Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 10
jikinta Dan tasan batada tsarki, su farhaan anxo ana lalabe lalabe iffaat ta dakatar dashi ta hanyar gayamai batada tsarki kuma ta gaji ya barta tayi bacci, ga injin dinsa ya riga yadau zafi, farhaan Dan takaici ya rasa abinda zaiyi sai daukar key yayi ya fita yaje kozai samu gunda xaiyi aiki yanda yayi tsingau dinnan, iffaat ta gane ina ya nufa amma Sam bata kulashiba. farhaan bayan ya tafine yaje kuma yakasa Neman matan banxar, haka ya samu daki ya kwanta yanata juyi har bacci ya daukeshi bai farkaba sai guraren 3 Subhanallahi, ya tashi da sauri ya dawo gida koda yaxo ya tarar da iffaat zaune tana kallo abin ya bashi mamaki kallon iffaat cikin dare.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??92 Na Hauwa M. Jabo Yana shigowa ko kallonsa batayiba, duk kunya ta kamashi, gashi ma abinda yajeyi ya kasa aikatashi ya Dan Sosa kai yace bakiyi bacci ba!? Tace nayi faarkawa nayi yanxu, yaga kamar batayi fushiba sai ya matso kusa da ita zai zauna tayi xunbur ta tashi kada ka kuskura ka matso kusa dani tamai kallon raini kamar taga wani kashi, Ta kalleshi ai shi mai hali baya barin halinsa tunda ka saba da Neman mata wallahi ba abinda zaisa ka daina, ya xa'ayi na iya bacci bayan na auri miji manemin mata, ido cikin ido ta kalleshi tace farhaan nayi Dana sanin aurenka, nayi baqin cikin kasan cewa tare dakai, babban abin godiya ga Allah shine ba'abinda ya shiga tsakaninmu, bare ayi xancen hada zuri'a na tabbatar da yarana sai sunyi baqin ciki da samin uba mazinaci irinka.!! Amma yanxu kaga Hankali kwance zan nemi wani miji nayi aurena kuma wallahi saina fadawa umma halin da kake ciki.. Farhaan zuciya tayi xafi waishi take gayawa zata nemi miji tayi aure, yaso ya mammaketa amma sai ta wuce shi nan ya zauna yana Allah wadaran halinsa yayi tsaki yafi sau dubu ya kasa shiga dakin har bacci ya saceshi, iffaat kam ko dar bata ga bacciba gari ya waye kamar kada tamai breakfast Amma ta daure ta hada mai taxo tasa qafa ta shureshi ya tashi, ta kalleshi a wulaqance tace to aje ayi wanka a tsarkake jiki ayi sallah, a karya aje gun Neman wasu matan, aranshi yace wai dan wulaqanci da qafa xata tayar dashi yaji bala'en haushi Dan kuwa da atayar dashi da qafa gara a gyaleshi, kuma ga magan ganun banxa tana gayamai ya kalleta waike waya gaya miki Neman mata naje?! Cikin isa da tsabar rasjin kunya Tace sabida ba namijin kirkin da xai bar gidansa 12 na dare ya dawo 3 sannan yace ba gun banxa yake zuwaba, bare kaida akasan halinka na Neman mata.... Farhaan dai ya kasa magana yayi wanka ko karyawa yakasa yi ya Dan saba tana bashi a baki yau kam yasan koxai mutu bazata bashi abakiba, Haka ya dawo office guraren yamma ta qare girki tayi kwalliyarta kamar ba itaba. .. [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??93 Na Hauwa M. Jabo Tamai sannu da zuwa, ya amsa bayan ta juya ya kalleta mace kamar hawainiya sai chanxa wa takeyi, yaje yayi wanka. ta kawo mai abinci Dana safe Dana rana na yamma ma Dan ba yanxu yakeciba da sai ta hado mai dashi kuma duk sai ya cinyeshi, ta ijiye tace yaci wai ya qoshi, tamai kallon banxa kasan Allah wallahi sai kacishi, ya kalleta yanda ta hade fuska hakadai yayita durawa yana qarewa yaje yayita amai ko sannu bata cemaiba yana fitowa tace Allah yasa dai matan basu maka cikiba!! dagachin abinci sai amai ta bashi dariya sosai wai ciki, ya nemi guri ya zauna, bai tankataba haka dai iffaat take da farhaan kullum cikin yi masa habaici take, da rana taci uban kwalliya da dare ta saka arnan kayan bacci ta kuma fuske abinta, ranar da ya qara nemanta tace sai yaje asibiti an duba shi idan bashida rashin lafiya, farhaan kam ya shiga uku kullum cikin baqin cikin yarinyar nan yake, lallai yanxune yake sanin haqiqanin WACE CE ITA... dama hausawa sunce Dan hakin daka raina shi yake tsole maka ido, ai kuwa ga iffaat tana wanashi Son ranta, farko yace bazaije asibiti ba daga baya da yaga jan ran nata yayi yawa sai tsingau yakeyi haka ya daure yaje aka dubashi, lafiya lau yake ya kawo mata result tana kwance da kayanta na daukar allhaki ta tashi zaune ta duba taga lafiyanshi lau tace saura Abu daya kuma yace bayason yaji ko miye wallahi sai ta bashi haqqinsa, iffaat taga da gaske yakeyi idonsa sunyi jaa sai xuba masifa yakeyi hankalinta ya tashi tasan ba hanyar guduwa amma ta fuske ta nuna kamar bataji tsoroba farhaan kam matseta yayi ya cire mata kaya duka cizo duk yasha amma ina saida yayi nasarar kawar da budurcinta Allah sarki iffaat ta bani tausayi..... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??94 kuka take tamkar ranta zai fita, Yaxo yana lallashinta yana bata haquri ya samu ya mata wanka da gashin jiki yayi toweling dinta ya kawota daki gaskiya taji jiki ba kadan ba bakinnan nata haka ya mutu murus kamar ba itaba, ba'ajima ba sai xaxxabi, farhaan shi kanshi yasan bai mata dakyauba yama manta sabon shigace an saba da masu wakeken abu shiga daya kamar an kada guga a rijiya, wannan kam a tame take fam shima da gyar ya samu shiga, ko Suhaila ma kusan haka take but na iffaat yayi yawa, Ya kira Dr. su yamai bayani ya kawo mai yan magunguna ya tayar da ita ya bata taqisha yayi yayi amma taqisha sai rawar dari take ga xafinda takeji a gurin, itakam ji take kamar ma ya yageta, farhaan dai anyi jinyar iffaat bata mai magana Sam, ko kallonsa ma batayi idan yaxo rufe idonta takeyi yaxo yayita surutansa ya gaji ba amsa... Kwananta uku a kwance ko lecture bata xuwa, ranar na hudu ta tafi skull, bayan sun fito lecture ta hadu da armiya'u suna tadi armiya'u dai kullum maganarta daya a kyautatawa miji a sha Abu Dan qara ni'ima, iffaat ta kalleta, ke kullum xance daya abinda ko dadi babu! Armiya'u ta kalleta tayi murmushi yarinya baki maida hankalinki bane abinda kawai zance miki wallahi so sweat, iffaat kam bazata iya fadar cewa sai yanxu ta shigo system ba sai ta basar da maganar... Ta dawo gida taga farhaan zaune batako kalleshiba ta wuce daki tayi wanka ta fito taje tayi girki, ta kawo mai yace dauke abinki baxanciba kamar bataji mi yake fada ba ta kama hanya ta wuce abinta janyota yayi da qarfi nace ki dauke baxanciba, kallon mamaki tamai taga yanda ya daure fuska aranta tace ai tunda ka biya buqatarka shikenan banida daraja. har zatayi magana kuma sai ta fasa da duqa zata dauki abincin farhaan ya janyota wato daukewa zakiyi ko? Bazaki tambayeni dalilin yin hakaba,? Haba iffaat miyasa kike min hakane? kuka ya kubce masa iffaat miyasa kike min hakane eeeh ? Kullum kina azabtarda zuciyarda ta damfaru da qaunarki, Dan kawai Kinga na damu dake matseta yayi sosai jikinsa itama dai hawayen suke xuba a idonta, ta fara magana tana kuka basai na kawo mukuba kawai akan Neman matanshine shi kuma yace tuni ya daina koda bata aminta 100% ba amma taji ta gamsu.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 95A Na Hauwa M. Jabo Hmmmm. Wai har sun shirya an yafi juna sunci abincin tare... Wata sabuwar soyayyah ce a Gidan ma'auratan gwanin bansha'awa suna kula da junansu yanda yakamata. Yanxune iffaat take fahimtar abinda armiya'u ta taba gayamata na cewa farhaan bamuqacine na gaske lallai hakane kullum dai yajishi ciki uhummm. Abin ba'a cewa komai. Iffaat ta cika alqawari takai goggo makka kuma ta dauko qawayenta na qauye dije da rukayya an baiwa mazajensu lebaranci a companyn su farhaan suna shanawa suma ga dukkan alamu suma su waye su xama yan gayu, amma bana tunanin dijee zata waye Dan har yanxu tana nan sai a hankali.. Bayan shekara 7 Koda naxo naga iffaat da yara uku mamaki ya kamani naso naga iffaat da ciki amma ina banganiba sai yayanta na gani.. Mace daya namiji biyu Macen taci sunan Suhaila sai maxan dayan sunan mahaifin iffaat mahmoud dayan sunan mahaifin farhaan habeeb. Farhaan ya zama kamilallen mutum kamar bashiba, iffaat kam har yanxu saidai idan ba'asamu damaba.. Dan Ko yau da naje muku gidan, saman bishiya na ganta tana tsinkowa tana wurgowa qasa yaranta suna cabewa sunata jin dadi, farhaan ya shigo ya duba bata yasan ina taje ya girgixa kai, yaje ya kirata tana ganinsa ta diro saman bishiya saida naji tsoro na dauka ta karye sai na tuna fiye da wannan ma tayi.. taje ta rungume shi tanamai oyoyo yace bawai na hanaki hawa saman bishiya ba, ta kanne ido tace waya iya raba monkey da hawa bishiya dariya yayi ya tuna lokacinda tayi mai fitsari saman bishiya yace monkey ne, Suhaila ce ta shigo itada habeeb cox shi Mahmoud jinjirene, Suhaila da wayo tace Abba mu anti amarya mukeso.! gidansu hameed na uncle Ali an musu anti amarya kullum sai yace mana mu bamuda anti amarua, muma munason anti.... iffaat tace kiji yarinya da gulma xanci gidanku yanxu, ba anti amyaba anti ango bace min da gani, sakarya kawai...!! Suhaila ta wuce tana gunguni, Farhaan kam dariya yakeyi sosai, iffaat ta kalleshi miye haka.?? Daga jin anyi xancen amarya sai wani washe baki kakeyi... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA.. ??95B Na Hauwa M.jabo To amaryaf taxo ina daidai da ita, yadan muskuta dama akwai wata yarinya Dana gani ta kwanta min arai inaga xan kawoma su Yy Suhaila ita tunda tanason anti amarya, Yy Suhaila suke kiran Yar tasu da ita. iffaat hararanshi tayi tace wallahi baka isaba, yayi dariya yace kefa kika ce taxo kina daidai da ita,! Ta fuske tace eh ta murguda baki, farhaan yayi dariya ya tashi ya shige, har yakai qofar bayi bari nayi wanka xan kawo miki ita ki ganta.. Iffaat kam taji ba daidaiba, harya fara wanka ta kasa haqura ya fito ta bishi bayi Yy farhaan waida gaske kakeyi? Yayi dariya sosai sannan yace eh mana ya wanke ko ina xai dauraye jiki ta kashe fanfo ta fara bala'e wallahi baxai yiwuba, ai wannan sharrine, yace aah kinji yarinya ke kinxama chuss dole na dauko sabuwa a Leda na bare ta kenifa sai nayi mace hudu Dan ki sani, kii kunna min ruwana mana, ta fara kuka, wallahi sai ta gayawa umma yace umma ai xataso a kawo mata sabuwar suruka ta haifo mata jikoki, ba kece kin daina mini wankaba ai dole na nemo mai mini wanka Dan ni Dan lelene, cikin kuka tace xan riqa maka wanka wallahi, yace to ki fara yanxu, ta kuwa kunna ruwa tamai wanka Tass suka fito ta shirya shi sai yan hawaye takeyi, abin yabana bashi dariya ba kadan ba, tana zaune saiga Yy Suhaila ta shigo iffaat tace ke get out masu tsokane tsokane kawai, yarinya tayi tsaye bata gane dawan gariba, farhaan yace Yy Suhaila kuje wasa kinji yarinyar anti amarya tace yeeeeeeeee ta tafi da gudu, farhaan yaga yanda iffaat ta hade fuska ta miqe da qarfi zata fara yankomai bala'e ya janyo ta ta fado jikinsa haba Yar gidan umma ni na Isa na qara aure yanda nake da mace kamar ki ai kin wuce 1 of 4 ke ta dabance kullum sweat kike qarawa, ya fara kissing dinta, tace bayan kace min chuss yace wallahi wasa nake miki kinfi komai daraja a gurina kece sanadin shiryuwata kuma kin haifomin Yaya masu kyau masu kama dake, ta qara shigewa jikin sa tana mai nata salon nidai sai na fito na basu guri suci soyayyah kar na makance,.... TAMMAT BI HAMDILLAH.... Qarshe wannan littafin kenan Ina godiya ga dinbin masoya da suke bibiyar ta a wannan Dan qaramin littafi na WACE CE ITA.. ina godiya ga masu bani shawara da Masu mini gyara hadda masu zagi ban barku a bayaba ina godiya matuqa Allah ya saka da alkhairi, Nasan hausar tawa sai a hankali kuna qoqari gurin karantawa... Naso littafin yafi haka, akwai abubuwan da naso na saka wayanda zasu qara nishadantar daku amma kuma inaa exam ta matso kusa... Ayi haquri da wannan sai mun hadu wani book mai suna........... nagode sosai Don shawara ko gyara ga number ta +98936 594 4638 Banda tambayar wane guri nake please... HAUWA MUHAMMAD JABO take muku fatan alkhairi. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10