Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
bishiyoyi daga can nesa suna gani. Sai da su sarki larbusa suka yi nisa da tafiya suka bace sannnan su Humairu suka fito daga cikin sakon da suka buya suka karewa sansanin kallo suka ga ragowar dakarun da aka bari sun kai su dari. Koda ganin haka sai hankalin Humairu ya dugunzuma suka rasa dabarar da zasu yi su shiga cikin sansanin bare har su binciko inda aka tsare iyayensu mata da kuma masoyansu su Laila. Cikin tsananin damuwa Hashlar ya dubi Humairu yace, ya kai abokina yanxu ta yaya zamu iya afkawa cikin wannan sansanin har mu ceto rayuwar iyayenmu da masoyanmu tunda gashi Kimanin dakaru dari ne ke zagaye da wajen. Idan muka ce zamu taresu gaba daya ba zamu iya hallakasu ba tunda mun jarraba dasu a baya mun gani. Da kyar da sidin goshi muka kashe irin su mutum uku. Koda jin haka sai Humairu yai shiru yana mai sunkui da kansa kasa kuma ya shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ya dago kai ya dubi Hashlar cikin murmushi yace, dabara ta fado mini muyi kokari mu shiga cikin sansanin cikin labiya da sumame mu kashe mutum biyu kacal daga cikin masu tsaro wadanda ke daf da farkon sansanin sai mu janye gawarsu mu boyeta sannnan mu cire tufafin jikinsu mu sanya. Sai dare yayi sannnan zamu koma cikin sansanin muci gaba da yi musu dauki dai,dai muna kashesu har sai mun karar dasu sannnan mu binciko inda mutanenmu suke mu kubatar da rayuwarsu. Koda Humairu yazo nan a zancensa sai Hashlar yai ajiyar zuciya sannnan yace "Na yarda da wannnan shawara taka, amma wai shin ka manta ne cewa wadanan mutane sun fimu tsawo da kauri sossai? " Ai koda mun sanya irin tufafin jikinsu suna ganin kankatarmu zasu gane cewa mu ba nasu bane. Humairu yace, "Na da hakan amma kada ka damu akwai dabarar da zanyi mana. Koda gama fadin Hakan sai Humairu ya zare wata sharbebiyar wuka a jikinsa sannnan ya kwanta a kasa da rub da ciki ya kama tafiya akan ciyawa kamar kadangare. Cikin hanzari shima Hashlar yayi koyi dashi. Haka dai Humairu da Hashlar suka ci gaba da tafiyar rub da ciki a cikin ciyawa har suka iso farkon sansanin inda wadansu dakaru biyu ke tsaye suna ta kallon gabas da yamma kudu da arewa suna muruzai,kuma sun dafe kubben takubbansu. Jira kawai suke suji motsi a wani wurin su kai hari, tsakaninnsu Humairu da wadanan dakaru biyu bai wuce taku uku ba. Kai inba don yanayin suturar dake jikinsu Humairu yazo daya da tarin ciyawar dake dajin ba da lallai sai dakarun sun gansu. Ko kyakkyawan numfashi su Humairu suka yi sai wadanan dakaru sunji. Koda Humairu yaga sun kusanto daf da dakarun biyu sai ya dubi Hashlar yayi masa inkiya. Nan take su biyun suka daka tsalle sama daga kwancen tamkar yan biririka suka dira akan wuyan dakarun suka shaftare makogwaronsu da wukake. Take dakarun suka zube kasa matattu Sai suka janye gawarwakin dakarun can baya nesa da sansanin sannnan suka cire tufafin jikinsu suka watsasu a wani rami. Kafin Humairu da Hashlar su sauya tufafin dakarun sai suka cusa ganye a cikin tufafin mai yawa ya kumburo sannnan suka sanya, sai gashi girman jikinsu ya karu ainun, ya Kai irin na dakarun, nan dai suka sake labewa a cikin duhuwar har sai da dare ya raba sannnan suka mike suka sami wadansu dogoyen itatuwa masu gwafa suka zurasu a cikin wadandunansu ya zamana cewa tafin kafarsu akan gwafar itatuwan suke suna takasu sai gashi sun kara tsawo kai kace tabbas sun kasance Samudawa irin dakarun sarki larbusa. A haka suka shiga cikin sansanin suka rinka yiwa dakarun kissan mummuke. A haka suka sami nasarar kashe Kimanin dakaru tamanin da biyar. Wadanda suka rage mutum goma sha biyar ne kacal. Abinda ya sa su Humairu basu sami Damar kashe mutum goma sha biyar din ba shine, sun ware kansu sun zauna a tsakiya sansanin sun kunna wuta sun kewaye wutar suna jin dumi suna hira. Har su Humairu suka gama kashe Dakaru tamanin da biyar din wadanan guda goma sha biyar basu san abinda ke faruwa ba, kuma shugaban dakarun wanda aka baiwa ajiyar sansanin a hannunsa yana cikin masu jin dumin... DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA BIYU PART 4 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ****** Abinda ya sa su Humairu basu sami Damar kashe mutum goma sha biyar din ba shine, sun ware kansu sun zauna a tsakiyar sansanin sun kunna wuta sun kewaye wutar suna jin dumi suna hira. Har su Humairu suka gama kashe dakaru tamanin da biyar din wadannan guda goma sha biyar basu san abinda ke faruwa ba kuma shugaban dakarun wanda aka baiwa ajiyar sansanin a hannunsa yana cikin masu jin dumin. Bayan su Humairu sun sami nasarar kashe wadanan dakaru sai suka hango inda aka zuba 'yan uwansu mata a cikin wani katon keji duk an zuba musu sarkoki a hannayensu da kafafunsu, gasu a kwance suna ta faman shara barci. Humairu ya kare musu kallo daya bayan daya gaba dayansu amma sai yaga babu buduwarsa laila a cikinsu sai mahaifiyarsa, mahaifiyar Hashlar budurwа Hashlar da sauran iyayen abokansu da kuma 'yan matan abokan nasu. Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsu kenan ya dubi Hashlar cikin tsananin damuwa yace, ya kai abokina kayi sani cewa idan muka ce sai mun ceci rayuwar gaba dayan matan nan asirinmu ne zai tonu a hallakamu. Na duba gaba dayan matan dake barci a cikin wancan keji babu masoyiyata laila a cikinsu. Abinda nake so da kai shine, ka lallaba cikin sanda kaje ka bude kejin ka kwance sarkokin da suka daure uwata da mahaifiyarka da kuma masoyiyarka hulaiza sannnan ka tashesu daga barci ba tare da sauran 'yan uwansu sunji ba. Ni kuma zan tafi neman masoyiyata a cikin wadancan tantunan. Mu hadu da kai a can karshen wannan sansanin inda dakarun nan suka daure giwayensu. Na gama akwai dawakai guda biyu a wajen sai mu gudu a kansu " Koda jin wannnan batu sai murna ta kama Hashlar, nan take ya durfafi inda wannan keji yake yana sanda shi kuma Humairu sai ya nufi inda sauran tantunan sansanin suke ya leka su daya bayan daya har ma ya wuce ta bayan wadanan dakaru goma sha biyar masu jin dumi basu ganshi ba. Yana zuwa tantin dake gaban wadanan dakaru ya leka cikinsa sai ya hango masoyiyarsa laila da matar sarki larbusa a zaune suna hira. Zuraiha ta dubi laila tace, yake wannnan budurwа kiyi sani cewa na ceci rayuwarki ne daga hannun mijina ba don komai ba sai domin ina kishin ya tara da wata 'ya mace in ba ni ba. Tuni na gane nufinsa cewar so yake ya tara dake. Na sani cewa keda yan uwanki duk kuna cikin bakin ciki marar misaltuwa gamida tsananin fargaba da tashin hankali domin an kashe dukkanin mazajenku, an kone kauyenku kurmus ya zama toka kuma yanzu gashi kun zamo bayinmu zaku ci gaba da yi mana bauta daga nan har Izuwa karshen rayuwarku. Zan iya kubatar da rayuwarki ke kadai ki gudu daga wannan nahiya gaba daya amma sai idan zaki daukar mini alkawari guda daya. " Koda jin wannnan batu sai mamaki ya kama laila ta dubi zuraiha tace, ke kuwa wane irin alkawari ne haka kike son na daukar miki?" Zuraiha tayi murmushi sannnan tace, idan mijina ya gama kama sauran tsirarun kasashen da ke wannan nahiya zai zamo DODON MAZA a duniya ya zamana cewa gaba dayan nahiyoyi suna tsoronsa. A sannnan ne duk abinda ya bukata daga kowacce nahiya dole ne a bashi don tsoron kada ya kai FARMAKI. A sannnan ne mulkinsa da dukiyarsa zasu bunkasa ya kai babban matsayin da ya dade yana mafarkin kaiwa. Yayi mini alkawari cewar idan ya kai wannan matsayi zai bani shugabancin kasuwanci nahiyar gaba daya domin ni banida burin da ya fi na zamo sauraniyar attajiran duniya a wannan zamani. A takaice ina son na tara dukiyar da babu mai yawanta. Banida tabbacin mijina zai iya cika mini wannan alkawari. Ni kuwa a cikin zuciyata na yanke hukuncin cewa idan har bai cika mini wannan alkawari ba na nakasashi ya zama kamar mace a cikin maza kuma yana ji yana gani zan gaje karagar mulkinsa nayi yadda duk naso. Bazan iya samun nasarar nakasta mijina ba ya rasa komai nasa face na mallaki jinin dan da matar sarki Aryan ta haifa ba ya cika shekara goma sha takwas a duniya. Na gano hakan ne a cikin binciken tsafin da nayi. Bukatata dake shine, bayan na tserar da rayuwarki nan da cikar shekara goma sha takwas ki samo mini jinin wannan yaro ki kawo mini. Koda mijina ya cika alkawarin dake tsakaninmu ba zan fasa ajiye jinin ba don babu mamaki a gaba ya tashi alkawarin namu." Lokacin da zuraiha tazo nan a zancenta sai laila tayi shiru tana tunani da nazari domin tasan cewa abinda zuraiha ke son tayi dai-dai yake da cin amanar matar sarki Aryan wato diban jinin danta ba tare da ta sani ba. Kafin laila ta gama tunani tace wani abu sai kawai suka ga Humairu tsulum! Ya shigo cikin tantin ya sawa zuraiha kaifin takobinsa a wuyanta sannnan yace, "Ba zan bar masoyiyata ta dauki irin wannnan alkawari ba na cin amana." Cikin tsananin farin ciki da mamaki laila ta mike tsaye zumbur zata taho wajen Humairu sai zuraiha ta daka mata tsawa ta tsaida ita sannnan ta juya ta dubi Humairu cikin murmushi ba tare da shakkar komai ba. Kawai sai ta danna kaifin takobin tasa akan wuyanta amma sai kaifin ya kasa yankata. Al'amarin da ya matukar razana Humairu da laila kenan. Zuraiha ta sake duban Humairu tayi murmushi tace, ba za ka iya kasheni ba kuma yanzu idan nayi maka ihu ragowar dakarun da baku kashe ba kai da abokinka Hashlar zasu rugo nan har su hallakaku. Idan har buduwarka ta daukar mini wannan alkawarin yanzu lallai zan fatar daku daga sansanin nan lafiya ba tare da dakaru sun ganku ba. Ku nake sauraro, yaya kuka gani? " Koda jin haka sai hankalin Humairu dana laila ya dugunzuma suka kama kallon juna kuma suka rasa abinda za su ce. Daga can sai laila ta dubi Humairu tace, ya kai masoyina kayi sani cewa bamu da wani sauran zabi face mu dauki wannan alkawari in ba haka ba kuwa ni da kai da Hashlar da iyayenku mata babu wanda zai tsira da rayuwarsa. Tabbas na san cewa abinda ya kawoku kenan domin ku tserar da rayuwarmu" Koda jin wannnan batu sai jikin Humairu yayi sanyi ya dubi laila yace, shikenan sai ki ki daukar mata alkawari ". Nan take laila tayi rantsuwa da darajar iyayenta cewar lallai bayan shekara goma sha takwas in dai tana raye zata nemi gimbiya zuraiha a duk inda take ta kawo ma ta jinin dan sarki Aryan Koda jin haka sai farin ciki ya lullube zuraiha ta dubi Humairu da laila tace, "ku saki jikinku ku biyoni a baya kawai " Koda gama fadin Hakan sai zuraiha ta mike tsaye ta fice daga cikin tantin, Cikin sauri Humairu da laila suka bita a baya. Ta gaban wadanan dakaru goma sha biyar masu jin dumi su zuraiha suka wuce amma dakarun basu gansu ba kuma basu ji motsinsu ba har zuraiha ta kaisu Izuwa bayan sansanin inda suka tarar da dawakai guda biyu, suna zuwa wajen suka ga Hashlar tare da mahaifiyarsa, mahaifiyar Humairu da kuma hulaiza. Ba tare da bata wani lokaci ba suka dora iyayensu mata akan doki daya, dayan dokin kuma suka dora laila da hulaiza suka yi gaba. A sannnan ne ya dubi zuraiha yayi mata godiya sannnan ya dada tabbatar mata da cewa lallai masoyiyarsa laila zata zamo mai cika alkawarin dake tsakaninsu. Nan take Humairu da Hashlar suka yiwa zuraiha sallama suka juya suka falfala da matsanancin gudu kafin cikar wani lokaci mai tsawo tuni sun riski iyayensu da 'yan matansu dake gudu bisa dawakai. **** A can kofar birnin LURHAJ kuwa, tuni su sarki Aryan sun gama shirin jiran isowar abokan gaba, wato su sarki larbusa amma su sarki larbusa basu iso ba sai da rana ta take. Tun daga nesa karar sawayen giwayensu ya tashi hankalin mutanen birnin LURHAJ. Su kansu su sarki Aryan da suka jeru a sahu sahu a gaban kofar birnin sai da suka firgita domin kasa ce ta kama rawa tamkar zata dare duk abinda ke kanta ya rufta ciki. Sa'adda rundunar su sarki Barham ta matso kusa suka yi arba da rundunar sarki Aryan suka ga suma suna da yawan gaske sai suka cika da murna domin sun san cewa yau takubbansu zasu sha jini su more. Cikin tsananin kaguwa dakarun sarki larbusa suka kama zare makamansu tun gabanin a basu umurni suka fara ihu da kururuwa. Shi kuwa sarki larbusa sai ya fara kyakyata dariyar mugunta musamman da ya yi arba da sarki Aryan ya kare masa kallo yaga girmansa bai wuce na dan tsako ba a gaban shirwa in aka dangantashi da nasa girman. Nan take sarki larbusa ya zare tasa takobin ya zunguri giwar da yake kai, ta fita da gudum ta tunkari sarki Aryan a Lokacin da sauran mukarrabansa suka rufa masa baya suna a guje bisa giwayensu. Koda ganin haka sai shima sarki Aryan ya zaburi dokinsa kuma ya zare takobinsa yayi kan sarki larbusa tare da tasa rundunar suna biye da shi. Koda rundunar biyu ta hadu sai aka ruguntsume da azababben yaki. Ihun mazaje, rurin giwaye da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, jini ya rinka fantsama da malala yana cukuduwa da kasa. Al'amarin su Humairu kuwa, koda suka shafe sa'a uku suna tafiya sai suka yada zango a bakin wata korama domin su huta. A sannnan ne mahaifiyar Humairu ta shiga basu labarin wata sarauniya wacce wani almajiri ya shigo fadarta yana bara. Take sarauniyar ta mike daga kan karagarta tazo wajen almajirin ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace, "zan baka abinci kaci ka koshi yanzu ya kai wannan tsoho, amma ba zaka iya biyana ba da komai domin ni bana bukatar abinci ko dukiya. Koda gama fadin Hakan sai sarauniya larbisa ta juya taja taja tsohon har Izuwa cikin gidan sarautar. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta mutanen gari da sauran masu fada aji saboda ita dai larbisa bata kasance mai tausayi da jin kan talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar da abin hannunta face akan bukatarta kawai. Lokacin da sarauniya larbisa ta kai wannan almajiri cikin babban falo na turakarta wanda girmansa ya kai na wani gida guda sai tsohon ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalle domin bai taba tsintar kansa a cikin waje mai ni'ima da daula ba irin wannnan. Gaba dayan falon a shimfide yake da wata irin darduma mai tsananin laushi da zarar ka taka darduma sai kaji kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi. Kujerun dake zagaye da falon gaba dayan an yi su ne da zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu da daya. A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun dawisu wanda akayi shi da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima ruwa na ta zuba ta cikin dawisun yana taruwa akan wani katon faranti na lu'u lu'u abin dai akwai ban sha'awa da ban al'ajabi. A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya wadanda suma da lu'u lu'u akayi su sai sheki da walwala suke. Duk inda almajirin ya duba a cikin falon sai yaga Kuyangi ne tsala tsala suna ta hidimar goge-goge da gyare-gyare. Tabbas wannan wuri ya cika aljannar duniya. Koda suka iso tsakiyar falon sai larbisa ta dubi almajirin tace, ya zauna bisa daya daga cikin kujerun falon. Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini ainun, yaga cewa shi dai bai kasance basarake ba ina shi ina zama akan irin wannnan kujera. Kawai sai ya zauna a kasa dirshan bisa wannan darduma mai taushi. Koda ganin haka sai sauraniya larbisa da kuyanginta suka bushe da dariya domin basu taba ganin wanda yai irin wannnan kauyancin ba. Sarauniya larbisa ta dubi shugabar kuyanginta wacce ake kira da suna HULAIRA tace da ita aje a kawowa bakona duk irin kalar abincin dake gidan nan. Hulaira tace,an gama ya shugabanta " Nan take Hulaira ta juya ta fice daga cikin falon, ita kuma sarauniya larbisa sai ta dubi almajirin tace, bayan ka huta zan dawo gareka da yamma domin mu yi 'yar hira kafin na sallameka ka tafi saboda kazo mini da bayani wanda ya jefani a cikin wasi wasi. Lallai ba zaka tafi ka barni a cikin duhu ba. Koda gama fadin Hakan sai sarauniya larbisa ta wuce Izuwa can cikin turakarta. Sai da ta jima tana tafiya sannnan ta kule almajirin ya daina hangota. Nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa a ransa, "wai shin Yaya cikin turakar sarauniya larbisa zata kasance a kyau da kawatuwa?"lallai dole ne ya ninka nan falon a komai. Jin kadan da tafiyar sarauniya larbisa sai ga wadansu Kuyangi dabam su goma sha biyu sun shigo cikin turakar kuma kowacce na dauke da katon farantin abinci. Akan kowanne faranti akwai abinci kala shida. Nan take kuyangin suka ajiyewa almajirin farantan abinci a gabansa suka juya suka fice. Ba tare da jiran komai ba almajirin ya bude kwanukan farantin farko dake gabansa, kawai sai ya kama cin abincin hannu baka hannu kwarya Cikin dakiku kadan ya cinye abincin dake cikin kwanuka shida gaba daya. Al'amarin da ya firgita gaba dayan kuyangin dake cikin falon kenan suka fara tunanin anya kuwa wannnan almajiri mutum ne? " A iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin mutumin da ya taba cinye koda kwano daya ba na abinci kasancewar kwanukan manya ne kuma cike suke taf da abinci. Sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye abincin kwano daya. Lokacin da almajirin ya gama da abincin farantin dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya gwamutsa abincin kwano shida akan farantin duka ya kama ci. Nan da nan ya karar da abincin ya janyo faranti na uku. koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin suka firgice suka ruga wajen falon a dimauce suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin. Abu dai kamar wasa sai da almajirin ya cinye gaba dayan abincin dake kan farantan goma sha biyu. A sannnan ne almajirin yai gyatsa. Dama an kawo masa ruwa inibi a cikin tambulan guda. Koda ya kafa tambulan din a bakinsa sai yayi masa kurba uku ya zukeshi duka. Shi kansa wannan tambulan din sau tari idan aka cikoshi da ruwan inibi komai yawan bakin da suka zo gida basa shanyeshi gaba daya sai kaga sun rage wani abu. Sa'adda kuyangin suka ga ya cinye gaba dayan wannan abincin kuma ya shanye ruwan inibin sai suka kara dimaucewa suka ruga Izuwa cikin gidan sarautar suna ihu da fadin cewa, tabbas aljani ne a cikin alon sarauniya ba mutum bane". Koda jin wannnan bushara sai dakarun tsaro na gidan sarautar suka zare takubbansu suka ruga Izuwa cikin falon sarauniya larbisa suka yiwa almajirin kawanya. Al'amarin da ya matukar baiwa almajirin mamaki kenan kuma ya tsoratashi domin bai san laifin da yayi ba har da a kazo aka yanyameshi haka.. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 2 PART 5 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ****** Sa'adda kuyangin suka ga almajirin ya cinye gaba dayan wannan abincin kuma ya shanye ruwan inibin sai suka kara dimaucewa suka ruga Izuwa cikin gidan sarautar suna ihu da fadin cewa, tabbas aljani ne a cikin falon sarauniya ba mutum bane ". Koda jin wannnan bushara sai dakarun tsaro na gidan sarautar suka zare takubbansu suka ruga Izuwa cikin falon sarauniya larbisa suka yiwa almajirin kawanya. Al'amarin da ya matukar baiwa almajirin mamaki kenan kuma ya tsoratashi domin bai san laifin da yayi ba har da aka zo aka yanyameshi haka. Ana cikin wannan hali ne labari ya riski sarauniya larbisa bisa abinda ke faruwa. Koda larbisa taji wannan abin al'ajabi sai itama ta cika da tsananin mamaki. Cikin hanzari ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta taho cikin falon nata. Da shigowarta cikin falon ta iske dakarunta sun yiwa almajirin kawanya suna tsuma ba tare da sun afka masa ba, ga dukkan alamu suma sun tsorata ne bisa ganin gagarumin aikin da yayi. Nan take sarauniya larbisa ta dakawa dakarunta tsawa suka jajja da baya har Ta hango almajirin zaune a tsakiyarsu yana kyarma cikin alamun tsananin tsoro har ya jike sharkaf da gumi. Al'amarin da ya baiwa larbisa tsananin mamaki kenan, nan take ta gamsu a cikin zuciyarta cewa lallai wannan almajiri ba aljani bane mutum ne domin inda aljani ne babu abinda zai sa ya tsorata bisa ganin dakarunta Izuwa kansa. Larbisa ta dubi dakarun nata da dukkan kuyangin dake cikin falon tace, kowa ya fita barsu " Cikin gaggawa suka bi wannan umurni, falon yayi tsit! Tamkar mutawa ce ta gifta. A wannan Lokaci ne larbisa ta taka taje har daf da almajirin ta zauna tana mai yi masa wani irin kallo na rashin yarda tace, Ya kai wannan tsoho bani labarinka ka sanar da ni komai bisa gaskiya, idan kuwa kayi mini karya bazaka fita daga nan ba a raye. Lokacin da almajirin yaji wannan tambaya sai yai ajiyar numfashi, nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya subuto masa sannnan ya dubi sarauniya larbisa yace, yake wannnan sarauniya kiyi sani cewa ni dai sunana HUZAILATUL MARWASU kuma na fito ne daga can kudancin duniya a wata kasa da ake kira madinatul sauwaba. Mahaifina ya kasance kusurgumin matsafi wanda yai nisan kwana a duniya domin sai da ya shekara Dari hudu da arba'in da uku a duniya sannnan ya mutu a Lokacin ina da shekara shida kacal a duniya, kuma nine dan auta kuma tun ina jariri uwata ta mutu ta barni. A wannan Lokaci ragowar yan uwana su hudu duk sun haura shekara goma sha. Daga mai shekara Ashirin sai mai Ashirin da 'ya'ya. Wadanan yayye nawa sun taso da hikima gamida sauran daukar ilimin tsafi a wajen ubanmu. Nan da nan kowannensu ya zamo shahararren boka, ni kuma sai na taso da dakikanci, duk abinda aka koya mini bana iya yi. Ko karanta mini dalasiman tsafi mahaifina yayi bana iya biyawa kamar yadda Ya biya haka kuma na kasance malalacin gaske bana iya yin aikin komai koda kuwa sharar gida ne. Bisa wannan daliline sauran 'yan uwana suka tsaneni. Bugu da kari, sai na taso da tsananin cin abinci mai yawan gaske, amma kuma idan naci na koshi ina iya yin kwana Ashirin da daya ban kara cin komai ba sai dai nasha ruwa. Wani abin mamaki kuma shine, a tsawon kwana Ashirin da dayan bana kawar da bukatar bawali ko bayan gida. Sai da ta kai cewa na cinye gaba dayan abincin dake gidanmu wanda mahaifinmu ya tanada a rumbu wanda a takaice zamu iya shekara goma muna amfani dashi. Duk wannnan halaiya tawa ba ta taba sa mahaifina ya tseneni ba face ma yana dada nuna mini soyayya da janyoni a jikinsa. Su kuwa 'yan uwan nawa sai haka yasa suka dada tsanata ya zamana cewa idan mahaifinmu ya aikemu cikin gari ko kasuwa sai su yi mini dukan tsiya akan hanya. Wani lokaci ma dukan kawo wuka suke yi mini har sai jama'ar gari sun kwaceni, sai dai a dawo dani gida jina-jina. Kafin a kawoni gida sai yan uwan nan nawa su rigani komawa suce da mahaifinmu sun hadu ne da abokan gabarmu 'ya'yan wani bokan garinmu an fafata yaki. Sau uku haka na faruwa, don haka sai mahaifin nawa ya hanani fita ko ina. Ya zamana cewa kullum muna tare dare da rana. Ko barci mahaifina zai yi sai ya tabbatar da cewa ina kwance akan kirjinsa. A kullum idan na tuna irin yanayin hallitar dana taso a ciki na dakikanci, lalaci da cin tsiya. Sai na kamu da tsananin bakin ciki. Nayi ta kuka. Shi kuwa mahaifin namu sai yayi ta rarrashina yana mai cewa, ya kai dana kayi sani cewa akwai ranar da zaka rabu da duk wadanan matsaloli,amma sai a bayan mutuwata bayan kayi wata doguwar tafiya. Lallai kafin mutuwata zan sanar da kai bangaren da zakaje a cikin duniya domin ka rabu da wannnan matsaloli. A sannnan ne zaka sami wata gagarumar daukaka irin wace ni kaina ban samu ba. Kayi hakuri da duk irin muzgunawar da 'yan uwanka za su yi maka daga nan har Izuwa ranar mutuwata domin hakurin naka shine zai kaika Izuwa kan tafarkin daukakarka. Na sani cewa yan uwanka basu da buri wanda yafi su hallakaka saboda ya zamana cewa ba zaka ka mallaki komai ba daga cikin dukiyar dana tara. Babu yadda basu yi ba don su hallakaka amma sun kasa domin ina baka kariya ta musamman. Duk abinda ke faruwa a yayin da kuka fita kasuwa ko cikin gari ina gani daga nan a cikin madubin tsafina. Duk sa'adda kaga jama'ar gari sun zo sun ceci ranka a hannun 'yan uwanka to ba mutanen gari bane ni ne na rikede Izuwa siffar mutane nazo muku. Wannan bakar wahalar da kake sha a hannunsu itace alamun samun daukakarka ta nan gaba. A duk sa'adda mahaifin namu yazo nan a zancensa sai na fashe da kuka nace,"ya kai abbana yanzu idan ka mutu waye zai iya ci gaba da ciyar dani alhalin yanzu ma kana ciyar dani ne da karfin sihirin tsafinka?" Idan baka nan ya za'a yi na tsira daga shairin 'yan uwana?" Da jin wannnan tambaya sai mahaifina yayi murmushi yace, "nayi maka alkawari ko a bayan raina baza ka fuskanci matsalar komai ba, kuma ba zaka sha wahala ba ta dogon lokaci." Haka dai mahaifina yaci gaba da rarrashina yana bani baki a duk sa'adda nake cikin damuwa ko tashin hankali. Wata rana da farkon dare sai mahaifina ya kamu da tsananin rashin Lafiya har ya kama kumallon jini. Nan fa muka hadu mu biyar din a kansa,a Lokacin da hankalina yayi matukar dugunzuma na fara kuka. Su kuwa sauran yan uwana ko kadan babu alamar wata damuwa a fuskarsu kawai sai suka kama yake. Mahaifin namu ya dubi sauran yan uwan nawa yace dasu, ku tafi Izuwa cikin daji ku nemo mini ganyen bishiyar suljara. Shine kadai abinda za'a jika mini na sami sauki". Koda jin wannnan batu sai hankalin yan uwan nawa ya tashi. Babban cikinsu ya dubi mahaifin namu cikin alamun matukar damuwa yace, ya kai. Abbanmu ka sani cewa ganyen bishiyar suljara yana da matukar wuyar samu a duk cikin dazuzzukan garin nan, zamu iya kwana a daji muna nemansa " Da jin haka sai mahaifinmu ya fusata yace, shin yanzu wahalar da zaku sha a daji tafi lafiyata muhimmanci kenan a wajenku? Idan har baza ku tafi neman Wannan ganye ba yanzu take zan lalata dukkan sirrin tsafin da kuka mallaka kuma na kone dukkan dukiyata dake cikin gidan nan. Koda jin wannnan batu sai yan uwan nawa suka juya suka fice daga cikin dakin suna guna-guni cikin fushi. Sai bayan yan uwana sun dade da tafiya daji sannnan mahaifina ya mike zaune da kyar sannnan ya jany@oni Izuwa jikinsa ya rungumeni akan kirjinsa. Kawai sai naji hawayen idanunsa na zuba akan fuskata. Cikin karfin hali ya bude baki yace, ya kai dana ka saurara da kyau ka natsu kaji jawabin da zanyi maka. Idan har ka rike abinda zan gaya maka yanzu lallai zaka sami daukakar da tafi tawa ma. Kayi sani cewa na aiki yan uwanka ne Izuwa can daji domin na sami damar da zan sanar da kai babban sirrin dana adana maka a cikin zuciyata tsawon shekara da shekaru. Ka sani cewa tsananin kaunarka da tausayinka da nake ji bisa yanayin hallitar daka kasance ne ya sa na adana maka wannan babban sirri. A yau kuma nan bada dadewa ba wa'adina zai cika na bar wannan duniya. Da zarar ka ga na mutu kayi sauri ka shiga cikin turakata ka dafa bakin akwatina na karfe da hannu na hagu, take akwatin zai bude. Zaka ga wata jakar fata a ciki sai ka dauki jakar ka ratayata a kafadarka ka fice daga cikin gidan nan. Kana fita zaka ga gidan nan ya nutse Izuwa cikin karkashin kasa ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen. Daga nan sai ka juya ka nausa yamma kayi ta tafiya har ka fita daga cikin garin nan ka nausa daji. Duk iya tsawon tafiyar da zaka yi kada kayi waige koda zaka ji sukuwar giwaye a bayanka. Duk inda ka gamu da mutum ko aljan kada kayi masa magana kuma idan aka yi maka magana kada amsa. Kana shiga garin ka bude wannan jaka taka zaka iske babu komai a cikinta face dinare mai yawan gaske sai ka nemi abinci mai yawa wanda zai isheka har ka koshi ka siya. Amma ka tabbatar da cewa a boye zaka cinye wannan abinci ba'a gaban jama'a ba. Kada ka kuskura ka kwana a wannan gari da zarar ka koshi sai kayi harama ka sayi doki ka hau ka cigaba da tafiya. Ina mai tabbatar maka da cewa sai ka shekara arba'in da biyar kana wannan tafiya kana ta keta dazuzzuka da birane. A sannnan ne zaka cika shekara hamsin da daya a duniya, kuma a wannan Lokaci ne guzurin dake cikin jakarka zai kare, ka iso wani babban Birni inda wata mashahuriyar sarauniya ke mulki. A sannnan ne yunwa zata gallabeka don haka ka nemi hanyar gidan sarauta. Kana zuwa fada ka wuce kai tsaye Izuwa gaban katangar mulki

Chapter 5 of 9