Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA DAYA PART 1 LITTAFIN YAKI typing NASEER SHEhu post real prince rayyan ******* Kai da ganinsu kaga sadaukai, musamman idan kayi la'akari da yanayin siffofin jikinsu, Tafe suke a cikin faffadan dajin a cikin shiga irin ta kwararrun mafarauta wacce ke nuna cewa sun san sirrin daji matuka,kuma babu alamar tsoro ko shakkar komai a tare dasu. Komai dakewar mutum idan ya tsinci kansa a cikin irin wannan mugun daji da zaratan samarin su bakwai ke kutsawa dole ne ya razana saboda kwarjininsu da irin yanayin bishiyoyi,duwatsu da koramu dake cikinsa, da kuma tsananin shirunsa,domin kunne baya jin sautin komai face na kukan tsuntsaye, sai kuma mugun gurnani na manyan dabbobin daji. Wadanan ZARATAN SADAUKAI sun fito ne daga wani karamin kauye da ake kira GARUL ASWAR wanda ke karkashin birnin LURHAJ inda sarki ARYAN ke mulki, ZARATAN SADAUKAN bakwai sun hada da Humairu, ILsam, Zuraif, Hashim, Sahal, Kaimur,da Hashlar. Dukkaninsu sun shaku da juna saboda tun suna yara basu taba rabuwa ba, bisa wannan dalili ne suka dauki alkawari komai na rayuwa tare zasu yi, hatta Aure kuwa, ko farauta suka fita idan ma mutum daya ne ya sami nasarar kamo dabba to fa sai dai a raba dabba gida bakwai dai-dai, idan kuma kowa ya kamo tasa bazai tafi da ita gida ba sai dai a tara duk dabbobin a waje daya a rabasu dai-dai kowa ya debi rabonsa Sai da su Humairu suka shafe sa'a daya da rabi suna gudu a cikin daji suna bin wata Barewa,amma sun kasa cimmata, ya zamana cewa su basu gaji da gudu ba, ita kuma barewar ta kasa samun wajen tsira. Shi dai Humairu yafi kowa gudu a cikinsu, don haka shine akan gaba, ILsam yafi kowa iya harbi da baka,kuma shine na biyu a iya gudu,don haka duk inda Humairu ya dauke kafarsa anan yake saka tasa. Zuraif shine yafi kowa iya tsalle da hawa kan bishiyoyi tamkar Danbiri. Hashim shine mafi sanin sawun kowacce irin dabba, shi kuma Sahal Allah ya hore masa jin sauti a kunnensa, domin yana iya jiyo sautin sawun zaki ko giwa daga nisan tafiyar zango, kuma a duk inda dabba tayi kuka zai iya fadin nisan tazarar dake tsakaninnsu da ita. Kaimur Allah ya bashi tsananin karfin kirji, domin ko da zaki ya hada kirji sai dai zakin ya fadi, shi kuwa a tsaye daram zaka ganshi, kai hatta manyan bishiyoyi idan Kaimur ya fusata yana iya bangajesu da kirjinsa kaga suna tuttukowa daga cikin kasa har jijiyoyinsu suna zubewa kasa. Shi kuwa Hashlar Allah ya hore masa iya sarrafa takobi, komai yawan dakaru ko dabbobi in dai yana rike da takobi babu abinda zai sameshi sai ya tarwatsasu ya kashe na kashewa - Masu Gudu Sun Gudu. Bayan su Humairu sun kasa kama wannan barewa sai ILsam ya fusata ya ruga Izuwa kan wani dutse mai tsawo ya tsaya cak! Sannnan ya dana kwari akan bakansa ya saita wannan barewa duk da cewa tana gudu kuma ta bashi tazara mai yawa saura kiris ma ta kule sai ya tabe bakansa iya karfinsa ya saki harbi, take kibiyar taje ta soki barewar a kuibinta cikinta na hagu ta bullo ta kuibin dama. Saboda karfin harbin sai da barewar tayi sama ta cake a jikin bishiya ko surawa bata yi ba , ta zama gawa. Koda su Humairu suka ga wannan gagarumar bajinta da ILsam yayi sai suka hau shewa suna yi masa tafi da jinjina, nan take suka sami inuwa suka zauna sannnan suka fede barewar suka tsireta a jikin ice mai gwafa suka hada wuta suka fara gasata domin suci. Idan suka gama sai su kara gaba su koma gida, dama haka ka'idar farautarsu take, wato kullum idan suka fito sau daya suke aiki, ma'ana duk abinda suka fara arangama dashi to fa in dai sun kamashi bazasu sake neman wani dabam ba. Bayan barewar ta gasu sunci sun koshi sai kuma kishirwa ta addabesu, gashi baduda sauran ruwa a cikin buttocinsu duk sun shanye, haka kuma tun safe da suka shigo dajin rana ta fito da wuri ta kwalle kuma sun dade da yawa suna falfala azababben gudun da suka sha Lokacin da suke kokarin kama wannan barewa. Nan take suka yanke shawarar tafiya neman ruwa,da yake sun san dajin sossai sai suka durfafi wata hanya wacce zata kaisu Izuwa ga wani rafi wanda ake kira HUZURA sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna tafiya sannnan suka fara hango rafin huxura. Tun daga nesa suka hango wani abu kamar mutum kwance a gabar rafin tamkar gawa, domin ko motsi bayayi Cikin hanzari su duka suka ruga Izuwa bakin rafin, da zuwansu sai suka iske ashe kuwa mutum ne a kwance cikin jini kaca-kaca ba kyan gani mutumin bai mutu ba amma idanunsa sun fara rufewa suna lumshewa da budewa alamar cewa ransa na daf da fita, kuma sai bude baki yake yanason ya fadi wani abu amma ya kasa. Cikin sauri ya durkusa bisa guiwoyinsa ya dora kan mutumin akan cinyarsa sannnan ya dubi ILsam yace " maza ka debo masa ruwa a cikin rafin nan ya sha" ILsam ya cika umurni da gaggawa,koda Humairu ya baiwa mutumin ruwa yasha sai yai dogon ajiyar numfashi sannnan ya dubesu daya bayan daya su bakwan nan, kawai sai ya gyada kai yace, "YA ku wadanan mafarauta ina mai shawartarku daku ruga da gudu ku koma Izuwa cikin kauyenku ku hada jama'arku gaba daya ku gudu daga wannan nahiya gaba daya, domin masifar da ta bullo a wannan nahiya tafi karfin kowa da komai. Wannan hali da ku ka na shiga sanadiyar masifar ne, kuyi sauri kuje ku ceci mutanenku in ba haka ba kuwa duk mazan dake kauyenku duk sai sun zama gawa. Koda jin wannnan batu sai mamaki ya kamasu su duka, har ma wasu daga cikinsu suka fara dariya domin ganin suke kamar dacin mutuwa ne yasa wannan mutumin yake sambatu. Shi kuwa Humairu bai dauki abin da wasa ba. Don haka sai ya gyara kwanciyar kan mutumin akan cinyarsa ya dubeshi yace, ya kai wannan mutum, wai shin wacce irin masifa ce haka tazo wannan nahiya tamu?" Mutumin ya kara bude baki da kyar yace "wadansu irin mutane ne sukazo mana wadanda adadinnsu ba zai kirgu ba, kuma kirarsu irin ta mutanen farko ce, saboda girmansu idan suka hau kan doki take kashin bayan dokin yake karyewa, don haka ne yasa basa hawa dawakai sai dai giwaye, suna dauke da mahaukatan makamai irin wadanda idanu ma bai taba ganinsu ba. Ina dada gaya muku ku gaggauta barin dajin nan ku koma kauyenku ku ceci jama'arku " Gama fadin Hakan keda wuya sai idanun mutumin suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare, ya zamana cewa babu wani abu dake motsi a cikin jikinsa. Humairu ya shimfide gawar mutumin a gefe daya, sannnan ya dubi sauran jaruman shida yace, to fa kun ji sakon da wannnan mutumin ya isar mana dashi. Ina ganin zai fi kyau kuzo mu koma gida da sauri domin ni dai jikina ya bani cewa maganar da mutumin nan ya fada gaskiya ce."caraf sai ILsam yace, haba ya kai Humairu ya ma za ai ka yarda da maganar mutumin dake kan gabar mutuwa? " Ai ni ina ganin cewa kawai radadin fatar rai ne yasa shi sambatu ". Cikin fushi Humairu yace "to idan kace haka, menene kuma abinda yayi masa wannnan mugun raunika ajikinsa?" Idan ma sara ne na takobi tunda muke yawo a dazuzzukan nan bamu taba ganin dabar da ta yawa mutum irin wannnan rauni ba. Idan dukkaninku babu wanda zaiyi amfani da wannnan shawara ni kam sai nayi amfani da ita. Koda gama fadin Hakan sai Humairu yaje bakin rafin ya cika battarsa da ruwa ya tsuke bakinta, kuma ya ratayata a kafadarsa. Kawai sai ya falfala da matsanancin gudun tsiya ya nufi hanyar da zata mayar dashi kauyensu na Garul Aswar" Koda faruwar hakan sai su ILsam suka hau kallon juna, tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba,kawai sai ILsam yabi bayan Humairu da gudu, nan take sauran samarin ma suka yi koyi dashi, wato gaba dayansu suka ruga Izuwa hanyar gida. Bayan sun shafe sama da sa'a daya da rabi ne suna gudun suka tsaya cak. Gaba dayansu cikin tsananin tashin hankali suna haki, sakamakon abinda suka hango a gabansu. Ba wani abu suka hango ba face turnukewar hayaki mai yawan gaske acan kauyensu. Saboda yawan hayakin har basa iya hango komai na kauyen, hatta gidajensu na bunu kuwa. A firgice suka zare makamansu lokaci guda suka sake rugawa da gudu domin su isa cikin birnin. Kaico! Suna shiga cikin garin sai sukayi BAKIN GANI, domin sun fara tuntube ne da gawarwakin mazajen garin duk inda suka duba basa ganin gawar mata ko ta yara sai ta maza samari da tsofaffi. Koda ganin wannan Al'amari sai su Humairu suka fara kuka domin sun fahimci cewa an kashe gaba dayan mazajen kauyen nasu, ko mutum daya ba'a bari ba. Gawarwakin mazajen dake zube a wajen sun haura dari uku kuma babu babban abin takaici face ganin irin mugun kisan da akayiwa mutanen, babu gawar da zaka ga sara daya a jikinta sai dai biyar ko sama da haka, Nan fa kowanensu ya fara lalubar gawar mahaifinsa, Humairu ne ya fara ganin gawar mahaifinsa yaga an sharbe masa makogwaro kuma an fede kasan cikinsa har tumbinsa ya fito waje. Koda da ganin wannan gawa sai Humairu ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda ya cika kauyen gaba daya har ya amsa kuwwa Izuwa cikin daji. Kash! Rashin sani yafi dare duhu, inda Humairu yasan abinda zai biyo baya sakamakon wannan ihu da yayi da bai yi shi ba. Ashe rundunar wadanan mugayen mutane da sukazo suka yi wannan muguwar barna basu dade da barin kauyen su Humairu ba. Tazarar dake tsakaninnsu da kauyen bata wuce ta tafiyar rabin zango ba. Ai kuwa sai suka jiyo wannan ihu da Humairu yayi, nan take shugaban dakarun wani jibjejen kato wanda kamar zanashi akayi saboda girma da munin gaske. Ya dubi wadansu zakwakuran dakarunsa guda uku kacal! Wadanda su kansu yin arba dasu ba karamar masifa bace saboda kwarjininsu, Ya daka musu tsawa yace, ku koma da baya Izuwa wannan kauye da muka baro, lallai akwai sauran namiji acikinsa. Ku tabbatar da cewa baya numfashi, kuma ku ciro kansa kuzo mini dashi domin na tabbatar da cewa yaje kasa. Idan banga sabon jini a jikin kan ba nasan kun kasa cika aikinku, don haka kuma zaku sheka barzahu. Koda jin wannnan umurni sai zaratan dakarun uku sukayi sujjada ga shugaban nasu sannnan suka kada giwayensu da baya cikin sauri suka nufi hanyar da zata mai dasu kauyen Garul Aswar. Koda ganin wannan abin da ya faru sai wadansu mata guda goma sha hudu daga cikin wadanda aka kamo a kauyen Garul Aswar suka fashe da kukan bakin ciki. Wadanan mata ba wadansu bane face iyayen su Humairu da yan matansu wadanda zasu Aura. Da farko da wadanan mata suka ga cewa sa'adda wadannan samudawan mutane suka barko musu mazajen nasu basa nan ba'a kashesu ba,sai suka cika da murna duk da cewar sun san abune mawuyaci su sake saduwa dasu,amma yanxu da suka ga an tura a kashesu sai murna ta koma ciki, suka cika da tsananin bakin ciki. * * * A can kauyen Garul Aswar kuwa, kamar yadda Humairu ya ga gawar mahaifinsa ya rungumeta yana kuka haka suma sauran abokan nasa shida duk suka ga gawar iyayensu maza, suma suka kama kuka cikin matsanancin bakin ciki. Bayan sun dan jima ne a wannnan hali sai suka mike tsaye gaba dayansu suka shiga neman matan kauyen da sauran kananan yara, amma sai da suka kewaye kauyen gaba daya ko mace daya basu gani ba,kuma basu ga yaro ko daya ba. Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsu kenan suka tabbatar da cewa lallai kwashe su akayi gaba daya aka tafi dasu. Nan take duka suka fusata ainun, jikinsu ya kama tsuma tsuma, saboda tsananin bakin ciki suka fara tunanin daukar fansa. Duk wanda ka kalli fuskarsa a cikinsu sai kaga har tana yatsini saboda fushi, Humairu ne kadai mai dan sauran nutsuwa a cikinsu domin su ILsam ma kamar wadanda suka zautu domin sun kasa zama sun kasa tsaye. Koda ganin haka sai Humairu ya kira sunayensu daya bayan daya duk suka zo gabansa suka tsaitsaya. Cikin nutsuwa ya dubesu yace, "Abinda nake so ku fahimta shine, mu bakwai kacal bamu isa mu bi wadanan mugayen mutane ba, mu yakesu har mu karbo iyayenmu da masoyanmu, domin Sarkin yawa ma yafi Sarkin karfi bare ma ga yadda wannan mutum ya siffanta mana yanayin wadanan mutane, karfi ma sun fimu, saboda haka ina mai shawartarmu damu bi wadanan mutane Izuwa inda suke domin muyi nazarin yawansu, karfinsu da karfin sihirinsu ba tare da sun ganmu ba, sannnan muyi tunanin hanyar da zamu bi mu karbo mutanenmu a hannunsu ta hanyar hikima da dabara koda kuwa ba zamu iya yakarsu ba. Sa'adda Humairu yazo nan a zancensa sai Sahal, Kaimur, Hashlar suka fusata ainun suka nuna cewa yaushe za a tsaya wani bata lokaci ace sai an tsaya nazarin wadanan mutane, ai kawai abi sawunsu ba wani tsoro ko labiya a afka musu ko su ko mu tunda sun gama cutar damu tunda sun baje mana garinmu kuma sun kashe mana gaba dayan mazajenmu, yanzu mune kadai mazajen da basu mutu ba a wannnan kauye ". Kaimur ne yayi wannan jawabi. Koda ILsam yaji abinda Kaimur ya fadi sai Ya fusata ya daka masa tsawa yace, "shin baka da hankali ne ko kuwa ka sami tabin kwakwalwa ne?" Ashe ka manta cewa tsawon shekara da shekaru a iya tasowarmu Humairu ne yake bamu shawara bisa duk abinda ya kamata muyi a duk sa'adda wata matsala ta bijiro mana kuma muna amfani da shawarar tasa a dace ba a taba fuskantar rashin nasara ba. Saboda me yanzu kakeson ka kawo mana rudani a cikin al'amarinmu? " Da jin haka sai Kaimur ya mike tsaye zumbur! Ya zare takobinsa yayi kan ILsam a fusace shima ILsam sai ya zare tasa takobin ya yiyo kansa yana huci tamkar bakin kumurci. Saura kiris su hadu su kacame da yaki sai Humairu yai sauri ya shiga tsakaninnsu yace, "yanzu kuna ganin fada da junanmu shine abinda zai warware mana matsalar dake gabanmu?" Koda jin haka sai jikin kowa yai sanyi, kunya ta kama Kaimur da ILsam suka sunkui da kawunansu kasa, har Humairu ya bude baki zai ce wani abu sai suka ji kasa ta kama girgiza, ai kuwa suna dago kawunansu sama sai suka hango wadansu giwaye manya-manya guda uku sun durfafo inda suke a guje. Ashe karfin takun sawayen giwayen ne Ya haddasa wannan girgizar kasa. Ba giwayen bane suka firgita su Humairu ba, mutanen dake kan giwayen sune wadanda suka fi razanasu. Wadansu irin girda-girdan mutane ne wadanda ko a misalin mutanen farko masu ma su daban suke. Saboda tsawon mutanen sai kaga kamar idan suka mike tsaye kansu zai iya tabo sararin samaniya. Kaurin kwanjinsu guda daya kamar an cure mulmulan kasar gini guda arba'in a waje daya. Gaba daya jikinsu a murde yake kuma cike da damatsa da jijiyoyin kai da gani kasan cewa taurin jikin nasu zai zo kunnen doki da taurin dutse. Kai da gani ba tambaya kasan cewa baza a rasa nono a riga ba. Wato dole ne su kasance masu karfin Allah ya isa. Dukkanin samudawan uku na rataye da wata irin zabgegiyar takobi mai tsawo,fadi da tsinin gaske, Wacce nauyinta yafi gaban daukar karti goma majiya karfin gaske, amma samudawan ji suke kamar kara suka goya a bayansu. Tun sa'adda su Humairu suka hango wadanan samudawan a guje bisa wadannan giwaye sai dukkaninsu hankalinsu ya dugunzuma domin sun tabbatar da cewa kawarda samudawan ba karamin aiki bane. Tun daga nesa samudawan uku suka zare takubbansu suka wangame bakunansu suna masu kwarara uban ihu,duk da cewa su Humairu sun firgita da ganin wadanan samudawan sai suka dake suka ki guduwa. Lokaci guda suka kalli junansu su bakwan kawai sai kowa ya gyara zaman makaminsa a hannunsa, sannnan suka kwarara uban ihu a lokaci guda, amma karfin sautin ihun nasu su bakwai bai kai na basamude daya ba daga cikin wadanan samudawa uku da suka durfafosu a guje. Kawai sai suma suka rugo da gudun tsiya a jere suka durfafi samudawan, inda mutum na nan a tsaye a Lokacin da wannan abu ke faruwa da cewa zaiyi su Humairu sun haukace domin yasan cewa ajalinsu suka tara. Yayin da ya rage baifi saura taku biyar ba giwayen samudawan su takesu Humairu sai kawai samudawan suka ga su Humairu sun daka tsalle sama sun kawo musu wawan hari a sama, ai kuwa suma sai suka maida martani. Koda su Humairu suka fado kasa a bayan giwayen sai dukkaninsu suka kasa mikewa tsaye. Daga can sai Humairu ya mike tsaye shi kadai, koda ya dubi sauran 'yan uwansa su shida sai hankalinsa yayi mummunan tashi domin dukkaninsu babu wanda bai sami karon rauni ba a jikinsa. Wani a cinyarsa, wani a damtsen hannu wani a gadon bayansa, Hashlar ne kadai babu rauni mai zubarda jini a jikinsa amma ya doku sossai a gadon bayansa, nan dai shima Hashlar ya yunkura ya mike tsaye da kyar a Lokacin da samudawan uku suka juya da baya da giwayensu sun daga manyan takubban nasu sama, suka sukwano giwayen aguje domin su zo su turmushe su Humairu, a wannan Lokaci ne Kaimur ya ga sara a kirjin daya daga cikin samudawan har jini na zuba Koda ya dubi bakin takobinsa yaga jini na diga kawai sai ya Humairu yace "zamu iya yin wani abu akan wadanan mutane amma fa sai munyi da gaske. " Cikin razana da matukar damuwa Humairu yace, "yanzu ya zamuyi dasu idan har muka bari suka iso nan sai sun turmushe yan uwanmu dake kasa." Hashlar yace "Ai wannan karon basu zamu kaiwa hari ba giwayensu ya kamata mu tsaida su ta kowanne haki kuma mu gocewa duk irin harin da samudawan zasu kawo mana.ta kowanne hali mu kai giwayen kasa kafin su iso nan haka sai kazo mu ruga mu taresu. Kafin Humairu ya bude baki yace wani abu tuni Hashlar ya falfala da gudu ya tunkari giwayen uku, ai kuwa shima Humairu sai yayi koyi dashi. Su kuwa wadanan samudawan uku dama a matukar fusace suka durfafo a guje a karo na biyu musamman saboda raunin da aka yiwa dayansu. Saura taku daya jal giwayen su talitse Humairu da Hashlar sai suka goce suka shiga karkashinsu, cikin zafin nama Hashlar ya huda cikin giwayen biyu da takobinsa shi kuma Humairu ya huda cikin giwa ta uku. Lokaci guda giwayen uku sukayi tutsu suka yar da mahayansu sannnan suka fadi a kasa tim! Kamar tsauni ne ya rugurguje kuna so kuwa Duk da dai remake ne amma 1_4 nake dashi kuna so DUGUNZUMA!!! LITTAFI NA 1 PART 2 LITTAFIN YAKI ***** A wannan Lokaci ne Kaimur ya ga sara a kirjin daya daga cikin samudawan har jini na zuba Koda ya dubi bakin takobinsa yaga jini na diga kawai sai ya dubi Humairu yace, "zamu iya yin wani abu akan wadanan mutane amma fa sai munyi da gaske. " Cikin razana da matukar damuwa Humairu yace, "yanzu ya zamuyi dasu idan har muka bari suka iso nan sai sun turmushe yanuwanmu dake kasa." Hashlar yace "Ai wannan karon basu zamu kaiwa hari ba giwayensu ya kamata mu tsaida su ta kowanne hali kuma mu gocewa duk irin harin da samudawan zasu kawo mana. Ta kowanne hali mu kai giwayen kasa kafin su iso nan don haka sai kazo mu ruga mu taresu. Kafin Humairu ya bude baki yace wani abu tuni Hashlar ya falfala da gudu ya tunkari giwayen uku, ai kuwa shima Humairu sai yayi koyi dashi. Su kuwa wadanan samudawan uku dama a matukar fusace suka durfafo a guje a karo na biyu musamman saboda raunin da aka yiwa dayansu. Saura taku daya jal giwayen su talitse Humairu da Hashlar sai suka goce suka shiga karkashinsu, cikin zafin nama Hashlar ya huda cikin giwayen biyu da takobinsa shi kuma Humairu ya huda cikin giwa ta uku. Lokaci guda giwayen uku sukayi tutsu suka yar da mahayansu sannnan suka fadi a kasa tim! Kamar tsauni ne ya rugurguje. Su kansu samudawan uku sunyi matukar mamakin yadda akayi wadanan 'yan kananan bil'adama guda biyu suka yi wannan gagarumar jarumtaka cikin zafin nama haka. A fusace samudawan uku suka mike tsaye zumbur suka sake rugowa Izuwa kan Humairu da Hashlar aka kacame da azababben yaki. Nan take Humairu da Hashlar suka raina dukkan jarumtakarsu kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun domin sun san cewa suna cikin TSAKA MAI WUYA saboda a koyaushe zasu iya zama gawa Ba wani abu bane ya haddasa hakan ba face ganin tsananin zafin naman samudawan da karfin saransu da kuma girman takubbansu da karfinsu. Abu na farko dai shine, duk sa'adda samudawan suka kawo musu SARA DA SUKA suka kare sai su ji kamar dutse aka kwadawa nasu takubban, saboda nauyin takubban samudawan har nauyin na rinjayarsu suna faduwa kasa, sai dai kaga sun yi sauri sun mike tsaye. Abu na biyu kuma duk sa'adda takubbansu Humairu suka hadu dana samudawan sai nasu Humairu sun dakushe, tartsatsin wuta da hayaki na tashi. Abin tsoro ma shine, tunda aka fara gurmuzun su Humairu sun kasa maida martani ko sau daya sai dai kokarin kare kai da gani kasan cewa anfisu karfi da iya yaki nesa ba kusa ba. Nan fa samudawan suka kuntatasu suna kokarin su hallakasu acikin kankanin lokaci sannnan suje su hallaka ragowar 'yan uwansu dake kwance a kasa sun kasa tashi. Su kansu su Zuraif dake kwance a kasa din suna numfashi sama sama sun karaya bisa ganin irin tsananin karfi da jarumtakar samudawan sun san cewa dayansu ba zai tsira da rayuwarsa ba. Lokacin da aka sami lokaci mai dan tsawo ana wannan gurmuzu sai Humairu da Hashlar suka fara gajiya ya zamana cewa da kyar suke iya kare harin samudawan. Faruwar hakan keda wuya sai daya daga cikin samudawan wannan wanda Hashlar ya sara a kirji ya sami nasarar dankarawa Hashlar sara a hannunsa na hagu take hannun ya tsinke ya fadi kasa. Hashlar ya kurma uban ihu a Lokacin da jini yai tartsuwa daga cikin dungulmin hannun, kawai sai Hashlar ya tafi kasa luu! Kamar sumamme ya tsugunna bisa guiwoyinsa. Basamuden ya sake daga takobinsa zai sare kan Hashlar sai ILsam dake can a kwance magashiyan yai wuf ya dana kibiya akan bakansa ya harbota, take kibiyar ta huda gadon bayan Basamuden ta hudo ta kirjinsa. Ko ihu basamuden baiyi ba tamkar kaya ce ta sokeshi kawai sai yasa hannu ya zaro kibiyar ya fasa sare kan Hashlar ya juya da baya a fusace ya ruga Izuwa inda su ILsam ke kwance. A wannan Lokaci wadannan samudawan sun sa Humairu a tsakiya sun dada kuntatashi suna so suyi masa kisan gilla, amma saboda ganin an sarewa Hashlar hannu daya sai ya fusata ya kara ZAGE DANTSE yana kare kansa. Koda wancan basamuden ya isa kan su ILsam sai ya hau su da sara da yake dama a matukar galabaice suke sai suka kasa kare kansu. Kaico! Nan fa ya dinga daddatsasu suna ihu, jini na fallatsi da famtsama abin ba kyan gani. Cikin dakiku kadan yai gunduwa- gunduwa da sassan jikinsu. Hashlar dake tsugunne da dungulmin hannu cikin galabaita shine ya fara hango abinda ya faru ga sauran yan uwansu, ai kuwa sai ya kwarara uban ihu ya fashe da matsanancin kukan bakin ciki. Nan take jikinsa ya kama tsuma, bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur! Ya ruga da gudu Izuwa kan wannan basamuden da yayi wannan danyen aiki. Gashi a sannnan babu takobi a hannun Hashlar saboda hannun nasa mai rike da takobin shi aka sare. Koda basamuden ya juyo ya ga Hashlar ya rugo gareshi ko makami babu a hannunsa sai yai murmushin mugunta sai shima ya rugo gareshi cikin bakin nufi, ai kuwa suna haduwa sai basamuden ya kawowa Hashlar mugun sara da kafa da nufin ya tsargeshi gida biyu, cikin bakin zafin nama Hashlar ya goce, takobin basamuden ta sari kasa ta nutse a ciki. Kafin basamuden ya zaro takobin tuni Hashlar ya tattara karfinsa gaba daya ya gabza masa naushi da daya hannun nasa lafiyayyen a cikin kunnensa na dama, saboda karfin naushin sai da jini ya furzu ta cikin daya kunnen na hagu Nan take basamuden ya kama tangadi a tsaye. Hashlar yasa hannunsa ya zare takobin badakaren wacce ko a mafarki bai taba zaton zai iya dagata sama ba, saboda girmanta da nauyinta amma sai gashi ya dagata da hannu daya, kawai sai ya lumawa basamuden takobin a cikinsa, a wannan Lokaci wadancan samudawan biyu sun kai Humairu kasa suna shirin tsireshi da takubbansu sai kawai suka jiyo ihun dan uwansu. A razane suka waigo koda suka hango shi a tsaye yana layi ga takobi a cikin

Chapter 1 of 9