Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
house girl kake rungumewa kana photo da ita?? Haba farhaaah kada ka mayar dani qaramar yarinya mana! no hafsa wallahi ba haka bane kin gane yarinyar batada wayo ko kadan kuma zata tafi gauyensune da umma ta dawo shine na siyo mata tufafi, kuma wallahi kinji na rantse umma tace in siya mata duk abinda take so, tunda ta kusa tafiya, kiyi haquri wallahi ba komai tsakanina da ita, mi zanyi da mai aikina, haba aiba class dina bane, yarinyace fa qarama ya kanne mata ido, ai dama ka gware a sweet mouth, yayi kissing din gefen fuskarta, muje daga ciki tana jikinsa har suka shigo, dakinsa suka wuce nan dai yachi gaba da rarrashi har mai afkuwa ta afku, nidai jabo idan zasuyi labewa nake sai sun kammala inshigo ciki, Allah ya shirya mana zuri'a kwanan hafsa biyu a gidan amma farhaan bai bari sun hadu da iffaat ba Dan a labarin data bashi ya gane ba qaramar yar ta'adda bace kuma bata mantuwa bare yafiya, daukar fansa gunta wajibine.. ********** Ayau ne su umma zasu dawo farhaaah Dan dole ya karbo mata tufafin da ya dinka mata atamfa biyu les uku, yace ta saka idan su umma sunzo ya bata turaruka da sure duk ta riqa sakawa, da yamma su umma da abbansu da farahnax suka iso farhaan ya rungume farahnax suna tafe suna tadi, da guduna naje gunta ina hajiya sannu da zuwa ta kalleni, iye yarinyar hajiya an girma an qara kyau haskene kawai bakiyiba har yanzu, ina zatayi haske tunda bata wanka, ta gaida Alhajin nasu ta gaida farahnax kaman batajiba ta qara gaisheta, da dalla mata harara, kin ishi mutane, haba naji mana, farhan ya kwashe da dariya, yace sister ba sauqi ai iffaat akwai naci tun xuwan iffat jininsu bai hadu dana farahnax ba, ta tabe baki, tajoyo gun hajiya tafara surutu batama bari su hutaba saida farahnax ta daka mata tsawa sannan ta natsu, Sumi sumi ta wuce dakinta bata qara fitowaba sai gobe da safe shima hajiya ta kirata tazo aci abinci, farahnax tana bacci lokacin da sai taga tsiya, ***** Bayan kwana hudu da dawowarsu, suna zaune hajiya da Alhaji suna kallo, saiga daya daga cikin yan matan farhaan tazo, tana zuwa taga iyayensa saita wayance tace kuskuren gida tayi, tana fita iffaat tacema hajiya wallahi qarya takeyifa hajiya qawar farhaan ce nan ma take kwana har dukana ta tabayi TOFA ZATA TONA ASIRIN FARHAAN MUJE ZUWA ...... [12:58AM, 5/1/2015] .: WACE CE ITA..?? 28 Na Hauwa M. Jabo Qawa kuma Alhaji ya maimaita?, eh lokacinda tazo tayi kwana hudu anan har na taba mata kaya ta mareni, hajiya tace amma dakinki take kwaniko?? Aah dakin farhaaah take kwana ai ba ita kadai bace sunada yawa, yace min duk qawayensa ne, yace wai anan wayewane, sabida nace mai mu qauyenmu iskancine, umma tace hardake yake kaiwa dakin nashi?? Aah hajiya ni kullum dukana kawai yakeyi, nan dai madam iffaat tayita bada labarinda ba'atambayetaba, ganin duk sunyi shiru ransu a bace yasa tasha jinin jikinta a ranta tace koda yaya farhaan yace aboki mace gun namiji a birni shine wayewa so ba komai bane, taci gaba da kallonta sukam tuni sun bar gun sunje daki domin tattauna xancen wayo farhaan Neman mata yakeyi.!!! Ran umma yayi matuqar sosuwa, saida tayi hawaye, Abba yayi ta bata haquri, Da yamma farhaan ya dawo da farahnax coz tunda suka dawo cikin yawo suke, umma ta turkeshi da ba zata! Tace mai dazu baka nan daya daga cikin budurenka tazo nemanka, ya Sosa kai budurwa umma?? Eh inaga bakuyi waya ka gaya mata iyayenka sun dawoba hala? Ko kuma tana sane tazo ta nuna kantane ko qawayenka zance a yanda kake cewa kai wayayye, nan umma ta shiga yimai fada kamar numfashinta zai dauke Dan takaici, iffaat ce taji magana fada fada tafito taga abin mamaki ana yiwa farhaaah fada, farahnax ta koreta, umma tace ta tsaya, taja ta tsaya, ai ita ta fada mana yarinya yar albarka, farahnax ta taso a fusace tazo gun iffaat kinyi muna funci kinji dadi munafuka kawai, iffaat tace haba daga fadan gaskiya saikice nayi munafunci ai ba qarya nayiba labari na baiwa umma kuma ni bansan fada zata masaba, kee ina magana kina magana sakarya kawai ta wanketa da mari, kamin ta sauke hannu tuni iffaat ta aiko mata da nata saqon Marin,umma tace that is very good iffat, ta gane very good coz malamansu na makarantar boko kamin a koresu yana cewa very good, idan aka bada amsa yaji dadi kin min daidai gobe sai ki qara dukanta, umma ta kalli iffat tace duk ta dakeki ki rama ran farahnax ya gama baci koba kamai ta girmi iffaat anxo ana siyamata raini a gunta. fau zata wuce dakinta, kowa yayi tsit a palon Abba yace ta dawo duk Ku zauna har umma ta zauna, ya kalli farhaan daya sunkuyar da kanshi a qasa tunda aka fara zancen, abba ya kalli farahnax da tasha mari umma nacewa good, ya kalli iffaat da tayi wani rasha rasha da ita a qasa tana kallonsu, Abba ya fara magana yace farko dai iffaat ba gulma takawo manaba labari ta vamu kuma da ita yarinyar batazoba da naxamu saniba, a yanda na fahamci labarin itama farhaan ya gaya mata, har take cewa a garinsu maiyin haka Dan iska shi kuma yace anan wayewace kunga ita bata daukeshi bad thing ba cox haka ya nuna mata, ya juyo ya kalli farahnax millions time na gaya miki ki daina saurin fushi, ke macece Aure zakiyi ba abinda haka zai haifar miki nan gaba sai nadama, iffat kin burgeni da kikayi jarumta irin haka amma ki riqa haquri kuma ki kula da Wanda ya girmeki, tace Tau Alhaji., ba ko wanne mutum bane zai iya yanda kikayi, kai farhaan bayan sallar maqreeb ka sameni a daki... Abba ya tashi umma ta bishi, farahnax ta juyo gun iffaat ke ni zaki Mara......?? [6:05PM, 5/2/2015] .: WACE CEE ITA..?? 29 Na Hauwa M. Jabo.. Farhaan duk da baiso yin maganaba saida yayi, lool farahnax ki fita hanyar iffaat ya fiye miki, banason kina biye mata yarinta Yana damunta kuma bakisan ko waye itaba, tace WACE CE ITA bayan house girl dinmu..! Nidai na fada miki ya miqe ya fita iffaat ma tashi tayi taje dakinta, tana zuwa tahau hada kaya, kawai ita dole ta koma qauye ita ba zata iya zama a gurin da tanaji tana gani a mata bata ramaba, sabida haka gara qauyensu, suci uban juna da yan qauyensu ******* Ki bari sai an kusa sallah mana, aah hajiya inason inyi azumi gidan mu, goggo ita kadaice a gida, kamar tayi goggo aikin takeyi, bayanda ba'ayi da itaba, amma iffaat ta rufe ido tace gida take so dole suka haqura suka barta.. sun shirya mata goma na arziki akace farhaan yakaita, baisan qauyen ba amma an mai kwatance sai ya gane ita kuma dama da an isa garinsu zata gane gidan su. Suna kan hanyar komawa yake gaya mata zai tafi karatu UK bazai dawoba sai bayan shekara uku saidai ya riqa zuwa hutu, ita kam duk daya a gurinta, Dan ta gaji da zaman birni ba abokai, sun Isa qauyensu yara kuwa tun daga farkon gari suke bin motar har aka shigo ainihin qauyen, iffaat tace ya tsaya, yace mun kawone tace kaidak ka tsaya, ya tdaya. leqowa kawai tayi ta kallesu batama fitoba gabaki daya yarannan suna ganin iffaat a mota suka watse, suna ihu wallahi ippatu ce kozo mi gudu, bawanda ya manta da ita, cox har yanzu su dije da rukayya ana xuba iskanci son rai a gari... Sun Isa gidan su ta tarar anyi ginin bulo an gyara ko ina abin ya bata mamaki, farhaan har ciki ya shigo goggo na ganin iffaah ta Hau salati, da mamaki Dan batasan zatazo yauba koda matar da ta dauketa tace mata qarshen wata zata dawo kamin azumi kenan tayi sallah gida sannan ta koma. Aka fara shigowa da kayan abinci kala kala, ita kanta iffaat batasan dasuba, sannan ga kayan sallar da umma ta mata kala uku shima farhaan ya dinka mata guda biyar ya qara biyu daga baya, goggo ma an kawo mata atamfa guda biyu baki yaqi rufuwa Dan murna.... Muje zuwa muji anya iffaat zata iya rayuwa a qauye ko yaya?? [6:11PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 30 Na Hauwa M. Jabo ************* Kamin kace kobo duk qauye ya dauka da dawowar iffaat chikin mota mai kamar jirgin sama. Ko ina sukasan jirgin sama oho!?? kowa zuwa yake mata sannu, wasu kuwa gulma ake zuwayi, bawanda yasan aiki tajeyi birni sabida goggo bata fadawa kowaba duk wanda ya tambayeta sai tace ai tana birni gun qanwarta, Su dijee an tafi biki chan nesa dasu, basu ji labarin dawowar iffaat ba sai da la'asar bayan sun dawo, suka zo ganin iffat, ganin ta ya sasu farin ciki koda batayi wani haskeba amma tadan chanza suka fara baiwa juna labari, iffaat natajin haushi anyi shegiya da yawa bata, cox dijee tayi hatsabibanci bayan tafiyar iffaat, tayi wata qawa ummulkhairi wacce itama hatsabibiyar gaskece, bata wasa hakadai take yanda suke, itama iffaat ta basu labarin ta'addancin da tayi barni, amma bata fadi cewa qawayen farhaaan bane, sunsha dariya matuqa, anyi kewar juna, A tunanina iffaat zata bar abinda takeyi a qauye koba komai anje birni kuma ta fara Dan wayewa tanason ta zama Yar gayu, Ashe ni jabo bangane bane, iffaat iskanci da la'ana sai abinda ya qaru, bare yanxu da suka zama su hudu, ni kaina ina tausayawa iyayen yaran, kowa kuka yake dasu a qauye sun gagari kowa ga iffaat an dawo. ****** Iffaat take tambayar goggo ya akayi aka gyara gidansu, goggo ta bata labarin cewa ai yayantane dake birni sukazo ganinta suka tarar batanan kuma suka tarar da babanku ya rasu, to su suka gyara gidan suka bata wata takarda wai duk lokacinda kika dawo ki nemesu, zasuzo su ganki, sun kawo min alkhairi kala kala daga birni, ainikan naci arzikin yayan kishiya, Wannan karon Goggo bata tsangwmawa iffaat kaman daba, shi yasa suke zaman lafiya, ba ruwanta da harkarta itama haka, Ranar suna hira da goggo take cewa Wai ihhatu a birni bakiyi saurayiba, ta zare ido ta dafe qirji saurayi goggo!!! nida ko fitabanayi, nan iffaat ta gayawa goggo aikinta goggo taji tsoro, Allah yasa dai baya biyoki da dare, daga ke saishi a gida ba koea. iffaat tace taaab nida ko shiri bama bamayi, nan ta fadawa goggo ta'addancin da tayi,goggo bataji dadiba koda dama tasan za'ayi haka, nan goggo tadan fahimtar da iffaat yakamata ta gane ta girma yanxu tadaina shirme da shiririta, kina ganin idan kikaci gaba da haka zaki sami mijin Aure,?? a qauyen nan fa ba yarinyar da ta tabayin jini a gida, taji raaaas ta tuna itama tayi sau daya a birni amma bataabaiwa goggo labariba, ******* Maganganun goggo sun dan ratsa iffaat har ta fadawa qawayenta su daina tsokana ko su rasa mijin Aure duk da cewa basu dainaba amma sun rage kwarai saidak idan an musu suna ramawa, haka kuwa akayi sunyi sauqi sosai, har takai suna gaida mutane a hanya, amma fa idan ka tabasu zakaga bala'ee da masifa..... [6:17PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 31 Na Hauwa M.Jabo Rayuwa tana tafiya ayanda aka sameta, Tun bayan komawar iffat qauye takejin garin baya mata dadi amma bata gane komaiba sai take dauka kamar sabon da tayi da mutane birnine suma birni sunyi kewar iffaaat sundan saba da ganinta da tsiwarta idan sun tuna sai suyita dariya, idan ma farahnax tana magana akan rashin kirkin da iffaat ta mata sai su nuna mata ai itace batada gaskiya, akan me zata daketa,kusan duk bayan iftaar idan suka zauna sai anyi labarin iffaat tun farahnax bataso har abin itama ya riqa bata dariya kuma yana burgeta, duk Wanda yaji shaqiyanchin iffaat sai ta burgeshi, umma dai ta kula farhaan yaji dadin zama da iffaat, ranar bayan buda baki umma take cewa inaga bayan sallah mu tura azo mana da iffaat, naga duk kowa yaji dadin zama da ita, tunda yanxuma kaga bazamu komaba kai kadai zaki tafi ka kammala karatunka , koya kuka gani, eh umma duk sun amince, Iffaat ma zaman qauyen baya mata dadi matuqa kuma tanajin dadin harka da qawayenta saidai mafi yawan lokaci takanji tayi kewar umma, duk ta zauna takanyi labarinsu, amma bata bada labarin farhaaah, ************************* Yauda gobe ba wuya a gurin Allah, Ramadan ya qare anyi sallah lafiya su iffaat yan mata sai gantali akeyi a gari, ba mijin aure, ba mashinshini, abin yana damun iyayensu bama dijee ba da take yar lukuta ga manyan duwawun da suke biye da ita, gasuda tsini idan tana tafiya sai ta Dan duqe cox suna mata nauyi nima Jabo Dana ganta na dauka turosu takeyi, ita rukayya dama kamar bulala take, iffaat kuwa hips ne kawai take dashi mazaunanta basuda tudu irin na dijee dijee a gida tsini ake cema dijeee sabida tsinin maxaunnan ga gafafuwan nan nata kamar doya, qirar maxa takeda Allah ne kawai yayita mace... Akwai wani mai tura kura yana saida ruwa duk qauyennan shi kadai yake saida ruwan masu dadi, yakan sakawa ruwanshi alim idan sukayi kyau sai ya fita saidawa yazo neman auten dijee kuma an bashi, shima kasada yayi dan duk qauyen nan bai samu mataba sabida tsananin muninsa sai yazo neman Dije iyayenta suna Neman kai da ita tuni suka sallama, rukayya kuwa wani Dan uwanta za'a hadata dashi, su ippatu daikam ba Kowa har yanxu. Bayan sallah da sati biyu.... Ranar iffaat da qawayenta sunje yawo sun dawo sukaga mota mai kyau iffaat tasa aranta kamar tasan motar amma ta manta ina tasan motar, tana sanye da atamfarta ta sallah da yake yanxu gayu sukeyi an daina yawo ba takalmi duk sun iya acuchi maxa ataqaice duk qauyen ba Wanda yakaisu gayu da iskanci, motar ta tsaya gabansu farhaan taga ya fito daga motar, ai da gudu taje ta rungume shi, ba tareda damuwaba tanata dariya, su umma suka fito ai batasan dasuba tasaki farhaan taje gun umma ataqaice dai taji dadin ganinsu matuqa, farhaan rungumeshin da tayi yaji qamshin sure din daya bata yace kullum ta riqa gogawa Rexona na aloe vera ne kuma long lasting protection ne yace lallai yarinya ta waye harda saka turare.... [6:24PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 32 Na Hauwa M. Jabo Sun qarasa gidansu iffaat goggo tagansu ba zata duk da batasansuba amma ta gane farhan goggo harda tuntube Dan tsabar rudewa, baki kuwa har kunne tasan cewa zata samu alkhairi zuwansu, ta musu shinfida aka kawo musu fura sabuwa aka siyo nono aka xuba a cikin furar sun kwashi damu lafiyayye farahnax hadda santi da yake goggo ba qazama bace su iffaat ne dai ragajabul, mutane sai zuwa kallon su akeyi, iffaat dai bata gaida farahnax ba, ke ko kallon gefenta batayiba, iffaat tace wa farhaan yazo ta kaishi yaga gari, yakuwa biyota sun zaga garin tana nuna mai guraren da tayi hatsabibanci sunata dariya ko ina kallonsu akeyi wasu suna gulma ana cewa ta lalace, har yanzu ba miji amma ba halin magana yanxu mutum yaji ba daidaiba ba Wanda zai iya tunkararta da zancen rashin miji, dasu dijee aka zaga garin duk gunda ya masa kyau sai ya tsaya ya dauki photo har sukaje bakin ruwa, suka shiga kwale kwale yayi hotuna sosai, qarshe yayi photo da iffaat bakin ruwa, hotunan sunyi kyau sosai iffaat tayi haske yanxu cox kullum sai sunyi wanka tanason ta zama yar gayuuu.... Bayan sun dawo gida umma tace miyasa bamu tafi da farahnax ba, iffaat tayi sauri tace au dama tare akazo da ita?? Ni banma gantaba sai yanxu. Taci gaba umma kinsan farahnax ta tsaneni har na baro birni batamin magana, shiyasa nima na fita harkarta, kowa sharhin nata ya bashi dariya. duk suka kwashe da dariya, nan dai aka shiryasu sundaina fada, Su umma suna son a basu iffaat taci gaba da musu aiki, koda ba aiki takeyiba yanxu kamar yarsu take Dan Allah yasakawa umma qaunar yarinyar, dama ga iffaat akwai shiga rai, ran iffaat baiso tafiyaba amma idan ta tuna abinda goggo tace mata sai taji gara ma tabar garin wataqila birni ta samu miji tayi Aure, Sun tafi akan nanda sati daya za'a aiko a tafi da iffaat Sun ma goggo alkhairi sai washe baki takeyi, itakam yayan kishiya sun mata rana, koda bata haihuba ta moresu. **** Bayan Sati daya akaxo daukar iffaat ta buga qafa a qasa akan ita sam baxatajeba sai anyi bikin qawayenta dijee da rukayya, goggo tasata daki, ta mata huduba, Yanxu idan kika zauna har bikin su wallahi gulmarki kawai zasu riqayi ace har qawayenki sunyi Aure ke bakiyiba kinga ba dadi haka, gara kije birni abin ki, ki raqayin gayu kamar yar yarinyar nan danaga sunxo da ita har ki sami miji Dan gayu irinki kiyi aurenki a birni, idan kuma zama zakiyi bakin mutane yakamaki to shike nan. Maganar goggo ta shigeta , gara birni da qauye, ta hada kayanta taje tayi sallama da su dijee ransu baisoba tana babbar qawa ayi bikinsu batanan amma ba yanda ta iya itama taso ayi da ita, amma goggo ta hore mata kunne...... [6:46PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 33 Na Hauwa M. Jabo Iffaat an dawo birni system dinda Dana yanxu ba daya bane cox yanzu aikinta yafi Nada sauqi yanxu dakin farahnax take gyarawa Dana umma... Ranar iffaat ta qare aiki tana zaune ita kadai a Palo umma da Abba duk sun tafi aiki farahnax ta tafi skull taji sallamar mace ta amsa tashigo, wa zata gani yar baqarta, wacce take kwaikwayon gayu a gurinta, batasan lokacinda ta miqe tsayeba ta washe mata baki ta gaisheta a mutunce kamar ba itaba, yar baqa ta amsa tana mamakin waye wannan mai fara'a haka, duk da har yanxu da sauran qauyancinta batayi kama da house girl ba, ta zauna tana tambayar farahnax, tace ai ta tafi makaranta, amma ta kusa dawowa, suna zaune ta kawo mata ruwa da abin tabawa iffaat sai satar kallonta take, aranta tace ita ba wata kyakyawa bace sai iya gayu, Allah ya nuna mata ranarda zata zama Yar gayu irin wannan. Tana chikin tunani saiga farhaan ya fito, tana hangoshi sai naga ta sa hannu a jaka ta dauko turare ta qara fesewa a hankali ta mayar da sauri, batasan na gantaba, ta gyara zama tana wani murmushi. Farhaaah ya Iso, Tana wani kashe murya, yanda tamin magana daban yanda tamai daban wato akwai banbanci tsakanin mace da namiji ko duk chikin gayunne,?? Yaya farhaan kayi wuyar gani, ya dan sosa qeya abubuwan ne sai a slow zainb, ya kike yasu hajiya? Lfya lau tana wani maqe murya, araina nace dama sunanta zainab dama sai ita ance duk zainb haka suke da rawan kai da kurin banxa.. yanda take masa duk sonda nake mata sai naji lokaci daya na tsaneta, ta bani haushi, narasa dalilin da yasa raina ya baci.!! Kodai dan ta cika kurine yasa haka oho, hira suke dashi tasaki jiki tana fari da ido tana kashe murya tana Neman gindin zama, Ihuuun farahnax naje zainb khalifa kece gidan mu haka? Kai I miss much wallahi tunda kikazo bangankiba ina kika shigane? Wallahi karatunne kinsan sai a hankali,! hahaha hadda Ku gifted karatu na Baku wahala, chaiii dariss God oooooo, farahnax akwaiki da zolaya,sukasa dariya tajata suka wuce daki... Bayan sun wuce farhaaah ya juyo kaina yan mata yar gidan umma, har yanxu ba'a iya gayun bane, na harareshi na zubar Dan duk na tsaneshi duk haushi yake bani daya biyewa wannan zainb din, ya min kallon banganeba Mina miki kuma? namai kallon ya rage naka ni tashi na wuce dakina, na barshi yana mamakin mi ya faaru yarinya kamar hawainiya lokaci daya sai ta sauya, bayan da safee sun gaisa koma miye ya rage nata. ****************** Farhaaah yaune zai wuce Canada karatunsa, ana tadin rabuwa naji yana cewa yakamata asaka yarinyar chan makaranta, umma tace itama tayi wannan tunani Dan ranar taga yanda take sallah ban iya komaiba hatta alwula ma bata iyaba Kowa ya aminta da shawarar farhaaah na Sanya iffaat boko .. Farhaaah dai ya baqunci Canada yabar iyayensa da kewa. Muje zuwa muji yanda su iffaat za'a fara karatun boko idan ta waye ya style din zai koma.!!! [9:55PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 34 Na Hauwa M.Jabo ************** Tun ranarda farhaaah yabar naija gidan yake yiwa iffaat duhu da girma tin bata baiwa abin muhimmanci, amma tana damuwa matuqa yanxu har taji abin yana neman ya gagareta, haka takejin zuciyanta na wani bugawa duk lokacinda ta tunoshi, idan aka kira sunanshi sai taji kamar zuciyanta tafito waje, ta rasa gane yanayinda takejin ita ba wayoba bare ta gane cewa ta kamu. A duniya iyayen farhaan sunada kirki kuma sun mata halacci a rayuwarta a matsayinta na yar aiki amma sun mayar da ita kamar yarsu An nema mata mai lesson, haka an sakata makaranta tana zuwa, haka tana zuwa gun malamin hadda da farahnax suna karatu tare, gata da saurin fahimta so gun lessen da yawa ake mata karatun, Duk karatunnan da take lokaci daya idan ta tuna farhaaah sai taji ta manta komai hatta takan manta WACE CE ITA, In short rayuwa a gidan bata mata dadi ko kadan, umma tasha tambayarta mi yake damunta amma saita fuske tace ba komai idan aka matsa sai tace ta tuna babantane!! Sau tari zuciyanta takan mata qunci taji batason jin komai sai taje lanbu ta haye bishiya tayi kuka son ranta, ba Wanda yake jinta a gurin, idan ta qare ta dawo gida idan ma idonta sun nuna takance bacci tayi, ******** An Sami Hutun makaranta anan farahnax tasa rigima sai an tafi Canada gun Yaya farhaaah, da yake ita iffaat karatunta a baibai yake shi yasa takeshan wahala a gun lesson yanxu haka ko Hutu batada sabida anason a mata jumping to jss3 hakan yasa karatun ya danqaremata. Sun shirya tafiya canada Abba ya kaita gidan wani abokinsa Ajiya har su dawo daga Canada din. Kuma yace yarsace, gidan sunada mutunci abinda ya bani mamaki shine nan ne gidan su Yar baqa wato zainb khalifa sun mutuntani coz Basusan gaskiyar Wace ce ni ba, Dan zaman da nayi gun zainb khalifa na koyo abubuwa ba kadan ba gata very friendly saidai tacika rawar kai da jiji dakai sai qaryar yaruka kala kala, gashi malama iffaat yanxuma take koyon turanci bare wani yare, Dan sati ukun da nayi da yake zainb akwai surutu sai na rage jin zafinda da nakeji idan na tuna farhaaah, Allah mai iko tanason tayi tadin farhaan da yar baqarta idan ta tuna WACE CE ITA sai taja bakinta ta dinke,Dan ta kula kamar Yar baqa bunsurace Kowa so takeyi. Satin su umma uku suka dawo, sun mini tsaraba kamar nice yarsu, ba abin da yafi bugeni kamar kayan da farhaan yace a kawomin, da body spray na Rexona da sure, idan naji qamshinsu yakansa na riqa wani tunanin da ni kaina bana gane mi nake ciki .. [10:02PM, 5/4/2015] .: WACE E ITA..?? 35 Na Hauwa M. Jabo A cikin kayan da Yaya Farhaan ya siyomin hadda waya wai mu riqa gaisawa, ranar da aka bata kayan Dan murna ko bacci takasa yi, kuma wannan abinda takeyi bata gane komai, ** wayar ni ban iya komaiba hasalima nidai saidai na gaisa dashii in miqa musu, tawa wayar kullum tana qasan pillow karatu ya sakata gaba, ga abinda ta daukarwa kanta tunene tunanene... farahnax ta koya min yanda ake amfani da waya, ta kira min yaya farhaaah munyi waya dashi, Wanda tunda ya tafi saudaya muka gaisa shima ina fara magana ta tsinke, Mun gaisa sosai yanayi yana jefomin English ina ganewa amma bana iya bashi amsa, har yan kudin dake cikin suka qare abinka da international call.. Bayan kaman kwana hudu ranar na dawo lesson ina danne danne a wayar kawai tayi karo da maganar da sukayi da Yaya farhaan, zan iya CE muku duk yinin ranar abinda ta saurara kenan, ta rasa mi yasa komai nashi burgeta yakeyi, bama kamar idan taji dariyarshiba, itama saita dara haka take zama ta miqe gafafu tayita saurare tana dariya, wannan voice yasata walwala ranar farahnax taso ta gane sai kawai ta daina saurare dan bata iya delete ba, Sai yanzu ta gane mi wannan takardar da goggo ta bata tace yayyenta sunce ta kira take nufi, Ta nemota a cikin kayanta ta saka amma wayar tata ba kudi, ta je gun farahnax tace ta kira mata wannan number, farahnax kuwa chatting takeyi bazata iya bata wayantaba sai ta saka mata recharge card na 1,500 ta saka mata number tace ta kira, ta koma dakinta haka tayi ta kira ba tareda tasan kiran yana shigaba saida ta bar miss call 47... Ameen bayan ya dawo yaga miss call da yawa sai ya kira, Tayi sallama, ya amsa yadauka mamarshi ne Dan kusan muryarsu iri dayane, mama lafiya kira haka ?? sai tace ba Maman shi bane ya tabbatar da wrong number ne sai kawai yace wrong number ya kashe, bai tsaya yaji abinda zataceba, Itama dataga haka sai bata qara kiran number ba, *************** Kwanaki sun tafi iffaah ta waye iya wayewa kamar ba Yar aikiba, wani lokaci Idan sunfita tareda farahnax bazaka ganetaba cox tafi farahnax kyau nesa ba kusa ba, saidai har yanxu qauyancinta da yake nuturally ne sai bai saketaba tana taba abinta, gata bakinta baya shiru duk abinda ta gani saita tambaya gata a waye a dressing amma a aikace har yanxu da saura... shekara ta zagayo iffat zata koma qauyensu Dan sallah da azumi achan kamar yanda sukayi alqawari run farko,ta rasa gane dalilin da yasa ranta bayason komawa qauye kodan zancen goggo ne da take cewa za'a saka mata ido a qauye tayi zamanta birni! ko kuwa rabuwa da iyayen farhaan da, ko mahaifiyarsa ta kalla sai taji sanyi sabida tsabar kamarsu da farhaaah..... [10:05PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 36 Na Hauwa M. Jabo ************** Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa da da iyayen farhaaan.. Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da takeyi. Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba, hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah, sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa rashin gane takamammen abinda yake damunta. Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce. Hello Ta amsa tanajin dadi Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi bala'en bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye, na rashin dalili ta yi shiru. Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa duk lokacinda take tunanin yaya farhan take shiga wani

Chapter 4 of 10