Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hali?? Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba?? Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ?? Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi?? Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko daya. Tayi wani tsaki Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi fiffike taje ta Ganshi, Amma ba halin yin haka, Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada labari har yanxu ba tasan miye soba.. [10:11PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 37 Na Hauwa M.Jabo *********** Kwanaki sunja gaba har anyi sallah qarama, iffaat zata koma gidan aikinta a birni, tun lokacin da farhaaah yazo batayi waya dashiba jifa jifa tana kiran su umma ta gaidasu, kuma farahnax tana turo mata recharging wayanta. Ta shirya tsab sai birni, Su umma sunyi murnar zuwanta matuqa ko banza umma nasonta Dan akwai bada labarin ban dariya kamar me shi yasa daga umma har Abba zaune sukeyi tana basu labari suna kwasar dariya. Wannan karo an samu chanxi iffaat ta dawo amma ba komai tsakaninta dasu, musamman umman farhaan kunyar su takeji! Da kuwa zaune take tasasu gaba tana basu labari suna dariya, gashi kullum tanada sabon labarin da zata bayar, bata maimaici amma yanxu Dogon motsi bata iyayi gabansu, Ashe akwai abinda zai iya chanza wannan hatsabibiyar yarinya,?? Hmmm sai soyayyah.. soyayyar da ita kanta batasan tanayiba, Kai amma ni jabo na jinjinama duk soyayyar da tayi tasirin chanxa wannan yarinya koda ta qara wayewa yanxu... ******* Iffaat miyasa tunda kika dawo kika daina bamu labari?? ta sunne kai qasa tayi murmushi ba komai hajiya! Nidai wannan zuwa hutu baiyimin ba yarinya duk ta susuce sai rama takeyi? Ko wani Abu ya faru bakyason fada mana?? Laaa hajiya bakomai Abba yace ki kyaleta kinsan fa ta qara girma hankali yana shigarta, duk aka saka dariya, Farahnax ce ta shigo tare da wata yarinya kyakyawa zatakai 24yrs kyakyawace sosai, tana shigowa tace kinganta, yarinyar mai amsa sunan suhailah ta gaida su umma da abba a kunyace, ta kalleni cikin fara'a tace Ashe ma qaramace sosai gata kyakyawa kuwa saidai tafini kyau da kike cewa munyi kama., umma tace ai kuwa nima sai yanxu naga wannan kama da kuke cewa sunyi, saidai yata iffaat tafi kyau, sukayi dariya gaba daya iffaat ta gaisheda suhailah umma tace kuje daki mana, suka wuce umma tace na bisu mama na tashi na bisu, anan farahnax take baiwa Suhaila labarina sunata dariya, sai nadan saki jiki dasu dama wani lokaci zaman kadaicine ke haifar mata da damuwa bata saniba.. Suna tsaka da hira wayar Suhaila tayi qara, ta dauka tana kashe murya, duk da cewa da English suke maganar hakan bai hanani fahimtar dawa take maganaba kuma mi suke fadaba, farahnax tana bani labari amma hankalina Sam baya tare da ita qirjintane ke dukan uku uku wani baqin ciki Mara dalili takeji Wanda ya haifar mata da rashin natsuwa lokaci daya, Daidai nan kunnenta ya jiyo mata maganar da takasa tantance sanadiyar rudewarta sai ganinta tayi a asibiti....! [12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 38 Na Hauwa M. Jabo Tana bude ido taga Su umma sun zagayeta Yar budurwar na zaune gefenta itada farahnax, sai nan ta tuna da abinda kunnuwanta suka jiyo mata, LAAA KINGA NA MANTA IFFO BANGAYA MIKIBA, KINA QAUYE AKA YIWA YAYA FARHAAN BAIKO DA SUHAILA..!!!! Hawaye ne suka wanke mata fuska shaaaaar, idan bata mantaba Wannan maganar itace qarshe maganar da taji sai yanxu da ta farka ta ganta a asibiti, ta motsa hannu taji yayi nauyi ta qurawa Suhaila ido mi yasa taji tana Sonta aranta?? Amma sai take ganin kamar ba sontane takeyiba tsanarta takeyi,?? Tanajin Suhaila har cikin ranta amma kuma tsanarta tayi yawa a zuciyanta. tana tsaka da tunani umma ta dafataa ta mata sannu, ta kalli umma tace hajiya miya faru?? Ya akayi mukazo asibiti? Umma ta bata amsa da kin samu sauqi dai ko? suna haka sai ga nurse tazo ta dubata aka tabbatarda yanxu ba abinda yake damunta, illaa kawai ta rage tunani.... Ta tashi zaune anan farahnax ta bata labari muna tadi dake nake gaya miki an yiwa Yaya farhaan baiko da Suhaila sai kawai naga kin danne kai kina juyawa kika miqe tsaye sai kuma naga kin kika fadi sumammaiya, Suhaila ta katse wayar mukayo kanki muka kira umma taxo aka saka miki ruwa amma ko motsi daga qarshe sai Abba yace a kawoki asibiti, farahnax tace miyake damunki iffo?? Tunda kika dawo gida kika chanja ko su sukace miki ki riqa yi mana haka? Wallahi iffo banajin dadin ganin ki a haka, Dan zaman da mukayi na Saba da tsokanarki da labaranki Masu dadi, shiyasa ma na kawo Suhaila itama ki bata labarai sai Kuma haka ta faru, please ki saki jiki damu ke Yar uwarmuce kinji.!? Aranta tace da nasan abinda yake damuna Dana fada kodan samun natsuwar xuciyata.. Ta kallesu tayi murmushi ba komaifa, sai tayi shiru hawaye suka gangaromata,umma ta matso Ku bar min yarinta ta qarajin sauqi sannan Ku fara mata jarida. Dukansu suka saka dariya har iffaat din saida tadan murmusa. Saida ta kwana daya da yini sannan aka sallamesu. ** sun koma gida umma da farahnax suka sa iffaat gaba sai ta fadi abinda yake damunta. Amma ta murje ido tace bakomai koda yake ba komai din tunda ita kanta batasan abinda yake damunta ba, nifa tinda ta dawo Hutu banga dariyarta sau ukuba, umma tace nimadai banganiba umma ranar abbanku yace a kirata ta bashi labari amma tazo ba wani labari, Iffaat!! Na'am hajiya! Ki mana magana zama damune kike gajiya dashi ko kuma wani yake quntata miki ko kuma wani Abu yake faruwa a qauye?? Kawai sai ta fashe da kuka, kuka mai tsuma zuciya, ita kanta batasan sanadin kukanba, sukayita rarrashi har tayi shiru, ki fada mana minene idan mune mu gyara muryan ta a dishe tace wallahi Baku bane hajiya, nima wallahi bansan abinda yake damunaba haka kawai idan ina zaune sainaji raina ya baci ko kuma na riqajin inason wani Abu amma bansan ko miyeba qunci yamin yawa hajiya ta qara fashewa da wani kuka, sukayi chirko chirko, chan iffaat tace mamarta takeso ..... [12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 39 Na Hauwa M. Jabo Umma ta nunfasa tace idan wannan ne damuwarki karki damu xamu nemo miki mamarki duk inda take, ta danyi shiru amma jifa jifa takan zubarda hawaye, bayan kwana biyu, muna zaune palo nidai kamar hoto ko nace gunki kawai cika wuri nakeyi. Suhaila ce ta shigo ina ganinta naji qirjina ya wani buga, da Leda a hannu, tana murmushi ta gaida umma tace nazo dubiyar mara lafiyane suka saka dariya ai ga tanan taji sauqi, ta zauna tamin ya jiki, na amsa mata inata kallonta har tadan tsargu, suhaila tace iffaat wallahi kinyi kama da qanwar babanmu sosai saidai tafiki haske amma hatta gashinki irin natane ke ko murmushinku iri daya tafiyarku ma iridayace ke hatta maganarku iri dayane ke komai naku iri daya, duk aka saka dariya har iffaat din ganin yanda Suhaila ta jajirce da bayani, sai kun sami lokaci kixo muje gidan mu ki ganta a gurinta nake zaune, iffat ta amsa da insha Allah.... ***** Iffaat dai bata gane karatu yanxu, gashi an mata nisa sosai abubuwan da bata yisuba a lesson take samu a namatasu, karatun ma haushi yake bata yanxu, zaman gidan ya gundureta, idan har aka zauna Idan ba hirar farhaan akeyiba bata taba samun sukuni a rayuwarta, wutar sonsa kullum Dada ruruwa take a zuciyarta amma har yanzu bata gane cewa she is fall in love ba... Yar baqa qawarta tayi tambayarta har ta gaji sai tace ba komai, to batasan mi yake damunta ba bare ta fada, Zaman birni ya gagare iffaat, kusan kullum saita xubar da hawaye wace irin rayuwace wannan?! ta matsa musu akan ita sai ta koma gurin iyayenta ta gaji da zama anan, aka buga sama da qasa amma taqi amincewa har suka gayawa abba, Ranar yasa aka kirata ya tambayeta ko ana mata wani abinne tace ba abinda ake mata, iffaat bamu daukeki a matsayin Yar aikiba a matsayin Yar cikinmu muka daukeki wannan dalilin yasa har muka damuwa da damuwarki, muka sakaki makaranta Dan kema ki sami gata da yanci irin Wanda ko wacce yarinya take samu a gidan mahaifinta, iffaat kamar jiran abba take ta fara kuka kamar ranta zai fita, Abba nagode da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da alkhairi, abba wallahi ni kaina bansan abinda yake damunaba rayuwata bata min dadi ba abinda yake burgeni a duniya komai haushi yake bani, banason naci gaba da wannan hali na damuwa kuma na sakaku akan shakkun kanku, wallahi kun min komai a rayuwa kuma na gode, wata qila Idan na koma qauyenmu tunda nasan yayyena suna zuwa nemana wataqil Idan nagan su in sami sassauci. Amma Dan Allah Abba Ku mayar dani gida taci gaba da kukanta...... Tofa muje zuwa muji anya zata iya rayuwar qauye? Yama za'ayi ta gane cewa soyayyah ce take damunta...??! [11:44PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 40 Na Hauwa M.Jabo Abba Ku taimakamin ku mayar dani gidan mu, jikin kowa yayi sanyi yanda take kuka kamar ranta zai fita ta basu tausayi koni Jabo ta matuqar bani tausayi Dan saida nayimata qwalla, tabbas So bala'eeee ne, yana zautar da mutum ya rasa mi yake masa dadi yama rasa gane kansa,! zaiyi loosing din control dinsa ne gaba daya, ko manya ya suke fafatawa da soyayya bare yarinya Yar shekara 15 irin iffaat da har Yanxu batada wani wayo bare har ta gane wane hali take ciki.... Abba yace To ki daina kuka iffaat za'akaiki gida dama Dan kada ya zama mune muke shiga haqqinki ba tare da mun saniba amma tunda kince bakomai kin zabi hakan shikenan, dukansu basu ji dadin tafiyar da iffaat zatayiba, amma ba yanda suka iya dole su saka mata ido, farahnax ma ta sameta a dakinta tana kwance bayan ta hada kayan ta, yanxu iffo tafiya zakiyi ki barmu?? Muka miki dan Allah da har bakya iya zama damu?? Ta kalleta tace sister wallahi ba haka bane bakumin komaiba, kawai rainane baya min dadi kuma bansan dalilin hakanba, kuyi haquri Dan Allah, anan dai sukayi hirar qarshe, koda iffo taqi sakin jikinta... sun mata goma na arziki suka bata kudi masu yawa sannan akasa driver yakaita har qofar gidansu. Shikenan iffaat ta baro gidansu farhaan..... ******** Iffaat a qauyen su, Ashe yanzu bala'en yake bata saniba, yanzu take qara shiga damuwa yanzu take gane cewa ganin iyayen farhaaan rahamane gareta, amma kuma still bata gano hakanba, ganin su da takeyi yana raqe mata qunci matuqa, ta sukukuce kamar ba itaba kai duk Wanda yaga iffaat sai yayi mamakinta bata magana, Yar gayu kam da take burin zama ta Riga ta zama, saidai so silent yanzu take yanxu. goggo har tana tsoro kardai ba abin kunya tayo aka korota birnin ba!! ******* Watan iffat biyu a qauye ba walwala kullum fuskar nan a turnuqe kamar ta dijee dama dijee haka take ba sakin fuska su iffaat ne masu dariya, yanzu kam iffaat ta zama Yar baqin rai fiye da dijee.. Ranar iffaat ta tashi da ciwon cikinta har Yanxu goggo batasan ta fara period ba tasha magani ciwon ya fada mata tana zaune cikin runfar qofar dakinta da Dan tsinke a hannunta tana tsane a qasa taji sallama ta amsa batareda ta dago kaiba tsul goggo ta fito daki tana washe baki na dago kai na kalleshi, ke ihhatu bakiga yayanki yaxoba, koda na Dade ban ganshiba hakan bai hanani ganeshiba Yaya nane! Taje gunsa na fada jikinsa tna kuka shima dai yayi gwalla, suka zauna saman tabarma, Yaya Ameen yake cewa goggo kinsan kuwa ba nan nakeda niyyar zuwa ba sai naga na biyo ta kusa danan nace bari na shigo qauyen namu in gaisheki, Ashe rabon naga Yar mamane kullum zancenki take mana, nayi murmushin jin dadi Dan uwa Rabin jiki ciwon cikinta tuni ya ware sai murna takeyi tana xubar da yan hawayen murna.. Nan take Ya kira Mama ya gayamata ai gani ya sameni yanxu mama murna kamar ta kasheta yau taji autanta munyi magana ta ita inatajin dadi, Anan aka kitse akan gobe Yaya zaizo ya fafi dani daidai nan na Dan shirya, goggo ranta baisoba don iffaat ce rufin asirinta gata ba da bare jika..... [11:48PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA 41 Na Hauwa M. Jabo Tun da safee iffaat ta shirya kayan da take buqata sai rawar jiki takeyi duk da har yanxu zuciyanta a qunci take hakan bai hanata zagwadin ganin mahaifiyarta ba, goggo ta sakata taje tayi ban kwana da mutanen , taje tayi bankwana dasu, wasu nata mamakin natsuwarta kowa na fadin albarkacin bakinsa, taje gidan qawayenta dijee da tsohon ciki abin sai Wanda ya gani, tana tsaka da ban kwana akace mata yayan ta yazo zasu wuce, a gurguje tayi sallama ta dawo gida... Ranar goggo tayi kuka kamar ranta zai fita tana ganin kamar hanyar samunta duk ta to she kenan... ta manta samu da rashi na Allah ne.... **************** Guraren 6 na yamma suka Isa zaria birnin zazzau amma iffaat anyi bacci a mota so bata gane garinba, direct unguwarsu aka wuce da ita gyallesu, iffaat sun tararda mama tana ta gyare gyare tarbon autarta, tana ganina taxo ta rungumeni tana yan hawaye, nima hawayen nakeyi Yaya Ameen kuwa yanata dariya, yace mama murnace haka harda kuka haba miye aciki Dan ba iffaah tunda nida Yaya Ali mumanan, dama kullum ta damesu da zancen iffaah autarta, mama ta harareshi ai kowa matsayinsa daban, taja autarta suka wuce daki suna marmarin ganin juna, a takaqaice zuwan iffaat yayimusu dadi babban yayan su mai suna Yaya Ali shine babba kuma Allah ya azzurtashi matuqa tun bayan rabuwar mamansu iffaat da babansu ta dawo birni gurin yayanta dama chan su yayyen iffaat gurin yayan mamansu suke suna karatu so basuyi zaman qauye ba iffaat ce kawai gurin mamar kuma da suka rabu da baban sai ya kwace ta da qarfi da yaji... Yaya Ali Allah ya azzurtashi sosai bayan business da yakeyi tareda qanin mamanshi yana aikin Kaduna in short dai suna shanawa wannan gidan ma da suke ciki shiya Gina ma mamashi... Iffaat ta kalli gidanda suke ciki aranta tace wannaan gidan kenan gadansune zatayi duk abinda take so bawanda zai hanata rayuwa sabuwa jin dadi sabo komai sabo saidai batasan bazata iya chanza kuntacciyar xuciyartaba.... Lol. [11:57PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 42 Na Hauwa M. Jabo Rayuwa gidan mahaifiyarta Yana mata dadi matuqa tana samun gata ta kowane fanni, Sai yanxu ta gane cewa wannan garin garinsu farhaaah ne, koda ko za'a kasheta bazata bata gane gidan su farhaaan din amma dai ta gane makarantarda aka sakata da tana gidansu farhaaan nan guraren PZ ne. Yanxu kuma Hall Mark international school aka sakata kuma duk gurare dayane... mama ta samo mata mai lesson Yana mata a gida, islamiya ma tana zuwa anan unguwarsu ta gyallesu, saidai a tunanin iffaat xuwa gidansu gun mahaifiyarta zai sa ta daina damu wa batasan ba anan gixo yake saqaba ita zuciya kawai burinta takai ga wannan abin da takeso idan ba hakaba kuwa ba zaman lfya.. ***** Wata rana maman iffaat take tambayarta lfy bata walwala? Tace ba komai mama. Mama tace kodai bakyajin dadin zama damune? Laaaa mama wallahi ba haka bane nafison nan da ko ina har gidansu..... Sai kuma tayi shiru sai mama tace har gidansu waye?? Ba kowa mama, hmmmmm. nidai da yawa mama nakanji banajin dadine saina riqajin kamar inason wani abu Amma bansan ko miyeba haka zan kasance chikin damuwa.... iffaat tama mama bayanin abinda takeji, tace wani abin mama sai idan na tuna yaran gidan da nayi aiki,! Sai nayi tajin raina yana wani iri, kawai mama shine ba wani abubw kuma inaga kamar sabone ko mama, mama tayi murmushi tace Eh inaga sabon ne kawai. mamadai ta gano cewa iffaat wani take so amma itama mamar bata fahimci ko wayeba Kuma iffaat din har yanxu batada wayon da zata san cewa ta fada tarkon soyayyar farhaaan ne, mama da ta fahimci halin da yarta take ciki sai ta dada janta jiki ko zata mantar da ita wannan mugun ciwo da yake addabarta.. Sau da yawa idan iffaat ta shiga daki ta fara tunane tunane sai taga kamar ba ita bace.. taci kuka taci kuka har ta godewa Allah.... *** Wata rana iffaat bayan ta fito a class sai ga wasu yan samari sun wuceta tana jikin class suka fara mata hy yan mata ji mana,! iffaat kamar bata jisuba, sukayi iskancinsu suka gaji suka wuce bata ko daga kai ta kallesuba, har sukaje suka dawo suka qara mata tayi banxa dasu.... Bayan sun wuce tana zaune sai ta fara tunanin iskanchin da aka mata ta gyale, anya nice iffaat kuwa? Wacce Ko ba'akasa dani nakan siya, nakan sayi fada da kudina bare a tsokaneni, waima wayannan yaran zasu min iskanci na gyalesu tayi tsaki kamar an tsira mata allura, ta tashi ta fito tsakiyar makaranta don nemansu, fitanta keda wuya tayi karo da malamai suna kora a koma class juyawanda zatayi head boy dinsu ya fara tsula mata bulala tayi class a guje amma taji bulalar ba kadan ba taso ta bisu ta musu nata rashin kunya aka koreta, ko minti 10 ba'ayiba ta manta da abin ta koma tunaninta da baida natija ,..... [12:11AM, 5/6/2015] .: WACE CE ITA..??43 Na Hauwa M.Jabo ********* Wata rana Suna hira da mama take bata labarin tanada ya, yarinyar yayanta ne lokacinda babanki ya kwaceki to lokacin aka bani ita, to ina take mama? Tana Qatar karatu takeyi wannan shekarar zata kammala data qare sai a mata aure,! iffaat tayi dariya da shewa Ashe dai mama mun kusa shan biki, kinsan kuwa inason biki a rayuwata, lokacinda muna qauye kullum sai naje biki ko ba'a gayyaceniba kuma ni bandamu da su bani abinciba kawai mukanje muyi tsokana, idan za'a kai amarya da dare mu sami allura muyita tsikarawa matane ko Ku muyiwa yayansu da suka Goya suyita kuka sai mu boye, mama Dan tsabar dariya saida ta kai kwance, tashajin ana cewa iffaat ta gagari Kowa a qauye amma ba tasan abin yakai hakaba, nidai jabo araina nace to iffaat kan tayi hatsabibancin da yafi wannanma!! Yanxu kinga mama biki namu sai yanda mukayi ko, mama cikin dariya tace eh, da yake har baiko ma an mata ai. Habawa? Ashe munada biki duk suka saka dariya... iffaat tanatason ta tambayi mama hoton yar tata amma Sam ta manta har ta kusa dawowa! *** Ranar da Yar mama zata dawo gidan mu yasha gyara anyi girke girke kala kala, guraren qarfe 2pm ta sauka Kaduna daga chan aka daukota aka kawo ta Zaria da yake an barni gida, isowarsu keda wuya, wazan gani a matsayin yar uwata?? Suhaila matar da akayiwa farhaaah baiko da ita, wani rass taji ni kaina jabo sai da naji bugun zuciyarta kuma na tabbatarda kuma Masu karatu kunjiyo kobakujiba???? Suhaila tana ganina tahau dariya tana tambayata farahnax, cox ita achan tasañi, tace iffo surprise dina kukayi haka? So happy wallahi ina farahnax din? Itakam iffaat tsaye tayi tana mamaki abinda take gani, wato Suhaila itace yarinyarda aka baiwa mamanta kuma itace matar farhaaah! Sai yanxu ta gane kamar da akace sunyi da Suhaila, Ashe jini dayane, sai yanxu ta gane dalilin da yasa takejin Suhaila cikin ranta amma kuma miyasa take tsanar ta?? Suhaila sai washe baki take tana tambayarta farahnax, mama tace keewai waya gaya miki tasan farahnax? Ke dadi miji dadi dangin miji!! Laaa mama wallahi gidansu fa nake ganinta farko, itace wacce nace miki akwai wata cousin din farhaan mai ban dariya kuma kunyi kama kin tuna mama? Eh na tuna to itace, nifarko ma na dauka aiki take a gidan sai ranan umman farhaan tace ba Yar aiki bace yartace, anan dai na fayyace musu komai mama da Suhaila suka gane cewa gidan su farhaan goggo ta kawoni aiki, mama taji dadin yanda umma ta kula dani har tana cewa suruka ta gari...... Nida Suhaila mun dinke mun zama kamar abokai dukda ta girmeni nesa ba kusaba cox lokacin ina 16 ita kuma tana 24 ne, duk iyayen farhaan sun ganeni sunata jin dadi, mama kuwa hadda zuwa godiya yanda aka kula da yarta har umma tana cewa a qara bata ita... **** Bansan miyasa nake tsanar Suhaila ba nakan kwatanta boyewa araina amma duk ranarda naji sunyi waya da farhaaah to kuwa duk yanda zanyi sai nasan yanda zanyi muyi fada da Suhaila da yake ita ba mai kulawa da qananan abubuwa bace so bata kulawa dani Sam. Banxa takeyi dani kamar ba da ita nake yiba, nayita gabata har na gaji na sauko. Mama ta kula kamar na tsaneta amma ita kanta bata gano dilin hakan ba, Ranar mama ta kirani take tambaya ta miyake faruwa tsakanina da Yar uwata nafara kame kame, ba komai, mamadai tayi ta min wayo har na fara magana wallahi mama nikaina bansan dalilin da yasa mafiyawan lokuta nake jin na tsanetaba haka kawai take bani haushi kuma wallahi mama banajin dadin abubuwan da nake mata ta fashe da kuka, mama ta rarrasheta, taso ta gano sirrin amma aranta tace bari saita qara gwadata. Tofa MUJE ZUWA MUJI IRIN GWJIN DA MAMA ZATAMA IFFAAT... DA KUMA WANE IRIN MATAKI ZATA DAUKA AKAN HAKA, ZATA IYA ADALCI KO KUWA SON KAI ZATAYI TSAKSNIN YARTA DA YAR RIQONTA?? [11:13PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??44 Na Hauwa M.Jabo ****** Ranar da farhaaah yazo Nigeria goben aranar aka hada mai tarba ta musamman a gidan su iffaat, duk da cewa bata iya komaiba kuma har yanxu bata taba shiga kitchen da sunan girkiba amma ta nemo hutunan girki a internet, an hada kayan komai da komai ana jiran Yy farhaan, tayi kwalliyar da itakaitaa bansan ta iyataba kuma batasan dalilin da yasa tayitaba, Suhaila ta tsaya tana kallonta kinganki kuwa wallahi kamar wata amarya, please kimin irin kwalliyanki, ta kuwa xauna gaban iffaat nidai jabo nace su iffaat Masu haye hayen bishiya sune ake kwalliya haka, ai yanxu kam taci uban Yar baqa zainb khalifa da iya kwalliya iffaat ta dara tace kina nufin kwalliyata tafi taki kyau? Sosai ma kuwa nidai kimin tun basu qarasoba haka iffaat ta tsinci kanta da gyashin yiwa yayar tata irin kwalliyarta, ta nemi dalilin yin hakan ba dalili, Suhaila har ta gaji da bibiyarta akan ta mata irin kwalliyar ta iffaat ta nace akan bata iyaba itama Sa'a tayi tama kanta....... Guraren la'asar saigasu farhaan da farahnax sun iso gidan ita Kuma tana dakin Yayanta tana hada wasu kaya kamin baqin su Iso, dariyar farahnax taji tana tambayar ina iffaat take, ta hango farhaan, wani raaas taji zuciyata ta shiga harbawa kuma batasan daliliba, farhaan guy ne lafiyayye duk yanda namiji yake cikakke mai lafiya to farhaah yana cikinsu dogo ne mai jiki daidai shi yanada faffadan qirji haka yanada sajee a fuskarshi wanda ya kwanta yayi luf a fuskarshi, yana zuwa naga yy Suhaila taje ta fada jikinsa ya rungumeta, iffat taji wani dum dum dum...!!! wasu emergency hawayene suka bulbulo daga fuskata, lokaci daya taji ta qara tsanar Suhaila da farhaan, kee mi kikeyi anan ga baqi chan tun dazu naji suna kwala miki kira,? Ta waigo ba tare da tasan ko wayeba, idonta sun Riga sun rufe, ta watsamai harara, miya dameka da abin da nakeyi anan.!? Sokoko yayi yana mamaki, iffaat kinsan wa yake magana kuwa?? Tace a gadare nasani Yaya ameen ne yake magana, kaiiii iffaat too lallai bakida kunya, Ta kalleshi ido cike da hawaye tana kuka tace Kaine bakada kunya, ni inada kunya Kaine kaine Yaya, ta fada jikinsa tana dukan qirjinsa sai jin yayi tayi deef tayi tana Neman faduwa qasa, kamin kace kobo ta sumaaa..... [11:20PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 45 Na Hauwa M.Jabo Ya riqeta ya dagota yana jijjigata yana kiran sunan ta, amma iffatu ko motsi haka ya dauketa chak dama ba wani aukine da itaba, yakaita dakinsa yaci gaba da jijjigata yana fadin sunan ta, farahnax yaji tana kiran iffaat iffaat kina ina?? Ya xuba mata ruwa shiru,Yayi sauri ya tura qofa yayiwa mama waya bata daukaba tana chan suna gaisawa da suruki, ya dakko ruwa a fridge ya qara zuba mata yarinya still ko motsi yaga kamin yaje ya kira mama zata iya mutuwa, tuni ya fara hawaye yana kiran sunanta yana jijjigata, Muryar mama yaji, Aminu naga ka kirani lafiya? Nidai kuje Ku gaisa fa yaron chan mai Neman qanwarku Suhaila, mama kizo iffaat ba lafiya, Subhanallahi.!! Miya sameta ta shigo da takalmi a qafa taga yarta kwance kamar gawa ta fara jijjigata, taqara watsa mata duka ruwann dake cikin robar swan din, iffaat tayi wani gwauro numfashi ta bude Ido kadan ta kalli yayanta ta kalli mamanta ta fashe da kuka, mama ta rungumeta tana rarrashinta, wai ya akayi haka aminu miya sameta?? Wallahi mama kawai naga ta tsaya jikin window tana kallon su farhaaah da sukazo shine na tambayeta miya faru,.................. Yayi bayanin komai umma ta kalleta taga ta rufe ido lallai xatonta ya zama gaskiya, tayi jeeem amma ba halin magana wannan tashin hankali har ina.!? Suna zaune jugun jugun dasu saiga Suhaila ta shigo, iffaat wai ina kika shiga tun dazu sunata nemanki Yy farhaan kuwa ya kawo miki....... Ai bata qarasa zancen ma taga su mama an xuba uban tagumi ta kallesu mama miya sami sister na?? Hankalinta ya tashi, mama batace komai. iffaat kuwa sai ma qara runtse ido tayi wasu hawayen suka ci gaba da sauko mata, tsanar ta takeji a ranta Yaya Ameen zai fara mata bayani mama ta katseshi. Kije ki sallami baqinki ki dawo mama wallahi ba zan iya komaiba sister na acikin wannan halin mama miya faru da ita,? bakomai bane kune kullum cikin saka takalmi masu tsini garin rawar kai ta fadi kanta yadan daki jikin qofa shine kawaifa, Ta dafe qirji Allah sarki sister sannu kinji bara na kirawosu anan suxo su dubaki ta miqe tana sauri Iffat da qarfin hali tace kada ki kirasu banason ganinsu bana so, mama tayi sauri ta toshe matabaki, Batasan lokacinda ta fada hakan ba lallai iffaat soyayya tana wujijjigata, suhaila ta waigo mi tace mama?? Cewa tayi kada ki kirasu, Nima ina ganin ki barsu kada hankalinsu ya tashi,... [11:25PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??46 Na Hauwa M. Jabo To mama mixance dasu?? Yy amin yace kice na aiketa har yanxu bata dawoba, ta tafi cike da baqin cikin da jimamin faduwar Yar uwarta Allah sarki Suhaila akwai sanyin hali. Bayan ta tafi yaya yake tambayar mama miyasa baki fada mata gaskiya ba?? To sai kawai nace tana kallon su sai ta suma ai kaga dole aji tabakinta kamin ayanke hukunci,ya jinjina kai hakane, anan suka zauna har saida su farhaan suka tafi, Suhaila taxo ta fada musu sun tafi, su tashi su koma cikin gida. Iffaat tace ita batason chikin gida dakin yayanta zata zauna, dama iffaat da naci sukayi sukayi Amma inaaa ko bude Ido batayiba bare ta tankasu suka gaji suka barta, har sunkai bakin qofa, Suhaila ta dawo. Suhaila tace Iffaat na kawo miki kayan da Yy farhaan ya siyo miki?? Ta daka mata tsawa da bataso. saida su mama suka jiyo kuma duk abinnan da akeyi idonta a rufe suke taqi budesu, tana budewa hawaye ne zasu fito.. ******** Bayan faruwar haka da yan kwanaki iffaat yanda take jin ta tsani Suhaila ba dalili yana matuqar damunta, duk abinda takeyi idan Suhaila ta saka hannu sai ta tsani wannan abin tabarshi kenan har abada, idan kuwa ta saka bakinta sai ta gwaleta gaban ko waye, ranar maman Suhaila hajiya kulu taxo gidan yini dan yinin da tayi ta fahimci yanda iffaat ke yiwa Suhaila sai ranta baiyi dadiba har take tambayar Suhaila tana kuwa jin dadi bayan xuwan iffaat?? tace lfy lau idan kikaga tana haka to wani

Chapter 5 of 10