunani a ransa cewa anya kuwa maganar da laila ta fada masa ba gaskiya bace?" Koda yaji ya fara wannan tunani sai ya mike tsaye zumbur ya fito daga cikin tantinsa ya Dakawa gaba dayan dakarunsa tsawa yace, "kowa ya kintsa a juya da baya domin a koma wannan kauye na Garul Aswar, wato kauyensu Humairu. Gama fadin Hakan keda wuya sai aka jiyo sautin sawayen giwaye sun durfafo sansanin. Nan fa kowa ya zuba idanu akan hanya sai aka ga su Sarkin yaki garbuza sun dawo a sukwane fuskokinsu a murtuke babu annuri kamar wadanda aka aiko musu da sako mutuwa. Garbuza na rike da wani buhu dauke da wani abu a ciki, da isowar garbuza gaban sarki larbusa sai ya tsaida giwarsa ta tsaya cak,ta daga kafafunta na gaba sama alamar tana gaisuwa ga sarki larbusa sannnan ta ajiye kafafunta kasa. Sarkin yaki garbuza ya sauko daga kan giwar rike da wannnan buhu kawai sai ya zazzage abinda ke cikin buhun agaban sarki. Ba komai bane face kawunan wadanan samudawan uku na sarki larbusa wadanda ya turasu su kashe mutanen da aka jiyo rurin ihunsu bayan angama da kauyen Garul Aswar. Koda sarki larbusa ya ga kawunan wadanan dakaru nasa sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa, gaba dayan dabbobi da tsuntsaye dake dajin sai da suka razana suka kama guje guje daga cikin ramuka suna neman sabuwar maboya, wasu kuma suna sauya sheka. Nan take sarki larbusa ya dubi giwar Sarkin yaki garbuza ya gabza mata naushi a ciki take giwar tayi ruri ta fadi kasa ta baya rikica, ko motsi ba ta kara yi ba ta zama gawa. Larbusa ya kara kwarara uban ihu wanda yasa dukkan dakarunsa da bayin da aka kamo suka dimauce suka rinka dunkule jikinsu saboda razana, kasa ma ta kama girgiza Sarkin yaki ne kadai bai fita haiyacinsa ba. A wannan Lokaci idanun sarki larbusa sun kada sunyi jawur tamkar garwashin wuta kuma ilahirin kofofin gashin jikinsa sun bude suna fitar da tiririn zufa. Tunda Sarkin yaki garbuza yake tare da sarki larbusa bai taba ganin fushinsa ba irin na wannnan lokaci. Cikin tsananin fushi da kakkausar murya Sarki larbusa ya dubi Sarkin yaki garbuza yace, yaya akayi aka kashe mini wadanan dakaru nawa?" Sarkin yaki garbuza ya risina a cikin alamun tsoro da biyayya yace, "ya shugabana Lokacin da muka isa wannan kauye sai muka iske sababbin gawarwaki na samari guda biyar sannnan kuma muka ga gawar wadanan dakaru naka. Abinda na fahimta shine, wadannan samaru sun cika jaruman gaske kuma sune suka yi ragas da dakarunmu uku. Sarki larbusa ya dubi garbuza yace, wane irin kisa kuka iske dakaruna sun yiwa samarin biyar? " Garbuza yace, sassarasu suka yi gunduwa-gunduwa. Koda jin haka sai sarki larbusa ya jinjina kai yace, Samarin basu biyar bane akwai ragowar su, ragowar tasu ne suka kashe dakaruna kuma sun gudu sun bar kauyen. Jeka tantin matata kace da ita tazo wannan fursuna yanzu Nan take Sarkin yaki yaje ya cika umurni sai ga zuraiha tareda laila ta tasota a gaba. Da zuwansu sai sarki larbusa ya zare wata karamar wuka mai karfin tsiya a jikinsa ya yanki damtsen hannun laila wajen ya dare jini yai feshi. Laila ta kwalla ihu sakamakon tsananin zafi da taji. Sannnan sarki larbusa ya dora tsinin wukar akan makogwaron laila yace, "mutum nawa ne basa nan daga cikin mutanen kauyenku a sa'adda muka far masu?" Jikin laila na karkarwa tace, mutum bakwai ne" Koda jin haka sai sarki larbusa ya bushe dariyar mugunta yai jifa da laila tamkar an jefar da tsumma ya dubi Sarkin yaki garbuza a fusace yace, maza ka sake diban dakaru dubu uku ku bazama neman wadanan ragowar jaruman biyu a duk inda suke. Lallai ku kawo mini su a macce ko a raye kafin sarki larbusa ya gama rufe bakinsa tuni Sarkin yaki garbuza ya ruga Izuwa inda giwarsa take yana mai yafito dakarunsa da hannu. Nan da nan dakaru dubu suka dane nasu giwayen suka rufa masa baya suna masu tsala gudu ba sassauci. ME ZAI FARU IDAN SU SARKIN YAKI GARBUZA SUKA HADU DASU HUMAIRU? " SHIN BURIN SARKI LARBUSA ZAI CIKA NA MALLAKAR NAHIYAR GABA DAYAN SANNNAN YA KARA GABA? TA YAYA SU HUMAIRU ZASU IYA KUBUTARDA 'YAN UWANSU MATA DA KANANAN YARA DAKE TSARE A HANNUN SU SARKI LARBUSA? Mu hadu a Dugunzuma littafi na biyu don jin cigaban wannan kasaitacen labari. DUGUNZUMA!-2 LITTAFI NA BIYU PART 1 LITTAFIN YAKI #NASEER SHEHU TEARLOW # ****** Lokacin da gari ya waye a birnin LURHAJ sai sarki ARYAN ya shirya taro na musamman kuma na gaggawa shida yan majalisarsa. Bayan kowa ya hallara a cikin taron sai ga wani sabon Al'amari wanda ya daurewa 'yan majalisar kai suka cika da tsananin mamaki. Ba wani abu bane face ganin shigowar sarki Aryan tare dasu jarumi Humairu su biyu dukkaninsu a cikin shigar yaki. Cikin firgici 'yan majalisar suka mike tsaye gaba dayansu suna masu matukar al'ajabi amma dayansu baice uffan ba har sarki ya zauna akan kujerarsa da ya saba zama. Humairu da Hashlar suka tsaya a bayan kujerar da sarki ya zauna. Sarki Aryan ya dubi yan majalisarsa gaba daya yai gyaran murya sannnan yace, "ya ku yan majalisata na sani cewa kun yi matukar mamaki bisa ganina a cikin shigar yaki da nayi da wadannan mafarauta. Koda sarki Aryan yazo nan a zancensa sai yai shiru, kawai sai ya dubi Hashlar. Nan take Hashlar ya warware yankakken hannunsa mai dungulmi kowa ya gani, Al'amarin da ya firgita yan majalisar kenan hankalinsu ya dugunzuma ainun fiye da farko sarki yace, "ya ku yan majalisata kuyi sani cewa masu iya magana sunce gani ya kori ji. Dukkaninku kun san cewa wadanan mafarauta na bayana da suka zo daga kauyen Garul Aswar sun kasance gawurtattun jarumai masu dakawa maza gumba a hannu kuma su bakwai ne. Dare da rana basa rabuwa amma a yanzu wani babban bala'i yazo mana wanda ya kashe sauran abokansu mutum biyar shine sanadin rashin hannu daya ga Hashlar kamar yadda ya nuna muku kuka gani. A yanzu haka an baje kauyensu na Garul Aswar an kashe dukkanin manyan mazajensu, an sace matayensu da kananan yaransu. Koda sarki

Chapter 3 of 9