Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
raina kamar iffaat amma itace take gwadamai axaba, iffaat kuwa tana samu ya saketa ta fita da sauri ta wuce gida tana zuwa ta fada dakinta ta kulle tana kukan takaicin rayuwa da mutum irin Yy farhaan ta daga kai taga hoton Yaya Suhaila da Yy farhaan sun rungume juna suna dariya tayi tsaki,ta tashi ta cireshi ta saka a drawer ta dawo taci gaba da tunaninta har barawo bacci ya dauketa, bayan ta tashi taje gun mama.. Ah ah yaushe kika dawo? Tayi murmushi wallahi tun dazu na dawo nasan kina bacci lokacin shi yasa banma zo natayar dakeba, okay suka yi tadi mama tana tanbayarta ta gyara Gidan dakyau kuwa? Dan tasan son jiki ya mata yawa Laaa mama kin manta nayi aikatau suka saka dariya gaba daya, Yaya Ameen ne yazo da Yaya Ali suka zauna akayi tadin dasu suna cikin magana Yy Suhaila ta kira... Sister sorry na sakaki aiki da yawa,!laa kinji dai Yy Suhaila wane aiki kuma idan ban mikiba mawa xan yiwa, ta fara godiya, wallahi idan kinamin godiya zan kashe wayata, to nabari yi haquri, kin tarar da farhaan a gida?? Wallahi Naso nace idan yananan ki masa Dan girki, Tseeeet tayi kamar ruwa ya cita qirjinta yake bugawa, lokaci daya ta tuna abinda ya faru tausayi Yy Suhaila ya kama ta Amma bazata iya fada mataba, hello kinajina kuwa sister? Tayi xumbur ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi.. Inaji Yy Suhaila, to ki bawa mama wayar na miqawa mama ta tashi tsaye, Yaya Ali ya kamo hannunta.. bayan sun qare yace wani abokinane yakeson ta kinma sanshi Nurane mama tace nikam ko sunansa banaso bare shi na tsani wannan yaron akwai shegen rawar kai, iffaat tace wallahi nima mama na tsani Nura kamar me nima dai jabo ba abarni a bayaba gun tsanar sunan Nura mugu. Duk aka saka dariya kowa ya tsani Nura Allah sarki har ya bani tausayi...... ** Goben ranar tinda safe Suhaila tayi waya da iffat ta gaya mata sun kamo hanya Guraren qarfe 11 iffat na zaune da mama dasu yaya da yake yau Saturday, wayar iffat tayi qara laaaa yy Suhaila hatman sun iso, hello Yy Suhaila kuna ina? Kun kawo hala? Taji namiji yace ke sister din Suhailar ce ?? Tace Eh kai waye? Sorry Dr ne daga Chika, yayar Ki sun sami accident Allah ya mata cikawa driver kuwa gashinan kwance ya kakkarye? Iffaat wata irin qara ta saka ta fadi sumammiyaaa.... [12:18PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 59 Na Hauwa M. Jabo Mama tayo kanta tana tambayar lafiya amma ina iffaat ta riqa ta suma, Yy Ali ne ya dauki wayan ya kira number Yy Suhaila, Dr. Ya masa bayanin da ya yiwa iffaat yace babbar motace ta shiga gabansu suka yanka daji anan motar ta wuntsila rai yayi halinsa Yaya Ali ma dashi da qarfin halinsa sai da yayi kuka, ya yiwa mama bayani tuni gida ya rude da koke koke Yy Ali yayiwa baban Suhaila waya ya fada Masu abinda yake faruwa kamin kace kwabo labarin rasuwar Suhaila ya baje family namu kowa yaji mutuwar Suhaila cox Suhaila mutunce mai mutunci ga haquri da kawaici, bata shiga harkar da ba nataba kai mutuwa tana dauke nagari. farhaan kam da ya samu labari mutuwar tsaye yayi bai samu damar maganaba saida yaga gawar Suhaila, sannan ya fara kuka kamar qaramin yaro kamar wani zararre, lallai ta tafi tana binsa basussuka cox bayajin tayi wata biyu yana kyautata mata kullum cikin muzguna mata yake, su farahnax kam haka ta dawo kamar mahaukaciya, mutuwar ta ratsa kowa a gidannan musamman iffaat da farhaan da maman Suhaila.!!! Iffat koda ta farfado har an kai Yy Suhaila makwancinta wayyo Allah, mutuwa mai raba da da mahaifi miji da mata Yaya fa qanwa aboki da aboki. Mutuwa tayi yankan qauna a wannan family... cikinta ma anciroshi da ranshi amma da yake wata7 ne kwana biyu yayi yabi uwar shi, cikin da farhaan yayi burin ta zubar tun tana amarya zan iya cewa ma bayason cikin. Sauda yawa Suhaila tana kiran iffaat qanwarta ta fada mata abinda farhaan yake mata amma tace kada ta fadawa kowa, kuma bata taba fadaba Mutuwar Suhaila yasa iffaat ta qara tsanar farhaan gani take kamar shiya kashemata Yar uwa! amma fa still sonsa yana cikin zuciyarta, hmmm soyayya manya..! ***** Arba'en din Suhaila yayi daidai da fara jarabawar su iffaat mutuwar Suhaila tadan natsar da ita kadan dama iffaat ta iya matsuwaa idan Abu ya faru da ita! sunyi neco da waec lfy sai jiran saka mako, xubi xubi iffaat tana zuwa gidansu farahnax ta gaida mamarshi da farahnax din da kuma qawarta Yar baqa zainb khalifa, Ranar tana zaune dakinta taji sallamar farhaan, da yake Gidan idan aka shigo dakinsu yana daga gefe ne sai dakin mama, tanaji ta gane tayi banxa dashi. Sunyi hira da mama, tanaji yana tambayar ina iffaat tace tana daki, Har ta manta da wani farhaan yazo gidan. Chan taji sallamar sa a dakina, Dan amsa sallama wajibine da nasan iffat ba zata amsa maiba, taci gaba da aikinta, ya zauna ya fara sun batunsa, yaga ba nasara, yace iffaat....... [12:21PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA.?? 60 Na Hauwa M.Jabo Iffaat miyasa kike min hakane? Koba komai ni Dan uwankine tun kamin mu hadu da margayiya, kuma naxo na auri yayarki, kina tunanin kodan wannan ai bai dace ki riqa min wani gani ganiba, ki tuna kin min laifinda ya dace na hukuntaki amma na gyaleke na yafee miki..! Anti masifa madam iffaat ta watsa mai kallon banza hadi da wata uwar harara! Laifin me na maka oga? Wato ma ni na maka laifi ko?? Ka manta chin mutuncin da kake yiwa Yar uwata? Kamanta wulaqancin da kake mata?? Ka manta yaudarar da kake mata?? Sannan duk ka shuresu kaxo kana cewa ni na maka laifi?? Ta daga kai tayi karo da hotonta ita da Suhaila sun rungume juna suna dariya. Hawaye ne suka wanke mata fuska tayi missing din Yar uwarta abar sonta, farhaan ya kamo hannun iffaat yana zaune iffaat Dan Allah ki yafemin! Nasan ban kyautawa Suhaila ba ko kadan, wallahi sai yanxu nake ganin irin rashin kyautatawar Dana mata idan kika yafemin tamkar itace ta yafemin ta kasa kwace hannunta daya riqe batace komaiba.! Tayi ajiyar zuciya ta karbe hannunta, ta zauna har ya qare surutansa batace masa komaiba, wallahi iffaat ina tsananin son Suhaila, ji tayi ya daba mata wani gwaho a zuci har saida ya gane. Nasan baxaki yardaba amma gaskiyane na fada miki, ya gaji ya tashi Ya qara wuta.. ***** Iffaat yan mata result ya fito ana kiciniyar shigarta jami'a ta sami damar shiga cikin nasara an bata course dinda takeso kuma. Dai dai lokacin auren farahnax ya matso sai shirye shirye suke qawayen amarya, komai itace gaba itada Yar baqa sai iyayi suke, anyi auren farahnax lafiya ankai amarya Gidan mijinta da ke abuja, iffaat dai kam kullum sai tayi sabon saurayi amma ko kallo Basu ishetaba karatun ta ta saka gaba.! Ranar umma tayi rashin lfy sunje dubata itada mama da maman suhaila, umma ke tambaya ta yaushe zatay aure? Ko sai ta samo mini mai saida ruwa irin na dijee, akasa dariya kunya ta kamani na tashi na shige lanbu don demo abincina na da na barsu su nan..... KU BIYOMU DON JIN ABINDA IYAYEN WAYANNAN YARAN ZASU TATTAUNA AKAI, jiya banyi posting ba wallahi network yamin tsiya nayi nayi fcbk dina ya bude yaqi buduwa kuyi haquri.!!! [10:49PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..??61 Na Hauwa M.Jabo Suna tsaka da labarin su saiga farhaan ya shigo ya gaida surukansa yama ummanshi ya jiki ya shige dakin abbansa, Bayan ya wuce ne maman Suhaila take cewa Allah sarki yaronnan har yanxu bai nemi mataba? Umma tace kedai bari gashinan Bansan mi yake jiraba, niko ga shawara, mizai hana a hada farhaan da iffaat aure. Mama tayi dariya kai hajiya kulu ina kika taba ganin rigima da rigima sun hadu duk sukasa dariya umma tace lallai kam Dan farhaan da iffaat basa zama guri daya. Mama tace koda yake shi aure daban ne wata qila sai kiga sun zauna lfy. Gaskiyar magana dukansu sunyi na'am da shawarar hajiya kulu maman Suhaila sun tsaya akan zasu shawarci mazajensu suji, Suna zaune suna tadi saiga iffaat da ta ciki kyale da su mangoro da gwaiba umma tace um um mai hali baya barin halinsa..! duk suka saka dariya, taje ta wanko ta kawo musu suka farasha, dama ita qa'idarta idan zatasha mangoro saita mulmulashi yayi laushi yayi ruwa sannan tasha. Ta kuwa miqe qafafu ta saka basket dinda ta saka kayan a ciki ta fara shan mangoronta tana zaune saiga farhaan ya shigo ya kalleta, xaman da tayi ya bashi dariya ya tuna mai da lokacin da take qarama sai yaji bari ya tsokaneta komai ta fanjama fanjam.!! Wai umma wannan Yar taki ba university take xuwaba? Umma tace eh chan take kaga yata an zama yan mata ko..!! Inafa yan mata har yanxu bata wayeba! Kalli Dan Allah yanda take shan mangoro kamar wata Yar ruga,! ruwan mangoromangoro suna bin hannu, ya kwashe da dariya hadda buga qafa ya gama quleta ya kalli umma anya kuwa zata sami miji a haka?? Umma tace ka sakawa yata ido dayawafa miji kam sai ta xaba Dan ma bakaga yanda ake layiba dukansu suka dara nima dai jabo na dara kuma Masu karatu sai Ku dara.!! Iffaat tace umma ki barshi, ta dago ta kalleshi ido cikin ido tace mijina sai ka Ganshi wayayye na gaske ba irin wayewarkaba, ba Wanda yagane habaicin da ta masa sai shi damu Masu karatu. Yadan Sosa kai yayi murmushi qarfin hali mama bari na tafi tunda kun hanani mangoro, umma tace sai kace wacce da debo ta sammaka, yace waa ai wannan tafi dijee rowa.! da zai fita ya hada da gefen chinyarta ya take saida tayi qara ta jefeshi da qallon mangoro...... [10:57PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 62 Na Hauwa M. Jabo Mama tace Waike iffaatu bakida kunya ko, miye na jifanshi da kwallon mangoro? umma tace rabudamin da ya, wallahi shiya tsokaneta ina kallonsa ya taketa, Dan ya taketa sai ta jefe shi, karki sa mata baki Dan Allah ke iffaat tashi ki shiga ciki. Bayan ta wuce umma tace kin ganiko,? Haka suke kamar tom & Jerry, hajiya kulu tace ai aure daban yake alkhairin sa zamu nema kawai,... *** Hajiya kulu na komawa gida ta sami mijinta mahaifin Suhaila tamai xancen ai tuni ya amince abbah ma da umma ta masa magana ya amince 100% mama ma haka tayi shawara da su Yaya Ameen akan wannan auren kowa ya aminta yanxu ya rage aji ta bakin gogayen... Abba da umma suka kira farhaan aka fara masa maganar Dan tsananin rudu da tsoro saida ya manta yana gaban iyayensa, atafau farhaan yace aah miye dalilinsa yace kawai matsayin farahnax ya dauketa, shi bazai iya auren taba tun ana lallashi har Abba ya yanke dole ya aureta ko bayaso, kana tunanin zamu aura maka macen da zakayi kuka da ita? Duk cikin mu ka fimu sanin WACE CE ITA! cox ka zauna da ita tun tana Yar mitsiyayarta, Farhaan dai kawai yajisune amma Sam bai amin taba, Itama madam iffaat an mata maganar farko dariya ta saka musu irin ga zancen nan Mara kan gado. Da taga dai da gaske akeyi kawai saita saka musu kuka! Aka buga Sama da qasa tace bazata auri mijin yayartaba... Abba Suhaila ne yace sun Riga sun yanke magana ba chanji ba mijin yayartaba ko waye shi zata aura.. Nikam jabo abin mamaki ya bani yanda iffaat tayi jinyar son farhaan tun batada wayo amma yanxu ga dama ta samu tace batasosa! Uhum kuma ga dukan alamu da gaske takeyi, ta daga ba nasara taci gaba da kuka ta wuce dakinta, Yaya Ameen ne yabi Yar qanwarsa yana lallashi, Haba iffaat miye aibin farhaan? Kina gani wallahi guy ne gashinatsatse ga kamala, wallahi yanzu dagyar ki sami namijin na kirki kamarsa baya shaye shaye baya Neman mata. ta dago kai da sauri ta kalleshi amma sai ta kasa fadar cewa yana Neman mata, kowa ya shedeshi ke kanki shedace akan haka! Sabida kinyi rayuwa dashi, iffaat dai batace komai ba har Yy Ameen ya qare rarrashinta ya tashi ya fito! Ta miqe wallahi da na auri farhaan gara na shiga duniya.... [10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 63 Na Hauwa M.Jabo Tun daga ranar ta kamawa su mama mutunci ta daina musu magana tadaina chin abinci ba ruwanta dasu ita dole fushi, anyi sati biyu da maganar sai ranar taji su yy da mama suna maganar, ana maganar daurin aure kuuut saidai wata ba itaba, ta miqe tsaye ta riqe kunkumi ta fara shawara da zuciyarta yanxu ita iffaat har sun isa su mata auren dole? Waima...! Idan ta saka musu ido zasu aurar da itane, su Basu damu da damuwartaba, abinda ya fado mata kawai ta gudu, kai guduwa ba jarumta bace, duk macen da za'ayiwa auren dole ta gudu ba jaruma bace,so bataso ta gudu a ganinta ba jaruma bace duk wani tunani sai taga bai dace da itaba, nidai jabo zaune nayi ina kallonta ina jiran muga abinda zata aikata, amma ga dukkan alamu ba wani Abu da ya rage gwagwalwarta bata aiki, sai fashewa tayi da kuka.. Yanda ta tsani halin Yy farhaan ko sonsa zai kasheta bazata aureshiba, tanada mahaukacin kishi Tayita tuna yan matan farhaan din da yanda yake musu ta runtse ido da qarfi ta daki madubi tace Nooooooooooo, ta na kuka tana dukan madubin duk ya yayyanke mata hannu, ashe su mama sun jiyo mama ko a jikinta, Yy amin ne yaxo gunta da sauri ya riqe hannunta duk ya yayyanke, ya yiqeta ya kalleta yaga yanda ta rame tana juyowa ta fada jikinsa tana kuka, tana cewa Yaya ka taimakeni wallahi banason sa Yy Ku aura min wani not Yy farhaan, yace to shikenan kiyi shiru zamuyi magana da mama, dagyar ya samu tayi shiru ya dauko first aid yadan gyara mata hannun ta ta ta yayyanke, ya jata da hira har tadan saki jiki, qarshe yace tazo su fita yawoooooo... [10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?64 Na Hauwa M. Jabo No ka tafi Yaya ni baxanjeba ya rarrasheta har ta amince suka shirya suka fita. Sunje wani park ne suna shan ice cream, hakan ya faranta mata rai matuqa suna sha suna tadi a hankali yy amin yake nuna mata illar abinda takeson tayi, suna tsaka da magana tana yan kalle kalle charab ta hango wani abu wacce ta hango ba shakka itace ba qarya budurwar farhaan ce ramcy, tayi murmushi su ramcy ananan da yake Yy baisan taba tana kallon ta har ta shige ba'ayi minti goma sai kuma ta hango farhaan, wani rasss taji ko shakka babu tare suke da farhaan amma da yake shi mai wayone a hankali yake takunsa, wai farhaan wane irin jarababben mutum ne? Tayi tsaki, yy amin yace miya faru kuma? Ta kalleshi idonta sun kada sunyi jaa ba komai! Ya ba komai, ta dago mai idonta da har sun zama qanana tace ba komai yy, sukaci gaba da tadinsu amma Sam bata tare da yy amin tanachan tana tunanin farhaan, kusan 30mnt Basu fitoba ta kasa haquri ta miqe tsaye, ina zaki kuma? Y tace ina zuwa yaya ya kalleta, yanxu zan dawo Yy, ta wuce da sauri ta shiga Ashe cikin gurin hotel ne ta fara dubawa duk ta zagaye gurin bata gansuba, sai taje gun reception ta tambayi farhaan mutumin yace mata yanada baquwa wani rass taji, tace ai na na sani shi yace nazo na karbi saqo yayanane, ya kalleta sosai sai ya gaya mata number dakinsa wani dumm dummm dummmm takeji, ana mata zagaye a zuciya ta isa gofar dakin tayi jimm ta daure ta bubbuga saida ta buga uku sannan aka bude, ramcy ce ta bude qofar iffaat ji tayi kamar ta shaqeta ta mutu ramcy bata gane iffaat ba Sam.! ta watsa mata harara, tace lfy iffaat ta daure tace yy farhaan yace naxo na karbi saqo na kaiwa umma, tanajin haka sai ta saki fuska, okay bari na kirashi, ta kwala mai kira yazo yana zuwa ya ganta......... Tofa. [11:19PM, 5/12/2015] .: WACE CE ITA..?? 65 Na Hauwa M. Jabo hankalinsa ne ya tashi! Ya rude yama rasa mizaice mata, itama haka wato wani tashin hankalin sai mutum yama rasa mi zaiyi, ta kalleshi tayi murmushin qarfin hali tace sannu Yy farhaan.!! Kamin ya bata amsa hawaye ne suka zubo mata batasan dalilin zuwansuba, gaskiya hawayennan sun kwafsa mata taso tayi chin mutunci cikin ruwan sanyi amma ina kuka ya kwafsa mata, bazai yiwuba chin mutunci ana kuka baiyiba, da sauri ta bar gurin tana juya kenan sai ga yy amin yaxo nemanta, lafiya kike kuka? Tace Ta hadu da wata qawartace shine take bati labarin mutuwar mijinta ......... Eyyah Allah yajiqanshi ina take? Tace sun wuce, farhaan yana jinsu kuma yaji abinda tace, yayi tunanin zata tona masa asiri amma ina bata fadaba, Suka kama hanya idon iffaat Sam bata gani gabanta hawayene suke rally a fuskarta.! ta kasa jurewa sai wani Abu takeji yana taso mata,ta rasa gane kanta, Yy amin yana gefenta yanata bata labari amma taqi bari su hada fuska kuma taqi cemar komai, har suka isa suka zauna!! Waike har yanxu kukan kikeyi? Ta dago kai ta kalleshi, wallahi Yaya ta bani tausayine tana matuqar son mijinta amma mutuwa ta rabasu, sai na tuna da yy Suhaila... yace Eyyah sai haquri Allah yajiqanta ya Dan qara lallashinta har tayi shiru amma zuciyanta cike da tunani.! Har suka dawo gida tunani takeyi. Shiko farhaan yana ganin sun bulle ya kori ramcy tana tambayar lafiya ya daka mata tsawa akan ta bace mai da gani, ta tattara yan kayanta ta wuce, ya fada kogin tunani,! Baisan miyasa wannan yarinya takeda bala'en tasiri rayuwarsaba, duk abinda yake a boye yake yinsa, amma kuma bawai yana damuwane da kada a Ganshi ba amma yana jin haushi idan iffaat ta Ganshi..! Gashi tun tana qarama tasanshi da wannan hali,amma har yanxu baidainaba, yasan yana fama da sonta kuma tun tana qarama yakejin haka yaqi qasqanta hakan ne, ya yakamata fa ya daina. Kai wannan mitsitsiyar yarinyar tama isa ta hanashi abinda yakeso!? Amma miyasa take yawan kamashi? Yaja tsaki ya juya ya miqe tsaye yana zagaye dakin. Chan ya daki iska yace auren ta kawai zan aminta dashi shine zaiyi maganinta, shima ya huta da azabar rashinta. haka dai ya qare yan tunane tunanensa cike da damuwa. Iffaat kuwa ana isa gida ta fada daki ta kulle ta fara sana'ar tata yanda take kishin farhaan tasan wata rana kisan kai zatayi, gara kawai ta nemawa kanta zama lafiya ta aureshi, ba wata hanya da takeda da ta wuce ta amince masa kamin baqin cikin sa ya kasheta ko banxa zata rage azabar rashin ganinsa da take fama da ita, haka har bacci ya dauketa, Yy amin ne ya tayar da ita daga bacci, ya kawo mata pizza tayi murmushi Yy amin ne kawai yake rarrashinta idan tana fushi mama kam ko kallo bata ishetaba itama haka.... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 67 Na Hauwa M.Jabo 20/5 idan ban mantaba yayi daidai da ranar daurin auren yy Suhaila kuma shine ranar brdy dina ni Hauwa Jabo wannan ranar itace rana mafi girma da daraja a idon iffaat wannan ranar ita ta chanxa ta daga jerin yan mata zuwa matar aure a wannan ranar ne ta taka matsayi na Chika da kamala, Farhaaan kuwa jinsa yake gashinan dai ya rasa abinda yake damunsa tsorone ko kuma murna ko baqin ciki gashinan dai kamar ba angoba.. Ba wani shagali da akayi, Dan zance muku iffaat har ranar dauren auren ta saida ta sulale taje makaranta wayanda sukasan da zancen auren suna ta mamaki irin ga serious student dinnan, basusan dawar garinba, ai kuwa tana dawowa tasha fada gun mama haka dai aka qare taro akan gobe za'akai amarya gashi Kuma amarya gobe ma tanada test gashi ance sai ta fadawa ogan zata iya fita, sai kawai haqura tayi, ankai amarya gurin su umma suka mata nasiha, nidai tunda nake ban taba ganin amaryarda ana mata nasiha tana kallon mutaneba sai iffaat ba Dan sunkuyar dakai ba komai haka umma na mata nasiha ido cikin ido tana kallon ta har abin ya baiwa umma dariya amma ta fuske Abba ma yayi har ya bata kudi yace ko zata buqaci wani Abu. Daganan aka kwashi amarya aka kaita Gidan mijinta PURHUUN... Abokan ango sun rako ango yan matan amaryar da suke nan su black one ZZ da najma da meena slow sune suka sayi baki idon amarya tar akansu Allah ne kawai ya dinke bakinta batayi maganaba Dan kuwa taso tayi magana, an sayi baki kowa ya kama gabansa amarya ta tashi ta cire kayan jikinta dama sun dameta kuma gata da jin zafi kamar me, ta saka wasu kayan tana danna waya saiga farhaan ya shigo ta kalleshi shima ya kalleta ta mishi kyau itama ya mata kyau uhuuuuum ya zauna gefen madubi. Iffaat ya kira sunanta koni nan Jabo saida na jiyo bugawar zuciyarta, ta dago ta kalleshi, Ya fara yan maganan ganun da ake yiwa amarya sannan ya qara jadda mata cewa yanxu da da ba dayaba akwai haqqinsa akanta itama haka yana cikin mata nasiha sai yaga ta dauki waya hello tana dariya, shiru yayi yana kallonta tana rai nashi yana maganaba tana waya tsaki yaja ya kwanta abinshi ta qare wayarta itama ta kwanta nayita jira ko za'ayi wani Abu amma har na gaji ba wani bayani na fito abina..... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??66 Na Hauwa M.Jabo Taci pizzar sosai suna dan labari sama sama chan ya sako zancen auren ta da farhaan irin dai yana son ta amince ya nuna mata illar fushin iyaye akan yayansu, jiki a sanyaye tace mishi ta amince, Dan murna baisan lokacinda ya tashi yayi rawaba ya juya itama abin ya bata dariya nima Jabo abin ya bani dariya, yana ta saka mata albarka, yaje jikinsa na rawa ya gayawa mama da Yy Ali sun ji dadi ko ba komai sun yanke shawarar idan taqi aminta za'a bar auren.. *************** Magana ta kowane ban qare ta kan kama iyayen sai murna suke sunata shirye shirye, amma amaren kam ko a jikinsu, ana saura kwana biyu daurin aure saiga goggo da dijee da rukayya sunzo, koda sukazo iffaat tana skull Dan ita wannan shirye shirye bai hanata zuwa makarantaba, Koda ta dawo bakin qofar dakinta taga wasu takalmi Masu kama da kito amma dai na matane, ta shiga dakin saiga su dijee anyi arshe arshe tsakayar daki da yayanta biyu rukayya ko yarta daya da ciki ta kallesu ta kwashe da dariya harda durqusawa qasa Dan dariya, tayi dariya saida ciknta yayi ciwo suko sun tsaya kallon ikon Allah ta dago ta qara kallonsu nan ma ta kwashe da dariya dijee tace ke bamusun iskanci Dan kin zama Yar birni zaki ijiyemu kina mana dariya kamar Kinga tutu...!! ta harareta ta zauna da kyau tana dariyar tace wallahi mamaki nakeyi wai dijee da Yara har biyu! Ta qara saka dariya dijee ma sai ta dara, ta kalli yayan tace amma dai dijee kina dukansu ko? Rukayya tayi charab ta chabke tace ai yanzu duk bala'en dije akansune Dan har danbe tanayi da uwayen yara akansu, dijee tace ke rukayya banason sharri da zuwa ko gaisawa ba'ayiba zaki fara mini sharri, nan dai qawayen suka yini suna tadi suna dariya duk da qauyanci su bai sa ta gyamacesuba tunda itama chan aka fito sun cire mata kewa matuqa kuma bata bari suka gane cewa auren nata sai a hankali bane.... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 70 Na Hauwa M.Jabo Taje ta zauna sai ta kasa chin abinchin don an hanata fita kuma sai a hanata xuwa skull... Wasa wasa iffaat na Neman wata daya Gidan farhaan baya kulata itama bata kulashi amma rashin xamansa gida na damunta ko ina yake zuwa Allah masani kuma bata gane takunsa, Ranar tana zaune dabara ta fado mata yanda zata gane ina yake tafiya, bayan ya dawo gantalinsa na dare ya kwanta bacci, dama batayi bacciba tana jiransa ya dawo ya ijiye wayansa tana tabbatarda yayi bacci ta dauki wayansa ta shige bayi ta kulle ta danna power off screen din yayi duhu ta duba da kyau sahun hannunsa ya yake zana pattern dinsa bataci wuyaba tana zagaya yanda taga sahun hannunsa yabi tayi sa'ar bude wayar pattern dinsa ba wahala ma, tana budewa ta fara aiki, farko saida ta budamai Google account sannan taje play store tayi downloading din latitude tamai register dama tana dashi ta dauko wayanta tayi sending request ta karba shikenan ta gama da wannan duk inda yake matuqar data dinsa a kunne take zata Ganshi baya buqatar GPS latitude din, ta shiga SMS bata sami komaiba taje contact ba wani number da bata yarda dashiba harda searching na sunayen yan matansa data sani amma babu ta duba logs nan ma babu da qanqaro WhatsApp a kulle yake kuma da pin number kawai zai bude bata wahalda kanta ba taje gallery ba wasu hotuna daga nashi sai iyayensa sai kuma na margayiya Suhaila, gasunan sunfi 100 wani qololon baqin ciki da kishi ya taso mata ganin hotunan da Wanda suke tare da Wanda rake ita kadai amma ba nata ko daya kamar ta goge amma kawai saita fasa har zata fita sai taga wani folder ta shiga akwai wani aciki ko wanne an rubuta empty haka tayita dannawa saida ta wuce folder 14 sannan takai gunda aka rubuta Mrs PURHUUN, ta shiga ciki hotunan tane aciki daga kan wayanda ya mata lokacinda ta fara koyon gayu gun Yar baqa Dana zuwa qauyen da yayi wasu ma ya saka su a cikin frame mai heart wasu kuma itada Suhaila ne amma an gutsure Suhaila ko farahnax wasu ma batasan ya dauketa suba irin tana zaune dinnan tana shirme ko kuma tana surutunta tun kamin ta qare wayewa gasunan dai kala kala, mamaki da jin dadi suka mamaye mata zuciya ganin ya damu da ita hatta hotunanta a wayar, sai wani video da ta gani rawar da suka tabayine itada farahnax a daki sukayi video ko ina ya samu ohoooo tana tsaka da kallo taji yana qwanqwasa bayi tsoro da tashin hankaline suka baibayeta..... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 69 Na Hauwa M. Jabo Tace Idan da kana dukana ada yanxu akwai banbanci wata qila ada ina gyalewa ko kuma ina ramawa to ka sani yanxu akwai banbanci, ni matar aurece inada yanci kuma nasan yancina so ka kiyaye hannunka daga Taba matar aure.! Ta sake mai hannu da qarfi Ta wuce abinta ya bita da kallon Mamaki hadida zargin abinda ya kawota yi anan ya akayi tasan yana nan ya daki iska baima jira karuwarshiba ya fito da qarfi koda ya fito bata ba labarinta ya shiga mota gudu yake kamar ya ya hira sama koda ya isa gida bata isoba yayi kusan 30mnt sannan ta iso da ledojin abinci a hannu.! Tana zuwa ya daka mata tsawa ina taje? Ta kalleshi dukda taji tsoro amma bonewa tayi, ta danqaramar uwar harara, kamar ma bada ita yakeba, tana Neman guri ta zauna ya fincikota ke badake nake maganaba, ta kalleshi ido cikin ido tace mai inda yaje chan taje? Mi kikaje yi achan nanma ta bashi amsa abinda kajeyi achan shi najeyi.? Idonsa suka kada sukayi jaaa sun firfito waje iffaat kinsan abinda kike fada ya qara fincikota ya mannata a garu kinada auren nawa zakije gurinnan ? Ko kin manta ke matar

Chapter 7 of 10