Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
cikinsa kuma Hashlar na tsaye akansa sai suka rabu da Humairu suka rugo da gudu Izuwa kan Hashlar. Kafin su iso tuni Hashlar ya zare takobin daga cikin dan uwansu ya fadi kasa matacce, Kawai sai ya taresu suka fara sabon gurmuzu, a wannan Lokaci ne Humairu ya kyalla ido ya hango irin mugun kisan wulakancin da aka yiwa yan uwansu, shima sai ya fashe da kuka. Cikin tsananin fusata ya mike tsaye zumbur duk da cewa akwai sara a jikinsa guda uku masu zubarda jini, kuma jini na yoyo a hancinsa da bakinsa, kawai sai ya dauki takobinsa ya ruga da ya kaiwa Hashlar dauki, wato ya tayashi yaki da samudawan ya zamana cewa biyu da biyu ake yakin. Hakika sau tari tsananin bakin ciki da asarar masoya tana sa mutum ya fusata ya sami karfin da shi kansa bai san yanada irinsa ba. Lokacin da aka fara wannan sabon bakin gurmuzu tsakanin Humairu, Hashlar da wadanan samudawan biyu sai labari yasha banbam domin abin mamaki ne ya faru... Duk da cewar ko a zahiri mutum ya kalli gurmuzun yasan cewa samudawan sun fisu karfi, girma da zafin nama amma sai gashi su Humairu sun zame musu alakakai sun kasa kaisu kasa. Babu ma wanda yafi bada mamaki face Hashlar wanda ya zama nakasasshe mai hannu daya. Da hannu daya ya cigaba da amfani da wannnan katuwar takobin suka yi ta taki da dayan basamuden. Shi kuwa Humairu da tasa takobin ya tari abokin gwamin nasa sai dai duk sa'adda ya sami nasarar sarar jikin basamuden sai yaga baya yi masa wawan raunin kirki saboda takobin tasa ta gama dukushewa. Duk sa'adda samudawan suka kawo ma su Humairu sara suka goce duk abinda takobinsu ta samu walau bishiya ko dutse sai dai kaga abin ya rabe gida biyu tamkar ansa wuka an raba tufa. Sai da aka shafe rabin sa'a ana ana wannan gurmuzu babban abin da ya dugunzuma hankalin Hashlar shine duk da cewa yana saran abokin gwamin nasa yana yi masa rauni kuma jini nata zuba a jikinsa amma yaki faduwa kasa, koyaushe ma kamar kara kuzari yake saboda tsananin fushi da taurin zuciya bisa ganin an kashe musu dan uwan guda daya. A bangaren Humairu da nasa abokin yakin ma abinda ke faruwa kenan, ana cikin haka ne abokin fadan Humairu ya doki kirjin Humairu da kafa. Saboda karfin dukan sai da Humairu yai baya a sama da gudu tamkar an cillashi daga cikin baka sannnan ya fado akan gawarwakin yan uwansu su Kaimur a matukar galabaice. Da kyar ya yunkura ya mike zaune, koda ya ga gawarwakin su Kaimur wadanda akayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu, kai dabam, hannaye da kafafu dabam dabam ga jini male male yayi wanka a cikinsa sai ya kwala ihu yai jifa da takobinsa kuma ya mike tsaye zumbur ya ruga da gudu Izuwa kan abokin gwamin nasa. Ai kuwa shima abokin gwamin nasa yana ganin haka sai ya yarda tasa takobin ya rugo da gudu Izuwa gareshi yana wani irin ihu wanda ka iya firgita mazaje dubu daruruwa a filin yaki su dimauce. Burin wannan basamuden shine su hada kirji shida Humairu domin ya tabbatar da cewa idan hakan ta faru sai kasusuwan kirjin Humairu sun kakkarye. Saura kiris su hadu kuwa sai Humairu yai tsalle a sama cikin shammace ya kama wuyan basamuden da kafafunsa biyu, a saman ya murde masa wuyan, take wuyan ya karye ya bayar da sautin karyewar kakakass! Nan take basamuden ya sulale kasa matacce karar karyewar wuyan tasa ce ta janyo hankalin dan uwansa ya juyo da baya a Lokacin da shima ya sami nasarar damkar wuyan Humairu ya daga shi sama da hannu daya ya shakeshi , sai gashi kafafun Humairu suna wutsil wutsil a sama kamar an shanya busasshen tsumma akan igiya iska na walagigi dashi, Idanun Humairu kuwa suka yi bulu-bulu kamar zasu fado kasa harma ya fara kakarin mutuwa, Koda wannan basamuden yaga dan uwansa ya fadi kasa matacce sai yai jifa da Humairu tamkar ya yarda jikakken tsumma sannnan ya kurma uban ihu ya daga takobinsa sama ya ruga da gudun tsiya a matukar fusace Izuwa kan Hashlar, Shi kansa Hashlar a wannan Lokaci ya karaya domin bai ma san abinda zai yi ya kare kansa ba, tunda gashi babu makami a hannunsa kuma kafin ya ruga inda ya yarda takobinsa tuni basamuden ya cimmasa don haka sai ya tsaya cak yana tunanin dabarar da zai yi. Ya rage saura taku daya jal basamuden ya cimmasa sai kawai yaga kibiya ta faso ta cikin kwayar Idon basamuden ya tsaya cak! A gabansa kamar an binne ice a cikin kasa. Take basamuden ya fadi kasa a sandare ya danneshi suka fadi kasa tare da kyar Hashlar yasa hannunsa mai kyau ya ture gawar basamuden daga kansa sannnan ya hango cewa ashe Humairu ne ya dauko kwari da bakan marigayi ILsam ya harbo basamuden. Humairu da Hashlar suka tsaya cak a nesa da juna suna kallon gawarwakin yan uwansu, Nan take suka fara zubarda hawaye, daga can kuma sai suka rugo da gudu suka rungume juna sannnan suka fashe da matsanancin kuka. Komai rashin imanin mutum idan dubesu a wannan Lokaci dole ne yaji tausayinsu musamman idan yayi la,akari da babbar asarar da suka yi ta abokansu mutum biyar wadanda suka shaku da su ainun tun kurciya kawo Izuwa girma. Bugu da kari gashi sun rasa iyayensu maza kuma an rabasu da iyayensu mata da kuma masoyansu wato yan matan da suke da burin su aura. DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA DAYA PART 3 LITTAFIN YAKI ******* REAL RAYYANU SAEED . Komai rashin imanin mutum idan ya dubesu a wannan Lokaci dole ne yaji tausayinsu musamman idan yayi la'akari da babbar asarar da suka yi ta abokansu mutum biyar wadanda suka shaku dasu ainun tun kuruciya kawo Izuwa girma. Bugu da kari gashi sun rasa iyayensu maza kuma an rabasu da iyayensu mata da kuma masoyansu wato yan matan da suke da burin su aura. Cikin gaggawa Humairu ya cire rigar jikinsa ya nannade dungulmin hannun Hashlar domin har yanzu bai daina zubarda jini ba sannnan suka mike da kyar suka tattaro sassan jikin abokansu suna ta kuka. Da kyar suka sami damar haka rami suka binne sassan jikin abokan nasu suka sa kabarin a gaba suka ci gaba da kuka har Izuwa tsawon sa'oi Bayan sun yi kuka mai yawa har sun gaji sai suka kurawa junansu idanu. Humairu ya dubi Hashlar yace, " ya kai abokina kuma dan uwana gudu daya wanda ya rage mini a duniya yanzu dai kaga irin bala'in da ya same mu mun rasa komai kuma mun rasa kowa yanzu menene abinda kake ganin ya kamacemu?" Koda jin wannnan tambaya sai hawaye sake zubowa Hashlar yace, " ya kai dan uwana ni a ganina rayuwa a duniya bata da wani amfani muddin babu masoyi Ka sani cewa babu wani abu da zai iya gusar mana da bakin ciki dake cikin zukatanmu bisa abinda muka rasa. Saboda haka ni ina ganin cewa abu mafi sauki a garemu shine mu kashe kanmu kawai domin mu tafi Izuwa ga inda masoyanmu suka tafi domin babu wani jin dadi da zamu samu anan gaba wanda zamu ji dadinsa. Wanne dadi ne zai dawo mana da abokanmu?" Wane dadi ne zai dawo mana da iyayenmu da kuma matan da muka kamu da tsananin soyayyarsu?" Wanne dadi ne zai dawo mana da ainihin kauyenmu na Garul Aswar da mutanen cikinsa? " Dukkan burinmu ya ruguje kuma dukkan farin cikinmu ya rushe." Sa'adda Humairu yaji wannan batu sai yaji ya kamu da tsananin bakin ciki fiye da koyaushe don haka bai san sa'adda ya sake fashewa da matsanancin kuka ba. Ba zato ba tsammani sai yaga Hashlar ya zaro wata karamar wuka a kugunsa ya daga sama zai kirba a cikinsa cikin bakin zafin nama Humairu yai wuf ya rike hannunsa yace, "Haba dan uwana ashe kamanta cewa har yanzu iyayenmu mata da yan matanmu na nan a raye a hannun wadanan samudawan azalumai?" Koda jin wannnan batu sai jikin Hashlar yayi sanyi yai jifa da wukar hannun nasa ya sake rungume Humairu, suka ci gaba da kuka tare. Tsawon yan dakiku suna manne da juna sannnan Hashlar ya janye jikinsa daga cikin na Humairu ya dubeshi yace, ka sani cewa ni da kai bamu isa muje mu tunkari wadanan mutane ba. Har mu iya kwato iyayenmu da yan matanmu, tunda gashi da kyar da sidin goshi muka kashe irin su mutum uku, idan har kuwa baza mu iya kwato su ba menene amfanin rayuwarmu a doron kasa?" Da jin wannnan tambaya sai Humairu ya jinjina kai yace, hakika ni da kai ba zamu iya wannan aiki ba.amma ka tuna cewa idan har da rai da akwai rabo. Har abada hikima da basira basu karewa ga dan adam. Ni a ganina zamu iya karbo jama'armu amma bata hanyar tarar wadanan mutane gaba da gaba ba. Kodai mu nemi taimakon wadansu al'ummar daga can wata nahiyar dabam ko kuma mubi sawunsu ba tare da sun sani ba har musan dabarar da mukayi muka sato jama'ar tamu a cikinsu. Wannnan shine kadai abinda zamu iya yi a yanzu. Lokacin da Hashlar yaji wannan shawara da Humairu ya kawo sai yai shiru yana nazarinta a cikin zuciyarsa har Izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can sai ya dago kai ya dubeshi yace, ka bani kwana biyu nayi tunani akan wannnan shawara da ka kawo. Amma yanxu ya zama wajibi mu tashi mubar wannan wuri domin idan yan uwan wadanan samudawan suka ji shiru, dole ne su aiko wadansu jama'ar tasu, suzo suga abinda ya faru. Humairu ya gyada kai yace, tabbas maganarka gaskiya ce, amma a yanzu ina yakama mu doso?" Hashlar yace, ai babu inda ya kamata muje face babban Birninmu na LURHAJ domin mu sanarda sarki ARYAN abinda ya faru a kauyenmu saboda asan matakin da za'a dauka tun karfinsa wadanan mutanen su isa can. Ni ina ganin cewa ma acan ya kamata mu tsaya a yaki wadanan mutane tare damu domin mu dauki fansa akansu. Koda jin wannnan batu sai Humairu ya kada kai yace, " naga alama kana wasa da Al'amarin wadanan bakin samudawan da baro a wannan nahiya tamu. Shin ka manta ne da bayanin da wannnan mutum yayi mana a bakin kogi? Cewa yayi fa mutanen yawansu ya wuce kima bai san adadinsu ba. Kana ganin yadda uku daga cikinsu suka kashe mana abokanmu biyar muma da kyar muka tsira daga hannunsu. Ina mai tabbatar maka da cewa koda basu fi su dubu biyu ba zasu iya hallaka gaba dayan dakarun sarki ARYAN. Batun ayi fito na fito da wadanan mutane bai taso ba. Kuma akwai bukatar muga adadinsu da idanunmu sai dai a yanzu abu mafi sauki shine mu ruga Izuwa birnin LURHAJ mu sanarda sarki ARYAN abinda ake ciki. Yanzu dai tunda wadanan abokan gaba gabas suka nufa mu sai mubi ta kudu muyi shatale- tale mu rigasu zuwa birnin LURHAJ. Koda jin wannnan batu sai Hashlar ya gyada kai yace, tabbas na yarda da wannnan shawara taka dari bisa dari. Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa suka zauna Humairu Humairu ya kwance raunin Hashlar wato dungulmin hannunsa ya wankeshi da ruwa sannnan ya debo garin magani ya barbada akansa, sai jini ya tsaya cak ya daina diga. Cikin sauri suka kama dawakansu suka hau suka zaburesu suka nufi bangaren kudu suna waigen kabarin da suka binne abokansu suna zubda hawaye. * * * A can bangaren tawagar wadanan samudawan mutane kuwa, wadanda adadinnsu ya haura miliyan uku da dubu dari hudu, sun ci gaba da tafiya ne basu yada zango ba sai bayan sa'a biyar sa'adda yammaci yayi sossai sannnan sarkinsu wani mummunan garjejen kato wanda ake kira LABARUSA ya tsaida giwarsa ta tsaya cak! Sannnan ya daga hannu sama yana mai bada umurnin kowa ya tsaya. Ai kuwa nan take kowa ya tsaya, Dakaru suka sauko kan giwayensu. Dama fursunonin da aka kamo an daure kafafunsu da hannayensu da sarkoki, babu yadda dayansu zai iya guduwa kuma acikin wani katon keji aka durasu wanda akayi masa tayoyi na karfe guda Dari da Ashirin a kasansa, giwayene suke jan wannan keji ana tafiya dashi. Koda sarki ya lura da cewa wadanan fursunoni da aka kamo sun galabaita ainun kuma yunwa da kishirwa sun addabesu sai ya bushe da dariyar mugunta, nan take ya dubi badakare wanda shine Sarkin yakinsa ana kiransa da suna GARBUZA yace dashi, A bude wadanan fursunoni a kaisu bakin waccan koramar su sha ruwa a basu abinci suci domin Banason daya daga cikinsu ya mutu kasan irin aikin da nake son suyi min nan gaba. Nan take garbuza ya bada umurni aka bude wannan katon keji aka rinka fito da fursunonin ciki wadanda dukkaninsu mata ne, matasa da tsofaffi sai kuma kananan yara. Duk wanda ka kalla a cikinsu sai kaga yana zubarda hawaye saboda tunanin daginsa da ys rasa. Nan dai aka tusa Izuwa bakin wannan korama wanda duk yai gardama sai a zabga masa wata katuwar bulala mai fasa fatar jiki don haka bisa dole suka bi umurni. Daga cikin wadanan fursunoni akwai iyayen sh jarumi Humairu da kuma yan matansu guda bakwai wadanda zasu Aura. Wadanan yan matan bakwai duk sun kasance kyawawan gaske amma daya daga cikinsu ta fita zakka domin duk ta fisu kyau nesa ba kusa ba kuma ana kiranta sa suna LAILA. Laila itace budurwа Humairu, mai biye ta a kyau itace HULAIZA itama kuma budurwа Hashlar ce A koyaushe wadanan yan mstan bakwai suna tare da juna basu rabuwa kamar yadda samarinsu suka kasance suma kawayen juna ne tun kuruciya. Lokacin da aka kai su Laila bakin korama sai suka jeru su bakwan suka tsugunna suna shan ruwan, a wannan Lokaci ne huzaila ta dubi laila Lokacin da idanunta suka ciko da kwalla tace, "ya ke kawata ki sani cewa ina cikin alamun fargaba da tashin hankali domin inaji a jikina cewar wadanan dakaru uku da aka tura su koma can kauyenmu lallai sun sadu da masoyanmu sun kashesu saboda haka ni yanzu banga amfanin rayuwata ba muddin babu masoyina Hashlar. *****naku Smart Rayyanu DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA DAYA PART 4 LITTAFIN YAKI ****** Lokacin da aka kai su Laila bakin korama sai suka jeru su bakwan suka tsugunna suna shan ruwan, a wannan Lokaci ne huzaila ta dubi laila Lokacin da idanunta suka ciko da kwalla tace, "ya ke kawata ki sani cewa ina cikin alamun fargaba da tashin hankali domin inaji a jikina cewar wadanan dakaru uku da aka tura su koma can kauyenmu lallai sun sadu da masoyanmu sun kashesu saboda haka ni yanzu banga amfanin rayuwata ba muddin babu masoyina Hashlar. Abinda na yanke hukunci shine zan fada karkashin wannan korama na kashe kaina. Gama fadin Hakan keda wuya sai hulaiza ta yunkura zata yi nutso Izuwa cikin koramar. caraf! Sai laila ta riketa tace, "saboda me zaki hallaka kanki alhalin baki da tabbacin cewa masoyinki ya mutu "? Ki tuna cewa dakarun da aka tura su kashesu har yanzu fa basu dawo ba, babu mamaki masoyanmu ne suka sami nasara akansu. Ni na sani cewa masoyanmu mazaje ne wadanda mutuwarsu ba karamin bala'i bane domin sun cika jaruman gaske, koda kuwa zasu mutu sai sunyi mummunan barna. Ni ina ji a jikina cewar har yanzu masoyina Humairu yana nan a raye kuma komai rintsi da tsanani sai ya biyo sawu ya cecemu ni da mahaifiyarsa. Saboda me ke hulaiza ba kya jin wannnan abu da nake ji?" Koda jin wannnan batu sai jikin hulaiza yayi sanyi ta fasa kokarin hallaka kanta, laila ta dubi dukkan yan matan nan tace,Abin da nake so da ku shine mu saurara Izuwa wani lokaci tukunna domin mu tabbatar da halin da masoyanmu ke ciki. Idan har mun tabbatar da cewa suna nan a raye basu mutu ba to muma zamuyi kokarin mu gudu. " Cikin firgici hulaiza ta dubi laila tace, "ta yaya kike zaton zamu iya guduwa daga hannun wadanan samudawan mutane?" Ta yaya zamu iya kwance wannan sarka dake daure da hannayenmu da kafafunmu? " Kafin hulaiza ta gama rufe bakinta tuni an gabza mata naushi a fuska, take ta kife a cikin koramar jini na zuba ta hancinta da bakinta, cikin sauri laila ta dago ta sama, ba wani bane ya naushi hulaiza ba face sarki labarusa. Fuskarsa a murtuke ya dubi hulaiza sannnan ya dubi laila a fusace yace, na fahimci cewa kune masu hikima da basira a cikin dukkanin fursunonin nan kuma kuna yunkurin guduwa. To ku sani cewa duk wadda tayi yunkurin guduwa a cikinku sai nayi mata mugun wulakanci sannnan nayi mata kissan gilla. Koda gama fadin Hakan sai sarki labarusa ya mike tsaye, har ya juya zai tafi sai ya sake waigowa ya dubesu gaba daya yace, " naji kuna mafarkin cewa masoyanku suna nan har yanzu a raye, ina tabbatar maku da cewa dayansu baya numfashi a doron kasa. Zamu tsaya anan mu yada zango domin mu jira dawowar dakaruna uku dana tura su kashe masoyan naku domin kuga kawunansu da idanunku ". Caraf! Sai laila ta tari numfashin sarki labarusa ba tare da jin tsoro ko fargabar komai ba tace, " nasan ko su waye masoyanmu. Ina mai tabbatar maka da cewa mutuwarsu ba karamin aiki bane, Idan kuwa har sun mutu tabbas suma yaran naka sai sun mutu, Kayi nazari yaran naka sun dade basu dawo ba, Menene ya hanasu dawowar? " Ba komai bane face mutuwa?" Koda jin wannnan batu sai sarki labarusa ya fusata ainun, jikinsa ya kama tsuma, wani irin zazzafan gumi ya fara karyo masa. Gaba daya fursunonin dake wajen sai da suka firgita ainun. Kai ba ma fursunonin ba hatta sauran dakarun sarki labarusa sun tsorata saboda sun san cewa duk sa'adda labarusa yayi irin wannnan fusata wanda ma bai san hawa ba bare sauka sai kashin kaji ya shafeshi. Ita kuwa laila ko alamar razana babu a tare da ita, "kawai ma sai ta juyo ta fuskanci sarki labarusa ta tsaya a gabansa tamkar an ajiye kyanwa a gaban kura, tace, idan maganata ta bata maka rai ka kasheni ko ka huce takaici amma ka sani cewa duk ranar da masoyina yayi arba da kai sunanka gawa. Sa'adda laila tazo nan a zancenta sai kawai akaji sarki labarusa ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya Al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki kenan, daga can sai ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa yadda tsawonsa yazo dai-dai dana laila ya zamana cewa suna daf da juna har tana jin hucin numfashinsa tamkar gurnanin zaki yace, "ke yarinya kiyi sani cewa a cikin duniуаr nan kaf babu wani mahaluki mai karfin damtsena da iya yakina in dai ya kasance bil'adama. Ta yaya kike tsammani cewa masoyinki zai iya yi mini wani abu? " A rayuwata babu abinda na tsana sama da zama babu abokin gaba. Abinda zai hanani na kasheki yanzu shine, ina son na kama masoyinki a hannuna nayi masa kisan wulakanci da karfin damtse a gaban idanunki. " Laila tayi murmushi tace, abinda ka fadi dai-dai yake da mafarki, kuma mafarkin da ba zai taba tabbata ba. Kafin laila ta gama rufe bakinta tuni Sarkin yaki garbuza ya maketa ta fadi kasa sumammiya, kawai sai ya zare takobinsa zai datsata gida biyu caraf sai sai sarki labarusa ya cafi hannunsa yace dashi, saboda me kake son kasheta?" .. A kwashe su gaba daya daga cikin koramar nan a mayar dasu cikin keji amma ita wannan marar kunya a kaita cikin tantina a daureta. Kai Sarkin yaki ka debi dakaru hamsin ku juya da baya kuje wannan gari da muka baro kuga abinda ya faru tunda mun tura mutanenmu su uku har yanzu basu dawo ba " Sarkin yaki ya risina yace an gama ya shugabana. Nan take aka tusa keyarsu hulaiza Izuwa cikin kejin su aka kullesu ita kuwa laila a sume wani badakare ya kwanceta daga cikin sarka yan uwanta ya sabata a kafadarsa ya kaita tantin sarki labarusa ya daureta a jikin dirka. A wannan Lokaci babu abinda zai baiwa mutum tausayi face ganin yadda aka gwamutsa kananan yara, wato fursunonin da aka kamo a cikin keji wani kan wani, sai kuka suke saboda matsuwa ga kuma yunwa domin abinci da aka basu suka ci basu koshi ba. Da yawansu ma iyayensu mata ne suka rinka jefa musu nasu abinci da aka basu su suka hakura. * * * Al'amarin su Humairu da Hashlar kuwa, Lokacin da suka kama hanya suka durfafi birnin LURHAJ sai suka yi ta falfala gudu kamar zasu tashi sama. Abinka da wadanda suka saba da gudun, sai da suka shafe sa'a bakwai cif suna gudu basu huta ba. Ko kishirwa ce ta kamasu sai dai kaga suna gudun suna daga battar ruwa suna kwankwada. Bayan cikar sa'a bakwai dinne suka iso birnin ARYAN. Da zuwansu kofar birnin suka sha mamaki domin sun iske masu gadin a zaune cikin farin ciki da nishadi sun gaiyato wani makidi daga cikin gari ya baje kolinsa har wadansu karuwai su uku sunyi shigar banza suna tika rawa su kuwa masu gadin sai shan giya suke suna ta kyalkyala dariya. Koda masu gadin suka hango mutum biyu a guje sun durfafo birnin sai suka mike tsaye zumbur! Shi makadin ya daina kidan, karuwan suka kame. Cikin hanzari masu gadin suka zare makamansu suna jiran ko ta kwana Koda su Humairu suka kara matsowa kusa sai masu gadin suka shaidasu, don haka sai suka mayar da takubbansu cikin kufe. Da karasowarsu sai shugaban masu ya taresu yace, lale marhaban da manyan ya'yan sarakunan farauta, shin lafiya kuwa na ganku a sukwane haka? " Humairu ya budi a Lokacin da yake faman haki yace, Babu lafiya, kowa ya shigo ciki ku rufe kofa akwai babbar masifa tafe! Ba tare da gardamar komai ba masu gadin suka bi wannan umurni jikinsu na rawa. Kai tsaye Sarkin kofa ya yiwa su Humairu jagora Izuwa fadar sarki ARYAN. Fadace kasaitacciya wadda akayi mata ado na gani da fada da kayan alatu dangin su zinare, lu'u lu'u da sauransu. Girman fadar ya wuce karamin misali sai abinda ido ya gani. Sarki ARYAN saurayi ne matashi kuma kyakkyawan gaske. Sannnan ya kasance gawurtaccen jarumi wanda bai san tsoro ba kuma gwarzo ne mai dakawa maza gumba a hannu. Yana da wata kyakkyawar mace guda daya mai tsananin kyau ana kiranta da suna LUSHIRAT na dauke da tsohon cikin haihuwa yau ko gobe. Tsananin farin ciki dake tare da sarki ARYAN da matarsa lushirat a halin yanxu bisa ganin tana daf da samun haihuwa ya wuce misali domin basu da wani buri a duniya wanda yafi na ganin sun haifi magajinsu. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin sun shekara goma sha uku da yin aure ko batan wata lushirat bata taba yiba. Babu irin neman maganin da basu yi ba kasa-kasa nahiya-nahiya amma shiru sai a wannan shekara ne a wata na biyu rana daya aka wayi gari akaga lushirat ta tashi da laulayin ciki. Yanzu tsawon wata takwas kenan da samun juna biyu amma dai-dai da rana daya ko dakika daya sarki ARYAN bai yarda ya rabu da lushirat ba saboda farin ciki da kansa yake kula da lafiyarta kuma ko ciwon kai yaji ta ambata sai ya tara dukkan likitocin garin a kanta. Yauma kamar kullum sarki ARYAN na zaune a fadarsa bisa karagar mulki, gimbiya lushirat na zaune a damansa ya rike hannunta suna duban juna cikin murmushi. Makada da mawaka suna debe musu kewa. A wannan Lokaci fadar ta cika makil ga fadawa da sauran mutanen gari har da ma baki daga ketaren kauyuka da birane saboda rana ce ta kasuwar birnin. Kwatsam! Sai akaji an busa algaita alamar cewa baki sun shigo fada. Nan take jama'a suka dare suka samar da hanya a tsakiyar fadar kowa ya juyo ya dubi kofar shigowa kuma akayi tsit kamar mutuwa ta gifta. Sarkin kofa ne tare da Humairu da Hashlar suka shigo. Koda hangosu sai sarki ARYAN ya mike tsaye ya sauko daga kan karagarsa ta mulki ya taho garesu, Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba'a taba ganin sarki ARYAN ya sauko daga kan karagar mulkinsa ba domin ya tarbi wani bako ba, Komai muhimmancinsa saboda izzа da jin kai sakamakon girman kasarsa,karfin mulki da dimbin dukiyar da ya mallaka. Abinda ya kara daurewa mutane kai shine, bakin ma da sukazo ba wadansu masu muhimmanci bane, kauyawa ne kuma mafarauta wadanda basa zuwa fada sai sau daya a kowanne wata domin su kawowa sarki kyautar abubuwan gwaninta da suka farauto a daji don nuna jarumtakarsu. Yanzu gashi mafarauta sunzo a farkon wata kuma su bakwai ne suka saba zuwa amma yanzu su biyu ne jal. Su kansu su Humairu sunyi matukar mamaki da suka ga sarki ARYAN ya sauko daga kan karagarsa ya tarbesu da kansa. Cikin hanzari sarki ARYAN ya riski su Humairu ya kama hannun Humairu fuskarsa cike da annuri tamkar wanda yaga dan uwansa na jini wanda suka dade basu sadu ba. Kawai sai ya rungume Humairu yayi masa rada a kunne yace, duk sakon da kazo dashi kar ka fadeshi anan fada sai mun Kebe." Koda gama fadin Hakan sai sarki ya kama hannun Humairu dana Hashlar ya jasu Izuwa can inda karagar mulki take. Maimakon su zauna sai ya dubi fadawansa yace, zanje na gana da bakina don haka na sallami kowa. Nan take yan majalisarsa suka mike tsaye suka fara fita daga fadar kowannensu yana mamakin dalilin da yasa sarki ya tashi fada a yanzu. Sarki ARYAN ya dubi wani hadiminsa yace, a kai Humairu da dan uwansa masauki abasu abinci suci su huta tukunna. Nan take hadimin ya jasu Humairu suka fice daga fadar. Humairu na waigen sarki ARYAN kamar yaki bin hadimin, kai da gani kasan cewa hankalinsa a tashe yake kuma lallai akwai sakon gaggawa a bakinsa wanda yake son ya isar ga sarki. Shi kuwa sarki ARYAN sai yaje ya kama gimbiya lushirat ya taimaka mata ta mike tsaye da kyar saboda nauyin jikinta,ta dora hannunta bisa kafadarsa suka tafi Izuwa cikin gidan sarautar. Lokacin da aka kai su Humairu dakin bakin aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma sai suka kasa cin komai suka yi tagumi domin su kadai ne suka san irin tashin hankalin da suke ciki. Ai kuwa suna cikin wannan hali ne kofar dakin ta Bude sai ga sarki ARYAN da kansa ya shigo. Humairu da Hashlar suka mike tsaye don girmamawa a gareshi a Lokacin da suka ga alamun tsananin tashin hankali karara akan fuskarsa, sarki ARYAN janyo kofar dakin da hannunsa ya rufeta don kada wani yaji abinda zasu tattauna sannnan ya dubesu daya bayan daya yace, nasan sakon da kuke dauke dashi. Tabbas kuna dauke da mummunan labari ne na baiyanar bakin samudawa a wannan nahiya tamu wadanda suka je kauyenku suka kashe dukkan mazajenku kuma suka kame matayenku Daga baya kun dawo daga farauta kuka iske wannan bala'in Ihun da kuka yine mutanen suka jiyo aka turo mutum uku kacal daga cikinsu kukayi babakin yaki dasu har suka kashe yan uwanku mutum biyar. Da kyar da sidin goshi kai Humairu da Hashlar kuka kashe wadanan mutane uku. Haka ne ko ba haka bane?" Cikin tsananin mamaki kuma cikin hadin baki Humairu da Hashlar suka ce, yaya akayi kasan wannan Al'amari? DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA DAYA PART 5 LITTAFIN YAKI NASEER SHEHU TEARLOW ******* sarki ARYAN janyo kofar dakin da hannunsa ya rufeta don kada wani yaji abinda zasu tattauna sannnan ya dubesu daya bayan daya yace, nasan sakon da kuke dauke dashi. Tabbas kuna dauke da mummunan labari ne na baiyanar bakin samudawa a wannan nahiya tamu wadanda suka je kauyenku suka kashe dukkan mazajenku kuma suka kame matayenku Daga baya kun dawo daga farauta kuka iske wannan bala'in Ihun da kuka yine mutanen suka jiyo aka turo mutum uku kacal daga cikinsu kukayi babakin yaki dasu har suka kashe yan uwanku mutum biyar. Da kyar da sidin goshi kai Humairu da Hashlar kuka kashe wadanan mutane uku. Haka ne ko ba haka bane?" Cikin tsananin mamaki kuma cikin hadin baki Humairu da Hashlar suka ce, yaya akayi kasan wannan Al'amari? Sarki ARYAN ya sami wuri ya zauna sannnan yayi ajiyar zuciya yace, "Duk na ga wannan Al'amarin ne a cikin madubin Bokana KURHAS IBINI LAMRAS a yau din nan da safe. Yanzu haka boko kurhas ya hada nasa-inasa ya gudu ya bar wannan nahiya tamu gaba daya domin yace wadanan mutane da suka zo sai sun shafe gaba dayan kasashen dake wannan nahiya tamu. Yaya za'a yi na gudu na bar jama'ata kasata da dukiyata?" Nan ce mahaifata babu abinda zai rabani da ita face mutuwa. Bana son jini na ya zuba a ko ina face akan kasar mahaifata. Na yarda zan mutu amma ba zan mutu rago ba, kuma sai dai na mutu akan tafarkin tsare mutuncina dana jama'ata. idan naso zan iya guduwa nida matata muje muyi sabuwar rayuwa a wata nahiya dabam. Amma ai abin kunya ne ace ni sarki mai cikakken iko kamata ace na gudu na bar jama'ata da mulkina. Ba zan iya guduwa ba na

Chapter 2 of 9