Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma wannan yarinyar ni tamini sosai, ammafa sai ta zama mai haquri Dan farhaan akwai fadin rai da fushin bala'e sai kina haquri kinji yan mata? Ta amsa da to kamar da gaske, ya sunanki da sauri nace ippatu. Matar ta maimaita iffaah suna mai dadi! Sai naji tafi kowa iya sunana yanda ta fada ta wani juya baki, "kunsan bahaushe baya banbanta "P""F" duk daya yake kiransu" Maman farhan ta mini nasiha ta kira yarta farahnax amma shiru bataxob, dakanta tace muje in nuna mini dakinki da zaki zauna, tashin hankali koni Jabo dakin ya burgeni bare wata yar qauye irin iffaaah... An gaya mata aikin da zatanayi, zata gyaramai dakinsa tattara mai kaya takai ma mai wanki ya wanke, ta wanke bayi, ita zata riqa tashinsa da safe yaje skull. Hummm iffaat kam sarkin bacci wa zata iya tayarwa daga bacci, Naji matar gidan ta burgeni cox batada gyama kuma ba wulaqanci haka mai gidan amma su hatsabiban yayan yan wulaqanci ne tasan ma korarta zaiyi Dan bazai iya zama da itaba. ******** Kwanan hajiya Fati hudu da iffaaat anyi sa'a ba wanda ya tsokaneta bare ta rama, yau zasu bar naija su koma UK da yarsu farahnax, akabar farhan da iffaaat a gidan. Da gani jininsu ko kadan bai haduba amma ba yanda ya iya mamarshi harda rantsuwa akan cewa bazai chanza taba, dole yayi haquri koda na shekara dayane, ya fahimchi yarinyar batada kunya dole ya saitata.!! Bayan tafiyar su hajiya ya dawo daga rakiyansu da yayi a airport ya shigo gidan, Keeee come here, taxo gabanshi tamai qiqam kamar ice ta tsaya, Oyaaaa get seat tazauna bawai ta gane mi ya fada bane kawai a makarantar boko kamin a korota taji maliminsu na cewa seat down ta gane cewa acikin biyun daya na nufin zamame tunda yana fada kowa yake xaunawa, haka yana cewa come here sai taga anje gun malami. sai itama tayi hakan, akayi Sa'a ta gane farhaan ya dauka tanajin English ganin ya mata Dan biyu ta gane sai ya fara bayani Hausa da turanci saida yayi yayi yace have u get me.? Yaga ko motsi batayiba, ya qara tambaya shiru kakeji yagane aikin banxa yayi, keee ya daka mata tsawa. Kina jina?? eh inaji. to mi nace?? Ta harareshi mi kace kuwa? Duk maganar da nayi bakiji abinda naceba. Ta tabe baki ai ban dauka dani kakeba to da uban wa nake, zanci ubanki fa.! ta miqe zunbur ta nunashi da yatsa kada ka qara zagar min baba sabida ya rasu idan ka qara zagin babana zan rama masa kaji na fada maka. Ta murguda baki ta maka mai harara... Farhaan kam gaskiya tamai yawa ya tsaya yana kallon baqauya tazo tanamai rashin kunya har gida wai kuma Yar aikinsa, anya kuwa tasan WACE CE ITA anan gidan? ba shakka batasan WACE CE ITA ba nine xan Sanar da ita WACE CE ITA a gidannan, baice mata komaiba yaci gaba da kallonsa.... [4:00PM, 4/27/2015] .: WAYE ITA..?? 10 Na Hauwa M. Jabo. Ta kalleshi in tafi?? Yayi banza da ita, ta qara tambayar sa yayi mata banxa, ta kama hanya zata tafi ya daka mata tsawa, ki dawo ki tsaya nan, taja ta tsaya kusan 30mnt tana tsaye, ta gaji zata zauna ya hanata Idan kika zauna sai na kakkaryaki, tayi tsaki, ta kauda kai, ya qare abinda yakeyi ina miki magana zakice baki dauka dake nakeba ko?? To waye a dakin da zanyi magana dashi? Ta kalleshi a wulaqance da chan dakake maganar dawa kakeyi?? sau nawa ina ganinka kana daura hannu a kunne kanata magana ko kuma kayi yare kana dariya, wani lokaci ai wata waya kake sakawa a kunnenka kayita magana kai kadai duk da uban wa kake magana? Kaga yanzuma na dauka da ubanda kake magana farko dashi kakeyi yanxu . Zunbur ya miqe yayi niyyar mammaketa sai ya tuna da abinda ummanshi ta fada mai "ban amince ka daki yar mutaneba marainiyace duk abin da ta maka kamin waya zan mata magana" sai ya koma ya zauna ya dun qule hannu itako tana tsaye ta riqe kunkuminta kamar mai jiran danbe, ya kalleta wata mummuna qazama da ita, ya rasa abinda zai fada mata ta gane WACE CE ITA. ya harareta yaja dogon tsaki, to ki zauna, ta zauna ya maimata bayanin da ya mata da dazu, shima dai iskancine yazai ijiye baqauya kamar wannan yana mata English to amma ai da yayi na farko ta gane, ya akayi ta gane? Koma yane ya rage nata.. Yace Inada abokai mata da maxa, kuma ko wanne yana zuwa nan gidan suna kwana wasu suna wata daya wasu suna sati biyu idan sunzo suma duk abinda kike min suma zaki musu hadda girki idan suna buqata zaki musu. Ni ban iya girkibafa Malam.! Gidanku basu koya miki girkiba ? Eh basu koyamin ba, ta fada cike da tsiwa,sai yayi banxa da ita ya fahimci yarinta na damunta amma zai gyarata a hankali, ya nuna mata WACE CE ITA a gidannan, OK ya rage naki, haka zaki girka musu in sun buqata, tayi banza dashi Dan tunda take bata taba yiwa goggo girkiba cox batama zauna gidaba bare tasan yanda ake girka abinci. Ko girkin murhu bata iyaba bare na gas, ya qara jaddada mata abinda umma tace bata ba fita waje, ba wasa da masu gadi, ba ruwanta da kowa aikinta kawai. za'ayi shegiya kuwa.! Yaqare fada mata abinda zai fada mata ta tashi ta shige dakinta. Tunda tazo gidan a Leda take kashi sai ta saka bola idan yayi yawa ta fitar dashi sabida duk dube dubenta bataga masai a gidan ba, shi yasa dakinta yake wari Dan bata damu da gyara komaiba, gurinda kawai akace ta gyara dakin farhaan take gyarawa.... [4:00PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 11 Na Hauwa M. Jabo ******** Ranar farko da farhaan yayi baqo wani abokinsa da sukayi karatu a UK. Tare sunyi missing din juna, farhaan yanata addu'a kada wannan kucakar ta fito ta kwafsa mishi Dan ya lura kanta rawa yakeyi ba kadanba, suna tsaka da gaisawa sai gata ta fito. Kamar an korota daga daki, Ku tashi zan goge nan gurin! Ta fada ba tareda ta kallesuba, Tafara share palon, meene kebakiga inada baqo bane,? maza ki bacemin da gani har ta fara shara tajiyo tsawan da ya daka mata ta miqe tsaye, tana yatsina fuska kai bakasan lokacin aiki na bane da zaka kwaso tarkacen abokanka kazo dasu Ku hanani aiki..! Habawa Ya wanke ta da mari tashin hankali..! ta dauki bokitinta na ruwan dattin data goge sauran guraren dasu, ta watsawa abokinsaA fuska, tunda shine silar adaketa, ta matsa daga nesa tana jiran hukuncin da za'amata da Wanda itama zatayi Dan bata yafiya, dukansu sun rasa abinyi abokinsa ya fara bala'e ya zaka zauna da mahaukaciya farhaaah, bakasan hadarin hakabane? Wannan wata rana zata iya kasheka wallahi, tana shigowa palon nagane batada hankali, Kaine Mara hankali baniba tana zazzare ido kamar lecturer ya titsiye jabo a clss bata iya karatuba, farhaan zaije gunta abokinsa yariqe hannunsa, cool down my man. Akwai banbanci tsakanin mai hankali da mahaukaci nasan da tanada hankali bazata taba yimin hakaba, muje daga ciki inyi wanka in chanja kaya kawai. Baqin ciki ya hana farhaan magana ya rasa yanda zaiyi, Dole ya nuna mata WACE CE ITA a gidannan. Abokinsa yaja hannunsa suka wuce daki ita kuwa hajiyar tachi gaba da aikinta. ((Allah ya tsaremu da aikin jahili da baqauye.)) ta gyara gunda ta jiqe da ruwa kamar bata zubarba, aikin ma fa yinsa kawai takeyi amma ba abinda ta iya bayi ruwa kawai take sakawa ta dauraye duk da cewa umma ta nuna mata wasu abunuwan, gadonsa kuwa sai Wanda ya gani da yake shima gwanine gun shiririta haka yake kwanciya akan gadonsa shi warine kawai bayaso. Bayan abokinsa ya tafi ya kwala mata kira ta fito ya nunata da yatsa wallahi yau sai kin bar gidannan Dan ba gidan ubanki bane, ko in hallakaki matsayaciya kawai, tofaaa ran ta ya baci ta tsani a zagi babanta ta kebe baki, ai bani nakawo kaina gidan na ubankaba, ubanka ya kawoni sai ka bari idan ubanka ya dawo sai ya maidani gidan ubana kamar yanda ya daukoni, ta fada cike da gadara da rashin tsoro. Sai ya saki baki yana kallonta ta juya ta koma dakinta ya bita da kallo, Ita kanta tasan zata iya gayawa farhaaah ko wace irin magana amma bata taba kawo ta kulla masa sharri ko daya a zuciyantaba, haka kawai yake bata tausayi kajifa.. Maamanshi ya kira, umma wallahi yau sai na babbala wannan qazamar yarinyar batada amfanin komai, umma dai nata bashi haquri dan tasan zai rina, nan ya kwashe duk abinda ya faru ya gayawa umma ita kanta umma ta jinjina wa wannan yarinyar da Karen aikinta. amma bata nunawa dantaba ta bashi haquri da kuma yimai kashedin ya fita hanyarta Kuma kada ya qara sa mata hannu, tace yakaiwa iffaaat waya, waye iffaaat umma?? Itayarinyar mana, baimasan sunantaba sai yau, kullum da yake kullum da keee yake kiranta ya kwala mata kira ta fito ya bata waya yaga dai batasan wayaba bata Masan yanda ake amfani da wayarba sai kawai ya sa speaker, taji ana kiran sunanta a ciki, farko ta dauka radio ne yake magana sai taji ana kiran sunanta habawa.... Ta wugar da wayar Da gudu ta koma daki jikinta na rawa abin ya bashi dariya sosai, sai ya bita dakin yana shiga wani qarni da wari ya tarbeshi ya kasa numfashi ya dawo Palo ya qara kiranta dagyar tafito, ni kaina Jabo abin ya bani mamaki Dan kuwa iffaaat ko lokacinda aka kaisu police station bataji tsoronda taji yanxuba Ashe Akwai abinda take tsoro....... Mujeee zuwa muji ta'addancin da zatamai kamin tafara.. [4:52PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 12 Na Hauwa M. Jabo Ta samu guri ta rakube nesa dashi, ya daure fuska ki karba umma zatayi magana dake, ina ummar? Magana take kuka kuka Ya zanyi magana da ita? Ki karba nace jiki na rawa duk ta rude ta karbi waya, ki daura a kunne takuwa danna waya a kunne,tayi mutuwar tsaye, Tana tsoron kar ta jata, wayar ma a juye ta daurata sai ya shareta, to kiyi magana, kamin tayi magana sai taji an sake kiran sunanta har zata wurgar da wayar sai kawai ta daure ta amsa, jiki na rawa, sundan gaisa, nan dai umma ta mata magana akan ta daina yiwa yayanta rashin kunya duk abinda yakeso ta mishi, ta amsa da to zata daina, amma hajiya kice ya daina dukana,!! gaban abokansa yake dukana kamar jakar gidansu, duka.!? Eh, kuma kullum saiya zagi margayi babana bayan na fada mishi babana ya rasu yadaina, amma kullum saiya zageni, kwallata ta cika mata ido batason a zagi babant ko kadan. umma taji haushi sosai ta bata haquri tace zatamai magana,daganan tadan bata labari har tana dariya, tama manta da tsoronda takeji,, haushi ya kama farhaan ya kira amata fada, ta bige dakai qaranshi, har tanata dariya, tana dariya shiko ya qura mata I do yana kallon haqoranta da sukayi wani tsatsa, ta qare ta kawo mai tana dariya ya kalleta ke wai laka kikeci hala,kinga yanda haqoranki sukayi tsatsa kuwa? Ta harareshi, ba laka naciba kashi nakecii, tayi tsaki ta wuce dakinta, ya bita da ido cike da takaicinta to waima miye amfanin kiran umma da nayi? Gashi ba abinda ya chanza! Kalli ko second goma ba'ayiba ta qara yimin rashin kunya, shima yayi tsaki lallai an hadashi da qaddara kuma umma tace sai ta dawo za'achanzamai ita, nanda shekara daya kenan lallai zaici uban yarinyar nan kuwa, dole ya nuna mata WACE CE ITA, a duniya ya rasa horon da zaimata taji haushi ko zata Dan natsu, ya kira kukunsu yace daga yau kada ya qara yin girki da ita, okay sir, ****** Da yamma mutuniyar taku ta tashi daga bacci ta nufi kitchen taga wayam ba abinci da Rana ma batachi komaiba yanxuma bataci komaiba, tana tsaye saiga farhaan ya shigo, abincin sa a shirye kamar yanda aka saba hadamai amma ba nata ta kalleshi fuska a yatsine, Ina abincina? Nine mai miki girki? Ko ni nasaba girka miki? Karki manta kema yar aikinace so ki kula kisan abinda kikeyi a gidannan ya bone. Ta kalleshi rai a bace to dan ina Yar aikinka sai akayi mine? Sai kada in nemi abincinda zanci? Ta kalleshi Ni yanxu mixanchi ? Yana kai spoon a baki ya tauna ba tare daya kalletaba Kici halinki ko ki girka da kanki idan kin matsu,.! Tofa yau za'aqure iffaaat yan mata...... [5:00PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 13 Na Hauwa M. Jabo Ta kalli kitchen din ko za'akasheta ba abinda zata iyayi a bayan buda fridge ba abinda ta iya, kuma ga wasu abubuwa kamar fridge akai taga ana girki. Za'ayi shegiya kuwa.ta kalleshi taga yana kai loma hankalinsa kwance., tayi tunanin ko ta barar mai da abincin da yake ci a jikinsa sai kuma ya bata tausayi, kawai saita rakube saida ya kammala Wanda ya rage shi tacinye.... **** Tafiya ta kama farhaan zuwa Lagos, ya tafi satinsa daya baidawoba. tun ranar da ya tafi batachin abinci saidai tabuda fridge duk abinda taga nacine ta dauko ta chinye, cikenta ya lallace kullum tana hanyar bayi, to anachin abinda ba'asaba Chiba wasu kuma ba bisa Qa'ida ake cinsuba duk wani abu da tagani mai Dan gishiri gishiri da zaqi zaqi ta gama dashi. Kaihar saida ta qare chiye chiyen takai batada abincin da zatachi yau. kwananta biyu bataci komaiba yunwa na Neman ta hallakata.. tunda tazo gidan bata taba koda fita wajen Palonba daga daki sai Palo sai kitchen, batamasan qofar da ake fitaba... Aranta taji ta fita haka ta biyo hanya tabi nan ta leqa chan har tayi karo da qofar fita, ta baya ta fita, Habawa, tayi murmushi taga S pool aranta tace wato gidan nan hadda qaramin kogi sukeda, ta waiga ta hango lanbu komai yaji fruit duk sun nuna wasu sun fado a qasa Habawa tayi ciki da sauri taci ayaba son ranta saida ta qoshi, sannan ta kwance Dan kwalinta tayo guxuri ta fito har zata wuce taga yanda ruwan nan sukayi sky colour sai suka bata sha'a ta tu6e ta fada tayi wanka sosai gata gwanar iya ruwa, gashi,an Dade ba'ahaduba ta Dade a ruwan sannan ta fito, dama tunda umman su farhaan ta tafi batayi wankaba kwana goma kenan, ta fito cike da nishadi an samu banxa, dagyar ta gane hangar komawa daki taje ta chanxa tufafi tunda wayannan sun jiqe, tana zaune Palo a qasa ta miqe qafafu ta saka fruits dinta tsakiyar qafafu, tanashan mangoro abin sai Wanda ya gani,taji qamshin turare hadi da dariya koda ta duba farhaan da wata mata yar gayu da qananan jaya a jikinta tasha attach fuskannan tasha fenti bakinnan yaji janbaki, ta rurungumo farhaan, tana mai shagwaba suna ta dariya, sun bata haushi haka kawai, ta miqe da dariyanta tagaishesu a tunaninta matarsace, matar ta mata kallon tsana da gyama ta kalleta a wulaqance ta zubar, hooney miya kawo almajirai a gidannan bayan kace min ba kowa dagakai sai masu aiki biyu. Wai itama mai aikinace, .matar ta wani jaa da baya honey wannan din?? Aiko hanyar databi bana son nabi tana magana ayangace tana wani rungumoshi, ran iffaaat ya bace tuni tasha magani aranta tace Dan an samu an gaishesu suke yiwa mutane wulaqanci ba matar shi bace ko uwarshice tamin iskanci zanci zan rama, taja wani dogon tsaki,ta murguda baki ta wucesu, hooney kana kallo mai aikin gidanku abinda ta mini...?? [2:48PM, 4/28/2015] .: WACE CEE ITA..?? 14 Na Hauwa M.Jabo Kiyi haquri tanada matsalar gwagwalwane, ta wani zare ido kana nufin mahaukaciya kake rayuwa,?? Haba Hoooney wannan ai gangancine ta fada da qarfi, har saida iffat tajiyota, ta waigo ta zare ido gasu masha Allah idonta, ido cikin ido tace; waye mahaukaciya?? Rufee ta rungume farhaan da qarfi kiyi haquri badake nakeba, rufee dai taji tsoro, hankalinta ya tashi qarshe taqi zama gidan tace sai dai ya kaita hotel Dan bazata zauna da mahaukaciyaba ta hallakata.! Haka dai rufee ta hana farhaan zama gida duk gajiyar daya kwaso saida yakaita hotol, kuma ta hanashi dawowa kar mahaukaciya tamai illa sai gobe da dare ya lallabata ya dawo gida, iffaaat dai fruits dinta takeci dare da rana amma taji jiki ba kadan ba har ta chanxa kala, kullum tana hanyar bayi tana gudawa. Dan ma Allah yasa ba irin zainb khalifa bace mai shegen ci da ba haka ba.. ******** Yana isowa ta fashe mai da kuka wallahi saika maidani gida!! angayamaka banida gata zata ijiyeni ba abinci wallahi saika maidani gidanmu ta riqe mai gefen riga tana kuka, anyi arziki bataci kwalarshibama. sai yanxu ya kula da ta Dan chanza kamar ta tame ta qara duhu ya tuna da cewa ya hana abata abinci.! Girjinsane ya buga to me takeci tsawon kwana 9?? Ya kalleta sai kuka take sai ta bashi dariya kuma, Ashe kawai abinda zaisaa wannan shu'umar kuka, yaji dadi aransa ko banxa ya rage baqin cikin ta kuma dama Dan ya bata wahala ya mata hakan.. Sorry iffaaahh, na manta dana hana abaki abinci, to mi kikeci kullum,?? bansaniba ta fada a yatsine wato kai ka yahana a bani abinci, wallahi Dana sani da ban mai kukaba duk a zuci take maganar.!! Kiyi haquri kinji, tana kallo ya kira kukunsa yace a riqa girki da ita,tace bazanciba gida zaka maidani, bai kulataba ya wuce abinsa. Bayan kwana biyar farhaan ya sallami rufee, Kwana na shida yazo da wata matar, Itama yar gayuce irin rufee saidai wannan tafi kyau, koda suka shigo iffat na goge Palo, yarinyar ta kalleta ke kawo min ruwa mai sanyi.! Ta fada a gajiye tafada kan kujera ta zauna iffat ko kamar batajitaba, aranta tace dama matansa biyu yaro dashi sai mata, baijira amsar iffat ba Dan yasan halinta sarai batada kirki, yanda ya gaji bazai iya fita nemawa ramsy hotel ba, ya dauko mata ruwan ya kawo mata kixo mushiga daga ciki kinga ana aiki anan ka shiga idan na huta zan shigo ta fada alalace, Ya wuce yabarta tana danna waya amma ranshi baiso barintaba, kee mai aiki idan kin gama kizo ki matsamin qafafuwana.... [3:00PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA.?? 15. Na Hauwa M Jabo Nan ma Tayi banxa da ita har ta qare aikinta, tana neman ficewa palon, ta kalli iffat kizo ki danna min hadda bayana kiyi min a hankali Na gaji sosai, tana magana a wahalce irin ta gaji dinnan, iffat nan ma ko ta mata banza ta fara waqar ta badi ba rai soyayyar jigon rayuwa da amana...... kusan kullum sai iffaat ta yi wannan waqar Dan tana bala'en Sonta kuma baiti biyu ta iya tun aqauyensu, ramcy taji shiru, ke kodai kurmace ke? Kurmane kuma zaiyi waqa,! Kee Ana magana kinyi banza da mutane, iffaat Tamata kallon wulaqanci, shi mijin naki yace miki aikina kenan danne dannen matansa?? Aikina biyune zuwa uku hajiya batace in ma matansa tausaba.! ta miqe zaune Ke marar kunyar yarinya, kina kallon mutane kamar kina kallon kashi, wai ma Waye matar tasa? Zan miki display a gidannan kuwa, iffat kam bata ko kalletaba taja tsaki ta wuce dakinta, ramcy a fusace ta tashi taje dakin farhaan, har ya fara bacci ihunta ya tayar dashi, ya zaku ijiye mai aiki Mara kunya a cikin gida yarinya har tana mini tsaki.! Yadanja tsaki ya rasa abinda zaice, aransa yace ki godewa Allah data tsaya akan tsaki, bayason ta fahamci koshi iffat ba ragawa takeyiba, cool down baby ba girman ki bane kina fada da mai aiki in kin kula yarinyace, xata qara magana ya janyota ya rungemeta.... nidai jabo danaga abin zaifi qarfina sai kawai na bar musu daki nayo waje. Guraren maqreeb suka farka daga bacci suka fito yunwa ta addabesu ya nema musu snack suci, ramcy tace indomie take so tachi, kuku kuma bayanan, to miye amfanin wannan yarinyar? Basai ta girkamin ba, no ki barshi xan girkamiki farhaan ya fada yana miqewa Dan yasan iffaat zubar mai da mutunci zatayi, ramcy dataga dai da gaske zai mata girkinne sai tace ta fasa amma zuciyarta fall da tunanin miye amfanin yar aikin, suna zaune suna hiransu suna dariya iffaat ta taso tazo gabansu ta wuce, wani warin datti ya daki hancin ramcy tace; kai amma wannan yatinya na wari! Ta toshe hanci, iffat ta waigo taceni nake wari? Farhaan yace ke ki matsa ki baiwa mutane guri,an fada kina wari qaryane bakya warin? Shima kallon banxa ya mata yaci gaba da hiranshi, ran iffat ya baci matuqa, ba'ataba fada mata hakaba wai tana wari sai yau, ko qauye su dijee da rukayya ne ake cewa suna wari ba wanda ya taba CE mata tana wari ta wuce fauuuuuh kamar guguwa ta tasooo, tana zuwa daki ta fara tunanin abinda zatama matar farhaan ta rama, cox taji haushin abinda ta fada mata, itaf ta dauka matarshice, batasan matan banxa bane, tayi wata dariya mugunta an samu idea ta miqe tsaye taje kitchen ta dauko man gyada, tayi zaune duk ta gogo gurin da ba carpet dashi tayis sai maiqo yake yaji oil sosai, cox ta taba zubarda man gyada a kitchen tafadi har sau biyu sai ta gane cewa yana fadar da mutum, ita kanta da tsantseni take tafiya har takai wani guri ta zauna, ba'ajimaba kuwa saiga ramcy an fito da kayan bacci kamar tsirara, tana fitowa daki tana yatsine yatsine, sai wayanta tayi qara juyawanda zatayi ta dauko wayan, kikajita teeeeem ramcy anfadi qasa ansha qasa, ta fadi saman hannunta tayi wata qara, iffat ta gyalgyale da dariya, tazo kanta tana kallonta tana dariya, ramcy kuwa sai kuka takeyi tace da bana wari Dana taimakeki Amma ina tsoron in saka miki warina ....... [3:43PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 16 Na Hauwa M. Jabo Maimakon ta dagata din amma ina sai dariya takeyi, ramcy sai kuka take tana ki taimakeni iffaat taci gaba da wa qarta ta badi barai, tayi sauri ta goge duk gunda ta saka mai,ramcy nata kiranta ta taimakamata amma iffaat kamar ma batajiba, hankalinta kwance, ramcy ta rarrafa taja jiki ta dauko wayanta ta kira farhaan ta gayamai faduwan da tayi da dariyar da house girl dinsa tamata ba'ajimaba saiga farhaan da Dr. Sunzo Dr. ya duba ramcy akace hannunta da qafarta sun targade, farhaan yaje dakin iffaat batanan yaje ko ina batanan kamar daga sama ya ganta ta chiko dan kwali da fruit lambu taje kenan, tana qarasowa ya wanketa da mari.!saida abinda ta debo ya watse, Ke dan ubanki Mara tarbiyar inace ke?? Mace ta fadi Dan bakida tausayi idan baki taimaketa kin dagataba ai bakya mata dariyaba, Dan Kinga ina gyaleki a gidannan kike abinda kikaga dama, karfa ki manta ke ba kowa bace illa yar aiki, kuma wallahi zan riqa chin ubankine, wawuya Mara tarbiya.!! Ya fada a hasale ya wuce daki gun ramcy, ranshi a bace yaci gaba da rarrashinta... ran mata ya bace ga duka ga zagin chin mutunci, ta fashe da kuka, ta fito harabar gida ta rakube wani guri tasa kanta a cikin chinya ta fara kuka, kuka take sosai cox ranta ya bala'en baci ba'ataba samun nasara akantaba irin wannan wato duk dabarar da zatayi dan ta rama abin da ya mata ta sai taji yana bata tausayi bazata iyaba, shegiyar matar ya kamata ta qara yiwa wani sharrin, haka taci gaba da kuka har farhaan ya fito zaikai ramcy asibiti ya sameta anan ya zabga mata harara ya wuce abinshi, har sukaje suka dawo tana kuka sai ta bashi tausayi yaje ya ijiye ramcy ya dawo, kewai mi kikeyi anan,? ki tashi ki shiga ciki kinzo kina ma mutane kuka, tayi banza dashi yayi yayi tun yana fada fada har ya dawo rarrashinta, har ya gaji taqi daina kuka kuma taqi tashi, ya gaji ya koma chikin gida, iffat dai ta gaji da kuka tayi bacci anan, har gari ya waye guraren 9 farhaan zaije skull yaganta anan kwance ya rasa yanda zaiyi da ita sai kawai ya dauketa a hankali yakaita Palo saman kujera ya shinfidar, ita kuma ramcy tana Palo zaune saman keken guragun da aka bata, tamai kallon tuhuma waye ka dauko, sheeeeeeee, ya dora yatsansa akan lebensa yace kada tashi, banganeba yar aikice kake dauka, yace batada lafiya, jiya sabida abinda na mata akan ki waje ta kwana. Ramcy tace then so what Dan ta kwana a waje, ya bata amsa da then so keep quiet kada ta tashi nace! Tamai kallon tuhuma farhaan ka gaya min WACE CE ITA?? [3:44PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 17 Na Hauwa M.Jabo Ya kalli ramcy kallon bangane mi kike nufiba, ya tambayeta WACE CE ITA?? Eh wace ce e ita.!! Wace ce ita kuwa bayan house girl dina, yayi guntun tsaki, ki kula kada ki tayar da ita bacci ba tada lfy, ya bata amsa ya fita abinshi, house girl ce hadda wani daukota,aranta tace yanda tasan farhaan da gyangyami ba yanda za'ayi ya kula wannan qazamiyar yarinya, yarinyar da ko qirqar danki yanxu takeyinsa. Ta gungura kekenta ta koma dakin farhan. Farkawan iffaat keda wuya taganta a saman kujera itada tayi bacci a waje taja tsaki ko wane aljanine ya daukota ya kawota nan oho? taje lanbu abinta ta nemi abinda zai qosar da ita taci ta haye wata qatuwar bishiyan mangoro mai sanyi bata dadeba ta fara gyangyadi da taga zata fado sai ta daura Dan kwalinta tayi yanda bazata fadoba. Farhaan yayi baqo kuma bayason yaga ramcy dan ba kowa yasa yana neman mataba, sai kawai ya janyoshi lanbu dama wasu takardune zasu cika tare, kusan awa uku sunanan suna aiki. bayan sun qare suna tadi suna dariya, sai kawai sukaga abu kaman ruwa saman kan baqo amma ruwan yellow ne har dai ruwan suka jiqe takardun da suka cija gabaki daya, takardun da da suka sha wahala kamin su sami signed su chika, sun miqe lokaci daya suna kallon sama cike da mamaki da tsoro coz sun gane ba ruwa bane fitsarine hadda diminsa... farhaan ne ya hangota tana sharar barchi, wato fitsarin kwance takeyi, yaja tsaki kunya da takaici suka isheshi kawai yaja abokin sa zo muje ciki, abokin yace minene?? wallahi wani hatsabibin MONKEY muke dashi, shine ya mana fitsari Dan Allah kayi haquri muje ciki kayi wanka ka chanza kaya, sai kuma ya tuna ramcy tana ciki bayason ya gantane shi yasa yama kawoshi nan ga wannan sakaran abinda ta musu, yaqara jan wani tsaki, ya zaiyi dole tasa ya bude mai dayan sashen gidan yayi wanka yadauko mai kayan sa ya saka, abokinsa yanata dariya abin ya bashi dariya matuqa yace farhaan wannan monkey da gani Dan iskane, farhaan ya murmusa ai hatsabibancinsa yafi wannan, ta ciki na ciki bayan ya sallami baqo yazo lanbu yaci qaniyarta sai kawai yayi karo da ita gefen bishiya tana wasa da qasa, abinda ya gani ya bashi tsoro matuqa idonta sunyi suntum kamar jabo tayi kuka.! Tana ganin sa ta kauda kai sai ya yazo gurinta, ya tsuguna umma tana gaisheki tace kiyi haquri zaginda ake miki,kinji tace in baki waya kuyi magana, cox yasan duk abinda za'amata taji haushi baikai a zagi margayin babantaba, yayi ta mata surutuai ko motsi batayiba bare ta bashi amsa har ya gaji ya tafi. Da yamma ta shiga gidan tasan farhaan bayanan sai ramcy zaune a Yar kekenta ta guragu tana cin Apple tana ganin iffaat tasha mur ta toshe hanci, iffaat saida taxo daidai ita ta wanketa da lafiyayyen mari, ta tureta saman kujera ta fadi, ta take qafar

Chapter 2 of 10